Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta rufe gida".

           Bayan sallar asuba, duk suka shirya, aroud 7:AM suka dauki hanyanr kano, bakura da zynah mota ďaya hjy da daddy sai driving suma mota ďaya".

    Da safe ma haka, zuba ido adyra tayi rana jiran shigowar bakura amma taji shiri, daga nan ta hau fushi bata sake tunanin kiransa ba kuma".

    Su daddy basu isa garin kunci ba sai bayan la'asar, kai tsaye gidan su zynah suka nufa, gani sune yasa en'zaman makoki duk suka zuba ido, da son gani suwaye a motar".

   Da shi motar su bakura ne a gaba, yasa shida zynah suka fara fitowa, sannan su daddy da hjy, duk en'zaman makokin sukabi su da ido suna kallonsu, galala, kamar basu taba gani mota a rasuwar suba, daga kiman har maigari duk suka mike suka yo kansu, da sannu da zuwa".

    Hjy na fitowa daga mota, ba tare da daddy ya gani ba, yawun dake bakinta ta tsarďan dashi, haďe da jan tsaki, zynah na kallonta da sauri ta dauke kansa tayi kamar bata gani ba suka nufi cikin gida".

     Zynah ce a gaba, hjy kuma a baya, tana tafe tana aibanta gidan, da haka har suka isa ciki, duk matan dake zaune jin sallama yasa suka juyo kansu, gani haka yasa hjy ta kara tsuke fuska ksmar tanajin warinsu, abinda ta mutumin kauye sai faman yake baki sukeyi suna kallon zynah da hjy".

   Har ďakin ummata zynah ta kai hjy, duk da ďaki babu laifi, domin a share yake tsaf babu datti, kuma ga ledar kasa daya rufe ko'ina, amma hakan bewa hjy ba, domin kin zama tayi a kasa, gani hakan yasa sadiya cewa ta zauna a bakin katifa".

     Nan sadiya ce ta fara gaida hjy, bayan su gaisa, matan dake waje, da gulma suka kara shigowa suna gaida hjy, amma dan tsabar rashin mutunci iri na hjy, ko kallo basu isheta ba, sadiya ce take amsa masu sai kuma zynah".

      Nan labari ya kai kunni rakiya, jin haka yasa rakiya cewa basai naje ba balle suyi min kallo banza?"

    Ruwan swan sadiya tasa aka siyo masu, dasu juice amma duk ba mai sanyi bane, sabida garin babu wata, mutum daya ne yake kunna genarato, a ranar kuma baya nan yaje cikin kano siyayya,  koda aka kawo saida ta ďibawa su bakura da daddy nasu sanna aka bawa hjy nata, kaďan kawai hjy tasha sannan tace zatayi sallah".

    Da sauri zynah taje ta zuba mata ruwa a buta, sannan tazo ta sanar wa hjy, to kawai hjy tace, tana mikewa ruwan swan ďin da sadiya ta siye mata tashi dashi tayi alwala sannan tazo ta fara sallah".

    Nan take sadiya ta fito da kuďi ta aiki wata kanwarta kasuwa tayo mata cefane, hjy na idarwa sadiya tace zynah ta rakata ďakin rakiya su gaisa".

    Zynah ce ke daga hjy na biye da ita, da takalmi hjy ta shiga ďakin rakiya, duk da mutuwar da akayi wa rakiya, amma besa ta daina masifa ba, suna haďa ido da hjy tun daga sama har kasa ta ďibi hjy dashi sannan ta zubar".

     Hjy dake tsaye tace sannunku".
     Buďe bakin rakiya tace, kema sannunki".

   Tun daga sannan rakiya bata sake magana ba, matan dake zaune a ďakin rakiya ne suka amsa wa hjy, daya daga cikin matan tace hjy ga gun zama"..

    Da sauri hjy ta dauki mayafinta ta rufe hancinta dashi, sannan tace ina gun zaman yake?"

