Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zan aika da shi lahira amma tunda kina tsoron kisan bari mu bi ta yarda kike so, zan
Aiko masa da fataken dare su ja masa kunne na k’arshe idan ya k’i yarda kuwa wallahi zai gane kurensa.”

Sakina ta d’an ja fasali kafin ta ce “Shikkenan, Allah yasa mu samu nasarar hakan, matsaloli sun yi min rufdugu a kaina, ga matsalar yarinyar nan da matar can ta saka musu ido akan lallai sai sun fitarda
miji, ga matsalar nan da muke ciki.

Kady ta dafa kanta murya a
raunane cike da tausayinta ta
ce "Komai zai daidaita Insha Allah, su yaran ki bar lamarinsu a hannuna zan samo musu mazaje na kece raini, tunda kyawawa ne ba zasu yi wuyar shigaba, nayi mamaki ma da har yau ba wani k'usan Gwamnati da yazo ya kawo musu hari, sai kace wad'anda aka yiwa asirin bak'in jini."


Ajiyar zuciya Sakina taja kafin ta ce Allah ya shige mana gaba, zan saka su tura hotunansu sai ki watsasu a status k'ila ta wajenki a dace tunda kina huld'a da manyan k'asar nan, da kuwa ranar nayi rawa da tsalle idan senator ko minister suka taya." Kady murmushi ta saki kafin ta ce "Ai
ba abin mamaki bane, kyawun da
suke da shi kad'ai ya isa yaja hankalin maza kansu, ki saka dai suje ayi musu makeup na
kece raini, sai a kira FARISH yayi musu hoto, don naga ya iya fidda
hotuna masu kyau." Ammi cike da
murna ta ce "Haka ma za'ayi wallahi kin kawo idea"



__________________________________

Daga ita sai Didi a parlourn, Didin tana taje mata dank’ararren gashin kanta da bata son gyarawa sai dai ta wanke, mita take tayi mata “Ke sai kace ba mace ba a haka zaki samu mijin aure, naga ko y’ar powderr nan ta y’an mata ba shafawa kike Ba kullum idanuwa a kod’e kamar nama, ai gwara ki dinga gyara jikinki ko kya samu saurayi kiyi aurenki ki huta da masifar Uwarki. Gobe zan baki kud’i dama ki siyo kayan kwalliya har da gazal da jam baki, don ance ko kana da kyau ka k’ara da wanka, amma lamarin tsoro yake bani ace har yanzu ba wanda yazo yace yana sonki, ko kuma don ana ganin y’an uwanki masu kalar larabawa, kema ai ba mummuna bace kawai da duhun fata ne da ke na kuma tabbata da rashin gyara.”


Shiru Hamda tayi mata, zuciyarta ta lula can tunani, sai yanzu da Didin tayi mata maganar sannan ta ankarar da ita, da sam ta manta a irin shekarunta ya kamata ace tana da saurayi ko da kuwa ace na wasa ne, ko me yasa ita bata da saurayin a tsayin rayuwarta ba wanda ya tab’a cewa yana sonta, ba mamaki rashin kwalliyar ne kamar yarda Didi tace idan kuwa hakane ya zama wajibi ta fara kwalliya, don da gaske itama tana son tayi aure ta bar gidannan fatanta da burinta ma bai wuce ta auri d’an wani garin ma, ta yarda zata dad’e bata zo gida ba.

Dai-dai lokacin da Didin take kame mata k’ak’k’arfan gashin nata ya turo k’ofa ya shigo, idanunsa a kanta, da tayi saurin sunkuyar da kai. Ya d’an tab’e baki had’e da zama gefen Didin.

Ta kuwa washe masa baki ganin ya turo mata leda shak’e da kaya gabanta. Kaya ne fal na ciye-ciye a ciki sai kayan tea da k’unshin ledar gasassun kaji a ciki, ga yoghurt masu sanyi.

