Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya mike, abinda zynah tayi ya batawa malam shehu rai amma yaya zaiyi, duk da har yanzu besan gaskiyan lamari ba, amma a yadda yaji rakiya ke magana yasan akwai alamar tambaya".

Yana mikewa suka fita, har ta kami hanya, bakura yace tazo suje a mota".

Cike da takaici malam shehu ya gangara ďakin rakiya, bayan ya zauna ne, cikin dabara da lallashi yake tambayar rakiya, akan furucin da yaji tanayi".

Rakiya bata boye masa komai komai ba".

Salati yayi ya sanar wa ubangiji, haďe da kiran rakiya kin cuceni, wlhy bazan yafe maki ba, duniya da labahi, yanzu da wani ido kikeso na kallo sadiya da Amina, banga laifin Amina ba duk abinda tayi, kuma insha Allahu a yau ďin nan sadiya zata dawo ďakinta, ita kuma Amina zan roketa gafara, akan abinda duk ya faru".

Cikin kuka rakiya tace sai me, idan kadawo da sadiya gidan nan, tazo mana, wlhy sai dai idan ba ni rakiya ba, domin sai tayi data sani dawowarta gidan nan, makwadaicin banza makwaďancin wofi, daga gani mota har jikinka na rawa, to wani yasani ko kuďin shan jini ne, domin ance yaeanci masu kuďin birni duk rn'mafiya ne".


Ba dare da malam shehu ya tanka mata ba, ya fice daga ďakin".

Su zynah suna isa kofar gidan ummata, tun kafin bakura yayi baki, hannu tasa zata buďe motar da fita, kallo daya bakura yayi mata ta dakata, har saida ya sami gu yayi parking, saida ya fita ya zagayo ya buďe ya amsa pakhryya sannan ta fito, dai-dai lokacin da hauwa na fitowa daga daga cikin gida, da sauri ta kwaďa mata kora da hauwa!!".


Hauwa na juyowa suna haďa ido da Amina, a guje Amina taje ta rungumeta tana kwalla, haďe da tambayar ina umma?"

Cike da mamaki sabida hauwa bata gane ta ba" hakan yasa ta tsorata da Amina, balle suna haďa jiki wani irin laushi da kamshi taji na tasowa daga jikin Amina, take jikon hauwa ya fara rawa".

Zynah dake rungume da ita, tana sakin hauwa a guje hauwa ta ruga cikin gida haďe da kwadawa umma kira, da sauri umma ta fito daga daki tana tambayar lafiya hauwa irin wamnan kiran haka? Umma umma da wasu mutane suzo suna tambayarki, wlhy umma matar kamar balarabiya,dariya umma tayi haďe da cewa labarabi kuma"".

Sallamar bakura ne ya katse umma, da sauri ta dago kai, zynah dake bayan bakura tana hango ummata a guje taje ta rungume umma haďe da fashewa da kuka,tana kiran ummata, umma,ashe dama zan sake ganinki a rayuwata?"


Itama umma dake rungume da zynah kukan takeyi, shiko bakura tsayawa yayi yana kallonsu, da'kar umma ta sai saita kanta, sabida gani subar mutum a tsaye, hauwa akasa ta dauko tabarma, ta shinfiďa mata ya zauna, hauwa dason yara hannu yasa ta dauki pakhryya, duk da dai batasan alakar dake tsakaninsu da ita".

Duk da kiwan pakhryya amma da hauwa ta mika hannu zata dauke ko musu bayi ba, taje".

Ďaki umma ta koma ta sanyo hijib sannan ta fito, kusa da bakura taje suka gaisa, lokacin itama zynah ďin ta shiga ďakin ummata, bayan su gaisa ne, umma take tambayar sa daga ina?".

Murmushi bakura yayi, sannan yake sanar da ita waye shi, wani kokan umma ta sake fasawa dashi, tana wa ubangiji godiya, bayan sallar isha lokacin su gama komai, umma da zynah da kuma bakura suka zauna suna hira, su hauwa da Fatima suna gefe rike da pakhryya suna mata wasa ita kuwa sai faman wage baki takeyi".