    Jin haka da shike rakiya ta fahimci abinda hjy ke nufi, tsaki tayi, haďe da cewa aikin banza, ni za'a kawo wa rainin hankali?".

   Ba tare da hjy ta tsaya jin abinda rakiya zata ceba ta fita daga ďakin".

         Koda aka gama abinci a ka bawa hjy, kin ci tayi, biscuit da juice hjy ta dauko daga handbag ďinta taci ta kwanta" kafin hjy ta kwanta saida ta feshe ďakin da turare, gani sadiya zata ruwa ďakin da sauri hjy tace a'a bata yarda ba, sabida bazata iya kwanciya a ďaki irin wannan kuma a rufe kofa ba".

         Sadiya bata nuna damuwar ta ba, haka ta tashi ta buďe kofar,a lokacin ran zynah ya baci sosai sabida tunda suka shiga ďaki hjy take masu wani irin kallo na raini, gashi kuma duk kokarin da sadiya keyi a kanta bata gani".

      Washe gari kuwa babu yadda ba'a da hjy ba tayi wanka amma taki, a cewarta bazata iya amfani da ruwan garin ba" nan  hjy ta tsama sai dai su tafi, daddy beki ba, sabida shima akan hanya yake, daddy kuďi masu yawa ya bawa sadiya da rakiya, shima maigari da liman ba'a barsu a baya ba, alkhairi yayi masu sosai, kafin su tashi saida sukayi masa addu'a sannan su daddy suka dauki hanya shida hjy, bakura kuwa yace tare zasu dawo da zynah".

     Bayan anyi addu'ar uku ne, bakura ya shigo har ďakin umma, hira sukayi sosai, nan ya tambayi umma abinda take bukata, duk da umma najin kunyar bakura, amma babu yadda zatayi,sabida yadda bakura keyi mata kamar wanda ya daďe  da saninta, nan umma ta faďi masa, bakura da zynah suka shiga kasuwa siyayya sosai sukayo sannan suka dawo, bayan an kawo kayan cikin gida ne zynah tace a dauki buhu daya na shinkafa a bawa rakiya".

      Shidai matsiyaci ko a tandun mai aka sashi fitowa yakeyi tarmasasau, koda  aka kai mata shinkafar dake tasa aka dawo dashi haďe da kuďin ta daddy ya bata, a cewarta ita ba matsiyaciya bace".

    Har umma ta mike zataje, bakura da zynah suka hanata zuwa, dole yasa ta hakira".

    Sati su bakura da zynah bakwai suka suma abuja".

          ~~~~   ~~~~  ~~~~

                *ABUJA*

Su zynah basu iso gida ba sai dare, sabida basu tashi a wuri ba, hakan yasa beje gidan su hjy ba, bayan suyi sallah sukaci abinci zasuci kwanciyarsu sukayi".

   Da safe bayan suyi wanka su shirya, bakura yace suje su gaida daddy da hjy da gajiyar hanya, haka suka nufi gidan hjy".

Bakura ke dauke da pakhryya har suka isa, da sallama suka shiga, lokacin daddy na falo shida su Am'abuwa da Yah-na suna hira, hjy kuma tana ciki, har kasa suka duka suka gaida daddy, shima da fara'arsa ya amsa masu, haďe da sanya hannu ya amshi pakhryya, nan suka gaisa dasu Yah-na da Am'abuwa, suka kara gaisheta da hakuri".

   Duk hiran da sukeyi da bakura bata sanya masu baki ba, saida ta jima sannan ta mike ta sallamesu ta koma gida, nan tabar pakhryya shima bakura be daďi ba ya nufi gidan adyra, pakhryya na wasa ta zame ta sauka kasa, tana wasa, da haka har ta rarrafa ta shiga ďakin hjy, lokacin kallo ya dauke wa su Yah-na da Am'abuwa hankali".

