Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauran ranaku, yana zuwa shago suka sanar mata da zuwan hjy".

    Shiruuu kawai bakura yayi yana tunanin ta ina zai fara?"

       Bayan ya koma gida, yana shiga, kai tsaye falon su hjy ya nufa, lokacin suna zaune dukkansu falo, gani yadda hjy ta daure fuska yasa, yasa bakura zuwa kusa da ita ya zauna, bayan ya gaisheta fuska a daure tace, bayan shago ina kake zuwa?"

  Ina ko zanje hjy bayan, shigo? Yau ma da kikazo baki sameni ba, motatane nakai gyara, sabida kwana biyun nan naji birkin motar tana rawa, yau ma wlhy dan Allah ya kiyayene" sannan kuma lokacin da kika kirani ina masallaci ina sallah, sann wayata tana slent, yasa banji kiranki ba, amma dan Allah kiyi  hakuri insha Allahu hakan bazai sake faruwa ba".

          tsakani dah da uwa sai Allah, nan hjy ta ije fushin da takeyi".

    Daga nan bakura yaci daga da gashinsa, ciki kuwa yananan yana girma, yanzu haka cikin zynah wata hudu kenan".

            *~~~~~      ~~~~~~*
                     *KUNCI*

Me hali baya fasa halinsa,bayan rakiya ta zubar wa zainab da wacce cikin, sai gashi taje ta sake wani,

Wannan karon ma, haka sukaje inda aka basu magana suka zuwar da wacce, cikin dare rakiya ta dauki magani batawa zainab, a cewarta kafin safe, cikin ya fita, tunda zainab tasha magani jini yake zuba mata, har asubs, rakiya bataso kowa ya sani ba, amma gani zainab nayi kamar zata mutum, yasata kiran sadiya, tazo ta taimaka mata".

Gani irin jini dake zubowa daga jikin zainab yasa sadiya fahimtar abinda ake ciki, amma kama bakinta tayi tai shiru, tunda basu faďi mata ba, ita kuma tayi alkawarin bazata tambayesu ba".

   Hankalin malam shehu ya tashi matuka, sabida yadda yaga jini ke kwararowa daga jikin zainab".

Babu irin tambayar da baiwa rakiya ba, amma taki faďi masa, cewa kawai takeyi, yayi hakuri ya kwantar da hankali, bataso ya yanke hukunci cikin fushi, kuma koma menene ya bari har zainab ta samu lafiya sannan sai ta faďi masa".

Ana sanar asuba,  rakiya da sadiya suka dauki zainab zuwa asibiti, da'kar da taimakon Allah aka samu ragowar cikin ya fita, kwanata biyu, kuma duk sadiya ke kwana da ita, sannan aka sallamesu".

  Bayan kwana biyu lokacin girki ya dawo hannu rakiya, cikin dare, rakiya ta tashi zaune, tagumi tayi tayi shiruu kamar me tunanin, juyawar da malam shehu zaiyi yaji bata kusa dashi, da sauri ya mike ya zauna".

     Gani yadda tayi tagumi yasa malam shehu tambayar lafiya".

Kai kawai ta kaďe haďe da cewa babu komai, da kar malam shehu ya lallabeta, kukan mana ficci tasa mata, tana faďin, naji zan faďi maka amma dan Allah inaso kayi min alkawarin koda na faďi maka, bazaka dauki kowani mataki a kaiba, sabida tariga ta rokeni, dana rufa mata asiri, na yafe mata, kuma kada nabari koji wannan maganar".

    Kaga idan har kata da zance, ya nuna ban rufa mata asirin ba kenan, kamar yadda nayi mata alkawari".

    Nan malam shehu yace yaji kuma ya amince, ba zai tada maganar ba".

  Nan rakiya ta kwashe karya ta shrya wa malam, har kukanta winwinwin, akan zuban jini da tayi, sariya ce, ta zuba mata guba a cikin abinci, ina fitowa bayi yana tana zubawa, koda nayi mata magana sai tace nayi hakuri na yafe mata, sannan kuma na rufa mata asiri kada na bari kaji maganar".

