Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa akan kyawun sa tun bai damuwa da irin kallan da suke mashi harya fara tsarguwa da kanshi,sadda kanshi yayi kasa yaci gaba da tafiyar shi har ya isa sashen Ammar neman izini yayi hadiminsa yai mashi iso zuwa wajen shi a falo ya iske shi zaune.
tunda Sadauki ya taho Ammar ya rasa natsuwar shi baki daya kallan bege da so yake masa..yana iskwa gaban Yarima Ammar ya duka ya gaida shi sannan ya dauko kaya yabashi yace."inji Ado yace inkawo maka."hankalin Ammar ba akan aiken Sadauki ya ya mika masa yake ba baki daya yana kan fuskar shi yagama shagala da kallansa yanda yaga yaki karba hakan yasa ya dago kansa a hankali ya dubi Ammar yaga kallan shi kawai yakeyi yarasa dalilin dayasa mutane ke kallan shi irin haka kodai yana da wani aibun ne a jikin shi shima kallan kanshi yakeyi saidai baiga abunda suke kallo a jikin shi ba.....
Sadauki yata shi zai tafi batare da ya jira umurni daga Ammar din ba."Tafeedah."yakira sunan shi take saida yaji kirjin shi ya buga jin kalmar Ammar ya ambace dashi cigaba da tafiya Sadauki yayi batare da ya dawo ba da sauri Yarima Ammar yasha gaban shi."bakaji ina maka magana."? Dan rufe manyan idanuwansa yayi ya bude yace"Sunan daka kirani da shi ya sakani rudani....abinda nasani sunana Umar kuma ni bawa ne."mamaki karara saman fuskar Ammar yasan dai baiyi kama da bawa ba bako shakka ya hada jini da jinin sarauta ko masu tarin arziki yanayinsa kadai ke fallasa nasabar sa."kafadaman gaskia dai."?"Iyakar gaskyar kenan abunda na sani ma fada maka."sake maimaitamin abinda ka fada."dan murmushi ya saki wanda ya kara bayyana usulinsa da kyawunsa yace."Umar sunana kuma ni bawa ne."ba dan an aminta dakai ba amma zaka iya tafiya."a hankali ya dan karkarto da kansa ya dubi Ammar kallo daya ya sake cire kansa gefe yace."ka tambayi Ado zai baka labarina."
Har yanzun zuciyar Ammar ba harbawa badan komai ba yana mamakin lamarin Umar aransa yana ayyana abubuwa da dama aransa."haka Allah ke halittarsa kayimani kama da wani abokin arzikina sunan shi Tafeedah saidai ba anan garin yake ba garin su da nisa gaske a kasar Cameroon yake cikin Masarautar Burhaan."du da kasancewar Sadauki na cikin yanayin asiri hakan bai hana gaban shi faduwa ba ya tsananta faduwa sosai ya shiga cikin dogon tunani amma yakasa tuna komai....saima aikin kallan Ammar din yakeyi kamar wanda ya rasa wani abu nashi....izinin tafiya yai mashi."shikenan Umar zaka iya tafiya saidai zan nemeka zuwa wani lokaci."gyada masa kai yayi sannan yai mashi godiya ya tafi.
ranar Ammar kwana yayi yana tunanin Umar yayi mamakin yanda yayi Kama da Tafeedah,sai tuno ranar da sukazo wasan da'ba yakeyi.
shiko Sadauki koda ya koma daki ɗan gutun bargon shi ya shimfida ya kwanta,sai tunanin maganar da Ammar yai mashi yakeyi har yayi bacci bai tuna komai ba,wannan kenan.

