Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hashim da Aryan suke tangan,wannan karon Sadauki shine na bakwai, ba abinda yakeji a cikin kunnuwan shi sai kalmar yayana yi sauri yayana! idanunsa ya rufe yana jin zuciyar shi ke bugu da sauri da sauri kamar zata fado kasa kanshi nayi mashi wani irin ciwo kamar zai fita daga kanshi komai ya coshe mashi ya kasa tuna komai sai kalmar da yakeji ta kayi sauri yayana!!kafin kaftawa da bissimillah Sadauki yayi masu fintin kau Allah yaba shi sa'a ya dauko tutar karshe ya juyo da ita a hannun shi
baki daya wajen ya kaure da murna tun daga bayi har Sakunan da yan kallo suka hau murna wajen ya kaure da ihu kowa sai murna sukeyi danko Zubaina batasan ta fasa uwar karaba wanda yajanyo hankalin duk wanda ke wajen saida ya juyo yana kallanta.
Umar ya isa wajen Sarakuna yakai ma Sarki Abdullatib tuta hannu yasa ya amsa,fuskar shi dauke da murmushi mikama Umar hannu yayi sukeyi musabaha kowa sai murna da farin ciki akeyi sauran Jaruman na isowa suka fara rungume junan su suna taya junan su murna sannan suka koma suka zauna suma zama bada jimawa ba aka fara sanar da sakamako wannan karan sunayen mutane ake kira bana Masarauta ba, alkalin wasa yafara cewa."UMAR ADAM shine ya lashe gasar tseren doki,Ammar Abdurrahman yazo na biyu, sai Hafiz Yunus yayi na ukku,Aryan Abdurrahman yazo na hudu,haka akaita lissafo sunayen Jarumai har akaje ga wanda yayi na talatin,baki daya wajen ya kaure da ihun murna,jarumai suka daga Umar sama sunata murna.
Wani irin son Umar ne yakara shiga cikin zuciyar Sarki Abdurrahman yau yakara tabbatar da cikakkar Jarumtar Umar ranar haka akaita farin ciki da murna basu jima ba aka tafi hutun awa biyu. Ammar na komawa yasa aka kira mashi Umar yana zuwa ya bashi abinci da ruwa yasha ya huta.
Bangaren Sarki Hamza zaune yake fa'da shida jama'ar shi anata fadanci Sarkin Fada ya iso dan aiken Roowan ya kai gaisuwa sannan ya bada sakon Sarki Abdulbasit Abdulkarim,yana amsa Sarki Hamza yasa aka bashi masauki sannan yasa Magatakarda ya karanta mashi sakon dake cikin wasikar.

_Bayan gaisuwa irin ta addinin musulunci fatan sakona ya riskeka cikin aminci,dalilin dayasa na aiko maka da wannan sakon domin in tambayi lafiyar ka data iyalanka kwana biyu banji wani motsi daga gareka ba na damu da yawa yakama ta ace nasamu sakon ka kuma ina zuwa nan da mako biyu insha Allahu,kagaidamin da dukkan zuri'a daga Sarki Abdulbasit zuwa ga Sarki Abduljalal bissalam_

Kallan kallo ya biyo baya tsakanin Sarki Hamza da magatakarda ga fa'da ta cika damkam da mutane fada tayi shiru ba wanda ya iya furta uffan a cikin su,takaici ya cika Sarki Hamza tashi yayi ya bar fadar sanann ya bukaci ganin Magatakarda a sashen shi harya zai fita ya dawo ya kalli Shamaki yace."ka shirya zuwa gobe zaka tabbatar dani a matsayin Sarkin Burhaan."angama ranka shidaede da haka ya fita.
★★★
zuwa yanzun sunfara shawarar yanda zasuyi su koma Burhaan dan su ga halin dasu Ammi ke ciki da dan uwan su,sun jima suna nemawa kansu mafita daga karshe Shattimah yace."zamuje Roowan wajen Nafeesa sati mai zuwa."Allah yakaimu."

