Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kasa,duk inda zai gifta idanun mutane a kansa musamamn yan uwansa bayi sai kallan shi sukeyi suna zaginsa wai ya cika wuce wuri da daukar kai komai sai ya nuna yafi kowa,alhalin shi din ba kowa bane duk abinda sukeyi Umar najin su amma bai nuna ya damu ba saboda yasan jin zafi sukeyi mashi dan ma Allah yasa ya hadu da Abba Ado yasan da sai yasha wahalar su, yana isa ya tsaya bakin turakar ta saidai ba kowa wajen wajen sashen Fadila ya nufa yai mata sallama sannan ta fito daga dakin ta....tayi mamakin ganin Umar saboda taga ya rabu sa zuwa akalla yakai sati biyu bai zo aikin shiba,gaishe ta yayi sannan yace yana bukatar tayi mashi iso zuwa wajen uwar dakinta....
shiga tayi ta taddata sama kujera zaune a dan makimancin dakin da take hutawa ta harde kafa daya sman daya cikin wata doguwar riga mai masifar kyau ga kyakkyawan gashin kanta kwance lif a saman gadon bayan ta koda Zubaina ta kalli Fadila take kauda kai batareda tace mata komai ba...
dukawa tayi bisa guiwowin ta gaida gimbiya Zubaina saidai ko amsawa batayi ba ita kanta tarasa damuwar uwar gajiyar ta.....cikeda ladabi fada mata sakon Umar da sauri Zubaina ta kuma kallon ta fuskar ta cikeda alamar tambaya.....
"Allah yataimaki uwar dakina,Umar kesan ganin ki yace ayi ma shi iso."kallan da Zubaina tayi mata kadai shi ya baiyana mata amsarta godiya tayi sannan ta fita bada jimawa ba saiga Umar yayi sallama,tunda ya shigo gimbiya Zubaina ta kafe Umar da manyan idanuwan ta masu firgitar da wanda ake kallo kanshi sadde a kasa harya karaso gabanta a hankali ya duka gaban ta cikeda girmamawa,bata daina kallan Umar ba,ta rasa dalilin dayasa take jin Umar din a ranta."Allah yaja da ran gimbiya ta, barka da hutawa ranki shidade,uwar dakina tafi ta kowa alkhairi ina fatan kina cikin aminci da walwala,Umar na kawo gaisuwa Allah yakara maki lafiya da nisan kwana."har yanzun kansa na sadde kasa.
Sihirtacciyar ajiyar zuciya gimbiya Zubaina ta sauke yayin da sanyayyiyar ratsastsar muryar sa na yawo cikin kunnuwan ta amon sautin sa na yawo a sassan jikin ta a hankali ta ware idanun ta masu tsanamin haske ta kuma azawa saman kyakkyawar fuskar sa tana mamakin yanda akai yau Umar yai mata magana mai tsawo tkamar haka abinda bai taba yi mata ba tasan komai nasa a takaice yakeyin sa....tunda yayi maganar yake sauraron yaji amsar da uwar dakin sa zata bashi sai yaji tayi shiru a hankali ya dago kansa ya daura idanunsa akan fuskar gimbiya Zubaina kwana biyun da yayo bai ganta ba sai yaga ta rame masa duk da takara kyau da haske."Allah yasa uwar dakina tana lafiya."?ya tambaye ta cikeda kulawa,dan murmushi gefen baki ta saki wanda ba lallai ka gane tayi shiba muryarta a matukar sanyaye tace."Umar."sake kallan ta yayi yace."Allah yataimake ki."miyasa ka daina zuwa waje na."maida kanshi yayi kasa yace."tuba nikeyi uwar daki na ba daga gareni ba ne sako nw daga Mai martaba yace in dinga kula da Jarumai sannan ya haneni da kasancewa mai maki hidima ina fatan zakiyimin afuwa"waya fada maka wannan sakon."