Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

y’arta ba ta barin kowa ya d’auketa. Kullum rayuwarsu suke yi a d’aki. Ko Na aika nace ta bani yayarku Najwa sai ta hana,
Har na hak’ura na tattara ta na zubar.



Ranar suna yaro yaci sunan kakanku muna kiransa Hammad shine a can k’asar waje sanda ya tafi baki fi shekara hud’u ba har yau kuma baiyi sha’awar dawowa ba.


Ko shekara ba suyi da komawa ba suka dawo Nigeria gaba d’aya, don lokacin ubanku arziki ya zauna masa har ya siyi gida Anan cutar da Malam yake yi ya buk’aci ya dawo ya fara kula da k’annensa don ya tabbatat ciwon ajali yakeyi.



Kamar yarda Sadiya take da tsohon ciki, wannan karan ma Sakina cikin ne da ita sai dai nata karami ne.


Ranar da Sadiya take nak’uda na lura Sakina a k’age take taga abinda Sadiyar zata haifa, don dama kaf nice nake karb’ar haihuwarsu. Abin ikon Allah sai ga Sadiya ta haifi santalelen yaro wannan karan ma namiji.


Sakina kuma da ta tashi haihuwa itama ni na karb’i haihuwarta sai ga shi ta haifi mace._
[1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: _~ALƘALAMIN JIKAR NASHE


YA ABIN YAKE ?

LIttafin Nazeefah Nashe.

08033748387




Follow me on wattpad

Nazeefah381



ELEGANT ONLINE WRITERS

(Haɗin kai shine takenmu.)





********************************

Hankalinta a tashe take duban yarinyar kafin ta ce “Wannan karan ma Mace ce?”

Ina murmushi na amsa mata Macece kyakykyawa kuwa har tafi Najwa kyau.” Wani tsaki tayi, kafin k’wallar da ta taru a idonta ta zubo mata cikin muryar kukan ta ce “Ya Allah yaushe Zaka cika min burin da na dad’e ina fata.”

Da sauri na janyo ista’aza raina a b’ace na ce “Sakina me kenan? Shin ba zaki godewa Allah ba da ya baki kyautar yara matan? ki kuma yi addu’a Allah yasa su zame miki sanyin Idaniya.”

Hawayen fuskarta ta d’auke kafin Ta ce “Ni ban ta’ba son haihuwar mace ba, kullum burina da tunanina a haihuwar yara maza yake, sai gashi Sadiya tana samu ni ban samu ba.”

A zafafe nace Allah ne yaso ya jarrabeki, sai kiyi ta istigfari, da kika samuma kike haihuwar wasu suna can suna rok’on Allah ya basu yaran ma kowane jinsi ne amma bai basu ba, Sai ke da kika samu har kike k’ok’arin tantance jinsin da kike so, ki tuba ga Allah kafin yayi fushi dake.”

Na mik’a mata yarinyar ta karb’eta cikin halin ko in kula sai kuma ta saki d’an murmushi ba mamaki na ganin yarinyar kyakykywar gaske ce.




____________________________________ Bayan sunan yarinyarta ta biyu da sati biyu Najma Allah ya karb’i ran Malam bayan ya sha doguwar jinya, tabbas mun shiga alhini da tashin hankali kuma mutuwar ta shiga jikin mu sosai bare ni da nake ganin mutuwar tasa ni aka yiwa. Haka Rabbi yake baya barin wani don wani yaji dad’i.


A tsukun lokacin bayan na fita daga takaba mahaifinki ya kammala wannan ginin da muke ciki Muka tattara muka dawo, cikin birnin Kano.


Anan aka yi bikin Lauratu da Gadanga da ya auri k’anwar Sadiya Murjanatu.

Anan kuma iyayenki suka ta hayayyafa har zuwa sanda aka zo kan cikinki, Sakina ta dinga murna da fallasuwar cikin, mu dai bamu san dalili ba.


