Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sallama"

Tana hjy, dama kira nayi na sanar dake, muna asibiti".

Da sauri hjy tace keda wa?"
Amina ce ta haihu"..
Kafin ta karisa maganar, tsaki hjy tayi, sannan tace, saime?dan ta haihu?".

Jin haka yasa Am'abuwa ta fara yiwa hjy nasiha, cikin masifa hjy tace,ke dakata nifa na haifeki, bake kika haifeni ba, sabida haka kisan abinda kika ciki, idan ba haka ba, ranki ya baci".

Sake wani tsakin tayi haďe da kashe wayar ta".

Bakura dake zaune kusa da ita, kallo daya yayi wa Am'abuwa ya gano ba alkhairi hjy ta faďi akan haihuwar ba, ďan karamin tsaki kawai yayi, aroud 12PM daya daga cikin nurse ce ta fito tace subada kayan da za'a sawa baby".

Dukkansu a lokacin ne, suka tuna da maganar riga, hannu yasa aljihunsa ya cire A.T.M ya mikawa Am'abuwa yace taje ta cire kuďi, tayi siyayyar daya dace".

Zynah bata falka ba,sai bayan azahar, ta samu sauki sosai, akan yadda suka kawota".

Saida bakura yaga zynah ta samu sauki sosai, sannan ya kira daddy ya sanar masa da haihu".

Daddy yayi murna sosai da kuma fatan Allah shi ďaiyaba".

Kwanan zynah biyu a asibiti aka sallamesu suka koma gida, bayan su koma ne, bakura ya kira daddy ya faďi masa yadda sukayi da hjy, da kuma dokar data sanya masa, murmushi daddy yayi sannan yace kada ya damu, zai mata magana".

Koda daddy yayiwa hjy magana duk a banza, maganar kada ya fita a gidan Adyra kan ta yafe masa,amma zuwa duba mai haihuwa kam babu yadda daddy bai yiba amma taki zuwa dubasu".

Tunda suka dawo daga asibiti Am'abuwa ce ke kwana dasu, ita kuwa Yah-na, ko lekau, batazo ta duba suba, balle taga baby, hakan bai dami bakura ba, sabida yasan ta hannu damar hjy ce".

Gani haka yasa bakura tafiya gidan hjy Ashe yaje ya sheda mata, hakuri kawai ta bashi, sannan tace kada ya damu zatazo tayi mata magana, koda hjy Ashe tazo tayi mata magana, nan ma duk a banza, daga karke dai, daga karke dai zuwa tayi taje gidan bakura ta dauko babyn ta kawo mata akan tasa mata albarka".

Mikewa tayi tabar mata ďakin, kaďan ya rage ma ta ture baby ta faďo daga bakin gadon da aka ijeta".

Sabida bakin ciki har kuka saida bakura yayi, haka kullum yake yawo, a gidan zynah yake yini shida Am'abuwa, baya tafiya gida sai dare, saiya barsu da Am'abuwa, dama tunda suka dawo daga asibiti Am'abuwa take kwana dasu".

Kwana hudu da haihuwa hjy ta kasa ta tsare dole sai dai Am'abuwa ta dawo gida, idan ba haka ba zata tsine mata, babu shiri ta koma gida".

Suleja bakura yaje ya sanar wa kanďe da haihuwar zynah, kuma yanaso tazo ta zauna dasu har tayi arba'in".

Bayan tayi masa barka ne tace itafa bazata samu zuwa ba, sabida anan take samu tayi sanar da take cin abinci, amma idan ta bisu waye zai bata kuďin da take samu?".

Bakura yace kada ta damu,tayi lissafi tun daga ranar daya dauketa har zuwa ranar da zata dawo zai biyata".

Nan ya dauketa suka tafi abuja,

Abu namu magani a kwabemu, bakura da kansa yaje shago ya haďo wa zynah kayan su turare, na jiki dana ďaki, da kuma na gyaran jiki, nasha dana tsarki, da kansa duk ya gwada mata yadda zatayi amfani dasu" Sannan ya dauki Am'abuwa sukaje kasuwa, ita ta zubawa zynah kayan fitar suna masu rai da motsi, basu dawo gida ba, saida ta nuna masa telan da yake masu ďiki, suka bashi kayan kuma yace zuwa jibi yakeson kayan".