Fara’ar Didi ta yawaita cewa take “Yanzu na san Hammadu ya dawo k’asar nan, wallahi da a zuciyata har na fara tunanin ko ka zama zumbuli ne kakan marowata, har na fara tsinewa Ingila gaba d’ayanta don na tabbatar su suka koya maka rowa, kai da kake kyauta kamar baka so, Ina matar taka ta dawo kuwa?” Ya d’an girgiza kai yana sakin murmushi ganin yarda take cin naman kamar wacce a shekara sau d’aya take ci. Tsaki taja kafin tace “Zancen banza zancen wofi, to zaman me take a gidan nasu? Ta barka anan wa zai kula da kai, idan kazo nan kaci abinci, cikin dare kuma wa zai gyara maka shimfid’arka, fisabilillahi A’a nifa bana son shegantaka daga kwana biyu shine za’a tafi har hud’u, ina ce tuni aka yi sadakar bakwan uban nata, wanda ya mutu ba ya mutu ba fisabilillahi na meye kuma zata rashe waje ta zauna kai kuma ta barka da rungumar filo cikin dare da mafarkai barkatai”

Tsaf ya had’e fuskarsa ganin zata yi masa b’aranb’arama a gaban Hamda, itama Hamdan kunya ce ta d’an kamata don sarai ta san inda zancen Didin ya dosa, ta mik’e ta shige kitchen gwara ta tsiri wanke-wanke akan ta zauna jin hirar Didi marar kan gado.

Tana jiyoshi yana yiwa Didin sababi, da sanar da ita shi ya amince matar tasa taje a zafafe yace “Kuma ni nace miki idan bana tare da matata ina rungumar pillow da mafarkai cikin dare?da zaki bani kunya gurin k’aramar yarinya.”

Tsaki Didi tayi ta ce “Zancen banza Zancen wofi Hamdan ce yarinya? Allah na tuba itama tun yaushe na gama gane aure take so, ai Ina lura da mafarkan da take yi da matse filo a k’irji, don haka ma zan sanar da ubanku ayi mata aure.”

Hamda da take kitchen ji tayi kamar ta nutse cikin k’asa saboda bala’in kunya da gaske yau Didi ta shammace ta ko a ina ta tab’a kamata tana rungumar pillow? ita ina ruwanta ma da wata soyayya, don takaici har wata y’ar k’walla ce ta zubo mata, yanzu wani kallo Didi take so Yaya Hammad yayi mata?

Shi kuwa don takaici kasa ce mata komai yayi, a fusace ya mik’e ya fice daga d’akin yana mamakin tsofaffi yarda ba ruwansu suke sakar zantukan da suke so son ransu ba tare da sun tauna abinda zasu fad’a d’in ba. Ya tabbata Hamda tana can tana jin takaicin furucin Didin. Shi kad’ai kuma sai ya saki murmushi ya girgiza kai kawai ya fad’a sashen mahaifiyarsa.




_____________________________

Hamda kuwa cikin takaici ta amsa kiran Didin da take ta k’walla mata.


Ta fito daga kitchen d’in fuskarta a had’e tana cono baki, ji take kamar ta rufe Didin da duka.

Didin data lura da b’acin ran kan fuskarta taje Tsuka ta ce “Kamar kumbo kamar katanta, shima haka ya fita yana muzurai dad’in abin dai a dake ba zan daku ba, a zage ba zan zagu ba sai dai a zageni a zuciya, wannan kuma mutum shi ya jiyo, k’arya aka yi miki ba auren kike so ba ranar fa ina kallonki kina barci kina faman matse k’afa.”

Hamda ta d’ago ta watsa mata wani kallon takaici kafin ta ce “Wallahi Didi ba kyau, Allah fa yana kallonki, ki ji tsoron Allah yanzu me kike so Yaya Hammad ya d’aukeni?”


Dariya Didin tayi ta ce “D’an nema, yazo da k’warin gwiwarsa da alama yunwa yake ji, anzo cinye min abinci,daga maganar gaskiya kuma ya fice, ba don halinsa ba d’auki abincinsa ki kai masa ko don himulin siyayyar nan da yayi mana.”

