Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*


[2/7, 11:31 PM]



*CIKIN DUNIYARMU*
1⃣
Follow me on whatpad @Rashuna


___________________
*ONE*

*KANO*
K/B/layi.

Kallon abincin da suke ci nayi, hawayen idona yana son zubowa kan kuncina, gashi har a zuciyata yunwar nake ji amma bazan iya ciba, kallon Safnah nayi nace.
"Pls my Safnah ke ki bani tunda su sun hanani. ”
Dariya tayi mini tace.
"Ai yasin yau indai baza kici da kanki ba sai dai ki hak'ura.”
Juyawa nayi zan bar gurin da suke, hawaye na sakkowa bisa kuncina sai ji nayi Aysha tace.
"Tsaya Teema Nazz na baki ai ni dake bata b'aci.”
Juyowa nayi na galla mata harara, alamar naji haushi kenan, muryar Aunty Sakina naji tana cewa.
"Rabu da su Teemah zo nan na baki da kaina.”
Share hawayena nayi na isa gareta, ta 'yebi abincin a plate ta shiga bani, du³ baifi cokali goma ta bani ba nace mata.
"Na k'oshi. ”
Saboda sanin halina yasa bata matsa mini ba ta bani ruwa nasha.
Misalin k'arfe 8:30pm shine dai² lokacin tashinmu daga aiki, muka yiwa Aunty Sakina sallama, har lokacin babu wacce naiwa magana ina fushi dasu har muka tari adai daita sahu, Safnah da Sarat aka fara saukewa a kunya store, mu kuma aka wuce damu layin d'an dare me nama, Aysha ce ta fara shiga gida saboda gidansu ne a farko har lokacin ban kulata ba sai kumbura fuska nake.
Da sallama na shiga d'an madai daicin gidan namu, da hanzari na isa gaban Ummi da idonta yayi jazur saboda hayak'in ice, karb'ar abun fi fitawar nayi daga hannunta ina.
"Ko da zan fita sai da na gaya miki kada kiyi aikin awarar nan komi dare na dawo zanyi.”
"Ina tausaya miki ne *MUNASSAH* kin fita tun safe, kin dawo da daddare me makwan ki wuta sai ki hau wani aikin. ”
"Amma Ummi kece fa kike gaya mini, duk wuyarnan da muke sha wata rana sai labari, kinsan matsalar ciwonki ba'a so kuna zuwa gaban wuta, dan Allah Ummi ki mini alk'awarin baza ki sake ba.” Shafa kaina tayi tace.
"Na miki alk'awari Munassa, Allah ya albarkaci gabanki da bayanki, ya baki yara masu ladabi da biyayya fiye da yarda kike mini. ”
Takai k'arshen maganar tana d'auke k'wallar idonta da sauri don kada na gani.
"Amin” Nace ina cigaba da fi fita wutar har ta kama, sannan naja hannun Ummi zuwa d'aki, bayan mun zauna na kalleta nace.
"Ummina albishirinki. ”
"Goro, Munassata, nasan duk abinda zai fito daga bakinki me matuk'ar dad'i ne, gaya mini ina jinki. ”
"Ashe ana kaiwa su Yaa Nazee ziyara mu bamu sani ba, sai d'azu naji ana hirar, wai ana kai musu garin rogo, suger gyad'a me gishiri, k'uli² amma ba dakakke ba, indome, kayan shayi, bread, ruwa na leda ko na jarka, man shafawa, maclean sabulun wanka da na wanki.”
Katseni Ummi tayi da cewa.
"To mu yanzu ina muka ga kud'in siya masa dukkanin abubuwan nan?”
"Ai dama na fad'a ne don kiji irin abubuwan da ake kai musu, nidai yanzu ina da 1000 gobe insha Allahu zanje, zan kashe masa 800, nayi kud'in mota da 200, awara ma sai na dawo zan soya don kar na makara, dama na gayawa Aunty Sakina ba zanje goben ba. ”
"Allah yashi miki albarka Munassa, bazan gaji da gaya miki wannan kalmar ba a ko da yaushe, Allah ya yaye mana wannan duhun rayuwa da muke ciki ya kawo mana haske cikin RAYUWARMU.”
"Amin Ummina. ”
"Ga abinci can d'auko kizo na baki.”
"A'a Ummi nidai na k'oshi.”
Bata matsa mini sai naci ba saboda tasan halit tata, ko ya naci abinci to ya isheni amma in har na k'ara to ranar bazan kwana lafiya ba, Abba da Yaa Nazee sunsha sintiri dani asibitoci har da na k'asashen waje akan rashin cin abincina, k'arshe har suka gane halitta ta tace daga Ubangina.


