Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakinsa ya tsuke don sosai yake jin haushin tuna lamarin gaba d’aya.

Mahmah dai hankalinta ba a kwance yake ba, tana son ta hana Hammad tafiya da Hamda amma Dida ta hanata, ta ce ta kyaleshi ba wani abu bane don ya tafi da itan, ta kuma ja kunnen d’iyarta Nanna akan ta kyaleshi kada ta sake yi masa maganar don a yanayin da yake tsaf zai iya sakinta idan har ta cigaba da jayayya da k’in bin umarninsa. Haka tilas ta hak’ura sai dai ta k’udirtawa ranta sam ba zata bar Hamda ta yi rayuwar jin dad’i ba, tilas sai ta bak’anta mata har ta gwammaci ta bar gidan da k’afafunta.




_____________________

Suna fitowa daga Immigration office d’in ta ga ya d’auki hanya bai tsaya ko ina ba, sai wani k’aramin gida. Ba tayi magana ba har ya tsayar da motarsa ya fita ya bud’e k’aramin gate d’in. Ya shigar da motarsa y’ar madaidaiciyar harabar gidan. Zama ta yi har sai da ya ce “Fito mana.” Ta d’ago ido tana dubansa kafin cikin dauriya ta ce “Ya Hammad me zan yi?” Tsahon second yana dubanta kafin ya ce “Umarni na ba ki, ki fito kuma daga yau kada na sake jin kin kirani da Yaya Hammad ai ki na ji aka ce ni d’in ba wanki bane, Ubanki ne don haka ki dinga kirana da Daddy kamar yarda kika ji su Kamla na kira na. Ki fito na ce.” Ganin yarda ya tsare gida ne ya sata saurin fitowa. Gaba yayi a zuciyarta ta ce “Ashe dai mutumin nan mafad’aci ne?” Sai kuma ta kama bakinta da sauri tunawa da ta yi matsayin mahaifi ya ke a wajenta. Idan ta tuna hakan sai ta ji wani iri a ranta. Ya murza key ya tura k’ofar k’aramin parlourn. Sannan ya shiga parlourn tsaf da shi sai k’amshi yake. Tana so tambayeshi gidan waye sai kawai ji ta yi ya ce “Gidan abokina ne, mazaunin k’asar Birmingham, anan yake zama da matarsa idan sun zo hutu, shi yasa nima yanzu nake jin takaicin rashin gina gidan kaina, amma insha Allah soon zan gina ko don gudun kora daga gidan mutane.” Ta juya tana k’arewa madaidaicin parlourn kallo kafin ta ce “To me zan yi anan?” “Zama za kiyi kafin mu san abin yi, idan sauryin naki ya shirya auren sai na aurar da ke, ko ba shi da yarda zai ajiyeki sai na ba shi Aron nan, kafin ya samu inda zai ajiyeki.” A raunane ta d’ago tana dubansa kafin ta ce “Amma Yaya Hammad ba ni kad’ai zaka bari anan ba ko? Ka kawo min ko Kamla ce.” Tsaf ya tsaya ya k’are mata kallo kafin ya saki tsaki ya ce “Idan na sake jin kin kira ni da Yaya sai na murji bakinki, kuma ba Kamla zan kawo miki ba Kamlo zan kawo miki, ba kiji yarda mu kayi da uwarta bane, ko ke kurma ce ba ki ji mai uwarta ta ce ba, idan za ki shirya rayuwa ke kad’ai ki shirya na gaya miki.” Ya fad’a yana shigewa wani d’aki. Hamda ta bi bayansa da kallo hannayenta akan k’uncinta ta zabga uban tagumi, da gaske dukkan lamarinsa mamaki suke bata, shi kamar ma babu abinda yake damunsa daga bayyanuwar Sirrin nan..... Allah dai ya sa Zunnuraini ya shirya aurenta, ta samu zuciyarta da addu’a.


To sai mu ce Ameen.





Jikar Nashe ce..
[1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: ALK’ALAMIN JIKAR NASHE


YA ABIN YAKE?


