Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai da ta fito a guje duk da kiran da Ammin take zabga mata.


Tunda ya fito ya zubawa k’annensa ido yana mamakin yarda suka girma lokaci guda. Har zai shiga sashen mahaifiyarsa Hamood ya kama hannunsa had’e da fad’in “Big Bro rufa mana asiri idan ba so kake Didi tasa ayi yak’in duniya na biyu ba.”

Ya d’an bud’e ido yana kallon k’aninnasa, saboda sam ya manta a irin wannan lokacin Didin tana kasancewa ne a gidansu.

Ya juya direct ya nufa sashenta, yaransa da matarsa suna bin sa da sauri. Mahmah da take tsaye a window Ta saki Hamdala don farin cikin ganin yaronta, duk da kawaici da Alkunya ya hanata fita ta ganshi.



Didi da azama ta mik’e tana janye k’afarta da Hamda take shafawa Man zafi. Cikin fara’a kamar bakinta zai yage take fad’in Maraba lale, Oyoyo da mutanen Birmingham Masha Allah tubarakallah. Ta rungumeshi cikin tsananin farin ciki.

Hamda kuwa idanunta cikin na Kamla tana mamakin tsananin kamarsu. Su kansu su Khairi kallonta suke musamman Nanna da ta kasa janye idanunta daga kallon yarinyar mai kama da tata d’iyar Kwabo da Kwabo. Saboda duk zuwan da take Hamda lokacin tana makaranta shi yasa basu tab’a had’uwa da ita ba.


Hamda cikin ladabi ta durk’usa ta gaida Nanna, ita kuwa ta jata a jiki tana kallon Didi da Hammad da ya rintse idanunsa yana mamakin yarda yarinyar ta sake girma, da gaske kuma tsananin kamanninsu ya sake bayyana da Kamla musamman yanzu da suke zaune waje d’aya.


Cikin Masifa Didi ta dinga korar mutanen da suka yi dandazo a falonta. “Haba yau naji masifa, a bar mutum ma ya huta da jikokinsa ba za’a bari an zo an zuba musu ido kamar me? Ni jaraba ta yaran gidannan ta fara isata, mutane ga ido k’wala-k’wala, duk sun bi sun gado manyan idona na masifa.”
Ta dinga mita bayan sun tafi sun barta da jikokinnata sai kace su ba jikokinta bane, ko da yake su kansu sun san soyayyar da takewa Hammad daban ce, ko kuma don kasancewarsa shine Jikanta Babba a maza tunda Najwa da suke kira Yana ta girme masa.


Sai da suka tafin sannan ta zuba idonta akan Hamda ta saki baki tana kallon kamanninsu da Kamla.

Gaza shiru tayi har sai da ta magantu “Ikon Allah, ikon gaske kai kuma Hammadu sai ka haifo mai kama da Hamda kwabo da kwabo, ko wa suka yo a dangi don mu dai kaf danginmu ba masu kama da mutanen itofiya (Ethiopian).

Idanunsa ya zuba yana kallonsu, a duk sanda kuma ya kallesu sai gabansa ya buga fad’uwar gaba ta sameshi, baya son ana yawan ambaton kamanninsu haka ne yake sawa yaji k’irjinsa kamar ya tarwatse.


Nanna ta ce “Ai haka lamarin ubangiji yake, ba abin mamaki bane musamman kasancewarsu Jini d’aya, ai k’arfin jini ya zarce haka.” Hammad ya sake jin dukan da k’irjinsa yake ya tsananta musamman da ake ta nanata kalmar Jini d’aya. Anya kuwa wannan sirrin da suke k’ok’arin k’udindunewa nan gaba kad’an kuwa ba zai fallasu ba.

A sama ya jiyo muryar Didi tana tsaki “Ayi mace lusara, kina girma kina cin kashi abincin ma jira kike nace ki d’ebo ki kawo musu? Bayan tun safe muke tsaye akan digadiginmu muna aikinnan amma ba zaki tashi ki kwaso su ba.”

Ita dai Hamda bata bari ta k’arasa mitar ba, sai tsintar ta suka yi a k’ofar kitchen, Nanna Ta sake binta da kallo tana yaba kyau da tsarin halittar zubin jikin yarinyar, farin ciki ya cikata da ta tuna itama Kamlanta haka zata dawo mai kyau idan ta girma.

