Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fitowa da d’an hanzari, duk da matarsa batanan shi kad’ai ne a part d’in nasa, yaransa na can
Wajen Hamda da Sam suka k’i rabuwa da ita, musamman Kamla.


A hankali yake taku kafin ya k’araso parlourn.
Gabansa ne ya buga sosai, ganin mutanen zube a parlourn nasa, sanye cikin bak’ak’en kaya, hatta da fuskarsu sun k’unsheta ba zaka tab’a shaidasu ba, idanunsu sanye da Glass.

Duk da ya tsorata da ganinsu,
Sam jarumtarsa bata bayyana hakan ba, sai ma b’ata fuska da yayi, ya kuma isa wajensu cikin takun sa na gadara. Da ginshira da komai tamkar jinin sarauta ya ce “Lafiya?”

Mai suffar samudawan daga cikin su ya mi’ke tsam da niyyar kai masa duka, da sauri d’aya daga cikin su ya tare shi “Kada ka fara ka san ba abinda muka zo yi ba kenan, aiko mu aka yi mu gusar masa da tunaninnasa na shekara da shekaru, ta hanyar wannan maganin da tabbas idan ya sha shi ko kalar uwar da ta haifeshi ba zai sake tunawa ba, balle ubansa sunansa ma sai an masa Tarjama...” yana jin su suka shek’e da dariya had’e da Kai masa shak’a........
[1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: Alk’alamin Jikar Nashe

YA ABIN YAKE?



https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e


Follow me on ArewaBooks

@nazeefah

On Wattpad @Nazeefah381



13

✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽


Kamar an farkar da Abbu cikin daren, akan idonsa Samudawan suka shiga sashen Hammad d’in bayan sun sumar da masu gadi har biyu da suke bakin gate d’in.

Hankalinsa a tashe ya kira y’an sanda kafin cikin sand’a ya nufi part d’in su Hammad d’in yana bin bango, akan kuma kunnensa suka yi wannan furucin, da yayi barazanar hargitsa kayan cikinsa. Addu’a ya shiga yi akan Allah ya kawo police d’in da wuri.

Cikin hukuncin Ubangiji duk da dukan da suka yiwa Hammad d’in bai yarda ya sha k’wayar da suke tura masa a baki yana furzarwa ba.

Ance Sarkin yawa yafi sarkin k’arfi, don haka kafin kace me tuni sun wahalar da shi, duk da ya kafe akan k’in shan maganin.

A lokacin ne kuma y’an sandan suka bayyana cike da k’warin gwiwa suka danna kai sashen bisa jagorancin Abbu.

K’ok’arin gudun da suke ne yasa police d’in danna musu harbi a k’afafunsu, sun yi nasarar kama mutum biyu, yayinda uku suka tsere.


Ba wani b’ata lokaci suka gark’ame su da ankwa, a kuma lokacin ne mutanen gidan k’arar harbin bindiga ya farkar da su, Dama Didi da Hamda ba barci suke ba, a razane suka fito duka d’aukacin jama’ar gidan suka nufi inda suke jiyo harbin.


Cikin tashin hankali Didi take kiran sunan Hammad “Ubangiji Allah kasa ba su kashe min jika na ba”
Ta fad’a idanunta akan Hammad d’in da yake kwance magashiyyan Abbu yana k’ok’arin d’aukansa don su kaishi asibiti amma ya kasa, ga shi gidan ba maza duk suna gidajensu shi kuma Hamood yana makaranta.

Mahmah kuwa kuka kawai take ta kasa katab’us, sai Ammi ce cike da kissa ta kama k’afafun Hammad d’in suka kinkimeshi da Abbu don zuwa asibiti, hankalinta a tashe don bata san mai zai je ya dawo ba idan Hammad d’in ya farfad’o, ba mamaki a take a wajen ya tona mata asiri, da ta sani bata bi gurguwar shawarar kady ba gashi ta kaita ta baro. Dole ta nemi mafita a gaggauce kuwa kafin wankin hula ya kaita dare.


Bugun da suka yi masa a baya da gefen muk’amik’insa shine yake masa ciwo sosai sai kuma dukan da suka yi masa a kai da yayi sanadiyyar sumansa. Haka likitan yayi musu bayani kafin suyi masa allurai aka kuma jona masa drip barci mai nauyi ya d’aukeshi.