? "Allah yaja da ran gimbiyar Zairana Yarima Aryan ne"ajiyar zuciya ta fesar tace."Shikenan,Umar kaman ta nafada maka bana aan kana yimin nisa."Allah ya huci zuciyar ki,kasancewa ta bawa kaskantacce bai kamata ya kasance da gimbiyar da labarin ta ya karade illahirin Nahiyar nan ba kiyi hakuri hakan ba girman ki bane,kuma matsayina bai kai nan ba."Karka kuskura bakin ka yasake furta kalmar kaskanci agabana,kafi karfin kaskanci Umar,duk bawan da gimbiya Zubaina tasa da kanta a kawo shi zuwa gareta yafi karfin kaskantacce....badan kai ka furta wannan kalmar ba lallai da sai na datse harshen ka!ka kiyaye gaba Umar "Allah yataimakeki uwar gijiya ta,Umar na tuba"
"ba laifi girman ka ne,ko kana da bukatar wani abu."? "Aaa,banda bukatar komai,fatan Umar akoda yaushe ki kasance cikin aminci."
bakaramin dadi Zubaina tajiba harda murmushin ta,shima din murmushin yayi mata,shi kanshi saida yakara tabbatar da tsarin halitta irin ta gimbiya Zubaina.
Shiru ne ya karade illahirin wajen na yan dakiku lafin yace"Allah yataimakeki sako ne daga gimbiya Zinatu tace in kawo maki."a hankali Zubaina ta ansa ta aje gefenta tana jin farin cikin ganin Umar."Allah yakara girma da daukaka zan koma bakin aiki na."mikewa yayi ya juya zai tafi."Umar."Wani kalan yanayi ya dirar mashi wanda ya kasa gane irin shi a hankali ya juyo da fuskar shi ya kawata ta da annuri"wane kalan aiki zakayi."? "uban gidana ya umurce ni zanje wajen Jarumai."kada in sake jin bakin ka ya ambaci kalmar uban gida ni kadai ce uwar dakin ka."zan kiyaye da izinin Allah."yauwa,zaka iya zuwa ka kula dasu kamar yanda Mai martaba ya bukata."Umurnin ki shine abin alfaharina,Allah yakara maki lafiya"girman ka ne Umar zaka iya tafiya"godiya nike."tafiya yayi gar yakai bakin kofa zai fita ta kuma kiran shi.....sake juyowa yayi ya kalleta"ga wannan kayi afani dasu wajen bukatun ka kuma bance kaiman musu ba."wannan ba karamin girmamawa bane agareni Allah yakara girma da daukaka."Amin."fita yayi inda yabar Fadila a nan ya isketa sallama yai mata sannan ya tafi.
kiran gimbiya Zubaina ra tsinkaya da sauri ta shiga ta duka gabanta "Fadila ki hada man kayan da zan sa."angama ranki shidade."
Ranar haka Zubaina ta wuni cikin farin ciki tagama yarda cewa Umar ya shiga cikin ranta tasaba dashi tana mamakin yanda tayi saurin sabo da shi."ranki shidade angama hadawa."sannu Fadila zauna." Zaman tayi tana jan Fadila da surutu kamar ba ita ba,itama Fadilar firar take mata saidai aranta tana zargin uwar dakin ta,na son Umar amma bata kaida tabbatar da zarginta akai ba,tasan muddin hakan ta kasance lallai uwar dakin ta zata shiga matsala a wajen mahaifin ta saboda duk yanda yake sonta bai yarda da wulakanci ba kuma shi bai da gwani...."Fadila hadaman ruwan wanka yau ina so zanje ziyara."angama ranki shiade." bada jimawa ba ta gama hada mata ruwan wanka."angama hadawa ranki shiade."tahi tayi ta shiga wanka.
★★★
