Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abinda kike bukata."ba abunda nike bukata ranki shidade." suna fita bayin da za'ayi tafiyar dasu suka rugo da gudu suka kwashi gaisuwa sannan suka daukar mata kayan ta,suka tafi sashen Mai martaba,saida ta shiga wajen Hajia ta tayi mata sallama sannan ta wajen gimbiya Bilkisu can ta iske gimbiya Rukayya tareda yarima Ammar sukayi masu ban kwana sai zolayarta sukeyi."Allah yasa kuje lafiya ku dawo lafiya."Amin."suka amsa rakkiya sukayi masu suna shi masu albarka.
Baki dayan suka fito basu jima da fitowa ba suka kama hanyar tafiya Masarautar Sirika.
★★★
Sarki Abdulbasit Abdulkarim zaune cikin Fa'dar shi ya tara baki daya hakiman shi bayan kowa ya hallara yai masu bayani akan sakon gayyatar da Masarautar Sirika ta aiko masu,sannan ya nuna masu anfanin zuwa wasan yaci gaba da cewa."saidai ni yace masu zanyi tafiya mai matukar mahimmanci,saidai na umurci ko wane Hakimi a cikin ku,kuda Jarumai ukku ukku a kowace shiya sannan ina so zuwa gobe za'ayi wannan tafiyar."angama ranka shidade Jarumai sun karbi gwajin daya dace Allah yakaimu lafiya."Hakimin Sumani shine zai wakilci wannan tafiyar,ina maku fatan alkhairi."godiya sukai mashi,sannan yasa Sarkin Taska yaba Hakimin Sumani kudi masu yawan gaske saboda suyi guzuri,sannan ya hadasu da Dawakai masu nagarta da aminci,baki daya suka kama mutun talatin zasuyi tafiyar duk da bayin su,fatan alkhairi Sarki Abdulkarim yai masu suka tsaida lokaci da misalin karfe takwas na safe zasu dauki hanya.
___________
tunda aka aiko da sako Sarki Hamza yarasa yanda zaiyi da ranshi ga Sarki Abduljalal baida lafiya kuma yasan Sarakuna na bala'i bashi matsayi da mahimmancin gaske kasancewar shine Sarkin
Sarakuna...yasan matukar suka samu labarin rashin lafiyar shi,tabbas zasuyima Burhaan tsinke dan su nema mashi magani, idan ko har ya kuskura sukazo lallai asirin shi ya gama tonuwa,kuma yasan kashin shi ya bushe,abinda yasani bazai taba bari susan Abduljalal bai lafiya ba."matsiyacin gashi yaki mutuwa saboda taurin rai irin nashi."ya fada yana kaima iska duka."babban kuskuren dana tafka yanda ba kama rabi da kwatar Jaruman Burhaan na daure su gidan yari baccin haka da sai in tura su sannan sai insa Shamaki ya wakilce su."ya fada kamar wani zararre yace."ba yanda zanyi saboda duk wahala tasa sun lalace,matsalar daya kowa ne Sarki so yake yaga Sadauki dan iskan yaro,idan ma na data su sunje zasu ce ina Sadauki?ya akai baizo ba!kuma na tabba yanda 'yan Masarautar nan basu sona tsab zasu tona mani asiri suce munyi mashi kurciya yabi duniya! nasan daga ranar asirin mu yagama tonuwa yanzun minene mafita."? Shi kadai keta surutan shi kamar zararre ba abinda yake nema sai mafita yanda zai sanar dasu baida damar zuwa wasan da za'a gabatar....ranar dai haka Hamza ya wuni yana neman mafita saidai yakasa samarwa kanshi mafita.da haka yakoma fa'da yakira magatakarda yasa aka mai dawa Sarkin Sirika amsa sannan yasa aka kira mashi dan aiken da aka aiko mashi ya bashi takardar sannan ya hada shi da guzuri harda kudi masu nauyi saida ya bashi da haka yakama hanyar komawa gida.