Zaune take a dakin gimbiya Bilkisu sai murmushi takeyi ita kadai da kaganta zakasan tana cikin farin ciki,sai magana gimbiya Bilkisu takeyi mata saidai baki daya hankalin ta ya tafi wajen tunani har saida ta taba ta sannan ta dawo cikin hayyacin ta."lafiyar ki kike tunani irin wannan? inata magana amma baki jini ba?" shagwabe fuska Gimbiya Zubaina tayi cikeda sangarta tace."Ummi walahi tun shekaranjiya nikejin nishadi a raina narasa abindake damuna,kulun ina cikin farin ciki da nishadi."hmm ya'ta kenan fadaman miyasame ki na farin ciki."murmsushi tayi tace."kiyima yarki addu'a kawai....ina son zuwa wajen Anty Mabaruka ina kewarta sosai."da shashantar da zancen ta hanyar kawo labarin Mabaruka."da kin kyauta saidai kinsan Abban ki bai son kina masa nisa."Ummi nasan bazai hanani zuwa wajen Antina ba"Allah yasa." "Amin Ummi."sake gyara kwanciyar ta tayi tad daura kanta saman cinyar ta tace."yaufa nan zan wuni wajenki bansan hayaniya zan shiga daki in kwanta."yakamata kici abinci."nakoshi daga wajen Anti Mufeedah na gudo,ita dole saina tayata aiki yaya Aryan, zaiyi baki."shine ko kitayata."haba Ummi duk hadimanta saina tayata aiki dazun muke abu daya nagaji shiyasa na gudo nan in huta."Kema watarana kinaso atayaki aikin ai"idan na huta anjima zanje intayata."shikenan ya'ta ki huta lafiya."
*********************
Wai kai yaushe zaka daina wannan damuwar iyeh? bakada aiki sai yawan tunani gaskia muddin bazaka rage wannan damuwar ba ranka ne zai mugun baci."kiyi hakuri Umma narasa yanda zan cirema kaina wannan damuwar saidai nakasa kullin raina nabani Juwairiyyah na cikin damuwa,gasu Ammi suma suna cikin yanayi...wallahi Umma ko bacci nike sai Sadauki ya fadomani a cikin zuciyar ta"Hakuri zakayi Mukhtar addu'a kawai zamu dinga yimasu yafi wannan damuwar? jiba kaga yanda ka koma ko abinci baka san ci duk kayi baki ka rame...gaskia banjin dadin ganinka a haka indai kanasan kaga farin cikina yakama ta kadaina wannan damuwar."shikenan Umma inaso insamu lokaci in kaima Umman Shattimah ziyara."daka kyauta gaskia...yanzun dai yakamata kaje kahuta hakanan."Toh Umma sai anjima."Haka rayuwa takasance ga Tafeedah baida wata walwala balle ya samu sukuni tunda ya baro Burhaan yakasa samun nutsuwa sai yaga kamar akwai abinda ke faruwa da yan uwan shi......
Akwana atashi yau ake sunan Asma'u ba kananan kuɗi Shattimah ya kashe ba shida Malan Audu sukaje kasuwa suka sawo duk abinda ake bukata ko rago saida ya yanka ma Asma'u ukku,kamar yanda kuka sani yaro yaci suna Ahmad.gayyatar mutane malama Zaliha tayi duk wata mace dake kauyen nan saida ta shaida sunan Ahmad akaci kasha har akabar shi ko washe garin suna bayan angama soye saida Asma'u tasa Zaliha ta dibe nama ta aika mutanan karkaran nan, sannan ta dibarma mutanan gida,wata katuwar silba ce ciki akasama Shattimah yasamu wani waje ya juye haka kowa yaita farin ciki nan mai jego taci gaba da samun kulawa ta musamman.
--------------------------
Sadauki ke sallama da gimbiya Zubaina yakai minti shabiyar tsaye bata fito ba baki daya ya gama kulewa wannan zuciyar na nan ba abinda ya sauyata koda ta fito cike da izzah gamida kasaita ta isa saman killatacciyar kujerarta ta zauna wadda ta kawati da ado.na lu'u lu'u da jawhar a jikinta.