Nan suka tsaďance ya biya"

Ban garen Adyra kuwa, ashe yawan fitar da bakura keyi yana damuta, tanaso da tambayesa amma tana shakkansa, amma yau kuwa yariga tasha alwashin saita tambayesa inda yake zuwa yakai dare, gashi yana sallar asuba idan yabar gidan baya dawowa sai dare".

Da shike, gobe suna, tunda ya fita bai dawo gidan ba sai bayan *11:PM* tana zaune a falo tana jiransa, yana isowa da sallama ya shigo, Adyra na zaune amma bata amsa masa ba, juyawar da zaiyi ya ganta zaune, sannu da gida kawai yace, yasa kai zuwa ciki".

Da sauri ta bisa cikin ďaki, yana shiga ya fara tubewa, Adyra itama tana shiga ba tare data dubi fuskansa ba, tana wai kai dan Allah ina kake zuwa ne, kakai har dare baka dawo gida ba?"

Tambaya kika ko niman sani?".
Tambaya nakeyi".
To gun matata nake zuwa"...
Wht????".
Tace" Sannan tace, kai haba wasa dai".


Ina wasa dake ne, balle har kiyi tunani ba gaskiya nake faďi ba? Ko hjyn da taje niman auren naki bata sanar dake inada mata bane?"

Take hankalin Adyra ya tashi, domin duk maganar da bakura ke faďi gani take kamar wasane".

Nan take ta sulale ta faďi a kasa, idonta nakan bakura kam, ko kibtawa batayi, shiruuuuuuu tayi na ďin wani lokacin, can kuma kamar wacce aka tsikara, da sauri ta mike, haďe da cewa wlhy karyane, baka isa bakura, nice da kishiya? It can possible".

Bakura naji haka murmushi kawai yayi mata, ba tare daya tanka ba, yaci gaba da tubawarsa, yana cikin rire riga kenan tayi tsalle ta cukuikuye masa rigan, yadda ba zaiga gabansa ba".

Sakeni, kawai yace mata".
Kin sakinsa tayi, saima tsine masa da takeyi, tana faďin Allah ya isa, shegu tsinannu, ma yaudara".

Tambayar darko da bakura yayi mata, shine, waye ma yaudaran? Ni ko su hjy?"

Oho, koma waye, kuma wlhy yau saika sakeni, azalumai kawai"..

Kafin ta rufe maki, ji kawai tayi tass tass tass, har sau uku akan fuskanta".
Wani irin ihu tasa, nan ta kara rikesa sai dai suyi ďanbe".

Igijeta yayi ta faďi a gefe, sannan ya a karisa tubewarsa, gani ta dauki waya tana kuka, daga gani iyayenta zata kira, yasa bakura karbe wayar, dashi ya shiga toilet, bayan yayi wanka ya shirya, da wayar yaje falo ya kwanta, duk zagin da take masa, be tanka ta ba".

Ranar kwana tayi tana tsine su hjy da daddy" Duk abin yana masa ciwo, amma haka ya ďanne, domin a cewarsa ba'anan ya kamata ya hukuntata ba".


Da safe kuwa yana sallar asuba yayi wanka ya fita, be bar mata wayar ba, dashi ya fiya, yaje gun suna" A masallaci ya raďa wa yarinyarsa suna *FATIMA* sunan anty Am'abuwa kenan, amma zasu rinka kiranta da *PAKHRYYA* yau kusan kwana yayi a gidan"


Washe gari bayan kanďe tayi pakhryya wanka ta shirya ta, bakura ya dauketa zuwa *WUSE MARKET* gun wanzamai ya kaita, zani sukayi mata, irin nasa, na barebari,sannan ya dawo da ita".

Tunda Adyra taji cewa bakura yana da wata matan bayan ita, ta daina kulasa, ko a jikin bakura, sabida ba itace a gabansa ba".

Bayan kwana buyu da suna, yace ta shirya zasu tafi unguwa, da farko kin zuwa tayi, saida ya fito mata a namijinsa sannan ta dauki mayafi suka fita, kai tsaye gidan su hjy suka nufa".

Gani gidan hjy ne, tace bazata fita a motar ba, itafa saida ya medata gida, ďan bataga abinda zatazo tayi a gidan ba".

Fika ta karasa, hannu yasa ya fisgota, janta yakeyi kamar wani kayan banza, har zuwa ciki".