Dole Abbu da Didi ne suka kwana a asibitin don Sadiya bata zo ba bata son surutun Didi, shi yasa tayi zamanta a gida, Ammi ta so zama amma Didi ta ce a sabida me? Don kalan dangi, to ki fita idona wannan ba huruminki bane me kika had’a dashi? Banda auren ubansa da kika yi, maza-maza ki tattara komatsanki kiyi can wajen samudawan y’an matanki da
Kika ajiye kina adon d’aki da su.”

Ranta a tunzire ta tafi, dama taso zama ne ko ta samu mafita, wannan karan yarda take jin zuciyarta da tsoron tonuwar sirrinta, tana tunanin da kanta ma zata iya kawar da Hammad idan ta samu faraga sai gashi tsohuwa Didi tayi mata kanda garki, ta hanata sakat don haka jikinta a salub’e ta tafi, had’e da aniyar sake wani shirin ko da na zuba masa guba a abinci ne, sai dai tana tsoron a kamata, don haka zuciyarta ta amince da shawara d’aya da zata zartar da ita da zarar ya warke ya koma gida.



____________________________________

Da sassafe Hamda ta gama duk wasu aiyakunta, har peppe soup da sinasir tayiwa su Didi da zummar idan tayiwa yaran wanka su tafi gaba d’aya su duba Babansu.


Tana cikin shafawa Kamla mai Mahmah ta aiko idan ta gama shiryasu suje gaba d’aya.

Tsaf ta shirya su cikin kayansu na yau da kullum English wears kasancewar har lokacin basu saba da kayan hausawa ba.

A zaune suka sameta a parlour da coolers a gabanta, ta zabga uban tagumi so take taje duba yaronta amma tana tsoron tijarar Didi, gashi wad’annan mutane na jiya sun tsaya mata a rai, ya kamata tabbas ta bincika wajen sanin ko su waye, dole akwai wanda ya saka su ba zuwan kai bane.

Sallamarsu ce ta sata sauke wani dogon numfashi, idanunta akan Kamla da Hamda, da suka yi tamkar ya da k’anwa.

Har k’asa Hamda ta durk’usa ta gaisheta kafin su Kamla suma suyi koyi da ita. Mahmah ta saki murmushi zuciyarta tana jin dad’in yarda Hamdan take kula da y’ay’an d’an uwanta ta ce “Masha Allah, inye yaran Anty Hamda har an shirya, to maza kuzo mu karya sai akaiku asibiti ku gano jikin Babanku ko.”

Khairi ta zaro ido “Me ya samu Dad?” Kafin Mahmah ta bada amsa Hamda tayi saurin cewa “Fad’uwa yayi yaji ciwo kad’an, ai tafiya ma za muyi Mahmah saboda mun karya.” Mahmah ta jinjina kai,
“Duk dai baki gaji ba, ga d’awainiya da su ga girki to ubangiji yayi miki albarka.” Murmushi ta saki tana amsawa cikin jin dad’i da gaske tana son jin wad’annan addu’ar abinda bata tab’a samu ba daga bakin mahaifiyarta, sai dai Mahmah Abbu da Didi sai kuwa Malaman islamiyyarsu da kullum suke sambad’a mata albarka kwando-kwando.

“Ku tashi maza ku shirya kuje, ga driver can ya kaiku ga abinci ku kai musu.”

Da sauri Hamda ta ce “Ai nayi musu sinasir, kunun gyad’a da k’osai naga Ya Hammad yana masifar son su.”

Mahmah cikin sake Soyuwar yarinyar a ranta ta ce “Allah yayi miki albarka ya baki miji na gari, ya fahimtar da mahaifiyarki tarin ni’imomin da Allah yayi mata da
Ya bata ke a matsayin y’arta, ba’a ja da lamarin ubangiji amma da nace dama nice.”

Murmushi Hamda tayi hawayen idanunta na barazanar zubo mata, duk da k’ok’arin togacesu da tayi.

