Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muguwa ta riga ta bawa wani a gama, sannan aka kawomin raguwa, wlhy sai Allah ya sakami, kuma in sha Allahu sai kin kwashi kayanki a hannu".

    Tun daga lokacin usman ya kasa zaune ya kasa tsaye a gidan su uwani, a dole sai su rage kwanakin bikin da suka yanke".

    Gani haka yasa suka rage zuwa sati mai zuwa, nan usman ya shiga gyara gida, ďakin uwani yasha gyara da fanti, har bakin kofa saida aka bisa da farin alli, bakin kofa kuma shima aka masa siminti".

    Yanzu tsakani zainab da usman, magana mai daďi baya haďasu, gani haka yasa tayi yaji zuwa gida, sai dai bayi sa'a ba, sabida koda taje hakuri rakiya ta bata tace ta koma ďakinta, domin itama yanzu ta kanta takeyi, abinda zataci niman gagaranta yakeyi, hakan yasa dole ta koma, har usman ya rufe ďaki ya kwanta yaji ana bubuga masa kofa, kamar bazai tashi ba, sabida a lokacin har ya fara bacc, jin bugun kofar yaki karewa ne yasa shi mikewa ya buďe mata kofar".

       Suna haďe ido ya kwasheta da uwar harara, ba tare suyi wa juna magana ba, suka kwanta, da safe kuwa ya shirya zai fita da sauri zainab ta mike haďe da kiran sunarsa, ba tare daya juya ba, yace lfy?".

       Zaka fita baka bani kuďi kunu safe ba".

        Kije inda kikaje jiya ba tare da kin sanar dani ba kije su baki kuďi kunun".

    Me kake nufi usman?"
       Abida kunniki ya jiye maki to haka ne".

    Amma kasan idan baka bani abimcin ba Allah ba zai barka bako?"

       Ehh, kamar yadda kema Allah bazai barki ba".

     Allah ya isa".
  Ma uwarki".
Usman yana faďin haka yasa kai ya fice daga gidan".
Kwalla kwai zainab keyi, sabida magana ma ta gagateta".

   Ranar talata aka daura auren usman da aisha, (uwani), usman baki har kunni, gidan sa kuwa, en'uwansa su cika suyi fakil, habaici kuwa ba'a magana, hakan yasa zainab ta kasa fitowa daga ďaki".

      Da dare aka kawo amarya gidan mijinta, zainab tayi kuka har ta gaji, bayan mata suka watse ango da abokansu suka shigo,(na tabbata kowa yasan irin shegantakar da akeyi, idan aka rako ango, kunga kenan ba sai na bata lokaci wajen bayanin ba)" bayan su fita ne, usman sukayi abinda ya kamata, sannan sukayi alwala haďe da sallah raka'a biyu, bayan suyi ciye-ciye da lashe-lashensu, usman ya tambayi wani game da tsarki, duk ta bashi amsa, bayan su wanke baki ne suka kwanta".

     Wohohooo duniya, daďi kashe ni, aiki ga me yinta, idan bakayi bani waje nayi, tunda Usman ya fara romacing uwani gaba daya ruďewa yayi kamar wanda be taba kwanciya da mace ba, shi kansa bai san lokacin daya dauke zuwa bed ba, babu arziki usman ya tube uwani, sabida idan yace zai buta ta arziki ba lalla bane yasamu yadda yakeso, wani irin tsotso nono uwani usman keyi kamar zai haďiye su, duk uban kukan ta uwani keyi baisa usman ya kyaleta ba".

    Garin tsotso besan lokacin daya cijeta a nonon ba, ihuuuu tasa tana faďi zaka kasheni usman, saida usman yasha me isansa sannan ya koma ga H2 ďin ta, ihuu kawai uwani ke kwarrrrrrmawa, tani neman maceci, amma ai, domin usman yariga yayi nisa, ihuuuuu kawai usman keyi haďe da wani irin gurrrrrrrnani, kaman wani zaki,  tun uwani na iya magana har bakinta ya mutu, shiko usman ko a jikinsa domin besan ma tanayi ba"..