Hamda ta waro ido kafin ta ce “Ni zan kai masa abincin? Cabd’i ai kam ba dani ba. Da wani idon Zan kalleshi bayan kin gama kwaye min zani a wajensa.”

Didi ta zabga mata harara “Ni kike so in tashi in kai masa kenan ko? Da yake ni marainiyar wayonki ce, idan da Uwarki ce ai da ba ki fad’a mata haka ba, sai ni da kika ga na sakar miki ko? To ko ki d’auka ki kai ko nayiwa Gadanga waya yazo shi ya kai masa. Hammadun bai fi min uban kowa ba, duk cikinku wa ke kula da ni yarda shi yake yi, to wallahi ko ubanki sai na kira na saka shi ya kai masa abicin nan, tunda ke ban isa dake ba.”


Jin haka da sauri Hamda ta sunkuci tray d’in ranta fal da takaicin Didin.

Tana fita kuwa Didin ta saka dariya ta ce “Ja’ira y’ar nema banda nayi mata haka, ba zata je ba.”


Dai-dai zata shiga k’ofar sashensa shima ya sawo kai, ya dawo daga b’angaren Mahmah. Da sauri taja gefe kanta a k’asa murya na rawa tace “Didi ce tace a kawo maka abinci.” Banza yayi mata yana bud’e k’ofar. Ganin bai kulata ba ya sanya kanta cikin parlourn, da ba abinda kake ji sai k’arar Ac da sautin karatun alk’ur’ani daga bakin Sudais cikin suratul wak’ia, sai kuma sanyayyen K’amshin turarukan wuta, da suka gauraya da nasa turaren.


A dininig ta ajiye, cikin sauri har ta murza handle d’in k’ofar “Hamda” ya kira sunanta cikin ginshira wanda direct zata iya cewa shine karo na farko da taji sunan nata akan harshensa a dai yanzu da ta manyanta.

Kamar ba zata jiyo ba sai kuma ta juyo a hankali ta k’arasa inda yake zaune, tsawon seconds yana danna waya bai ce mata komai ba har ta ji ta gaji da tsayuwar sai taji yace “Aure kike so kamar yarda Didi tace?” Da wani irin shock take kallonsa kafin ta russunar da k’wayar idonta, duk da Cewa idanunsa ba akanta yake ba Ta k’asan ido yake kallon duk halin da ta shiga, yana cigaba da danna wayarsa ya ce “Ina jin ki, ke nake saurare, kina da tsayayyen saurayin da ya shirya maganar aure ne?” Wannan karan ba jikinta kad’ai ba har k’afafunta rawa suke mata ta rasa me yasa yake mata kwarjini ta fi jin shakkarsa fiye da Abbu mutumin da ta kwana da sanin cewa shine mahaifinta. “Ba fa na son rashin hankali, na miki magana kin mini banza, nace kina da tsayayyen saurayin da zuciyarki ta amince zaki iya aurensa ko Babu.”

Maganar ce ba zata iya ba, ta tabbata idan ta bud’e baki tayi magana muryarta rawa zata yi bai zama lallai ma ya fahimci me ta ce ba. da dai ace zai kalleta ne to da sai ta girgiza masa Kai, amma magana yake yi hankalinsa baya kanta, kamar yarda take hasashe, sab’anin haka tar yake kallonta ta yanayin da bai zama lallai ta fahimci ita yake kallo ba.

“Kurma ce ke?” Wannan karon a zafafe yayi maganar da alamun b’acin rai cikin maganar tasa ji yake tamkar ya kai mata mangari. Idanu ya tsatstsareta da su. Hakan yasa ta shiga wasa da yatsun hannunta kafin cikin dakiya ta ce “Bani da saurayi, kuma ma ni ba’a tab’a cewa ana so na ba, sannan ni ba ni na gayawa Didi ina son aure ba.” A rarrabe tayi maganar kamar mai in’ina amma tsaf ya had’e kalaman nata ya fahimcesu don haka ya saki wata ajiyar zuciya kafin ya ce “Auren naki kuma shi zai sama miki kwanciyar hankali ba, ya fitar dake daga k’angin bautar ba gaira ba sabar da kike ciki ba, don haka ki saka a ranki kin kusa aure, na baki sati guda jal ki fidda gwaninki kafin Na bar k’asar nan zan miki aure Na gaji da ganinki a wannan bak’ar rayuwar, da ba abinda zai samar miki y’anci sai aure. Kije kiyi k’ok’arin kawo min miji nan da sati guda, 3 months kawai zan yi a garinnan hakan yana nuni da cewa ana sallah cewa zan tafi, kafin nan insha Allah zan aurar dake.”

