Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka yace mata, duk basusan zasu soyewarsu bane, hakan yasa yace kada kowa ya rakasa, driver ne kawai ya yarda daya kaisa, ita kuwa zynah shirin larabawa yayi mata, domin hatta hannu saida tasa safa, balle kafa ko fuska"..

Ta rigasa isa airpot, sannan ya iso, bayan driver ya tafi ne, yaje inda take zaune ya amshi pakhryya, nan suka zauna suna hira, har lokacin da zasu shiga jirgi yayi, waje ďaya suka zauna, bayan an kammala komai suka jirgi ya tashi zuwa dubai"....








*mmn uswan ce📚✍*
🍀🍀🍀🍀

           _*ZYNAH!!!*_

               🍀🍀🍀🍀

*WRITTEN ✍ BY MMN USWAN*
_______________

©©©©©©

_*follow me on*_        

_*wattpad:Hauwa s zaria*_

_*Facebook group*_
_*Mmn Uswan*_

            https://www.facebook.com/groups/157572201857733/    
  
           ➿➿➿➿➿➿

_*BISLLAHI RAHAMANI RAHIM*_


_*In the name of Allah, The Beneficent, the Merciful*_


🅿3⃣0⃣-3⃣5⃣

       Su bakura suna isa, taxi ta samu masu, su h'au zuwa hotel ďin dazasu sauka".

    Pakhryya na hannu babanta yana mata wasa, idan ba dariya ba babu abinda takeyi".

"Suna isa sallah suka fara yi, domin shine gaba da komai, sannan bakura yasa aikai masu order abincu, suna gama ci sukai wanka, Pakhryya kuwa zynah na mata wanka bacc tayi".

Saida bakura ya huta sosai sannan ya kira hjy ya sheda mata ya isa, bayan su gama magana da hjy ne, ya kira Am'abuwa itama yashe mata".

         Ita kuwa Adyra bai samu kiranta ba, sai cannn cikin dare, tana bacc kamar a mafarki taji wayarta na ringimg da sauri ta ďaga, domin tasan ba kowa ne zai kirata a wannan lokacin ba sai bakura".

   Da sallama ta daga, haďe da gaishesa da gajiyar hanya, yace, hanya alhamdullh" Be dauki lokaci ba sukayi sallama".

   Wanka sukayi suka shirya cikin english wear,kalar kayan su irin daya harda Pakhryya, marron colour, ba karami kyau dressing ďin yayi masu ba, lokacin da zasu fita bakura ya dauko after dressing ya dora mata akan kayan jikinta, sannan suka fita".

  Tunda suka fita kuwa, basu dawo gidan ba, saida bakura ya kaita guri-guri, pict kuwa ba'a magana"

       Ban garen zynah kuwa, cire duk wani kunya tayi ta nuna wa mijinta tsatstsan tsagwaron soyayya, idan da suyishi kantakile ne to yanzu ta kile, wani abu idan tayi har mamaki bakura keyi, hakan yasa shima ya dirje ya nuna mata soyayya, pict kuwa duk inda sukaje sai suyi, bakura ke turawa facebook instagram," duk pict ďin da zasuyi Pakhryya na tsakiyarsu".

   A ban garen hjy kuwa kullum cikin kira takeyi ta tambaya ko yasamu kayan".

      Ana gobe zusubar Dubai hjy ta sake kira, tana tambaya, bakura cewa yayi, duk inda zaije dan yasamu yaje bai samu ba,shi isa ma gobe yakeso ya dawo gida".

  Da sauri hjy tace, a'a kada ya dawo, daga nan ya wuce india ko chana, maybe Allah yasa a samu a can"..

   Da sauri yace, to hjy, nan sukayi sallama, dama bakura ya faďiwa hjy hakane, amma har cikin zuciyarsa ba haka bane".