Wata rana taje asibiti ta dawo sai gata ta shigo d’akina da sauri ta zauna a saman kujera takarda a hannunta tana ta jifan Yayanku Hammad da murmushi, wanda bamu san dalilin da yasa ya tsaneta ba, duk da a lokacin bai zarce shekaru sha tara ba, yaro ne shi mai Kazar-kazar da fara’a ga son mutane amma tashi d’aya gaba d’aya halayensa suka canja ya zama mafad’aci, miskili da son kad’aicewa shi kad’ai ba kuma ya san ganin matar Babanku,
Ko me yake da zarar ya ganta yake barin wajen.

Kamar a tsorace yake da ita. Kuma tambayar duniya an masa ya ce “Bakomai” Ganin lamarin nasa kamar ya fara girmama Babanku ya tasa shi a gaba akan lallai sai ya fad’i dalilinsa, take ya sanar dashi son fita waje karatu aka ce ya zab’i k’asar da yake so ya ce “Birmingham” dake can a k’asar England.
Nan kuwa aka fara yi masa shirye-shiryen tafiya wajen.


Da murmushin ta mik’o min takarda tana cewa “Didi Burina zai cika, wannan karan cikin namiji nake d’auke da shi, bayan na k’i haihuwa har shekaru biyar saboda ina tsoron sake haihuwar mace sai gashi Allah ya cika min burina a wannan karan namiji zan haifa.” Ta fad’a idanunta cikin na Hammad, gani kawai nayi ya mik’e da sauri ya fice daga sashen nawa.

Nima cikin murna nace mata “Masha Allah, abin Allah kenan da har kina cewa kin daina haihuwar?”

Da murna ta mik’e ta fice ni kuma na bi bayanta ina taajjibin lamarinta.



Duk cikun-cikun da akayi na son Hammad ya tafi karatu Allah bai yi ba, sai da aka ja lokaci. A tsukun wannan lokacin ina hankalce da shi tsana mai tsanani ta shiga tsakaninsa da mahaifiyarki sam baya son ganinta. Sau tari na sha kama shi yana kuka amma tambayr duniya sai ya ce “Bakomai.” Har raina ya b’aci na tattara lamarinsa na watsar.


Cikin Sakina ya isa haihuwa, ta fara d’igimi da shirye-shirye, d’aki guda ta ware a b’angarenta aka zuba kayan yara maza, komai fari da kalar shud’i, kalar maza kenan a lokacin naji suna fad’a. Duk wani tattalin arzikin Sakina akan cikin nan ta k’arar dashi, har shirin Suna duk tayi.

Wannan karan ma, cikin dare ta fara nak’uda aka kira likita, da ni da likitar muka karb’i haihuwarta.


Tun da tayi nishi ko zafin nak’udar bata ji ba ta zuba ido tana son ganin mai ta haifa.

Nice Na zaro ki, gabana ya fad’i ganin dai wannan karan ma an kuma macece ta haifi mace, tun kafin a yanke cibiya Sakina ta cire kunyarta, cikin gwarancin hausarta take cewa na mik’o mata shi ta ganshi, gaba na ya dinga luguden daka ganin mace ce ban san kalar haukan da zata yi ba idan ta ganki, ban da kasancewarki mace duk a yaran da take haifa ke kika zo da duhun kala. Murmushin yak’e Na saki.

“Bari ki shirya a tsanake sai ki ga babyn, ki shiga ki gasa jikinki tukunna, Ai ba gudu ake ba.”

Bata min musu ba, ta mik’e ta shige toilet, ni kuma na fice da jaririyar nayi mata wanka tas a falo. Na sink’eta cikin kayan sanyi burina ta bata Nono a karan farko kafin ta san abinda ta haifa. Zai ma yi wuya na gaya mata yau.



A bakin gado na tarar da ita, tayi kyau sosai cikin shigar atamfarta England y’ar Ghana. Na mik’a mata Babyn bata kawo komai a ranta ba ta fidda wankakken Mamanta ta bata ta sha sosai ba tare da sanin me ta haifa ba.

Likitar naja gefe nace ta ja bakinta tayi shiru kada ta sanar da ita.


Amma me? Cikin talatainin dare na dinga jin wani irin bugu kamar za’a jijjige min k’ofa a razane na farka ina fad’in wanene?” Muryarta a shak’e ta ce “Ni ce” Na bud’e k’ofar gabana na fad’uwa ina fad’in Sakina Lafiya?” Duk da Na San dawar garin. Mik’o min jaririyar tayi fuskarta a had’e ta ce “Wallahi, ba zan shayar da ita ba, wallahi asiri aka yi min kuma bani da haufi Sadiya ce tasa matsafa suka canja min yaro na, namiji aka nuna min har a scanning a mafarkina kuma namiji na gani.”