__________

*KATSINA*
K/Durbi

"Mom kenan, a tunaninki zan bar wata ne ta haifawa *MIQ* 'ya'ya bayan ni na kasa haifa masa? ”
A k'ufule wacce aka kira da Mom tace.
"To ba gashinan ba kin barsa sun k'etare k'asa shi da matarsa, duk da kasancewarsa babban soja hutun wata guda 'ya d'iba don ya bawa matarsa kulawa, ke kin saki baki da hanci, da nayi magana kice don kina sonshi ne, ni yarda na tsani na bud'e ido na gansa haka na tsani ganin mutuwata, ko zanyi yawo tsirara bazan bari a haifi jika a gidan nanba, yarda nima ban dire d'a ko d'aya a cikinsa ba. ”
"Hmmmm Mom kenan, kina bani ma'maki, sai kace ba nonoki na tsotsa ba, to bari kiji gobe ko jibi zakiji tafiyata England, kuma wata d'aya da mutuwar *FAREESA* da Babyn cikinta zanyi aikin k'arshe na gama, ma'ana zanyi tsafin da baya sakin mutum sai dai idan ya mutu, zan hana dukkanin matansa haihuwa tare dashi, kuma zan hanasa yin aure ko da d'aya daga cikinmu ce ta mutu, domin shi da aure sunyi hannun riga sai dai in a lahira. ”
Tana kawowa nan ta juya ta bar falon.......


*ALK'ALUMAN NAGARTATTU*
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*


[10/2/2020/4:52 PM]


*CIKIN DUNIYARMU*
1⃣
Follow me on whatpad @Rashuna


_________________
*TWO*

*KANO*
K/L/D/me nama

Washe gari sai aro kurfoti nayi a mak'ota, naje na siyo gawayi na hura na barwa Ummi sauran aikin don na shirya na tafi gurin Yaa Nazz, saboda gudun kar na tafi taga ana zuwa neman awarar ta hura ice ta soya.
K'arfe 8:30Am nayiwa Ummi sallama zan tafi, ta bini da addu'ar Allah ya tsare na kuma gaishe mata da Yaa Nazee, a lokacin har an fara layin siyan awara.
Naje dai² k'ofar gidan su Aysha ita kuma ta fito zata tafi gurin aiki, aikuwa tace sai ta bini munje tare, ban b'oye mata ba nace mata nerata 200 kacal ta mota, sai kuma kud'in da zan masa siyayya, aikuwa tace muje itama tana da 200.
A dai-daita sahu muka tsayar, nace masa kurmawa prison, yace 300 mukace 200 in zaka, yace mu hau, har ya fara tafiya damu nace masa.
"Kayi yanke damu, kar ka bi damu ta *TEEMA NAZZ* .”
Yace kuwa. "To.”
A dai² bakin gate in gidan ya ajiyemu, komawa mukai da baya bayan mun sallamashi muka lalubo kantin da zamui masa siyayya, garin rogo na siya masa gwangwani 4 suga gwangwani 2, madara gwangwani 2, gyad'a me gishiri gwangwani 3, sai ledar pure water 2.
Anan bakin gate in sai da aka fara cage kayanmu tukunna muka shiga, wata rumfa na gano, da bencina a jajjere mutane ne fal a gurin b'arin mata da ban na maza da ban, gefe muka samu muka rakub'e ina jin kaina yana jujjuyawa.
'Ko da wasa ban tab'a tunanin k'afata zata tako gidan nan ba, sai gashi wai yau Yayana mafi soyuwa a gareni shine a cikin gidan, ba tare da hak'k'insa ba face k'aharu, sai gashi dalilin haka nima na tako k'afata cikin gidan, wanda ko a mafarki ban tab'a tunanin hakan ba, idan kuma ina tunanin yadda Rayuwarmu ta taso tun farko, ko da wai idan akace Rayuwarmu zata juya kamar yanzu bazan yarda ba, lallai mutum baya sanin rayuwa juyi² ce sai hakan ya faru a kansa, ko kad'an ban tab'a tunanin DUNIYARMU zata sauya a lokacin kad'an ba, sai gashi gaba d'ayama ta wargaje.'
Wasu siraran hawaye ne suka shiga biyo kuncina, zuciyata bata kuma tsinkewa ba sai da naji wasu suna tattauna abubuwa na ban tausayi, kifa kaina nayi na saki kuka har da shashshek'a.