BONUS PAGE 18


08033748387

✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽



Yau Didi jikin sosai ta mik’e idanunta sosai akan y’ay’anta da suka baibayeta zagaye da ita a gadon asibitin.
Gwaggonsu Amina ce har a lokacin ba ta iso daga Dubai, don ta ce musu tana hanya a cikin satin mai zuwa.

Didi so take ta yi musu maganar Hammad amma ba baki, sai da dabara ta fad’o mata sannan ta duni gadanga ta yi masa alamar ya samo mata abin rubutu. Shi kad’ai take wa fara’a bayan shi ko kallon arziki ba ta yiwa Abbu da Lauratu.

Gadanga ya fita zuwa motarsa, ya samo mata littafi sabo da biro yana jin dad’in yau za su San abinda yake ranta. Sam ya mance da wannan hanyar ta rubutu.

Yana komawa d’akin ya manna mata biro da takardar. Ta amsa sannan ta fara rubutun duk da dai ta fi ganewa Ajami amma haka ta dagura Hausar. Ina Hammad da Hamda? Shine abinda ta rubuta ta mik’awa Gadanga, ya yi tsai da ransa saboda bai San abinda zai ce mata ba, shi kansa bai ji dad’in hukuncin da Yayan nasu ya zartar be. Sai da ta sake tab’o shi ta tsatstsareshi da ido sannan ya saki ajiyar zuciya a hankali ya ce “Yaya ya kore su.” Didi ta mai da kallonta kan Abbu kafin ta mik’awa Gadanga hannu ya bata takardar da rubuta kalmomi guda uku ta mik’a masa “Ka yi gaggawar dawo da su, kafin na wa ran ya b’aci.” Daga haka ta mik’awa Gadanga takardar ta mayar da kanta Ta kwanta zuciyarta ce ta ke suya Idan ta tuna da lamarin.

Abbu kam Shiru yayi fuskarsa a d’aure saboda umarnin Didin ya zo masa a bazata. Sam ba ya jin zai iya yafewa Hammad wannan gungumemen laifin, ita kuma yarinyar da zarar ya cigaba da ganinta tsanarta ce zata dinga hauhawa a zuciyarsa. Sai dai ya san sarai ba shi da ja akan umarnin Didi musamman da ya lura ko son had’a ido da shi bata yi.

Ammi kuwa dama ba zuwa take ba, sabida tasirin idanun Didin a kanta yarda take k’in kula ta da banzan kallon da take mata dalilin kenan da yasa ta bi shawarar Kady aka kai Didin wajen malami ya d’aure mata baki, la’akari da duban da take mata ta san zata iya tona mata asiri. Shi yasa a daren ranar ta nemi shawarar Kady ita kuma ta bata shawarar a mannewa Didin baki, ba sai tana magana ba balle ta k’aryata Ta. Shi yasa Ammin take shan shatafinta ko bakomai ta cusawa Sadiya bak’in ciki goma da ashirin, dama ta tsaya mata a rai bata son ganinta burinta bak’in cikin Abin nan ya kashe su ita da Didin idan yaso ta mallaki gida ba wanda zai saka mata ido.


Budirinta take sosai, musamman na shirye-shiryen auren y’ay’anta Najma da Nasma, ba ta damu sam da halin da ahalin d’an borno suke ciki ba, cafkar naira take a wajen angwayen son ranta irin surikan da take so kenan, y’ay’anta su samu mazaje na kece raini ba ta damu da wa za su aura ba? Menene halayyarsa? Burinta kawai su samu Hamshak’an masu kud’i wanda suka ci suka tada kai ba matasan masu kud’i ba, shi yasa ba ta kyashin fitar da ko nawa ne akan y’ay’anta don tabbas ta san kwalliya zata biya kud’in sabulu.



******

Tsawon mintuna Ashirin yana zaune cikin motar yana jiran Hakimar tasa Nanna kenan, bai d’auka har a lokacin fushin take da shi ba da bai wahalar da kansa ya zo ba, da sai ya turo mata text ya ce mata jibi za su tafi. Dama yazo ne su fahimci juna ita kuma ta zauna ta na b’ata masa lokaci. A d’abiarsa shi mutum ne da ba ya son rainin hankalin y’a mace sam ba ya jura. Wa la Allah ko don ya taso da taurin zuciya tunda abin ya faru ya dainewa mata uzuri a rayuwarsa. Gani yake duk halinsu d’aya, shi yasa ko da aka ba shi zab’in aure ya ce su zab’a masa ko ma wacece ba shi da lokacin soyayya da y’a mace, shi yasa Sam fushin Nanna ba ya tasiri Akan sa. Sau tari da kanta zata yi fushin da kanta kuma zata sharewa kanta hawaye ta sauko ta zo tana neman sulhu a wajensa. Duka mata kud’in goro yake musu bai tab’a kallon mace ya ji yana sonta ko ya furta mata ba. duk da karakaina da matan suke a kansa da nuna masa soyayya baya jin komai a ransa game da su, shi yasa a yanzun yake mamakin kansa da har ya shiga hurumin Hamda yake tausaya mata, bai San dalili ba, ko don kasancewarta.... tsam ya yi da ransa yana cije leb’e kafin ya sauke ganinsa akan Nanna da take taku tamkar wahainiya duk don ta ja ra’ayinsa, Sai dai ta makaro don sau tari ko a b’angaren mu’amalar aure Nannan ce dai take kawo kanta gareshi ba dai shi ya nemeta ba. Ya lumshe ido bayan ya ja hucin ajiyar zuciya sannan ya danna button motar ta yi unlocking kanta, hakan ya Bawa Nanna damar shiga gaban motar, bayan ta sake d’aure fuskarta tamau,
Duk da gargad’in da Dida ta yi mata bata ji ba, burinta ta samu ta lallashe shi ya janye tafiyar da waccan bak’ar yarinyar da haka kawai ta ji ta tsaneta.

Murya a shak’e ya ce “Gaisuwar ma sai na rok’a?” Ta kuwa daddage ta cono baki kamar yarda k’ananun yara suke shi sai abin ma ya bashi dariya, amma ya gintse yana sake lalubo k’wayar idanunta ya ce “Me Yasa ba kya son zaman lafiya ne Nanna? Yarinyar nan fa ba ta da wani gata sai nawa idan na barta anan ina ki ke so ta jefa rayuwarta?” “Dida ta ce zata rik’eta.” Kai tsaye ta ba shi amsa. Shi kuwa yana murmushi ya shafi gefen kumatunsa ya ce “Akan me Dida zata rik’eta alhali nine mahaifinta kuma ina raye?” Wani abu ya tokare k’irjin Nanna ta d’ago a fisge tana kallonsa “Da gaske kenan ka amsa kai ne ka yi cikin nata? Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna. Don Allah to ya aka yi ka aikata wannan d’anyen Ai kin?” Still yana murmushin ya ce “A yarda labari ya bayyana kansa ance giya na sha ina cikin maye na kusanci uwarta...
Ya ja wani numfashi ya fesar da iskar bakinsa “Any way ba wannan ya kawo ni ba, ki zama ready jibi za mu wuce Birmingham kuma ki saka wa zuciyarki hak’urin Zama da ita don ta riga ta zama wani sashe na family na. Amma fa idan kina son zaman lafiya da ni.” Shiru tayi tama rasa abin cewa kafin ta saki wani malalacin murmushi ta girgiza kai “Idan kuma bana son zaman lafiya da kai fa?” “Ki wulak’antata” Direct ya bata amsa ba tare da ya ko kalleta ba. Nanna ta girgiza kai kawai tare da bud’e motar ta fice don tabbas idan ta cigaba da zama zata iya rusa masa kuka ita kuwa sam bata son ya ga karyewar zuciyarta. Ya je yayi ta tafiya da ita amma wallahi ita kanta yarinyar sai ta gudu da k’afafunta saboda izayar da zata dinga mata. Sam bata so yiwa y’ay’anta y’an uba ba Na halak ma balle wannan da ta zo ta haramtacciyar hanya.

Tana fita yana jan motarsa da mugun speed don kada ma ta saka ran zai bi ta ya lallasheta. Nanna ta ja sillan k’afafunta ta shige gida ita da kanta ta san bata da wani muhimmanci a wajensa, bai damu da ita ba.



_________________

Bai isa gidan ba sai da ya tsaya a wani mall ya siya mata kayan sawa don wanda tazo da su kala uku ne kacal kuma duk ta sakesu kullum wankewa ta ke ta Mayar, har underwears da kayan makeup duk Sai da ya siya mata.
Sannan ya samu wani trolley na zuba kaya mai kyau ya siya mata har da hand bag da shoes da turaruka, kaya dai fal masha Allah kamar me.


Tana rakub’e zaune kan kujerar parlourn tayi shiru hannayenta zube a kuncinta. Ta ji murd’a k’ofarsa sam bata firgita ba don ta San shine illa iyaka gyara zamanta da tayi had’e da saurin goge hawayen fuskarta, don bata mance gargad’insa na yau da safe ba. Ajiye kayan ya yi a tsakiyar parlourn yana amsa sannu da zuwan da take masa.

Direct d’aki ya wuce inda ya ke kwana kafin ya fito fes da shi cikin jallabiya mai gajeren hannu sai zabga k’amshin turaren HuGO BOSS Yake.

Kayan ya duba kafin ya ce “Kika kasa bud’ewa ki ga ko menene?” “Wannan ne a gabanka” ta samu kanta da furtawa a zuciyarta. “Na samu wancan saurayin naki ba yarda ban yi da shi ba ya amince ayi Aurenku ya tabbatar min bai shirya ba, har ce masa na yi sadaki kawai zai bayar amma ya k’i. Don haka ki k’addara a ranki dama ba mijinki bane. Na yanke shawarar da zarar mun je can idan kin kafe auren kike so akwai abokina Jamal mazaunin can sai na ba shi aurenki.” Idanu ta zuba masa kafin ta d’auke kai murya a sark’e ta ce “Ni ban ce aure nake so ba, na yi karatun Kawai.” Dole ki yi aure don idan ba aure kika yi ba Nanna ba zata barki ki zauna lafiya a gidanta ba. Ki Zama ready kuma jibi zamu wuce umarni ne kuma ba shawara ba. idan kuma kin ga ba zaki bi ni ba, kina da inda ya fini to ki gaya min na baki kud’in mota.” Shiru ta yi masa kamar ta ce eeh ba zata bi shi ba, amma da gaske bata da wanda ya fishi tunda an ce shine mahaifinta.



____________

Ranar da za su tafi tun wuri ta shirya tsaf cikin kammalalliyar shiga ta doguwar riga samfurin k’asar egypt. Kalar sea blue mai adon baby pink hakan yasa ta nad’e kanta da mayafin ruwan hoda. Ba k’aramin kyau ta yi ba duk da kasancewarta mai duhun kala hakan bai b’oye zahirin kyan fuskarta ba, dirarren jikinta ya bayyana a cikin rigar. Ta zura tattausan takalmi a k’afarta kalar pink. Ta bi jikinta ta feshe da turaren Almukhalad’ bayan ta shafa body mist na kamfanin oud. Sanda ta ji knocking d’insa sannan taja kyakykyawar trolley d’inta.


Tsam yayi da ransa yana k’are mata kallo shi kansa bai lura da yarda ya tsatstsareta da ido ba, har Sai da ya ji muryarta tana cewa “Ya Hammad ina kwana?” Tsaki ya ja kafin ya ce “Lafiya lau, sunan nan ba zai fita daga bakinki ba ko?” Sunkuyar da kanta kawai ta yi don bata jure wa kallonsa musamman idan ya kafeta da idanunsa. Bai sake magana ba ya juya ya fice janye da tasa trolley d’in, ita ma ta bi bayansa, tana mamakin yarda gabanta ya ke tsananta fad’uwa a duk sanda suke tare ko ta shak’i daddad’an k’amshin turarensa.

