Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta damo mata ta sha kuma sosai har sai da tayi gyatsa. Abbu murmushi kawai yake yana sake jaddada kimar Sadiya a zuciyarsa, da gaske ɗin ita ta dabance zuciyarta mai kyauce,Mai halin mutanen farko shi yasa kullum yake mata kirari da Hali dubu.



Kashegari kuwa aka sallamesu, ko kafin suje gida tuni Mahmah tayiwa Saliha waya ta ce ta gyara mata ɗakin da yake kusa dana Humaid nan zata saka Hamda a ciki, duk da bata da tabbacin uwarta zata yarda sai dai wannan karan Abbu ya tsaya kai da fata ya ce dole nema ta yarda tunda ita bata sonta bata isa ta hana wani riƙeta ba.


Suna shigewa sashenta Ammi ta fito a sukwane cikin bala'i ta shiga ɓangaren Sadiyar tana zuwa ta shiga surfa bala'in sai an fito mata da ƴarta ai ba uban wanine ya haifa mata ita ba matar shige kawai borar gida"
Sadiya murmushi ta saki kafin ta girgiza kai ta ce"Wallahi ba zata fito ba sai dai idan Ubanta ne yazo ya fitar da ita da kansa, kuma alhamdulillah borar gida ita ta zama uwar mazan gida mowa kuma ta haifi mata...... Wani kukan kura Ammi tayi, tayi kanta yasa na runtse ido don na tabbata ba za'a kwashe da daɗi ba.
[1/12, 7:42 AM] Nazeefah Nashe: _~ALƘALAMIN JIKAR NASHE


YA ABIN YAKE ?

LIttafin Nazeefah Nashe.

08033748387





Follow me on ArewaBooks

@nazeefah

https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e


ELEGANT ONLINE WRITERS

(Haɗin kai shine takenmu.)
_3











Ya abin yake?


Daban yake da sauran.


Da sauri Sadiya ta fincike wuyanta
haɗe rai sosai tayi ta ce "kada ki fara kada kiyi wannan kuskuren, ko ina yarinya ban yarda da dambe da kishiya ba, balle yanzu da nake da ƴaƴa da jikoki har da surikai."

A zafafe Ammi ta ingijeta tare da ɗaga hannu zata zabga mata mari dai-dai lokacin da drivern Didi ya danno hancin motarsa cikin gidan tare da sakin gigitaccen horn, bisa bin umarnin Didi don sanar da masu gidan zuwanta, wanda hakan shine tambarinta.

Cak Ammi tayi da hannunta cikin matuƙar ɓacin rai da haushin bayyanar jarababbar tsohuwar, tayi tsaki ta fice daga sashen Mahmahn da sauri don ta san tabbas Didi tazo ta tarar da wannan tashin hankalin ranar na lahira ma sai yafi ta jin daɗi. Mahmah tayi murmushi kafin ta furta “Gaba da gabanta”da ki tsaya mana. Sannan tayi azamar fita don tarar Didin.



Fuskar Didin a washe take kallonta, da duk jama'ar gidan tana amsa gaisuwarsu cike da murnar samunsu lafiya, ahalin Sakina ne kawai bata gani ba. Bata damu kanta ba ta san dalilinsu na ƙin zuwa bai wuce ba sa son tayi musu gorin rashin aure ba, alhali ba mijin suka rasa ba suna dai jiran wanda ya ci ya tada kai.

Murya a cunkushe ta kalli Sadiya ta ce"Ita hakimar kishiyar taki tana ina?"
Mahmah ta ɗan yi jim kafin ta ce "Ina ji sallah take tunda baki ganta ba." ta samu kanta da gillara ƙarya duk don ta gyara lamarin. Didi ta kalli agogon hannunta kafin ta ce "Sallahr walaha take Kenan da sha biyun rana? Sadiya kenan kishiya kike karewa don kada nayi mata sababi? ai ba tun yau na san Sakina bata ƙaunar taga nazo gidannan ba, saboda bata son na sawa yaranta ido to wannan karan a shirye nazo tsaf wallahi ba zan bar gidannan ba sai na aurar da iyayen matan da ta girke a ɗakinta, su ba zawarawa ba su ba ƴan mata ba, shi kuma soloɓiyin mijinku ya saka mata ido sabida baya son laifin balarabiya."

Sunkuyar da kai Sadiya tayi kafin ta ce "Kiyi haƙuri Didi ai aure lokacine da zarar lokacinsu yazo ko suna so ko basa so sai sun yi."

Dai-dai lokacin da Ammin ta shigo kuma duk wani sababin Didin akan kunnenta take yi ranta ya sake ɓaci shikkenan wannan matar zata zo ta ɗaga mata hankali.

Fuskarta ba yabo ba fallasa tayi sallama haɗe da faɗawa cikin parlourn. Didi ta zuba mata ido tana jijjiga kai ganin yarda Sakinan ta cono ɗankwali har gaban goshi,alamar dake nuni da cewa a shirye take da amsar duk wani rashin mutunci na Didin.
Murya a cunkushe ta fara gaisheta Didin ta yamutsa fuska kafin ta ce "Ai Sakina da kin bar gaisuwarki tunda ba dole nace sai kinzo kin gaisheni ba, ba buƙatar ta nake ba gaisuwar da za'a yiwa mutum ana faman ɗaga hanci dai-dai nake dake wallahi, ki bini a hankali kafin ki kaini bango." Sakina dai ɗan murmusawa tayi wanda direct zan iya kiransa dana rainin hankali ta miƙe cike da izza tace "A huta lafiya Didi" daga haka ta kaɗa zaninta ta wuce ta bar Hajja Didi da hangamemmen baki don kuwa ta hango raini tsagwaronsa a fuskar Sakina, girgiza kai tayi kawai tana kallon Sadiya tace "Shahara iyye! Cabd’i jam" girgiza kai itama Sadiyar tayi ita kanta tana mamakin yarda Sakinah ta fetsare har haka? Didin da ko ido mutane basa iya haɗawa da ita idan tana magana. Ita dai murya a sarƙafe ta hau bata haƙuri sannan ta miƙe don ta bawa Didin waje ta huta har ta kai bakin ƙofa Didin tace "Ina Hamda ne ban ganta ba ko bata gama gallafirin makarantar kwanar bane?" Sadiya ta girgiza kai ta ce tana ɓangarena bata da lafiya ne yau ma aka yi discharging ɗinmu daga hospital ai da tuni kin ganta ta fito."

"Subhanallahi me ya sameta haka? Yanzu haka shaiɗaniyar uwarta har yau bata san annabi ya faku ba ko? Wannan mata sai kace wacce tazo a zamanin jahiliyya ƙiri-ƙiri ka ƙi ƴarka ba laifin tsaye ba na zaune, muje in ganta ai gwara da aka mayar da ita ɓangaren naki, naga uban da zai ce sai ta koma gurin wulaƙantacciyar matar can da ta zamewa mijinki matar jaraba." Ita dai Sadiya murmushi kawai ta saki ta bi bayan Didin tana tafe tana riƙe zaninta da yake shirin faɗuwa.



A kwance suka sameta idanunta a lumshe lokaci guda ta sake zabgewa dama ita ba jikin arziki ba kyalan-kyalan take tamkar ta faɗi ko don bata da kwanciyar hankali ne Allahu ya alamu. Didin da sauri ta ƙarasa gefen gadon ta zauna tana dafa goshin Hamdan, da kyar Hamdan ta buɗe idanunta da suka zama tamkar garwashi ta zuba su akan Didi tana sakin wani malalacin murmushi, tana shirin miƙewa Mahmah ta ce "Koma ki Kwanta Ke da ba kya jin daɗi." Wani kallo Didi ta zabga mata kafin ta ce "Ta zauna a ina? Bayan Allah ya kawo ni, ke tashi dahalla mu wuce idan banda kafirin iyayi na Sadiya me ye haɗinki da ita da har zaki rabamu? Sadiya ta gumtse dariyarta ta ce "Ayi haƙuri Didi bari na taimaka mata ta koma ɓangarennaki" "Ya dai fi, in banda shegantaka ba ita take taya ni hira ba, sai kuma a barni can a zaune ni kaɗai kamar wata mayya dama ku gidannan ba wani yawan arziki ba kowacce ta tsaya ragwanta daga haihuwa biyar kawai ni sai da na haihu sau goma sha huɗu ke da kanki kin sani zama ne kawai Allah baiyi zasu yi ba, Huɗu kacal Allah ya raya min na kuma gode masa a hakan ma, muje dahalla kin tsaya min wani iyayin banza."


Ammi da take tsaye a jikin window ta hango fitowarsu ana rirriƙe da Hamda wani abu mai kama da tausayi yaso shiga ranta amma sai tayi tsaki kawai ta saki labilan zuciyarta na sake ɓacin ran ƙin barinta ta cigaba da wahalar da Hamda da aka yi, yarinyar da ko sunanta bata son ji bare karo da baƙar fuskarta.



Didi suna shiga ɗakin ta hau damawa Hamda fura da nononta mai kyau da tazo da shi, sai garin fura mai ƙanshi da aka yi mata dakan hannu sai zabga ƙamshi yake. Sosai damun yayi kyau sai ƙamshi take bata saka mata sugar ba sai zuma farar saƙa.


Da kyar Hamda ta miƙe ta karɓi furar ta fara sha dama Allah ya zuba mata son fura don dai bata samu ne sai Didi tazo, don wani lokacin da gangan Ammi take dama furar kuma ta hanata ta bawa masu aiki saboda ta san tana tsananin son furar. Ta lumshe ido tana jin daɗin zuwan kakartata da ta tabbatar soyayyar da take mata babu algus. Sosai ta samu ƙwarin jikinta har ta miƙe da kanta ta shiga toilet tayi alwala tazo ta tada sallah a gefen Didin da take sallahr itama.


Suna idarwa suka jiyo sallamar su Muneerah Najma da Nasma fuskar Muneerah ce kawai a washe banda ta su Najma da suka yi kamar an aiko musu da saƙon mutuwa.


Muneerah da sauri ta isa wajen Didin tana gaisheta, itama cike da kulawa take amsawa tana son Muneerah musamman da yake ita sunanta taci "Ina kika shiga tun ɗazu ban ganki ba?" Muneerah tana ɗibar fura ta ce "Wallahi Didi Islamiyya naje da na gaji da tsimayin zuwanki.".Didi ta ce "Masha Allah ubangiji ya bada nasarar karatu. Ku kuma asararru ina kuka shige ana nan dai ana haɗa kafaɗa da iyaye an ƙi aure ko? To ku kwana da saninku wannan karan da shirina nazo inma ku fitar da miji ko ni na fitar muku acan Gwarzo cikin dangi ko abokan arziki, na baku wata ɗaya kacal wallahi wannan karan ba zan karɓi uzirinku ba ko kun wuce azimi ba zaku wuce sallah ƙarama ba insha Allah ku haƙura ku zaɓi ko waye tunda govenor da shugaban ƙasar har yau ba su ganoku ba, sai ku rungumi haƙuri kafin furfura ta fara bayyanar muku a gida, don kyan da kuke taƙama da shi zagwanyewa zai yi matuƙar babu aure shashashai kawai." suna gama gaisheta suka miƙe ransu a. ɓace da tijarar da take musu suka ƙarasa wajen Ammi Suna shiga taga alamun Didi ta kunnosu tsaki tayi kawai tayi kafin ta tambayesu mai ya faru? Najma ta zauna tana zuba tagumi ta ce "Jarrabar tazo yaushe zamu ga dai-dai daga zuwanta har ta fara zancen aure wai mu zata haɗa da ƴan gwarzo kurt da kuwa sai ta gwammaci kiɗa da karatu wallahi don ba mai saka ni auren mutumin ƙauye."
Tsaki Ammi tayi kafin ta ce "Ya zama kuwa dole na tashi tsaye wajen samo muku mazaje na kece raini ko da kuwa zanyi yawo tsirara burina naga kun auri mazan kece raini da zanyi tunƙaho dasu a matsayin surukai tunda dai Allah bai bani yara mazan da nake burin naje gidansu na baje mulkina ba, kamar yarda waccan tsohuwar take baje nata, tun ina yarinya ban fi shekara sha shidda ba nasa wa raina son haihuwar ƴaƴa maza ganin yarda yayar Mamma na take baza mulki a gidajen ƴaƴanta maza Ita kuwa Ummi mu kawai ta haifa mata bata da inda take zuwa tayi tunƙaho sai daga baya ta haifi ƙaninmu shikkenan na sawa zuciyata burin haihuwar maza amma Allah bai cika min burina ba, duk da ƙoƙarin da nayi tayi akan haka."