tafiya tayi nisa gasu Umar har sun kusa shiga kasar Sirika baifi awa biyu ba sukai,waje suka samu suka yada zango da gudu Idris ya iso ya rikewa Zubaina sirdi ta sauka,cikin kankanin lokaci bayi suka fara hada abinci kafin wani lokaci aka fara raba abinci aka bawa.
Zubaina dasu Ammar sai Mai martaba zaune a masaukin da aka tanadawa mahaifin su kafin su huta suci gaba da tafiya,Umar yakawo masu abincin cike da girmamawa ya duka ya aje masu sannan yakai gaisuwa wajen Mai martaba,ya ansa cike da annuri,nan ya gaishe da su Ammar suka amsa sannan ya aje masu abincin cike da da'a, shidai Sarki Abdurrahman na mamakin Umar yanda yake gabatar da ayyukan shi,kamar wani dan babban mutun cikeda nutsuwa bayan ya gama kawo masu abincin su, sannan ya koma wajen Abba Ado sukaci nasu a tare sannan kowa ya gama suka kara hutawa bayan sallar la'asar sukeyi sallah lokacin rana tayi sanyi sukaci gaba da tafiyar su cikin aminci.....
___________
"Godiya zakuyima Allah daya sake hada fuskokin ku a wannan lokacin...farin ciki shine ya dace da fuskokin ku bawai kuka ba."insha Allahu Umma."yawwa,kuyi sauri ku fito ina jiran ku Allah yaimaku albarka."amin Umma."suka amsa baki dayan su.Wanka Shattimah ya shiga ba tareda ya kuma cewa komai ba.harya shiga ban daki ya rasa gane kukan mi yakeyi na murna ne ko akasin haka...koda Shattimah ya fito murmushi ya sakarma Tafidah ji yake kamar ya hadiye shi tsabar kaunar da yake mashi a matsayin shi na ɗan uwan shi wani irin shauki da kaunar juna ke fisgar su sai suke gani kamar a mafarki haduwar data zame masu ta bazata kallan juna kawai sukeyi kamar masu baki."Tafidah..Shattimah"suka ambaci sunan juna atare baki dayan su suka saka dariya suka sake rungume juna cikeda so da kauna,zama sukayi gefen gado kowa da abinda yakeji a ranshi"kaga yanda ka koma?nayi kewarka dayawa kullun kana cikin zuciya ta"rike hannun shi Tafidah yayi yace."nagodema Allah daya sake hadamu cikin aminci Shattimah ina Ammi?ina Mai martaba?ina Juwairiya?ya labarin Asma'u."?a jere ya jefomasa tambayoyin ya kafesa da idanunsa yana jiran amsar sa."share hayawen da suka zibo masa yayi yace."ka gafarceni Mukhtar nasan nayi maka laifi."laifin me?bakaimin komai."akan na tseretar da rayuwar Asma'u na baro Ammi da Abba,Juwairiyama bani da labarin su."ajiyar zuciya ya shide mai nauyin gaske yace."ina sonka dan uwana kaci jarumi ko nine abinda kayi shi zanyi kasani ina tareda kai duk wuya duk runtsi."tare suka fito wajen Umma