Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Nagode)

____________________________________


Tunda ya isa k’ofar gidan surikansa ya yi parking kansa kawai ya d’ora akan sitiyarin mota yana jin yarda zuciyarsa ke bugawa da tsananin b’acin rai gami da tururin bak’in ciki. Me yasa Abbu zai yanke hukunci cikin fushi ba tare da shi ya ji ta bakinsa ba, ko a kotu ake kafin zartar da hukunci dole sai an ji ta bakin mutane guda biyu. Amma zai bawa Sakina mamaki zai nuna mata shi ma ya iya rashin mutunci kamar ko wane d’an zamani. Ya runtse idonsa gami da cije leb’ensa da k’arfin gaske tamkar zai huda shi, sai kuma ya saki yana furzar da tururin b’acin rai, da gaske sai ya rama yayi alk’awarin yin ramuwar gayya a lokacin da bata yi tsammani ba, sai ya tozartata gaban kowa sai ya kuma fito da ainahin b’oyayyiyan halinta kowa ya gani an kuma yi Allah wadarai da ita. Duka wad’annan zai yi su ne a lokacin da
Ta sakankance ta manta da batun
Shi kuma zai bayyanar mata a matsayin ramuwar gayya.

Wayar hannunsa ya shiga dialing
Bayan da yaji Abulkhairi na kiran Dad Dad mun zo ba. Cike da takaici ya d’an shafa kansa.

Nanna da take zaune kusa da Mamanta ta d’aga wayar “Ki fito ina waje.” Shine kawai abinda ya ce ya katse wayar, Nanna ta tab’e baki don tuni ta saba da halinsa in dai wannan ne. Mayafinta ta yafa ta fice da sauri don ta ji dalilinsa na zuwa shi da ya ce sai dare zai zo d’aukar ta.

Turus ta yi ganin yarda fuskarsa take a matuk’ar d’aure zata iya cewa tun bayan aurensu bata tab’a ganin fuskarsa a wannan yanayin ba. Ko lokacin da yake shiga wancan yanayin idan an b’ata masa rai bata tab’a ganin fuskar sa ta koma haka ba.
Ba tare da ya yi magana ba ya bud’ewa yaran k’ofa yana dubanta cikin yanayi na bada umarni ya ce “Ban amince ko da wasa ki je Gidan mu ba, kuma ku shirya nan da 1 week za mu koma inda muka fito.” Idanunsa cikin nata tana k’ok’arin samo kalmar da zata furta masa, tambayarsa take son yi amma kafin furucin ya fito ya ja motar da mugun speed. Nanna ta saki ajiyar zuciya had’e da furta Allah ya kyauta ya kuma saukeke lafiya. Amma wannan jaraba har ina ayi mutum sai kace mai shafar Aljanni.

Jikinta a sanyaye ta shiga gidan nasu, Ummanta na ganinta ta ce “Lafiya? Ko k’in zama suka yi ya rakito su nan?” Nanna ta girgiza kai “Ko d’aya, kawo su ma ya yi ya kuma ce ko da wasa kada na sake na koma gidansu, ban san dalili ba.” Umman ta girgiza kai had’e da
Lalubo wayarta ta shiga kiran Yayarta.
Sai da tayi ringing sosai kafin Sadiya ta d’aga zuciyarta na harbawa dafatan Allah yasa ba wannan labarin mara dad’in ji bane ya je kunnen K’anwarta da wani ido zata kalli y’an uwanta ta ce “Eeh, hakane Hammad ya yiwa matar ubansa fyad’e har ta haifa masa y’a da kunya ai, duk da tana tantama idan har hakan ya faru da gaske. Jin k’anwarta ta Dida na ta fad’in hello Yaya ba kya ji nane? Na ce me ke faruwa a can gidan ne Hammad ya kawo yara har kuma yana gargad’in Nanna da kada ta sake ta sake zuwa ko k’ofar nan gidan.” Sadiya ta saki ajiyar zuciya, murya a dashe ta ce “Wallahi d’an sab’ani aka samu Dida, ta bi umarninsa kada ta zo d’in har muga abinda hali yayi, yanzu haka muna asibiti da Didi bata uhm ba ta uhm-uhm har yanzu kuma likitocin ba su ce da mu komai ba.” Dida ta saki salati kafin ta ce “To Allah ya kyauta, ya yi mana maganin koma menene, ita kuma Didin wani asibiti ta ke sai mu zo ai yanzu.” Kamar ba zata gaya mata sunan asibitin ba sai kuma ta daure murya a cunkushe ta sanar mata, had’e da kashe wayar, tana sake lalaubar numberr Hammad amma still bai kunna wayar ba. Gabanta ne yake fad’uwa bata son Hammad d’in ya je ya aiwatar da wani abu cikin fushi, sai dai ta san bata da halin tafiya ta bar Didi da iyalinta a cikin wannan yanayin.