      Hjy dake bacc ji kawai tayi ana shafe mata kafa, da sauri ta buďe ido, tana buďe ido pakhryya ta gani tana tsaye rike da kafar hjy tana mata dariya, tsaki kawai hjy tayi sannan ta koma ta kwanta".

   Duk da haka bata daddara ba, cigaba da jawa hjy kafa tayi, gani haka yasa hjy ta dauke kafarta daga gun, da yake pakhryya me kiriniyane, take side dorower tayi ta haye kan gadon, hannu tasa tana jawa hjy dankwallin dake kanta".

    Cikin jin haushi hjy ta zuba wa pakhryya mari, a gigice tasa kuka, gani yadda tasa kuka ne, sai hjy taji babu daďi a ranta, nan ta dauketa tana lallashinta har tayi shiri".

   Nan sukaci gaba da kwanciya
  Gani pakhryya bata da niyyar bacc yasa hjy sauka daga gadon ta fito falo, su Yah-na da Am'abuwa suna gani pakhryya a hannu hjy, duk haďa ido sukayi suna kallo juna batare da suce komai ba".

       Hjy na zuwa ta mika wa Yah-na pakhryya sannan ta koma ta zauna kusa da daddy, suna cikin hira pakhryya ta sake komowa gun hjy, tun daga lokacin duk ranar da bakura ya kawo pakhryya, bata cika yarda da kowa ba idan ba hjy ba, duk yadda hjy takai ga kin daukarta dole ta hakuri, yanzu kam duk ranar da ba'a kawo pakhryya har wani iri takeji, kodan sabida gyaran da take mata a ďaki".

     Yau da gobe ya wici wasan yaro, idan da sake bakura ya saba da halin adyra, musamman ma bikin su Yah-na da Am'abuwa daga gabato, domin yanzu be vika zata a kasuwa ba, abinda gyaran yayyunsa da yakeyi".

      Kusan kullum yana gidan hjy, idan yazo da safe baya komawa sai dare, idan ranar da yake gidan adyra ne kafin magrib yake tafiya, idan kuma gidan zynah ce, har bayan isha yake kaiwa, sabida yasan ita ďin mai fahimtane".

     Da lokaci yayi bakura yaso tafiya maiduguri da zynah, amma hjy tace bata amince ba, sai dai yaje da adyra, tunda ana daura aure zasu dawo nan abuja ne, tayi hakuri idan suzo abuja sai taje taga gida".

   Duk da beso haka ba, amma ya ďanne bai nuna mata ba, sai yasan ta bata masa show nasa, sabida gaba daya da ita yayi niyyar tafiya, hakan yasa ya gyarata sosai, sabida kada suje a raina mata wayo, to amma yaya zaiyi, tunda umace".

       Koda bakura ya faďi wa zynah, duk da bataji dadi ba,amma yaya zatayi, dole ta hakura, tun ana saura sati suka kwashi jiki zuwa maiduguri dukkkansu, babu wanda aka bari a abuja sai zynah kawai, duk abinda suke ciki daddy be saini ba, sabida ya rigasu tafiya".

    Bayan su bakura su tafi ne,zynah tayi kuka sosai, tunda suka isa aka fara wasa, har zuwa ranar daurin aure, ko wani prgrm da za'ayi tare suke zuwa da adyra, abu gwani sha'awa tankar basu faďi a tsakaninsu".

     Biki yayi biki kuďin da aka kashe faďinsa bata lokaci ne, bayan kwana biyu da biki duk suka dawo abuja, ya rage amare da angwayensu, suma ranar da suka ciki sati duk dawo abuja, washe gari kowa ya dauki matarsa zuwa kasashen waje cin amarcinsu".

   Anan gun bikin ne, malah yaga yarinya yace yanaso, bayan dawowarsu abuja ya sanar wa hjy Ashe, hjy Ashe batayi kasa a gwiwa ba ta sanar wa alhj maigidanta".

