Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi waje daya hakan kamar zaifi."yaya kana ganin...."haka nafaɗa Zubaina bana son musu" ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu."yanda kace haka za'ayi." sallama yai mata ya tafi......yana fita ta kishingida tana tunanin ta yanda zata iya rabuwa da Umar har tsawon mako biyu bata ganshi ba tasan zata takura sosai....ba yanda ta iya tunda an nuna mata fin karfi.
★★★
Zaune yake yadawo daga karbo abinci yana shiga dakin su yafaraci ga wara muguwar yunwa tana dawainiya dashi yanda yake cin abincin kai kace bai taba cin abinci ba sai hannu baka hannu kwarya yakeyi.....koda Ado ya shigo ya iske dan na shi bai koshi ba daukar nashi yayi ya bashi,dama shi har daki akesa bayi sukawo mashi nashi saboda zuwa yanzun ya zama babban bawa ko aiki baiyi saida susa bayi aiki kuma shike zuwa ya sawo bayi idan yaga bawa baida isassar lafiya ko bazai iya muriya ba, sai su siyar su dauko wasu shiyasa wani lokacin har fadanci yakeyi kuma ba sashen da bai shiga a cikin Masarautar tsabar aminci da akayi da shi...saida Sadauki ya koshi sannan Ado ya dauka yaci yana gamawa Umar din ya tashi zai fita dakatar dashi Ado yayi"Umar zanyi magana da kai."komawa yayi yazuna"inajinka Abba"kamar yanda kasani dazun Yara Ammar ya same ni yace gobe da karfe bakwai na safe ka shirya za'a fara baka gwaji zaka zauna cikin jaruman Zairana saidai dole ka kara maida himma akan abinda akasa ka!"ɗan murmusawa yayi yace."Haba Abba ina Umar ina zama Jarumi, ina tsoron kada mutanan ne sun sani a hidimar su inzo in fadi kaga ai naji kunya Sannan na kunyata mutane masu matukar daraja.... kar su ga danna shigarma Yarima Aryan wasa rannan su daukeni matsayin wani jarumi."dariya Abba Ado yayi yace."Ummarul-Faruq kenan kai Jarumi jajircewa kawai zakayi."Abbana niba Jarumi bane ainahin yanda akeyin wasan jarumta ma ban sani ba, bare har in zama jarumi."Hmmm Umar kenan,artaba dakai kadai batare da gasa ba....dole gaban maza ya fadi balle kuma kazo a matsayin Jarumi yakamata ka dauki gabata da girman da Allah yadora maka kuma ka kara godema Allah saboda wannan ba karamar baiwa bace Allah yamaka ba...saboda haka karka kuskura kace zaka sare kazama Jarumi kuma gwarzo Allah yaimaka albarka"Amin Abba nagode da kwarin gwiwar da kake bani."
-----------------------
"Allah yataimakeka sannu da hanya"yauwa gimbiyata,ina yan uwanki."? "Gasunan tafe ranka shidade dagani ka kwashi gajiya."murmushi yai mata yace."Gaskia kam,amma gajiya tabi jiki ba kamar jiya na.....ya ya'ta Mufeedah tanata fama ko?Allah yasauketa ladiya kullun tausayin yarinyar nan na kara kamani"Amin ranka shidade,dayake tanada karfin halima."Allah Sarki, kinga da Allah yasa mijin Zubaina bai mutuba nasan da Allah yanzun naga jikana mafi soyuwa a gareni."Allah yataimake ka kadai nuna kaunar yarinyar nan fiye da kima"Aminatuna kenan, kaf Ya'yana ba wanda bana so abinda yasa kikaga inaba mamana kulawa fiye dasu kinga ita ce karama a cikin su,amma kaf ya'yana ba wanda yafi wani duk daya suke a wajena."murmushi tayi....suna cikin labari sai gasu gimbiya Bilkisu da Rukayya sun shigo suka zauna gefen mijin nasu suka sashi tsakiyar su kowa a cikin su na kokarin kyautatama mijin nata"Abban Ammar ya hanya."