Daga Dubai basu tsaya ko ina ba, sai india, nan ma kwanansu hudu sukar kasan zuwa england, daga nan basu tsaya ko ina ba sau saudia, bakura yaso suyi aikin hajji ne,duk da dai shida yayyunsa suriga suyi amma kogi beki kari ba, sai dai gashi ba lokacin aikin hajjin bane dole yasa sukayi ummah, nan ma susha pict kamar babu gobe".

    Allah sarki adyra, kwata-kwata bakura ya mance kamar yana da wata mata nayan zynah, dama hausawa suce matar shige bata daraja,gani be cika kiranta ba, yasa utama bata kiransa, haka taci gaba da zaman kadaita"

   Duk inda suke hjy na bibiye dashi wajen kira da massage, harda video call take cewa suyi, dai-dai lokacin yana cikin wana kanti yanawa Pakhryya siyayya saiga kiran hjy, da sauri yace zynah ta dawo bayansa, saida ta dawo bayansa sannan yayi receiving call ďin, haďe da sallama, duk da ba ganisa takeyi ba, amma hakan be hana bakura dukawa ba, abinda su ringa da su saba".

      Bayan su gaisa, hjy tace, bakura yaya kuma haka?"
  Eh wlhy abinda yasa nazo nan, zuwa nayi na duba ko zan samu anan, idan ma ban samu ba, nasan baza'a rasa wasu kalar ba, kuma inasa ran suma zasu samu shiga".

   Ok, amma dan Allah kaduba masu kyau da kamshi".

Ok, kawai yace".
Har zata kashe wayar, can tana waye a bayanka,kuma kamar da baby a hannunta?".

Da sauri yace, ban santa ba, amma ina gani kamar itama siyayya tazo yi".

Ok, hjy tace, sannan sukayi sallama, satin su biyu a saudia,  bakura beso komawa gida a wannan lokacin ba, amma jin ance daddy ya dawo dole yasa suka haďe kaya zuwa nigerin".

  Zynah tayi kyau iya kyau, idan ba kasanta ba, ba lalla ne in kaganta yanzu ka ganeta ba, domin gaba daya ta canza kota kowani ban gare, domin bakura yayi kokari sosai wajan gani ya koya mata turanci, da larabci, barbanci kuwa, zama yau da gobe yasa ta iya, domin yanzu bai cika ji mata hausa ba, cikin ukun ga daya yake mata, turanci, larabci, or barbanci, kuma dole ta bashi amsa, idan ma tabashi da hausa ba amsata yakeyi ba, dole yasa ta iya, Pakhryya kuwa itama shi suke mata".

   Bakura bai faďi ma kowa yana hanya ba, sabida kada azo tar bansa,a gansa da zynah, suna sauka bakura ya dauki mai taxi zuwa jabi, hanyar baya ya nuna masa, wanda zai kansu dai-dai da ta inda gidan zynah yake, bayan su sauka ne, ya sake komawa yaje ya shigo ta gate ďin gaba, sallamarsa cikin falo yasa duk mutane dake zaune a falo suka amsa da mamaki".

  Da sauri bakura ya saki jakar dake jannunsa yaje ya rungume daddy yana masa sannu da zuwa, gani bakura ya kara kyau da kiba, yasa daddy cewa, amma aure ya amsheka, kada yadda kayi kyau kuwa babana?"

   Dukkansu dariya sukayi, nan shima aka shiga masa hannu da hanya, hjy tace meyasa be faďi kamar yana hanya ba azo a tar besa?"

    A'a hjy, so nake na shammaceku". Duk dariya sukasa, jin daddy yace ina matarsa, take hjy ta canza fuska, kamar ba ita ke dariya ba, kan bakura na duke yace suna suleja,amma yau ko gobe zanje na dauko su, ya kamata kawai daddy yace".

  Ita kuwa hjy, tsaki tayi" Bakura bebar gidan ba sai bayan isha, saida yafara zuwa sukayi sallama da zynah sannan ya tafi gidan Adyra".

Har ta kwanta, taji ana knocking, kafin ta tashi saiga kiran bakura ya shigo wayarta, saida tayi tsaki sannan ta daga wayar, shiruuuuu tayi babu ko sallama, ji kawai tayi ance zo ki buďe min kofa".

   Bata musa ba taje ta buďe basa, tana buďe wa bakura ya kai mata runguma yana faďin oyoyo matata, wani irin hankaďa takai mata, haďe da cewa dallah ja kabani gu, dan walakanci sai yau ka tuna kanadani?"

    Shima kansa yasan bai kyauta ba, shi yasa be nuna fushi ko damuwa ba, sabuda yasan koda dabba ka'ije a gida zaka waiwaiyeshi balle mutum ďan Adam, ita kuwa Adyra  bedroom ta koma tayi kwanciyarta, saida ya  rufe gida sannan ya bita bedroom ďin".

Yana shiga tube wa yayi ya shiga wanka,yana fitowa ko bayan bacc be saba ba, yaje ya samu bakin gado ya zauna, juyawa yayi yana kallonta haďe da cewa tashi ki ďibomin ruwa, Adyra najinsa amma ko motsi batayi ba, balle tayi yunkurin tashi, bakura ya sake magana, nan duk a banza, mikewa yayi yaje ya ďibi ruwan da kansa yasha sannan yazo ya kwanta".

      Har Adyra ta fara bacc taji bakura na shafota, hannu tasa ta bige masa nasa hannu, duk da haka beyi fushi ba, saima kokarin jawota jikinsa da yakeyi, yana faďin haba my madam, yanzu sabida Allah fushi kikeyi dani? To naji koma menene kiyi hakuri".

      Duk bakura na maganar ne yana shafeta, shiruuuu tayi ko motsi batayi, shi kuwa bakura yaci gaba da cewa, nasan kina fushi sabida rashin kiran da banyi maki bane ko? Wlhy wasu al'amura ne suka shami kai amma kiyi hakuri".

   Gani har a lokacin bata tanka masa, kuma yasan ba bacc takeyi ba, yasa bakura hayewa jikinta yana kokarin kai mata kisss".

     "Da sauri ta turesa ta mike zaune, tana faďin, dallah can malam, ni zaka raina wa hankali?to wlhy baka isa ba, kuma abinda kakeson yi wlhy bazan bayar ba, ai ba sha-sha-sha bace ni, kaje ka kwaso jatabarka kazo ka sauke anan, to bazan bayar ba"...

    Dallah can malama bakima gode ba, taimakoki fa zanyi, idan ba taimako ba kema kinsan nafi karfinki,".

     "Taimako fa kace?"
"Kwarai da gaske"

Allah ya kiyaye, kai bakura bari kaji wlhy idan banda iyayenka su boye min ba, wlhy babu abinda zanyi dakai, banza ma yaudaran banza ma yaudara wofi, kuma wlhy Allah ya isa tsakanina daku, bazan taba yafe maku ba, azalumai kawai".

    A isgilance bakura yace,in da ke kisan kunya har zaki kalli kwayar idona kice iyayena su yaudareki? Ni'eemat kenan, zaki iya faďin abinda yafi haka, amma nasan iyayenki basu isa su faďi haka ba, sabida susan taimaka masu akayi""..

    Da sauri Ni'eemat tace, taimako fa kace?".

    Kwarai da gaske,ko kuma nace sabida kuďin iyayena, idan badan kuďinsu ina na taba gani daga tayi sai a sallama? Koda shike, dole suyi haka sabida susan er'tasu kwankoce,"..

   Da ssuri ta dakatar dashi, da cewa kaiiiiiii bakura ya isheka haka, duk abinda zamuyi kada ka sake ka zagan min iyaye".

A marerece yace dan Allah, da gaske kinaso iyayenki? Allah sarki, kuma haka ne fa, iyaye sunada matukar daraja da mutanci, amma a gun er'su".