Nan bakura ya kara tambayar umma asalin abinda yasa zynah tabar gida" Umma bata boye masa komai ba, hatta sanadiyar barinta gidan malam shehu, tayi tana kuka, zynah dake zaune itama kukan takeyi, bakura ya tausaya masu matuka".

Shima bakura be boye mata komai ba, akan aurensa da zynah" *shi ciki ba'a yisa dan cin tuwo kawai ba, hakan yasa bakura be faďi wa umma abubuwan da suka faru dashi kafin aure ba"*

Su hauwa da Fatima umna tasa suka gyara wa bakura ďakin dake zaune, zynah ta kara gyara masa, duk ta feshe dakin da turare".

Gani 11:PM yayi yasa umma cewa yaje ya kwanta, sabida gajiyar hanya, ummace ta fara mikewa, sannan bakura ya mike, gani zynah dake zaune bata mike ba, umma tace tashi kije ku kwanta mana, wani irin kunyane zynah taji, domin taji maganar yayi mata wani banbanrakwaiiii" Babu yadda zatayi dole yasa ta mike, shi kuwa bakura jin haka dariya yayi haďe da yi mata gwalo".

Dole yasa ta mike suka nufi ďakin, yana jawota yayi suka faďa katifa, yana mata dariya, da cewa wato dan kinga umma shi ne kika guduna ko? To ai ba kekadai ce da umman ba, har dani, dariya zynah tayi sannan tace nima bance nikadai ce da ita ba".

Ohh bakura yace, haďe cewa kima ce mana, duk dariya sukasa, su daďe suna hira sannan sukayi sallama, ta tafi dakin umma, nan suka dora sabo hira, na kuka dukkansu suyi kuka na dariya kuma suyi dariya".

Kafin gari ya waye maganar zuwa zynah duk ya karaďe gari, labari har wajan maigari, hakan yasa maigari yace yanason ganisu, tare sukaje har gun maigari, daga maigari har en'gari zuwa sukeyi ana kallon zynah, zainab ma tazo, duk da taji daďin gani er'uwanta amma kushe da hassada ya hanata da nuna jin daďin, da kuma tsoron ummata".

Anan ne magana ya fashe, kowa yasan gaskiyan san gaskiyar zance, malam shehu ba karami kunya yaji ba, bayan su koma gida hakuri sosai ya bawa Amina, haďe da rokon ta yafe masa, Amina na kuka tace ta yafe masa".

Gani kayan dake jikin zainab duk susha klin su koďe yasa zynah ta ďibi wasu daga cikin kayanta ya bawa zainab, ita kuma rakiya alkhairi zynah tayi mata sosai, amma besa rakiya tayi godiya ba, ita kuwa zynah da shike ba shine a gabanta ba, shi isa bai dameta ba, domin inda ta daka tata ma, da bata kalleta".

Kwanan su zynah bakwai suka shirya zuwa abuja, bakura ya dauki karamar wayar zynah ya bawa umma, yace duk abinda take bukata ta kirasa ta sanar dashi, su hauwa da Fatima harda kukansu, itama zynah kukan takeyi, kuďi masu yawa ya bawa umma da malam shehu, itama umma ta haďa masu tsaraba sosai.

Aroud 10:AM suka dauki hanya zuwa abuja".

Bayan tafiyarsu ne, malam shehu yaje har gidan da sadiya take, hakuri ya bata sosai, sannan yace tazo su koma gida".

Sadiya ta tubure tace babu inda zata, babu yadda malam shehu beyi da sadiya ba, amma taki yarda su koma, dola yasa ya hakura ya tafi".

Yana shiga gida kai tsaye ďakin rakiya ya nufa,yana sallama ko amsa masa batayi ba, banza dashi tayi, hakan yasa malam shehu yana shiga ya hauta da faďi, itama da shike a jirace dashi take, nan ta kama, yana faďi tana faďin, da shike yasan hslin rakiya sarai da iya tijara da rashin mutumci, gani yadda take daga murya, yasa ya fita a ďakin sabida kada makwabta suji".