Gimbiya Saratu dauke da wata katuwar kwarya,ta gama ware magungunan da suka gama hadama gimbiya Masa'uda itada bokanyarta kowa ne hadi da sukayi sun gama fada mata yanda zatayi anfani dashicikin wata katuwar leda ta saka shi.
ita kanta tasan sun hadama su Hamza, mugun tuggu.dariya ta kece dashi ta kalli bokanyar ta tace."aikin ki na kyau yau din nan zan tada bawan da zakai man asirran nan,saina tarwatsa rayuwar mutanen cen,ymuddin Yalwa tayi anfani dasu yanda ya dace na tabbata Hamza bazai kara tasiri ba a Masarautar Burhaan ba."hakan yana da kyau."tasa baiwarta ta kiramata bawan da zata aika bada jimawa ba suka shigo ya gaishe da gimbiya Saratu sannan ta mika mashi leda"ka rike ledar nan da kyau kamar ranka!karka kuskura kaba kowa wannan sakon sai gimbiya Yalwa hannun ka hannun ta."angama ranki shidade."ga guzurin da zaka rike har ka isa,ka kara kiyaye wa."angama Allah yataimaki sarauniyar Yurii."gyada kai tayi sannan ya kama hanya.
___________
koda gimbiya Zubaina tagama shiryawa fitowa tayi itada da Fadila ba inda suka sauka sai sashen Yarima Ammar wajen Gimbiya Zinat suna shiga ta samu waje ta zuna,ita kuma Fadila ta gaishe da gimbiya Zinat sannan ta basu waje."Wannan irin kyau?kai autar Umma kinga yanda kika kara kyau?saidai kace wata sarauniyar kyau."hmmm Adda na kenan,kedai kina san ki yabeni kawai."dama nasan bazaki yarda ba amma da ace kin kalli madubi daya baki amsa."dama na gani kyau ba tareda kwalliya ba"?murmushi gimbiya Zinat tayi tace."kin san kyawawa ko ba kwalliya kyau sukeyi."shikenan naji nasan dole sai kinsa na yarda nagode da yabawa."Hmm naji dai."fira suka cigaba da yi."kinga har na manta dauko mani dambun nama na."Ayyah kanwata kiyi hakuri banyi zaton yau zaki zo ba,aida na ajemaki."tabb yau koda mijin ki yazo nan,bazan yarda ba sai kinyo mani"bata kai haka ba ai amma nan zaki wuni ko."? "Aa zanje wajen Umma." bari in tashi yanzun nan zan hadama tauraruwa ta abinda take so"Aa bazan wuni ba nacema Umma yau zanje wajen ta kuma nasan ni take jira dana tsaya, ki tabbata ina binki bashi."Shikenan,amma dai zaki jima wajen Umman ko."? "Eh zanjima"ba damuwa sai kin jini."yawwa Anty na nagode."rungume junan su sukayi sannan Zubaina ta fita zuwa wajen gimbiya Amina.
Tana shiga sashen mahaifiyar ta,ta same ta zaune samana sallaya tana lazumi har kasa ta duka ta gaishe da Umman ta,itama Fadilar gaishe ta tayi cikeda girmamawa,har zata fita ta kirata tace." Fadila dauki abinci kici."nagode Allah yakara girma."dauka tayi tanajin dadi a ranta godiya tayi sannan ta tafi.
"Ranki shidade barka da hutawa"yauwa Zubainatu kin fito."Eh,Umma daga gidan yaya Ammar nike"kin kyauta,zumunci abune mai kyau"Umma yaushe zamuje wajen Umma Rukayya."