********

Babu b’ata lokaci Drivern Hajiya Dida ya sauke su a asibiti ita da Nanna da su Kamla da tun bayan faruwar lamarin jikinta ya saki duk da bata da wayon gane komai amma ta tabbatar abin da ya Farun ba mai kyau bane, musamman ganin yarda aka doki Daddynta, bata san me yayi ba abu d’aya ta rik’e da ta ji ana cewa Hamda y’ar Daddy ce. Sun duba Didin zuwa lokacin an kai ta d’akin hutu tun bayan da aka samu nasarar numfashinta ya daidaita, sai dai ba su samu fuskar da za su tambayi kowa komai ba, ganin yarda fuskokin nasu suka bayyana matuk’ar tashin hankali.

Sai da Sadiya ta rakosu sannan Nanna ba tayi k’auran baki ba ta ce “Mahmah ina Khairi ne, na ga kowa anan d’in ban ganta ba ko tana gida gurin Hamda” “Bata gida tana asibiti gurin Anty Hamda Dad ne ya kaimu aka yiwa Anty Hamdan allura.” Abulkhair ya fad’a. Nanna bata kawo komai a ranta ba ta ce “Allah sarki me ya sami Antyn ta ku?” “Fad’uwa tayi da ta ji Amma ta ce Daddy ne Babanta, wai Daddy ne ya haifeta...”
Wannan karan Kamala ce ta fad’a itama idanunta na zubar da hawaye ta cigaba da cewa “Shine Granny ya Zane Daddy ya doke shi...” Tsoro da firgici ne ya bayyana a fuskokinsu gaba d’aya. Sadiya ba bakin magana sai sunkuyar da kai da ta yi kawai idanunta na zubar da wasu hawaye masu zafi, duk da bata so fitar maganar ba Ta san dole wata rana zata fita, tunda ance zancen duniya ba ya b’uya. Sam basu lura Da Nanna ba sai da suka ga ta yi zaman y’an bori tana shirin rusa ihu Dida Ta zabga mata tsawa “Ki ka fara ihun nan sai ranki yayi masifar b’aci, asiri kike so ki tona mana, Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna, Yaya Sadiya abin da nake ji a bakunan yaran nan gaskiya ne?” Sadiya da kanta ke k’asa ta d’aga kai murya a dashe ta ce “Duk da ban ji ta bakinsa ba amma alamu da dama sun nuna haka d’in ne. Wallahi saboda tsananin b’acin rai ji nake dama na mutu na huta.” Dida ta jingina da motar ta bayan ta nad’e hannayenta a k’irji, ta rasa ma me zata ce sai can ta busar da iskar bakinta ta ce “Yaya ya kamata mu ga Hammad ta kowane hali ko da
Kuwa a gidana ne.” “A ina zan gan shi, kiran duniya na yiwa wayarsa ta k’i shiga, shi kuma ubansa ya kore shi daga gidan gaba d’aya ba tare da ya tsaya ya ji ta bakinsa ba.” Nanna ce ta mik’e fuskarta a had’e ta ce “Ni na yarda, na yarda jininsa ce sabida a kamanninta da Kamla ya isa ya tabbatar da hakan.” Ta fad’a wasu hawaye na gangaro mata. Sannan ta juya ta kalli Kamla ta ce “Ke ya sunan asibitin da kuka kai waccan shegiyar Antyn ta ku?” Kamla da ta diririce ganin yanayin Mommyn nata da sauri ta ce Standard” Mota kawai suka ga ta fad’a da sauri. Dida cikin masifa ta ce “Ke Nanna bana son hauka bud’e motar nan kafin ranki ya b’aci, hauka ki ke?” Ta san sarai mahaifiyarta kaifi d’aya ce kuma bata da wasa hakan yasa jikinta a sanyaye ta bud’e motar. Ta koma baya had’e da bawa driver da yake can gefe key d’in suka shiga motar gaba d’aya har Sadiya. Nanna sai sake b’ata rai take, tana sake danna kiransa amma bata shiga. Har Driver ya ja motar don isa asibitin Standard d’in.