"Zubaina na isa lambu tasa aka kira mata Sadauki akaro na biyu takai minti Ashirin tana jiranshi ta gaza zaune ta gaza tsaye ji take kamar ta kurma ihu tunda take bata taba jiran wani mahaluki a duniya ba sai Umar tsawon mintoci talatin gajiya tayi da zama ta mike tana fesar da zazzafar isakar bakinta ta juya zata tafi can ta hango shi ya taho cike da nutsuwa yake tako a kame kansa sadde kasa,baki daya hankali da tunanin Zubaina sun koma kan Umar daga nesan take kare mashi kallo mai dauke da tarin shauki yayin da kwayar idonta ke fitar da tsantsar begen sa zuwa ruhinta bata kara tabbatar da zatan ta akan Umar ba sai yanda taga yana tafiyar sa kamar wani ɗan basarake ita dai tasan koda Umar yana bawa ya dace da rayuwar ta da tsarin ta yanzun ne takara tabbatar da Umar shine mijin data dade tana tsumaye mijin ta alakanta dukkan burin ta na duniya akansa mijin daya jima a cikin ruhinta mijin datayi imani shine ta jima tana jira yazo a cikin rayuwar ta....lallai kam idan har abinda takeji game da Umar shi ne SO ya tabbata ta fada a tarkon SON Umar tarkon da bataji zata uya fita cikinsa zuwa yanzun tayi nisa akan son UMAR batajin zata iya rasa shi kuma zata iya komai akan shi harya iso gabanta bata san ya karaso ba kuma bata daina tunanin data lulaba hasalima batasan ya ison ba.
A nutse ya dukawa ya gaisheta cikeda girmamawa."barka da wannan lokaci,Allah yataimaki Uwar dakina." kuri tayi mashi da manyan idanuwan ta masu tsananin haske da daukar hankalin wanda aka kallo baki daya hankalin ta na kanshi takasa daina kallan shi labban ta sun mata nauyi ta gaza amsa gaisuwar shi,har saida yakara maimaita gaisuwar da yai mata akaro na ukku sannan ta amsa,tana shide ajiyar zuciya.
Cikin takun kasaita ta koma ta zauna saman shimfidar da aka tanadar mata.
izinin zama tayi mashi daga gefen ta saidai yaki zama saida yaga baccin ranta sannan ya zauna badan yaso hakan ba."Umar."yaji ta ambaci sunan shi a sanyaye da sauri ya dago kansa take idanun su suka hadu dana juna,kallan ta kawai yake yanda ta furta kalmar Umar cikin wani irin salo marar misaltuwa ya amsa da."Na'am,Allah yaja da ran Uwar dakina barka da hutawa"cikin wani irin amo yayi maganar da muryar sa mai sa zuciya natsuwa."ajiyar zuciya ta shide tace."yawwa Umar."dan shiru ya biyo baya kowa ya gaza furta komai tarasa ta ina zata soma magana shi kuma yayi shiru ne yana jiran yaji umurnin ta saida ta nisa sannan tace."A gaskia Umar ka cancanci kowane irin yabo ka kara tabbatarma duniya waye kai ka kara tabbatar ma Masarautar Zairana kaidin Jarumi ne gaskia Umar ka cancanci abaka lambar yabo kuma ajinjina maka a maidaka Sarkin Jarumai bana Zairana kadai ba idan na kiraka da Sarkin Jaruman Afrika banyi laifi ba saboda kacancan ta,inaimaka fatan alkhairi"dan murmusawa yayi wanda ba lallai bane agane yayi sa ba yace."ina godiya Uwar gijiya ta,Allah yakara daukaki"hmmm...Umar kenan,ada ya daace ka dinga yi mani kallan uwar gijiyarka ba yanzun ba."a hankali ya dago kanshi ya kalle ta yace."ranki shidade...saidai ban fahimce kiba."? "Hakane Umar nasan bazaka fahimta ba,idan na kiraka da Jarumi,gwarzo kuma Sadauki ai ina ga banyi laifi ba ko."?
Tunda Zubaina ta ambaci kalmar Sadauki baki daya numfashin Umar ya fara halbawa da sauri da sauri,kanshi ya kulle kam baki daya yarasa mike mashi dadi a rayuwa"Umar."ta kuma kiran shi muryar ta na rawa rawa,sake kallan ta kawai yayi baice da ita komai ba,cigaba da cewa yayi."daga yau sunan Sadauki da kai ya dace."saboda mi."?ya samu kanshi da tambayar ta kai tsaye."dan murmushi tayi tace."Saboda ba'a Sadauki raggo kuma duk mai sunan Sadauki kowa yasan Jarumi ne na gaske,kalar Jarumi irinka bai dace da kowa ba sai da gimbiya Zubaina"hannayen sa yasa baki daya ya dafe kansa yana kallan ta cikeda mamaki bawai mamakin maganganun ta yake ba Aaa yanda take koda shi tana kai shi matsayin da baikai ba."ya kayi shiru Umar."rausayar da kanshi yayi kamar mai tunanin wani abu yace."Allah yai maki yawan rai,kamar yanda kika sani tun asali Umar dai BAWA ne kuma duk wani halin jarumta anahin tama bansan yanda ake yin ta ba,kuma duk abinda kikaga nayi wajen gasar nan bawai iyawata bane daga Allah."nasani Umar du da haka dole ka amsa sunan Jarumai."wannan karonhar ya kosa da maganganun da take mashi baki daya ya gaza gane kansu yanajin ta ne kawai bawai dan yana fahimtar taba kanshi ya coshe ya gaza banbance komai."shikenan saidai kisani duk wannan abun ba gwanintar Umar bane sa'ar ubanjine, ki gafarce ranki shidaee bai dace kina kiran Umar da sunan Jarumai ba kai tsaye ba sunayen Sadaukaiba ba cancanta a gareni ba lallai kam matukar kinayi mani wannan inkiyar zan iya shiga damuwa,kisani Umar ba kowa bane face BAWA marar 'yanci wanda baida kowa dai mahaliccin shi......Bata bari ya ida maganar da yakeyi ba ta daka masa uwar tsawa"Umar!"ta kira sunan sa zuciyar ta ba halbawa kamar zata faso daga kirjinta ta kutto kasa."kada na kara jin bakin ka ya furta kalmar rashin 'yanci a gareka! kai mai 'yanci ne Umar koda ka kasance bawa a idon duniya to kasani a idon gimbiya Zubaina kai ba bawa bane Umar,kafi karfin a kiraka da bawa,kuma ya zama dole ka amsa sunan Sadauki daga yau in dai ni zan kiraka ya zama dole ka amsa sunan Sadauki."yanda ta ida maganar zaka tabbatar da irin zafin da zuciyar ta ke mata shidai bai sake ce mata komai baki daya zancen ta sake hargitsa sa takeyi kansa na kara masa nauyi duk sanda zata kira shi da Sadauki,zaune yake gafenta kawai yana sauraron ta."Umar."ta kuma kiran sunan shi a raunane cikin wata irin siga mai wuyar fassara. "a yau na kara tantance abinda nikeji a akan ka,basan taya zan fara shaida maka abinda ke raina ba."maida dubansa yayi akan ta ya ga tsantsar damuwar dake kwance a saman fuskar ta sai ya samu kansa dajin tausayin ta yace."mike faruwa,mike damunki."bakasan abinda ke faruwaba ko Umar? "Allah ya huci zuciyar ki ban san abinda ke faruwa bako"Inason ka kara bani aran hankalin ka Umar kuma kasa idanun kacikin nawa."shidai kallan ta kawai yakeyi."Umar"ta sake kiran shi,ya amsa atakaice "Na'am."ya maida kansa kasa."ina SON ka Umar."a razane ya dago kansa ya kafeta da firgitattun idanun sa ya gaza furta uffan baki daya kanshi ya juye mashi har juwa take neman dibar shi daga zaunen da yake,rumtse idanuwan sa yayi ya kuma budesu samn kyakkyawar fuskar ta yaja numfashi ya fesar yace."ban fahimce ki ba."INA SON KA."ta sake maimaita mashi da dake itama tana kallansa take ya mike tsaye itana mikewar tayi dukkan su sun kasa furta uffan ita tana sauraron amsar shi,shi kuma kansa ke sarama shi numfashin shi na sarkewa maganar uwar gijiyar shi ta firgita duk wani tunanin shi ta hautsina shi taya za'ayi ace gimbiya Zubaina kamar gimbiyar Zairana ta furta kalmar SO ga bawa kamar shi! bawan ma bawan ta sannan hadimin ta."Baka ce komai ba Umar."juyo yayi daga bayan daya bata hannayen sa sarkafe da juna ya goya su saman bayan sa ya sake kallan ta yace.
_______________
Anan na kawo karshen shafukan kyauta na wannan labari gamai bukatar son ci gaba da bibiyar wannan littafi ka/ki hanzarta biyan kudin ku domin ayi tafiyar nan daku, saboda tafiyar nan ta daban ce kuma ta musamman ce akan naira (300) kunji yanda salon sa yake yanzun aka fara wasan inada yakinin zai nishadantar daku zai fadakar daku harma ya wa'azantar daku da izinin Allah.