Yana fita tace, banza da kadawo kaga aiki da cikawa"....








_*kuyi hakuri da wannan, yau da gobe ne, mesa a mari amarya🙀😻*_



_Ina gani kamar labarinmu yazo karke insha Allahu. Sannan kuma juma'a asabar lahadi, ba lalla ne nayi posting coz ranaku inada lecture kodama zaku samu gaskiya ba zaiyi yawa ba, ina fatan zaku fahimceni ngd_








*mmn uswan ce📚✍*

🍀🍀🍀🍀

           _*ZYNAH!!!*_

               🍀🍀🍀🍀

*WRITTEN ✍ BY MMN USWAN*
_______________

©©©©©©

_*follow me on*_        

_*wattpad:Hauwa s zaria*_

_*Facebook group*_
_*Mmn Uswan*_

https://www.facebook.com/groups/157572201857733/
                    
           ➿➿➿➿➿➿

_*BISLLAHI RAHAMANI RAHIM*_

_*In the name of Allah, The Beneficent, the Merciful*_

_*Fatan alkhairi gareku, bazan mance da kuba, ubangijin Allah ya amitarmin daku*_

_(Anty Rukky-mmn Abdul jalal) (Sis maryam L.I) (Rahma Muhmmed nalele) (Zainab bugaje) (Anty Haleema Auwal) (Anty Maimounath O.G) (Bilyn Abdull ce) (Zainab Shu'aibu) (my doter jamila janaf) (Aufana) (Umme Abieda) (mmn ahamed-Mardiya ko'ije) (chibado Muhmmed) (Real mai dambu ce) Rahma Abdullahi) (fasma niger) (Sis narja'atu) (Rahina m Abubakar er'garinmu) (Hafsat Ibrahim, anty sisi) (my name sake hawwa,Real smsher)kai dama wanda bansamu damar ambata ba, duk kuna raina, Alkhairi Allah ya gaida min ku, sann kuma ya biya mana bukatunmu na Alkhairi Ameen_

🅿4⃣0⃣-4⃣5⃣

   Malam shehu yana fita, zuwa yayi gun liman da wani kani baban sadiya, ranar wanka ba'a boyan cibi, ko kafin malam shehu ya isa garesa, labari duk ya karaďa gari, hakan yasa malam shehu be boye masu komai ba, ya zare gaskiyan zance ya faďi maki".

   Duk da su san bai kyauta ba, amma babu yadda za'ayi su goyawa sadiya baya ta kashe aure, sabida aure ba abin wasa ba, Allah da kansa ya halarta saki amma kuma bayaso yita, idan ba ya zama dole ba".

    Tare suka je gidan sadiya, shinfiďa ta kawo masu, bayan su zauna, suka gaisa, sannan suka faďi mata abinda ke tafe dasu".

   Shiruuuuuu, sadiya tayi tana sauraransu har suka kare, sannan tace dasu suyi hakuri, ita kam yanzu ta hakura da auren malam shehu, amma idan yanada ra'ayin kwashe yaransa ga sunan bata hanasa ba".

    Su liman suyi iya kokarinsu,amma taki, hakan yasa dole ya hakara, maganar yara kuma yace su zauna a gun ummansu zaifi masu kwanciyar hankali".

    Malam shehu bai so haka ba, dan dai kawai bashida yadda zaiyi da ita ne".

_*To malam shehu, dama haka rayuwa take, kuma dama shi mai hakuri bai iya fushi ba, idan aka kuresa Allah ya kyauta*_

          ~~~~    ~~~~~    ~~~~~

              _*JABI ABUJA*_

  
   Su zynah basu isa gida ba sai gab da magrib, kai tsaya gidansu suka nufa, bayan su shiga gida, zynah ta haďa masa ruwan wanka, kafin ya fito ta shiga kitchen indomie da kwai ta ďora masa, sabida shine kawai abicin da yafi saukin dahuwa, kafin ya fito har ya nuna, juyewa tayi a plate ta kawo masa bedroom ta ije a gefe".