            Usman be kyele uwani ta huta ba, sai da yakai geji sannan ya sauka, a lokacin jikin uwani yariga yayi weak, jawota yayi jikinsa ya rungutme ta,tunda bacc ya daukesu basu falka ba sai takwas na safe".

     Usman ne ya fata tashi, yana tashi yaje yayi wanka sannan ya haďe uwani, saida ya taimaka mata taje tayi nata wankan".

        Lokacin zainab na kallonsu ta labule, har ta kasa tafiya usman ya dauketa zuwa ďaki, wani irin bakin ciki ne ya tokari zainab, batasan lokacin data fashe da kuka ba".

Saida sukayi sallah sannan usman ya dauki kofi yaje gun maishayi  ya siyo mata, suna sha suka kwanta, shiru-shiru da zainab taji ne, ga kuma uban yunwar dake addabanta, tun batayi niyyar zuwa tayi wa usman maganar abin karyawanta, har dai ta gaji da jira, dole yasa taje tayi sallama, ba tare daya tashi ba, yace lafiya?"

    Dan Allah kafito muyi magana".
Faďi basai na fito ba, ina jinki".
Kamar ta juya, amma idan tayi zuciya yaya zatayi da yunwar dake adddabanta".
Dole yasa tace kuďin abin karyawa nazo amsa".

Ba tare dayace komai ba, hamsin ya dauka ya hurga mata a kasa, yace shigo ki dauka".

    Batada yadda zatayi, dole yasa ta shigo, jin shigowarta ne yasa usman kara matse uwani a jikinsa, ita kuwa tana bacc batasan abinda suke ciki ba".

      Kwallane suka zubo wa zainab, da sauri zainab a dauka ta fice daga ďakin".

   Tun daga lokacin usman ya canza kwata-kwata, kuskure kaďan zainab tayi sai usman yasha magana, balle yanzu daya sani uwani cikakkiyar mace, gori da cin mutumci sai abinda ya mance".

      Kuma gashi koda taje gida rakiya bata bari ta zaune,hakan yasa al'amura suka taru suka cishewa zainab, ta rasa uwar tayinta".

       Ban garen rakiya da sadiya kuwa, kullum cikin takalan sadiya takeyi masifa, da shike ba shine a gaban sadiyan ba, yasa bata sauraran rakiya, talla kuwa da take dorawa su hauwa da Fatima duk ta sauke, dama rashin mataimaki ne yasa, amma yanzu kam alhamdullh, banda kayan abincin dasu bakura suka bata, ga uban kuďin da bakura ya bata, koda zata bukaci wani abu, shi isa yanzu batada lokacin rakiya, gani zata matsa mata, katanga tasa aka ja masu a tsakani, sai dai idan su haďu a bayi,ko gun murhu".

   Hakan ba karamin bakanta wa rakiya rai yayi ba, shi isa kullum cikin neman ta faďa takeyi, amma sadiya bata kulata, su jauwa da Fatima kuwa, duk safe sadiya ke turasu suje su gaida rakiya, sannan kuma har ruwa take sawa su ďiba mata, sabida yanzu batada wani yaro a gaba, shi isa sadiya take sawa su taimaka mata, amma duk rakiya bata gani, zagi da cin mutunci takeyi masu, idan su hauwa suje su faďi wa sadiya hakuri take basu,a cewarta wataran sai labari"..

      Satin usman da uwani huďu da aure, uwani ta fara zazzabi da amai,gani haka yasa usman tafiya sanar wa innarsa, bata bata lokaci ba,tazo, gani halin da uwani ke cikine yasa ta dauki uwani zuwa asibiti, suna zuwa gwajin farko suka gano ciki ne da uwani".