? Rike baki tayi alamun maganar tazo mata a bazata tace"Hmm Zubaina kenan,kema kinsan Abban ki bazai taba bari keyi mashi nisa ba"Umma ki tambayar mani shi"kirufaman asiri Zubaina! Ina ni ina turakar Mai martaba da wannan zancen? ina magana cewa zaiyi nike zugaki dan kidin ga yawo, duk yanda baki tunani Abban ki ya wuce da tunanin ki yanzun ya gama rudewa ni har tsoro yake bani,kwarama kije kisamu Hajia kila idan tafada mashi bazai yi musu ba,niko idan nayi magana zai iya kullata ta,tunda ba kaunar abinda zai rabeki yakeyi ba."Umma ba wani abu bane fa magana kawai zakiyi mashi..."kinga Zubaina bana son musu ina fata kin fahimce ni." "na fahimta."kin kyauta"shiru ya karade illahirin dakin Zubaina tace."Umma kina ganin Abba ya rabani da Umar wai baya son yai mani aiki"wani irin kallo ta aika mata kamar bataji taba tace."mi kenan."? "Umar mana gaskia ina son amaido mani bawana."Kedai bakijin magana Zubaina Umar din mi? so kikeyi kisa ubanki ya wulakanta ni ko? wato kedai Zubaina duk abinda iyayen ki keso ba shi kike so ba ko? miya hada ki da hadimi namiji?Dan takamar ke kikasa a sawo shi sai me?kefa da bakinki kika ce baki son namiji a kusa dake,duk kin tsane su har gadara da ikirari kikeyi kina cewa mijinki na nan zuwa ko kunyr iyayen ki bakiji sai yanzun?zaki zo kina maganar Umar?wai amaida maki shi a matsayin hidimin walahi Zubaina ki kiyayeni,ni bana ciki da sakarcin ki!" "Kiyi hakuri Umma,badan komai yasa nike son sa ba saidan Jarumtar sh"kada in sakejin wannan bakin naki ya furta kalmar Umar a matsayin hadimin ki idan ba kuma jin haka saina fasa maki baki!koni uwarki ban isa ubanki ya bada umurni in bijire masa ba ballan tana ke da bai wuce akarya ki ba."idanuwan gimbiya Zubaina har sun sauya launi"Umma ki fahimce ni ban..."zan wanke ki da mari kika kuma magana yanda ba kowa wajen nan zan zaneki sai kin rasa mai cetonki sakarai shashasha ana nuna maki gaskia kina bijirewa ki kara cewa uffan kigani yanzun jikin ki zai gaya maki."hawaye suka fara sauka saman kuncin ta.sai fada Gimbiya Amina keyi.
Ammar keyi tayi masu Sallama amma basu jishi ba yanda yaga mahaifiyar su na fada hakan yasa ya karaso da sauri yasan halinta bata iya fushi ba tana iya lakada mata duka kamar yanda ta fada dama tana jin haushinta duk abinda zatayi sai Mai martaba ya dinga ganin laifinta duk abinda zata aikata sai yakare kanta yace ita ke sata"dan Allah kiyi hakuri Umma"kyaleni da yarinyar nan,dagani jikinta ya rabu da zafi shiyasa,kuma ai uban naku shine ya sangartata bai san yaga ana mata fada idan bashi kadai ba idan kuma tayi laifinta sai yakare kaina sai kace wata marar 'yanci."Allah huci zuciyar ki Umma kidaina fadan nan."_dole nayi fada Ammar,ke kuma kikara yiman maganar kina son amai da maki Umar matsayin hadimin ki,walahi koda zanyi dana sani saina maki dukan mutuwa,shashasha dake"Umma,dan Allah kada ranki ya baci nasan daga nan ma tabar maganar baki daya."kaifa ke cimata albasa Ammar."sai kuka takeyi ba abinda ta tsana a duniya irin fada,hakuri Ammar yaita bata"Umma kiyi hakuri,bansan ranki zai baci ba"taya zaki sani tunda ba hankali ya wadace ki ba."Ammar yai taba Umman su hakuri sannan tayi suna cikin zaman kuramen da suka tsunduma sai ga yar aiken gimbiya Zinat ta shigo ta kawo ma gimbiya Zubaina dambun naman ta izinin tafiya akai mata sannan ta tafi.