Wani irin bugun k’irji ne ya Sameta, kafin ta runtse ido cikin wani yanayi da kai tsaye ba zata bashi suna ba, abu d’aya Ta sani kamar yarda ya ce Aure ne mafitar ta,
Abin tambayar wa zata kawo nan da sati guda kacal? Ita da ba’a tab’a cewa ana sonta ba.

“B’ace min da gani”
Taji muryarsa daga sama, hakan yayi saurin dawo da ita cikin hankalinta, duk da ba kallonta yake ba ta tabbata da ita yake, don haka da sauri ta juya har ta na yi kamar zata kifa.



_____________________________

Ko da tazo barci, kasa barcin tayi tana kallon Didi da take sallolin Nafilfilunta hakan yasa itama ta mik’e a fili ta furta Barci ba nawa bane gwara na kaiwa Rabbi Kuka ne yayi min maganin damuwata sannan ya kawo min Mijin Aure Kwana kusa.



⭐️Sanye take da Hijabin Islamiyyarsu da yazo mata har k’asa, fuskarta d’auke da nik’af sai dai ta d’age shi sama.

Yau kam har da y’ar powderrta da jambakinta light pink ta goga. Dai-dai bakin gate zata shiga taji ance “Y’an mata salamu Alaikum.” Da sauri ta juyo tana amsa sallamar duk da ta d’an firgita a karon farko sai dai bata bayyana hakan ba.Matashin da zai kai shekaru Arba’in ko kusa da haka ya jefeta da wani murmushi da yasa ta saurin d’auke ido daga kansa “Kiyi hak’uri na tsayar dake a hanya, sunana Zunnurain idan ba damuwa numberr wayarki zaki bani, nafi awa biyu anan ina jiranki tunda zaki shiga islamiyyarku Na ganki,kwarjininki ne ya hanani yi miki magana....” Hamda da kyar ta d’ago kanta tana masa kallo na biyu, kafin ta daure ta nuna masa wajen zama da yake gefe kad’an a kuma daidai lokacin Motar Hammad ta danno Kai, har ya yi parking ya fito idanunsa ya na kansu, kana ganinsa kaga matashin Dattijo da ya kusa cika shekaru Arba’in cif, wannan karan sanye yake cikin farar shadda fara tas sai zabga k’yalli take, kansa sanye da zanna bukar da tayi masa kyau sosai cikin takunsa na isa da ginshira ya isa wajen da suke zaune, cikin wata k’aramar bukka.
Tunda ya nufosu gaban Hamda ya ke dukan Tara-tara, da sauri ta sunkuyar da kanta, tana gani ya mik’awa mutumin hannu da a shekaru zasu iya kai d’aya. Suna gama gaisawa ya shige gida sai sannan Hamda ta samu salama ta d’ago idanunta cikin na Usman tana murmushi shima murmushin ya sakar mata, a hankali ya furta “Yayanmu ko?” Ta d’aga kai tana wasa da zoben hannunta. Shikkenan tashi ki shiga gida, sai na dawo insha Allah don naga ba ki sake da ni ba sosai, kuma ma ya kamata na fara neman iso kafin na zo wajenki..."
[1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: Follow me on ArewaBooks


https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e


Follow me on Wattpad
@Nazeefah381

12

✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽

Tunda ya fara maganar tayi k’asa da kanta sai da taji yayi maganar neman iso wajen Iyayenta sannan ta d’ago tana masa wani irin duba
A tsorace take kallonsa, kasantuwar ba’a tab’a tareta da magana kwatankwacin wannan ba.
Taji zuciyarta na wani irin bugu kamar yarda dai hakan take faruwa ga tarin y’an mata, a karo na farko da saurayi ya taresu da kalmar Na gani Ina so.