? "alhamdulilah...ku sanar da ya'yan ku gobe da misalin karfe goma ina bukatar ganin su a turaka,amma ba laifi idan kuma kun kunzo,amma kusani wannan zaman na ya'yana ne."Allah yakaimu lafiya."Amin." gimbiya Rukayya tafara bashi tufa yana ci daman dakin ta yake suna mashi fira su kuma sauran suka fara yi mashi tausar kafa baruwan su da mugun kishi,soyayya sukema junan su gwanin birgewa koda agaban ya'yansu ne ba ruwan su da wata kunya har sun saba saboda zuriyar Sarki Abdurrahman zuri'a ce mai hadin kai da sanin yakamata dama da Zubaina kadai yake samun sabani a cikin ya'yan shi itama wajen fidda miji ne.koda tayi auren farko yace bazai kara takura mata ba,zai aura mata zabin ta idan ya dace da ita.
sunjima suna cin abinci tare da mijin su sannan ya tashi ya shirya ya tafi wajen mahaifiyar shi suma kowa ta koma sashen ta....
___________
" tashi ki shiga wanka kinji yar albarka kinga kada ruwanki ya huce....na fahimci baki san kina wanka da ruwa mai zafi dama yaran zama ni kunfiya san jikin ku dayawa"murmushi tayi tace."Umma duk nagaji shiyasa kibari saida safe sa nayi yanzun bacci nikeji Umma."kinga zaki tashi kokuwa saina saba maki!."a shagwabe Asma'u ta tashi cikeda kasala ta shiga ban daki."salan kuma ki watsa ki fito dan nasan zaki aika."Umma zanyi Allah."ah toh nadai fada maki."Hajia Mansura ta dauki jikan nata tayi mashi wanka sannan ta shirya shi tsaf kamar ka sace shi yanda yayi kyau, da tagan shi sai taga kamar Sadauki.....
tana tayi mashi rawa Asma'u ta shigo dakin ta fara shafa mai."Umma na kedai kin fiye jida dan nan naki kamar yafi kowa"murmushi tayi tace."kinji abinda kika fada dama yafi kowa kuma kinsan sabon jini da shiga rai dole in so shi sosai kinga bari in tashi in shiga madafa inga yanda suke aikin nan kinsan yau Abban ku zai dawo dole in tsaya da kaina in girka abinci"Umma kenan, rayuwar ku tayimani....kwara akara kulamana da Abban mu."Hmm yar nema kema kinzama kamar yayan ku kenan ba ruwan shi da kunya."Umma ai dole muyi raha da iyayenmu,ba rashin kunya bane"ke daman bazaki yarda ace ga laifin da Ahmad ya yiba....bari intafi kada ki rikeni da surutunki kisa aimani ba daidai ba."Umma nima zan shigo natayaku aiki"Aaa kedai ki kulaman da jikana yafi wannan aikin lada,kindai ji abinda na fada maki ko."? "Umma dan Allah"nadai fada maki"shikenan Umma na saikin dawo."tana shiga madafa ta fara hada girkinta ita da yan aiki suna mika mata kayan bukata,sannan ta hadama mijin ta kunun Aya saboda yana son shi sosai tana gama hadawa taji an rungume ta."Ummana ina kwana."Lafiya lau sai yanzun ka fito?karfe goma yanzun fa."duk na gaji kinga jiya nabi su Kamal munyi gwaji doki,kuma kinga na rabu dayi shiyasa."ai kun kyauta yanzun kaje ga kalacinka can na ajemaka a dki "Umma na koshi banjin zanci abu mai nauyi yanzun saidai ko bakin shayi ne idan akawai zan sha"wahala taka Shattimah....wai kai baka gudun kada yunwa takama ka"?murmushi ya sakar mata yace."inda sabo na saba Umma dako shayin ma ban iya sha"lallai kam ya kamata ka dinga cin abinci mai nauyi."Shikenan Umma yanzun dai bani shayin in fara sha daga baya naci abincin"ko kaifa."dariya sukayima juna cikeda so da kaunar juna.....