Suna shiga falo yayi hurgi da ita, dai-dai lokacin hjy na fitowa daga ďakinta, gani hakan yasa ta fito da sauri haďe da tambayar lafiya?".

Jin haka yasa Adyra fashewa da kuka" Bakura yana shigowa yace dama alkawari na dauka wa kaina, bazan hukuntaki a gida ba sai a gaban hjy, dan haka yanzu zan maki hukunci dai-dai da laifinki".

Hjy najin haka tace subhallilahi, me zangani haka?
To wlhy baka isa ba, a gaban tawa?"

Dukawa yayi har kasa yace, dan Allah hjy kiyi hakuri, domin nariga nayi alkawarin hakan, sabida ita bazanyi kaffara ba".

Cike da mmki tane,
Mai tayi maka?".

Ba tare daya tanka hjy ba, yaci gaba da cewa, ke idan kinada kunya kyayi magana? Banza wawiya sha-sha-sha, mara kamu kai, Allah wadarai dake, banza er'iska kawai"...

Kafin ya karisa, tuni hjy ta daukesa da mari, tana faďi lalla bakura, abin naka har yakai ga haka? A gaban tawa? Zaka rika zaginta".

Faďa sosai hjy taci gaba dayi masa, duk yadda bakura yaso yayi mata bayani amma hjy taki sauraransa, da zuciya ya ďibi bakura ficewa yayi ya bar gidan".

Kai tsaye kasuwa ya nufa, bai sske bi ta kanta ba, saida dare yayi sannan yazo ya dauketa, zuwa gida. Har yasa kafa zai fice yasake juyowa yace, na rantse da Allah idan kika leka nanda bakin kofa Allah ya isa ban yafe maki ba, sannan yasa kai ya fice daga gidan" Tunda yabar gidan, gidan zynah ya koma da zama, bai sake bi ta kanta ba".


*★★★★ ★★★★*


Kwaanci tashi babu wiya, har zynah tayi arba'in, daga ita har pakhryya sun gare suyi kyau sosai, musamman ma pakhryya tayi wayo sosai, ita kuwa zynah tasha gyara har taji babu daďi, ina ruwan nida abata, bakura ka gyara ďah/ matan wasu ma balle taka".

Kanďe nata koma gida sulaje ba, saida takai kwana hamsim sannan bakura ya haďa mata sha tara ta arziki, sannan ya kaita har gida, gani irin hidimar da yayi mata,ba karami daďi taji ba".

Ban gare Adyra kuwa, hankalinta yayi matukar tashi, sabida yau tsawon kwana arba'in kenan batasa bakura a ido ba, gashi kuma batada da kuďi a waya balle ta kirasa, ko takira hjy ta sanar mata da abinda ake ciki".

Bakura yana meda kanďe gida, be biya shago ba, gida ya dawo kai tsaye hannu biyu ririke da kaya, ganisa rike da kaya, da sauri zynah ta ije pakhryya dake hannunta tazo ya amshisa, haďe da yimasa hannu da zuwa".

Murmushi bakura yayi, sannan yace kema sannu, gani zata zauna ne yasa bakura cewa a'a zo muje daga ciki, hannu yasa ya dauki yar'sa, sannan suka shige bedroom".

Suna shiga ya kwantar da pakhryya a gefe,sannan ya zauna a bakin gado, hannu yasa ya dauko ledar daya shigo dashi, nan yafara ciro kayan daya bayan daya, kayane nata dana pakhryya, masu kyau da tsada, sabida murna zynah batasan lokacin da tayi masa tsalle a jiki haďe dayi masa godiya, shima rungumeta yayi yana meda mata da dariyar da take masa".


Runguma sosai bakura yayi mata, gani zayi mata kiss da sauri ta nimi sauka daga jikinsa, gani haka bakura yace lafiya my zynah?".

Shiru kawai tayi, ba tare dace masa komai ba, hannu yasa ya sake jawota jikinsa, a sanyaye tace dan Allah kabari".

Na bar me kuma zynah?"
Abinda kakeson yi mana".
Mamaki ya kamasa, kasake jawota yayi jikinsa yace zo my wife, faďimi manene?".
Babu komai, kawai tace".