____________

Daidai lokacin Hammad ya fito daga hotel d’in da ya kama d’aki, zuwa lokacin da zai bar garin, don baya son zuwa gidan ko wane aboki balle aji dad’in tambayarsa dalilin barinsa gida.
Sanye ya ke tsaf cikin shigar k’ananan kaya fuskarsa ta yi wasai ya samu nutsuwa sosai, tun bayan da zuciyarsa ta aminta da shawara d’aya da ya yanke. Sai baza k’amshin turarensa ya ke Hugo Boss, duk inda ya bi kuma idanun mutane a kansa saboda yarda yake taku, duk da da alamun b’acin rai a fuskarsa hakan bai b’oye Sirrintaccen kyan da yake da shi ba.

Ya bud’e motarsa k’irar Mercedes Benz bak’a wuluk ya shiga. Sai da ya tsaya a eatery d’in hotel d’in ya karb’a musu abinci mara nauyi da drinks sannan ya finciki motar da mugun speed, haka nan yake tuk’insa ko don ya saba da driving d’in Birmingham ne yana mantawa a Nigeria yake musamman Kano garin taron cunkoso.



________

Ko da ya shiga d’akin Khairi kawai ya tarar a zaune da wayar Hamdan a hannunta tana dannawa. Ita kuwa Hamda tana kwance a saman bed d’in idanunta a lumshe, daga yanayin yarda yaga hawaye
na zuba a idonsa ya tabbatarwa kansa ba barci take ba. Khairi ta masa sannu da zuwa kafin ta amshi ledar hannunsa don dama yunwa take ji.


A bakin Gadon ya tsaya yana k’are mata kallo kamar ranar ya fara ganinta, gaba d’aya ta sake zubewa ta rame lokaci guda. Ya saki siririn tsaki a fili kafin ya bubbuga gefen katifar gadon murya a tsaurare ya ce “Ta shi malama na san kina ji na.” Idanunta da suka jirkita launi daga farare tas zuwa jajaye ta bud’e da kyar ta saukesu a kansa, gabanta na fad’uwa da ta tuna shine wai a matsayin mahaifinta. Tana k’ok’arin bud’e baki tayi magana ya dakatar da ita don ya san ba abu mai dad’i zata furta ba. “Ki rik’e duk wasu tambayoyinki bana son jin su, don ba zaki samu amsa ko d’aya ba.” Ta had’iye wani abu a mak’ogoronta mai d’akin gaske tana mamakin halayyarsa tamkar mai gani har hanji. Ya sake kakkafe ta da ido “Ki mik’e ki ci abinci Malama, zan kai ki wajen passport suna jira na.” Babu alamun wasa a tattare da shi, ta tabbatar a yanayin da take bata isa ta ce masa ta k’oshi ba, don haka ta ja kwanon take away d’in ta d’au cokali kenan aka danno k’ofar aka shigo. Gaba d’aya suka d’aga kai don ganin su waye, Nanna ce a gaba sai Dida da Mahmah da suka shigo sun bar su Kamla a motar.