   Zama tayi tana jiransa ya fito, sannan ta shiga tayi nata wankan da alwala, domin a lokacin pakhryya tana bacci, yana fitowa da sauri ta mike saida ta shinfida pakhryya ďan karamin table ďin dake tsakiyar ďaki ta bashi ya zauna, sannan ta dauko towel tana goge masa jiki".

   Murmushi kawai yayi me dauke da nuna jin daďin abinda takeyi masa, bayan ta gama goge masa ne, gani lokacin zafi ne yasa batayi tunani shafa masa mai ba, short nicker ďinsa ya daika yasa, sannan yace zynah ta dauko masa jallabiyarsa, yana sawa ya fara sallah" Lokacin ne ita kuma ta shiga toilet tayi nata wankan da alwala".

       Bakura yana idar da sallah daukar abincinsa yayi yaci gaba da ci, lokacin ita kuma zynah fito daga wankan sallah takeyi, duk suna gamawa tace zaka tafi kenan ko?"

   Bai amsa mata ba, wayarsa ya dauko ya lalubo number ta ya fara kira, lokacin adyra na zauna tana kallo wayar amma bata daga ba, bakura yayi kira har ya gaji amma taki dagawa, saima wani tsaki tayi ta juya wa wayar baya, bakura na gani haka, ya kashe wayar bai sake bi ta kanta ba, mikewa yayi ya cire jallabiyar dake jikinsa ya haye gado ya kwanta".

    Zynah taso ta masa magana,amma kuma sai ta fasa, bayan ta gamawa pakhryya wanka haďe da bata kunu, kwanciya tayi, duk da gajiyar da suka kwaso amma bai hana zynah faranta wa mijinta ba, domin sai da yaji ya kai geji ďan kansa sannan suka kwanta".

   Da safe kuwa bayan ya shirya, dai-dai lokacin zynah ta kare wa pakhryya shiri, daukarta yayi suka nufi gidan su hjy, da sallama ya shiga, Am'abuwa dake zaune da sauri ta mike tazo ta amshi pakhryya, amma a yau pakhryya kin zuwa tayi, babu yadda Am'abuwa batayi ba amma taki zuwa,dariya kawai Am'abuwa tayi sannan suka karisa cikin falon, Bakura yana zauna pakhryya ta kafa wa hjy ido tana kallonta,  dukawa bakura yayi har kasa ya gaida hjy, duk a lokacin pakhryya na kallon hjy, gani haka yasa Am'abuwa ta mike ta fisgi pakhryya da karfi daga hannu bakura, ba tare da hjy ta ankara ba ji kawai tayi an dora mata yarinya a jiki".

   Da sauri hjy tasa hannu zata cire pakhryya daga jikinta, take pakhryya tasa kuka, haďe da rikewa hjy wiyar riga da karfi tana kuka, duk da kukan da takeyi besa  hjy ta kyaleta ba, da karfi ta cire wa pakhryya hannu a wiyarta har zata hurgata kenan, ihuuuuuu pakhryya tasa, taci gaba da rike hjy, dole yasa hjy ta kyaleta a jikinta amma baďan taso ba".

   Hjy na kyaleta taci gaba da wasa, tana tsotse wa hjy yatsutsin hannunta".

  Daga bakura har Am'abuwa suna haďa ido murmushi sukayi, gani haka yasa bakura mikewa zuwa gidan Adyra, yana isa tun daga bakin kofa ya fara sallama, lokacin adyra na kitchen tana haďa jin sallama yasa ta leko gani bakura ne tsaki tayi sannan ta koma kitchen ďin".