“Kin amince min?” Ta jiyo maganarsa daga sama tamkar dirar mikiya. Da sauri ta d’aga kai, don bata da zab’in da ya zarta hakan, Wa take da shi bayan shi? Da zata ce bata amince masa ba?

Ta tabbata Allah ne ya kawo mata mafita a lokacin da ta kai kukanta garesa cikin sakankancewa da cewa Jallan ya amsa mata. Sai ga shi a cikin lokacin da bai gaza kwana biyu ba kacal Allah ya aiko mata da Zunnurain ya aureta, ashe dai ba zata bawa Yaya Hammad kunya ba, kamar yarda yace ya bata kwana bakwai, zata je masa da labari mai dad’i Samun Miji a gab’ar data dace.

“Kisa min digit d’inki” Ta sake jiyo maganarsa wannan karan ma a bazata. Da sauri ta kalli wayar hannunsa tana girgiza kai tare da cewa “Bani da waya.” Ya kuwa dad’e da ido a bud’e bisa ga dukkan alamu tarin mamakinta ne yake nema ya karshi, a zamanin nan da waya ta zama ruwan dare ace zabgegegiyar budurwa kamarta da ta fito daga zabgegen gida bata da waya? Abin a jinjinawa lamarinta ne don kuwa yayi girman da ya kamata ya girgiza zuk’ata.

“Wasa kike amma?” Ya sake jefo mata tambayar, ta girgiza kai tana turo baki kafin tace “Da gaske bani da ita, bata yarda za’a yi had’uwar farko na jaka da wasa alhali ba ban san ko kai waye ba.”
Ya jinjina kai had’e da sakin murmushi, “Shikkenan, na yarda dama kamila kamarki bai kamata aji zance akasin gaskiya a bakinta ba, zan dawo jibi da misalin takwas na dare, insha Allah zan taho miki da waya.”

Tamkar tace masa Ya barshi, sai dai ita kanta tana buk’atar rik’e wayar, kamar yarda taga k’awayenta na rik’ewa, Abbu ya tab’a siyo mata amma Ammi na kyalla ido ta k’wace ta, taji ciwon hakan a ranta, sai dai bata damu sosai ba, saboda ta san hakan ce take faruwa a duk sa’ilin da Ammin taga abu mai mahimmanci da zai sata nishad’i a rayuwa, sai ta san hanyar da tayi ta k’wace.

“Ki shiga gida beauty, naga a gajiye kike sai Allah ya dawo dani.”


Murmushi ta d’an sakar masa kafin ta tura wangamemen gate d’in gidan nasu, ta d’aga masa hannu kamar yarda shima yayi waving d’inta.


Da shigarta Kamla da suke wasa a harabar gidan ta taho ta d’aneta da gudu, haka kawai jininsu yazo d’aya da yarinyar, kai gaba d’aya d’iyoyin Hammad ma suna sonta tamkar yarda take sonsu cikin tata zuciyar.
Peck ta bata a kumatu, a kunne kuma ta rad’a mata “My Kamlulu, dirar yaushe? Yaushe kuka dawo daga gidan Granny?” Kamla ta d’an cono baki had’e da cewa “Ni nafi son nan gidan, can ba dad’i shine Mom tace a dawo damu ita sai jibi zata dawo.” Hamda taja hancinta had’e da cewa to Parrot wa ya tambayeki, ina Khairi? Da Abul khair? Tayi mata pointing b’angaren Didi da hannu, “Suna can suna cin wani abu wai zogale, nifa na kasa ci amma Sis Khairi tana taci wai dad’i ita da Dad nifa idan naci am sure I will vomit it.” Ta fad’a tana kakarin amai “Please Anty Hamda will you cook noodles for me?” Hamda ta gyad’a mata kai, dai-dai lokacin da take tura k’ofar parlourn Didi.