Wannan karan Nanna da gaske take don sam fuskarta ba annurin rahma ta saukesu akan Khairi, had’e da nuna mata k’ofa “Fita Malama, ban ga dalilin da zaki zauna jinyar shegiya ba..” Da sauri mahaifiyarta ta mata wani kallo ganin Hammad ya d’ago a fusace yana wurga mata wani irin kallo mai cike da gargad’i Dida ta ce “Ke Nanna saurara mana, bana son hauka uban wa ya ce miki shegiya ce?” “Idan ba shegiya ba me kike so a kirata Dida? Ni na tabbatar ko Hammad ne yayi cikin ta to uwarta ce ta ribaceshi, bisa son zuciyarta na son haihuwar d’a namiji, don haka Hammad a matsayina na uwarka ya zama dole ka sanar da ni yarda abin yake, kafin ka saka zuciyata ta buga ka yiwa sauran y’an uwanka a sara, don na lura kai baka d’aukeni da muhimmanci ban da haka ai da tun lokacin ka sanar da ni gaskiyar abinda yake k’udundune, yanzu ga shi ita ta wanke kanta kai ta saka ka a bala’i.

Gaba d’aya Hamda ji tayi kamar duka sassan jikinta ya daina aiki, kanta kuwa jinsa take kamar ya tsage biyu saboda masifar da take ciki, ina ma rabbi ya agajeta ya d’auke ranta ta huta.

A zafafe Nanna ta ce “Kin ga yayi shiru ba zai fad’a bane, sannan
Kuma yazo ya tare a gaban shegiyar y’arsa ya nunawa duniya da gaske shi yayi cikinta, to wallahi muddin yace zai dinga shiga huruminta sai dai ya sawwak’a min.”
“Saki nawa ki ke so?” Suka ji ya fad’a muryarsa a kaurare ba tare kuma da ya kalli kowa ba, kamar yarda suka tarar da shi idanunsa akan waya har a lokacin hakan yake. Tsoro da razani suka shigesu gaba d’aya, ba su sake firgita ba sai da suka ji ya ce “Ina sauraranki, saboda ina tabbatar muku mahaifiyata ce kawai ba zan iya rabuwa da ita akan wannan yarinyar ba, don haka ba shiga huruminta kad’ai ba daga nan
har Birmingham zan tafi da ita zata rayu da nine a k’ark’ashin inuwa d’aya har sai aurenta ya tashi, saboda duk duniya a yanzu ni ne gatanta don haka Idan kin ga ba zaki iya zama da ita ba you are free to go, kada azo ana nayi ba daidai ba..”

Tsawon lokaci d’akin ya d’auki bak’uncin shiru baka Jin komai sai saukar numfashinsu da sautin kukan Nanna da furucin Hammad yazo mata a bazata ta kuma rasa a ma’aunin da zata ajiyeshi tabbas idan ya kafe sai ya tafi da yarinyar nan Birmingham ya taro k’wallan masifa....


Jikar Nashe ce...
[1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: ALK’ALAMIN JIKAR NASHE


YA ABIN YAKE?