Shi kuwa Hammad tunaninsa daban yake ta yarda yake mamakin girmanta, duk da ba wata k’iba bace da ita amma duk wasu halittu na y’an matancinta a cike taf da albarkatun ubangiji. Yayi ta’awwizu da tunanin hakan da yayi don ya San sarai ba shi da hurumi anan.


K’ememe Didi ta hanasu tafiya wajen Mahmah da ta kasa zuwa ta gansu, anan suka zube akan daddumar Didi mai taushin gaske suka ci abincin mai dad’I don Didi gwana ce wajen girki shi yasa Hamda ita ma ta koya. Ta iya girkuna kala-kala.


Shigowa U U D’an Borno ya yi yana fara’a, da farin cikin ganin yaronsa da familynsa.

Da sauri Hammad da Nanna suka durk’usa don gaisheshi haka nan su Khairi da Abul khair ma suka gaisheshi.

Idanunsa akan Kamla yana dafe da kan Abul khair ya ce “Didi kin ga ikon Allah ko? Tunda naje barkar yarinyar nan na ce miki kamar su d’aya da Hamda, don har hotonta Na d’auko a waya Na had’a da Na Hamda wallahi ba banbanci ko kad’an banbancin d’aya ne wannan lotsawar da Hamda take da shi a k’asan hab’a ita Kamla a gefen Hanci take da shi. Tabbas kun haifawa Hamda y’a don nan gaba ko guduwa tayi da ita ba wanda Zai ce ba y’arta bace.”


Gani suka yi kawai Hammad ya rik’e kansa ya mik’e, had’e da cewa “Godiya nake Didi, bari naje na gaida iyalan Abbu” daga haka yasa kai ya fice da sauri bai saurari surutun Didi ba.

Su Nanna ma suka bi shi suna dariya.


B’angaren Ammi ya fara shiga direct, yana fatan ya iya danne b’acin ransa idan yayi arba da fuskarta da kai tsaye yake kira bak’ar Fuska. Addu’oi ya fara yi a zuciyarsa kafin ya saka kai cikin sashen nata.


A zaune ya sameta saman kujera, gaba d’aya yanayinta zaka kalla ka tabbatarwa kanka da gaske yau bata cikin nutsuwar zuciya, don dai ko kallabin kanta bata d’aura ba balle akai tajallin gyaran gashi.

Idanunta k’ozai-k’ozai babu kwalli. Guri d’aya ta zubawa ido, da alama tayi nisa cikin zuzzurfan tunanin da ya ke mata kaikawo a zuciya.



Bata ji sallamarsu ba sam, sai k’amshin turarensa da ya riga ya zauna rad’am a hancinta ba tun yau ba tun yana saurayi shine dai ainahin turaren da yake amfani da shi.

K’amshin ne ya farkar da ita cikin razani, idanunsa kuwa suka gauraya cikin nata.

Y’ar fara’ar da take fuskarsa ya d’inke tsaf, tare da amsa gaisuwar su Najma da suke gaisheshi cikin mutuntawa, kasancewar sun san shi mutum ne da baya wasa da su tun suna yara balle yanzu da ya mallaki hankalin kansa.


Shigowar Kamla ne yasa Ammi wani irin mik’ewa da sauri cikin razana tana dubanta. Ganin yarda idanu suka yi yawa a kanta sai kuma ta sunkuyar da kai ta waske tana jan hannun Abulkhairi.

Abin mamaki madadin shi da yake matsayin d’a wajenta ya gaisheta, itace take gaisheshi cikin basarwa da sunkuyar da kai tamkar dai surikinta.


Mintuna uku cikakku bai k’ara a d’akin ba, ya mik’e da sauri ya fice, yana jin zcuciyarsa kamar ana hura masa wuta. Suma su Nanna suka d’unguma suka bishi.

Hakanne ya bawa Ammi damar shigewa d’aki a sukwane tana sake lalubar numberr wayar babbar aminiyarta da tun safe take nema bata shiga. Wannan karan ma dai still wayar a rufe take kamar yarda ake ta sake jaddada mata a waya.