  Wani irin kallon banza tayi masa, haďe da tsaki, daga sannan  bata sake tanka masa ba, sabida ita kanta tasan bata kawo budurcinta gidan ba, duk abinda zata gani daga garesa dole tayi hakuri, *duk abinda ya sami shamuwa watan bakwai ne yaja mata" Yau inda ta kama kanta be isa ya kalli fuskanta ya kirata da kwanko ba"*

_Kalu bale gareku en'mata, kai budutci gidan miji ba karami kima da daraja yake karawa mace ba, kuma wlhy duk rashin kunyarsa da rashin mutuncinsa be isa ya kalli kwayar idon ka ya faďi maka magana data danganci wannan ba, idan har kikakai budurcinki gidansa, idan zai maki wani rashin kunya, wlhy kinada right da zaki tsaya a gabansa da full comfedacen ki faďi masa magana, sabida shi ya bareki, bakisan kowa ba bayan shi. Amma idan kwanko kikaje ina kikaga bakin magana, kema kinsan sai abinda Allah yayi" Allah ka tsaremu ka tsare mana yaranmu ka kuma rabasu da sheďanu maza hatsabibai ameen_

Hayewa gadon tayi ta kwanta, duk da maganar yana cinta amma babu yadda ta iya"

  Shima bakura dauko wandonsa yayi yasa yana faďin banza kawai, a zuciyarsa kuma ji yake kamar ya koma gidan zynah".

   ______________

Duk da kasancewar Usman ďan kauye ne, amma da shike yayi karatu, shi isa yake amfani da babban wayar, yana hawa social media kamar su whaAspp instegram facebook, yana kwanta shiga zainab, ta dora kai a jirkinsa suka kallon pict a instegram, sunayi suna hira, sai Usman ya kamo pict ďin su Zynah da bukura,har ya wucesu sai kuma ya dawo da baya, kurawa pict ďin ido yayi sosai, sannan yace zainab".

Na'am".
Dan Allah matan cikin pict ďin nan bata maki kama da Amina ba?"

    Itama kallo pict ďin tayi sosai,sannan tace, ehhhh wlhy amma dai kamace, ina Amina taga haka? Babu mamaki tanacan tana karuwanci, domin kwanaki ummata taji lavarin wai  anganta a gidan wata magajiyan karuwai".

        Duk da magana da takeyi, jikinta ya bata cewa amimce,  amma hasada ya hanata ta fahimci haka".

    Usman yace, amma wlhy su birgini, kuma matan sunyi kama da Amina sosai, dubi er'su kyankyawa, ina ma da nine, tsaki zainab tayi, haďe da cewa to bakai bane sai kayi hakuri".

Tayi maganar ne haďe da fisge wayar ta ije a gefe".

___________

Da safe bayan bakura ya shirya zai fita, yace tashi muje kiyiwa daddyna sannu da zuwa".

Hararansa tayi, haďe da cewa ban zuwa"

Daddyna ne fa Ni'eemat"
Sai me, idan daddyn kane?"

Ficewarsa yayi, ba tare daya sake tanka mata ba".

Yana fita saida ya fara zuwa gidan su hjy ya gaishesu sannan ya fita zuwa gidan zynah, yana shiga dai-dai lokacin ta fito daga wanka kenan, pakhryya kuwa an riga anyi mata nata, kwance take a kan gado tana wasa".

   Hannu bakura yasa ya dauketa yana faďin oyoyo my doter, nan pakhryya ta fara masa dariya, zynah tana fitowa suka gaisa, haďe da tambayr su tashi lafiya,fita tayi tare ta kawo masa abin breakft, koda ba inace da girki ba, amma idan mijinta yazo baya hanata karbansa, bakura na karyawa ita kuma tana shieyawa, suna gamawa bayan ta meda kayan kitchen da dawo har zata dauki pakhryya hannu bakura yasa ya rike mata mata hannu, jawota yayi jikinsa yana faďin my wife gaskiya kiyi kyau".

   Murmushi tayi masa, sannan tace nagode".

    Gani yadana niyyar bata mata kyalliyarta da sauri ta mike tana masa dariya, shima mikewa yayi yana mata dariya yace dauko mayafi muje ki gaida daddy".