Da aka kwashi 'yan layin gaba suka shiga Aysha ce tayi saurin zama a gaban itama, saboda idan muka tsaya layi sai yazo kanmu zamui matuk'ar dad'ewa, me karb'ar sunan wa'yanda akazo gurinsu ne yazo yana karb'a, da akazo kan Aysha ta tab'oni nace masa.
"Nazirr Abdulhamid Bak'o.”
Yace. "Wata Anguwa?” Nace.
"K/Naisa.”
An d'an jima da karb'ar sunayen, sannan akace muzo mu shiga, da muka shiga ma sai da aka bincika kayan kowa, sannan aka bamu wani d'an kati kowa ya sak'ala a wuyansa, idan wani ya fito babu shi to ba za'a barshi ya fito ba ya zama d'an ciki, ina kallon Aysha tana kuma damk'e nata ta cikin hijabi, wani d'aki muka shiga muka zazzauna a benci, sannan wa'yanda akazo gurinsu suka fara shish shigowa, ina hango Yaa Nazee na fashe da wani irin kuka, shima k'asa yayi da kansa yana kuka k'asa², nidai bamu samu damar magana dashi ba, sai Aysha ce take ta tausarsa, can na d'ago kaina muka had'a ido dashi, idonsa d'aya ya kumbura wani kukan na kuma fashewa dashi, ina jin gandirobar dake gurin yana nasiha da adaina kuka, yace mu tashi lokaci yayi, kayan da muka kawo masa Aysha ta bashi, sai a lokacin ya bud'i baki da k'yar yace.
"Abba bai mutu ba yana nan da ransa. ”
Ji nayi wata juwa zata zubar dani daga zaune Aysha tayi saurin rik'oni, shikuma gandiroba ya tisa k'eyarshi waje, ya fita yana waiwayonmu, Aysha ce ta rik'oni muka fito, ina jin wani yana.
"Ki daina mana kuka, bama son kuka munfi son kuyi mana addu'a. ”
Da muka zo fitama ina jin gandirobobin suna cewa.
"Idan kinsan kuka zaki dinga zuwa yi kada ki kuma zuwa.”

Kan muje gida, ciwon kai da ciwon k'irji ya sark'e mini, amma haka na dinga daurewa don kada na tayarwa da Ummi hankali, d'aki na sulale na shige na kwanta.
_Abba yana raye bai mutu ba._
To shin yana ina, dama k'arya aka mana akace ya mutu, to meyasa aka aikata hakan?”
Bani da me bani wa'yan nan amsoshin a yanzu dai.
Kuka me rad'ad'i da zafi na fashe dashi, ina jin kaina kamar zai dare gida biyu, haka zalika k'irjina ma wani irin suka yake mini.



_________________
*ENGLAND*
Kwance take cikin yalwataccen k'irjinsa tayi lamo, sam bata k'aunar abinda zaiyi sanadiyar barinta jikinsa, a cikin bawon wanka suke don ruwan d'umin sosai yake mata dad'i, hannu ya saka ya shafo cikinta, nan take yaji Babyn yana wutstsilawa a cikin, wata dariya ya saki yace.
"Zumata kinji kwa yarda Babyna yake wul wulgawa?”
Dariya tayi itama tace.
"Haba Zumana, ni da abin yake cikina amma kake tambayata naji? ”
"Wallahi tsabar farin cikine yayi mini yawa, wannan shine k'wanmu na takwas a duniya, ina kuma fatan da ya zamo rayayye, kar shima yabar CIKIN DUNIYARMU a yayin da muka fara saka ran rayuwa dashi. ”
Shafo fuskarsa tayi cikin sanyin murya da karayar zuciya tace.
"Kada ka damu Miq, insha Allahu wannan Babyn rayayye ne sai dai ni nakan ji kamar zan tafi na bar CIKIN DUNIYARKU, kuma ina jin kamar ta silar zuwansa duniya duhun dake lullub'e da rayuwarka zai yaye haske ya bayyana a gareka.”
"In sha Allahu baza ki bar Duniyarmu ba Reesah, zamu rayu dake tare da Babynmu bi izinillahi Rabbi. ”
"Amin to.” Tace tana kuma shigewa jikinsa, wankan sukayi suka fito, yana shafa mata mai itama tana shafa masa a haka har suka gama shiryawa, wayarsa dake kan mirror ce tayi k'ara yaje ya d'auka, yana ganin me kiran ya wani saki lallausan murmushi.
"My Sumyy.” Shine farkon abinda ya fara fad'a, yayin da hakan yazo dai² da bugawar k'irjin Fareesah.
"Haba My Miq, shine ka d'auke matarka kuka yi nesa dani bayan kasan rayuwata tana tattare da taku.”
Ta fad'i hakan a shagwab'e
"Sorry my Sumy ai tana haihuwa zamu dawo insha Allah. ”
"Kai dai kawai ka d'auke matarka kun tafi ne, saboda kana zargin ana kashe maka 'ya'yane.”
"Subhanallahi! Daina fad'in haka Sumy, sai kace banyi tawakkali ba, kuma ban yadda da k'addaraba? Duk yarana da suke mutuwa dama Allah yayi ba masu tsawon rai bane, don haka kar in kuma jin kin fad'i haka. ”
Cikin fashewa da kukan kissa tace.
"To ai kaine ka rabani da kanka, bayan kasan yadda nake zama idan har baka tare dani, bana jure rashinka idan har ya wuce na kwanakin da kakewa matanka, pls ka taimakawa rayuwata mana, kuma ita kanta Fareesah tana buk'atar kasancewata tare da ita. ”
"To² naji my Sumy, nima ai nayi kewarki sosai, don haka Faisal zai shirya miki komai, gobe iwar haka muna tare da juna. ”
Wani ihun farin ciki ta saki ta sakar masa mahaukacin kiss ta wayar, Fareesah kuwa k'irjinta ne ya shiga dokawa ta dinga binsa da kallon tsoro.........

ALK'ALUMAN NAGARTATTU.
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*


[11/2/2020/5:29 PM]