BONUS PAGE 17

08033748387


✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽




Ajiyar zuciya kawai Hamda take saki, jin zantukan Nanna da suka zo mata a bazata, sam bata tsammaci haka daga bakinta ba, Lura da cewa ta nuna wa yaranta k’auna, amma a yau ta wanke idonta tana furta muggan kalamai a kanta tamkar ma bata tab’a saninta ba, kawai don k’addara ta hau mata. Me yasa ba za su yi mata uzuriba? Dubi da cewa itama ba laifinta bane da bisa son ranta ne da bata amince ta zo duniya ta wannan k’azantacciyar hanyar ba. Ta sake rintse idonta gam jin cece kuce yana sake yawaita tsakanin Nanna da mai gidanta. “Wallahi Mahmah ki yi masa magana muddin ya ce sai ya tafi da ita to tabbas sai dai ya san yarda zai yi da ita ba zata zauna min a gida ba.”
Fuskarsa a tamke ya dubeta had’e da furucin “San da na siyi gidan ko aurenki ban yi ba, balle ki ce da kud’inki na siya, idan kin san tashin hankali za ki koma min da shi you better stay at your father’s house.” Zata sake magana cike da zafin rai Dida ta daka mata tsawa “Nanna bana son rashin hankali ki bari a yi komai a nutse. Duk wannan maganar ba ta da amfani.” Kuka ta sake fashewa da shi “To ku gaya masa kada ya tafi da yarinyar nan, wallahi zan iya aikata komai idan na ce komai ina nufin komai.” Cikin b’acin rai ya mik’e zai fice har ya kai k’ofa ya ji Mahmah ta daka masa tsawa. Tsak ya tsaya had’e da juyowa yana facing d’inta. “Me kake nufi da tafiya da ita? Ko kana nufin da gaske ka karb’eta a matsayin y’ar cikin ka, Hammad kada kace min da gaske yarinyar nan jininka ce?” Ya d’ago kai yana kallonta cikin tafasar zuciya sai dai lab’bansa sun gaza furta furucin komai illa idanunsa da suka jirkita launi zuwa ja. Ya sunkuyar da kansa kawai. Har zuwa san da Dida ya fuskanci tabbas ba zaida ce komai d’in ba, ta dafa kafad’ar Sadiya cikin taushin murya ta ce “Yaya mu bi komai a hankali, insha Allah komai zai bayyana kansa, a yanzu na fuskanci halin da Hammad yake ciki sam ba zai iya furta komai ba.” Sadiya ta bud’e baki zata yi magana Dida ta yi saurin girgiza mata kai, don ta lura idan har aka cigaba da kucincina maganar tsaf Hammad zai iya datse igiyar auren y’arta, ko ba haka ba ita Hamdan ce ma ta bata tausayi, ta lura ba a k’aramin rud’ani da firgici take ciki ba, kada a je ta rasa hankalinta ko zuciyarta ta buga haka kawai an saka ta a halin ban ji ba ban gani ba. Idan har Hammad ya matsa sai ya tafi da ita, ita zata rik’e ta madadin a had’a ta da Nanna a zo a haifi d’an da ba shi da ido. Don haka ta girgizawa Sadiya kai alamar kada ta ce komai, ta kuma k’arasa gaban gadon murya a tausashe ta dafa kan Hamda da ya d’au zafi rad’au ta ce “Ki yi hak’uri kin ji, komai zai daidaita ubangiji Allah ya ba ki dangana, duk abinda kika ga ya faru ga bawa muk’addari ne daga Allah kuma bawa ba zai iya goge k’addararsa da Ubangiji yada rubuta masa ba, ki yi ta addu’a a zuciyarki ubangiji Allah ya baki ikon amsa jarabawarki Allahumma la sahla illa ma ja’altuhu sahlan wa anta taj’alal Hazna iza shi’ita sahlan. Tana yaye duk wata damuwa da nauyi zuk’ata.” Daga haka ta yi mata sallama suka fice. Hamda ta bi bayanta da kallo, tana jinjina kyakykyawan hali irin nawannan mahaifiyar Nanna, tunda abin ya faru ita kad’ai ce ta fad’a mata abinda ya kwantar mata da hankali kad’an, ita ce matar da ta lallasheta da furuci mai warware fushin zuk’ata, wani abu kad’an daga cikin abinda yaaka tokare k’irjinta ya sauka, a hankali wasu siraran hawaye suka fara biyo k’uncinta. Ta shiga nanata waccan addu’ar da Dida ta gaya mata. Sai ga shi a hankali barci duk da ba za’a kira shi mai dad’i ba yazo ya d’auketa. Tana sakin ajiyar zuciya akai-akai. Hammad da yake zaune ya zuba mata ido, wani abu mai kama da tausayi yana tsirga masa cikin zuciyarsa, da gaske yana jin tausayinta, idan kuma ya tuna ta hanyar da aka sameta sai ya ji zai iya sadaukar da Duk wani farin cikinsa matuk’ar ita za ta yi farin ciki.