Tana faɗar haka hawaye ya shiga gangaro mata akan fuskarta wanda hakan yake nuni ƙarara da zallar ɓacin ran da yake zuciyarta.


Ko da Abbu ya dawo zancen dai ɗaya ne Didi ta tareshi da shi ta kuma tabbatar masa wannan karan da gaske take dole ne ta aurar dasu da son su ko ba son su, su suka kawo mijin ko akasin haka ta sake jaddada masa "Idan har kaga hakan bai faru ba tabbacine na rashin rayuwata, amma ko sharafa nake a gadon asibiti sai na aurar dasu banda tsiya ko Munirah da Hamda sun kai munzalin aure. Shima kuma Hammad ka sanar dashi ya tattara ya dawo gida Yaro shekara sha uku yana can zube a ƙasashen masu jajayen kunnuwa yayi sammakal ko matarsa yana can aka Kai masa ita, ai barewa ba tayi gudu ɗanta yayi rarrafe ba. To wannan karan da shirina nazo ƙwal uban kowa zan ci har shi Hammad ɗin da ku iyayensa." Abbu dai sunkuyar da kai yayi yana jaddada mata za'a yi yarda take so.



Haka nake so Didi, ki soyawa kowa gyad’arsa a hannu y’an k’wal uba..
[1/12, 7:42 AM] Nazeefah Nashe: _~ALƘALAMIN JIKAR NASHE


YA ABIN YAKE ?

LIttafin Nazeefah Nashe.

08033748387


Follow me on ArewaBooks

@nazeefah
https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e


ELEGANT ONLINE WRITERS

(Haɗin kai shine takenmu.)
_4





*******************************



Da asubar fari, da tayi sallah bata
koma ba, tana zaune gefen Didi suka yi azkar kafin ta karanta abinda ya sawwaƙa daga Alƙur'ani mai girma. Bata koma barcin ba, kasancewar ta ɗan ji sauƙin jikinta gyara sashen Didin tayi tas. ta wanke toilets uku da suke sashen ɗaya a Parlour biyu a sauran bedroom ɗin da suke sashen Didin inda ta mayar da ɗayan bedroom ɗinnata duk da dai Didin bata yarda su raba ɗaki ba tare suke kwana. Tas gurin ya fito sai zabga ƙamshi yake farin ciki ya lulluɓe Didi yana daga dalilin da yasa take son Hamda, sam bata da ƙiwa ko kaɗan. Wanka Didi ta shiga tana faɗin kema sai ki shiga kiyi wanka ga sabbin kaya nan da na ɗinko miki don na san waccan gallafirin uwar taki ko kayan ubanku yayi muku ba bari take ki saka ba, ta gwammaci ta haɗaki da gwanjo ina nan Ina jiran ranar da zata zo tana neman gafarar ki, to ko cikin shegen Ki tayi ai iya ɗiban albarkar da zata yi kenan, balle laifinki ɗaya wai kinzo a mace, shikkenan tun ranar da aka haifeki ake gumurzu da ita bari muyi walaha mu karya na baki labarin da kika daɗe kina son ji na san yanzu shekarunki sun kai sha bakwai tsab kwanyarki zata ɗauki labarin takaicin uwarki mai hali kwatankwacin na jahiliyya, na tabbata ita da kanta banda an saka mata ido tsaf zata iya hallakaki a lokacin, kai mun ga tashin hankali Ƙiris fa ya rage ta zauce sabida masifa.