       Bakura beyi fushi ba, binta yayi zuwa kitchen ďin, yana shiga ya rungumeta ta baya, yana faďin oyoyo my wife, kucu-kucu adyra keyi tana kokarin kwance jikinta, gani yariga yayi mata riko da bazata iya kwancewa ba, yasa ta ha'u zaginsa, ta uwa ta uba, haďe da cewa ya koma inda ya fito, mugu azalumi, ďan wuta kawai".

   Duk da yaji zafin zaginsa da tayi masa amma be nuna mata ba, dariya kawai yayi mata, haďe da cewa, dama haka rayuwa take idan wani na kinka da kwana, wani kuma da shekara yake sonka".

Oh!! dai adyra tace"
Juyawa yayi ya fita, batare da ya sake tanka mata ba".

  _To en'uwa na mata, shifa namiji mai mata biyu ba'a masa haka, domin a lokacin da kika bata masa er'uwanki zata faranta masa, amfani gida biyu kenan, magani gobara._

   Yana fita gidan zynah ya sake komawa, yana zuwa kwanciya yayi, yayi baccinsa" Bai tashi ba sai bayan 12:PM saida ya sake wanka yayi sallah yaci abinci sannan ya leka kasuwa.

   Pakhryya kuwa ba'a medata ba,sai bayan la'asar, shima bakura yana tashi daga kasuwa gidan zynah ya sake dawowa, tun daga sannan be sake komawa gidan adyra ba".

   Tun daga lokacin bakura be sake komawa gidan adyra ba, kuma be sake kiranta ba, gaba daya ya haďa ta ya bawa banza ijiyarta".

    Data gaji da zama gani bazata iya jure hakan ba, shiryawa tayi zuwa gidan hjy, da kuka ta isa gidan, gani ta shigo ba kuka ne, yasa hjy mikewa daga inda take zaune, a gigice ta tareta da lafiya meke faruwa?"

    Cikin kuka take magana, gani haka yasa hjy ta kamota ta zauna, saida ta numfasa sannan hjy ta sake tambyrta, nan take cewa, hjy rabon bakura da gidan ta sati daya kenan, kuma koda ta kirasa a waya baya dagawa".

    Nan take hjy ta dauki wayarta domin kiran haka, tayi kira yakai sau biyat amma ba'a daga ba, gani haka yasa hjy ta bawa adyra hakuri tace ta koma inda, in sha Allahu zatasan abin yi, har da daukar kuďi tayi mata masu yawa, dasu turare, sannan sukayi sallama".

   Adyra na fita hjy ta dauki mayafi zuwa gidan zynah, ashe koda take kiran bakura yana gida, yazo cin abincin rana, Allah ya taimakesa ta baya yabi, hjy na isa gidan kai tsaye ta shiga da sallama, jin saallamar hjy ne yasa zynah ta fito da sauri, har kasa ta duka tana gaida hjy".

     Hjy dake tsaye
bata amsa ba".

Ina bakura?".
Yana kasuwa, dama haka bakura yace ta faďi wa hjy koda ta tambayesa".

        Nan ta hau zagin zynah, inda take shiga ba man take fita ba, har da cewa karuwa mara asali,duk da maganar yayi wa zynah zafi amma sai ta matse bata nuna mata ba, sai faman bawa hjy hakuri takeyi".

   Duk da haka hjy bata daina aibanta tata ba, saida ta gaji ďan kanta sannan ta fita".

  Hjy na fita, da sauri bakura ya fito, hannu yasa ya dago zynah dake duke, juyota yayi har ya buďe baki zai fara magana"..........

Da sauri zynah tasa hannu ta rufe masa baki tana masa murmushi, duk yadda yaso yayi magana, amma zynah ta hanasa".

       Da yamma lokacin ya tashi daga kasuwa biyowa yayi gidan hjy, bayan su gaisa, hjy take tambayrsa dalilin da yasa baya kwana a gidan adyra, kuma gashi koda ta kiraka baka dagawa".

          Nan bakura ya kwashe komai ya sanar wa hjy,amma duk da haka hjy bata amince ba, faďa tayi masa sosai sannan tace daga nan ya wuce gidan adyra, kuma idan ya biya gidan zynah kafin yaje bata yafe masa ba".