   Sali hali yafi sani kama, hakan yasa basuyi kasa a gwiwa ba suka tafi nema masa aure, nan take aka basu, haďe da sanya masu rana,.

     Tun daga ranan bakura yasha alwashin wannan tafiyar da zynah za'ayi da shike ba lokaci me tsayi suka saba, nan hjy khursum da hjy Ashe suka shiga shiri, kwana hudu ya rage biki suka tafi maiduguri, duk yadda bakura yaso tafiya da zynah wannan karonma haka hjy ta hana, a cewarta sai dai ya tafi da adyra idan yanaso yaje ta matarsa ne, idan kuma ba zaije da ita ba, to kuwa sai dai kuwa ya huta, jin hakan yace duk su zauna ba zaije da kowa daga cikin ba".

       Duk da haka hjy baya yarda ba, duk inda bakura zai shiaga idon hjy nakai, ko zatagansa da zynah, ranar da aka daura aure ita da ďangin su Ashe suka dauko amarya zuwa abuja, shima bakura da malah motarsu na bayan nasu hjy".

     Biki kam ya kawatu sosai, kwana damĝin amarya da ďangin hjy Ashe uku duk suka koma gida maiduguri".

  Duk a lokacin amarya na gidan hjy, bayan tafiyarsu ne hjy Khursum ta dauki amarya zuwa gidan mijinta, *gwarinfa L.I.D. STREET* hjy ta jima tana masu nasiha sannan sukai sallama, shima bakura be daďe ba yayi sallama".

Tun bayan biki hjy take zazzbi, amma a lokacin an dauka cikine, hakan yasa babu wanda ya damu, bayan kwana biyu, gani jikin nata babu daďi yasa bakura cewa zynah tana gama aiki tazo gidan hjy ta rika dubata, sabida yanzu gida babu komai".

    Idan zynah taje yau, gobe kuma sai Adyra taje, amma ita bai faďi mata ba, sabida ba a gidanta ya kwana ba".

    Zynah bata kiba, yadda bakura yace haka takeyi masa, ranar data fara zuwa, lokacin hjy na ďaki kwance, hakan yasa suka shiga har cikin bedroom".

    Bayan su gaisa bakura yace hjy ga zynah tazo tayaki zama, koda kina bukatar wani abu, take hjy tace bata bukatar komai sabida haka ta fita mata a gida, idan ba haka ba wlhy zata mata Allah ya isa"..

*kai jama'a kuji fa, koda hjy Khursum ke faďin haka, pakhryya na zaune kusa ta mirrow tana wasa. Wannan wani irin bakin haline dan Allah?"*

Jin haka yasa bakura cewa zynah ta tashi ta tafi gida kawai, zynah tasa hannu zata dauki pakhryya, kuka tasa tana zullo, akan bazata ba".

    Jin kukanta hjy tace idan kin san bada gidanku kikazo da ita to ina bukata ki ijeta".

     A sanyaye ta cire hannu daga jikin pakhryya ta fita, zuwa gida".

   Zynah na fita hjy tace wa bakura ya kira mata adyra tazo, bakura be musa ba, nan ya dauki wayarsa ya fara kiran adyra, ashe koda bakura ke kira tana zaune tana kallon wayat amma da batayi niyya ba, hakan yasan ta zuba wa wayar ido".


Bakura yayi kira har ya gaji da kira,bata gana ba, hjy tace yadai sake kira wata kila bata kusa da wayarne".

A kira na biyu shine adyra ta daga wayar haďe da sallama, bayan su gaisa ne bakura yake sanar mata hjy ce ba lafiya, kuma tace tazo sabida ita kadai ce a gida, koda tasamu abokiyar hira".

To kawai tace,ganinan zuwa".
Hjy da murnanta, bakura yace bari naje na dawo kafin tazo".

To hjy tace, tunda bakura ya fita, hjy kesa idon adyra amma shiru, gani har azahar yayi bata zoba yasa hjy daukar waya ta kira ta".