Dishes din Umma ta bude sannan ta samu faranti karami ta zuba mata ta mika mata saboda tasan halin gimbiya Zubaina duk yanda takai ga san abu matukar akai mata fada ko ranta ya baci bazata ci abun ba wannan dalilin na daya daga cikin dalilin da yasa Sarki Abdurrahman bai san yaga 'yarsa na fushi"Maida hankali ki cinye shi duka"na koshi."harara ta wurga mata cikeda tsare fuska tace."ba neman ba'asi na tambaye ki umurtar ki nayi."ba shiri ta fara cin naman tana ajiyar zuciya Yarima Ammar keba kanwar ta shi hakuri harta dan saki jikinta saboda Zubaina na mugun shakkar gimbiya Amina tunda ta fahimci kalar son da mahaifin ta ke mata shiysa ita kuma bata mata da sauki musamman idan tana wulakancin ta saboda bata son ta kara sangarcewa....
Maganar mai martaba suka tsinkaya yana shigowa baki dayan su suke gaishe shi saman wani babban kafat ya zauna wanda yake dauke da kilissai kala kala bayan ya zauna gimbiya Amina ta dauko katon tire dauke da kayan marmari iri iri ta aje mashi sannan ta aje mashi kwaryar dafaffiyar madara"barka da rana ranka shidade"yauwa gimbiyata ya fama da jama'a."Alhamdulillah."shiru ya dan biyo baya ya gyara zaman shi ya maida dubans ga Zunbaina dake ta faman fushi yace."Mama na ya zaki tisa abinci a gaba kina yaguna idan baiyi miki ba ki aje mana."kamar jira takeyi ta ture flat din gefen ra."Jiya nasa Jakadiya ta kawo mani su Hussain akace sunyi bacci."Allah ya taimake ka,basu jin magana da sungama wasa sai suyi bacci da wuri"ai haka yara suke saidai addu'a,kaga sai su tayani fadanci....Allah yaimasu albarka "Amin." "Mamana wai mike damun ki naga duk yanayin ki ya canza"? "bakomai Abba."nafi kowa sanin farin cikin ki,masto kusa dani, fadaman minene da muwarki."? " kaina ke ciwo"saidai baki saba karya ba Zubaina."
(yanzun idan nafadama Abba akan Umar ne Umma tayimani fada mizai faru?nasan ba ita kadai ba hatta ni sai raina yai mugun baci zaice na raina shi ban girmama umurnin shi ba.)"Mamana tunanin mi kike."? Murmushi ta dan kakaro tace"daman ina san kaiman izini zan kaima Umma Rukayya ziyara."har yakai tuffa bakinsa kenan ya aje,sannan ya kalli Zubaina saidai kalla mamaki yake mata...."kinsan me kike fada?ni ne zanbarki kiyi tafiya mai nisa har zuwa Kasae Cameron? lallai kam kema kinsan hakan ba mai yuyuwa bane bazan iya bari kiyi irin wannan doguwar tafiyar ba,koda aure yakai ki can saidai dan ba yanda zanyi ne"Abba kwana daya da yini mun isa kuma saika hadani da bayin da zasu rakani"Mamana kenan kinsan me kike fada kuwa?ni Abdurrahman zan hadaki da bayi kawai dan zaki kaii ziyara? Kuma ba muharramki ba, naji zan hadaki da bayin dawa yakama ta kuyi tafiyar."? Ya karashe maganar yana mata murmushi.
Ammar ya kalli Umman su cike da mamaki yaga Mai martaba zaima Zubaina rijiya.cikeda zumudi tace"Abba,saika hadani da uma....kallan kinsan sauran umman ta ta aika mata da sauri ta sadda kanta kasa cikin sanyin murya tace"wa'anda kaga sun dace Abba."haba gimbiya Amina bai kamata kidinga yimata hannunka mai sanda ba,kibarta ta fadi ra'ayin kanta."
"ki ida fadar abinda kikayi niya kinji ya'ta ko kina nufin bawan nan Umar."? "Allah yataimake ka bakina yayi ya kadan ya furta sunan Umar agaban ka bayan kace baka son ko a hidima na ya kasance taya zance shi" gyada kansa yayi cikeda gamsuwa yace."kin kyauta ma kanki Mamana.....sannan ni bazan barki kitafi wajen Rukayya ba, saboda tafiyar tayi mani nisa kuma bana san kina nisa."toh Abba." kada kidin ga jin haushin mahaifin ki da gangan kinji har yanzun baki tambayata abinda ya dace dake ne shiyasa, ni kuma duk abinda kike so zan maki amma fa sai abinda yake dai dai dake idan naga zai cutar da rayuwar ki lallai bazan taba yimaki shiba ki tambayi mahaifin ki duk abunda kike so ni kuma zan maki shi "toh Abba nagode Allah yakara girma"Amin mamana tafi ta kowa."Murmushi tayi.
"Ina fatan gwajin da ake bayarwa yanayin yanda ake so ko."? "Eh,ranka shidade."Allah yataimaka."