     Daga mmn usman da shi kansa usman ďin murna sukeyi, tun daga lokacin mmn usman ta hana uwani aikin komai, tace koda da wasane kaďa usman ya sake bari uwani tayi wani aiki a gidansa, idan zainab bazatayi ba, to kuwa ta kama kanta, domin yanzu zamanta a gidan usman tamkar taimakonta yakeyi, domin ko abincin da take cire masa ya is a tayi masa duk abinda yasata ba tare da korafi ba".

   Shagwaba kuwa a gun uwani sai abinda ta mance, shi kuwa usman ji yake kamar ya amshi cikin dake cikimta ďan taimaka mata".....

  ____________

Barno, tun bayan tafiya da akayi da hjy Khursum egypt, en'uwanta duk hankula be kwanta ba, en'uwa da abokan arziki kowa cikin jijimi suke, amma babu wanda yayi tunanin zuwa ya dubota, sabida ba'a nan nigeria bane, mmn Adyra ce kawai taso zuwa ta dubo er'uwanta, sai ita da shike ba ba wani haline da ita ba, sai dai karfin hali kawai".

   Hakan yasa ranar wata sunday aka haďa family metting, nan aka fasawa kowa abinda zai bayar, koda aka haďe kuďin ba wani mai yawa bane, sabinda hannu ba daya ba, hakan yasa leadre ďinsu yace tunda abin ya zama haka, gwama a tura masu da kuďin kawai zaifi, sabida yadda alhj ke hidima idan sha'ani ya tashi be kamata a zuba masu ido ba, washe gari ranar monday aka tura masu kuďin, koda daddy yaga kuďin ba karami daďi ne yaje ba, kiransu yayi daya bayan daya yana masu godiya".

    _en'uwa wai meshi kenan fa, ina kuma ga wanda bai dashi, balle ma duk kuďinka kogi baiki kari ba, taimaka wa en'uwa ba karamin daga maka daraja yakeyi a cikin dangi ba, kuma baka sani hakan nada daďi sai lalura ta sameka. Allah yass mu dace._

            ~~~~    ~~~~    ~~~~

   
                 _*EGYPT*_

Alhamllhh dukkan tsanani yana tare da sauki,ciwo ko kariyar arziki ba karamin jarabawa bace a gun ďan Adam, Allah idan katashi jarabtanmu ka jarabemu iya imaninmu, kuma kabamu ikon cinye wannan jarabawar Ameen Allah ".

     Ayau hjy Khursum take da wata biyu cifff a egypt ba tare da tasan inda take ba, zynah da Am'abuwa kai har da ma bakura su cika " ya"yan albarka,muddin hjy zata jikinta da kashi ko fitsiri to fa da bakura za'ayi aikin wanka kayan, dade da rana daya be taba ķyamar hjy ba, zynah ita haka,  yau cikin dare, daga zynah har bakura suna duke a kan hjy, dukkansu suna yi mata karatun alku'ani mai girma a kuune, bakura na kunne hagu zynah kuma tana kunne dama, Am'abuwa kuwa tana kwance ita da pakhryya suna bacc, sabida su gaji".

     Suna cikin karatun kenan babban yatsarr hannu hjy ya fara motsi, ba tare su lura ba, sukaci daga da karatunsu".

    Dama duk dare idan kafar Dr ya dauke haka suke mata, cannn kuma sai tayi motsi da kafa, a lokacin ne suka lura, zynah ce ta fara gani, hannu tayi amfani daga wajan nuna wa bakura, gani hakan suka kara zurrfafa karatun da sukeyi".

    Sunfi minti talatin sunayi, ba tare da hjy ta buďe ido ba, kamar daga sama sukayi tana faďin innalillahi wa inna'ilihi raju'un, iya kacin abinda hjy tayi ta memetawa kenan".