Adyra na kallo taki daga wa, ringing ďin wayar na tsikewa adyra tace, bazan zoba, haka kawai nazo ki addabeni da masifa".

Bakura be dawo gidan hjy ba sai bayan la'asar, yana zuwa hjy tasa masa kuka, gani haka yasa hankalin bakura ya tashi, da sauri yaje kusa da ita yana tambayarta meke damuta".


Tace kai ne ke mata ciwo, kamar zai rabe biyu".

To kin sha magani?"
Eh nasha amma har yanzu be sauka ba, gashi gaba daya jikina yayi min nayi kamar ba tawa ba".

Ina Ni',eemat ďin?"
Bata zo ba"...
Bata zo? Kamar yaya?"
Shiru hjy tayi".


Nan take ya dauki waya zai kirata, hjy ta hanasa".

Dole bakura ya hakura da kiran adyra, nan ya zauna yaci gaba da kulawa da hjy".

Gani har dare yayi be dawo gida ba, yasa zynah ta kirasa tambayesa yana ina?"

Gidan hjy ya faďi mata".
To kodai nazo ne?"
Aa ki bari kawai, da safe zan shigo".

To Allah ya kaimu, kuma ya bata lafiya".

Ameen ngd yace,sannan sukayi sallama".

Tun daga lokacin bakura be sake kiran adyra ba, itama bata nemesa na" yanzu ko gidan zynah baya zuwa, yana kusa da hjy, gani jikin nata kamar yayi zafi yasa bakura daukarta zuwa ssibiti, yana zuwa aka basu gado".

Acewar Dr jininta ne ya hau sosai, duk da suna iya kokarinsu a kanta amma ciwo kullum sai karuwa yakeyi, bakura ke kwana da ita, babu yadda zynah batayi ba,akan ya barta ta rinka kwana da hjy, amma yaki, ita kuwa goge batama kira ba balle tasan halin da ace ciki".


Ranar da hjy ta cika kwana uku a asibiti, suka tashi babu hannu babu kafa, bakinta ya koma gefe, tun cikin dare likitoci sukai cannn a akan amma sai a hankali, bakura kuwa idan ba kuka babu abinda yakeyi".

Nan ya sanar wa daddy halin da ake ciki, take daddy yace bakura ya dauketa zuwa egypt, jirgin karfe goma sukabi zuwa egypt, kafin su isa tuni daddy ya kammala komai, su kawai ake jira".

Suna isa aka dauketa zuwa asibitin, nan fa Dr ya shiga dubata, saida ya gama dube duben da zaiyi sannan ya faďi wa daddy iya dadadin kuďin da zataci, dashi ke ba shine damuwar daddy ba, take ya biya su, sannan Dr yake faďi masu zata kai kamar wata biyu ana jinyarta, kuma ya kamata ta samu wani kusa da ita".

Jin haka yasa daďi da bakura suka fara tunani wanda zaizo ya zauna da ita, gani wata kusan tafi wata kusan hakan yasa, bakura yanke shawarar tafiya dauko adyra tunda yarinyar kanwarta ce".

Washe gari bakura ya koma gida nigeria kai tsaye gidan adyra ya nufa, tunda yana nima a garesa dole yayi hakuri da duk wani abinda zata masa".

Tana zaune tana cika da batsewa, bakura ya dukar da kansa yace kina lafiya ya gida? Kiyi hakuri nayi tafiya ba tare dana sanar dake ba, wlhy jikin hjy ce sai a hankali yanzu haka ma tana egypt juya ta kaita"..

Da shiri tace subhllh, duk jikin ne haka?"

Eh wlhy, yanzu haka ma zuwa nayi mu tafi dare dake, sabida Dr yace zatakai wata biyu a can kuma tana bukatar wani kusa da ita".

To Allah ya sauwake, amma ni gaskiya babu inda zani, haka kawai dan nice er'wahali shine za'a daukeni naje jinya? Ba'a kaini dan daďi ba saida wahala yazo, wlhy babu in zani".