A kujerar parlourn Mahmah ya zube idanunsa a runtse kafin ya bud’e ya zube su cikin na mahaifiyrsa da take ta kallonsa cike da murmushi. Rabin hankalinta kuma yana kan Nanna da y’an jikokinta da sam babu shakuwa a tsakaninsu. Taja hannun Abul khairi tare da fad’in “Maigidan da ba awo ba cefane.”

Sai da ya sauke ajiyar zuciya kafin ya samu damar gaishe da Mahmahn cikin k’arfin hali da dauriyar zuciya. Mahmah ta amsa masa zuciyarta cike da farin cikin zuwansa Nigeria.


Sun dad’e suna hira duk da shi rabin hankalinsa ba akan hirar yake ba, sau tari sai Nanna ta sako shi a zancen sannan yake ankarewa da nisan tunanin da ya lula.


Ganin da ya yi ya rasa samun nutsuwa ya mik’e ya nufi sashensa, don ya sake nazari sosai akan lamarin da kansa tsaye zai iya cewa ALMARA.




_____________________________
Cikin sa’a k’arfe sha biyun dare ta samu numberr aminiyarta ta ta shiga ta saki wata nauyayyiyar ajiyar zuciya, duk wani abu da ya tokare mata na b’acin rai ya sauka daga k’irjinta. Gani take tamkar ta samu mafita ta gama.

Murya a cunkushe ta ce “Ke kuwa Kady ina kika shiga tun safe nake nemanki?”

Kady daga can taja ajiyar zuciya “Ke dai bari, ya aka yi? Akwai matsala ne?”

Tsaki Nanna taja ta ce “Idan kin ji matsala d’aya kenan matsaloli dai yaronnan Hammad fa ya dawo k’asar nan.”

“Innalillahi!” Daga can Kady ta zabga kafin ta ce “Yanzu meye abin yi?” Ammi taja tsaki “Ke zan tambaya kady, wallahi kaina ya k’ulle kin jefa ni a matsala da na sani tun farko ban karb’i shawararki ba, takaicina d’aya ranar fallasuwar sirrina, ranar da za’a tono b’aragurbin k’wan da na burne, ranar da jama’a da dama za su......” kuka ne ya kufce mata. Kady tayi tsaki “Yanzu na barki kiyi kukan kenan? Idan kin gama kukan sai na kiraki, tunda kuka ne zai mana maganin matsalarmu.”

Had’iye kukan tayi da kyar ta ce “To yanzu ya kike so ayi?”

“Ki bud’e kunne da kyau ki jini, idan zai yiwu a salwantar da ran Hammad kawai idan ba haka ba komai na iya faruwa.”


Ammi ta saki ajiyar zuciya a karo na biyu kafin Ta ce “Kina ganin haka ne mafita?” Tsaki kawai Kady ta ja tare da latse madannin wayar ta mutu ta san sarai Ammin yanzu zata waske zancen kisan, duk da ita dai bata hango wata mafita bayan wannanba.



___________

Sai da ya yi wanka sannan ya samu nutsuwa, duk da har a lokacin yana jin yanayin yarda k’irjinsa yake duka, Kansa yana matuk’ar sarawa, a zahirin gaskiya ji yake ya
Kamata ya sanar da mahaifiyarsa zancen nan, duk da muninsa ya kai muni amma bai kamata ya b’oye mata ba ba yanzu ake ji ba gaba ake ji, tunda ya tabbatar Hamda bata da gadon mahaifinsa, Bai kamata kuma ta cigaba da amsa sunan Mahaifin nasa alhali shi yasa ba ubanta bane.......

To fa! Wannan shine Ya Abin Yake?
[1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: Alk’alamin Jikar Nashe.

Ya Abin Yake?


08033748387


Follow me on Wattpad

@Nazeefah381

ArewaBooks

@Nazeefah
https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e

Da safiyar ranar ta shirya tsaf, da azama ta ja motarta sai gidan Kady don sam kasa barci tayi jiya tambayar duniya kuma Abbu yayi mata sai ta ce Bata jin dad’i ne, shi yasa yau tana cewa zata Asibiti bai yi nawar hanata ba, don yanayin da ta kwana shi kansa abin ya yi matuk’ar rikitashi, sai ya ce tun bayan haihuwar Hamda bai tab’a riskarta a yanayi kwatankwacin na jiya ba.