Yadda take kuka sai taban tausayi, sabida yasa nace mata insha Allahu bazakaji maganar ba, to kuskuren da nayi, a lokacin ban dauki abincin na zubar ba,  sabida yadda naga tayi nadama, na dauka har cikin zuciyarta ne, ashe ba haku bane, kawai muna kwance cikin dare, naji yarinya na kukan ciki, kafin nawi wani yunkuri sai ga jini".

   Malam shehu dake zaune yace, anya kuwa, sadiya zata iya aikata hakan?.

Kodai gani kake kamar shirri nayi mata?"

  Ni bance haka ba, amma lamarinne abin dubawa ne".

Yan har kokwanton abinda sadiya zatayi kakeyi? Bayan kafi kowa sanin tun daga lokacin da Amina tabar gidan nan, sadiya ta janye jikinta bata shiga harkan kowa, to wlhy bari kaji, yadda Amina tabar gidan nan, sadiya bataki kowa ma yabar gidan ba, niba hatta kai da kanki, kuma bari kaji idan har bazaka dauki mataki akan hakan ba, ni zan dauka, domin inaji ina gani bazan zauna a kasheni ba".

      Gsni yadda ta birkice mada yasa malam shehu cewa yanzu me kikeso ayi?"

     Nidai banaso a karota a gidan, domi har ga Allah tausayi take bani, idan ka koreta a gidan da wanne zataji? Ga rashin miji ga kuma rashin yarinya, girki kawai zata daina yi, tunda ta nanne take niman halakamu, idan muyi sai takawo kwanu asa mata ita da yara, idan ma magani zatasa, wannan kuma kanta zatayi wa?".

       
     Koda girki ya zagayo kan sadiya, tana idar da sallar la'asar ta share gindin murhu ta gyara ko'ina".

  Tana cikin kwashe sharan kenan taga rakiya tazo tana haďa icce".

Da mamaki tace rakiya yaya haka kuma?"

    Ba tare data fasa abinda takeyi ba, kuma bata ďaga ba, tace jeki ki tambayi malam da kike zamansa, amma nida amsar tambayar a nan".

    Bakin kofa ta koma ta zauna tana kallo ikon Allah, bayan isha lokacin malam yanacin abinci rakiya dake zaune kusa dashi tana yi masa fifita, sadiya tazo ta duka a gefe, bayan ta gaishesa tace dan Allah malam magana nakeso muyi dakai".

    Faďi ina jinki".
Shiruuuuu tayi kamar bazata magana ba, amma kuma da taga baida niyyar tashi, dole yasa tayi maganar ".

    Yau nice da girki, kodai mantuwa kayi?"

   Ba mantuwa nayi ba, ina sane, nayi haka, kuma daga koda bakizo kin tambayi dalili ba, ni zanzo da kaina, daga yau  bazaki kara dora sanwa a gidan ba, rakiya ce zata rika yin abinci, idan tayi zata zuba maki keda yaranki".

    Ido kawai sadiya tabi malam dashi, har yakare magana".

  Har ta buďe maki zatayi magana, malam shehu ya dakatar da ita, da banason jin komai, idan kuma ba haka ba, nida kece a gidan nan".

Sadiya na kwallo ta mike zuwa ďaki, kuka sadiya tayi sosai, akan irin hukincin da malam shehu ya yanke a kanta batare da tasan dalili ba".

     Ita kuwa rakiya tun daga lokacin ta fito da sabon salo, wani lokaci koda malam bai kwanta da ita ba, idan har malam zai shiga ďakinta jansa da hira takeyi,wanda saiya dauki lokacin, bayan wasu awanni ko mintoci sai kaga ta fita da buta taje wanka, dan dai kawai ta cusa wa sadiya bakin ciki".

   Tun abin yana damu sadiya har tazo ta saba, sabida, duk da ba girki takeyi ba, amma malam shehu baya bari girkinta ya wuce ba tare daya bata hakkinta ba".