Sadaukin Burhaan na kudi tuntubi wannan number 08160508316.domin karin bayani.

Koda Talatu ta dawo wajen bokanta wani irin magani taba gimbiya Masa'uda kasakasa take mata bayanin shi da yanda za'ayi anfani dashi ba karamin dadi taji ba ganin yanda aikinta ya fara kyau."angaishe ki Talatu ina alfahari da ke,kice yanzun Hamza zaizo hannu."kwarai kuwa sai yanda kike so da kowa."nagode maki."

_Kowane irin aiki ne boka yaba gimbiya Masa'uda....muje zuwa muga yanda zata kaya👀_

Bakaramar ukuba Turaki ke shaba kullun da kalar walahar da yake sha baida wani galihu a cikin Masarautar kamar bai akowa.
Abdullahi yazo wajen mahaifiyar shi yakawo mata karar Hamza."yanzun dai kayi hakuri Abdullahi kaga dan uwan ka ne shi."Haba Goggo akan mi zan kyale shi duk ya mallake komai ya hana kowa sakat ga rashin tausayin da yake nunawa ga bayin sa kuma yasama matata ta kunkunmi ya hanata sakat haba Goggo."gimbiya Saude tace."ka bari zanyi ma Hamzan magana sannan maganar matar ka da kakeyi ka manta da wannan zancen tunda ma matarka da danka basu da wani anfani agaremu."haba goggo bai dace kice haka ba." suna cikin magana sukajiyo kakarin da Turaki keyi kamar zai mutu da sauri Abdullahi yata shi da gudunsa ya nufi dakin da aka rufe shi amma mahaifiyar shi ta hana shi mabudin dakin, yanajin danshi na neman taimako amma taki bude mashi daki,saida taga dama sannan ta bude dakin yana shiga wani irin wari da tsami ya daki hancin shi,da sauri ya dauko dansa zuciyar shi ba harbawa yanda yaga wulakancin da ake masa har saida yayi kuka tsabar tausayin sa daya kama shi jikinsa na rawa ya dauki ruwa yaba shi yasha,Goggo tace."idan kagama tausayin nasa saika maida shi ko."? "Bazan maida shi ba Goggo bayan da za'ayi inaji ina gani aka she mani da'na."bazaki abinda nike fada maka."kiyi hakuri bazan iya ba."da taga yafi karfin ta saita kyale shi.
bayi yasa suka dauki Turaki aka kai mashi shi sashen shi duk ya gama fita hayyacin shi.....
Bamda bala'i ba abinda takeyi tana cewa."saina tsine maka Abdullahi matukar baka maido Turaki ba saboda banga anfanin shi ba.....
____________
Tafeedah ne ya tsaye gaban mahifiyar shi ya gama shirin sai zai tagi damagaram zai gaishe da Umman Shattimah saboda yasan tana kewar danta,yana gama shiryawa ba inda suka wuce sai wajen dawakai ta rike mashi sirdi ya hau sannan yai mata sallama tayi masa addu'a sannan ya kama hanyar tafiya damagaram.....

A sashen gimbiya Rahama kuwa zuwa yanzun ba abinda takeyi sai kuka kmar ranta zai fita daga gangar jikinta daga taji Sadauki yayi aure kuma ita tasama ranta bazata auren mai mata ba,shiyasa ta daga hankalin ta bata da aiki sai kuka ga tsananin son Sadauki ya rufe mata ido soyayar da bai san tanayin ta ba ga tsananin kishi ta saka a ranta wai bata iya zama da kishiya.
Ba irin bakin da mahaifiyar ta bata bata ba amman a banza ba abinda ya sauya sai lma karuwa da kukan keyi ita janta gimbiya Karima harta sa mata ido sannan zuciyar ta na cikeda tausayin yarta....

itako Safiyya duniya tayi mata tofin Allahi tsinw komai ya rude mata bata samun sukuni ga kowa sai wajen mahaifiyar ta duk rame kullun sai mahaifin ta yai mata gorin akan ta haifi ya' mace ba wani sauyi ya tsaneta ita da yar ta, ga bai kaunar diyar ta ko miskali zarratin kullin cikin zullumi taje duk tabi ta lalace kamar ba ita ba tsoron ta daya kada mahaifin yasa aka kashe mata 'ya tasan zai aika,shiyasa bata samun cikakkiyar nutsuwa.
________
Umar ga fura ka tashi kasha kada yunwa tayi maka illah"toh Abbana walahi duk na gaji shiyasa."Allah Sarki Umarul-faruq kayi hakuri, wata rana sai labari kaji."toh Abba na."zama yayi yafara shan furar."Yau saura kwana bakwai muje wajen gasar nan"aje ludayin hannun sa yayi yace."ashe har lokaci yayi gaskia ni bana san zuwa."Haba Umaru ba saboda me."? "Saboda mutane bana son su"Murmushi Abba Ado yayi yace."Umar kenan, ai mutane rahama ne"hakane bana son ina ganin su dayawa."Hmm zaka saba kaji."to Abba."

_Yau Sadauki ke fadan baisan shiga cikin mutane Allah karaba mu daga sharrin sihirin Amin🙏_

Kwatan tama Umar ya dinga yi har saida ya daura shi saman hanya, amma sannan ya aminta zaije,aran shi yana mamakin halayen Umar shidai har yanzun yana son yasan asalin Umar dan de ya fahimci baisan maganar tunda har yanzun baisan me zaice ba game da kanshi.
saidai a wani sashen na zuciyar shi gani yakeyi anya Umar bai cikin turbar sihiri? antaba mutun da girman shi yace baisan waye shi ba? da iyayen sa!gaskia dole ya tashi tsaye kodan yasamama Umar magani dan yanaji a ranshi akwai babban al'mari atare dashi......