kallo daya tayi mashi ta kauda kai,yanda taga yasha mur ya turnike fuskarsa ba alamun annuri a cikinta saima ya kara mata kyau,takai minti biyar zaune amma Sadauki bai bi ta kanta ba bare yaje wajenta yakai gaisuwa saida taga yaki karasowa inda take sannan ta kira shi...."Umar bazaka isoba koni zanzo in sameka anan."sai a lokacin ya iso inda take saidai ko kallan ta baiba balle tasa ran gaisuwa a gareshi....kayan wankin ya mika mata hakan ba karamin bata mata rai yaiba,daga tsaye ya bata kayan.....da masifar ta ta rufeshi"waikai wane irin mutun ne kanada hankali kuwa? gimbiya Zubaina kake ba kaya a tsaye ko da'a babu? meyasa kake son batamani rai ne wai?baka iya gaisuwa ba? baka mani magana cikin biyayya a matsayinka na bawa na!ya kake so inyi maka ne."?kallan ta kawai yakeyi mamaki take bashi shi baisan me take son yaimata ba, tasa shi aiki yayi me kuma mi take so yai mata."kiyi hakuri."Dago kyawawan idanuwanta tayi ta daura masa tanajin wani irin nishadi na ratsata wanda takasa gane na minene ya bata mata rai amma kuma ta gaza hukunta shi."yanzun me kike so in maki."?ya tambayeta batareda ya sake kallanta ba"Ohni Zubaina wannan wane irin bawa ne mai yawan miskilan ci shidai ko magana zai mani a takaice yakeyin ta daganin shi baisan yawan magana...kuma tunda yana bawana ai baida wani zabi."a zahiri tace."inaso duk bayan wasu lokuta kadinga zuwa kana gaidani ba lallai wanki ne kadai aikin kaba,yanada da kyau ace kana cikin hadimai na masu kulawa da duk wasu bukatu."Ohh ni Umar wannan yarinyar ta cika san izzah da gadara kodan taga tanada kyau shiyasa take nuna isa? nifa bansan aikin wahala wai duk inda zata inbita tana mace sai kace wani akalan ta "Me kace? "Allah yakaimu." Murmushi kawai tayi mashi duk abinda yace taji shi,shima sai ya tsinci kanshi dayi mata murmushi.....
Wanda yai silar tsayawar numfashinta na wucin gadi ta rasa dalilin dayasa Umar ya shiga ranta ba kadan ba bata san taga ko faɗa tanayi mashi....kaji wai shi baisan wahala daganin jikin ka yasaba jin dadi amma ko ya'akai yazo a bawa ikon Allah....aranta take sake sake duk akan Umar din."zan iya tafiya?"Ba damuwa."ta bashi amsa tana ci gaba da kallansa."godiya nike uwar gijiya ta,ki huta lafiya."gyada mashi kai kawai tayi gashi tanasan taji amon muryar Umar din yana magana kasan cikakken namiji ne yayi maganar daman tana saon Jarumin na miji gaskia Umar yayi saidai bawa ne.....

yau gimbiya Mabaruka ta tashi da nakuda cikin ikon Allah batafi jimaba ta haifo yarta mace kwakkyawa da ita ba karamin farin ciki Haidar yayi ba, tsabar murna ranar ko Mabaruka tasha kyautuka,daman shi yafisan diya mace a rayuwar shi ya dauki son duniya ya daura a diyar tunda aka haifeta da kyal yake ba yan barka ita kullin tana hannun shi kamar ya hadeta dan kauna
```Hmm wayaga su Haidar anzama Abba Allah ya raya`
******
Yau ake sunan 'yar Safiyyah kai kace ba'a komai Hamza ya hana taron suna dan kawai an haifi mace ko ragon suna kin siya yayi ga duk kudin data tara a wajen Sadauki ya anshe ya cinye saidai Jarmai shi ya siyo mata rago daya ya yanka mata aka sha sunan Kursiyyah tana cemata Amira...ita kanta Safiyyar duk ta rame tayi baki sabida bata samun kulawa ko kadan tunda ta haihu danma tana samun dan rangwami wajen Umman ta....

Zaliha ce keta kuka yau su Asma'u zasu wuce hatta Asma'un kuka take saboda ɗan zaman datayi dasu har sun saba wanda yau kwanan su ashirin da daya da haihuwa kimamin sati ukku kenan amma ji sukeyi kamar sun shekaru aru aru tare.
Shattimah ya basu kudi masu yawa sannan sukai ban kwana ya daurata a doki,ya anshi ɗan ya rungume a doki sukaciga ba da tafiyar su.....

Baki daya bayin Burhaan tunda akai addu'ar bakwai na Yusrah kullin sai sunje fa'da sunyi zanga zanga wanibi Hamza ya kyalle su,wani lokacin kuma yasa aita dukan su amma hakan bazaisa su daina ba duk sun kara zama abin tausayi,tsabar rashin yan'cin da suke fama dashi a cikin Burhaan.....

Labarin haihuwar Mabaruka ne ya karade Zairana sai murna akeyi yau kimamin kwana biyu kenan da haihuwar.
gimbiya Rukayya tacema Zubaina ta shirya zasuje Agadas suga jaririya....
tana murnar zuwa taga yar uwarta da jaririyar su,amma zuwa yanzun tasaba da Umar bata san yana mata nisa ta fahimci idan tana ganin shi yana sakata nishadi saidai haryanzun ta rasa dalilin hakan...amman tafi ganin kawai dan yanada kwarjini da haiba shiyasa.....