Tsananin mamaki yasa na kasa ce mata komai sai karb’ar yarinyar da take shirin yar da ita nayi, ko pampers babu a jikin yarinyar sai tsala ihu take.



Raina a b’ace nace “Yanzu Sakina wannan wani shirme ne? A darennnan zaki kawo min yarinya ya kike so nayi da ita? Ina da abin bata ne? Kina ganin tana Kuka.”


“Wallahi sai dai ta mutu, in dai da Nono na zata rayu wanda na bata ma don ban san mace bace.”

Daga haka ta juya a fusace ta shige sashenta, duk da kiran da nake k’wala mata amma tayi burus dani.

Tilas na juya da ke cikin d’akina, Na jik’a dabinon ajwa a ruwan zamzam shi na dinga baki har aka wayi gari.


Da Asuba Babanku ya shigo b’angarena kamar yarda ya saba shigowa duk asuba.

Mamakine ya kamashi gani na da yarinya a zaune na zuba uban tagumi. Hankalinsa a tashe ya dinga tambayata “Lafiya?” Na ja ajiyar numfashi idanu na cike da kwalla Na fara gyara zama ina Bahijja
labarin abinda ake ciki, Salati ya saka. Dai-dai lokacin da Hammad ya shigo, Babanku ya mik’a masa yarinyar ya ce “Karb’eta kaje falo ina fitowa.” Wata irin zabura yayi yaja baya yana girgiza Kai, kamar yaga abin tsoro sai kuma ya fice da sauri cikin tsananin b’acin rai.

Mamaki ya kama mu ni da Babanku, sai dai ya girgiza kai ya fice da yarinyar a hannunsa.

Dambarwar tsiya aka kwasa, tsakaninta da shi akan sai ta shayar dake amma ta k’ek’asa k’asa ta ce sam ba zata yarda ba sai dai ya saketa.

Ganin lamarin ya ta’azzara yasa naje nace ya fice na karb’i yarinyar da zummar na bawa Sadiya da ta nuna tana sha’awar rik’eki, amma nan ma ta k’ek’asa k’asa Ta ce bata amince a bawa Sadiya ke ba, ta karb’eki a hannuna sai dai sam ta k’i yarda Ta shayar dake sai dai madara haka kika tashi a gantale wajen y’an aiki, wani lokacin na karb’oki wani lokacin ta bani haushi na k’yaleki.


A tsukun lokaci abin Hammad ya ta’azzara dole aka sadashi da asibiti nan ya fara ganin likita, aka d’ora shi kan magani muka samu ya samu lafiya ya tattara ya tafi karatu.


Bai sake waiwayar garin ba sai bayan shekara hud’u lokacin da ya dawo sai kuma yazo da sabon salo ya dinga janki a jiki, yana nuna miki Soyayya da kulawa, kuma ko Uwar da ta kawo ki duniya ma bata isa ta dokeki ba matuk’ar yana wajen, sai muka lura a lokacin ma kamar wani shakkarsa da tsoronsa take ji.


Bana manta wata rana kin dawo daga Islamiyya baki fi shekara biyar ba shi kuwa a lokacin shekararsa ashirin da hud’u,kika yiwa Amminku laifi ko sugar kika zubar mata ta dinga jibgarki sai ga shi Allah ya kawo shi, ya dawo daga companyn mahaifinku da yake tab’a aiki a can, yana ganinki kina kuka yaja hannunki, kuka nufi wajen da take ya shiga surfa mata masifa abin har mamaki ya dinga bamu ganin yarda yake surfeta da masifa amma tayi shiru har ya gaji ya tafi.


Shine fa bayan kwana biyu ya gama shirinsa, sai gashi yaje Gwarzo yake gaya min zai koma Birmingham, hankalina ya tashi nace bai isa ba ya bari a masa aure.

Girgiza kai yayi ya ce “Ba zan iya k’ara ko kwana guda ba akan jibin da zan tafi idan kun shirya auren ku samo min matar a d’aura auren zan mata visa aka kawo min ita ina maraba da zab’inku ko wacece.

Shine fa muka sama masa Nanna y’ar yar Babarsa, aka yi auren aka tura masa ita.

shi kam bai sake dawowa ba amma ita Nanna tana zuwa hutu duk K’arshen shekara yaranne dai baya bari tazo dasu saboda makaranta.



Wannan shine abinda na sani na dangane da labarinki da dalilin tsanar mahaifiyarki gareki, a zahiri dai wannan shine bamu san bad’ininta ba, sai ki cigaba da hak’uri har Allah ya nuna mata ikonsa a kanki ba mamaki kece wacce zata zo tayi alfahari da ita nan gaba kad’an ki zame mata Sanyin idaniya.”



Tuni hawaye ya gama b’ata mata fuska, a yau ta tabbatar ba laifin da tayiwa mahaifiyarta laifinta d’aya da tazo a jinsin Mace, menene laifinta anan? Me yasa kuma bata tsani sauran y’ay’anta ba sai ita? Ko don ita bak’a ce? Tabbas hakane aka amsa mata daga can k’asan zuciyarta, ya zama lallai ta nemawa kanta mafita kafin ciwon damuwa (Depression) ya kamata.
[1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: _~ALƘALAMIN JIKAR NASHE


YA ABIN YAKE ?

LIttafin Nazeefah Nashe.

08033748387




Follow me on wattpad

Nazeefah381



ELEGANT ONLINE WRITERS











**********************************

BIRMINGHAM


Dake k’asar England.

Unguwar padstow Road Birmingham B24.


A cikin d’aya daga cikin gidajen rent d’in masu bala’in kyau. Gida ne mai d’auke da 3 bedrooms da 1 parlour sai kitchen da dinning area.


Kamar yarda aka san gine-ginen turawa wannan ma gini ne da yake d’auke da tsari, da zarar ka kalleshi tun a waje zai birgeka balle idan ka shiga cikin ainahin building d’in.


Nanna ce zaune gefe guda da waya a hannunta tana kuka sosai bayan samun sak’on mutuwar Babanta.


Ta sake kallon Hammad mijinta a karo na biyu kafin ta ce “Kayi wa darajar girman Allah ka bini mu tafi tare har yarannan, yanzu fa Khairi shekararta Sha d’aya amma bata san danginka ba balle nawa, sannan yanzu ma Baba na ya mutu kace ba zaka ba, wannan wace irin masifa ce wai me aka yi maka a Nigeria?” Ta fad’i furicin hawayen na sake kwarara a fuskarta na zallar b’acin ran mijin nata wanda wani lokacin idan ya rikid’e mata sai ya zama kamar bak’in kumurci don fad’a da b’acin rai, wani lokacin kuma suyi zamansu gwanin sha’awa.


Wannan karan ma ya rikid’e d’in, don runannun idanunsa ya d’ago ya zuba su a kanta, wanda ya sata had’iye kukan babu shiri. Tayi saurin mik’ewa zata shige d’aki da azama ya fincikota, rintse idanunta tayi tana jiran taji saukar mari kamar yarda ya saba a duk sanda ta kawo masa zancen zuwan Sa Nigeria.

Madadin marin wannan karan hankad’ata kawai ya yi ya mik’e da sauri ya shige bedroom d’insa ya kulle k’ofar har da murza key.


Nanna ta runtse idanunta, don ta San tabbas abinnasa yazo, idan abin ya tashi zame mata yake kamar mahaukaci, sai kace mai aljannu. A hankali furucin Ya Allah ya fito daga bakinta.

Ba zata bishi ba don ta san ko zata shekara tana bugu ba zai bud’e ba a wannan bad condition d’in da yake. Allah ma ya taimaka yau baya zuwa aiki da bata san yarda zata yi da shi ba.


Wayarta ta shiga lalube ta fara danna kiran Mahmah, gwara ta gaya mata tayi iya yinta ya ce Ba zai zo ba.

Bugu biyu Mahmah ta d’au wayar, dafatan Allah yasa surukartata taci nasarar shawo mata kan d’annata. Madadin daddad’an labarin sab’anin haka ta samu. Mahmah ta runtse ido zuciyarta na karyewa bata san dalilin yaronta Na rashin son zuwa inda suke ba, ko su suke son ganinsa sai dai yayi Musu Visa suyi tattaki su je. Gashi wannan karan Didi ta takura ta gaya musu dole su saka Hammad d’in yazo gida musamman da surikinsa ya mutu.

Ta ja aijyar zuciya kafin ta ce “Shikkenan, ki kyaleshi zuwa anjima zan kira shi, dama har yanzu yana shiga wannan condition d’in?”

Nanna ta ja ajiyar zuciya kafin ta saki kuka na nuna alamun zallar damuwa ta ce “In dai zan masa zancen da ya shafi Nigeria sai yayi.” Mahmah tayi jim kafin ta ce “Kin ga kuwa dole yazo ko dan na nema masa Magani, zuwa yanzu kam na tabbata ba k’alau tabbas akwai wani k’ulli da Allah ne kad’ai ya barwa kansa sani.”

Daga haka suka yi sallama, Mahmah ta lalubi numberr Hammad ta tura masa text.

Slm.
Ya zama dole ka taho Nigeria a wannan gab’ar idan ba so kake na bayyana maka b’acin rai na ba ta hanyar sallamaka a cikin zuri’ata.



Daga haka ta ajiye wayar, ta jingina kanta jikin kujera wannan karan zuciyarta ta kasa sukuni har sai da ta zubar da wasu tarin ruwan hawaye. Rashin gane takamaimai matsalar d’annata abin yana ci mata tuwo a k’warya kullu yaumin da abin take kwana ta tashi kuma, don dai ta kasance mace mai juriya ba kasafai take bari b’acin rai ya bayyana k’uru-k’uru a fuskarta ba.

Ta haddaci k’unshe b’acin rai tun farkon aurenta da mijinta, da ta tabbatar ba sonta yake ba yana zaune da ita ne kawai don itace zab’in Didi mahaifiyarsa, amma soyayyarsa kam tana ga Sakinah Balarabiya da soyayarta yake kwana yake tashi sau tari ya sha kiran sunan Sakina a cikin barcinsa ko a yayin da suke saduwar aure. Duk ta danne take zaune da shi da zuciya d’aya, ta kowane hali kuma burinta yi masa biyayya ko ta samu rahmar ubangiji tunda dai shi yayi umarni abi su.

Ta share hawayen da ya zubo mata a fili ya furta YA ALLAH ka kawo mana d’auki akan bawannan naka ka sanyaya zuciyarsa ka dawo min da hankalinsa gida.


____________________________________


Farkawarsa daga nauyayyen barcin da ya sureshi yaci karo da sak’on mahaifiyarsa. Zuciyarsa ce ta buga ya tabbata yau Mahmah fushinta ya kai mak’ura, don bata tab’a nuna masa b’acin ran wanzuwarsa a Birmingham ba sai yau. Shi kuwa ya tabbata idan yaje Nigeria ya sake ganin yarinyar nan ba abin mamaki bane zuciyarsa ta buga. Shi a nasa tsarin yayi sallama da k’asar sa ta haihuwa babu abinda zai sake mayar da shi. Me yasa Mahmah zata yi masa wannan furucin bata san zamansa anan shine kwanciyar hankalin kowa a zuri’arsu ba. Cikin wani irin yanayi ya murza goshinsa tare da furta Oh Allah.


Ya sake duba agogonsa sai yaga har lokacin dawowar yara tuni ya shige ya tabbata zuwa lokacin Nanna ta d’aukosu.


Wanka yayi kafin ya fita parlourn.
duk da zuciyarsa a tunzire take bai hanashi shafa kan yaran nasa ba da suke zaune suna buga ps game a tv. Idanunsa akan Yarinyarsa ta biyu Kamla, yana mamakin sake bayyanar kamatarta da waccan yarinyar Hamda da gaske suna kama sosai yarda take black beauty haka Kamla take da eye shape da mouth d’insu duk d’aya.

Cikin k’udirar Ubangiji sam ba banbanci a zubin a halittarsu, ba zai mance kamannin k’anwar tasa ba a idanunsa. Da sauri ya rik’e kansa yana tuhumar kansa da zamantowarta k’anwar tasa a zahiri take k’anwarsa amma a bad’ini shi da uwarta sun san sai dai su kira ta........
Ya runtse idanunsa baya son tuna matsayin yarinyar, abu ne da zai iya kiransa direct ABIN KUNYA da Allah Wadai.


Murmushi ya sakarwa Nanna da take tsaye da cup d’in coffee tea a hannunta tana mik’a masa, duk da ranta a b’ace yake kuma idanunta sun nuna ta sha kuka bata fasa kyautata masa a kowanne yanayi yake. Da gaske Nanna ta cancanci kansa tsaye ya kira ta da suna MACE TA GARI. Ta kowanne fanni ta cika ta tumbatsa bata da makusa ko kad’an.

Hannunta ya ja ya zaunar a gefensa bayan ya lura hankalin yaran su yana kan t.v game, don duk kasancewar suna rayuwar turai suna matuk’ar jajircewa wajen tarbiyyar yaransu.

Ya rungumota jikinsa sosai, kafin a kunne ya rad’a mata “Am very much sorry, zamu wuce Nigeria within this week Allah yaji k’an Baba.” Wani irin tsalle tayi tare da rugumeshi, wanda har sai da yaja hankalin yaransu. Abul khair ya ware ido yana furta What?” Nanna ta jashi jikinta had’e da cewa “Uban masu gida zamu je Nigeria k’asar da kuke son zuwa gashi har Babana ya mutu bai sanku ba.” Da Hausa tayi masa maganar kasancewar sosai suke musu Hausa shi yasa yaran suka iya yaren Hausa tunda nan ne asalinsu da tushensu.

Yaran ma sosai suka shiga murna
Musamman Khairi da burinta dama taje Nigeria. A ranar ya fara nema musu booking flight kafin kashegari yaje ma’aikatarsu ta Miller Hughes construction Building contractor ya sanar musu yana buk’atar d’aukan hutu. Bai sha wahala ba wajen amincewarsu musamman sani ba tab’a nema yayi ba.

Daga nan ya tafi makarantar yaransa Junior league of Birmingham sunshine school suma ya fad’a musu, suma suka nuna masa bakomai zasu bawa yaran kayan karatun da zasu dinga yi kafin su dawo.


Shikkenan suka fara shirye-shirye yayi waya ya sanar da Mahmah da Abbu zuwansu in the next four days. Gaba d’aya gidan murna aka d’auka na zuwan Babban Yaya.



_____________________________


Gefe guda kuwa Sakina hankalinta a tashe yake da zuwan nasa, a zuciyarta ba sak’e-sak’en da ba tayi ba, wato bai ji abinda tace masa ba akan sake dawowarsa Nigeria shine zai sake dawowa, sam bata san wanzuwarsa a gidan gudun bankad’uwar sirrinsu. Shi yasa ma take ta bankawa Malamai kud’i akan a cire masa son gida gaba d’aya a ransa.


Hanakalinta ba k’aramin tashi yayi ba ta shiga suntiri cikin bedroom dinta cikin mummunan b’acin rai tabbas lokaci yayi da zata san mataki na k’arshe da zata d’auka akan Hammad, duk da dai ta san ba zai tab’a fitowa ya gayawa duniya wannan sirrin ba tunda shina kamar ya d’au wuk’a ya dab’awa kansa ne.




_____________________________

Gidan a hargitse yake sosai da shirin dawowar Hammad d’in. Abbu yasa an fitar da kayan da yake sashensa tun yana saurayi gaba d’aya, akayi fenti tare da canja komai Na toilet da furnitures d’in ciki. D’aki biyu ne da parlour kawai a ciki sai wani k’aramin kitchen. Guri ya d’au harami sosai sai jiran dawowar Babban Yaya.


Y’ayan su Gadanga k’annen Abbu duk Didi tayi musu waya akan su zo. Musamman kasancewar lokacin hutun second term ne anan k’asar mu ta gado Nigeria.

Yaran Gadanga Ali k’usar yak’i hud’u: Salima Salima Salman sai Salma.

Ita kuwa Asma’u yaranta uku Sajeed, Sajida sai Sajjad.