Daga jin yanayin horn d’in motar Kady Ta tabbatar mutuniyartace ita kanta sam bata cikin nutsuwa don haka yau da wuri ta sallami mai gidan, tana shirin kiranta a waya sai gata ta bayyana. Da sauri ta bud’e k’ofar hasashenta kuwa ya yi dai-dai don Sakina ce cikin wani irin yanayi ta shigo parlourn, wullar da jakarta kawai tayi ta ce “Kina ganin kashe Hammad shi zai rufe b’aragurbin sirrina?

“K’warai kuwa.” Kady ta masa mata cike da k’warin gwiwa “Rashin salwantar da rayuwar Hammad shi yake nuni da fallasuwar b’aragurbin k’wan da zai girgiza ahalin D’an Borno.”

Sakina tayi tsai da ranta, kafin ta saki gwauran ajiyar zuciya, ta ce “Bana son salwantar rai, zan saka dai a sake masa gargad’i had’e da tabbatar masa da k’udirina na k’arshe idan har ya sake ya bayyanawa mutane gaskiyar lamari.”

Kady tsaki ta ja, kafin ta ce “Ni ban ga dalilinki na rashin son kashe shi ba, mutumin da rayuwarsa kamar wata bala’i ce ga taki rayuwar, ke da kanki kince baya miki kallon mutunci balle ya girmamaki, kina tunanin idan ya cigaba da yi miki haka uwarsa ba zata so sanin dalili ba? Kina tunanin idan ya b’oyewa kowa zai iya b’oyewa mahaifiyarsa?”

Sakina ta share zufar da ta game goshinta. Hankalinta a tashe ta ce “Tabbas zancenki na kan hanya, saboda yarinyarsa Kamla yarda kika san kaki yarinyar nan Hamda tayi saboda tsananin kamarsu, ni kaina har mamakin bayyanuwar kamar nayi, wallahi abin ya bani tsoro kamar dai wata ishara ce Allah yake so ya nuna....”

“Shi nake so ki gane, ki cire duk wani shakku a kawar dashi daga doron k’asa, ina dalili? Tun ranar da abin ya afku na sanar da ke a kawar da shi kika wani ce a gargad’eshi, alhali kwalliya bata biya kud’in sabulu ba namijin dai da kike so baki haifeshi ba, kika tsaya cewa wai yaro ne zai ji tsoron tona hakan ga kowa, to ga dai yaro nan ya girma kuma yana shirin bankad’a duk wani sirri idan ba kiyi wasa ba, haba idan da nice ai da tuni an wuce wajen.”

Sakina ta ja ajiyar zuciya “Shikkenan, ki bari zan shigo yanke shawara anjima insha Allah.” Daga haka suka yi sallama, Sakina kam ta samu salama a zuciyarta ta kuma amince da shawarar Kady tana ganin hakan kawai shine mafita a gareta, da ahalin D’an Borno family gaba d’aya.


_____________________________

Tun asuba da ta farka bata koma ba gyara sashen Didi tayi kafin ta tafi sashen Amminta nan ma ta gyara. Wanka kawai tayi ta dawo parlourn Didin ta zauna had’e da d’aukar Alk’ur’ani tana karatu, Didi kuwa lazimi take, da radio a gefenta tana saurarar labaran BBC Hausa.
Sai da Takwas ta cika sannan ta shiga kitchen don d’ora abin karyawa kasancewar juma’a ce Didin bata azimin tsofaffi don idan watan azimin tsoffin ya shiga sau hud’u take yinsa duk sati litinin,talata,laraba da Alhamis.

Kunun tsamiya da ta saka wadataccen lemon tsami tayi musu, sannan ta soya musu k’osai da dankali da k’wai.

Kafin kace me? Har ta gama, ta kawo Daddumar Didin ta jeresu. Didin shi mata albarka kawai take tana fad’in Uwarki tayi farar haihuwa sai dai ita bata san haka ba shashasha, a zamanin nan samun yarinya mai hali irin naki ai sai an tona.” Murmushi kawai Hamda tayi. Dai-dai lokacin da aka yi knocking k’ofar sashen Didin.