Tofah wata sabuwa inji yancaca nikam in akalar Zubaina ta fuskanta ko kusan abinda take nufi sai naji daga gareku.

Shiri kawai gimbiya Rukayya takeyi yau zasu tafi Agadas wajen Mabaruka dan ko Sarki Abdurrahman haka ya hada sha tara ta arziki yace aikaima diyar shi,gimbiya Amina ba abarta abaya ba ita tahada kayan uwa...

Abangaren Zubaina kuwa jitake kamar karta tafi batasan Umar naimata nisa ko kadan ganin shi nakara debe mata kewa tunda Fadila ta hadama uwar dakinta kayanta take ta dube dube ko zataga Umar ya shigo amma shiru kuma har magana saida taimashi akan ya dinga shigo wa akai akai amma baizoba, wannn dalilin ne yasa ta kudurci a zuciyar ta lallai saita yima Umar wulakanci ta fahimci baibin dokokin ta,yana bawanta zai dinga bijirewa umarnin ta.
har Mai martaba ya aiko ta fito ita ake jira amma Umar ba amo ba labari haka ta fita duk batajin dadin jikin ta,ta fahimci Umar ya shiga ranta kuma tana tausayin shi abinda bata taba jiba akan dan Adam sai akan shi yanzun tana kimanta bawan ta, gaskia wannan lamarin na damunta,harta isa sukayi sallama da Mai martaba suka kama hanya.
kafin su fita kofar Masarautar zairana ta hadu da Umar ya guyo uban itace abayan sa zaikai madafa inda akema bayi abinci kallan shi kawai takeyi a take taji tausayin shi,kuma taga sun hada ido dashi tana kan doki,saidai shidin ko kallanta bai kuma ba bare tasaran zai gaidata,gashi dasu Umman su take balle tayi mashi magana.
haka Zubaina ta tafi tana mamakin halaye irin na Umar shidai mutun ne wanda duk mulkin ka ko arzikin mutun bai damun shi,balle yadinga yimaka daddoha yana kamun kafa,kamar yanda sauran bayi keyi,ba abinda yake hada shi da Zubaina sai gaisuwa,yaimata aikin da ta sashi.
daman shi baisan yawan magana ko kadan shiyasa bai shiga harkar kowa, sai Abba Ado shima ya dauke shi mahaifin shi, shiyasa wasu bayin ke ganin cewa Umar ya fiya girman kai dan yana ganin Allah yai mashi kyakkyawar halitta shiyasa yake ganin kamar yafi kowa,dan ma yazo a bawa aida abinda zaiyi sai yafi haka....
(Allah Sarki da kunsan waye Umar da baku fadi hakaba mutumin da ya manta kanshi da kowa nashi taya zai san abinda ake kira girman kai? Kawai dai rashin son magana jinin shi ne da kasaitar da kuke fada duka)

_Yar Mutan Kankia ce❣️_

Share
Pls

*SADAUKIN BURHAAN*
_(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_
A Kingdom Story👑

*NA*
*JAMEELA JAMEEY*
_(Ya'r Mutan Kankia)_

*BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM*

_SHAFIN KYAUTA_

BABI NA SHIDDA

Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300) Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello.shaidar biya ta 08160508316.

Ku hanzarta ku mallaki naku domin wannan tafiyar ta dabance,na tabbata bazakuyi dana sanin siyen sa ba,kunji salon Izzah ko Mulki to yanzun wasan zai soma domin ba'ayi komai ba,kedai ki kasance da Jamila yar mutan Kankia🥰

Zuwa yanzun gimbiya Masa'uda ta addabi rayuwar Hamza banda zagon ƙasa ba abinda takeyi masa ba kadan ta saki jikinta da bayi ba hakama talakawan Burhaan badan komai ba kawai dan ta cimma burinta.
shiko Hamza yabi ya damu kanshi akan labarai daketa yawo akan abinda Barde ya aikata ya ketawa BAIWA haddi magana ta karade illahirin kasa da kewayen kasar Burhaan da,harya fara samun sakonni daga sassa daban daban na kasar Cameroon da sauran Masarautu daban daban dan tabbatar da gaskiar lamarin da ake shashi fade akai....
kuma yasan ba mai mashi wannan tuggun kamar Masa'uda shiyasa yasa a ranshi sai yayi maganin ta.