Bayi ne da yawa a bakin sashen Galadima Hamza sai uban hanaya ke tashi wajen suna kiran."bamu amince da mugun zalincin da ake mana ba dole akwatar mana hakkin mu."amma kamar ba asan sunayi ba, sun kai sama da awa biyu suna abu guda sai lokacin Yarima Barde ya fito ya tsaya a sheke yake kallan su,baki daya suka nemi suyo kanshi daya bayan daya yake kallan su idanun sa suka sake dallo wata kyakkyawar baiwa....take ya saka sha'awarta a cikin zuciyar shi,gigitttar tsawa ya daka masu mai firgitarwa."waya baku damar zuwa wajen Mai martaba?miyasa zakuzo kuna zanga zanga har wannan wajen?wannan rashin sanin kimar nagaba ne!kodan kunga ana kyaleku shiyasa zaku dinga fidda jiniyoyin wuya kuna mana hauka....kamar dai kun manta ko su waye ku a Masarautar nan."munzo a kwatar mana hakkin mu akan kaika yanda kaco zarafim yar mu bataci ba bata sha ba."dariya ya sheke da ita ta shakiyanci yace."miye a ciki kamar ni Yarima Barde na shakata da diyar ku,bayan itadin baiwa ce, yakama yayi ku godewa Allah da har Barde kamar ni dan Sarki jikan Sarki tattaba kunnan Sarki kuma haifaffan Burhaan ya hada jiki danl yarku ai kun samu tabaraki."wannan zalinci bazan zamu yarda ba koda ire iren mu zasu kare sai mun kwatarma kammu 'yanci."wani bawa ke fadan haka.
"Kai darwami,kawo mani waccan baiwar ka kai mani ita sashena yau zan gwada masu karshen tasha."
ba tareda bata lokaci ba darwami ya damketa yafara janta baki daya bayin nan sukayi kanshi suma suna janta ga Sarkin bulala na dukan su kamar jakuna haka sukaita wulakanta su, aduk suka karaya yanda sukaga ana dukan su kamar za'a kashe su, Hamza ne ya fito cikin bangaren nashi a matukar kufule kana ganin shi kasan ya gama fusata da kama darwami mummunar tsawayi har saida suka firgita yace."karka kuskura ka kara jan yarinyar nan kasa ba kada hankali ne? zaka dinga jantabaceman daga ni idan ba haka ba zaku sha mamaki.A sanyaye suka wuce shima darwamin tafiya yayi."sannan ya koma kan bayi yace"ku kuma daga yau na kawo karshen wannan zanga zangar da kukeyi a cikin Masarautar nan!idan ba haka ba walahi ni nan Sarki Hamza saina karar da ahalinku kaf!ku baceman da gani tunkan dare yai maku marassa mutunci ni zaku wulakanta?ku a suwa zaku dinga ja da karfin iko da izzata har kun isa kuja da karfin mulki irim na Sarki Hamza kuna bayin? idan kuna gani kuna takama da shakiyanci ni zan gyara maku zama a cikin Masarautar nan dan haka ku kama gabanku tun muna shaidar juna! ke kuma uwar bayi da kai shugaban bayi daga kanku zan fara nuna misali."baki dayan su duk suka tsaya cirko cirko....Sarkin horo kasan abinda ya dace dasu."rufe bakin Hamza keda wuya ya farmasu da duka da halbi cikin kankanin lokaci dogarawan sa suka masu ruf da bulalu.tunda Hamza yabada umurni yakama gabansa ya shiga cikin turkar shi......