hannun su sarke dana junan su.da salama dauke abinki su basu iske kowa ba sai Asma'u da Halimatu suna fira sai dariya sukeyi abunsu,sallama suka sakeyi a karo na biyu,Asma'u ta dago kanta ta amsa masu sallamar take idanuwan su suka hudu dana Tafeedah a kidime irin kidimar dake nuna tsantsar maki a saman fuskar ta, ta mike tsaye har jikinta yadan hau kyarma tsabar mamaki sai take ganin kamar abinda take gani a gaske ne kodai mafar ki takeyi shima kansa anasa bangaren haka yake yana cike da al'ajabin ganin Asma'u duk dayasan Shattimah ya taho da itaba saida bai tsammace ta nan din ba."Tafeedah kaine?kodai mafarki nikeyi."Murmushi ya kirkiro yalwatacce yace."Nine ba mafarki kikeyi ba."girgiza kanta tayi alamun bata yarda ba ta dubi Shattimah dake ta murmushi tace."Ya Ahmad dagaske ne Ya Mukhtar ne."? "haba dai kanwata,ki kwantar da hankalin ki mana abinda kike gani gaskia ne....Tafidan Sadauki ne dai wanda kika sani aminin Shattimah masoyi ga Juwairiyyah,yaya ga Turaki shi ne dai."ajiyar zuciya ta shide sannan ta saki wani irin kuka mai tsuma zuciya dur kushewa kaaa tana kuka,Halimatu ke bata hakuri itama hawayen takeyi.
Hajia Mansura ce ta fito da sauri ta iso wajen su ta daga Asma'u tana bata hakuri,dan tasan babban abinda zai sata kuka ba wani abu bane illa mijinta data tuna tasan da ya na nan tabbas yana tareda da abokansa kuma aminansa yau gashi ta gansu tare da juna bashi...tajima tana lallashin ta kafin ta daina kukan da takeyi."Ashe rabon rai kanga rai."Jamil ya fito daga dakin shi yana murnar ganin Tafidah."Jamil manya dan kanina ya girma."kwarai kuwa Mukhtar kaga dai yanda ya koma."Sannu da zuwa Abba."yawwa da'na ya hanya."Alhamdulillah."baki dayan su suka runguma suka zauna saman katon kafat shimfide anjere kayan abinci akai da kayan marmari iri iri kowa ya zauna duk wanda kagani a cikin gida zakaga yanda suke cikin farin ciki,suka hau cin abincin su cikin farin ciki da jin dadi.
Suna gama cin abinci aka hau fira kowa na maida yanda akayi,Lami ta dauko Amir ta kawoma Umma ce ta."Hajia ya tashi."af kinga murna tasa na manta da angon nawa."ga dan ku."ansar shi Tafidah yayi ya kwantar da shi jikinsa yana jin kaunar yaron har cikin zuciyar shi kallansa kawai yakeyi ba abinda yake gani a jikin fuskar yaron sai Sadauki."Allah gwanin yau nine rike da jinin Sadauki Allah Sarki." hawayen farin ciki yaji sun shido mashi da sauri yasa hannu ya share."Allah yarayaka bisa tafarki madaidaici."Amin."suka amsa,yana karajin son shi da kaunar shi har cikin zuciyar shi."kawo Amadun ka huta."Murmushi yayi yace."Umma ban gaji da daukar shi ba."toh shikenan."wasa ya dinga yima yaron yana karajin tsantsar son shi,sun jima suna fira, kiran sallar da akayi ne ya tada su daga firar da sukeyi sannan ya mikama Umma suka tafi masallaci.