Tsaki Didi tayi kafin ta ce “Jaraba, ko waye kuma da safiyar nan? Allah yasa dai lafiya.”
Hamda ta kalli agogon parlourn ta ce “Didi k’arfe 9:30, yanzu ai ba sassafe bane.” “Gurinki ne ba sassafe ba wajen mutanen gidan nan kam ai ba mamaki yanzu suka yi juyin farko.” Hamda dariya ta guntse kafin ta k’arasa bakin k’ofar. Cikin sanyin muryarta ta ce “Wanene?” “Bud’e” kawai ya ce cikin dakewar tasa muryar.

Gabanta ne ya fad’i sanin cewa shine tun jiya ta haddaci muryar tasa, da zarar taji take riskar kanta cikin wata irin razananniyar fad’uwar gaba.

Hannunta na rawa ta murd’a handle d’in k’ofar bayan ta murza mukullin da yake jikin k’ofar.

K’amshin turarensa ne ya fara dokar hancinta kafin ya shigo idanunsa a kanta, yarda ta mak’ale jikin bangon ya tabbatar masa da yanayinta na rashin sabo da jama’a. Kamar a tsorace take da mutane bata sakewa da su, kullum yanayinta na nuna kamar ace kyat ta zura da gudu.

Idanunta a k’asa cikin rawar murya ta ce “Ina kwana?”

D’auke idanunsa ya yi daga kanta kafin ya amsa da “Lafiya” ya shige ya barta a tsaye ta bi bayansa da kallo sanye yake da jallabiya mai gajeren hannu, wanda ta bayyana damtsen hannunsa da gashi ya kwanta luf a jikinsa.


A gefen Didi ya zauna yana gaisheta cike da Kamala, idanunsa akan coolers d’in da suke zube bisa daddumar, dama ji yake kamar an wawashe masa kayan cikin sa kaf, ko don daga training wanka kawai yayi ya taho nan wajen Didi, kamar yarda ya saba tun a da, in dai Didin tana nan da safe nan wajenta yake karyawa.

Cup kawai suka ga ya d’auka ya fara tsiyayyar kunun da yake cikin flask d’in sai zabga k’amshi yake na lemon tsami da kayan k’amshi. Da turirin da komai ya kai bakinsa, har hakan ya ba Hamda mamaki ganin yarda yake cin k’osan da zafinsa cikin hanzari ko ta kan Irish d’in bai bi ba. Haka dama shi yake cin abincinsa a hanzarce musamman idan yana jin yunwa, shi yasa yake da k’akk’arfan jiki kuma ginanne mai d’auke da murjajjiyar fata.

Tsaki Didi tayi tana harararsa “Ni fa Hammadu bana son iya shege, waye ya gayyato ka nan kake shirin cinye mana abinci? Shi yasa ga kanan a tsaye k’ik’am da kai.”

Fuskarsa ya d’aure sosai kafin ya ture kwanan k’osan cikin fad’in “Alhamdulillah” Didi ta saka salati bayan ganin ya wawashe k’osan tas guda biyar kacal ya bari.

Murmushi ya sauke a fuskarta ya ce “Kin san rabona da irin abincin nan kuwa?” “Ina zan sani tunda ni ba Allahn musuru bace, kawai ka zo ka wawashe k’osan nan yarinyar nan ko ci ba tayi ba, tun safe take aiki akan digadiginta, ina ruwana y’ar uwarka ka cuta don wannan biyar d’in dai ba bata zan ba wallahi.” Ta fad’a tana dangwalar yaji ta cinyeshi tas.

Hamda mik’ewa tayi ta shige d’aki don dama ita ba gwanar karya wa bace da wuri. Yabi bayanta da kallo cike da tausayinta sai ji Didi tayi ya saki ajiyar zuciya ya ce

“Har yanzu uwarta bata karb’eta a matsayin y’a ba tamkar sauran y’ay’anta?”

Tsaki Didi tayi ta ce “Yaushe zata karb’eta ai Umaru ya cuceku da ya auro muku jahila, wannan zuwan ma da nayi haka na zo na tarar da ita a galabaice ciwon sanyi ya kwantar da ita, saboda tsabar aikin azaba da take bata. Allah wadaran dai Halin Sakina mai farar fuska bak’ar zuciya.”

