Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta sake ta fito daga cikin motar idan ba ango ya iso ba,  tun tana game har bacc ya fara daukar ta, kamar daga sama taji ance idan kiga daga ki fito muje".

  A yadda bakura yayi mata maganar ta dauka mafarki takeyi, gani ba mafarki bane, shine ďin dai, dole yasa ta fito"..

A sanyaye ta fito, gani duk idanu jama'a yana kansu yasa bakura rike mata hannu har zuwa heght table, nan wasa ya tashi zanga-zanga, gidan uwa da uba su nuna masu gata sosai,  wasa bai tashi ba sai aroud threeAM sannan suka tashi".

Gidan hjy aka sake meda amarya, shi kuwa ana isa gidan sa ya nufa, yana isa gida, gani zynah tayi zaune tana game a wayarta, daga fuska da zasuyi suka haďa ido da bakura, take taji gabanta yayi mummunar faďi".

Da sauri ya kariso kan gado, kallo ďaya tayi masa yasata cewa, wannan kayan kuma fa, daga ina kamusu kamar wani ango?"

    Bakura yayi kamar baiji abinda take ba, hannu yasa ya amshi wayar dake hannunta ya ije agefe, sannan yace my zynah magana nakeso muyi dake amma da sharaďi".

    Zynah tace sharaďi kuma?"
   Eh sharaďi".

Saida ta tattara hankalinta gu daya haďe da zuba masa ido, sannan cewa ina sauraronka".

       Saida da ya mike ya cire malum-malum ďin dake jishi sannan ya dawo ya zaune, suna kallo juna hannu yasa ya kamo mata nata, shiruuuuu yayi na ďan wani lokaci, yana tunani ta ina zai fara mata bayani, kuma idan ya faďi mata, yaya zataji, gata da tsohon ciki, gashi nasha ji ana cewa ba'aso a rinka faďi masu abinda zaita masu da hankali".

   Kodai na bari har Allah ya sauketa lafiya ne, saina faďi mata? To idan tazo taji a wajan wasu kuma fa? Kai gara kawai na faďi mata da kaina zafi sauki da ace wanine ya gaya mata".

  Maganar zynah ce ya dawo da bakura daga tunanin da yakeyi, tace ina sauraranka".

    Dan Allah zynah inaso kiyi wa magana ta kyakkyawar fahimta, wlhy nima kaina dan babu yadda na'iya ne, kinsan duk abinda akafi karka akai dole kayi hakuri, kuma nasan ba komai yasa su hjy da daddy sukayi min haka illa sabida abinda na aikata ne,amma nidai dan Allah inaso ki fahimceni dan Allah my zynah".

Nasan ba lalla bane kiyi amanna da abinda zai fsďi maki, amma ni nasan har ga Allah gaskiya ne, kuma har cikin zuciyata".

       Zynah kin riga kin zama wani sashi, ko nace reshe a cikin jikin rayuwata, wanda nake gani idan ba dake ba, a gaskiya zan samu nakasu, ki fahimceni wlhy Allah ma sheda ne, banyi haka dan ci maki fuska ko wani kanci ba, nima kaina Allah ya gani tirsasani akayi"..

Cikin sojin da lilin da yasa yake jiro mata wannan zancen tace, babu komai daka ka damu".

   Saida yayi shiruuu na ďan wani lokaci sannan yace, ina ranar dana sallameki, zan tafi gida maiduguri ďin nan?"

Eh".
To maganar gaskiya duk abinda abinda na faďi maki ba gaskiya bane, maganar gaskiya shine, tun ranar da daddy ya dawo, hjy tayi masa magana akan aurenmu, shine daddy yace, tunda nayi abinda dakeso,dan haka suma bazan hanasu abinda suke soba, akan yasa suke yanke shawarar auramin er'kanwa hjy".

  Zynah ban masu musu ba, sabida nasan idan har naki yarda to karshenshi nasan zasuce sai dai mu rabu dake, ni kuma Allah ya gani, bazan iya rabuwa dake ba, kinji dalilin amincewa ta kenan".

   Amma dan Allah kiyi hakuri ki yafe min, na boye maki da nayi,plss".

   Duk da zynah najin babu daďi a zuciyarta,amma gani halin da mijinta ke ciki yasa ta ďanne nata damuwar,cikin nuna rashin damuwa tace ďan dan wannan shine duk zaka damu kanka?"

     Da sauri bakura ya daga kai yana kallonta".