            *~~~~~~     ~~~~~~~*
                     _*JABI*_

Bayan wata biyu daddy ya dawo daga Germany, duk suna zaune a falo suna hira, cikin wasa da dariya, me dauka da jin dadin gani mahaifinsu, duk cikinsu babu wanda yayi tunanin sanar wa daddy abinda ake ciki".

  Da safe bayan bayan goma, duk suka shigo ďakinsa gaida sa, kamar yadda suka saba, bayan su gama gaisuwa, har su mike hjy ta dakatar da bakura, su sauran suka fita".

       Gwiwa bibiyu bakura ya duka a gaban iyayensa".

    Hjy ta meda dubanta ga alhj dake zaune  cikin girmamawa ta kira sunan sa, da alhj".

  Amsawa yayi da na'am, yana kallonta".

    Kallo da yake mata ne, yasa hjy dukan ta kanta kasa, shiru tayi ta rasa ta ina zata fara masa bayani".

   Gani tayi shiru yasa alhj cewa ita sauratanki".

   Nan ta fara kame-kame, haďe da wasa da yatsun hannunta, alhj yace kiyi magana mana Khursum".

    Sannan ta fara da, da farko dai kafi na fara magana, zan fara da baka hakuri, sabida nasan duk kokarin da nakeyi akan yaran nan ba gani kakeyi ba, haka ma bai faru ba, yaya aka kare balle kuma ga wannan abinda ya faru".

   Da sauri alhj ya dakatar da ita,da cewa dakata, nine nace maki bana gani kokarin da kikeyi akan yaran nan? Kome kike nufi, kinga Khursum idan zakiyi magana kawai kiyi idan kuma bakida abin faďi to dan Allah ki tashi ki bani gun, tun kafin raina ya baci".

   Matsalar mata kenan, kana nisa ana kawarka amma kuma kana dawowa sai an bata maka rai, sabida Allah daga dawowar jiya-jiya mutum ki bata masa rai".

  A lokacin ne ta fara magana, dama wata matsalace ta taso, wannan yaron nan, wlhy yaje ya""..

Daga nan kuma ta kuma yin shiru, ta kasa karisawa".

     Bakura dake duke, jin yayi hanji cikinsa yayi wani irin kara, gabansa yayi mummunar faďuwa".

     Alhj ya ďubi bakura dake duke yace, bakura lafiya, wani abune ka aikata da har ake juyayin faďi min?"

  Shiru bakura yayi, saima matsawa gefe da yayi".

  Nan dai hjy ta cire tsoron da takeji ta zaiyana wa alhj abinda bakura yayi".

  Shiruuuuu alhj yayi na ďan wasu mintoci, ido kawai ya zuba wa bakura".

   Bakura dake duke, wani irin kunya ce ta kama sa, domin ji yayi kamar kasa ya buďe ya shige, sabida kunya".

    Alhj yafi minti goma a haka sannan yace, yanzu sabida Allah abinda kayi ka kyauta mana kenan, haba-haba-haba bakura ina tarbiyanka da ilimi suke da har zakaje ka aikata irin wannan aika aika, amma kasan idan har mukayi fushi dakai bazaga dai-dai ba a rayuwar ka ko?"

Yanzu duk ďawainiyar da mukayi dakai tun kana ciki, irin sakayyar daya dace damu kenan ko? Inaso kasani duk girman da zakayi,bakafi karfin idan kayi laifi mu hukutaka ba ko?"

Yanzu abinda Allah wannan irin abin da aikata dame yayi kama? Ďan shege a gidana? Haba bakura, wlhy kwata-kwata banji dadi ba".

    Tunda daddy ya fara magana bakura baice komai ba, har saida  daddy ya kare magana sannan bakura ya fara bashi hakuri, haďe da niman gafararsu, sannan kuma ya amsa laifinsa".

    Bakura yasan babu abinda keta wa daddy da hankali irin yaga kukan yaransa, hakan yasa bakura yayi amfani da wannan damar ya shaho kan daddy, kuka sosai bakura keyi, yana kuka yana rike da kafar daddy ".