    Himm kawai yace, yana fita kamar yadda hjy tace haka bakura yayi, saodai kiran zynah yayi ta waya ya sanar mata, bata nuna bacin ranta ba, babu komai kawai tace masa"

     Yana shiga dai-dai lokacin tana fitowa daga wanka, ko kallonsa batayi ba, saida ta shafa abinda zata shafa sannan ta dauki kayan baccnita tasa, Bakura dake tsaye murmushi kawai yayi, haďe da cewa ni wlhy Ni'eemat kina bani mamaki, ke kullum bazaki canza ba? taran mijin ma baki iya ba?"..

   Ko zaka koya min ne?"
  Me zai hana, idan na koya wa matata yadda ake tarban miji a tawa gani ai ba abin kunya nayi ba".

    Suna haďa ido, wani irin uwar harara ta harbesa dashi haďe da hayaewa gadon".

    Da sauri bakura ya bita kan gadon, haďe da kamota, yana faďi tashi ki kawowa mijinki abinci yaci".

Buďe bakin adyra tace, nima a bincine kazo ka cini"..

Da gaske?"
Kai fa kasani".
Kafin ta juya tuni bakura ya hayeta,adyra tayi kokarin turesa amma ta kasa, bakura be sauka na har saida yakai geji, sannan ya sauka yana yi mata dariya".

  Adyra kuwa, baki be mutu ba, kusan kwana tayi tana zaginsa, da safe ma haka, bakura bebi ta kanta ba, tashi yayi yaje ya shirya, yana gamawa yaje ya haďa tea, falo ya dawo ta zauna yana sha, adyra na fitowa suna haďe ido, cikin jin haushi tace oh!! An dai ji haushi".

Mudai ji haushi, domin na tabbata bani kadai naji haushin ba, au na mance bance maki yaya gajiyar jiya ba, ko za'a bani na kara ne?".

   Dariya ya kwashe mata dashi, jin haushin hakan yasa adyra inda take shiga banan take fita ba".

    Ashe duk abinda takeyi hjy na bakin kofa tana jinsu, jin zagin yayi yawa ne, ita kuma nazata iya jure jin hakan ba,da sauri ta juya ta koma da baya".

        Tunda hjy ta koma gidan irin maganganun da adyra ke faďi wa bakura ya dami hjy, yadda abin ya dameta ji tayi kamar ta kira hjy Ashe ta sanar da ita, sai dai kuma idan tayi haka tamkar da tona wa kanta asirine, dole yasa ta bar maganar a zuciyarta yaci gaba da cikinta, domin ko daddy taki faďi mawa,abinda sufi kusa da adyra akan daddy".

   Shi kuwa bakura, al'amarin adyra ya daina damusa, domin idan da sabo yariga daya saba"Shiyasa yanzu idan ya shigo gida in har be takareta suyi faďa ba, bayajin daďi".

      Cikin satin nan daddy zai dawo, sabida zasuje gida maiduguri, shida bakura, akan maganar auren su am'abywa da Yah-na, gakan yasa daddy yace wa bakura ya shirya yana isowa zasu tafi gida".

    Tunda adyra taji labarin tafiya gida, tun daga lokacin ta fara lallabarsa, sabida tanason zuwa gida".

      Da shike bakura ya gano, duk yadda tabi haka shima yake binta, da haka har daddy ya dawo, ranar tafiyarsu yayi, zynah ce kawai ya sallama amma banda adyra, har suka isa, gani yamma yayi be dawo gida wayarta ta dauko ta kirasa, bakura yana daga, saida suka gaisa, haďe da tambyarsa ya kasuwa, a lokacin ne yake sanar da ita yana maiduguri, take tasa ihu  haďe da hurgi da wayar""""..

               ~~~~    ~~~~~
 
                   *kunci*

Tun bayan komawar su zynah abuja zazzabin malam shehu ya tashi, da haka har ya kaisa ga kwanciya".