Daga haka ta shige wanka wannan damar Hamda ta samu tayi saurin ficewa tana mamakin surutun Didin.


Sashen mahaifiyarta ta shiga, dama da spare key a hannunta ta buɗe a hankali, shiru ta tarar da parlourn da alama barci suke tabi gurin da kallo duk datti ɗan kwana biyun da tayi bata yi shara ba. Dama ita Ammi sam taƙi yarda ta ɗau mai aiki don tace gata bata buƙatar wata mai aiki. Ta ɗaure Hijabinta a ƙugunta ta shiga wanke kwanukan kitchen ɗin ta gyarashi tsaf burinta ta faranta mata ko ta samu ta goge tabon ƙiyayyarta a zuciyar Ammin.

Kan kace me? Ta gyare gidan tsaf banda ɗakunan barcinsu ta wanke har toilet ɗin parlourn sannan ta saka turarukan wuta a burner da humidifier tuni gidan ya ɗau wani irin Ƙamshi daga haka tayi sauri ta fice ta koma sashen Didi.


A saman sallaya ta tarar da Didin da alama sallahr walaha tayi, ita kanta Didin ita Ta koyar da ita sallahr walahar, tana sake jaddada mata ɗimbun ladan da yake cikin Sallahr walahan da tarin nutsuwa da mai yinta yake samu a zuciyarsa, ga shi Allah yana amsa addu’arsa ba da jinkiri ba.


Wankan itama ta shiga ta yiyo sannan ta ɗauro alwalarta ta saka tsaleliyer atamfarta da Didin ta ɗinko mata kaya ne kala goma dama ta saba duk sanda zata zo sai tayi mata don ta san kafin tazo nata sun mutu tunda ba wata sutturar arziki uwar take barinta ta saka ba.
Idan ka shigo gidan ma zata zaka yi ƴar aiki ce, Saboda tsabar yarda zaka ga kayan sun ƙojale don tsufa ga kanta da baya samun cikakken gyata fatarta ma don dai Allah yayi ta cikin jinsin mutane masu taushin fata ne, da duk wahala bata jemewa tabbas da ba ta kai haka kyauba.


Tayi kyau sosai ɗinkin kuma ya zauna a jikinta tamkar ba daga ƙauye aka ɗinko mata su ba. Ta cukuikuye gashinta ta danna cikin ɗankwali don rabon da ta tajeshi har ta manta balle ta saka man kitso, ko wanke shi tayi haka take barinsa.


A gefen Didi da take lazimi da jug ɗin furarta a gefe ita ma ta tada sallahrta cikin nutsuwa. Sai da ta idar tayi addu’ointa Didin Ta tura mata cup cike da fura tace “Maza kwankwaɗeshi tas ki bani cup don na san waɗannan mashiriritan kafin su kawo abin karyawa sai goma ta gifta shi yasa wannan karan zan saka ya kawo min kayan abincina kaf da kaina zan dinga girki ba zan iya zaman jira ba, girkin da sai an ga dama sannan ake yin mai daɗi ko a zabga mai da maggi to bana ba dani ba kowa ta riƙe banzan abincinta."

Ita dai Hamda murmushi ta saki kawai tana kai cup ɗin furar bakinta. Ta shanye tas zuciyarta cike da farin ciki. Har zata kishingiɗa ta kwanta sai kuma ta miƙe ta ce "Didi baki ba ni labarin ba." "Ƴar nema ashe kina so bari mu ɗan runtsa tunda yau ba islamiyya sai na baki anjima yanzu kam idanuna har yaji yake.” Duk da ba haka ta so ba haka ta hakura don ta san idan ta matsa Didin zata iya cewa ta fasa.




________________________________

Ammi na fitowa ta ga parlournta tsaf sai baza kamshi yake da sauri Ta isa bedroom ɗin ƴan matanta don a tunaninta su suka yi sharar tunda Ta san Hamda na can ɓangaren Didi turus tayi ganinsu sheme suna barci har Muneerahn da take zaton ita tayi.