  To tace, tana dauka suka fita, bakura na rike da pakhryya, suna tafe suna hira har suka isa".

     
     "Da shike bakura ne a gaba, yasa shine ya fara sallama ya shiga, su hjy da daddy dasu Yah-na Am'abuwa suma duk suna gun a zaune, bakura na shiga har zynah tasa kafa zata shiga, hjy na ganita da sauri ta mike haďe da cewa ina zaki? wlhy idan kika sake kika shigo na lahira saiya fiki jin daďi".

   Jin haka da sauri ta meda kafarta waje, kasa karisawa bakura yayi, cakkk yaja ya tsaya, daddy ne yace jeka ka shigo da matarka"..

   Jin haka yasa jikin hjy sanyi, kasa karisawa tayi, dole ta dawo ta zauna, saida bakura yaje ya mikawa daddy pakhryya sannan yaje ya kamo hannu zynah suka shigo tare".

     Asanyaye ta shigo, har kasa ta duka ta gaida daddy, haďe da yi masa sannu da zuwa, daddy da fara'arsa ya amsheta, ita kuwa hjy koda ta juya gun hjy tayi gaisuwa yakai baki uku amma hjy bata amsa ba, gani haka yasa ta juya ta gaida sauran sannan ta zauna, a gafe daya".

   Daddy ko sai faman wasa yakeyi da pakhryya, tana masa tsalle a jiki, Am'abuwa nasa hannu ta amsheta pakhryya tasa kuka tana kallo daddy, babu irin rarrashin da basu mata ba, amma taki dole yasa daddy ya amsheta"..

      Tunda zynah ta zauna, hjy ta daina magana, duk maganar da sukeyi batasa baki ba, suna haďa ido da zynah wani irin uban harara take mata, tunda taga haka, bata sake bari su haďa ido ba".

       Ashe daddy ya lura da haka, mikewa yayi haďe da kiranta zuwa cikin ďaki, suna shiga daddy ya hauta da zagi, abinda be taba yi mata ba kenan, tunda suke"

  Yana cewa jahilar banza jahilar wofi, ashe haka kike? Wlhy khursum kin ban mamaki, haka kawai kisa masu yarinya a gaba? Ke idan akayi wa naki yaran haka zakiji daďi? To wlhy daga yau sai yau, kada na sake ji ko gani kwatankwacin haka, idan har nagani to wlhy sai nayi mummunar saba maki, ni musulmine nasan kaddara, sabida haka na daukesa a matsayin kaddara, idan banda Allah yana bari mutum da kayansa, daba Allah ne kadai yasan abinda zasu aikata ba".

Kibar gani ba'a gida nake ba duk abinda kike yiwa yaran jama'a idan suzo aiki inada labari, ke a rayuwarki baki yiwa yara fata na gari, daga kice masu karuwai sai barayi,sabida Allah idan kece aka yiwa naki haka zakiji daďi? To wlhy bazan yarda da haka ba, sabida nima bazanso yarana suje wani gun ayi masu ba, idan banda Allah yana amfani da zuciyar mutum ba Allah kadai yasan irin abinda zasu aikata ba, babu mamaki da awaje zasu haifi yarinyar ga, idan banda jakanci irin naki kodan albarkacin wannan yarinya bazaki raga mata ba?"

        Daga yau sai yau, idan har kinaso mu zauna lafiya dake, inaso ki kyalesu su wala" Buďe baki tayi zatayi magana, da sauri daddy ya dakatar da ita".

Dole yasa tayi shiru, badan taso ba, mika mata pakhryya yayi shi kuma ya kwanta, dole yasa ta riketa, yana kwance suna magana, pakhryya kuwa sai faman wasa takeyi a hannu hjy, dan ma hjy taki bata saurareta ba".

Su jima suna hira sannan hjy ta mike taje ta mikewa Am'abuwa ita, ita kuma ta mikewa zynah" su daďe a gidan sannan suka kamo gida".