Gani haka yasa daddy sa hannu ya dagosa, saida daddy ya kara yi masa faďa sosai da kuma ja masa kunnin kada ya kara, domin wlhy idan yakara, koransa zaiyi a gidan".

     Bakura yace yaji kuma ya amince, sannan daddy yace yanzu ina yarinyar take?"

   Baďe bakin bakura yace hjy ce ta koreta daga gidan, yasa na medata inda aka daura mana aure"..

  Aure fa kace?".
Bakura yace eh".

Nan daddy yace ya faďi masa gaskiya, tsakaninsa da Allah, yadda aka fara tun farko, domin bayaso a shegonta masa daya daga cikin zuri'asa".

    Nan bakura ya kwashi komai ya faďi wa daddy, sannan yace idan ma yana gani kaman karya yayi yazo suje inda aka daura auren".

   Daddy yace, da kasan aure kakeso, meyasa baka sanar dani ba?"

    Shiru bakura yayi"

      Daddy yace, ya shirya da la'asar ya kaisa gidan kanďe ďin".

To kawai bakura yace, bayan bakura ya fita alhj ya faďa hjy Khursum da faďa domin yafi gani laifinta akan bakura, sabida me zata rika fita ta bar gida daga shi sai yarinyar aiki, bayan tasan idan mace da najimi suna tare na ukusu shine sheďan".

Batayi musu ba, itama ta amsa laifinta, tunda tasan hanayi haka".

Shima kansa bakura ďin haka ya farune, tun ranar da hjy dasu Yah-na sukaje gidan hjy Ashe, kuma tunda suka fita basu dawo ba sai dare".

   Bayan alhj ya numfasa, sannan ya take ce masa, tunda har bakura ya iya aikata masu haka, yanzu fushi da faďa ba nasu bane, tunda har ya iya shirya wa ransa abinda ransa keso, sabida haka bai isa ya hanasu abinda suma suke soba, dan haka yanzu wani aure zasuyi mata".

Tsawa alhj ya daka wa hjy, haďe da cewa kanki daya kuwa".

Gani haka yasa hjy kwatar da kanta cikin dabara ci galaban alhj ya amince".

Bakura yana kita ya kira kanďe, yace taje A P.C.quarters ta dauko zynah, sabida anjima zasuzo da dadynsa".

     Bayan sallar la'asar daddy ya shirya zuwa suleja, bakura ne ke driving, suna isa bakura ne yaje ya yayi sallama da kanďe,  tare suka fito dare da kanďe, tana rike da tabarma, bayan ta shinfida masa ya bayan ta zauna suka gaisa, a mutunce, sannan taje ta kawo masa ruwa da lemu".

      Su ďan jima, sannan alhj ya faďi mata abinda yake tafe dashi".

            Hankalin kande bai tashi ba, mikewa yaji taje ta kira malamai da yayi yagoran daura auren, nan yazo yayi masa bayani komai, daddy yaji daďin hakan, har da alkhauri saida yayi wa malami da ita kanta kanďen, sannan daddy yace amina ta fito suje gida".

    Bakura baki har kuuni, kanďe tayi masu rakiya har bakin mota, suna cikin tafiya ne daddy yake kara yiwa bakura faďi, da gatansa da komai amma yazo yayi irin wannan auren kamar wani mara gata".

  Hakuri kawai bakura ya bawa daddy, ita kuwa zynah, wasa takeyi da wayar ta, sabida bajin barbanci takeyi ba, su kuma bada hausa suke magana ba".

     Bayan su isa, daddy yace su Yah-na da Am'abuwa su kwashe kayansu su haďa a ďaki daya, bakura ya zauna a ďakin kafin a saman masa inda zai zauna".

     Gani yadda cikin yayi girma sosai yasa daddy cewa kata hjy ta bari tayi aiki, duk abinda takeso tayi magana".

   Gani alhj yana nan, duk abinda yace haka akeyi mata, Am'abuwa ce ta kaita asibiti, awon ciki".

   Kwanansu biyu a alhj ya kama masu haya, duk area daya suke, amma kowa da part ďin sa, su hjy suna sama, su kuma suna kasa".