_SIRIKA_
Tamkan take da yan Adam anata hada hada ba abinda akeyi sai tarbar baki kamar ba gobe ba abinda sukeyi sai murnabaki keta zuwa daga ko ina na kasar da sassa daban daban na duniya ba abinda Sarki Abdullatib keyo sai basu masauki mai kyau da tsari,Sarkin shela ke sanar da isowar Sarkin Kesar bakaramar murna Sarki Abdullatib yayi ba da kanshi yaje ya tarosu cikeda farin ciki baki daya suka dunguma suka rakasu masaukin su.ranar haka suka wuni suna tarar baki ta ko ina.....



_Yar Mutan Kankia❣️_


*SADAUKIN BURHAAN*
_(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_
A Kingdom Story👑

*NA*
*JAMEELA JAMEEY*
_(Ya'r Mutan Kankia)_

*BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM*

_SHAFIN KYAUTA_

BABI NA SHA TARA

Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300)Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.shaidar biyanki ta wannan layin 08160508316.

Sun iso Kasar Sirika da misalin karfe hudu na yamma basu wani bata lokaci ba suka dauki hanyar shiga cikin Masarautar kai tsaye, saidai duk motsin da Umar zaiyi yana cikin idon gimbiya Zubaina baki daya ta mayar da hankalin ta rankata kaf akan sa tana alkinta abubuwa da yawa atare dashi babban abunda ta fahimta shidin mutun ne mai kirki mai tsananin girmama na gaba dashi....yar tafiyar nan da sukayi tare takara ganin kyawawan dabi'un Umar da girmama mutane ka tawadu'u bai damu da komai ba ya rike matsayin da Allah ya kaddara mashi na BAWA.wannan itace babbar dabi'ar dake kara burge gimbiya Zubaina ga Umar takara yarda da yanayin sa na rashin son yawan magana da hayaniya shidin mutun ne ba bai shiga harkar kowa.Batayi aune ba taji anata uwar shela tun daga nesa aka fara sanar da isowar mutanen Zairana.
Yayin da Jaruman Sirika ke tsaye bakin kofa suna jiran isowar su cikeda farin ciki suka taresu sai murna sukeyi cikin kankanin lokaci Sarkin Sirika da sauran Sarakuna wa'anda suka rigasu isowa suka fito suka tari Sarki Abdurrahman cikin karramawa da tsantsar girmamawa cikin kankanin lokaci labarin isowar mutanen Zairana ya karade illahirin Masarautar kai tsaye sashen baki aka nufa dasu aka basu masauki mai kyau da tsari wanda ya dace dasu aka warema kowa da'irar shi dama wajen Jarumai daban,gimbiya Rahama ita ta tari gimbiya Zubaina tasa bayin ta suka kaimata kayanta dakin ta,sannan ta hada Fadila da babbar baiwar ta Murjanatu haka suma sauran bayin da akazo dasu masauki uwar bayin Masarautar ta basu,sai murna sukeyi abin dai sai wanda ya gani.
Shi kanshi Umar masaukin su aka basu,a cikin manyan bayi ya zauna tareda Abban shi.ranar har marece baki aketa tara daga sassa daban daban na duniya musamman lardin Afrika.
danko mutanen Roowan suma sun iso kuma anbasu masaukin su mai tsari da nagarta,su kuma Hakiman da sukazo masaukin Sarki Abdulbasit akaba su aka mutunta su yanda ya kamata bada jimawa ba yan Masarautar Yurii suma sukazo suma aka karrama su cike da girmamawa da karamci,shima Sarki Kabir Usman yayi farin cikin haduwa sa yan uwa shi Sarakuna.
Koda gimbiya Zubaina tagama wanka ta sake kayadoguwar riga marar nauyi ta saka saboda duk ta gaji sabili da tafiyar da suka kwasa mai nisan gaske.
gimbiya Rahama ta shigo dakin da Zubaina ke ciki tsaye tayi tana mamakin kallan halittar da Allah yaima Zubaina tana al'ajabin kallar kyau da take dashi wanda ganin ta yafi jinta yanda ake gayawa mata wacce gimbiyar Zairana sai taga kamar masu bada labarin ta suna karage mata kyawunta gani dai ya kori ji inji malan bahaushe.duk da ada da takejin labarin kywunta sai take ganin kamar harda zuzzutawa saidai yau takara yarda da ganin Zubaina yafi jinta,Allah yayi halitta dole ake saka gasa akan aurenta saboda ta cancanta....ɗan gyaran murya tayi sannan ra kumayin sallama a hankali gimbiya Zubaina ta juyo ta kalli gimbiya Rahama sannan ta dan saki murmushi a saman fuskar ta saidai ba lallai bane ka gane tayi shi a hankali gimbiya Rahama ta karaso ta zauna saman gado fuskar ta dauke da murmushi,itama murmushin tayi mata,sake yimata sannu da hanya tayi sannan tasa aka shigoma da Zubaina kayan abinci masu dadi da tsari na alfarma."ga abinci kici kafin mu kara gaisawa,angaishe da gimbiyar Zairana"ina godiya gimbiyar Sirika ki huta lafiya" dan rausayar da kanta tayi tace."Allah yasa nabarki lafiya."