A motar ma kasa nutsuwa ta yi, ta shiga danna wayarta tana game, har suka isa k’ofar gidan su Nanna sai sannan ya yi magana bayan ya rage sautin karatun Alk’uranin da yake ji “Ki shiga ki ce su fito, mun kusa makara kada mu yi missing flight.” A diririce ta shiga kallonsa shi kuwa bai sake magana ba illa cigaba da waya da wanda zai karb’i motarsa da ya yi, yana sanar da shi su had’e a airport.

Zuciyarta na rawa ta bud’e motar ta fito. Sarai ta san gidan su Nanna don ba wannan bane karan ta na farko a zuwa, sun sha zuwa da Didi biki ko suna ko gaisuwar mutuwa.


Tun daga waje ta fara sallama, tsoron Nanna ne fal a ranta, yanayin masifarta yana razanar da ita. Tsaf ta lura Nanna mafad’aciya ce ta gaske. Sab’anin mahaifiyarta Dida da ta kasance mai sauk’in hali.


Tura k’ofar ya yi dai-dai da fitowar Nanna daga d’aki, fuskarta a cukurkud’e da alama nasihar da Dida ta yi mata ce ta tunzira Mata zuciya ban da abin Nanna ai gaskiya Dida ta gaya mata d’a dai na kowa ne, kuma duk wanda ya haihu ba halin k’warai bane gareshi ya wulak’anta zuri’ar wani, musamman tunda bai tara sani ga Allah ba balle ya san shi ba zai iya jarrabarsa da abinda ya jarrabi wani sashi daga cikin al’umma ba ki yi nazari da kyau Nanna duniya juyi-juyi ce, idan kin rik’e nasihata za ta amfaneki zubar da ita kuwa zai iya zama da na sani a gareki. Ta mik’e ta fito ba tare da amincewa da shawarar mahaifiyar tata ba.

Kicib’us d’in da suka yi a bazata yasa zuciyar Kowannensu ta d’auke wuta na tsawon d’akikai, kafin Nanna ta zabga mata harara ta kuma k’i amsa gaisuwar da take ta jera mata muryarta na rawa. Da gudu Kamla ta zo ta rungumeta a fusace Nanna ta janye ta had’e da jan kunnenta da k’arfi “Last warning da zan miki shine ba ke ba y’ay’ana.....Saboda ni y’ay’ana tsarkakkune da aka haifesu da aure ke kuwa kwamacalar da take kan ki kad’ai ta isa a guje ki, bayan kasancewarki shegiya...” wata irin gigitacciyar tsawa Dida ta sakar mata fuskarta d’auke da b’acin rai ta kalli Khairi “Je ki kira mun Babanku a mota yau da kaina zan ba shi umarnin ya saketa tunda ba ta jin maganata..”
[1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: ALK’ALAMIN JIKAR NASHE


YA ABIN YAKE?


BONUS PAGE 19...

08033748387

✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽

Nanna jiki na rawa take kallon Dida da nufin bata hak’uri, sai dai Didan ko kallonta ba tayi ba, saboda ranta ba k’aramin b’aci ya yi ba, Ta rasa wace irin k’wakwalwa ce da Nanna sam albasa ba tayi halin ruwa ba.

Ko da Khairi ta sanar masa da sauri ya fito daga motar duk zatonsa Nannan wani mugun abu tayi wa Hamda, tabbas yau da ta gane Kurenta.

Turus ya yi a bakin k’ofar falon Didan ganin Hamdan lafiya lau take. Cikin sakin fuska Dida ta ce ya shigo ya zauna. Kamar ba zai shiga ba sai kuma ya daure ya saka kai ya shiga.

Bayan amsa gaisuwarsa Dida ta ce “Gata nan Hammad tunda ba taji duk shawarar da na bata game da ta hak’ura ta rik’e yarinyar nan, ka saketa kawai saboda idan ka tafi da ita ba k’aramin tashin hankali zata sakawa zuciyarka ba. D’agowa ya yi idanunsa cikin na Nannan yana mamakin yarda gaba d’aya ta sauya kyawawan d’abiun da ya santa da su. Tsaki kawai ya ja kafin a hankali cikin ladabi ya ce “Ki rabu da ita Dida, kada ma ki sawa zuciyarki b’acin ranta. Da zarar mun je can zan yi solving d’in abin ba dai yarinyar ce bata son gani ba, to muna zuwa zan aurar da ita ta tare a gidanta.” Dida ta saki tsakin takaici “Bata isa ba wallahi, kai da gidanka kana da ikon kawo duk wanda kake son ya zauna tare da kai, sai dai ita ta bar gidan.” Agogo ya kalla murya a cunkushe ya ce “Ki yi hak’uri, ya zame mata tilas ma ta gyara,
Yanzu za mu wuce kada mu yi missing flight.” “Shikkenan Hammad Allah ya tsare ya baka ikon sauke nauyin da yake kanka.” Har bakin k’ofa ta raka su, tana sake jan kunnen Nanna cikin nasiha da lallashi. Jikinta dai ya yi sanyi a zahiri amma a bad’inance ita kad’ai ta san takaicin da yake nuk’urk’usarta.




______________________

A tsorace Hamda take sosai a cikin jirgin, musamman kasancewar wannan shine first flight d’in ta. Duk ta bi ta takure kanta ta kasa sukuni, yana lura da duk wani motsinta shi yasa ya ce Khairi ta koma kusa da ita. Khairi kuwa ta murje idonta ta koma duk da hararar k’asan ido da Mommynta take zabga mata.


Tun tana tsoro har ta saki jikinta ta zauna ganin tafiyar ba nan kusa bace. Abincin jirgin ne dai sam ta kasa ci saboda aman da take ji, kuma ma yanayin abicin nasu bai yi mata ba.



Kusan asuba suka sauka a k’asar ta England cikin birnin Birmingham, sam ba tayi tunanin garin da sanyi har haka ba shi yasa bata tanadi rigar sanyi ba, shima kuma bai yi azancin siyo mata rigar sanyin ba. Sosai ta dinga rawar d’ari hak’oranta na kafkaf kamar za su datse harshenta. Samun kansa ya yi kawai da zare jibgegiyar rigar sanyin da take jikinsa ya mik’a mata. Hannu na rawa ta damk’i rigar ta saka. Tana jin nutsuwa na sauka a ranta. Tsaki Nanna ta ja a fili tana mamakin dalilinsa na kaffa-kaffa da yarinyar har da wani cire rigarsa ya bata, bayan ta san shi da matuk’ar jin sanyi. Bai damu da kallon da take wurga masa ba yayi gaba cikin takunsa na k’asaita.



K’arfe 8:00 daidai suka isa bakin gidan su. Ya saka mukulli ya bud’e y’ar madaidaiciyar k’ofa. Gidan na nan tsaf da shi kasancewar yayi wa mai hidimar gidan waya tun shekaranjiya shi yasa ya gyara gidan tas. Sai zabga k’amshi yake. Ta samu kujera ta rab’e ganin ba wanda ya bi ta kanta. Hannayenta zube a k’uncinta tana mamakin yarda rayuwa take juyin waina da ita. Dubi dai yarda lamarin ubangiji yake ikonsa a kanta ko a mafarki ba ta tab’a zatan zuwa k’asar nan ba, sai ga shi Allah ya kawota. Sai dai rashin sanin irin rayuwar da zata yi ne yake fad’ar mata da gaba daga yanayin matar gidan ta fuskanci k’warai ba tayi na’am da zamowarta cikin gidanta ba.