Lauratu tana da hud’u: Sa’ad,Sa’adatu sai Sadik da Saddik’a.


Nan kuwa gidan Umaru Usman Dan Borno da aka fi sani da UU D’an Borno kamar yarda kuka sani Sadiya Na da yara biyar Hammad Humaid Sai Hamidan da Abdul Hameed da Humaid.



Ita kuma Sakina (Ammi Na da Biyar) Najwa ce babba sai Nasma da Ahlam sai Muneerat da Hamda. Wad’anna sune jikokin Didi tsohuwa mai ran k’arfe, mai tsage gaskiya duk d’acinta. Manyan duk an aurar dasu idan ka cire d’akin Ammi da mace d’aya jal ta aurar. Inda ta auri wani hamshak’in d’an kasuwa suke zaune a can k’asar ibadan yanki yarbawa duk da bahaushe ne ya zab’i zaman ibadan a can ya ke duk wasu kamfaninnikansa saboda rashin kishin arewa.



_____________________________

Da k’arfe hud’u na yammacin ranar ta juma’a suka Sanka a airport d’in Malam Aminu Kano international airport da ke birnin kano.



Kaf k’annensa maza da cousins brothers d’insa ne suka zo tararsa.

Suka fara saukowa daga jirgin, ransa ya b’aci lokacin da ya fara shak’ar iskar Nigeria.


Sanye yake cikin black jeans na companyn Gucci, Sai casual T.shirt Na companyn Tommy Hilfiger dake U.S da rigar sanyin Tomford Bumber a jikinsa sai zabga k’amshin turarensa na kullum yake Emporio armani oud. K’afafunsa sanye da takalman Dolce and Gabbana logo embossed leather slippers, bak’ake Wanda suka haskaka kyakkyawar tausashshiyar fatar k’afarsa. Idanunsa kuwa cikin black glass suke Na companyn Gucci. Hannunsa da yake d’aure da agogo k’irar Gucci bracelet watch ya kalla. Yana sauka daga matattakalar jirgin fuskarsa a d’an d’aure yana sakin tsaki akai-akai musamman ganin arnen zafin da ake kwararawa a k’asar Nigeria mai barazanar dafa fatar mutum, musamman Su da suka dad’e basa k’asar. Ya ilahil Alameeen’ ya fad’a murya a cunkushe.

Daga kallon farko idan kayi masa zata zaka yi saurayi ne da ba zai haure matakin shekaru takatin ba ba zaka Ta’ba bashi shekaru har talatin da takwas ba.



Da gudu k’annesa suka rungume y’an cutest yaransa. Idanun Hamood cikin na Kamla da sauri ya bud’e baki yace “Masha Allah Hamda’s carbon copy.” Da sauri sauran ma suka kai dubansu kanta suna ta’ajjabi da mamaki a zahirance suka ce “Wannan dai Hamda ka haifo y’a.” Gabansa ne yake fad’uwa a duk sa’ilin da suka had’a Hamda da y’arsa, duk da zahiran shima ya san suna kama irin kamar nan da dole idan Na gansu ka san JININ SU D’AYA.
[1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: Alk’alamin JIKAR NASHE


Ya Abin Yake?


Page 9.


08033748387


Ina macen datake fama da ciwon mara in mijin yana saduwa dake kirinka jin xafi to kixo kimallaki female care

Ina masu fama da basir constfree tea yana magnin basir yana gyara fata tayi kyau

Royal jelly ya gyara mace yafito mata da shafe dinta kama daga breast hips duwawo

Fat bunner yana rage kitse ina wanda kitse ya mata yawa a jiki kigarxayo kimallaki naki 09131164861

Gamai bukatan yin register xai iyayi yasaya afarashin company

Company ght zakiyi registered akan 4500 kikawo mutun biyu suyi siyaya company zatabaki 36000 inbaki shiryaba karkimin mgn ngd



_________________



Haka suka d’unguma zuwa ainahin main House d’in su da ke unguwar Hotoro G.R.A.


Mutanen gidan suna jin shigowar motocinsu suka fita a guje domin tararsa.


Sakina ce kawai bata fito ba, da yaranta masu bak’in hali Najma da Nasma. Amma hatta da Muneerat

Please Login or Register in order to submit comment