*Akwai grp na maza dana ware maku saboda kuma kun karbi wannan labari zaku cigaba da payment sannan zaku turo shaidar biyan ku ta number da zan bayar*

Ya kuke ganin wannan labarin zai wakana?Ga gimbiya Zubaina ta furta kalmar so ga bawan ta Umar kuna ganin zai karbi soyayyar ta?? sai yaushe ne Umar zai dawo cikakken Sadaukin sa?Sadaukin ma na Burhaan??Ya labarin Sarki Abdurrhaman ya zai dauki bukatun 'yarsa? Ya kuke ganin karshen azzalumai zai kasance a cikin wannan labarin?kada ku manta tun daga Izzah ko Mulki kuka ji yanda abubuwa suka wakana har zuwa Sadaukin Burhaan kunsan dai shine jigon labarin,hmm garin dadi na nesa....

_Domin mallakar naki tura shaidar biyanki ta wannan layin 07034464517,acct details 0777512438,Jamila Abubakar Bello,Access Bank._

*Send ur evidence via this number 07034464517,kada ki turo ta wannan layin 08160508316.saboda layin zai kasance kasa...siyen nagari maida kudi gida.*


_Yar Mutan Kankia ce❣️_


Share
Pls

*Kada kifitar mani da littafi waje Sadaukin Burhaan na kudine akan naira dari Ukku domin karin bayani tuntubi wannan layin 07034464517*
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment