Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hawaye na zubo mata, ya zama dole ta fallasa sirrin nan, ko Ammi Ta hankalta ta nemi tuba ga Allah, Sannan zuciyarta itama ta huta da dogon tunani, idan ba haka ba kuwa tabbas zuciyatta zata buga. Ranar dai kam akan idonta aka yi kiran Assalatu abinda bata tab’a yi ba kenan a rayuwarta.


_________________

Sukuku ta tashi da safen, duk da barcin da yake rinjayar idonta, amma ba zata iya yi ba, Neman wanda zata tunkura da zancen take direct zuciyarta ta amince ta jewa da Anty Lauratu da zancen idan yaso ta gaya mata kada ta sake ta ce ita ta gaya mata.

Ko da ta fito parlour suna zaune suna karyawa gudun kada Ammin ta jefa ayar tambaya a kanta yasa ta zauna ta fara tsakurar abincin, tana turawa da kyar kafin ta mik’e tana zarar tissue, Ammi ta kalleta “Ke kuma sai ina ina ce yau baki da
Lectures?” Munira tayi saurin girgiza kai tana gyara farin glass d’in da ke idonta ta ce “Ammi ina da group discussion amma ba zan dad’e ba zan dawo.” “Ai shikkenan ki dawo da wuri don mu zamu je gidan Kady yayunki suna da bak’i kuma kin san bana son barin shiyyata ba kowa.” Da sauri ta d’aga kai tana ficewa daga parlourn tana jin Najma na cewa ta tsaya tayi dropping d’inta a motar Ammi amma ta zura da gudu, gwara ta shiga napep ba ta san kowa ya san inda zata, musamman Lauratu da bata shiri da Ammi, shi yasa ma Ammin bata bari suje gidanta.


A bakin gate d’in gidan mai a daidaita sahun ya ajiyeta ta zaro d’ari biyar ta bashi kafin Ta saka kai Ta shige had’e da cewa ya bar canjin.


Lauratun ce kawai a gidan duk yaran sun tafi makaranta, dama babbar y’arta sa’ar Hamda ce. Cikin mamaki take kallon Muniran ta ce “Ikon Allah yau kece a gidan amma dai Sakina bata san nan kika zo ba? Kuma fa yanzu da kika ganni mayafi nake shirin yafawa yau nace a wajen Didi na zan wuni”
Munira murmushin yak’e ta saki kafin ta ce “Ya naji gidan shiru?” Lauratu ta ce “Wa zaki samu duk sun tafi school daga ina haka?”
Tana murmushin ta ce “Daga gida mana” Lauratu ta sake gyara zama ta ce “Amma dai ba lafiya ba? Don haka kawai Sakina ba zata bari kizo gidan nan ba, haka kawai ta cusa muku k’iyayyata.” Munira ta ja fasali kafin ta ce “Wallahi, Amma ba k’alau ba wata gagarumar magana ke tafe dani amma ban san ta yarda zaki d’auki abin ba, ko ma ta yaya kika d’aukeshi please kada sunana ya shigo.” Nan ta shiga bata labarin da ya hautsina kayan cikin Lauratu kafin ta gama kuwa gumi ya jik’ata sharkaf duk da sanyin a.cn da yake parlourn, hankali tashe ta mik’e tana struggling a parlourn ta ma rasa abin cewa illa zuciyarta da take wani irin duka, fatanta da burinta a lokacin kada Allah yasa hasashenta ya zama gaskiya, duk da komai ya nuna kansa k’uruk’uru tun a lokacin da ace sun kasance mutane masu tsinkaye da sun fahimci abinda yake tsakanin Sakina da Hammad, kafin cikin Hamda ya bayyana, me yasa idanunsu suka rufe suka kasa gano dalilin takun sak’ar Sakina da Hammad, lokaci d’aya yaron ya juye ya zama mai bak’ar zuciya, ya kuma tsani had’a inuwa d’aya da Sakina Why? Lauratu ta fad’a da k’arfi had’e da rotsa wani verse da yake gefe a fili ta furta tabbas Sakina ta cucemu idan har hasashen mu ya zama gaskiya, tayi wa zuri’ar d’an Borno mummunan tabon da zai bi mu har kan tattab’a kunnenmu a ina aka tab’a yin haka?

Ganin yarda hankalinta ya tashi ne ya kad’a hanjin cikin Munira, sam ta manta zafin ran k’anwar ubansu Lauratu, me ya kaita zuwa ta bayyana mata wannan gungumemen sirrin? Cikin rawar murya ta ce “Please Amma, don’t include my name, don Allah.” Ta fad’a tana durk’ushewa a gabanta hannayenta a had’e alamar rok’o. Fuska ba annuri Lauratu tayi mata wani irin kallo kafin ta mik’e ta zari Car key, da wata iriyar murya ta ce “Ba abinda zai saka ni fad’ar sunanki, amma am sorry to say ba abinda zai hanani tonawa Sakina asiri yau, sai dai idan kafin na k’arasa gidan na mutu.”

Gaban Munira ya shiga duka, ganin har Lauratu ta kira Umma Asma’u ta rattaba mata bayani, kasancewar ita a dubai suke zaune da yaranta da mijinta ba damar ta zo ji tayi kawai Umma Asma’un ta saka kuka tana fad’in “What a nonsense Lauratu?” D’if ta kashe wayar ta mayar da kiranta kan Gadanga, kafin ta kira Babansu Hammad ta ce tana da meeting da su a sashen Didi kuma urgent ne, hankali tashe duk suka dinga barin wajen aikinsu, suna tafiya gida.

A hanya ta sauke Munirat “Ki wuce School kamar yarda kika sanar mata, ba zan ce ke kika gaya min ba Allah yayi miki albarka.”

Munirat jikinta a sanyaye ta fice daga motar, tana fatan Allah yasa ba gagarumar matsala ta janyo a familynsu ba sai yanzu take da na sanin fitar da maganar da Ta sani barinta tayi a ranta ko da zata zama ajalinta.



⭐️
Kamar an jehota haka ta shiga b’angaren mahaifiyarta Didi, tana zaune da casbaha a hannunta tana latsawa, idanunta akan a k’warin talabijin tana kallon tashar Saudi Sunna, kasancewarta masoyiyar madinatul munawwara, girgiza kai kawai take tana sauraran hadisai tamkar tana gane larabcin da suke yi.

A fitgice ta d’ago tana zube idanunta a kan Lauratu y’ar autarta, cikin masifa ta ce “Amma Lauratu baki da hali ko kad’an wallahi, fisabilillah banda rana ce b sai nace gamo nayi ba ki shigo min haka bagatatan ba sallama, haba kina girma kina cin kashi, wallahi sai da gabana ya yanke ya ce ras Allah ya raba mu da mugun halinki Lauratu.”

Da Didin ta dubi yanayin fuskarta da bata cigaba da kwararato ba, sai da ta dasa aya sannan ta d’ago tana duban idanun Lauratun da suka yi jajir kamar gauta, da sauri ta ce “Hasbunallah, Allah yasa
Dai ba mijinki bane ya sako ki.”
Lauratu ta ja ajiyar zuciya kafin tace “Gwara min ace sakina yayi wallahi, da wannan gundumemiyar masifar da ta tunkaro mu.” Tuna k’irjin Didi ya shiga luguden daka jin zancen Lauratu wace masifa ce da har ta fi saki? Ta jefawa Lauratun tambaya ba tare da ta shirya ba, Lauratu ta saka gefen mayanfinta ta goge hawayenta, Didi ta ja tsaki shikkenan ta faru ta k’are Wata yayi wa ciki, ya tafka miki tsiyar halin mazan kenan? Ko kuwa Kishiya zai yi miki?” Tsaf Lauratu ta shanye kukanta tana girgiza kai ta ce “Wallahi, duka Didi gwara wannan akan masifar da ta tunkaro zuri’armu ta D’an Borno.” Kafin kace me sai ga Didi ta shige toilet da sauri saboda juyin da cikinta yayi, anya Lauratu tana cikin hankalinta kuwa? Ta dad’e a toilet d’in kafin ta fito tana yarfe gumi ta kalli Lauratu “Kinga Lauratu tun muna shaida juna da ke ki gaya min me ya faru? Kafin ki kaini gadon asibiti.” Lauratu ta shiga dube-dube kafin ta ce “Ina Hamda?” Didi ba baki sai d’akin Hamda data nuna mata, Lauratu ta saka baki ta k’wala mata kira, sai ga Hamda ta fito da sauri, don ta san Amman tasu bata son jira.

Ido kawai lauratu ta tsira mata ba tare da amsa gaisuwar da take mata ba, ta ce “Kirawo min d’iyar Hammad, Kamla.” Hamda da sauri ta koma d’aki don can ta baro Kamlan tana game da sabuwar wayar da zunnuraini ya kawo mata.
Kamo hannunta kawai tayi suka taho parlourn, Lauratu ta k’ura musu ido tana sake jin fad’uwar gabanta na k’aruwa kafin ta ja fasali ta ce “Didi k’ura musu ido ki gano min ko akwai banbancin da ni na kasa ganowa.” Tsaki Didi ta ja kafin ta ce “Kaji min zancen banza, da wofi to tun yaushe ake fad’ar kamanninsu, wani abu ne don ta yiyo kamannin k’anwar ubanta, bana raba d’aya biyu a can ahalina na farko sai kayi shishshigin d’ebo kamannin wani, wanda ba mamaki tun tale-tale kafin a haifeni ma suka zo duniyar suka yi rayuwarsu suka koma, shine Me don Hamda tana kama da Kamla?”

Dai-dai lokacin Abbu da Gadanga suka shigo, ido suka zubawa Lauratu don duk hankalinsu a tashe suka taho, sun zata wani abin ne ya samu Didin, ita d’in ma ido ta kafa musu kafin ta ce “Kuyi hak’uri na tasoku rana tsaka, wani abu ne mai firgitarwa yasa na fito da ku daga office, Yaya ka dubi Hamda da Kamla ka gaya min akwai banbanci a zubin halittarsu.” Ta fad’a tana kallon Gadanga, da yayiwa su Hamda k’uri da ido, sai kuma ya girgiza Kai, “Sam ba wani banbanci sai yau ma na sake tabbatar da zahirin kamanninsu da ake ta fad’a a dangi, wani abu ne ya faru?” Girgiza kai tayi kafin ta ce “Hamda ku shiga ciki.” Suka wuce
Kuwa suka shiga duk da Hamda hankalinta ya kasa kwanciya, sai da ta rab’e jikin k’ofa.

Lauratu taja ajiyar numfashi kafin ta ce “Abbu Kayi hak’uri da abinda zan fad’i amma Hamda ba y’arka bace, y’ar Hammad ce!

Kafin tayi aune suka ga Didi tayi wani irin mik’ewa ta kai mata damk’a cikin matuk’ar tashin hankali, da sauri Gadanga ya rik’ota yana k’ok’arin zaunar da ita ta fisge jikinta “Bar ni Gadanga barni in shak’e yarinyar nan ta mutu na daina jin wannan zantukan banzan, mu zata b’atawa sunan dangi wace irin maganar banza ce wannan?”

K’arar da suka ji da fad’uwa a k’asa ne yasa suka bazama ciki. Hamda suka gani kwance a corridor ba alamar numfashi tattare da ita hakan ya tabbatar musu da taji zantukan da suke fad’a. Didi ta saka salati tana b’allawa Lauratu harara “Shikkenan kin yi kisan kai, na tabbata yarinyar nan ta ji wad’annan banzayen zantukan naki to wallahi ba zan rufa miki asiri ba, y’an sanda zan kira yanzu su gark’ameki.” Gadanga dai bai ce komai ba ya d’aga Hamda cak ya shigar da ita cikin bedroom ruwa ya shafa mata kafin ta kawo gauran numfashi. Idanunta a runtse ta damk’i hannun Gadangan fad’i take “Baffa da gaske ne abinda kunnuwa na suka jiyo min? Da gaske ne ni y’ar Yaya Hammad ce ba y’ar Abbu ba?” Gadanga ya share zufar da take karyo masa don shi dai a hasashensa akwai k’amshin gaskiya a zancen Lauratu, baya son ya gasgata ne gudun afkuwar wata matsala. Ya kama hannunta duk da idanunta a runtse suke ya ce “Ba gaskiya bane ki kwantar da hankalinki, ba ta yarda za’a yi labarin nan ya zama gaskiya, kina jina?” Hawayen ta share da kyar ta d’aga Kai, shi kuma ya mik’e ya fita parlourn jikinsa a salub’e, gaba d’aya gwiwoyinsa sun sare da kyar yake jansu kada Allah ya tabbatar da wannan zancen na lauratu a bigiren gaskiya.


Zaune ya samesu jigum-jigum banda Didi da take ta yiwa Lauaratu masifa kamar zata cinyeta, ita kuma Lauratun ta kafe akan abinda take fad’e gaskiya ne, Abbu dai yana zaune kansa a k’asa shi kad’ai ya san halin da zuciyarsa take ciki a lokacin bai k’i Allah ya d’auki ransa ba kafin tabbatuwar lamarin a bigiren gaskiya. Idanunsa sun kad’a sun yi jazur, fuskarsa kuwa tamkar bai tab’a dariya ba tunda aka halicceshi, kan nasa a sunkuye ya d’ago yana sauke ganinsa akan Lauratu kafin su ji ya ce “A ina kika ji maganar nan?” Lauratu da ta tsorata da ganin yanayinsa musamman yarda ya tsatstsareta da manyan idanunsa da suka jirkita suka koma mata wani iri murya na rawa ta ce “Wallahi ina zaune a gida Munira ta zo ta same ni da zancen..........” kafin ta gama bada labarin tuni zuciyar Didi ta daina aikinta yarda ya kamata fata take ace mafarki take ba gaskiya kunnuwanta suke jiyo mata ba. Shi kuwa Abbu gaba d’aya yaji ana wata irin hajijiya da shi kafin ya kalli Gadanga ya ce “Ka kira min Sakina da Hammad ka kira kuma Sadiya.” Daga haka ya mayar da kansa jikin kujera ya runtse ido da gaske duk da a zaunen yake jinsa yake kamar zai fad’i wannan wace irin masifa ce tayi musu dirar mikiya a zuri’ar D’AN BORNO? Tambayar da yakewa zuciyarsa kenan da yaji tayi masa nauyi kamar Dutse. Didi kuwa bata uhm bata uhm-uhm sai wani irin kallo take bin lauratu da shi tana tunanin anya kuwa Lauratun jinin ta ce da suka haifa ita da mijinta Usmanu? Ban da a gida ta haifeta tabbas da tace an musanya mata Lauratu, saboda halayenta kaf ya sha banban da na yayunta, duk da bata tantama nata halayen ta d’ebe kaf har ma tana tunanin nan gaba kad’an zata shanyeta.


Mahmah ce ta fara zuwa jikinta a sanyaye ta shigo tana mamakin dalilin wannan zaman da rana tsaka gagal haka, bata ce komai ba ta zauna tana amsa gaisuwar Lauratu da ta ganta tamkar a firgice.

Ita kuwa Sakina (Ammi) da sak’on ya sameta wata iriyar mummunar fad’uwar gaba ce ta sameta hakan ya tabbatar mata koma kiran menene ba alheri bane. Jiki na rawa ta mik’e tana lalubar mayafi don ta san bata da damar da zata kaucewa kiran Didi.

Hammad ya rigata zuwa, shigarta parlourn ta hangoshi zaune kan kujera duk da a yanayi na rud’ani yake ba zaka tab’a gane hakan a tare da shi ba, ya san za’a rina ya kuma san irin wannan ranar ko mu dad’e ko mu jima zata zo, ranar da yake mafarkinta yau ga shi ta zo ko da wani ido Sakina zata dubi mutanennan ta basu labarin abinda ya faru? Ya sauke gwauran numfashi lokacin da yaci karo da fararen k’afafun Sakinan tana shigowa falon, sune dai wad’ancan fararen k’afafun da ba zai tab’a manta a yanayin da ya gansu ba a wancan lokacin, ya runtse ido bayan ya hango shigowarta tana taku tamkar bata son taka k’asa haka halittarta take tun fil’azal Sakina mai yanga ce. Tabbas yau zai fito ya fad’i Gaskiya ko ya huta da bak’in cikin da yake kwasa a zuciyarsa shekara da shekaru.

Tun kafin ta k’araso taji kanta ya sara ta tabbatar kuma wannan zaman ba na lafiya ba, Allah dai yasa zaman ba akan wancan b’aragurbin k’wan bane da idan ya fashe warinsa sai ya addabi duk wani ahalin zuri’ar d’an Borno zai kuma girgizasu matuk’a da gaske.

A can gefen Abbu ta zauna duk da tun da ta shigo bai d’aga kansa ba. yanzun ma bai d’aga ba ya tabbatar dai itace tun bayan da
Ya shak’i k’amshin turarenta.

Shirun da yaji gurin yayi ya tabbatar masa da cewa ba za su iya tunkararta da zancen ba, hakan yasa kansa na k’asa cikin wata iriyar murya da sam ba tayi kama da ta Abbun ba saboda kaurinta da bud’ewarta ya ce “Sakna ina so ki fad’a min Hamda y’ar waye?” A firgice ta d’ago ta zubawa Hammad ido tana da tabbacin shi ya gaya musu, maganar ta razanata matuk’a ainun duk da ta san lallai lokacin zai zo ba tayi tsammanin zai zo da sauri haka ba, murya a shak’e tana duban Hammad da wani irin yanayi kallo mai fassara tabbas zaka gane kurenka, tayi k’asa da kanta sai ji suka yi ta fara fad’in “Hammad ka cuceni, na San tabbas wannan ranar zata zo, duk da ba a hayyacinka kake ba, amma komai ya faru ne sanadiyyar kayan maye da ya fara sha a lokacin, ba kowa a gidannan duk kun tafi Gwarzo ranar da Baba mak’oci mahafin Sadiya ya mutu a ranar lamarin ya afku, sam ban san ya fara shaye-shaye ba da ban bud’e masa k’ofa a lokacin da yayi bugun ba tsautsayi ina bud’e masa na ji.... sai ta fashe da kuka “Kuyi hak’uri ba zan iya k’arasawa ba abu d’aya na sani Hamda y’arsa ce ta cikinsa.

“Kina da Shaida?” Suka ji Gadanga ya ce cikin b’acin rai har a zuciyarsa bai yarda da zantukan Sakna ba. Da sauri ta d’ago ta watsa masa wani kallo kafin ta ce “Eh ina da shaida, ko wannan dawowar ma sai da ya sake turo min sak’on banza ta waya, akan ko na amince na zo na same shi ko ya fad’awa duniya Hamda ba y’ar Abbunsa bace, har cewa yayi sai yayi min Sharri.” Da sauri suka ga Hammad ya mik’e cikin razani ya kai mata wata damk’a. Abbu ne shima a masife ya mik’e ya kwad’a masa mari, yana k’ok’arin buga shi da bango a zafafe Gadanga ya tareshi yana fad’a “Haba Yaya,
Ka bari a bi lamarin nan a hankali, ke Sakina ina message d’in da ya turo miki?” Hannu na rawa ta bud’e message d’in ta mik’awa Gadanga Zufa ce sosai ta dinga zuba a jikin Gadanga don dai tabbas ga numberr Hammad ban b’aro-b’aro bayan yayi dialling a wayarsa ya tabbatar ita ce. Sakina Kallon Hammad kawai ta ke tana sakin murmushi k’asa-k’asa. Gadanga tsit yayi kansa a k’asa da wani idon zai kalli Abbu yace masa Eh da gaske D’anka yana neman matarka Abin fa da kunya kuma yana da girma ainun.

Bak’uncin shiru ne ya bak’unci falon kowa ya rasa bakin magana zuciyoyinsu ne kawai suke wani irin bugu na tashin hankali, shi kuwa Abbu tuni ji da ganinsa suka yi d’if, Didi kanta ta zama kamar gunki idanunta ne kawai suke kwararar da hawaye amma ko hannu ta kasa d’agawa. Hammad ransa ne ya dungunzuma ya b’aci yana zaune zufa ce kawai take karyo masa bai yi auneba yaji an rafka masa katako a kansa Abbu ne tsaye a kansa Gadanga yayi saurin rik’eshi “Haba Yaya kada ka yanke hukunci cikin fushi mana ka bari mu tabbatar da gaskiyar abinda ta fad’a, ai shi ba muji ta bakinsa ba.” Kuka Ammi ta saka da k’arfin gaske tana sake cewa Wallahi ba k’arya nake masa ba da gaske nake masa.” Abbu zuciyarsa Ta sake tunzira ya sake yin kan Hammad da duka “Ali ka barni na sumar da yaron nan, zata yi masa k’arya ne? Na tabbata abinda ka gani a waya ba abu ne mai kyau ba shi yasa ka kasa nuna min, wallahi ko ka bari na jibgeshi ko kuma na tsine masa, ya tashi yaja shegiyar y’arsa su fice min daga gida na tsani ganinsa.” Kafin su yi aune suka ga Hammad ya mik’e idanunsa sun kad’a sun yi jazur dai-dai lokacin kuma suka ji ihun Khairi tana fad’in Anty Hamda Anty Hamda, Ali yayi saurin shiga corridor d’in sai dai kafin yaje ya tarar numfashinta ya d’auke ya dawo da sauri yana fad’in “Yaya ka bi abin nan a hankali kada azo ana kisan rai ga yarinyar can ta fad’i.” A zafafe ya ce “Ta mutu mana burina ai mutuwarta idan bai janye ahalinsa sun bar min gidana ba wallahi sai na tsine masa.”
Da sauri Ali ya juya gurin Didi don yayi mata magana jin bata saka baki ba, sai dai me?daga Didi har Mahmah kamar basa cikin hankalinsu. Yayi saurin kama Didi yana kiran sunanta amma sai yaga ta fad’o jikinsa bata ko motsi da sauri ya hau jijjiga ta hankali tashe yake kiran “Shikkenan wannan masifa tasa mun rasa Didi, yanzu Lauratu kin kyauta da kika kawo wannan zancen Allah wadaran wanda ya fara tono b’aragurbin k’wannan.” Ammi ta zubawa Lauratu ido tana mamakin yarda Lauratu ta san maganar ita duk a zatonta Hammad ya kawo idan kuwa haka ne bai kamata ta tona wa kanta asiri ba, da sai ta kafe akan ba haka bane, tabbas tayi b’aranb’arama. Ita kuwa Sadiya sai a lokacin ta ja wani doguwar ajiyar zuciya a kuma lokacin ta samu damar kwararar da hawaye, sai dai ko da ta juya babu Hammad ba alamarsa a falon. Hankalinsu su kuma gaba d’aya yayi kan Didi sun kinkimeta don kaita asibiti. Gadanga yana ta fad’in a had’a da Hamda da take yashe amma Abbu yace “Wallahi Gadanga zan raba jiha da kai ka sake shiga hurumin Hammad da iyalinsa da gaske nake na rabu da shi har abada tunda har zai iya shiga gonata.” Ras gaban Mahmah ya buga ta juya da sauri don komawa itama a sama ta ji maganar Abbu “Kema kina shiga huruminsa a bakin igiyar aurenki daga rana mai kama ta yau na zare shi daga sahun yarana.” A karo na farko Mahmah ta jiyo ta watsa masa wani kallo abinda bata tab’a yi ba a rayuwarta sai cewa tayi “Sai me don ka sake ni ba zan fasa shiga hurumin yaro na ba, aurennaka da sam ba adalci a cikinsa, ka sake ni mana Ummaru kawai saboda rashin adalci ba zaka tsaya kaji ta bakinsa sai kawai ka gasgata ta kai tsaye, sabida ita bata laifi.” Da sauri Lauratu ta jata jikinta “Kiyi hak’uri Anty Sadiya, kada kiyi haka bari muje asibitin mu dawo na tabbatar Hammad yaron kirki ne wallahi sharrin hatsabibiyar matar can ne, amma yanzu ya d’au zafi da yawa bai zama lallai ya gane yaren ba, idan muka dawo sai ayi zancen a nutse.” Da kyar ta lallab’ata ta yarda ta bisu.




✍🏽✍🏽

Zuciyarsa a zafafe ya sake komawa Falon Didin har a lokacin tana nan yashe a k’asa babu wanda ya sake bi ta kanta, k’wafa yayi ya shiga toilet ya d’ebo ruwa da sauri yazo ya watsa mata, ta kuwa farka idanunta cikin nasa tana sakin wata nauyayyiyar ajiyar zuciya. Kuka take shirin sakar masa ya zabga tsaki had’e da b’ata rai ya ce “Kada ma ki fara ba lokacin kuka bane yanzu, lokacin kuka ya wuce tunda kin riga kin fahimci wacece ke, ki mik’e ki tarkato duk wani shirginki da takardun makarantarki ki fito mu tafi.” Ganin yarda fuskarsa take ta tabbatar ba wasa a lamarinsa ya sata ta mik’e ba shiri don ta lura sarai zai iya kai mata duka idan ta kuskurewa umarninsa. Sai dai ina taku biyu tayi ya jita a kansa ta fad’o tsaki ya saka ya tabbatar da gaske ba zata iya takawaba tsam ya mik’e da ita a jikinsa ya shimfid’eta a kujera da kansa ya fad’a cikin bedroom d’inta shi da Khairi suka had’a mata takardunta da litattafanta ko ta kan kayan sawa bai bi ba ya fito har su Kamlan ya tasa a gaba ita kuma ya mik’ar da ita yana rik’e da ita suka nufi mota. Dole ya kaita asibiti kafin aiwatar da duk wani shirinsa.

Da mugun speed yake jan motar bai kaita asibitin da suke zuwa ba wani can daban ya kaita, Khairi ya bari a wajenta bayan likitan ya sake tabbatar masa tana buk’atar nutsuwa sosai don jininta yayi mugun hawa. Ya kalleta a zafafe ya ce “Wallahi idan baki daina kuka da sakawa kanki damuwa ba, tsaf zan tattara in tafi in barki idan yaso ko kasheki ne su yi ni ba ruwana, an gaya miki suna da asara ne idan zuciyarki ta buga kika mutu, kina kallo dai suka yi watsi da lamarinki ta tsohuwar uwarsu kawai suke, dama idan na dawo kina kukan nan sai na murje bakinki, ga waya nan Khairi ki kira ni idan tayi kuka, haba fin mutane idon kukan kika yi?” K’asa kawai tayi da idanunta bayan ta d’auke sautin kukan tsaf. Ta bi bayansa da kallo bayan ya tasa Kamla da Abulkhairi a gaba yana fad’in “Muje na kaiku gurin uwarku.”


To fa! Mai karatu duka-duka anan na kawo k’arshen free pages amma ina tabbatar muku yanzu labarin ya fara wannan duk shimfid’a ce dad’in yana nan gaba. Kai dai kawai ka biya naka kada ayi babu kai.

Ga duk wanda ya siya riba biyu zai had’a don akwai free littafina na zumuncin zamani da zan dinga yi muku posting d’insa a cikin group d’in. Sai na jiku.


Normal group 300

Vip 500

Special people wanda za’a dinga turawa privately 1000 kacal

Zaka biya ta wannan account d’in

2118666253 UBA sai ka tura shaidar biya ta wannan layin

08033748387.


Ku biyo ni don jin yarda ABIN YAKE
Jikar Nashe taku ce!
[1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: Ya abin yake?

Nazeefah Nashe

08033748387

BONUS PAGE...

16..


(Saboda wasu da suka buk’aci a
D’an k’ara musu free pages shi yasa zan d’an k’ara ko 3 pages ne. Zuwa lokacin ku yi ta payment. 3 to 5 pages kawai zan k’ara.

Please Login or Register in order to submit comment