*Allah ka bamu yara masu sonmu ba wanda mu muke so ba, shisa a duk lokacin a bawa ko rokon Allah kada yace shi ga abinda yakeso, yana da kyau ka nimi zabin Allah, domin kuwa duk abinda ya zabar maka in sha Allahu shine alkhairi a gateka, ba sai mace kaďai kejin kan uwa ba, har da namiji, kai nimi masu albarka kawai.*

   Sannan daga zynah har bakura dukkansu kwalla sukayi, haďe da gidiya a gun ubangiji, amma basu daina karatun ba, hannnnnkali hjy Khursum take kokarin buďe ido, saida ta buďe sau uku tana rufe wa,sannan tazo ta buďe sosai, gani su zynah da bakura ne a kanta, hawaye kawai suke gangaro mata ta gefen ido".

Gani haka suma suka rungumeta suna kuka, a lokacin ne Am'abuwa ta falka, gani abinda sukeyi ne yasa ta saukowa daga kan gadon da take kwance tayo kansu, kamar a mafarki taga idon hjy a buďe, cikin kuka ta rungumeta".

    Nan bakura ya sanar wa daddy, sannan kuma yaje ya sanar wa Dr nan yazo suka canza mata drip ďin dake hannunta, kafin safe hjy har tafara magana, gani zynah yasa hjy jin kunya, domin a halin yanzu ta rasa gane abinda ya kawo zynah inda take, ita da take son gani Adyra amma kuma sai taga zynah ce ke faman aiki a kanta".

    Am'abuwa ta kira en'uwa da abokan arziki duk aka sanar masu,har da hjy Ashe, hjy Ashe najin haka ta fashe da kuka, washe gari ta isa egypt gun hjy Khursum, suna haďuwa da kuka hjy Ashe taje ta rungume hjy Khursum".

    
Idan kuma koma gida nigeria kuwa, tun daga lokacin da bakura suka tafi da hjy, be sake waya da adyra ba, duk da yana zuwa nigeria duba shago, amma beyi tunanin zuwa inda take  ba, iya kacinsa gidan zynah anan zaije ya kwana, har ma ya gyata mata gida kafin ya koma, idan kuma maganar bukata ne, acan ďin ai da matarsa yake, duk da ba shine a gabansa ba, amma tsakani mata da miji sai Allah sai dai idan basu samu gu ba".

      Hakan yasa ya tattara al'amarin adyra ya zuba a gefe, dan a halin yanzu ma har mantuwa yake kamar yanada wata mata amma maganar abinda yana sawa a siye a kai mata".

              Duk da kemar bakura yana dami adyra amma a ganita zudda wa kai mutunci ne ta dau waya ta kirasa, bayan taji labari yana zuwa nugaria amma be iya zuwa ya dubi lafiyar ta ba, tunda haka ya zaba wa kansa, itama bazata kira sa, koda shekara nawa zai yi, domin tasan koda ta kirasa tasan cewa zaiyi yanada mara lafiya, to ina ruwana da rashin lafiyarta, tunda ba uwata bace, tama mutu mana".

   Daga ban garen maiduguri kuwa, kullum suke waya da ummata, haka take zama tayi ta shirya wa umma tata karya, tana bata labarin jikin hjy, ita kuma umma tata duk abinda zata faďi tana yarda, sabida a duk lokacin da zasuyi magana, kamar wata me allalmusu, duk abinda zata faďi yana zuwa iri daya da abinda daddy yake faďi masu akan hjyn".

   Kwana hjy Ashe bakwai sannan ta dawo, jiki kam sai son barka, domin a hakin yanzu hjy tana iya komai da kanta, sai dai wanda baza'a rasa ba, su zynah da bakura basu dai bata tuwan addu'a tana sha ba, duk da rashin gani Ni'eemat a gunta yana damuta,amma tunda Dr yace ta daina yawan surutu yasa tabar abin a zuciyarta".

    A lokacin da mijin Am'abuwa yake zuwa duba hjy ne, tace ta haďa kaya tabi mijinta haka, ta gode Allah yayi mata albarka ya bata masu saka mata".

      Da shike ďan albarka ne yace ya yafe mata ta zauna taci gaba da jiyar hjy har lokacin da zata samu sauki, yanzu haka ma gobe zai koma gida Nigeria's nan suka sallama, kuďi masu yawa ya bawa Am'abuwa haďe da sallar saiya sake dawowa ďuba mai jiki".