_______________
Koda dare yayi ranar su Shattimah basuyi bacci baki dayama basujin baccin fira kawai sukeyi duk abinda yafaru saida Shattimah yafadama Tafidah komai duk daga farko har karshe ba abinda yakeyi sai kuka suna kara tausayin Ammi da Mai martaba aran su dan lokacin da Tafidah yabar Burhaan abubuwa basu cabe da yawa ba kamar yanzun." ina son insan wane hali kabar Juwairiyyah? gyada kansa yayi ya numfasa yace"Gaskia tana cikin hali bata da wani gata tunda nabar Burhaan da Allah suka dogara shine zai masu gata saboda har dukan ta Barde keyi saboda yakasa samun ta a ya'mace shiyasa ya dinga gana mata azaba iri iri daga karshe na maidota wajen Mai martaba ba irin bala'in da ba'ayi ba nida su Hamza,ana nan naji su Hamza sunyima Asma'u mugun tuggu da surkulle zasu kashe Asma'u cikin dare,a daren ranar na gudu da Asma'u.....yanzun haka Ahmad baida cikakkar lafiya sihirin da suke aiko mata ya jefe shi yanzun haka magani nike nemar mashi"Allah Sarki abin gwanin tausyi.kayi kokari matuka ka taimaki zuri'ar Sadauki ka zama dan uwa na rufin asiri a Allah yasaka maka da alkhairi."amin."ni kaina bansan dame zan gode maka ba,Allah yabar zumunci mai dorewa"Amin...yanzun abinda nikeso mu samu lokaci mu koma Burhaan"Nima abin da nike so kenan yaushe zamu koma."? "Zamuyi magana da Umma komi kenan kaga sai mu shirya muje ba zato ba tsammani."Allah yakaimu."Amin."
KASHE GARI
Gimbiya Rahama ta shigo wajen gimbiya Zubaina a lokacin da ta iske ta har Fadila tagama tayata shiryawa ta sha kyau cikin wata doguwar riga ruwan hoda da ratsin sararin samaniya sai alkabbar itama ruwan hoda ce(pink) duk wanda yaga Gimbiya Zubaina bako shakka zaiji ta burge shi ita kanta gimbiya Rahama saida ta yaba kyaun da kawar tata tayi saboda ta burgeta samun waje tayi ta zauna Fadila ta gaida gimbiya Rahama sannan ta fita dan basu waje su gana.
"barka da zuwa gimbiyar Sirik "yawwa ya gajiyar tafiya."?murmushi tayi tace"Gajiya tabi jiki."masha Allah ya Sirika akwai dadi ko."? "Eh da dadi gaskia."tace tana kara fadada annurin fuskar ta."Sunana gimbiya Rahama Abdullatib Muhammad inamaki barka da zuwa Masarautar Sirika kuma ina fata zaki zama kawata."Allah yabarmu tare....ni kuma sunana gimbiya Zubaina Abdurrahman Abubakar naji dadin kasancewa dake."jinjina kai tayi tace."Daga yanzun kin zama kawata kuma aminiya ta"gimbiya Zubaina na godiya."Murmushi suka sakarma junan su,sukaci gaba da labarin su kamar wa'anda suka dade da sanin juna suna cikin fira sai ga baiwar gimbiya Rahama tazo ta gayama uwar gijiyar ta ta, Mai martaba nasan ganinta a sashen shi itada gimbiya Zubaina."zaki iya tafita." bayan gimbiya Zubaina ta kara kimtsawa sannan suka tashi suka tafi sashen Sarki Abdullatib.....
★★★
Gimbiya Masa'uda tasa aka dauko mata asiran da Yautai ya aje mata suna komawa sashen ta ta bude su sai murna takeyi sannan suka dauki dauri daya taba Talatu tace."Duk wahala ki tabbatar kinje bakin sashen Hamza kin binne shi,kada kiyarda wani ya gan shi."ansa tayi tace."angama uwar dakina cikin daren nan zan binne shi."kin kyauta."tana fita itama gimbiya Masa'uda ta wuce sashen Sarki Abduljalal ta iske shi kwance ko magana bai iyayi saidai ido da yakebin kowa dashi bayan ta zauna Saminu ya gaisheta sannan tace ya bata waje zatayi magana da mijin ta, kamar bazai fitaba, saboda bai aminta da ita ba,saidai baida hurumin yin hakan ya fita ya bata waje."Abduljalal kenan ashe har yanzun baka mutu ba?lallai kam gaskia kayi nisan kwana,kana da taurin rai! yaka mata ace ka huta zuwa yanzun....gashi dai ɗanka yayi batan dabo ya bace babu amo babu labari,sannan ga Matarka can garkame a gidan yari hakama yarka tana can cikin kaskanci da wulakanci,uwa uba kai gaka kwance baka iya tsinana ma kanka komai kazama abin wulakantarwa ashsha Abduljalal dama mutuwa kayi daka huta da ganin kaskanci irin wannan saidai kasani nan da ɗan lokaci kadan zaka zama sakarai wawa da ranka zakaji na zama Sarauniyar Burhaan ta dindin."kallan kawai yakeyi yanajin dacin maganganun sa a cikin kokon zuciyar shi da haka takaraci wulakancin ta takama gabanta.