Shiru Hammad yayi duk da fuskarsa ta nuna zallar b’acin rai bai ce komai ba, ya had’iye abinsa had’e da mik’ewa, ganin Didin na hamma alamar barcin hantsi take buk’ata.

Ko da ya koma sashensa, tararwa yayi su Nanna har sun shirya, gidansu zata je kuma ta rok’eshi kwana biyu zata yi da yaran gaba d’aya.

Mahaifiyarta Yayar Sadiya ce (Mahmah) uwa d’aya amma uba kowa da nasa. Ita dangin nata mahaifin a gwarzo suke ita kuma na Mahaifiyar Nanna anan Kano suke.



__________________________

Yana kwance a parlourn da yake b’angarensa yaji ana buga k’ofar da k’arfi tamkar za’a cireta.

Rintse ido yayi sam baya son tashi daga kwanciyar da yake, amma ya lura koma waye a uzurce yake daga yanayin bugun na rashin nutsuwa.



“Waye?” Ya fad’a cikin cunkusashshiyar muryarsa daga can b’arin aka ce bud’e ka gani”

Ba zai manta muryar ta ba, muryar shaid’aniyar matar nan ce k’awar Sakina wato Kady, ba zai manta wancan lokacin ba, da tare suka aikata abinda har yau yak’i barin zuciyarsa ta huta , bisa son zuciyarsu suka kuma buk’aci tilas ya rufa musu asiri.

Fuskarsa ya tamke sosai kafin ya bud’e mata k’ofar, don a shirye yake wannan karan ko da mai suka zo ya shirya karb’arsa.


Kallon-kallo suka shiga wurgawa juna bayan ya bud’e k’ofar, Mamaki ne ya kama Kady ganin yarda Hammad d’in ya zama wani ingarman namiji, kamar ba yaronnan da shekarun baya suka.....

Tayi saurin katse tunaninta ta hanyar sake kallon fuskarsa, sai taji tana shakkar zancen da tazo masa dashi, da alama bata tsammaci ganin sa haka ba, cikakken namiji da yake tashe da k’arfi da lafiya, daga yanayin fuskarsa ta san wannan karan ba zai d’au rainin hankali ba.

Da baya da baya ya juya cikin parlourn, wannan damar suka samu suka rufa masa baya.

Tuni har ya zauna kan kujera yana murza goshinsa da d’an yatsa, hakan ce take kasancewa a duk sanda ya kai matuk’a a b’acin rai ko tashin hankali.

Tsawon lokaci parlourn ya samu bak’uncin shiru, su sun kasa magana saboda yarda yayi musu kwarjini a parlourn, shi kuma ya runtse idonsa saboda sam baya son yayi ido da ido da su, ji yake tamkar ya shak’esu ya kashe su ya huta.

Idanun nasa a runtse ya ce “Me ke tafe da ku? Ko kuma kun zo kuyi abinda kuka saba ne?”


Da sauri Ammi tace “Subhanallah, ko d’aya wallahi, wancan karanma kamar yarda na gaya maka wallahi sharrin shaid’an ne. Don Allah ka manta ka d’auka ma kamar ba a yi ba wallahi rud’in zuciya ne da son haihuwar d’a namiji ta kowane hali.”

Idanun nasa a runtse yake sakin wani murmushi da kai tsaye zaka kira shi na takaici murya a kaurare ya ce “In manta da abinda ya faru fa kika ce? To idan na manta ita kuma yarinyar a wani mizani kuka ajiyeta? Ya zaku yi ku fahimtar da mutane cewa bata da gadon Abbu, a lokacin da ya rasu? Ko kuwa kuna son nayi shiru Allah ya kamani da laifi?
Dole ne ko ba yau ba in sanar da duniya wannan bak’in labarin.” Har zuwa lokacin da ya kai aya, idanunsa still a lumshe suke amon muryarsa ne kawai yake tashi a parlourn cikin isa da ginshira. Ammi ta kalli Kady kafin tayi mata alamun kinga taurin kansa ko? Jin shiru basu ce komai ba, ya bud’e idanunsa ya sauke su akan Ammi. “Yanzu yarinyar nan kina so kai tsaye na b’oye gaskiyar lamari a dinga kiranta y’ar Abbu alhali ni da ke mun san ba haka bane. Wannan karan a shirye nazo zan fallasa sirrinki, in huta da abinda ya tokare min k’irji shekaru da shekaru ko da kuwa Abbu ba zai yafe min ba........