Koda su Zubaina suka isa cikin Agadas baki daya tarasa mike mata dadi danma ganin Umman ta shiyasa ta saki jikinta dayake ita ranar zata koma Zubaina da gimbiya Rukayya su za'a baro,tunda suka iso Haidar ke murna yanata dawai niya dasu,har yanzun idan ya kalli Zubaina saiya kara yabawa da kalar baiwae da Allah yaimata shidai yana kaunar Zubaina duk da ya fidda son ta a zuciyar shi amma yasan kaunarta ajinin shine,ba karamin fira sukeyi da Zubaina bana yana jin dadin yanda ta saki jikinta da shi fiyeda Da.....
tafiyar da Shattimah keyi da Asma'u harta fara gajiya amma sai yace mata saura kadan su isa....
_Ko ina Shattimah zaikai Asma'u,a sannu dai zamuga manufar shi_

Sadauki ne zaune a dakin su,inda Abba Ado ke kara fadama shi kalar rayuwar Masarautar Zairana da kuma irin dabi'un uwar dakin shi....shidai mamakin ta kawai yakeyi yanda bata da ragi ko kadan a rayuwar ta,shidai bai son mutun mai yawan faɗa amma yasan tanada nata tsarin shiyasa takeyin hakan."kaji abubuwan dana fada maka?Umar ka kiyaye ka zamto mai yawan ɗa'a da biyayya ga uwar gijiyar ka duk abinda ta saka kada kayi mata musu sabida gimbiya ta tsani musu kuma tana son agirmamata sannan tana son a martaba izzar ta." "naji Abba..ni daman bansan hayaniya bazan yadda in shiga harkar taba bare tayi mani ihu."hakane amma kasan aiki da mace duk yanda kake kiyayewa saika kara hakuri da ita."Shikenan Abba zan kula."yawwa dan albarkana...yanzun dauki abincin ka kaci."minene wannan abun Abba."?Murmushi Ado yaima dan nashi yace." wasa-wasa ce nasan zatayi maka dadi."shima murmushin yayi yace"Gaskia ta burgeni dagaji zatayi dadi."kardai ace baka taba cinta ba Umar."? wani irin faduwar gaba ya riske Sadauki sai ya rasa amsar da zaibawa Abban nasa......
Gyara zamansa Ado yayi ya fuskance shi da kyau yace."niko ina so insan kai dan ainahin inane?wane gari kake."koda Sadauki yafara cin abincin shi ajewa yayi yana kallan Abba Ado......
yaka tsareni da kallo har haka lafiya."? "Kai zanyi ma wannan tambayar Abba!waye ni?daga ina nike?Menene asalina."?shekeke yayi yana kallansa cikeda mamaki taya za'ayi mutun magidanci kamar wannan ace baison kansa ba gashi a zahiri ba ciwon haukane ya kamasa ba bare ace baida hankalin da hankalinsa ras ya akai hakan ya faru?rasa amsar da yake nema yayi yaci gaba da kallansa."hmm!banda wannan amsar Abba abinda nasani sunana Umar kuma ni bawa ne! wanda ya saba da wahala marar 'yanci bansani ba ko zaka gamsu da ansoshin da na baka."numfashi mai zafi ya shidar har yanzun baice ma Sadauki komai shima ajiyar zuciyar ya shidar yaci gaba dacewa."bansan kalan wannan tambayar Abba tunda banda amsar su,amma kai idan ka sani ka sanar dani dan Allah waye ni."?
Hawaye kawai Ado yakeyi daman shi yadaɗe yana tunanin Umar bai cikin hayyacin shi duk wanda baisan waye shi ba ai dole a tausayama shi da gani akwai lamari mai girma dake tattare dashi....

Sadaukin Burhaan na kudine akan Naira dari Ukku(300)domin karin bayani tuntubi wannan numbar 08160508316.siyen nagari maida kudi gida.