Suna shiga sashen Sarki Abdullatib suka iske manya baki sai raha suke yi,sallama sukayi aka amsa masu sanann suka zauna saman wani kafat da ya gaji da tsaruwa da kayan ado irin na Sarauta komai yayi kyau"Allah yataimakeka barka da warhaka sakon ka ya riskemu"barkan ku da safiya ya'yana,ina fatan kuna cikin aminci."lafiya lau."suka amsa fuska sake."ya'ta ta kikaga Sirika,akwai dadi ko?matso nan mugaisa ya'ta ashe da raban ki gaisa da babanki,ya hanya" a hankali ta matsa gefen Sarki Abdulbasit ta zauna ta sadda kanta kasa cikeda da'a tace."hanya alhamdulillah Abba."? "Masha Allah ya'ta."
Gimbiya Rahama ta gaishe da Sarki Abdurrahman cikeda sakin fuska ya amsa.haka Sarakuna sukaita jan ya'yan nasu da fira Sarki Kabir Usman keta kallan Zubaina yana yabawa da nutsuwar ta shima suka gaisa,ranar sun jima sunata fira kowa yaga gimbiya Zubaina daman suna da labarin ta,Sarki Abdurrahman yace."ku tashi ku koma cikin gida kafin Allah ya kaimu gobe za'a fara gabatar da wasa."ku huta lafiya."sukace...tashi sukeyi sukai masu sallama,kowa na yaban su.....ranar ne jajibirin da za'a gabatar da wasan baki sukaita shigowa har lokacin baki basu bar shigowa Sirika ba...haka rayuwa ta kasance kusan lokaci lokaci gimbiya Rahama saita dubo lafiyar gimbiya Zubaina, amma wani lokacin sai ta dinga cewa ta fahimci Zubaina tana daukar kai abinda ta fuskanta tana da miskilanci da tsantsar nuna izzah.....