*Banda VTU idan kati ne kiyi snap din shi sai kituro mani ta namba ta dana bada MTN kadai*


_Yar Mutan Kankia ce❣️_


Share
Pls

*SADAUKIN BURHAAN*
_(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_
A Kingdom Story👑

*NA*
*JAMEELA JAMEEY*
_(Ya'r Mutan Kankia)_

*BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM*

_SHAFIN KYAUTA_

BABI NA SHA HUƊU

Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300)Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.shedar biyanki ta wannan layin 08160508316.
Bana son VTU kituro credit ta hanyar numbar dana bada sama.
_MASARAUTAR SIRIKA_
Bayi da sauran hadimai keta aiki cikin masarautar ba abinda suke kokarin yi sai sai gyara sukeyi ko ina na cikin Sirika....yau yakama saura kwana ukku afara gabatar da gaggarumar gasa wadda ta karade illahirin kasa baki daya harda makwabtan ta da wasu sassa na Africa baki daya.
uban bayi ne keta rabama bayi yan uwansa aiki kowa ya zakade yana aiki kamar ba gobe
A cikin dakuna da aka tanada dan bawa bakin da zasu zo suma uwar bayi da sauran hadimai mata sun bazama sai gyara sukema dakuna nan abin dai ba'a cewa komai,hidima akeyi cikin Masarautar ta Sirika ba dare ba rana kamar anayin wani gaggarumin biki haka ake hidima.
Sarkin yaki ne wajen Sarkin dawakai inda yasa hadimai suka gama gyara wajen dawakan sannan suka ware ingantattu kuma nagartattun dawakan da za'a gabatar da gasa dasu yayin da Jaruman Masarautar keta karbar gwaji kamar ba gobe burin kowace Masarautar ta lashe gasa kowa so yake ya zama zakaran gwajin dafi.
Sarkin yaki na gamam basu gwaji aka ware mutun goma sha biyar ya tantace wa'anda suka amsa sunan cikin jerin manyan Jaruman Sirika sune zasu wakilci masarautar su a gasar.

Koda Sarkin gida ya tabbatar da angama gyara komai yanda ya kamata sanarma dogarin Sarki Abdullatib yayi bayan Mai martaba ya tashi daga Fa'da suka biyo wajen domin yin rangadi ko ina ya gama gyaruwa an shirya shi musamman masaukin baki wani irin katafaran waje mai dauke da ɗakuna bila adadin wa'anda suka gaji da kayan alfarma da alatu a cikin na more rayuwae yau da gobe an wadata ko wane daki da shimfidu gwanin burgewa ga bayi a jibge wa'anda zasu dinga kula da wajen da duk abinda ke cikin sashen ana bashi kulawa ta musamman saboda komai na Masarautar sun gama tsara shi sannan kowa yasa aikin shi, Sarki Abdullatib na gama rangadi shida jama'ar suka raka shi zuwa Turakar shi.

Washe gari da safe da kisalin karfe goma Sarki Abdullatib ya hada gaggarumin zama na gaggawa a fadar sa sannan ya bukaci Sarkin yaki da uban bayi su halarci taron kafin wani lokaci fa'da ta cika dankam da dan adama kowa ya samu sakon Mai martana bayan kowa ya hallara Sarki Abdullatib ya shigo tareda Wazirinsa sai kuma Shamaki suna isowa kowa ya mike tsaye fadawa suka rufe Sarki da manya rigunan su ya zauna kowa ya kai gaisuwa ga Sarki sannan suka zauna."gyara zaki gyara ginzi Allah yataimaki Sarkin Sarakai angaishe da Sarki mai adalci Sarkin Sirika Allah yataimaki mahaifi g Gimbiya Rahama gaba salama baya salama."Sarkin zagi keda koda Sarki a hankali ya daga mashi hannun alamun yai shiru,gyaran murya Sarki yayi cikeda kamala yace"godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki da yasake hadamu a wannan waje,kamar yanda muka sani munje munyi taro da manyan Sarakuna an tsaida za'ayi babbar gasa a Masarautar Kesar amma duba da yanayin nisan da mukayi

Please Login or Register in order to submit comment