   Idan sabida nine kada ka damu, babu komai, nina kaina nasan mu tafka kuskure domin bamu kyauta ba,shi isa duk abinda hjy tayi bani gani laifinta, domin ba hjy kadai ba, kowaye ďansa yayi masa haka, ba zaiji daďi ba, musamman ma idan kayi la'akari da babbacin dake tsakanina dakai, kai ďan wanine, ni kuma ba er'kowa bace,bakura nikaina nasan kai ba sa'ar aurena bane, wlhy harga Allah nayi nadamar abinda muka aikata".

Da sauri bakura yasa hannu rufe mata baki, yana faďin dan Allah ki daina faďin haka, domin duk abinda kikaga ya sami bawa rubutaccene, daga ubangiji, dan Allah banaso muna tuno abinda ya wuce, nafiso mu dubi gaba ba baya ba".

     Himm zynah tace, sannan taci gaba da cewa, nidai wani abu daya nakeso kayi min".

    Da sauri bakura yace, ina sauraranki".

      Abu daya nakeso kayi min, idan har nasamu haka a gunka wlhy muhammed ka gamamin komai".

  Muhammed ban taba sani daďin rayuwa ba saida muka haďu da'kai, ban taba sani meye soba saida na haďu dakai, muhammed ina tsoron ranar da zaka juya min baya, ko kuma ka canza daga muhammed ďina dana sani,muhammed ina rokon Allah ya barni dakai har karken rayuwata, a kullum nayi sallah ina rokon Allah kada ya nunamin ranar da zaka juyamin baya, ko gana canji daga gareka, muhammed banid"...

Da sauri muhammed yace, zynah duk na fahimceki, ni muhammed nayi maki alkawari insha Allahu, hakan bazai taba faruwa ba, kuma da yardan ubangiji zanyi iya kokarina wajan gani na kiyaye dukkani hakkinki da Allah ya dora min, kuma na gode da Allah yasa kika fahimceni".

       Nan yayi bata magana mai kwantar da hankali"

Washe duk wanda suka rako amarya, suka koma,sai mutum biyu da suka rage, kanwar hjy da kuma kanwar daddy, da dare aka sake kiran bakura faďi sosai sukayi masu, haďe da ďanka masa amanar *ADYRA*  bayan sallar isha suka dauki amarya da ango zuwa *KAURA DISTIRITE* a nan ne daddy ya kama masu gida".

     Koda suka isa gida saida suka kara yi masa faďi, sannan sukayi sallama, nan aka baro ango da amarya".

Saida ya rakasu daga nan ya rufe gida,sannan ya dawo ciki".

    Shiruu bakura yayi yana kallonta, shi kansa mmkin wannan irin auren yakeyi, amma to yaya zaiyi tunda shi yajawo wa kanta, dole ya dauki duk hukunci da iyayensu suka yanke masa".

Gani yadda ta zauna ko motsi batayi, yasa bakura sa hannu ya rufe mata fuska, da sauri ta kauda kanta alamar jin kunya".

    Kallo daya bakura yayi mata yasan Allah yayi halitta a gun, ďomin ko makiyanta bai isa ya kirata da mumuna ba".

     Domin shi kansa yasan bazai haďata da zynah ba, wajan kyau wayewa iya kyalliya, murmushi kawai yayi mata, sannan yace tashi muje muyi sallah ko?ba tare musu ba ta sauka bakura na gaba tana biye dashi a baya, suka shiga toilet ďin"

Itace fara yi bakura shima yayi, sallah raka'a biyu ya jasu, bayan su idar yayi mata duk tambayoyin daya dace, kuma ta amsa masa, mikeya yayi yaje ya dauko ledar da malah ya bashi, haďe da cups da plate, kazane da fresh milk, ya dawo, koda ya zuba babu yadda baiyi da ita taci ba,amma taki, daga karke dai da kansa ya bata a baki, saida ta koshi sannan yaci masa".

Bayan su gama ya kwashe kayan ya meda kitchen sannan ya dawo, shi ya fara wanka, sannan itama yace taje tayi, kafin ta fito har ya shirya cikin kayan bacc pinch colour yayi masa kyau sosai, sannan ya fito mata da nata irin daya ne da nasa".

    Koda ta gama kunya ne ya hanata, fitowa daga toilet ďin, gani shiru-shuri bata fito ba, yasa bakura lekawa, ganita yayi tsaye a toilet ďin, ba tare daya shiga ba ya mika mata kayanta tasa sannan ta fito".