A wajen su Ammar kuwa zaune suke shida Yarima Yusuf sun zama kamar yan uwa sai labarin Sadauki sukeyi sunga har yanzun yan Burhaan basu zoba gashi gobe za'afara gabatar da GASA.suna mamakin kalan halayen shi daman wancan karan ma baizo ba,yanzun gashi baki dayan su shida Jama'ar shi ba wanda yazo.kowa na mamakin yanda akai basu zoba."abunda nike gani yafiye jiji da kaine shiyasa yake ganin kamar yafi kowa."kadai fada nima dai haka nike gani Allah yasa ganinsa yafi jinsa atoh"cewar Ammar."Amin....nidai koyayane ina son inga wannan Sadaukin jibi yanda labarin Jarumtar shi ya karade ko ina."gaskia kam."suna cikin fira suka tsinkayi sallamar Umar amsawa sukayi saidai baki daya hankalin Yusuf ya koma kan kalan Umar ya duka ya gaishe dan iyayen gidan sa,tunda Umar ya duja Yusuf ke kallan shi baki daya kyawun Umar yagama razana Yarima Yusuf gani yake kamar ba mutun ba tsabar mamakin kalar halittar da Allah yai mashi yakeyi.....Yarima Yusuf ɗan Sarkin BAIZA ne wanda ya samu gata mai tarin yawa a wajen mahaifin shi."Umar."Ammar ya kira sunan shi a tausasahe."Allah yataimakeka barka da hutawa"Umar ya gajiyar hanya"alhamdulilah."murmushi yayi yace."ina fatan ka kara shiryawa kasan gobe ne za'a fara wasan nan ko."? "Eh ranka shidade na shirya fatana Allah yabamu nasara"Amin Umar....kaci abinci."? "Eh,dazun yarima Aryan ya bani"yawwa Umar kaje ka kara hutawa kaji"Umar nagodiya,Allah yakara girma Amin Umar."ku huta lafiya."Allah yasa."yana fita sai mamakin sa yakara kama Yusuf yana al'ajabin natsuwar shi yanda yake magana a hankalce har saida yanayin sa ya fallasa shi yakasa hakura saida yayi magana"Ammar wannan yaron yai mani kuma ina son in tabbatar da gaske bawa ne shi "? "Kwarai da gaske...Umar bawa ne miyasa ka tambaya."gaskia ya shiga raina sosai da sosai walahi ina kaunar shi."jinjina kai yayi yace."haka Umar yake akwai shiga rai"amman fa ina san infanshe shi nawa zaka saida mani shi"? "Hmmm,Yusuf kenan....Umar ba bawan saidawa bane, kayi hakuri"miyasa kace haka?har akwai bawan daba na saidawa ba."kwarai da gaske Umar ɗan Sarkin bayin Zairana ne,kuma amintaccen bawa ne na amana"bakomai haka Allah ya kaddara a gaskia ina san Umar"haka yake akwai shiga rai kuma yana da saurin sabo....
★★★
Tunda suka tashi bayan sunyi sallar asuba wanka Tafidah yayi sannan Shattimah ya shiga suka shirya sannan suka fita zuwa falo suka gaishe da Umma bada jimawa ba su Kamal suka fito suma gaishe da Umman su sukayi sannan sukai mata sallama suka tafi hawan doki itako sai fada takeyi yanda basu gajiya da shiririta, kullin sai sun fita wasan doki kamar ibada sudai dariya sukayi suka tafi kowa ya hau dokin sa suka fita tseren dokin su.....