    Ranar da suka tare, hjy ta kira bakura, a dakin daddy ya ssmeta, cikin girmamawa ya zube a gabansu, bayan su gaisa yace gani hjy, take sanar masa da maganar auren da sukeso yayi".

   Gani zaiyi musu masu, da sauri ta dakatar dashi, da cewa tunda yayi abinda yakeso a matsayinsa na ďan a garesu, dan haka a matsayinsu na iyaye a gareshi, bai isa ya hanasu abinda suke soba, kuma bai isa ya ya tsallake wani maganar auren ba, domin uwarni suke masu ba niman izini ba".

   Kuma wlhy idan har yaki bin umarnisu, babu su babu shi, kada ya sake kallonsu a matsayin iyayensa".

    Dole yasa bakura ya amince, sannan kuma cikin satinnan ya shirya zuwa maiduguri, to kawai bakura yace, haka ya aminke jiki a sanyaye ya fita".

     Kafin ya is a gida, kokari yayi ya ďan ne damuwarsa, sabida kada zynah ta gano, da sallama ya shiga, lokacin tana zaune a falo tana jiransa yazo su kwanta, zynah tajin sallamarsa, da kar ta mike taje ta rungumesa, dariya kawai yayi mata, haďe da cewa maman swist, duk da nawin da tayi amma haka ya dauketa zuwa bed, a hankali ya shinfidata kamar wani kwai, sauka yayi ya tube yaje yayi wanka sannan ya dawo, sabida lokacin zafi ne yasa ko mai bai shafa ba, towel kawai ya daura yazo ya haye gadon, hannu ta buďe masa alama yazo".

    Dariya bakura yayi yana faďin nazo ina? Ke baki gani yadda kika koma ba,kafin ya karisa magana tuni ta kawosa ya faďo mata, ihuuu tasa tana faďin wayyoooooo Allah na".

A gigice yace kingani ko, dama abinda nake gudu kenan, mikewa yayi yana kokarin ďagata, zynah na gaji haka hannu tasa ta fisgo masa towel ďin dake daure a kugunsa  tana dariya, ko kafin bakura ya kamota, tuni ta murgina ta sauka daga gadon" Duk da babu komai a jikinsa haka ya zago, kafin ya kariso, tuni ta  mike, taje gudu kuma taji kafarta ya rike mata".

Bakura yana zuwa ya riketa yana faďin wana kama? Dariya ne yaci karfinta ta kasa magana, hannu kawai take ďaga masa alama yayi hakuri".

     Bakura yace bazan hakura ba, daukarta yayi zuwa bed yana faďin saina rama, yaye rigan da zaiyi yaga ashema ciki babu komai,  marin wasa ya zuba masa yana faďin yau kakata ta yanke saķa, ba kukan zafi mutum zaiyi ba, koda na jinine bai isa ya hanani abinda zanyi ba".

       Nan tafara bashi hakuri, tana faďin na tuba wlhy Allah bazan kara ba".

    Ďagata yayi ya cire rigan gaba daya, sannan ya haye cinyoyinta, yana faďin aifa sai kiyi".

   Gani da gaske yakeyi yasa zynah magiya harda kwalla, gani haka yasa bakura cewa to naji, amma yanzu munamin inda bakiso a jikinki sai na rama a gun".

     Ihu tasa tana faďin ko'ina inaso, gani taki nuna masa yasa bakura sama,da sauri take cewa a'a, in ya dawo kasa, hannu take sawa ta rufe, tana dariya, duk inda ya taba bata yarda, gani haka yasa bakura tsikaranta saida ya tabbata tayi nisa sannan ya duka, baki ya kai nononta ya fara sha, daya kuma yana murza kan, tun zynah na ihu har tayi shiru, sabida bakura gani iya sarrafa mace ne".

    Duk da karancin shekarunsa, amma bai hanasa iya sarrafa mata ba, duk yadda zaiyi taji daďi ya iya".

    Sun kusan awa daya a haka ďan bai sauka ba, har saida ya samu natsuwa sannan ya sauka, taimaka mata yayi sukaje sukayi wanka, sannan sukazo suka kwata, yana rungume da zynah sukai bacc ".