Ita kuwa adyra har yanzu fushi take da bakura, koda yayi mata magana bata amsa masa, hakan yasa ya shirya tafiya zuwa kano garin su zynah ba tare da sanar da ita ba, domin a yanda ya tsara wa kansa sai dai taji ya wuce, tunda tace tayi fushi da gaba".


Gabama harda mijin da kake aure, himm Allah shi kyauta"


Bayan kwana uku, bakura da zynah suka shirya zuwa *kunci* garin su zynah, bakura saida ya shake burn da tsaraba, ita kuwa zynah sai faman munra takeyi, saida suka biya suka sallami su daddy da hjy, gaisuwar bakura ne kawai ta amsa amma banda na zynah, data gaji da tsayuwarta ne ta mike suka fita, Am'abuwa har bakin mota ta rakasu, haďe da bawa zynah kuďi wai tayi tsaraba".

Zynah tayi godiya sosai, saida taga tashinsu sannan ta koma ciki".

Tunda zynah tace zata gane hanya, yasa basu biya gidan kanďe ba".

Zynah sabida murnan gani ummata ko kibta ido batayi, sai faman hura suke zubawa da mijinta' kamar yadda tace kuwa hakane, haka tayi ta nuna masa hanya, bakura baya musu, duk hanyar data nuna masa haka yakebi, duk da a zuciyarsa yana tunanin kodai su banta hanya ne? Da haka har suka isa garin""""....





  






*mmn uswan ce📚✍*

🍀🍀🍀🍀

_*ZYNAH!!!*_

🍀🍀🍀🍀


*WRITTEN ✍ BY MMN USWAN*
_______________

©©©©©©


_*follow me on*_

_*wattpad:Hauwa s zaria*_

_*Facebook group*_
_*Mmn Uswan*_

https://www.facebook.com/groups/157572201857733/

➿➿➿➿➿➿


_*BISLLAHI RAHAMANI RAHIM*_



_*In the name of Allah, The Beneficent, the Merciful*_



🅿3⃣3⃣-4⃣0⃣

Tun daga kofar gari, aka fata kallonsu, yara na gudu manya kuma, sai faman bin motar da kallo sukeyi, tintake camry ce motar, baka gani mutane dake cikin motar ssi dai su su ganka".

Da haka har suka isa kofar gidan, lokacin malam shehu yana dawowa daga sallamaci kenan, sabida yau ne ma ya fara fita sabida zazzabin da yayi fama dashi".

Gani mota tayi faki a kofar gidansa, saida yaja da baya tuku, bayan su parker ne, bakura ne ya fara fita, ya zagayo ya buďe mata murfin motar ya amshi pakhryya sannan ta fito, malam shehu dake makale a lungu yana kallonsu, saida yaji wani irin yarrrrr a jikinsa,amma duk da haka bai gane ko waye ba".

Saida ta gyara mayafinta sannan suka nufi hanyar gida, zynah na gaba bakura na baya, suka shiga cikin gidan. Gani su shiga gidan sane yasa malam shehu fitowa daga inda yake makale ya nufo gida, da sallama suka shiga gidan" dai-dai lokacin rakiya na fitowa daga banďaki, da sauri ta jada baya, haďe da tambayar malamai wah kuke nema?"

Murmushi zynah tayi sabida tasan rakiya bata gane ta bane, sannan tace inna ninefa".

A ladabce rakiya tace kecewa hjy?"
Saida ta kira yi mata dariya sannan tace nice amina"""..

A gigice tace amina fa kikace".
A lokacin ne ta kare wa Amina kallo sannan ta gano ita ďin ce, can zawa da tayi ne yasa ba zakaga neta ba".


Sulu-suluce rakiya ta faďi ta daka da ďuwawu darab ta zube a kasa, zama tayi dirrrrshap sai faman bin zynah takeyi da ido, baki kuwa a baďe yaki rufuwa".