             Bayan kwana uku da kwanciyarsa cikin dare ciwo yayi zafi, malam shehu yayi murkusu-murkusu har rai yayi halinsa,shiruuuu da rakiya taji ne har karfe takwas na safe malam shehu bai fito ba, yasa taje dubashi, tun kafin ta karisa bakin fokar take kwaďa masa uwar kora, amma shiru, hakan ne yasa ta karasa ďakin da sauri".

      Tana shiga ganinsa tayi yayi wani irin kwanciya, take gabanta yayi mummunar faďuwa, da sauri tayi kansa, koda tabasa shiru tayi,take tasa wani irin ihuuuu tana faďin na shiga uku na lalace".

      ",Abinka da kauye, take gida ya cika da jama'a har da sadiya da yaranta duk suzo, ba'a dauki lokaci ba aka yiwa malam shehu wanka aka shiryasa kamar yadda addinin musulinci yace ayi, bayan an kaisa ne, sadiya ta kira Bakura ta sanar dashi rasuwar malam shehu, salati yayi ya sanar wa ubangiji, sannan yace insha Allahu suna nan zuwa".

   Bayan su gama waya da sadiya ne yaje ya sanar wa daddy, washe gari bayan en'gidan mazajen su Am'abuwa da Yah-na suka neman aurensu, kuma aka basu, haďe da sanya masu rana, washe gari suka baro maiduguri zuwa abuja".

    Bayan su iso ne, daddy yasa bakura yaje yazo da zynah, saida yayi mata nasiha sosai sannan ya sanar da ita rasuwar malam shehu".

      Itama salati tayi, sannan yayi addu'ar Allah ya jikansa, daddy yace ta shirya gobe sanmako zasuyi".

Bayan fitar su, hjy ke tambayar daddy, a cewarta bata fahimci maganar da sukeyi ba".

    Nan daddy ya sake faďi mata, daga nan yace ta shirya suje tare""..

        Da sauri tace, wahhhhh!!
Allah ya kiyaye, saidai wata ba niba, gani daddy ya matsa ne ta amince zata".

        Bayan su koma gida bakura yaje gidan adyra, tana zaune a bakin gado, bakura na sallama bata amsa masa ba, gani haka yasa be biye tata ba, shima zauna , nan yake sanar da ita rasuwar malam shehu baban zynah".

   Tamkar bada ita yake magana ba, yana gama faďi ya mike haďe da sallamarta, domin tafiyar asuba ce zasuyi".

   Tsaki kawai tayi masa, ba tare da tace komai ba, har bakura yakai bakin kofar fita falo, da sauri adyra ta mike da cewa yanzu sabida Allah kayimin adalci kenan? Kwananka nawa baka gari  kuma yau da dawowarka kace zaka sake wani tafiya? To nan dai gaskiya bazan yarda ba sai dai kasan abinyi".

    Murmushi bakura yayi sannan yace, to yanzu me kikeso ayi?"

   Sai dai ka fasa tafiyar".
       Shi kawai kike so?".
            Eh".

     To kinga yanzu kinsan abinda za'ayi?"
       Sai ka faďi".

Bari naje na dawo, domin yanzu daddy yana jirana akwai wani maganar da zamuyi dashi ne".

    Duk da zuciyarta yana faďi mata, ba gaskiya bakura ya faďi mata ba, amma tace to saika dawo".

     Da ido ta bisa dashi har ya fita daga gidan".

    Bakura na fita ya kwashe da dariya, haďe da cewa sha-sha-sha".

   Tunda bakura ya shita adyra ta zauna zaman jiransa, shiru-shiru be dawo ba, wayarta ta dauko ta fara kiransa, lokacin bakura na tare da zynah suna shirya kaya, duk uban kiran da Adyra keyi yana gani amma be ďaga ba".

    Gani tayi kira har ta gaji, be ďaga dole yasa ta hakura da kiran, sannan taje

Please Login or Register in order to submit comment