Yau ba masifa yakeji ba, hakan yasa shi yin shiruuuu har ta kare, sannan yace hjy ce fa, idan bataci darajan uwar mijinki ba, ai zataci darajan yayar mamaki""..

Yayan mamata kace, bafa mamata ba, sabida babu inda zani, iya kacina da ita addu'a".

Ran bakura yayi mugun bacc, a fusace ya tashi ya fita zuwa gidan zynah" Yana shiga be tsaya ko'ina ba sai bedroom, kan gado ya haye ba tare daya tube ba,rum da ciki yayi yana kwalla, shiruuuu ta zynah taji ne yasa ta shigo bedroom ďin, gani yadda ya kwanta yasa zynah gano babu lafiya".


Kusa dashi ta zauna, a hannnkali take masa magana, gani yadda takeyi ne yasa bakura faďi masa damuwarsa" Take tace akan dan wannan shine duk ka dami kanka? Idan har ka amince, kuma bazai zama takura a gareka ba, ni na amince zanje nayi jinyarta har lokacin da Allah zai bata sauki""..


Da sauri bakura dake kwance ya mike zaune yana faďin da gaske my zynah? "


Kai kawai ta ďaga masa tana dariya, sabida daďi bakura besan lokacin da yayi tsalle ya jawota jikinsa ya rungume ba"..

Nan suka shiga haďa kayan tafiya, da safe jirgin safe sukabi zuwa egypt """"""....

       
      
   

    









*mmn uswan ce📚✍*

  
🍀🍀🍀🍀

           _*ZYNAH!!!*_

               🍀🍀🍀🍀

*WRITTEN ✍ BY MMN USWAN*
_______________

©©©©©©

_*follow me on*_        

_*wattpad:Hauwa s zaria*_

_*Facebook group*_
_*Mmn Uswan*_

          *THE🔚🔚*      
https://www.facebook.com/groups/157572201857733/

           ➿➿➿➿➿➿

_*BISLLAHI RAHAMANI RAHIM*_

_*In the name of Allah, The Beneficent, the Merciful*_



_wannan book ďin sadaukarwa ne ga taskar ďan-hamza, a gaskiya ni nama rasa ta iya zan fara domi gaba daya banida kalmomin da zanyi amfani dasu wajan godiya a gareka,sai dai kuwa nace Allah ya saka da alkhairi, wannan litafi sadaukawa ne gareka tare da babana Abubakar sadiq namiji *1* Allah ya amintarmin dakai, yasa kafi haka, ya karemin kai ya kuma bani uwa tagari Amen_


*KORAFI*

_naji korafinka sosai akan AISHA ayi hakuri ba laifina bane, haka ta ďoro mana, amma ga kaina bisa kan wiyata, afuwan afuwan insha Allahu hakan bazai sake faruwa ba, ko ba komai nima AISHA uwa tace, kakoga ance uwa mafi uban koda uban sarki ne,ngd ngd sosai_


🅿4⃣5⃣-5⃣0⃣

"Bayan isar su egypt a yanayin da zynah ta gama hjy a ciki, tayi matukar tausayawa hjy, kukan ba'a magana, daga ita har Bakura babu me bawa ďan uwarsa hakuri, daddy ne yayi karfin hali ya yayi masu magana, da kuka ba shine mafita a gare ta, addu'a kawai take bukata".

     Tun daga lokacin  daga zynah har bakura babu abinda sukewa hjy sai addu'a subata tasha ragowa kuma su fasha mata a jiki, likitici suma suna iya kokarinsu, amma duk da haka shiru kakeji, babu wani alamar sauki, kashi a kwance fitsari ma haka, gani haka ne aka koma yi mata amfani da pampas, na safe daban na rana daban haka ma na dare, wani lokaci ana sanya mata take batawa".