              *......   ........*

    Bayan wata daya, su hjy da sauran yaran gida duk su wuce gida barno, sabida bakin bakura saura kwana biyar".

   Tare hjy taso suje dashi, amma yaki yarda, yace su tafi kawai, zaizo da kansa".

    Hankali bakura a tashe yake, domin ya rasa yadda zaiyi ya sanar wa zynah maganar aurensa, kuma gata da tsohon ciki, dan yanzu ma tausayinta yakeji".

     Can kuma wani tunani yazo masa,  duk da beso boye mata ba, ko kuma yayi mata karya,amma dole ne ya sashi".

  Yace mata sunada wani taro da sukeyi duk karshen shekara, sukeyin sa, kuma idan za'ayi duk wani ďangi na nisa dana kusa, dole saiya hanci wannan taro, yanzu haka su hjy dasu Yah-na duk su wuce shine kawai  beje ba,kuma shine ake jira" yau yakeso yaje, kuma kwana biyar ko shida zaiyi".

   Jin haka yasa zynah bata damu ba, saima fatan alkhairi da tayi masa, da sauri ya shirya ya nufi aripot, ďan ta girji ma zaije,sabida bata lokaci da yayi, ba kowa yake tsoro ba illa hjy".

     Tun ana saura kwana biyu suka fara wasa, duk wani prgrm da akeyi a biki saida sukayi sa, rana kuwa ba'a magana, domin inda ba kasa ake gardaman kokawa".

    Ďikuna kala-kala hjy tayi wa bakura na ban mamaki, turare kuwa, faďa bata lokaci ne, ďangin uwa da uba su nuna masa gatansa, abokan alhj ma suzo ba ďan kadan ba daga abuja, wani kuma daga Germany ".

    Hakan yasa komai cikin tsari akayisa"Shi kuwa bakura bini-bini saiya kira zynah yaji yaya take domin daga daya hankalinsa na gunta".

    Ranar asabar, karfen goma aka daura auren  *MUHAMMED ALIYU MILAY DA AMARYANSA NI'EEMAT MOODU*

bayan la'asar aka kwashi amarya da kawayenta zuwa aripot, dama ďangin amarya da kuma na ango, haďe da iyaye zuwa abuja"

Inda idan su iso kwai wani dinner da kawayen hjy Khursum suka shrya mata, wanda basu samu wani maidugurin ba.










*mmn uswan ce📚✍*

🍀🍀🍀🍀

           _*ZYNAH!!!*_

               🍀🍀🍀🍀

*WRITTEN ✍ BY MMN USWAN*
_______________

©©©©©©

_*follow me on*_        

_*wattpad:Hauwa s zaria*_

_*Facebook group*_
_*Mmn Uswan*_
    https://www.facebook.com/groups/157572201857733/
            
           ➿➿➿➿➿➿

_*BISLLAHI RAHAMANI RAHIM*_

_*In the name of Allah, The Beneficent, the Merciful*_

🅿2⃣0⃣-2⃣5⃣

  Tun kafin su iso, a gidan hjy Ashe aka dafa masu abinci, suna isowa driving's suka kawo masu abincin".

                   Bakura ango, suna isa, gun zynah ďinsa ya nufa, tana kwance akan cushion sallamarsa kawai taji kamar daga sama".

     Kafin ta yukura ta tashi, bakura ya isa gunta, dukawa yayi a gabanta yana mata dariya, haďe da shafe cikin, yana faďin babyna, kina lafiya?".

       Au babynka kaďai zaka tambaya, ban dani ko?"

     Ohh!!! Srry baby, tunda so kike na gaidami miko hannu kiga".

Taimaka mata yayi ta tashi tsaye, yana rungume da ita suka shiga cikin ďaki, yana faďi nina isa? my mata tana fushi dani, yau kaina zai kwana a wiyata".

    Suna shiga a bakin gado ya zaunar da ita, sannan ya duka a gabanta yana faďin yanzu zan gaisa da matata".