tunda Tafidah ya tashi ya gama shiryawa zai tafi wajen Umman Shattimah yana so ya ganta sallama yaima mahaifiyar shi sannan ya hau dokin shi ya kama hanya,saidai daka ganshi zaka san yana cikin damuwa duk ya rame yayk duhu.....
tunda Allah yasa aka fiddo su Ammi domin suyi aikin bautar da suka sabayi anan ta hadu da diyarta duk tayi baki ta lalace ta rame ga wani irin mugun zazzabi da take fama dashi amma duk da haka saida aka fiddo ta dauke take da wani dargagen dutse zasu kaishi a wajen aje kayan itacce da manyan duwatsu....daidai ta kusa isa wata irin juwa ta dibeta take fadi saman dutse ya fasa mata hannu jini ya fara zuba da sauri Ammi ta rugu ta rungume yarta ga Asthmar ta,ta tashi daman muddin tayi aiki mai yawa sai tayi kamar ta kasheta haka take mata.
kamar jira wani katan dogari yazo yaita buga masu wata gurɗime miyar bulala ba Juwairiyyah hatta Ammi jitayi kamar ta mutu haka yasasu tashi amma Juwairiyyah bata iya ko mikewa,bako tausayi yacigaba da bugunta kamar jaka ko daga hannun ta bata iyawa,da Ammi taga zai kashe mata diya da sauri tazo ta rungume ta sai kuka take,ita ko Juwairiyyah tashin hankali yasa ta suma,duk da haka dogarin nan bai fasa dukan suba saida wani babban bafade yazo ya hanashi sannan ya sahirta masu.
wasu bayi ya kira yasa suka dauki Juwairiyyah suka kaita wata inuwa, nan yasa Ammi tacigaba dayi mata fiffita,ko wane bawa saida ya zubdawa su Ammi kwalla wai yau uwar Sadauki ce akema wannan ukubar sai kace bata a kowa,rayuwa kenan.....

gimbiya Zubaina a cikin maroon din lace tasha kyau kamar wata amarya anata shagalin suna kai kace itace mai jegon kaya kala daya sukasa da Mabaruka sai zolayar Zubaina ake wai jaririya taci sunan ta lallai soyayya tayi riba...shiko Haidar ya rike hannun matar shi cike da zolaya yace."ga karshen soyayya nan...kawai dai kyautata wane,kuma bai kamata amanta wanda ya hada aikin alkhairi ba." ita dai Zubaina ta rike yarta sai murmushi takeyi duk wanda ke wajen nan saida yayi tubarakallah domin kullun kyawunta kara bayyana yakeyi yanzun take kara zama budurwa.
ranar haka aka wuni ana shagali har dare baki daya Zubaina tagama gajiya tana wanka kwanciya kawai tayi amma ta gagara bacci Umar ke fado mata a rai,miyake yi?yaci abinci ko baici ba?abinda taje sakawa aranta kenan ta rasa yanda akai ta damu da bawan nan har haka?kafin wani lokaci har bacci yai awan gaba da ita.....


_Yar Mutan Kankia ce❣️_


Share
Saboda Allah

*SADAUKIN BURHAAN*
_(Daukar Fansa_ _Cigaban Izzah ko Mulki )_
A Kingdom Story👑

*NA*
*JAMEELA JAMEEY*
_(Ya'r Mutan Kankia)_

*BISSIMILLAHIR RAHAMIRRAHIM*

_SHAFIN KYAUTA_

BABI NA BAKWAI

Sadaukin Burhaan na kudi ne akan Naira ɗari Ukku(300)Acct details 0777512438 Access bank,Jamila Abubakar Bello kituro shaidar biyan ki ta 08160508316.

Waziri Bashir ne daure kamar wani barawo an riko shi sai dukan shi akeyi ba inda aka gurfanar dashi sai sashen Hamza a kishingide yake ga bayi da hadimai sunatayi mashi hidima,kamar ba gobe.