Ita kuwa Khairi suna shiga d’aki Nanna ta saka su a gaba da jan kunne, ko da wasa ku ka shiga sabgar shegiyar y’ar can wallahi sai na ci mutuncinku. Kamla idonta ya kawo ruwa sam bata son Mom take hanata huld’a da Hamda, saboda tana son ta sosai. Hakan yasa dole Khairi ta zauna ba tare da ta kira Hamdan sun shiga d’aki ba.


Har ya watsa ruwa ya kwanta don
Ya huta, sai ya tuna da ita ya san bai zama lallai Nanna ta kaita masauki ba, ba ma wannan ba yana lura da ita a jirgi ba wani abincin kirki ta ci ba. Don haka ya mik’e da sauri ya fita. Hasashensa kuwa ya zama gaskiya don tana rakab’e a kujera ta lula duniyar barci ita kad’ai ce a parlourn kamar mayya, ta takure jikinta da alama sanyi take ji sosai.

Hannu yasa ya d’an buga bayanta da sauri ta mik’e a d’an firgice idanunta sun yi nauyi saboda barcin da yake cikinsu. “Me yasa baki shiga d’aki ba?” Ta ware idonta kafin ta ce “Ba’a nuna min d’akinba ai.” Tsaki ya ja ya mik’e hannunsa jaye da trolley d’inta ya ce “Biyo ni.” Murd’a d’akin su Khairi ya yi ga mamakinsa sai ya ji shi a kulle abinda ba a yi kenan rufe d’aki a gidan ko menene dalilin hakan. Ya shiga Knocking k’ofar da d’an k’arfi. Cikin barci Khairi ta farka tana fad’in “Waye?” “Bud’e” ta ji muryar Daddynta, hannu ta sa ta murd’a sai ta ji d’akin is locked sai sannan ta tuna Mommynsu ce ta gark’ame d’akin duk don kada Hamda ta shigo. Murya a tsorace ta ce “Daddy Mom ce ta rufe da key.” Da k’arfi ya ce “For What reason?” Jikin Khairi ya soma rawa don sam bata son tashin hankali a rayuwarta ga shi ta ji Daddy kamar ransa ya yi mugun b’aci, ta kasa cewa komai sai zare ido take. Da sauri Hammad ya juya ga Hamda kawai ya sake ce mata biyo ni.”

Direct d’akinsa ya wuce da ita, dole ne ma ya yi maganin Nanna. Ya bud’e wardrobe ya d’au abinda zai buk’ata ya kalleta “Zauna anan kafin na gyara miki wancan d’akin.” Ta bi d’akin da kallo had’uwa da tsaruwar d’akin kad’ai ya isa ya burgeka balle yarda d’akin ya rik’e turarensa k’am tamkar anan ake had’a samfurin turaren kafin ta yi magana ya fice daga bedroom d’in nasa. Ta bi bayansa da kallo kafin ta sauke wata sassauk’ar ajiyar zuciya. Da zata iya kwanciya za tayi kawai amma ta fi so ta watsa ruwa tukun. Don haka direct ta fad’a had’adden toilet d’in nasa.


Shi kuwa yana fita d’akin Nanna ya wuce direct, Fuskarsa a had’e sosai. Ya tura k’ofar ya shiga. Nannan tana zaune gaban dressing mirror ta na shafa mai ta ganshi ya shigo da kaya a hannunsa ya zube kan gado. Sannan ya hau gadon ya yi kwanciyarsa ba tare da yayi mata magana ba. Cikin mamaki take kallonsa “Ban gane ba Yallab’ai, ina naka d’akin?” Ba tare da ya kalleta ba ya ce “Yana wajen Hamda.” Da sauri ta mik’e har towel d’inta yana shirin zamewa ta ce “Wani irin abu ne wannan zaka d’au master bedroom ka bata alhali akwai guest room.” Ya d’ago yana tsatstsareta da ido da tilas ya sata risnar da nata idon “Na fiki sanin da guest room d’in na bata nawan. Saboda ita ba guest ba ce yarda kike tak’ama da gidan nan itama

Please Login or Register in order to submit comment