    Ita kuwa Yah-na tunda aka kawo hjy tazo sau daya, ta tafi bata sake zuwa ba, har wannan lokacin".

     Bayan wata daya da jin saukin hjy aka sallamaesu, domin yanzu hjy ta dawo dai-dai, daddy yaso su biya germany su kara hutawa amma hjy taki, ďan haka suka kwashi kayansu gaba daya zuwa gidan Nigeria, suka inaso hjy Ashe ce da malah suka tar besu, daga airpot nan suka daukesu har gida, abinci kuwa kafin su isa hjy Ashe ta gama komai".

      Anan gidan su hjy duk suka kwata, har da su zynah, domin hjy tace su bari su huta kafin suje gida su kama aikin gyara"

   Kafin 12:PM gida ya cika ďangi da abokan arziki, matan abokan hjy duk suzo gaida me jiki, basu bar gidan ba,sai bayan la'asar, hjy Asiya ce ta kai har dare, sabida mijinta amini daddy ne sosai, taso zuwa egypt duba jikin hjy, abinda ya hanata zuwa, itama ba wani isasshen lafiya ne da ita ba, hawan jini ke damuta".

    Saida sukayi sallar isha sannan suka bar gidan ita da hjy Ashe".

     Koda adyra taji labarin dawowar su hjy, bata zobs sai ďayan washe gari sannan tazo, dai-dai da isowar en'maiduguri, hakan yasa gida ya sake cika fakilll da jama'a, gani haka yasa bakira daukar zynah suka tafi gidansu".

    Masu kuka suyi masu kuma jsjsntawa duk suyi, tsakani bakura da Ni'eemat kuwa sai ido, kamar akaya ta zuba ido tana kallonsa tana jira ya gaisheta, hakan yasa shima ya zuba mata ido".

        Su hjy da daddy suna ďaki, bakura yayi sallama, a ladabce ya zauna,  sannan ya meda dubansa ga daddy yace daddy inada magana da kai, amma Allah yasa ku fahimceni".

     Daga daddy har hjy suka tattara hankalisu su bawa bakura, nan bakura ya faďi masu yadda suke zaune da Adyra, da kuma yadda sukayi da ita a lokacin da yazo daukar ta".

  Himm kawai hjy tace".

Bayan sallar isha, lokacin duk su haďu a falo suna hira, nan hjy Khursum ta tada magana a gaban en'uwansu da sukazo daga gida msiduguri, har da kin zuwa jinyarta da tayi".

   Nan kowa yasa salati, itako mmn Adyra bata iya cewa komai ba, harrr sai da mutane daga gun sukayi shiru, sannan ta kira sunan bakura, bakura dake duke yace am'an umma".

Idan ka cika cikin uwarka da ubanka,inaso ka saki Ni'eemat saki uku"..............
Duk jama'an dake gun sukasa salati".

Umma taci daga da cewa, ke kuma dan ubanki daga lokacin daya baki takarda inaso ki nimi wata uwar amma bani ba, ke harrr kin isa ki raba mana zumunci, wlhy kinyi kadan".

Dan haka rubuta kabawa shege, take Ni'eemat tasa kuka tana faďin na duba umma, dan Allah kiyi hakuri ki yafe min".

  Mikewar da zatayi ta haye kan Ni'eemat, ta hauta da duka, anyi-anyi ta tashi daga kanta amma taki".

       Da kar aka samu ta sauka, gani bakura na zaune, beda niyyar tashi balle ya dauko paper da pen ya rubuta takarda yasa tayi kansa, da sauri aka riketa, dakar dakar aka samu ta hakuri,  saida komai ya lafa, hjy tace wa bakura ya kira mata zynah".

      Bakura na kiran zynah ta waya nan take tazo, da sallama ta shigo falon bayan su gaisa da baki ne, hjy dake zaune ta fara bayani, tanayi tana kuka, haďe da niman gafarar zynah, akan dukkani abinda ya faru a bayan".