   Bakin koda ta rabe ta tsaya, murmushi bakura yayi, sannan yaje ya kamo mata hannu har zuwa bed, saida ta kwanta sannan ya kashe light ďin dakin yayi addu'a ya kwanta".

     Can gefe takoma ta rabe, gaba daya ta kududune jikinta,  murmusawa bakura yayi haďe da  matsa dab da'ita, gani haka yasa tayi yunkura zata mike, da sauri ya rikota hade ya rungumarta,jin haka yasata kwanciya a jikinsa, tun yana magana sunajin numfashin juna har yakai ga haďewa, tun bakura nayi shi kadai, ta fara taimaka masa, daga nan wasa ya canza, lokacin da suka tube nicket ma basuda labari, saudai wani abin mmki bai daďe ba ya sauka".

 Be saka tabata ba har bacc ya daukesu, basu falka ba
har sai da aka fara kiran sallar asuba,".

  
      "Dama haka rayuwa take, yau farin ciki gobe akasin haka tunda sukayi sallama da bakura ta tafi gidan amarya take kuka, wanda ita kanta batasan dalilin kukan ba".

     Aroud ten hjy ta aiko masu da abin breakft, be wani ci sosai ba ya mike ya fice daga gidan".

  Tunda bakura yabar gidan bai sake komawa ba, har lokacin da er'uwan bbnsu sukazo sallamar Adyra, saida suka koma gidan hjy sannan suka haďu dashi, nan suka gaisa, sannan sukayi sallama, har airpot ya kaisu, suna dawowa ya sauke hjy, sannan ya juya da kan motarsa, kamar zai fita, gani hjy ta shige ya juya zuwa gun zynah".

     _shidai rami karya kurerene,nidai a tawa gani banga dalilin da yasa hjy taki faďi wa kowa bakura yanada wata baya ba,domin har ita kanta Adyra ďin batasan su biyu bane a gun mijinsu,yanzu duk ranar da Adyra ta gane anya kuwa Adyra zamansu zai dore ko yaya kuke gani wannan irin badakkalar zata kasance?. Shima kansa alhj Alaee baisan cewa hjy bata faďi ba nasan da shi zai faďi, amma koma menene dai zamuji anan gaba_

    Kwana uku da biki daddy ya koma  Germany, tun daga lokacin da bakura yabar gidan Adyra bai sake komawa da sunan kwana ba, idan yaje su gaisa shi kenan sai wani safe kuma, zai koma".

  Ita kuma tariga taci burin bazata tambayi dalilin sa na rashin kwanan da bayani, duk yadda takai ga bukata, amma tasan tunda ya ďanďana tasan dole ya dawo gareta, hakan yasa duk safe, saita dai-dai ci lokacin zuwasa, sai ta caba kwalliya, tasa kananu kaya wanda yake bayyanar mata da dukkani al'auranta a waje".

A tunaninta, zaizo inda take"
Shiko bakura ko a jikinsa, sabida duk da tsohon cikin zynah baya ganata biya masa bukata, a duk lokacin dayazo mata a shirye take data faranta masa rai, shi isa bayan zynah wata mace mata gabansa, domin duk abinda yakeso yana samu".


A kwana a tashi babu wiya a gun ubangiji, har su bakura sukai wata daya harma da kwanaki da aure, amma a zaman takewarsu kam babu canji, yadda dah yake zuwa ma yanzu baya zuwa, koda abu takeso, saidai ta kirasa ta waya ta sanar masa, shi kuma ya aiki yaran shagonsa sukai mata".

Abinda duniya daya ishi Adyra, hjy ta kira tana faďi mata tana kuka, salati hjy tayi ta sanar wa ubangiji, sabida a tunaninta ma yanzu ta samu cikin, za'a haifar mata jika, ďan so, ďan da kowa ya sheda bana bayan fage ba".

Bata tsaya su gama magana da Adyra ba ta tashe wayar, numbaer bakura ta kira, bugu daya ya dago, kazo gidan yanzu nan inaso ganita".

To kawai yace, saida ya jinkirta, sabida a lokacin yana gida gun zynah ce, yanzu bai cika nisa da ita ba, sabida yadda yaga cikinta ya koma kasa, da kuma a tarkardan scanning ya nuna bazata fi nanda sati biyu ba zata haihu".

Shi isa bayaso yayi nisa da ita, sabida haka kawai ma suje gidan hjy gaidata, hjy tayi mata koran kare, balle yace su dawo nan da zama".

Bayan minti talatin ya mike yayi yace wa zynah dake zauna bari naje na dawo".