Jikinta a sanyaye ta juya don ta tabbatar Hamdan ce dai tayi, wani abu ya Tsirga a ranta mai kama da tausayin uwa ga yaranta, sau tari tana tunanin sassautawa Hamdan sai dai tuni shaiɗan yake rinjayar zuciyarta wajen tunanin Hamdan a matsayin wata tashin hankali ce wanzuwarta a rayuwarta, mutuwarta a zahiri ita tafiye
Mata alheri shi yasa take takura mata ko don wataƙil zuciyarta ta buga ta rasu ta huta da baƙin cikinta, don tabbas idan Hamda bata mutu ba nan gaba kaɗan akwai tashin hankalin da bata so ya afku tana da rai wanda zai zamo tamkar tozarci ne mai girma a gareta da zuri’ar D’an Borno gaba d’aya.
Ta sha auna kashe Hamdan a ranta sai dai tana fasawa gudun fallasuwar asirinta da kuma tonuwar sirrin da ta riga ta bisne a cikin ƙasa.

Ta ja ajiyar zuciya bayan ta zauna ta nutse a cikin kujerar three seater ɗinta samfurin royal da take girke a babban parlourn, idanunta akan tv tamkar mai kallon labaran da ake yi sai dai gaba ɗaya zuciyarta ta Lula can tunanin wani zamani da ya shuɗe.



_____________________________

Barci sosai su kayi bayan idar da sallahr walahar akan faffaɗar daddumar Didin mai laushin tsiya da take ambula mata turare kullu yaumin don son tsaftace wajen ibadartata da yake can kusurwar ɗakinta.
Bugun ƙofar da ake yi ne ya farkar da su daga barcin Hamda ta miƙe don taga waye itama Didin miƙewa tayi tabi bayanta da hanzari don bata da jiki ko kaɗan shi yasa bata jin nauyin jikinta.


Saliha ce mai aikin Mahmah ta shigo hannayenta ɗauke da manyan warmers bayanta kuma Humaid ne yake biye da ita da flask ɗin tea. Didi ta dinga amsa gaisuwarrsu tana girgiza kai haɗe da duba agogo "Ba shakka, wannan abincin da mai za'a kirashi kenan na safe ko na rana? Kai jama'a ayi mata da shegen lalacin tsiya, to ni ba zan yarda da wannan tujarar ba bari wanda ya ajiye su yazo na faɗa masa ya jawa matansa kunne dama kada wacce ta sake ɗora sanwarta dani, su riƙe abincinsu can, zan dinga yi da kaina naga acan gwarzon ma da kaina nake yi to name za’a dinga wahalashsheni Allah na tuba abincin ma da ba ɗanɗanon arziki."
Ta faɗa tana buɗe coolerr abincin faten dankali ne da ya sha busashshen kifi da alayyahu sai ɗaya coolerr farfesun cow-tail ne ɗayar kuma gurasar larabawa. Baki ta taɓe,dan ta tabbatar dai abincin ba makusa sannan ta ce Hamda ta kwaso plates ta zuba musu.

"Ku tashi kuje ku ke kallona kamar kun samu akwatin kallo, kai kuma me ya hanaka zuwa makaranta." Humaid da yake duk a tsorace da faɗan tsohuwar ya ce "Hutun independent day muke." kallo ta watsa masa kafin ta ce "Wani abu ne kuma indafadan?" Ba Humaid kaɗai ba har ta Hamda sai da ta tuntsire da dariya Didi Ta ce “Kaji min aikin banza faɗar tawa kuke wa dariya? Aikin kawai to turancin faɗar annabi ce da sai na iya? ka tashi kaje kace ina son ganin ubanka tunda gaisuwar ma sai na roƙa." Humaid ya fice yana dariya Ƙasa-ƙasa a zuciyarsa ya ce "Drammer Queen"


Abincin suka ci sosai kafin Hamda ta kai kwanukan kitchen ta ɗaurayesu sannan ta dawo.

Man zafi ta ɗauko tana shafawa Didin a ƙafarta. Didin ta ce Alhamdulillah tunda ciki ya ɗauka bari na baki labarin asalinmu ciki da bai, da yarda aka yi auren uwarki da ubanki ba bisa son raina ba.....”