A baje ta gansu duka akan carpet sun yi Baja-baja da tarkacen b’awon gyad’a ga kwanon da suka ci zogale, shi kuma yana saman three seater yana danna waya.

Sallamar da tayi cikin sanyin murya yasa shi d’ago kai, idanunsa akansu ita da Kamla, sai ya sake ganin zahirin kamanninsa ashe da ba abinda ya gani.

Bayan ta gaida Didi ta gaisheshi, suma su Khairi suka gaisheta, ta amsa musu cike da kulawa, ta fara harhad’a plates d’in wajen, Khairi ta sa hannu tana tayata. Didi sai mita take “Baiwar Allah daga zuwanki zaki fara gyara waje, ai wallahi wanda ya aureki ya more mace, ba dai tsafta ba abinci kuwa idan aka ci naki kamar kunne zai tsinke, to ba dole na soki a
Cikin jikokina ba, mai kula da kai ai
Shine abin martabawa, ba wanda ya mayar da kai d’an iska ba, yanzu tunda nayiwa Hammad magana akan matarsa da taje ta rashe gindi ta zauna gidan iyayenta yake zaune nan yake ta cin magani ina ji ma har zagina yayi a zuciyarsa..”

Hamda ta ware ido tana kallonta kafin a hankali ta ce “Yaushe kika shiga zuciyar tasa kika gani? Ba fa kyau shaidar zur Didi?”

Sarai yaji abinda ta ce kafin Didin cikin kwararato ta fara masifa “Ubanki Damanga shine mak’aryacin, ban ga zuciyar tasa bane zance yace? Haka kawai mace don taga y’ar uwace ita sai ta zauna tayi ta abinda taga dama, ita kuma Sadiya da yake shashashace ko kuma kwad’ayin abin duniya oho mata? Taga uwarta tana auren maikud’i dad’in abin mun san komai ai ba shi ya haifi Nannan ba, nata uban da ya mutu matalauci ne sai bayan mutuwarsa sannan ta auri wannan Alhajin, Allah na tuba mu za’a yiwa k’aryar arziki, kai Sadiya ba dai son abin duniya ba.”

Wani kallo Hammad ya wurga mata kafin yayi k’wafa ya mik’e, murya a cunkushe ya ce “Kada ki sake jefa min mahaifiya cikin maganganunki balle ki jingina mata sunan banza.”

Salati Didi tasa cikin k’ank’ance ido tace “Kiji min Annamimanci, yaushe na zagi Sadiya, Sadiyar ba don ni ba ai ubanka ba zai zauna da ita ba, balle har a d’au cikinka
A haifeka kazo kana min rashin kunya, kaje ka tambayi Sadiyar idan bani na dinga banka mata magungunan mata ba, har ya mak’ale mata ya d’ura mata cikinka, ke bana baki labari ba?”

Hamda rintse idonta tayi, da sauri ta shige kitchen a zuciyarta ta ce “Kai lamarin Didi sai a addu’a kuma.”
Cikin cunkushewar bak’in ciki Hammad ya zabga tsaki yasa kai zai fice sai ji yayi Didin ta ce “K’aton banza kawai dama kada na sake ganin k’afafunka anan balle kazo ka cinye mana abinci kamar da ubanka aka siya min, dad’in abin wannan karan ba Ummaru bane ya siya min, Ali k’usar yak’i ne ya siya min, balle kayi fankama kace abincin ubanka nake ci.”

Shi dai Hammad girgiza kai yayi ya fice a ransa yana cewa zan koya miki hankali wallah, kafin na bar k’asar nan, mata sai zaro zance tamkar ba a gasa miki baki ba.



***********************

Sai da ta gama gyaran gidan, sannan tayiwa Kamla da Abul khairi wanka ta dafa musu Noodles, Jallop tayi musu a abincin dare da taji alayyahu da
Naman rago da busassan Kifi, sannan ta yiwa Didi kunun zak’in da ta saba sha duk dare.


Tsaf ta sake gyara gidan sai fitar da sihirtaccen k’amshi yake.