   Babban yayi su hjy ce, tayiwa hjy faďi haďe kuma da nasifa, shi dan Adam ba abin walakantawa bane, kuma kowa da kagansa a rayuwa yanada ranarsa, to kare ma yayi rana balle ďan Adam".

Ita dai hjy batace komai ba, idan ba kuka ba babu abinda takeyi".

Itama zynah dake duke kuka takeyi tana fadi babu komai ns yafe maki, Allah ya yafe mana baki daya".

       Nan mmn Adyra tace wa bakura, daga yau, umarni take bashi, yadawo da Ni'eemat cikin gida su zauna tare da hjy, daga yau kuma kada hjy su sake daukar er'aiki, tunda ga Ni'eemat nan, idan kuma batayi ba, bakura ya zuba mata ido ya kyaleta har taji labarin, musamman zuwa zatayi da kanta ta hukunta shi, tunda shi ya kasa hukunta ta".

   Nan akasa dariya, masu jin zynah da wasa kuma sunayi".

   Washe gari duk suka shirya zuwa gida maiduguri, bayan tafiyarsu da sati daya, daddy da hjy sukasa bakura ya kira zynah,  sukace ta faďi duk abinda tasoke in har baifi karfinsu ba, zasuyi mata".

     Zynah tana kuka tace babu komai, ita dai dama damuwarta daya ne, ummata takeso ta dawo kusa da ita".

   Da sauri hjy da daddy sukace idan shine kada ta damu".

   Washe gari daddy yasa driver da bakura suka tafi dauko sadiya,  dai-dai lokacin rakiya ta biya wasu samari akan idan dare yayi, suzu su sawa sadiya da su hauwa wuta a daki".

    Hakan yasa rakiya tayi bakin ciki ba kaďan ba, ranar  bakura ya isa, washe gari suka dauki hanyar abuja, daga kayan sawa babu abinda sadiya ta dauka".

    Karfe takwas suka isa abuja, zynah tayi murna sosai, a ďakin hjy suka fara sauka, saida sukayi sallah sukaci abinci, sannan hjy tace zynah taje ta gyara masu side ďin da bakura yayi samarta ka, kafin a saman masu inda zasu zauna".

      Kwana Am'abuwa biyu da dawowarsi mijinta yazo ya dauketa suka tafi gidansu, duk a cikin abuja ďin ne".

   Bayan wata daya da zuwan su sadiya abuja, Allah yayi wa Asiya rasuwa, an kwanta da ita Amma ba'a tashi da ita ba".

Kafin sallar asuba duk aka sanar wa su hjy khursum da hjy Ashe, hjy Khursum ta dauki sadiya suka tafi tare, cikin ikon Allah itace da zynah sai wata mata dake area suka yiwa gawa wanka suka shiryata".

     Dama tun a kauye idan anyi rasuwa sadiya ake kira, tayi wa gawa wanka, sabida tanada ilimin addini sosai, hakan yasa ta koya wa zynah".

   Anayi bakwai kowa ya watse, yarage yara da babansu, babu yadda en'wan Asiya basuyi da alhj Husaini akan yabasu yara su tafi tare ba, amma yaki, dole yasa  suka bar yaran tare da babansu, da shike ba masu girma sosai bane, babbansu 15year ne da ita, sabida basu sami haihuwar da wiri ba, sai kanninta biyu,maza".

   Lokacin da zai koma bakin aiki a germany gidan su hjy ya kawo yaran, tun daga lokacin haka yakeyi, suma da shike su saba yasa basu damuwa".

     Daddy ya haďa hauwa da Fatima ya sasu makarantan su Zara'u yarinyar Asiya".

Hjy nada wata biyu da dawowa sannan Yah-na tazo, tun daga kofar falo, hjy ta hanata shiga mata gida, babu yadda ba'a da hjy ba amma taki, har saida sadiya tasa baki, gwiwa bibiyu Yah-na ta duka mana rokon hjy gafara, ga shohon cikin dake jikinta, amma be hana hjy yi mata faďa ba, da kuma nuna mata kuskurenta".