A'a my minel ban yarda ba, gani tashi shiruuuu yasa bakura fara shafeta a hannnnkali haďe da lalabarta, kuka zynah tasa tana faďi masa irin wiyar da tasha lokacin haihuwarta, da kuma yanzu ummanta takeson gani".

Hakuri ya bata game da maganar wiyar da tashi a lokacin haihuwar, maganar zuwa gun umma kuwa, cewa yayi sai yaje suleja ya tambayi kanďe, address ďin garin, idan ta bashi sai yazo suyi shirin tafiya".

Da sauri tace,a nima nasan hanya, zanma iya zuwa da kaina".

Da sauri bakura yace, niwa!! Dan Allah ki rufemi asiri, idan ba so kike kisani a wani hali ba".

Dariya zynah tayi masa, haďe dayi masa gwalo, Au!!-ni kikayi wa haka?".

Jin haka yasa zynah sauka daga jikinsa da sauri, gudu tasa zata fice daga ďakin" Shima binta yayi da gudu yana kokarin kamota, nan suka fara zagaye ďakin".


Idan bakura zai kamota, sai ta doje masa,daga haka, da gangan yayi kamar santsi ya daukesa faďi yayi yana faďi wayyoooooo Allah na" Gani haka yasa zynah zuwa a guje ya faďa kansa tana fsďi subhallah, dan Allah ka tashhiiiiii". Karafffffff yayi ya riketa yana mata gwalo, tana kokarin mikewa ta gudu, wufffffff yana ya dauketa ya dorata a jikinsa, matseta yayi a kirjinsa yana kashe mata ido, haďe da tsikaranta, idan tayi tsalle sai bakura yasa dariya, da haka har wasa ya canza".


Ban garen Adyra kuwa, gani yau bazata iya hakuri ba, bedroom taje ta dauko mayafinta, ta fita zuwa gidan hjy, da kuka ta shiga gidan,a gigice hjy ta mike da Ni'eemat lafiya? Me yake faruwa?"

Nan ta kwashe komai ta faďiwa hjy, tana kuna, kamata tayi ta zaunar da ita, ďaki taje ta dauko wayarta, nan tafara kiran number bakura,hjy tayi kira yakai ten misss call amma bakura be daga ba, gani haka yasa hjy ta kira yaran shago, bayan su gaisa ne take tambayarsu bakura, yace ai yau kwata-kwata oga bezo shago ba yau".

Jin haka yasa hjy bata tsaya bata lokaci ba, hijab kawai ta dauka, ta fice zuwa gidan bakura, tana shiga a falo ta tsaya tana doka sallama, lokacin su bakura suna ciki, yana kan network, balle yadda ya daďe be ha'u online ba, shiruu da hjy taji yasata sakai zuwa cikin bedroom, tana shiga ganinsu tayi hajaran majaran, ihuuuu hjy tasa tasa salati, tana faďin na shiga uku, da jego amma kuke iskanci"!!!


Saida fa hjy ta koma falo kenan, take faďin haka, domin tana ganisu cikin wannan yanayi komawa tayi da baya".

Su bakura kuwa duk besan hjy nayi ba, zynah ce taji, kuma babu yadda batayi da bakura ya sauka ba,amma yariga yayi nisa, baysjin kira, balle yadda ya gwarata da kansa, abin bana wasa bane".

Hjy tafi thirty minutes tana jiransu amma basu fito ba, dole yasa hjy ta tafi".

Koda ta koma gida, Yah-na ce, tace kin dawo?".

Shiru hjy tayi, domin gaba daya wani iri takeji, ta rasama meya kanta gidan?"

Hakuri ta sake bawa Adyra, tace ta tashi taje, da kanta zata kawo bakura har gida".


Bakura kuwa saida yakai jeki, sannan ya dashi,daga kan zynah, bayan suyi wanka ne, zynah take sanar masa da zuwan hjy, da mamaki, yace shifa kwata-kwata bemaji zuwanta ba,jawota yayi suka kwanta, tare da pakhryya, ra suka sata a tsakiya"..

Suna cikin hira kenan saiga kiran hjy ya shigo wayarsa, a lokacin ne yaji kunya, da zynah tace hjy tazo ta samesa haka".

Amma yaya zaiyi, dole yasa ya mike yasa kaya yaje, kunya ya hana bakura daga kai su haďa ido da hjy, duk da itama haka ne a gareta, amma sai ta daure fuska, ta faske".