Yanayin yadda mata maganar ne yasa zynah yace kamar yaya?"

       Ido ya kashe mata, ba tare daya jira ta sake magana ba, hannu yasa ya kwamtar da ita, a lokacine zynah taji kamshin turaren jikinsa,  tana buďe baki zatayi magana, da sauri bakura ya tashe mata baki da nasa".

     Bayan suci suyi sallah, mai make-up tazo tayi wa amarya da kawayen amarya, sannan aka yiwa iyayen ango da kawayenta".

     Daga amare har su hjy da kawayenta duk su shirya bakura kawai ake jira, gashi su malah da sauran abokansa suyi ta kiran wayarsa bai daga ba"

   Da shike bakura ne kawai yasan bakura yana da mata, hakan yasa ya fara tunanin ko can yaje, ina zuwa kawai yace ma sauran abokan, ciki gida ya shigo gun hjy Khursum,  gefe suka koma a nan ne yake sanar da ita, tun daya suke kiran bakura amma bai daga ba".

    Nan hjy tai takirasa nan be daga ba, gani haka yasa hjy daukar mayafi, tace wa malah zo muje".

    Gida bakura suka nufa, suna isa kai tsaye suka shiga har ciki, da shike yabar kofar a buďe, a falo suna tsaya, malah ne ke sallama".

    Dai-dai lokacin bakura yana fitowa daga wanka, towel ne kawai daure a kugunsa, daya towel ďin kuma yana goge jiki dashi".

        Ji sallama a falo yasa shi fitowa ďan gani mai sallamar, yana fitowa da bakura ne sukayi ido biyu, gefe kuma ga hjy, suna haďe ido da hjy da sauri ya daure fuska kamar ba shib, itama wani irin kallo banza tayi masa haďe da qwafa, ba tare datace komai ba, ido kawai yasa ya fahimci abinda take nufi".

                 Da sauri ya koma ciki, dai-dai zynah na fitowa daga nata wanka, tambayarsa tayi da waye?"

  Hjy ce tazo"..
Da sauri zynah tace lafiya?"
Eh lafiya qlau, guna tazo, yanzu ma ni take jira, akwai inda zamu, amma komai dare zan dawo".

    Doguwar riga tasa haďe da hijab, da sauri yace ina zaki?"

           Zanje na gaida tane"
                 A'a, ki bari kawai".
  Duk bakura yana maganar ne yanasa kayansa, yana gamawa kamota tayi tayi mata kiss sannan ya fice".

  Ido kawai zynah ta bisa dashi, tana me girgiza kai".

Tun daga falo hjy ta fata zazzaga masa masifa, inda take fita ba nanne tashi shiga, shidai shiru kawai yayi, malah ne ke bata hakuri".

  Ko kafin su isa, har hjy Ashe su wuce da amarya, da kawayen amaryan".

       Kai tsaye ďakin su Yah-na hjy ta shiga dasu, wasu tsofaffine su uku zaune ďakin daga ganisu kakanninsa ne".

     Suna shiga hjy ta fita, sannan kanwar hjy Khursum ta shigo, ita tasa nakura ya duka gwiwa bibiyu, nan tsofaffin suka ďibi wani abu me kama da lalle, suka fara shafa masa, sunayi suna kawa, *yau ka fita cikin sahun samari, Allah yasa yadda mukazo biki kafin shekara muzo suna haka* amma duk da barbanci sukeyi, suna gamawa daya daga cikinsu ta rangaďa masa guďa akai, a lokacine zuciyar bakura ta karye, fashewa yayi da kuka, gani haka yasa sukaci gaba da yi masa tsiya".

     Saida sukai masa wanka da ruwan turare sannan kanwar hjy ta dauko masa riga da wando ta mika masa, toilet ya shiga yasa sannan ya fito, yana fitowa da kanta ta sanya masa malum-malumn wa gambari light blue, nan suka sake wani guďan, sannan aka bashi izini fito".

       Amarya kuwa har ta gaji da zaman jira, gashi ance kada

Please Login or Register in order to submit comment