Tunda aka shigo da Basheer ya duka gaban galadima Hamza,duk wanda hamza ya kalla sai yabar falon a sanyaye saida ya tabbatar da kowa ya watse daga shi sai Basheer sannan ya dauko kofi ya zuba ma Basheer dafaffiyar madara sai kamshi takeyi ya mika mashi cike da izzah gamida tsantsar gadara....kallan kofin kawai yakeyi saboda yasan halin Hamza zai iya anfani da wannan damar yaga ya halaka shi."karbi madara kasha koba komai kana bukatar hakan"Aaa nagode ko can bani shan madara."Hmm Basheer kenan dadai bansan waye kaiba,kaga malan umurni nike baka ka maida hankali kasha madarar nan tunkan nasa ka cikin ukuba...inda ina son inkasheka bata hanyar baka madara zanyi nasaraba nabarka ne don kagama shan ukubar duniya sannan ka tafi barzahu kaga Basheer sha madara."yana kyarma ya karba don yasan ba imani Hamza ya cikaba kuma idan yayi magana bai canzawa shiyasa ya karba abinka da maijin yunwa cikin kankanin lokaci har ya shanye madarar nan tas saidai kofin."kokaifa Bashir kasan shi mayunwaci bai jimirin ungu....ka taimaki kanka dan ba abinda Hamza zai fasa kamar yanda kasani meyasa nabada umurnin akawoni kai nan basai mu dinga jayayya dakai, muddin kasanar dani gaskia nayimaka alkawalin zanbaka makudan kudin da harka mutu saidai kaci abinda kaci amma bazasu kareba zan hada maka da jauhar da tarin lu'u lu'u da ingantacciyar azirfa da zinariya zan baka jajayen rakuma har guda goma,da tarin shanuwai da dawakai masu nagarta,sannan zaka dauwama a matsayinka na waziri a cikin Burhaan har abada.....Basheer ina zoben da yaya Abduljalal ya baka."?ya ida maganar yana murmushu.
(lallai kam ni Hamza zaima wayo natabbata koda na bashi duk wa'anan alwakalin da yayi bazai mani suba daga karshe zaisa a kashe ni...abin takaicin ma ya maida mani iyalina bayi....kuma bazan iyacin amanar aminina ba,koda zan rasa raina.)"ya da shiru Basheer."? Katse masa saken zucin da yakeyi ta hanyar tambayar shi"Allah yataimakeka ya jada tsawancin kwanan ka Allah ya damkamaka mulkin Burhaan kaifa uban gidana ne walahi billahi da ace nasan inda zoben nan yake ba abinda zai jaman wahalar da kaina har in bata lokaci na mai matukar anfani a gidan Yari kala daban daban ga duka banda azaba da nike sha iri iri, kayarda dani bansan inda zoben nan yakeba da ace nasani da nabaka kodan in samu sa'ida kaiman lamani natuba"lallai Basheer da dai ace ba'a masarautar burhaan aka haifeni ba kuma da ace ba Sarki Muhammad ya haifeni ba da sai kafada mani wadannan kalaman naka walahi Basheer zuciya bata da saukin yaudara balle kayi tunani a cikin zuciyar nan akwai digon tausayi ko jinkai ba abinda bazan iya aikawa ba kaga Basheer karka batama kanka lokaci ka fito da zoben nan Basheer idan ba hakaba lallai zaka rasa ranka a banza a wofi kasa matarka ta shiga takaba, diyarka kuma tazama marainiya daga karshe haka zasu wahala kuma su wulakanta a burhaan kai kwara bayi dasu daman can sun san matsayin su,kuma yarka tazama abin hutawata da nishadantarwa hakama matarka,muddin kace zaka cigaba da taurin kai akan zoben nan wlh ko Abdullahi yace zai yi abinda kayi saina salwantar da shi,kagako dani dashi ba wani bambanci,balle kai da ba abunda ya hadamu sai yan uwantaka ta kakanni zan kasheka Basheer maganar karshe da zan maka ka fiddo mani da Zoben Zarri."
"Ohh ni Basheer ya zanyi gashi mutumin nan baida imani tsaf zaya dinga alfasha da iyalina sannan ya wulakanta su, ya zanyi nabani ni Basheer...gaskia bazan iya cin amanar Abduljalal ba yana bukatar taimakona kuma amana ba karamar al'amari bane,? ya Allah ka kawomin dauki."a zahiri yace."Allah yakara maka girma da daukaka karya bata dace dani ba kamar yanda nafadamaka sama da wata bakwai wlh banda labari akan zoben zarri,nasan matsayin shi duk yanda mutun yakai da girma da nuna isa ko son mulki muddin babu zoben zairri ba mutun ba zama Sarki saida rikon kwarya,da ace yana hannuna mizai hana ban bakaba,ai kai ka cancanta da zama Sarki ba wani sadauki ba.......

*Sadaukin Burhaan na kudine akan naira dari ukku domin karin bayani nemi wannan lambar 08160508316,siyen nagari maida kudi gida.*

_________________
Ba abinda

Please Login or Register in order to submit comment