_____________________________

Asalin kakanku haifaffen garin maiduguri ne kasuwanci ya kawoshi kano Ƙauyen Gwarzo, inda anan Allah yayi arzikinsa yake kuma anan ya had’u dani ya aureni har muka hayayyafa duk a Ƙauyen Gwarzo. Haihuwata sha huɗu sai dai a ciki huɗu ne suka rayu mahaifinki Umar ne babba sai Aliyu kafin na haifi Aliyu kuwa yara uku na haifa tsakaninsa da mahaifinki sai dai basu zo da rai ba.

Daga Ali gadanga ƙusar yaƙi sai Gwaggonku Asma'u da take zaune a can ƙasar dubai da mijinta daga ita kuwa haihuwa biyar nayi ba rai kafin na haifi autata lauratu wato Ammanku Ta Janbulo daga nan ne fa haihuwar Ta tsaya min bayan nayi biyu ba rai. Ni kad’ai ce wajen kakanku Usmanu dan Borno bai sake aure ba duk da baloƙoƙon da danginsa suke masa wajen son ya ƙara auren acan gida borno har mata aka bashi amma yace ya yafe ni kad’ai na isheshi tunda ina yi masa duk abinda yake so baya son yazo ya had’a tashin hankali a gidansa yana zaune lafiya.


Haka suka gaji suka zuba masa ido duk da surutun da suke masa yasa auduga ya toshe kunnensa ya ce ba zai ƙara aure ba. Ni nan da kike gani na macece mafaɗaciyar gaske da ba na barin ta kwana in dai ka takaleni ka taɓo masifa bana shiga shirgin kowa amma fa bana yarda a taka ni. Hadizatu nake mutane da dama suna kirana wargi kike dai-dai Ƙugun kowane ɗan iska. Shi yasa duk garin Gwarzo in dai kika je kika ce kina neman Didi matar D’an Borno to kin gama samu na saboda shaharar da nayi a masifa, wanda bakomai bane sai zallar fad’ar gaskiya da mutanenku basa so yanzu.
Ko iyayenki Shakkata suke, saboda bana sakar musu fuska kamar yarda Kakanku yake sakar musu. Ba yabon kai ba dole Kakanku ya kasa aure sabida na riga na siye zuciyarsa da girki tunda shi in dai cikinsa zai d’auka to kin gama masa komai, idan kinga masifarsa to ya dawo gida ban gama abinci ba. Sannan ba yabon kai ba ina da tsafta dai-dai gwargwado, ga kwalliya kamar me don idan na cab’a kwalliya irin Ta mutanen da baki ga yarda yake zama yayi ta kallo na ba, na tabbata da yanzu zan yi wannan kwalliyar wasu ma mahaukata za su d’aukeni. Idan kuwa kika shigo gidana ba abinda zaki fara jiyowa sai k’amshin turaren wuta da na tsinke d’an Borno, don sana’ata kenan duk da ba wani ciniki nake ba kasancewar jama’ar garin mu basu damu da k’amshi ba. Ke na fa zabga iyayi ina yarinya Wani suna suke kira na da shi Delu iyayi har na haihu Umaru ya cigaba da kira na wai Delu, bisa tilas na koya masa cewa Didi shikkenan sai sunan ya bini. Idan kakanku yayi fushi wuyartana shafe baki na da jan jambaki nayi d’igo-d’igo a gefen k’uncina na ja siririyar jagirata, na bad’e fuskata da hoda pankeke shikkenan zaki ga ya daina fushin yana bina da ido yana fad’in Indiyana ni kuma kaina yana kumbura duk da ko a layin bak’ak’en India ba za’a saka ni ba, gashinta k’ak’k’arfa ne irin na hausawa, haka nan ba wani idon arziki gareni ba ga ni bak’a kamar yarda kika ganni d’in nan, amma don son ran kakanki yake kira na Indiyana ni kuma ina amsawa Cike da izzar nafi sauran mata, duk da wani ko a k’afa aka k’ulle masa ni ina tabbatar miki sai ya kunce ya arce ni da

Please Login or Register in order to submit comment