*Ku hanzarta ku mallaki naku domin wannan tafiyar ta dabance,na tabbata bazakuyi dana sanin siyen sa ba,kunji salon Izzah ko Mulki to yanzun wasan zai soma domin ba'ayi komai ba,kedai ki kasance da Jamila yar mutan kankia😍*


_Yar Mutan Kankia ce❣️_


Share
Pls

*SADAUKIN BURHAAN*
_(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_
A Kingdom Story👑

*NA*
*JAMEELA JAMEEY*
_(Ya'r Mutan Kankia)_

*BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM*

_KARSHEN SHAFIN KYAUTA_

BABI NA SHA ƊAYA

Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300) Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.shaidar biyan ki ta wannan number 08160508316.

*BURHAAN*
shigar shi dakin keda wuya ya sake wanke Barde da mummunan mari....ransa na matumar kuna da tarin bakin ciki lullube a cikin kokon zuciyar shi isakar bakinsa mai tsananin zafi ya fesar yace."tir da kai Abbas kabani kunya!bantaba zaton haka kake ba ka keta rigar mutuncina da ta martaba ta agaban BAYI kake wulakanta kanka da kanka kana ɗan Hamza!amma ka maida kanka wawa sakarai idan kana bukatar hutawa da waccan dakikiyar jakar baiwar har sai kabari wani ya sani balle kasa aka ma maka ita da karfi ashe kai wawane ban sani ba baka da fikirar da zakayi amfani da ita bazaka iya anfani da mulkin ubanka ba amatsayin ka na Yarima Barden Burhaan kuma mai jiran gadon karagar mulkin wannan Masarautar! shine zaka zubda girman ka da darajar ka gami da kimar ka tir da kalan halayen ka kabani kunya kuma kayi asara!"haba Mai martaba kawai dan na nemi baiw....sake wanke shi da mari har saida sauran zantukan sa suka tsaya cak a cikin bakin shi"ka kuskura nakara jin bakin ka billahilazim saina baka mamaki!duk iskancina da tijarancina bana bin mata!...kagan ni nan ni ba sakarai bane kuma ni jajirtacce ne kuma jarumi gwarzo banda tsoro ko kaɗan, kuma ni da kake gani na ina san girmana ban yarda araina ni ba! sai kai shashasha! kana da'na na jinina zaka zama sakarai! gaka dai da sunan Jarumai amma kwara sanhwami dakai kayi asara Abbas...kash kaicona wai ni BAYI zasuyi ma bore duk saboda kai Abbas! Badan komai ba saboda na haife ka,saidai kai bakasan allanka ba saboda baka iya wanke saba."kayi hakuri Abba."kayi gaggawar barin wajen nan idan ba haka ba saina baka mamaki shashasha dakai!."sadda kansa Barde yayi yanajin yanda mahaifinsa keta faman fada ta inda yake shiga bata nan yake fita ba.
Masa'uda ce tafe cikeda kasaita gamida izzah ga tunkaho tanayi saman hanya kana ganinta zakasan kalar farin cikin da takeji tsabar dadin da takeji ganin bayi nayima Hamza bore....tana shawo kwanar da zata sadata da sashen Galadima Hamza ta hangi Sarkin horo na dukan bayi kamar wasu jakai da sauri ta karaso bata san ta dakama shi tsawa ba ta nunashi da yatsarta manuniya."Karka kara dukan su! mamugunta azzalimai bayan kun gama zalintar su shine zaku bisu da duka."Allah yataimaki gimbiyar Burhaan...dama Sarki Hamza ne yasaka ni"batacemin daga ba Hamza ko Abduljalal ne! na haramta duk wani zalinci wuce kabani waje tunkan na saba maka."da sauri yabar wajen shi da 'yan ta wagar shi.