    Duk kwana biyu uku daddy ke zuwa  daga germany yake dubasu, shima bakura lokaci-lokaci yake zuwa nigeria yana duba shago, da shike akwai amana,hakan yasa suke tafiyar da harkan business ďin yadda ya kamata, sai dai abinda baza'a rasa ba".

      Sati hjy biyu a egypt sannan aka sanar wasu Am'abuwa da Yah-na, ranar da aka sanar dasu, washe gari Am'abuwa ta taso daga chana zuwa egypt, ita kuwa Yah-na sai bayan kwana uku sannan tazo".

      Am'abuwa tayi kuka ba kaďan ba, tun daga lokacin ta roki maigidanta arzikin zata tsaya tayi jinyar mamanta" Da shike mai fahimta ne, bai nuna damuwa akan hakan ba".

           Saida yayi kwana uku sannan ya koma ya ya barta a gun".

       Tun daga lokacin komai tare sukeyi, hakan yasa aiki yayi wa zynah sauki, ba kamar  dah ba".

      Sati Yah-na daya ta koma England wajan maigidanta, da shike shi be zoba,iitace kawai tazo".

      
             ~~~~   ~~~~~   ~~~~

                   _*KUNCI*_

Tun bayan rasuwar malam shehu , zainab ta fara gani canji daga gun usman, zagi da gori kuwa abin ba'a magana, daga shi har danginsa, balle tunda asiri ya tonu kowa yasan rakiya tayi sanadiyar malam shehu ya kori Amina daga gari, hakan yasa kullum magana ya tashi tsakaninta da dangin miji basu yi masa ta wasa, yanzu haka fita unguwa niman gagaranta yakeyi, abinka da kauye gidan suna da gidan biki, idan taje basu da aiki sai habaici, wasu kuma a gabanta suke faďi mata".

     Bayan sati bati da bikin kannin usman ya tada maganar aure zaiyi, sabida shi yanaso yadda aka haifesa shi ya haifi nasa, zainab da rashin hakuri da bancewar basira, kuma dama shifa gwano bayajin warin jikinsa, zainab najin sunar yarinyar da usman keso nan ta hau masifa da bala'i tana faďin wlhy idan har ina raye baka isa ka auro karuwa wacce ta kare rabawa maza kanta a waje ba, duk garin nan babu uban da besan uwani er'iska bace"..

    Dariya usman yayi haďe da cewa da gaske? Ke zainab idan kin san abinda kira kunya, ke kinada bakin da zaki buďe ki kira wata da sunan karuwa? To wlhy idan ba tonan asiri kike nema ba, nima kike nayi maki tonan asiri ba, gwama ki kama kanki da bakinki, in har kikaci gaba da aibanta min matata na lahira saiya fiki jin dadi".

   Banza er'iska er'mai mugun hali kawai, duk garin nan babu wanda besan mugun halin uwarki rakiya ba".

   Baďe bakin zainab tace badai uwata ba wlhy""".....

   Kafin ta rufe baki tuni usman ya dauketa da mari haďe da shaka, yana faďin sai uwarwa? Ehhh ko nace sai uwarwa?"

   Shiruuuuuu tayi sabida shakan da yayi mata yasa ta kasa magana, usman yaci gaba da cewa babu mamaki zaman gidan ne kika gaji dashi yasa,idan banda butulci irin taki zainab ke har kina da bakin da zaki buďe ki zani wani dan yayi karuwanci?"

   Kwalla ne kawai suke zubo wa zainab daga ido, gani haka yasa usman ya saketa haďe da binta da tokari, faďi tayi a kasa tasa kuka tana faďi Allah ya isa mugu kawai kuma wlhy sai Allah ya sakamin".

    Kai da gske, ashe dai wanda Allah zai saka mawa suna da yawa"..

      Muguwa azuluma kawai, duk na tattara aci burin zan rakarkashi amarci nima naji abunda kowa keji a ranar daren farkonsa, ashe

Please Login or Register in order to submit comment