Zynah bata bi ta kan rakiya ba, ta nufi hanyar ďakin ummanta, shi kuwa bakura duk inda tabi yana biye da ita, tun kafin ta karisa bakin kofar ta hango dakin a wangale, a lama babu mutum a cikin, hakan ya sata karisawa da sauri ta shiga ďakin".

Tarkace ne kawai ta gani a ciki, da alama ďakin ya daďe babu mutum a ciki"

A gigice ta fito daga ďakin ta nufo inda rakiya take, tana kokarin tambayar ina ummata""..

Sallamar malam shehu ne yasa katseta, duk da tanajin bakin cikin abinda yayi mata, amma yaya zatayi, tunda ba'a canza wa tuwo suna, hannu ya mika wa bakura suka gaisa, amma duk a lokacin malam shehu be gano Amina ce ba, rakiya dake zaune cikin karkarwan bakin tace, Amina kece haka?".

Cike da mamaki malam shehu yace wacce Amina?"

Babu abinda yafito daga bakin Amina sai ina ummata take? Malam shehu bebi ta kanta ba, daki yaje ya dauko shinfiďa ya shinfiďawa bakura, bayan su zauna ne suka gaisa, malam shehu yake tambayar bakura daga ina, domin har yanzu kokwanto yakeyi balle yadda gaba daya ta canza".

Zynah dake tsaye ta samu gu ta zauna kusa da bakura, murmushi bakura yayi sannan ya zaiyana wa malam shehu daga inda ya fito, da kuma aurensa da zynah, babu abinda malam shehu keyi sai kabbara, hannu yasa ya amshi pakhryya, sannan suka kara gaisa wa, ita Amina ta gaida babanta, haďe da tambayar ummata".


Malam shehu ya meda kallonsa izuwa rakiya dake zaune kamar wacce aka daure a gun, domin tunda ta zube a kasa bata mike ba".

Rakiya jeki ki kawowa surinkinki ruwa mana" A lokacin ne ta dawo daga tunanin da takeyi, tana mikewa, ďakinta kawai ta nufa batare dace komai ba".

Tana shiga tasa kuka wii-wii-wii kamar wacce aka daka, tana faďin meyasa nayi wa kaina? Meyasa nasa malam ya kori Amina daga garin nan? Yanzu ďubi yadda ta koma kamar ba ita ba?".

Shiru da malam shehu yaji ne yasa shi mikewa haďe da faďin bari akawo maka ruwa ko?"

Yana mikewa zynah tace bakura nifa banga ummata ba, Allah dai yasa ba wani abunne ya sameta ba" a'a zynah bari dai baba yazo muji inda take, maybe unguwa taje".

Himm kawai zynah tace, daga nan bata sake cewa komai ba, hannu tasa ta amshi pakhryya tasa mata nono a baki".

Malam shehu yana shiga ďakin rakiya gani tana kuka yasa shi karisawa ciki da sauri, haďe da cewa rakiya lafiya?"

Ko kallo malam shehu bai ishi ta ba, taci gaba da kukanta tana faďin na ohh!! Ni rakiya na cuci kaina, nayiwa kaina, wlhy dana sani bansa an kori yarinyar ga daga garin nan, dubi yadda ta koma?"

Cike da mamaki malam shehu yake kallo rakiya dake zaune ne".

Gani kada su raba abin kunya a gaban suriki yasa shi kita daga ďakin ta barta, taci gaba da kukanta".

Ta kofar baya malam shehu yayi yaje ya siyo masu kayan sanyi, sannan yasa aka dama masu fura da nono".

Bayan ya dawo ne, bakura da kansa ya matse ya tambayi malam shehu inda sadiya take".

Malam shehu ya rasa yadda zaiyi masu bayani, saida ya ďan jinkirta sannan yace tana gidan su".

Kafin ya karisa tuni zynah ta cire pakhryya a nono ta mikewa bakura ita, sannan ta mike, zomuje kawai tace".

Kunya ya hana bakura mikewa, ita kiwa zynah, tuni ta mike haďe da cewa zo muje, sannan

Please Login or Register in order to submit comment