Kusan awoyi biyu yana zaune kamar maigadinta yana kallon yarda take sauke ajiyar zuciya cikin barci. Ba ya son ya tasheta duk da kuwa za suje wajen passport, ya fi so ta tashi da kanta. Sai da ta k’ara mintuna talatin akan awa biyun sannan ta farka. Idanunta cikin nasa da ya kafeta da su, da sauri ta d’auke na ta idanun tana tattare gashin kanta da ya kwanto a
Saman fuskarta. Da kyar ta mik’e zaune tana dafe pillow, tana mamakin yarda ta yi barci sosai haka. Fuskarsa a d’an d’aure ya mik’e yana gyara wristwatch da yake hannunsa “10 minutes na ba ki, ki yi alwala ki yi sallah za mu je wajen passport kuma kada ki yi taking time sauri nake.” Bai saurari amsarta ba ya fice da sauri. Sai da ta fi minti d’aya a zaune kafin ta mik’e cike da kasala ta shige toilet d’in d’akin. Ita dai da zai bi ta tata da ya kyaleta ta shiga duniya tunda zamanta tare da su a gareta ba shi da wani amfani, musamman da matarsa ta nuna mata k’iri-k’iri bata son zamanta tare da su. Sam ba taga laifinta ba, dama y’ay’a irinsu haka mutane ke gudunsu ba sa son sam su rab’e su, duk da kasancewar ba laifinsu ba ne.


Mintuna biyar ta k’ara akan lokacin da ya bata, tuni ya je wajen Doctor ya amshi sallama, bayan Doctorn ya tabbatar masa damuwa ce silar ciwon nata, da zarar an kwantar mata da hankali everything will be alright Insha Allah.

A rab’e ya ganta jikin bango, tana hangoshi ta fara wasa da bakin hijabin da yake jikinta. Sai da ya isa gabanta sannan ya duba agogo hannunsa ya sauke kallonsa a kanta. Yana d’an girgiza kai, ba kuma tare da yace komai ba ya juya ya cigaba da tafiya. Ita kuma jin bai ceyi tazo ba kawai sai ta ja ta tsaya. Har sai da ya yi taku goma sai yaga tamkar bata bin sa. Hakan yasa ya jiyo tsaki yaja kafin ya ce “Jira ki ke na zo na d’auke ki ne?” Ya yi furucin ba tare da ya juyo ya kalleta ba. Sai sannan ta bi shi tana mamakin yarda yake mata abubuwa tamkar ana tilasta shi, ya k’yaleta mana ya k’yaleta ta kama gabanta idan yana ganin kamar ta zame masa wani kaya ne. Bai san haushi yake bata ba, idan ta tuna yarda suka bi son zuciyarsu suka samar da ita tada gurb’atacciyar hanya ya zama dole ta samawa kanta mafita ba wani Birmingham da zata bi shi. Ya aura mata Zunnuraini kawai.... Da sauri zuciyarta ta buga ta tabbata da kyar idan zata auru idan har mutum ya san wacece ita? Dai-dai lakacin da ta ci karo da motar ba tare da ta sani ba, shi kuwa yana kallonta ya k’i mata magana yana son ya ga yarda zurfin tunanin nata yaje.
Tsaki ya ja, a zafafe ya ce “Ki je ki bugar da zuciyarki a banza garin banzan tunaninki.” Da kyar ta d’ago jajayen idonta tana so tayi masa tsiwa amma kwarjininsa yana hana ta. Musamman idan ya tsatstsareta da idanunsa masu kaifin gaske.” Sai kawai ta runtse idonta, hawaye na kwaranyo mata ta fad’a motar. Yana kallon yanayinta ta cikin motar har da murgud’a bakin da ta yi, murmushi kawai ya saki ya tabbatar da abinda take k’unsawa a zuciyarta.