Da sallama ya shiga, hjy bata bari ya karisa shigowa ba, ta bisa , wani irin bari tayi masa har sau uku, sannan ta hau zaginsa, bakura bai damu ba, sabida idan da sabo yaci ace yasaba da halin hjy, kuma ko tantama ba yayi yasan duk tanayi ne, kan Adyra".

Har gaginta ne yasa su Am'abuwa da Yah-na fitowa daga ďaki, gani hjy na faman zagin bakura da sauri tazo ta ďuka tafara bawa hakuri haďe da rokonta ta daina faďin irin wannan kalmar akan ďan data haifa, sabida uwace, duk abinda za farta kamar yankan reza ne".

Bakura na duke a gaban hjy, duk abinda takeyi, shiru kawai yayi kamar badashi takeyi ba".


Cikin fushi tace tashi muje, bai musa ba yabita, Am'abuwa tasa ta dauko mata hijab da key ďin mota, da kanta ta jashi zuwa gidan Adyra, suna shiga taga Adyra zaune a falo tana faman kuka".

Gani hjy ne yasata share kwallanta, ďukawa tayi har kasa ta gaida hjy, tani tana hawaye,hannu hjy tasa ta ďagota, kamota tayi suka zauna, bakura dake tsaye yana kallonsu kawai yakeyi".

Faďa hjy tayi wa Adyra, akan meyasa tun farko bata sanar da ita ba, tabari har suka kai wani lokacin? Adyra batace komai ba, idan ba kukan da takeyi ba".

Gani haka yasa hjy ta koma lallashinta, tana bata hakuri,sai taga ta numfasa, sannan ta koma kan bakura dake zaune, idan har zai yaci amanar Adyra, bai bata hakkinta ba, Allah ya isa tsakaninta dashi, sannan kuma ta haramta masa fita har na tsawon sati biyu, ko bakin kofa ya leka Allah ya isa bata yafe masa ba".

A fusace ta mike ta fita daga gidan".

Hankalin bakura ba karami tashi yayi ba, sabida yadda yabar zynah, gashi kuma baya batada kaďan".

Ko kallo Adyra baiyi ba, ya mike zuwa bedroom Am'abuwa ya kira, ya sanar da ita yadda sukayi da hjy, sannan yace dan Allah ta taimakesa ta rinka leka masa zynah".

Tun daga lokacin Adyra take samu abinda takeso, amma daga wannan babu wani abinda ke shiga tsakaninsu".

Baya kulata, baya hira da ita, duk irin abinda zatayi bakura bazai taba daga ido ya kalleta ba' a cewarsa ba wasa da ita hjy ta turosa yayi da ita, sex ne kawai akace yayi, kuma shi yakeyi".


Wani lokaci tana bacc takejin mutum a kanta, kuma gashi ya fara babu sauki, domin koda karuwace iya kacin abinda za'a mata kenan, da bakura ya surfafeta kafin kwana uku duk ta rame, gashi duk lokacin da suke bakin aikin idan har zata buďe baki tace akwai zafi, a lokacin zai kara zurfafa abinda yakeyi mata".

Ranar da suka shiga kwana biyar, dukawa tayi gwiwarta bibiyu tana rokonsa, ya tafi haka, ta hakuri da abin, dariyan keta bakura yayi, sannan yace duk ďan halis yanaso ya gama da iyayensa lafiya, sabida haka bazai karya dokan iyayensa ba,

Ni yanzu ma da kika gani, tashi zakiyi muje ki bani hakkina".

Cikin kuka take faďin dan Allah kayi hakuri ka barni na warke, wlhy ciwon gurin yakemi, cike da isgilanci yace, ciwo?? Ai bakiga komai koba".

Gani batada niyyar tashi hannu yasa ya kamo mata nonuwarta da karfi, ihuuu tasa tana faďin na shiga uku, zan mutum, wayyo Allah na, duk da ihun da takeyi amma baisa bakura ya kyaleta, har saida ya haďata da bango, da shike rigan dake jikinta me zip a gabane, zuge zip ďin yayi, sannan ya banle bran ďin dake jikinta, harshe yasa ya fara wasa da kan nononta, jin haka yasa tayi shiruu, kamar ba ita ba".


Shiko bakura sai fama wasa dashi yakeyi gaďe da tsotsa, saida bakura ya tabbata tayi nisa sosai, ďan itama har shafe masa kai takeyi, a lamar jin daďin abinda yake mata, ba tare data ankara ba, kawai ya yanka mata cizo, wanda yasa har saida hakoransa suka fito a nonowarta".