Nan ta tambayesa, dalilin yin haka".yau da yake da lalama ta bisa, yana duke a gabanta, ya zauna mata komai, harda watsar da budurcinta da tayi a waje, sannan kuma ya tambayeta dalilin boye mata aurensa da sukayi"...



*~~~~ ~~~~~ ~~~~*

_*KUNCI*_



dan Adam kenan, kekikace an haihu, kuma kikace ďah ya koma".

Tunda rakiya ta amshi girki, ta hana sadiya, idan har taga malam shehu yashiga ďakin sadiya kusan kwana takeyi bata bacc, sabida bakin ciki".

A zuciyarta tace bazai yuwu ba, me girki daban me kwana da jiki daban, to wlhy cikin ciyu saidai ayi daya".


Daga lokacin ta fara lissafi, gani girki ya dawo kanta, rakiya ta tubure tayi furrrrrr tace, sai dai tace sai dai cikin biyu ya zabi daya, domi tagaji da yiwa kantuwar banza aiki, ita kuma tana kwana da miji".

Tun daga lokacin malam shehu ya daina shiga ďakin sadiya".

Bayan kwana biyu,bayan rakiya ta kare girki, barinsa tayi kitchen ďin ta koma ďaki, batafi minti biyar da shiga ďakin ba, tafara ciwon ciki, nan tasa zainab takira mata sadiya, bayan sadiya tazo, tace dan Allah ta taimaketa taje kitchen ta dauko mata abincin malam shehu, bata musa ba, sabida gani yadda take murkusu-murkusun ciwon cikin".

Tana daukowa ta ije sannan ta fita, bayan ta fitane, rakiya ta mike haďe da kwashewa da dariya, bayan malam yazo cin abinci, da sauri rakiya ta rike masa hannu tana faďin a'a malam ban shirya takaba ba, dama na barshi ka gani a matsayin sheda ne, malam da rashin fahimta yace, nifa ban gane ba rakiya ".

Nan rakiya ta shirya masa karya da cewa, da idona naga sadiya tana zuba maka guba a cikin niyar, ni kuma dai-dai lokacin ina fitowa wanka, na ganta, ita kanta bata san na ganta ba, idan kuma kana gani kamar karyane ka kirata kasa taci miyar a gabanka".


Kwaďawa sadiya kira tayi, da sauri ta fito daga ďaki, taje jin kiran malam, tana zuwa malam yace saidai ta dauki miyar taci a gaban sa, sadiya tace itafa bazata ciba, sabida batasan abinda rakiya ta zuwa a ciki ba, nan take rakiya tasa kuka da cewa sadiya tana tayi mata shirri".

Wannan ya faďi, wannan ya faďi, nan faďa ya tashi, gani haka yasa malam shehu koran sadiya daki, tun daga lokacin koda gaishesa tayi baya amsawa, ita kuma rakiya ta daina sawa yaran sadiya abinci, duk da malam yana gani amma beyi magana ba".

Suyi shari'a a gun mai gari har su gaji, amma besa malam shehu ya canza hali ba, gani haka yasa sadiya barin gida, ita da yara, ta koma gidan iyayenta, duk da babu kowa a cikin gidan, domin iyayenta duk su rasu, amma hakan be hanata zama ba, nan suka fata malejin rayuwarsu, tana soya masu gyaďa suna talla, a nanne suke samu abinda zasuci".

Tun daga lokacin da sadiya tabar gidan rakiya ta shiga yiwa malam shehu rashin mutunci iri-iri, zainab kuwa idan ta fita tun safe bata dawowa gidan sai dare, gani haka yasa malam shehu yace aure zaiyi mata ya huta".


Hakan yasa ya bada sadakarta ga garon maigari, domin dama kwanaki maigari ya bata basa magana akan zainab ďin, yace yana nima wa ďansa".


Ba'a dau lokaci ba, akasha biyan zainab da usman, usman yana murna zai ragargaji amarya, sai kuma be samu haka ba, ko kufar * kuyanbana* dake zaria be kaita buďewa ba, tun cikin daren ya naďa mata duka, domin kuwa usman ba mutuncine dashi ba, balle dama gani yake kamar wani uban kuďine ubansa ya kashe a wajan nema masa aurenta".

Da safe ta tashi zata tafi gida, yace wlhy idan har tasake tabar gidan to kuwa a bakin aurenta".