Da sauri Ammi ta katseshi ta hanyar durk’ushewa a gabansa gwiwa bibbiyu “Don Allah kada kayi min haka Hammad, kamar yarda kace yarinyar zaka duba, zaka shafa mata bak’in paint mai wuyar gogewa.” “Kina son kice min kina son yarinyar da tun farkon haihuwarta kika nuna mata tsana muraran, yarinyar da kika so hallakarwa banda da kwananta a gaba, yarinyar da kike gallazawa tamkar ba jininki ba? Yaushe kika fara Sonta? Yaushe kika daina cutar da ita? Yarinyar da tun tana jaririya kika so mutuwarta akan wanzuwarta a duniya, yarinyar da ba kya son farin cikinta, ko ba ke na kama da shinkafar b’era zaki bata a tea ta mutu ki huta ba, saboda nayi shirin fallasa sirrinki kika min asirin da na gwammace nayi rayuwa a birmingham fiye da k’asata Nigeria Am sorry to say wannan karan ba gudu ba ja da baya wajen bankad’uwar sirrinki ko da hakan yana nufin kaf zuri’ar D’an Borno zasu d’ora min laifin akan rashin sanar da su da wuri, na kuma shirya karb’arwa yarinyar nan y’ancinta ta kowane hali.”
Ya fad’a yana bud’e idanunsa da suka kad’a suka yi jajir, ya zuba su akan fuskar Sakina da take durk’ushe a gabansa, idanunta ta sauke k’asa ruwan hawaye na ambaliya a saman k’uncinta.

Kady ce ta ja wani wawan tsaki ta mik’e had’e da janyeta. “Mik’e yaje ya gayawa duk uban da zai gayawa, sai me? Idan kika tubure ubansa ne yayi cikin akwai yarda za’ayi dake ne? Idan ma ya fad’a dole shima Za’a tuhumeshi....” haka tayi ta masifa kafin su bar parlourn da sauri, kana ganinsu ka san a hassale suke. Allah yaso gidan ba kowa Mahmah tabi su Nanna gidan iyayenta, ita Didi sun tafi asibiti ita da Hamda. Don haka suka samu wannan damar suka shiga wajen nasa.

Ya dad’e yana cizar leb’ensa na
K’asa kafin ya furzar da wani hucin numfashi ya mik’e. Wanka ya shiga yana fitowa kuma yayi shirin zuwa gaida surikansa, Gidan su Nanna.




_______________

Kady a zafafe ta sake duban Sakina kafin ta ce “Wallahi kina so ko ba kya so sai an kawar da wancan banzan a doron k’asa, don na lura da shirin tozartaki yazo, kina ganin yarda yake cika yake batsewa idan ya san wata ai bai san wata ba shashashan banza, ba dai kince yarinyarsa da ita take kama ba?”


Sakina ta runtse hannayenta kawai kafin ta ce “Ban so zata kaimu ga jallin kisan kai ba, amma idan haka ne mafita ba yarda zamu yi, sai dai zamu aikata hakan ta hanyar da ba za’a saka mana zargi ba, wacce hanya kike ga zamu bi.”
“Kunce burkin motarsa da k’usoshin tayar motar ta hanyar had’a baki da ma’aikatan gidan nan ko mak’udan kud’i sai mu shak’a musu.........
[1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: Alk’alamin Jikar Nashe.

YA ABIN YAKE?

08033748387

Wattpad muna page 13


Follow me on Wattpad

@Nazeefah381



✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽
11


*******************************

Idanunta jajir ta sake zubesu a fuskar kady “Wallahi har ga Allah bana son kalmar kisan nan ba yarda zan yi ne tunda ya riga ya kafe ne, tun yana shekarun yarinta dama yaron nan kafiya ce da shi da d’an banzan taurin Kai.” Kady ta ja tsaki kafin itama cikin takaici ta ce “D’an banza kina kallon yarda ya rufe ido yana magana a gadarance alamar ko son magana da mu baya yi, ni fa da zaki bar ni da kaina

Please Login or Register in order to submit comment