Yana fara driving taji ya ce “Idan kin gama tsara yarda za ki gudu ki sanar min na baki kud’in mota.” Da wata irin razana ta d’ago tana dubansa ya aka yi ya San Sirrin zuciyarta? ya aka yi ya san abinda take shiryawa, kamar ta tambayeshi sai kuma ta yi shiru tana cigaba da wasa da hannunta
Tsawon lokaci suna tafiya kowa da abinda yake sak’awa a ransa, da gaske ba ta son bin sa Birmingham d’in nan amma sam ta rasa k’warin gwiwar da zata kalli fuskarsa ta ce ba za ta je ba.

Sun kusa isa gurin ya dubeta ta side d’aya kafin ya ce “Idan ba ki bini Birmingham ba, kina tunanin akwai inda za kije ki samu peace of mind, kina ji dai Mai gidan ya ce Baya buk’atar ganinmu mu bar masa gidansa.” Hawaye ta ji yana son zubo mata “Kada Ki fara min wannan kukan banzan, ki bani numberr saurayinki na yi magana da shi idan yaga ya shirya aurenki ya fito nan da kwana biyar na aura miki shi a wuce wajen, amma idan aka zo bincike wajen su Abbu asiri ya tonu fa?” Rintse idanunta ta yi ita ma tana jin wannan fargabar amma tana tunanin ai ba za su tona mata asiri ba, tunda idan sun tona kan su suka yiwa. “Ki ba ni numberrsa zan yi magana da shi.” Wani dad’i ta ji ya tsarga mata duk da gefe guda tana jin Shakka da kasantuwar hakan, tun da dai an ce zancen duniya ba ya b’uya. Bai sake mata magana ba har zuwa sanda suka isa Immigration office d’in. “Dama da zarar sun tambayi sunanki, kice musu Hamda Hammad na gaya miki.” Ta d’ago tana son tambayarsa ya tsatstsareta da idanunsa “Daga yau na canja miki suna, tunda ance ni ne Babanki, suma takardun makarantar gobe za mu je court ki yi changing name d’inki kin koma Hamza Hammad UU d’an borno.” Tsit ta yi saboda sam ba zata iya magana ba. Ya fice daga motar, kafin ya yi mata magana ita ma ta bi bayansa tana mamakin sunan da ya lak’k’aba mata.




*******************

Cikin ikon Allah likitocin suka samu nasarar farkar da Hajiya Didi, ta hanyar gark’ama mata oxygen aka dinga zuk’o numfashinta. Ta farka sai dai sam magana ta d’auke tsaf daga bakinta, ga ta dai idanunta biyu amma ba ta uhm bata uhm-umm sai hawaye da suke kwaranya a idonta sosai musamman idan ta so yin magana ta kasa. Da k’afarta da komai kuma hannayenta suna aiki, bakin ne dai ya d’auke, amma likitocin sun tabbatar musu a kowane lokaci bakinta zai iya dawowa.

Hankalin D’an Borno family kam a tashe ya ke matuk’a da gaske, musamman Abbu da lokaci d’aya duk ya fita hayyacinsa, shima a lokacin da za’a aunashi tabbas za’a tabbatar yana buk’atar a yi admitting d’insa a hospital.

Ita kuwa Ammi hankalinta a kwance yake ko banza dai ta san ta ture waccan matsalar, musamman ganin kowa hankalinsa ya kau daga kanta.

A kuma daren ranar ne Abbu ya turketa da tambayar me yasa sanda abin ya faru ba ta sanar da shi ba.” Cikin muryar kuka ta tabbatar masa da cewa tsananin kunyarsa ne ya sa ta kasa gaya masa kuma da wani ido ma zata iya dubansa ta gaya masa wannan abin kunyar. Kamar zai sake mata wata tambayar sai dai ya ja

Please Login or Register in order to submit comment