. dole yasa zainab ta hakura ta zauna" Kullum cikin zagi da cin mutunci, babu irin wanda bata gani a gun usman".


Ban garen malam shehu kuwa, tun bayan bikin zainab yake zazzabi,"""..



~~~~ ~~~~~ ~~~~

Koda bakura ya tambayi hjy da lilin boye wa Ni'eemat yanada mata da tayi, hjy bata bashi amsar haka ba, faďi dai tayi wa bakura sannan tace idan baso yake tayi masa bakiba,dai to".


Sani hali yafi sani kama, tan daga lokacin bakura ba karamin kiyayewa yakeyi ba, amma fa bai hanasa zuwa gidan zynah ďinsa ba, idan ya rage gajiya saiya tafi kasuwa".


Bayan kwana biyu hjy da kanta taje gidan, bakura lokacin yariga ya fita kasuwa, bayan su gaisa, hjy tace Ni'eemat".

Na'am hjy"
Gunki nazo, wata magana nakeso muyi dake, amma kuma inaso ki faďi min gaskiya, faďin gaskiya da zakiyi shi zaisa na sami maganin matsalar dake yawan shiga tsakaninku da mijinki,amma idan kikaki faďi min kuma tofa babu ruwata, da duk wani matsalar da zai sake tasowa a tsakaninku".


Mijinki yace bai sameki cikakkiyar mace ba, kada kiji kunya, ni uwarki ce, zanso ki faďimin gaskiya".


Nan tasa kuka, tana faďin eh hakane"
Salati hjy tayi ta sanar da ubangiji, sannan ta tambayeta garin yaya?"

Shiru tayi sabida batada amsa".

Gani kukan da takeyi yasa hjy, cewa kiyi shiru, ki daina kuka haka, Allah ya kiyaye gaba, kuma insha Allahu babu zanda zaiji wannan maganar, idan har wannan maganar ya fita wani yaji, tofa kece,amma bani da bakura ba, sai dai wani hanzari ba gudu ba, daga har iyayenki ban faďi masu kamar bakura yana da wata mata ba, kafin ke, kuma bana bukatar susan haka".


Ni'eemat idan har kika rufe wannan maganar to wlhy ina mai tabbatar maki babu wanda zaiji, Ni'eemat kifi kowa sanin a al'adarmu ta barebari babban abin kunyane ga iyaye ace yar'su batakai budurcinta gidan miji ba"


Ni'eemat idan har kika rufe wannan maganar, ina me tabbatar maki babu wanda zaiji abinda kika aikata".


Ni'eemat tasan hakan ba karamin abin kunya bane ga iyayenta idan wannan zance ya fita da sauri tace, naji kuma na amince, insha Allahu babu wanda zaiji"
Nan sukayi sallama".


Tunda daga lokacin hjy tasawa bakura ido sosai, duk motsin da zaiyi akan idanta, gashi ta tsani pakhryya dan ji takeyi kamar ta rufe ido ta bude taga bata raye".

Koda Am'abuwa ta daukota yini, ko kallo bata ishi hjy ba, haka kuma koda kukan jini zatayi, idan Am'abuwa bata kusa, hjy bazata dauketa ba, idan ma tare suke, sai dai ta tsallakata ta shige ďaki".

Yanda bakura yakejin zynah yanzu, koda yau ne yafara sanita sai haka, ga uban maganin mata dayake ďurra mata, planning kuwa tuni ya dade da bata magani tsarin iyali, wanda zai dauketa har shekara biyu".


Hakan yasa yanzu yake like da ita, dan ma hjy tasa masa ido ne, babu yadda zaiyi".

Gani takuran yayi masa yawa, karya ya shirya wa hjy, da cewa zaiyi tafiya zuwa *DUBAI* domin akwai wasu turare da mayuka da suka kare, gashi kuma ana bukatarsu sosai, idan haka yakeso yaje dubai ko zai samu, amma idan bai samu ba zai wuce har india,domin duk cikin kayan shagon sufi kawo kudi".


Jin haka yasa hjy bata musa ba, saima fatan alkhairi da tayi masa".

Yah-na ba matsalarsa bane, Am'abuwa kuwa ce mata yayi zaika zynah suleja idan yadawo daga tafiya zaije ya dauketa" Itama Adyra

Please Login or Register in order to submit comment