    Tawan Asiya biyar da rasu, ranar da alhj Husaini yazo gidan su hjy, lokacin sadiya tana falo suna hira da hjy yayi sallama, tunda ya shigo idonsa ke kan sadiya, gani haka yasa tabar gun, tana fita slhj Husaini yake tambayar hjy Khursum waye ita?"

   Bata boye masa komai ba, akan sadiya, alhj Husaini be tsaya su gaisa bama, balle suyi hira, ya mike ya bar gidan, yana fita ya kira daddy bayan su gaisa yake sanar wa daddy abinda ke ransa game da sadiya".

   Daddy yaji dadi hakan sosai, nan ya kora hjy ya sanar da ita, hjy Khursum batayi mamaki ba, sabida dama biri yayi kama da mutum, koda hjy ta sanar wa sadiya, sadiya bata musu sa, nan hjy ya fara zuwa zance, yara da rashin wayo, middu suga babansu yazo murna sukeyi sosai, hakan yasa koda maganar auren ya taso, ba karamin murna sukayi ba, samumman Zara'u sabida sadiya na koya mata duk wani abu daya shifi addini, alhamllh yanzu ta kara sani sosai ba kamar dah ba".

     Ita kanta zynah murna tayi sosai, bayan sati uku, ranar asabar aka daura auren sadiya da alhj Husaini, da dare su hjy Khursum da hjy Ashe suka rakata gidan alhj Husaini, kwana nan su uku da daura aure ya kwashesu zuwa germany, harda su hauwa da Fatima, haďe da nasa yaran"..

     Gani pakhryya ta tafiya ko ina, yasa hjy Khursum amsarta ta yayeta, a cewarta zynah ta huta da tsotso".

*******

Bayan wata biyar tun dare Yah-na ke nakuda, gani haka megidanta ya dauketa zuwa asibiti, nan akai ta fama, kwananta biyu tana labour daga karke har aka yanke shawarar za'ayi mata operatinon, cikin ikon Allah, saiga haihur yazo zanga-zanga idan banda kiran hjy babu abinda takeyi".

    Da kar aka samu baby ya fito, amma ta kafa, ba takai da akasan baby na fitowa ba, shi isa tashi wiya sosai, satinta ďaya sannan aka sallamesu, dole yasa aka kaita gidan su hjy, a lokacin ne ta kara sani uwa nada daraja da muhimmmanci, kara rokon hjy tayi gafara sosai".

          ~~~~    ~~~~~~

             _*kunci*_

  Tunda rakiya ta sami labarin
Sadiya tayi aure har ma ta tsallaka tabar kasan, yasa rakiya haďiyar zuciya ta yanke jiki ta faďi, gaba daya yanzu babu abinda ke aiki a jikinta, ita da gawa babu maraba".


Ba garen zainab da usman kafin uwani ta haihu zainab taga abu iri iri, daga gun uwani har gun usmab ďin, amma tun bayan haihuwar, hawalar da tashi, yasa gaba daya tayi sanyi da al'amarin duniya, yanzu haka koda usman ya taso zai yi mata walakancin daya saba, uwani ke hanasa".


Bayan wata biyar Allah ya azurta zainab da ciki, yayi da rakiya kuwa ta amsa kiran ubangiji, wanda a yanzu da haka zamansa mukeyi idan lokaci yayi".


****


A bangare adyra da bakura kuwa, ba karami sanyi tayi ba, hakan yasa ta roki bakura gafaran duk abinda tayi masa, shima kuma ya yafe mata".


Zynah kuwa dama bamai matsala bace, wanda tayi masu ma su yafe mata balle ita er'kallo, dykkansu bakura ya hadsu yayi masu faďa sosai akan su haďa kai, tun daga lokacin babu me jin kansu, duk da ba gida daya suke ba".



Please Login or Register in order to submit comment