Ɗago uwar bayi tayi tanajin tausayin su cikin sigar tuggu da munafunci tana basu hakuri,sannan tasa suka koma sashen su."Kubar komai a hannuna zan neme ku da kaina."mungode Allah yasaka da alkhairi."Amin."da haka suka tafi....banda kallan harara ba abinda take masu ga mugun nufi da kudure kudure cike a cikin zuciyarta....
cikeda gadara ta shige sashen Hamza."bazaka wuce kabar man waje ba ko sai ranka ya baci."kayi hakuri Abba natuba kayafe....tafin da sukaji anayi ne ya dakatar da Barde daga maganar da sukeyi baki dayan suka waigao sukaga Masau'da tana ta murmushin mugun ta tanaci gaba da tafin da takeyi a hankali take tako har zuwa gaban su."Hmmm Hamza kenan!manya manyan Burhaan ashe har wasan namu yakai haka? Tunkan tafiyar tai nisa harka soma marin d'an ka bayan gorin dakake mashi ashe kaimakasan shi din mazinaci ne lallai Hamza! Ashe hat kafara sarewa! hhhhhh."ta kece da matsiyaciyar dariya har saida illahirin falon ya dauki karar dariya taci gaba da cewa."ni jikanyar Usmanu! gaskia wasan nan nayi mani kyau iya kyau komai yayi....Hamza karka manta yanzun akara fara wasan! muddin kace zaka watsar da Masa'uda bazaka taba jin dadin zaman duniya bare kaji dadin rayuwar Burhaan."gelele haka Hamza kebin Masa'uda da kallon mamaki da al'ajabi."abin kunya wai yau BAYINE kema Galadima Hamza bore duk a cikin Masarautar nan! Hahahhha gaskia kabani mamaki daka kasa hukunta d'an ka kodan gujewa mulkin fadawa halaka nasan bazaka so karagar mulkin Burhaan tafi karfin ka ba."banda idanu da ya iya zubawa Masa'uda har yanzun ya gaza katabus mamaki da al'ajabin ta kawai yakeyi ba dan baiyi zaton bazata iya yi masa haka ba yasan abinda yafi hakan ma zata iya yi masa kawai yana mamakin kalar Jarumtar ta ne...."wayyo har kabani tausayi kanin Abduljalalu kamar ba kaiba.....duk takama da girman jurerar mulkin a haka?hmmmm karka damu Hamza,komai zai wuce kai dai kayima yayarka Gimbiya Masa'uda biyayya ko kasamu karbuwa a cikin Masarautar Burhaan kada zauna da Mulki amma ba mutane kaima kasan aikin banza ne,Jama'a itace ɗan Adam komai girman sa ko mulkinsa mutane sune rigar mulki."wani irin takaici ne ya tokare kirjin Hamza jiyayi kamar yai kwalla idanun sa sun koma kamar jan gauta a zahiri sai ya wayance ya kece da mahaukaciyar dariya saida yayi mai isar sa sannan yace"hahahhhh....Masa'uda kenan..!"tafa hannayen sa yayi saida suka bada sauti n gaske sannan yafara zagayeta cikeda izzah yaci gaba da cewa."sirri sirri!duk abinda kikeyi a tafin Hamza kike kema kinsan haka! Kar nike kallan ki a cikin Burhaan....hmmm karki manta na iya wanke allona kuma na sansa sannan ina ankara dake lokaci na dibar maki.kigama shakiyanci ki da kike ikirarin da'na ya nemi baiwa kisanu isa ce tajawo hakan!kalle ni da kyau Masau'da kika kuskura kikace zaki kara shiga sabgata hmmm! harkin bani tausayi....sannan na haramta kalmar yayata a bakin ki idan ba haka ba saina datse tsinnan harshen ki ko Abduljalaal dakike gadara dashi na girmi wannan a halin yanzun bare ke shashasha baki isa kija da Sarki hamza ba ki kama kanki."