Wannan daren dai Hammad yayiwa Didi yajin cin abinci, duk da
Dai ya san duk inda yaje yaci dole sai ya tuna abincin Didi ko yace abincin Hamda.


Tun Didi na basarwa har ta fara damuwa da rashin bayyanar jikannata, mafi soyuwa kuma a cikin jikokinta idan ka d’auke Hamda da ta biyo bayansa, bata jin ko y’ay’anta na cikinta tana yi musu soyayyar da takewa su Hammd d’in.

Gajiya tayi da jiransa ta sab’i gyalenta tana fad’in da kaina zanje bikonsa yanzu haka yana can Sadiya ta tasa shi a gaba, jarababbiyar yarinya ko kunyar d’an fari bata ji.” (Kuji Didi da K’arfin hali, ita da d’anta.)

Har ta isa b’angaren Sadiyar mita take kamar taci babu, hannunta damk’e da Na Khairi take cigaba da fad’ar “Wallahi Idan naje na ganshi wajen Sadiya ko abincin yake ci sai Na kifar, Allah Na tuba Matar da bata iya girki ba ma, ai kudai Ummal Khairi ba kiyi sa’ar Kaka ba, kamar yarda Hamda tayi sa’ata a matsayin kakarta ga shi babu ce kawai idan an bata ba zata girka ba.” Khairi dai murmushi kawai take wani zubin kuma ta tuntsire da dariya.

Danna k’ofar kawai tayi ba tare da sallama ba, a fusace ta shige d’akin idanunta cikin na Sadiya da suke zaune gaba d’aya da yaranta hud’u Hamid ne kawai baya nan,
Girgiza kawai Didi ta shiga yi ta zauna a kujera tana kad’a k’afa.

A tsorace Sadiya ta fara shirin gaisheta, da sauri ta saka hannu alamar dakatarwa, “Yau kam na gane dalilin Sakina na son haihuwar maza ashe wannan take gudu, ke yanzu Sadiya ba kijidon kunya ba, ki tasa yara a gaba kina gayaa musu k’arya da gaskiya wai ke mai y’ay’a, Ashe shi yasa naga Hammadu yau ya taho nan ya tare kin koya musu su raina mutane, Allah na tuba Banda na kasa na tsare ta ina zaki samu cikin Hammd d’in, kin san dai lokacin ko kallon arziki Ummaru ba yi miki yake ba, wato yanzu yara sun girma zaki fara iko da su, to wallahi ahir ki fita ido na akan Hammad sai na ci uban kowa a gidannan, su dama wad’annan ai tuni na sallama miki su, don daga gaisuwa ba abinda yake had’a mu da su, kin riga kin koya musu tsanata. Kai Hammadu tashi mu tafi.” Fuskarsa ya d’aure tamau, alamar ba inda za shi har sai da Sadiyar ta dinga had’a shi da Allah sannan ya mik’e fuskarsa a had’e ya fice.


Sai da Mahmah tagais fitarsu sannan ta saki ajiyar zuciya Humaid kuwa sai dariya yake don shi ya mayar da itabin comedian. Mahmah ta kai masa duka da pillow ganin yarda yake kwaikwayar Didin.




_____________

K’ememe ya k’i cin abincin har sai da Didin ta bashi hak’uri sannan yaci, don dama duk burga ce shi kansa yana son cin abincin ya kuwa ci da yawa, musamman kunun zak’in da ya dinga shansa kamar ba gobe, ta kowanne fanni zai iya dakar k’irji yace matarsa Nanna tayi hundred percent, inda take da matsala kawai a b’angaren girki ne, sam bata iya girki sosai ba, duk da tana k’ok’ari matuk’a da gaske wajen ganin ta iya d’in.




_____________________________

Cikin dare, don zai iya kiran lokacin talatinin dare, idan ya dinga jiyo motsin mutane kasancewar ba barci yake ba, yana ta duba ayyukan companyn su ta internet.

Motsin da yaji ya yawaita ne ya saka shi

Please Login or Register in order to submit comment