_Yar Mutan Kankia❣️_

*SADAUKIN BURHAAN*
_(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_
A Kingdom Story👑

*NA*
*JAMEELA JAMEEY*
_(Ya'r Mutan Kankia)_

*BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM*

_SHAFIN KYAUTA_

BABI NA ASHIRIN

Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300)Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.shaidar biyan ki ta wannan layin 08160508316.

Tunda a suba akaci gaba da gyara filin wasa,baki daya bayin Sirika aiki sukeyi ba kyakkyautawa kamar ba gobe,cikin kankanin lokaci suka gama gyara ko ina yayi tsaf gwanin birgewa.
Kayan wasa akata jidowa ana tarasu himili guda dasu iri iri duk abinda akasan Jarumi zai iya bukata an tanaje shi.
A sashen Sarki Abdullatib yana zaune tareda Sarki Abdurrahman bayan sun gama karyawa suna danyin fira jefi jefi kasancewar rana ta daga....Jakadiyar sa tazo ta kawo gaisuwa sannan ta nemawa Sarkin fa'da izinin ganawa dashi bada jimawa ba tayi mashi iso yana zuwa ya zube gaban Sarki ya kai gaisuwa.“Allah yakara maka lafiya sako ne daga Masarautar Burhaan.”batare da bata lokaci ba ya bada umurnin a shigo da shi,bayan ya kai gaisuwa wajen Sarki.“Allah yataimake ka wasika ce daga Sarkin Burhaan.” yana amsar takardar yabashi damar tafiya dama ɗan aiken su ne da suka tura....yana fita bada jimawa ba ya bude wasikar yafara karantawa.....

_Assalamu alaikum_
_Ina maku fatan alkhairi marar yankewa dafatan sakona ya sameka cikin aminci daga ni Sarki Abduljalal Muhammad zuwa ga dan uwana Sarki Abdullatib Muhammad ina mai baka hakuri akan rashin halatta ta wajen zaman da aka gabatar naso in zo Allah bai nufaba saboda wasu dalilai ina fatan za'a karbi uzurina...ga gasa iya gasa anhaɗa yakamata ace zuwa yanzun nakai kwana ukku a cikin Sirika saidai hakan bai samuba,ina kara baku hakuri...yau kimamin kwana bakwai na tura Jarumai na a Kasar Mali bazasu da woba sai mako mai zuwa naso na turosu sannan da'na shine shugaban tafiyar da fatan za'ayi mani uzuri koba komai bai dace ace nabar Masarauta ta ba kowa ba fatan za'ayi taro lafiya nagode daga Masarautar Burhaan zuwa ga Masarautar Sirika,bissalam_

Koda Sarki Abdullatib yagama karanta wasikar kallan Sarki Abdurrahman yayi, kana ganin yanayin fuskar shi zakasan baiji dadin sakon ba."sai mu karbi uzurin sa."cewar Sarkin Kesar."narasa wane kalan uzurine Sarki Abduljalal ke dashi duk yanda yake da tarin Jarumai fiye da sauran Masarautu amma ya gaza tado kashi dan su wakilci Masarautar sa."Sarki Abdullatib ya karasa maganar cikeda alhini a ransa."akarbi uzurin shi kun san baida wasa da ace yana da damar zuwa tabbas zaizo koba komai shine shugaban taron nan yanzun haka sunje bad taimako ne kunsan sun saba da taimakon mutane kuma da yasan wasan nan ya kusa lallai da ya tado manyan Jaruman sa,muyi hakuri tunda haka Allah yaso ni kaina naso inga da'na Sadauki amman idan muka gama gabatar da gasar nan,bayan an huta sai mu samu lokaci mukai masa ziyarar ban girma a matsayin shi na Sarkin Sarakuna." Sai kalaman Sarkin Kesar ya wankema sauran Sarakuna bacin ran da suka tsinci kansu nakin zuwan mutanen Burhaan sannan kowa ya amince da shawarar da Sarkin Kesar din yabagar duk kowa baiji dadin rashin halarta su ba saidai sun tsaida magana da an gama GASA zasu kai ziyarar ba zata.
Haka abubuwa suka kasance bada jimawa ba aka fara fita filin wasa sai fitowa ake kamar ba gobe duk an gyara wajen yayi kyau wajen Sarakuna daban haka na Jarumai ma daban sannan wajen baki daban hakama wajen bayi da sauran Jama'ar Sirika komai yayi kyau cikin tsari.
kowane Jarumi da kalar kayan Masarautar su a jikin su hakama bayin su da kagan su zaka

Please Login or Register in order to submit comment