Mahmah jikinta yayi sanyi matuk’a tana tsaye har suka shiga mota suka fita daga gidan. Ta ja ajiyar numfashi tana sake jin tausayi da k’aunar Hamda a zuciyarta a zahirance jinta take tamkar jininta.


__________________________


Da sauk’i sosai jikinsa, ganinsu yasa Abbu tafiya gida, Didi kuwa ta zubawa Hammad abincin a baki tana bashi kamar k’aramin yaro.

Sai da yaci ya k’oshi sannan ta gyara zama tana rik’e hab’a ta ce “Sadiya dai ta tabbata Asararriya, wallahi bana haufi Rashin ilimin nasara ke d’awainiya da Sadiya take yin wani abu tamkar zubin mutanen farko, to ko ni da nake y’ar zamnin da ai ba zank’i zuwa duba Ummaru idan lalura ta sameshi ba, balle har ta kai ga kwanciya asibiti, amma kuji min lusarar mace yarda ta bursune idanunta da toka tak’i zuwa dubata, Yanzu ai ka tabbatar daga ni sai ubanka Ummaru ne muke sonka, Sadiya kuwa da kai da
Babu duk d’aya ne a wajenka, shashashar uwa kenan lamba d’aya Sadiya kenan, har yanzu ruwan Gwarzo bai bar jikinta ba, ai zamu koma gidan da ni take zance.”

Hammad ya d’an bud’e idonsa kad’an yana harararta k’asa-k’asa, shi surutunta ya fara isarsa, ta daddage sai magana take, ta barshi ma yaji da matsalarsa. Ya
Zama dole ya sanar da duniya wacece matar ubansa da ta......


Bugun k’ofa ne yasa Didi shiru, shima kuma tunaninsa ya yanke a wajen, Nanna ce ta shigo da
Sauri ba tare da la’akari da Didi da take zaune ba ta rungumeshi a jikinta tana sakin kuka. “Tafiya zamu yi England Dear ba zan yarda su salwantar min da rayuwarka ba, dama ni na tilastaka sai kazo, ban san lamarin k’asar nan ya tab’arb’are haka ba.”

Ta fad’a tana shafa gefen fuskarsa da sakar masa peck a kumatu, sai ji tayi Didi ta ce “Auzubillahi, Kice Nanna duk harkar nasara kin d’abeta tsaf a kanki, yanzu baki ji kunya ba da ranar Allah kike dak’umarsa da manna masa sumba a kumatu, sabida ki nuna
Mana ke jarababbiyace.” Tsit Nanna tayi tana wasa da zoben hannunta, hankalinta ne a tashe sam bata lura da Didi da take d’akin ba balle su Hamda, duk da ita a wajenta hakan ba wani abu bane, musamman dubi da can yarda suke rayuwa.

Nanna tsit tayi tana jin Didin na sababi kamar ta ari baki, kafin ta mik’e tsama tana kallon Hamda Ta ce “Ai sai mu tattara mu tafi tunda jarababbiyar matarsa tazo, kada kuma tayi abinda idanunmu zasu makance, ah to don kinibibi kina son mijin kika tsallake kika tafi kika barshi, kin tafi agolanci gidan uwarki.”

Nanna dai ko tanka mata bata yi ba, don da zarar zata tanka mata sai Hammad ya k’ifta mata ido alamar tayi shiru. Tana kallo Didi ta tasa y’ay’anta a gaba tafi da su duk da Abulkhairi yaso zama amma ta ce “Sam, ba zan barka ba, haka kawai suje su bud’e maka ido a banza a wofi, don ina kallon almurin ubanka yarda yake narke idon nan shima jaraba ce take ci sa, sai azo ana abinda ba shikkenan ba, sahunka a likkafa ka wuce mu tafi, har kwad’on zogale zan maka.” Abul Khair tilas ya bita, suna fita Hammad ya saki murmushi kawai yana mamakin yarda tsohuwar bata jin kunyar furta duk abinda yazo bakinta.
Ita kuwa Nanna b’ata fuska tayi sosai don abin na Didi ya bata haushi, haka kawai ta hau mata sababi akan abinda ba shikkenan ba har da wani cewa Agolanci taje gidan mijin Uwarta, kullum sai tayi mata wannan gorin. Hammad ya ja hannunta yana murzawa a hankali da sauri ta janye hannunta, “Rufa min asiri, kada tayi mantuwa ta dawo kaga da gaske sai ta sake manna mana sunan Jarababbu.
Hancinta ya ja cikin wata irin murya ya ce “Kamar fa Didi ta shiga zuciyata, jarabarce take ci na, kin san ta riga ta gama sanina tun ina yaro.” Ya fad’a yana kashe mata ido da ya sata sakin murmushi tana sunne kai a jikin sa, da gaske ita ma tayi kewarsa. A cikin kunne ya rad’a mata “Close the door.” Sosai jikinta ya amsa yanayin yarda yayi mata magana har bata san sanda ta sake shigewa jikinsa ba.




_____________________________

Kwanansa biyu aka sallameshi, ya samu sauk’i sosai duk wasu rauni na jikinsa sun warke illa kafad’unsa da suke d’an masa ciwo kad’an.

Sai sannan Mahmah Ta ganshi duk da gorin da Didin tayi mata bai sata taje ba, don ta san da zarar taje d’in itace dai mutum ta farko da zata fara yi mata gori. Ya fara yamad’id’i da ita taje duba d’an fari duk da sunyi mata kara, shi yasa tayi burus da zancen Didin bata je ba.



Hamda ce ta gyare musu b’angarensu tas, sai zabga k’amshi yake, sannan su kayi musu sakwara da miyar egusi, aka had’awa Hammad zob’o mai abarba.



_____________________________


Da Yamma Ammi ta shiga dubashi, fuskarta d’auke da murmushi, ta sauke idanu a kansa, shi kuwa yana ganinta yayi kicin-kicin da fuska, baya buk’atar ganinta sam. Ta kuwa ci sa’a Nanna ta shige d’aki can ciki ta bar Ammin daga shi sai ita. Cikin wani salon murya ta ce “To ya jikin naka? Dafatan yanzu ka san ba wasa nake ba da nace maka zan iya aikata kisan kai, ko don waccan maganar ta mutu, ina so na sake jaddada maka matuk’ar ka cigaba da k’ok’arin fallasa sirrina tabbas rayuwarku kai da y’ar uwarka ko nace y’ar.........hmmn tana cikin had’ari don wallahi daga kai har ita zan iya b’atar da ku daga Doran k’asa, don haka ina k’ara jan kunnenka be careful.” Ta fad’a tana shafa gefen wuyansa inda raunin yake had’e da sakar masa wani kafirin murmushi ta ce “Mu huta lafiya, Kayi kuma gaggawar had’a ya naka ya naka ka bar k’asar nan shine kwanciyar hankalinka kai da waccan yarinyar.....” ta sa kai ta fice tana sake sakin murmushi, Turus tayi a bakin k’ofa, cikin fad’uwar gaba bayan sun yi ido biyu da..........
[1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: Al’kalamin Jikar Nashe..

YA ABIN YAKE?

Follow me on ArewaBooks

@nazeefah

https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e

08033748387


On Wattpad
@Nazeefah381


14
____________________________________

✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽

Ido biyu suka yi da Mahmah da take shirin shiga duba Hammad d’in, suka shiga kallon-kallo kowa da abinda yake rayawa a ransa, musamman Mahmah da haka kawai gabanta ya yanke ya fad’i.
Ammi ta d’an saki yak’en murmushi don bata son Mahmahn ta zargi komai a ranta, duk da hakan ma bata tsira ba, don Sadiya Ta san tabbas ba wani dalili Sakina ba zata sakar mata murmushi ba, yarda ta tsaneta har kowa ya fuskanci hakan. Ga mamakinta sai ji tayi Sakinan ta ce “Ya kuma mai jiki? To Allah ya tsare ya sake kiyaye gaba, ai ma an auna arziki.” Mahmah ta d’an yi murmushi kawai had’e da furta Ameen tana shigewa cikin sashennasa, haka kawai zuciyarta ta k’i yarda da lamarin Sakinan. Tana shigewa Sakina ta saki tsaki murya can k’asa ta ce “Algunguma, da ni kike zancen, shegiya bak’a kawai kin zo kin mamaye gida.”
Wayarta da ta shigo ne yasa ta saurin shigewa b’angarenta, ganin Kady ke kiranta. “Sakna mu godewa Allah yara dai sun yi kasuwa, Senator Aruwa na son Najma Shi kuma D’an majalissar birni da kewaye yana son
Nasma Wata irin shewa Sakna ta saka, don tsananin farin ciki bata san sanda ta dinga k’wala musu kira ba.

Su d’inma a sukwane suka fito samun labarin ya saka su rungumar juna suna shewa da gaske abin ya zo musu tamkar almara a lokacin da suka cire rai.
Ammi ta gargad’esu da jan bakinsu su tsuke gudun y’an hana ruwa gudu, ko zancen za suyi, sai dai suje gidan Kady, ta kalli Muneerah kafin ta ce “Saura kuma don ubanki na ji labarin ya fita, yanzu ke kika rage min na samo miki wani gwaskan d’an kasuwan ko b’arawon gwamnati, don ta waccan banzar bana tata kowa ma ya aureta ba matsala ta bace.”
Turus y’an uwan suka yi, zuk’atansu cike da tambayoyi game da dalilin da yasa Ammin ta tsani y’ar uwarsu, kullum abin yana damunsu ganin dai Ammin bata son yawan zancen yasa suka tattara suka watsar da lamarin.

Wannan karan dai kam sai da Munira tayi k’uru ta ce “Wai Ammi me Hamda tayi miki kika tsaneta har haka? Alhali Ko mu da kike nunawa k’auna ba ma yi miki biyayyar da Hamda take yi miki.”
Wani kallo Ammin ta jefeta da shi kafin ta ce “To uwata naji duka tukunna kafin na sanar miki, wallahi duk ranar da kika kuskura kika sake yi min makamanciyar wannan tambayar ranar na lahira ma sai ya fiki jin dad’i kinibabba kawai.” Sunkuyar da kai Kawai Muneerat tayi kafin ta mik’e ta shige bedroom d’insu da sauri. Tayi alk’awarin sai ta binciko dalilin da yasa ake yiwa y’ar uwarta wannan tsana ta ba gaira ba sabar, sam bata yarda da dalilin wai don an haifeta a mace bane, akwai dai wani b’oyayyen lamarin da dole zata bincikoshi. Ammi ta bita da banzan kallo sai taji ma duk farin cikin da take ciki ya b’ace b’at, saboda wannan zancen da Munira ta tsillo mata na waccan bak’ar yarinyar mai kalar mutanen Habasha. Ta ja tsaki kawai had’e da mik’ewa.




____________________________________


Zunnuraini, bayan kwana hud’u da had’uwarsu ya zo, cikin shigarsa ta alfarma sai zabga k’amshin turaren Miyaki yake yana asalin.

Suna zaune gaba d’aya a parlourn Didi har da Nanna da Hammad da yaransu sai Hamda da take gefe take tsakurar tuwon kamar bata so, haka kawai yau ta tashi da yanayi na fad’uwar gaba da b’acin rai shi yasa take zaune a gefe, duk da surutun da Kamla take damunta da shi bai sa ta cire damuwar da take ranta ba.

Sallamar yaron da yake musu sharar harabar waje ne ya dawo da ita cikin duniyar tunanin da ya zurfafa jin yace “Wai ana sallama da Hamda.”

Da sauri ta kai idonta wajen da Hammad yake, sai dai ko alamar yaji zancen bai yi ba, gaba d’aya hankalinsa yana kan Abulkhairi da suke buga TV game, a gark’amemiyar t.v d’in da take parlourn.

Didi tsaki ta ja tana zabga mata harara ta ce “Ji min y’ar banza, shin baki ji ana sallama da ke bane?” Jikinta a salub’e ta mik’e ra shige d’aki, Kamla na binta a baya, sai yanzu ta gane dalilin b’acin ranta, da fad’uwar gaba, duk sabida a karo na farko saurayi yazo zance wajenta. Ba abinda ta saka a fuskarta sai ma zumbulelen Hijabin da ta saka da ya kai mata har idon sawu, sannan ta rik’e hannun Kamla suka fice, ta k’asan Ido Hammad yake kallonta, ya saki ajiyar zuciya, a ransa yana mata fatan dacewa da abokin zama Na gari don shine kad’ai abinda Zai saka ta samu peace of mind Ta huta da gallababbiyar Uwarta.