Wani irin zafin taji lokaci daya, ita kanta batasan lokacin data saki fitsariba, ihu tasa haďe da zubewa a kasa tana kuka".

Kan cushion ya kama ya zauna yana kallonta".


Tun aroud alevan zynah keji ciwon mara, da yake da kuruciya, bata kawo haihuwa bane, idan ya faďi mata, komawa takeyi ta kwanta, idan kuma ya sake tasowa saita mike, da haka har bcc ya dauke daga idonta".

Tun tana iya kaida dawowa har yakai ga ta nemi gun ta zauna, dirrrshapp".

Idan ya yunkuro mata, kuka take sawa, isan kuma ya faďa tayi shiru".

Gani har karfe hudu bata daina jin ciwon ba, waya ta dauka, ta fara kiran bakura, dai-dai lokacin yana toilet yana wanka, dama baya kashe wayarsa, sai dai idan zai kwanta yasata a slent".


Gani haske a wayarsa da sauri ta daga wayar, dubawan da zatayi taga an rubuta mt favorite, ta dauka buduwace, tsaki tayi haďe da kashe wayar gaba daya".


Gani haka yasa ta fara niman number hjy ko Am'abuwa, duk da ga numbers ta wuce, amma bata gani ba, hawaye ne kawai suka aiki, wani kebin wani, sai faman juyi takeyi a tsakar ďaki".

Bakura dake wanka, tun cikin dare yakeji gabansa na faďi, kuma ya rasa dalilin hakan".

Yaso kiran zynah idan ya idar da sallah, amma yana idarwa ko tashi baiyi daga kan sallayar ba, bacc ya dauketa".

Aroud sevenAM labour ya tashi zanga-zango tunda taga wani irin ruwa mai yawa yana zubowa daga dabanta,hankalinta ya tashi daga daya ta tsorata, ihu kawai takeyi tana kiran muhammed yazo ya taimaketa".

Cikin bacc bakura yaga zynah cikin matsananciyar hali, tana ihu tana niman taimako".

A firgice ta tashi, yaje ya dauki key ďin motarsa ya kami hanyar waje, har yasa hafa daya, take maganar hjy ya tuna da maganar hjy, da sauri ya dawo cikin".


Me labour kuwa, ga haihuwa ta taso mata zanga-zango baby na nimar hanya, amma ita, sabida daga daya ta matse kafarta, duk da tanajin alamar abu a gabanta,amma baisa ta buďe kafa ba balle nishi,.


Sunan Muhammad kuwa bata sauke wani take dora wani, yazo ya taimaketa".

Gani babu sarki sai Allah wani irin ihuuuu tasa, haďe da fashewa da kuka ta koma kiran ummuta zan mutum kizo ki ceceni ummu""""""""











*mmn uswan ce📚✍*

 🍀🍀🍀🍀

           _*ZYNAH!!!*_

               🍀🍀🍀🍀

*WRITTEN ✍ BY MMN USWAN*
_______________

©©©©©©

_*follow me on*_        

_*wattpad:Hauwa s zaria*_

_*Facebook group*_
_*Mmn Uswan*_


https://www.facebook.com/groups/157572201857733/
                    
           ➿➿➿➿➿➿

_*BISLLAHI RAHAMANI RAHIM*_

_*In the name of Allah, The Beneficent, the Merciful*_

🅿2⃣5⃣-3⃣0⃣

     Wani irin matsananci kuka, zynah tasa haďe da kiran ummanta".

    Ban garen Bakura kuwa, cikin wani irin matsananci tashin hankali ne ya tsaci kansa a ciki".

   Take wani tunani yazo masa, da sauri ya ciro wayarsa ya fara kiran number Am'abuwa, Bakura ya kira Am'abuwa yafi sau biyar ba'a daga ba, har zai ije wayar, can kuma sai dai ya sake resending kiran nata".

       Kamar a mafarki, Am'abuwa take jin ringing, a hankali take buďe ido, buďewar da zatayi, taga wayarta ne keta ringing, kafin takai hannu wayar ta katse, can kuma saiga wani kiran ya sake shigowa".

                      Tana ďagawa taga number bakura ne, dah sauri ta amsa, haďe da sallama, ko gaisawa bakura bai tsaya suyi ba, yace Anty dan Allah ki taimakeni kije ki duba min Amina ko a gida".

          Lafiya, ta tambayesa?"
  Nima ban sani ba,amma dai dan Allah kije yanzu ina jiranki".