"Hmmm da gaske? sarki sarki,su Sarki manya! yaushe aka fige bare a sha roman??? waya shaidaka a matsayin Sarkin? kace dai Galadima Hamza mai rikon kwaryar mulkin Burhaan kanin Sarki Abduljalal."tayi maganar tareda wani irin shu'umin murmushi mai dauke da ma'anoni....."ballagaza shashasha idan ana maganar mutane wake sakoki? wai har kinsan dadin miji? bayan ke da kanki kika cuceshi sannan kika jefa shi cikin musiba da bala'i? Hmm nafahimci cacar baki da jaka kamarki lallai kam ba karamar asaraba ne a wajen Hamza! Sannan da kike takama ni ba Sarki ba ne to kisha kurumin ki saura kiris dubatan mutane su shaida Sarauta ta,jahila kece kanki ke cikin tukunya” waro idanuwanta tayi woje tsabar razana da kalamin sa tana mai cewa“ni kake fadama kalmar jahila?."
"Bace min da gani tunkan in baki mamakin da bakiyi zato ba! Sakara aura ka jakar mata ballagaza wadda batasan kimar kanta ba ki rubuta ki aje saina gyara maki zama a cikin Burhaan"zazzafan iskar bakin ta ta fesar tana huci tace."Mu zuba mu gani ni da kai shege ka fasa"
"Ke malama da kata karki kuskura ki zagi mahaifina matukar tsautsayi yasa kika zage shi saina wanke ki da mari"iyyeh ɗan karamin ɗan iska! Yaushe daren yayi bare garin ya waye kul! Na haneki artaba sa gimbiya Masa'uda ba dadi yaro ko tsohonka ya ya iya dani bare kai karen kaɗa miya! karka kuskura da uban ka nikeyi! ko uwar ka Uursiyyah bata isa inyi da ita ba bare kai! kaga wancan aura kan? jakin mazan? toh da shi nikeyi bakai ba,dakiki mazinaci....."ya daga hannu zai wanketa da mari kenan,Hamza ya hana shi."kyaleta Barde dani take wasan! kai dai ka gujema idanun mujiya...zaki iya tafiya jahila,marar 'yanci."Kayi magana mai anfani Hamza dani kake zancen."
tana fita ya dawo kan Barde"kaga irinta ko Abbas?Masa'uda da kake gani bakaramar shaidaniya bace,ita din makirace ajin farko ka kiyayeta! Kabani kunya bakada amfani agareni ni koda nayi tashen hatsabibin cina banjama uba na zagi ba sai kai! da kimata ni Hamza Muhammad Abduljalal ni ake gayama magana irin wannan duk saboda kai! kaskantattun bayi na suyi mani bore duk saboda kai! gaskia kayi asara walahi saina hana kowa motsi cikin Burhaan."Abba kayi hak...."ɗaga mashi hannu yayi a fusace tareda rufe idanunsa da yakejin su kamar zasu fado kasa tsabar zafin da suke mashi yace."Kai Barde karka kuskura kabari in bude iduna na ba tareda kabar wajen nan ba baka da anfani agareni! Kana nufin a haka zamu dauwama a mulkin Burhaan ɗin?kana ma ya'yan mutane fyaɗe? a haka zaka amsa sunan yarima mai jiran gado?.......Hmm,ba'a Yarima ɗan iska! haka kaga Yarima Sadauki nayi? ga aji ga kasaita,ga tarin haiba,banda miskilancin shi mai aji ga tarin izzar mulki uwa uba kyau da Jarumta wani abun sai amale Sadauki yayi a rayuwa! Sannan shidin mai kishin ubansa ne banda zuciya bai son raini uwa uba shidin mai tarin ilimi ne komai ya gama hadawa ina ma ace ni na haifi Sadauki lallai kam da nayi takama a nuna gadara,a cikin dubatan mutane, sai dai kash ashe wawa sakarai na haifa marar hankali"Abba kadaina ai baitani har haka dan Allah"dallah bacemin dagani malan ni da kake gani ina da kishin kaina dana 'yan uwa na, bacemin da gani!" ba shiri Barde yafita cike da bakin cikin kalmomin mahaifin shi.....

*Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari ukku kacal,Acct details 0777512438 Access Bank,Jamila Abubakar Bello.Ku tura shaidar biyan ki ta wannan no 08160508316.*

Kwance take saman tafkeken gadon ta wanda yasha ado na sarauta sai tunani takeyi,hawaye keta zirarowa a gafen idanunta ba abinda yake taba mata zuciya yanda Ammar ya rabata da bawanta Umar ta karfin iko,lamarin ya taba mata zuciya."bazan tata iya hakura da rashin Umar agareni ba,taya za'a rabani da shi dan Jarumi nima saboda Jarumtar shi nike son shi,bazai taba yuyuwa dole inyi magana da Mai martaba."hawaye dake ziroro mata sukaci gaba da sauka saman kuncin ta.
Fadila keta faman yima Zubaina Sallama sam bataji taba har saida ta tabata sanann ta dawo firgigi cikin hayyacin ta"Fadila ke ce,yaushe kika shigo ban saniba."? "Allah yataimaki gimbiya ra na dade da shigowa baki jini bane...Allah yasa dai lafiya."?ajiyar zuciya ta fesar tace"Bakomai."murmushi ta saki tace"har na samu sassauci a cikin zuciya ta,farin cikin ki shine nawa gimbiya ta Allah yabaki nasara....daman gimbiya Bilkisu tace in fada maki,Mai martaba nasan ganinki a sashen shi yanzun yanzun."a tsorace ta kalli Fadila duk da bata bari taga karayar ta fili ba tace."ko lafiya."? "Allah yataimake uwar gijiya ta, ina ga kamar ku duka yake nema...saboda na ga Raliya ta shiga sashen Yarima Aryan shima sakon Mai martaba ya riske shi,Allah ya karamaki tsawancin kwana yaka mata kitashi bansan inga ana jiran ki."banjima da tashi daga bacci ba,naso insake shiryawa sannan"wannan girmanki ne,saidai baki da wata atattare dake kamar yanzun kika gama shiryawa kinyi kyau kuma dama ke din mai kyau ce, kibari idan kindawo saiki sake siryawa."toh Fadila yanda kikace haka zakiyi"nagode da karamci uwar dakina ga alqabbar ki."saina dawo"Allah yatsare hanya......Allah yataimaki uwar ɗaki na mikike bukatar a dafa maki."? "kisa ahaɗa mani farfesun kifi."angama ranki shidade saikin dawo."tana fita bayin daketa fama da aiki suka duka sai gaisheta sukeyi amma ko kallo basu isheta ba wasu kuma ta daga masu hannu harta isa wajen Mai martaba. Bayan sun amsa mata sallama ta samu waje ta zauna kusa da Yarima Aryan sannan ta gaishe dasu cikin girmamawa kowa ya amsa.
"mama na miyasa kullin idan zanyi zama daku kece karshen zuwa kin cika shiririta"Allah yabaka yawan rai aimin afuwa ban dade da riskar sakon ka ba,amman ayimin afuwa"bakomai ya'ta matso kusa da Abban ki."matsawa tayi kusa dashi ta zauna."yasa hannunsa gefen fuskar ta ya shafa a hankali yace."Allah Sarki da yanzun ya'ta Mabaruka tana nan tare daku...Allah yaimaku albarka"Amin Abba....sannu da dawowa."yauwa,ya'yana abin alfaharina ina fatan kuna lafiya."? "Lafiya lau Abba."gyaran murya Mai martaba yayi yaci gaba da cewa."godiya ta tabbata ga Allah daya hadamu baki dayan mu a wannan waje....dalilin dayasa nasaka a kira mani ku ina son in isar maku da wani muhimmin sako munyi zama da manyan Sarakuna masu girma kamar yanda kuka sani da ance za'a gabatar da Gasa a Masarautar Kesar....saidai Sarkin Sirika ya nemi alfarma akan ayi shi a Kasar shi kuma za'ayi tsawon sati daya acan amma kwana biyar za'ayi ana wasan idan Allah yakaimu.....Ammar kaida dan uwan ka kune jarumai na yana da kyau ku jajirce sosai fiye da tunanina kuba jaruman ku horo na musamman fiye da Da......kunga yanda Jaruman Burhaan suke da jajircewa,har yanzun kaf Masarautun nan banga kamarsu ba, ina son kusani suma an aika masu da gayyata nasan zasu zo duk da Sarkin su baizo zaman da mukayi ba nasan dai akwai dalilin rashin zuwan shi,kuma shi aka ba shugaban taro."Allah yataimake ka, kace a wannan karon zamu hadu da Sadauki kenan."insha Allahu haka muke tunani."ranka shidade.....insha Allahu zaka samemu da jajircewa akan aikin mu"Allah yasa,ina alfahari daku Allah yaimaku albarka"Amin ranka shidade."
Maida dubansa yayi ga Zubaina dake fa faman wasa da zoben gold daketa walauniya saman yatsan ta yace"ya'ta."? "na'am Allah yakara maka tsawon rai"sako daga Sarkin Sirika,yace in gaishe ki sosai sannan yace idan za'aje gasa inje mashi dake,ko kina bukatar zuwa."? "ina amsawa nagode da karamci....eh Abba ina son zuwa"shikenan mamana Allah yakaimu lafiya."Amin."
"haba ranka shidade da ita za'a tafi?mace ce fa."? "Aminatu kenan,minene a ciki? yana da ɗiya fa ga gimbiya Rahama zasuyi kawan ce"shikenan Allah yakaimu da rai da lafiya"Amin."sake gyara kishingiɗarsa yayi yace."Babban dalilin kiran ku,akan bawan nan ne Umar."wani irin mummunan faduwar gaba ya doki zuciyar Zubaina har saida ta tafe kanta daurewa kawai tayi har saida Umman ta ta kalleta da alamar tambaya....tayi saurin sunkuyar da kanta a kasa jikin ta yai sanyi sosai." ban laminta da zaman shi cikin Masarautar nan ba....raina nabani akwai wani babban al'amari atare da yaron nan! anya ainahin bawa ne shi? kai da wuya."Ranka shidade...."yimin shiru Ammar ban baka damar magana ba"Allah ya huci zuciyar ka."ya sadda kansa kasa."dan haka inaso akira mani Ado yabani tarihin sa."rufe bakin sa keda wuya sai ga Abdussalam ya shigo da cikin so da kaunar junan su suka rungume juna ya zauna gefen dan uwan na shi....duk suka gaishe da Baffan nasu cike da girmamawa.." "ban laminta da Umar ba bana bukatar saman shi cikin Zairana."Allah yaimaka yawan rai ayi mani izinin magana"ba damuwa Abdussalam zaka iya magana."duk da yanzun na riski tattaunawar ku amma ya kamata kabi abin nan a hankali,kwanaki nasa ankira mani Ado na zauna dashi a fa'da duk saboda Umar yafadaman abinda yasani akan shi, lallai Umar bawa ne ya siyoshi a kasuwar gobir bayan jajircewa da yayi akan siyan shi wanda ya tadda

Please Login or Register in order to submit comment