A can bakin gate ta tarar da shi saman bonnet d’in motarsa yana danna waya hasken farin wata ya haske kyakkyawar madaidaiciyar fuskarsa, har a zuciyarta take jin Zunnuraini ya kwanta mata kuma zata iya zaman aure da shi. Don ita dai bata hango makusa tattare da zubin halittarsa ba.

Cikin nutsuwa take takun, hannunta rik’e dana Kamla har suka isa inda yake. Ya d’ago fuskarsa cikin murmushi yana tsareta da idanunsa gaba d’aya yarinyat ta gama tafiya da imaninsa tun ranar da yayi tozali da ita duk da bai ga zubin halittarta ba ta fuska kam tayi masa hundred percent irin matar da yake so, mai matsakaicin kyau ba mai manyan kyau ba.

Tsawon lokaci suka d’auka suna hira kafin ya sake sanar da ita ainahin wanene shi da sunan mahaifinsa da komai, sai dai gabanta ya fad’i jin cewa yana da mata har da yara biyu. Ganin ta firgita ya saki murmushi kafin ya ce “Kada fa ki damu, matata bata da matsala kuma ba gida d’aya zan had’aku ba.” Murmushi ta d’anyi lokaci guda kuma yana sake burgeta ganin ba halinsu d’aya da sauran maza ba masu kushe matansu na gida a yayin da suke neman aure madadin haka ma shi yabon tashi matar yake, nan take zuciyarta ta sake amincewa da shi hundred percent.

Da zai tafi ya mik’a mata sabuwar waya dal a hannunta, ganin ta k’i karb’a sai ya mik’awa Kamla had’e da fad’in ya sunan k’anwar tamu don da gani babu tambaya k’anwarmu ce ga kama nan b’aro-b’aro. Hamda murmushi ta saki kafin tace Baka canka daidai ba, Niece d’ina ce ba k’anwa ba.” cikin mamaki ya ce “Ai kuwa wannan ko y’ar waye tabbas mu ya haifawa y’a don kamar babu banbanci. Masha Allah, Idan kin gama shawarar please ki fad’a a gida Zan turo magabatana so samu ne ma ki azimi a gida na, amma na san yayi wuri don haka zan barshi Immediately after Sallah Insha Allah.” Da sauri ta shige Gida cikin matsananciyar kunya.


Da murna Didi ta karb’i kwalin wayar tana cewa “Masha Allah, haka muke so kab’akin arziki, kice saurayin naki mai d’an maik’o ne? Har da dalleliyar waya haka, gaya min waye ubansa anan garin? Burina ki auri wanda uwarki zuciyarta zata kusa bugawa ta mutu kowa ma ya huta, Allah yasa dai Ubansa yafi d’angote kud’i.”

Wani tsaki Hammad ya ja kafin ya ce “Ai duk halinku d’aya da Ammin shegen son abin duniya, madadin kiyi mata fatan samun mutumin k’warai sai ki wani ce Allah yasa Ubansa yafi d’angote kud’i, mhmn don dai baki san arzikin d’angoten bane, ke kuma shashasha ki tsaya daka tatata kada ki samo mutumin arziki ki tsaya neman mai dukiya
Ba mai zuciya ba.”

Sak’ek’e Didi tayi tana kallonsa baki a mele kafin tace “Kaji min mutum banda kai d’in wanta ne da sai nace bak’in ciki da hassada kake mata, waye yak’i dad’i a duniya inace ko kai yanzu d’iyar d’angote Ta ce zata aureka murna zaka yi.”
Bai bi ta kanta ba ya fice don ma ya cusa mata takaici har da jan hannun Nanna kamar zai mayar da ita ciki, duk da Nannan na turjewa Didi ta ce “Jarababbe, jarabar ta motsa ai ni yanzu lamarinku tsoro yake bani, mata ki bi ki nanik’ewa miji, Allah dai ya kyauta.” Dariya kawai suka fita suna yi. Hamda ma dariyar take kafin ta shige d’aki tana dafe da k’irjinta saboda tsananin bugun da yake mata.