    Yanayin dayya take magana ne, yasa Am'abuwa mikewa, duk da lokacin tashinta bai yi, amma yaya zatayi, hijab kawai tasa wanda ya sauka ya kai mata har cinyarta, ko sallamar hjy batafi ba ta fita".

     Zynah kuwa ta riga ta mika al'amuranta ga Allah, domin yanzu kam, ko kukan ma ya gagareta, ga kai ya riga ya faso,amma rashin nishi yasa baby bai fito ba".

         Koda Am'abuwa ta iso, tayi knocking har ta gaji, amma ba'azo an buďe ba, nan ta koma kiranta ta waya, nan ma shiru, ba'a daga ba".

    Zynah na kallon wayar amma babu halin ďagawa, domin ta kanta take bata waya ba".

     Tana cikin haka kenan, saiga kiran bakura ya shigo wayar ta, tana dagawa yace ina take?"

     Tunda nazo nake ta konking amma bata buďe ba, na kirata a waya ma bata ďaga wayar ba, nan hankalin bakura ya kara tashi sosai, nan yace ta zaga taje ta window bedroom ko Allah zaita ta hangota".

    To kawai tace, da sauri taje ta windom ďin da bakura yace mata, lekawar da zatayi ta hango zynah, cikin wani halin, taso kiranta, amma da shike ko'ina glass ne, koda tayi kiran ba lallane taji ba, nan ta fara kokarin kiran bakura, saiga nasa ya shigo, nake ta faďi masa halin da taga zynah a cikin".

     Ihu bakura yasa, a guje ya fito daga gidan, a wannan lokacin har ya mance wani dokar da hjy tasa masa, ko takalmi babu a kafarsa yaje ya shiga mota, a shiyace ya fisgi motar zuwa gida".

      Allah maji kan bayinsa, da kuma tausayi,wanda duk halin da zaka shiga idan har ka digara dashi, bi'izinillahi zai fiddakai, wani iko ta Allah, Allah mai hikima, ya kawowa zynah dabaran yi nishi, tana kwance ba tare data tashi ba, wani irin nishi tayi, haďe da ihuuuuuu mai karfi, take baby da mahaifar suka fito gaba daya, wani iri naunauyar ijiyar zuciya tayi, anan ta leme ko motsi batayi".

Baby kuwa, tunda tayi kuka sau biyu bata sake yi ba, duk halin da zynah ke ciki Am'abuwa tana kallonsu ra windom, hawaye ne kawai suke gangaro mata, sabida gashi daga zynah har baby suna niman taimako amma babu halin taimaka masu".

Tana cikin hali kenan, saiga bakura ya iso, ko parking da'kyau beyi ba, a fito daga motar, a guje yaje ya buďe gidan, kai tsaye bedroom ya nufa, yana shiga ne, Am'abuwa ta hangosa da glass, da sauri itama ta zago".

Bakura yana shiga gani halin da zynah ke ciki, ihu kawai yasa yana faďin na shiga uku zynah, zynah,!

Am'abuwa na shigo wa, itama ihu tana, bakura be tsaya bata lokaci ba, hannu yasa ya cicibi zynah dake kwanta, ya sagalata a kafaďa, ba tare daya bi takan baby ba, shi ta matarsa yake, Am'abuwa ce ta dauki baby cikin wani ďankwalin zynah dake kan gado, ta haďa da mahaifar suka fita zuwa mota".

A baya ya shinfiďata, sannan ya dawo suka shiga, suna shiga a tsiyace yaja mota zuwa asibiti, duk maganar da Am'abuwa keyi, jinta kawai yakeyi domin bemasan mai take faďi ba".

Suna isa taimakon gaggawa Dr suka bata, ita da baby, duk da tana motsi,amma batasan me sukeyi a kanta ba".

Bakura dake waje, sai kai da kawowa yakeyi, a bakin kofar ďakin, bayan su gama suka fito, domin tasamu bacc, yanzu hutu kawai take bukata".

Dr ďin tana fitowa,da sauri bakura ya taresa da Dr yaya jikin nata?"

Jiki da sauki, dama galabaita ne, amma idan suka samu hutu, insh Allahu komai zai dai-daita".

To kawai yace, a lokacin ne, Am'abuwa tayi tunani kiran gida ta sanar masu, number hjy ta kira, lokacin suna falo suna breakft, gani number Am'abuwa ne yasa hjy dagawa da

Please Login or Register in order to submit comment