__________________________

Ciwon cikin da ya murd’awa Muneerah cikin dare da misalin Sha biyun dare ne ya sata fitowa daga bedroom d’insu don ta samo magani a first aid box da yake d’akin Amminsu.

Kasancewar dare ne kafin ta murd’a k’ofar d’akin ta ji sautin muryar Ammin da alama waya take jin tana kiran sunan Hamda yasa ta dakata da bud’e k’ofar ta kara kanta sosai a jikin k’ofar sai taji Ammin ta cigaba da cewa “Kin san sarai ta yarda aka samar da yarinyar nan? Ta yaya kike tunanin hankalina zai kwanta idan ban kawar da ita ba, duk ranar da Umar ya san maganar nan na ha’intarsa da nayi ha’inci mai muni ina tabbatar miki Mami ba zan kwana da igiyar aurensa ba, don Allah Mami ki nemar min mafita wallahi kaina ya k’ulle, na rasa yarda zan yi, don na lura yaron nan bai k’i ya fallasa sirrin nan ba ko da shi zai kwana a ciki, na tabbata akwai abinda Hammad ya taka shirunsa ba yana nufin ya hak’ura bane musamman da na san ya kwana da sanin cewa ni na turo mutanennan suka yi masa duka cikin dare.......

Wata irin hajijiyace ta fara d’iban Munirat ji da ganinta duk suka d’auke na wuncin gadi, a take ta kurma wani uban ihu........✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽


Jikar Nashe//
[1/12, 7:43 AM] Nazeefah Nashe: ALK’ALAMIN JIKAR NASHE

(Mai tak’ama da ikon Subhana)


YA ABIN YAKE?
08033748387


Follow me on ArewaBooks

@nazeefah

https://arewabooks.com/book?id=635c58dc8a75f51b283a378e


On Wattpad @Nazeefah381


Last free pages.

15
✍🏽✍🏽✍🏽📖📖📖📖✍🏽✍🏽✍🏽
__________________________________

Da sauri Sakina ta fito daga bedroom d’inta, hankalinta a tashe dafatan Munira bata ji abinda take cewa mahaifiyarta a waya ba.

Turus tayi ganin Muniran a k’asa tana dafe da gwiyoyinta hawaye shab’e-shab’e a fuskarta, alamarta ya nuna kamar fad’uwa tayi. Sakina ta saki ajiyar zuciya kafin ta ce “Ke kuma lafiya cikin darennan kike kurma uban ihu?” Munirat ta tattaro duk wata nutsuwa Ta saka a fuskarta, bata son Ammin ta fahimci ta ji zancen da take, ta san idan har ta gane zata iya d’aukan ko wane mataki a kanta, don haka murya na rawa ta ce “Ciki na ke azabar ciwo, kuma na zo amsar magani sai na zame anan.” Ammi ta saka hannu ta mik’ar da ita had’e da fad’in Ayya muje ki sha maganin to, ko dai period pain ne?” Ta girgiza kai jikinta a salub’e, kafin ta bi bayan Ammin zuciyarta na sake mamakin halayyar Ammin.

Tana shan maganin tayi saurin ficewa daga d’akin, nutsuwa take buk’ata gami da dogon nazari akan maganar nan da ta jiyo, tabbas biri yayi kama da mutum, amma waye uban Hamdan shine abinda ta kasa ganewa.

Ta dad’e tana juyi a saman gadonta dafatan barci ya kwasheta amma ina wannan dare kam tuni suka yi hannun riga da barci, ciwon cikin ma tuni ta neme shi ta rasa, k’wak’walwarta ta tafi dogon nazari, tunaninta ya tsaya cak zuciyarta na wani irin bugu bata son abinda take tunanin ya tabbata, bata fata ko kad’an idan hakan ta kasance ba Ammi kad’ai ba su kansu abin kunya ne a wajensu.

HAMMAD zuciyarta take ta bata a matsayin uban da yayi cikin Hamda, idan ba haka ba me zai saka y’arsa tayi kama kwabo da kwabo da Hamda, kamar da kana gani ko ba’a fad’a maka ba zaka san sun had’a jini d’aya. Ta runtse idonta wasu

Please Login or Register in order to submit comment