*CIKIN DUNIYARMU*
1⃣
Follow me on whatpad @Rashuna


________________
*THREE*

*KATSINA*
G.R.A
Tsallen farin ciki tayi, bayan ta ajiye wayar, ta nufi sashen Khadija.
A kwance ta tadda ita kan doguwar kujera tana danna wayarta, ko sallama ba tayi ba ta shiga ta tsaya a kanta.
"To sarkin 'yan kishi, gobe in Allah ya kaimu zanbi bayan mijina, ke kuwa da waccen da bata da amfani sai dai ku zauna kuyi zaman gida.”
Wani kallon sama da k'asa Khadija tayi mata kana taja tsaki tace.
"Mugun nufinki ne zai kaiki can, kuma insha Allahu k'udirinki akan Miq bazai tab'a cika ba, da sannu zai gane ke ba masoyiyar shi bace mak'iyiyarsa ce, idan mu munyi k'ok'arin fahimtar dashi kin dak'ile duka hanyoyin to ina me tabbatar miki da baki yiwa Allah wayo ba, akwai abinda zai zame miki izina kan mugun nufinki akan *MIQDAD*”
"Hmmmm Khadija kenan, har yau baki sanni ba labarina kike ji, wai ta yaya ma za'ai na barki haka bayan kinsan dukkanin sirrinmu? To in baki sani ba yau ki sani, nice nan nai miki tsafin da yake danne harshenki aduk sanda kikayi k'ok'arin fallasa mini sirrina, na barki da abin a ranki yai ta damunki a zuci, kina gani zanci gaba da aikata mugun nufina amma babu damar ki kub'itar da shi, in baki sani ba yau ki sani na d'aure zuciyar Miq gaba da baya, duk wani wanda zai kawo masa suka a kaina bazai tab'a yarda ba, daga k'arshe ma k'iyayya ce zata biyo bayansa ga duk wanda yazo masa da sukata, nafi k'arfin tunaninki Khadija, haka zalika na wuce sanin da kika mini, a cikin sirrin nawa ma kaso d'aya kika sani cikin kaso dubu, kuma baza ki tab'a furta kaso d'ayan nan ga kowa ba, muddun kikai yunk'urin fad'e kuwa sai dai gawarki, don haka ni gobe zan tafi gurin mijina, sai kici gaba da kula da komi na gidan, kamar yarda kikace mugun nufina ne zai kaini, to tabbas shine zai kaini, idan kin isa masoyiyar Miq ta gaskiya kina iya kub'utar da Fareesah da abin cikinta daga tarkona tun kafin na isa, ni na tafi sai kuma mun dawo. ”
Har ta juya zata fita, sai kuma ta dawo da baya tace.
"Au na manta, Camera d'in da kika saka, bata isa ta d'aukar miki komi ba akan abinda muka tattauna, shiyasa nace Khadija baza ki tab'a jaa dani ba don na wuce saninki gaba da baya, har yanzu baki gama sanin wace ce Sumayya ba, a duba camera lafiya. ”
Ta fita tana sakin murmushin mugunta, hannun Khadija na rawa ta d'auko camera da ta mak'ala jikin bango ta saita babu abinda take gani face duhu dumd'in, sai kuma taga wani irin halitta ta ciki ya k'walla k'ara yana kiran sunanta, wata iriyar k'ara ta saki, ta sume daga inda take zaune, Sumayya da taji k'arar ta saki yalwataccen murmushi.
Fareeda tana daga sashenta taji k'arar Khadija, aikwa da hanzari ta nufo sashen nata don ganin lafiya, ganin Khadijan a sume ya firgita ta,
' Ita kuwa Khadija me ke damunta a rayuwa haka, a cikin 'yan kwanakin nan duk ta firgice, ta fice hayyacinta?'
Ruwa ta samo ta shafa mata a fuskarta, wata wawuyar ajiyar zuciya ta saki, kana ta fashe da wani irin kuka, kuka take kamar ranta zai fita, Fareeda tun tana tambayarta abinda ya faru har ta zuba mata ido, kuka take sosai, kuka irin wanda ka rasa mafitar nan, ji take zuciyarta tana mata wani irin ciwo.
'Wan nan wata iriyar matace mara imani, meyasa Allah ya sanyota cikin Duniyarmu?
Ya Allah ya Ubangiji ka kawo mana k'arshenta, Allah kar ka bata ikon cikar burinta, ya Allah ka kawo silar da Miqdad zai gane ba k'aunarsa take ba, sam bata cikin jerin masoyansa itace ta farko a jerin mak'iyansa.'
Fareeda da taga tak'i yin shiru, kuma ga dukkan alamu bata k'aunar ta san sirrinta, don haka jiki a sanyaye ta tashi ta fita, sai taji tana tausayawa Khadijan fiye da yarda take tausayin kanta, ita idan bata jin dad'i gurin Miqdad tana jin dad'i gurin iyayanta, ita kuwa Khadija babu uwa ba uba, ga dangi babu dad'i, ga miji ma babu dad'i, ga kuma k'aunarsa da Allah ya jarabceta da ita.



_____________
*ENGLAND*

Kallon Fareesah yayi da ta k'ureshi da kallo, ya d'age mata gira d'aya ya k'arasa gareta, d'agota yayi ya sanyata cikin jikinshi, tana jinta a jikinsa ta saki wani irin kuka da bata san dalilinsa ba, dabar barcewa yayi gurin tambayarta lafiya?
"Nima ban san meyasa ba, amma ina jin a jikina kamar zuwan Aunty Sumayya zaizo da sabon wani lamari. ”
"Babu abinda zai faru insha Allahu, kar fa ki manta duk cikin matana babu me k'aunarki sama da Sumy, tsabar soyayyar da take mini ce tasa take matuk'ar son abinda nake so, shiyasa take matuk'ar baki kulawa, wallahi Sumayya tana sonki ni na gas gata hakan kuma bata kishi dake kamar yarda su Khadija suke kishi dake, tsananin son da take mana ne shiyasa take son kasancewa tare damu, idan ban mata abinda take soba, sai taga kamar don ita bata haihuwa ne shiyasa nake gudinta, don haka kar ki damu da zuwanta, idan tazo d'inma wata k'arin kulawa zaki samu daga gareta. ”
"To amma sai nake ganin ba ayiwa su Khadija adalci ba, in ni ka taho dani saboda haihuwa to ita fa Aunty Sumayya. ”
"Shissssss Fareesah yi bacci, kada ki saka mini ciwon kai.”
Ya fad'i hakan tare da gyara mata kwanciya a jikinsa, lamo tayi a jikinsa cikin zurfin tunani, ita dai Allah yana gani ba tayi na'am da zuwan Sumayya ba sam ².........

ALK'ALUMAN NAGARTATTU
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*


[12/2/2020/6:05PM]


*CIKIN DUNIYARMU*
1⃣
Follow me on whatpad @Rashuna

PREE PAGE
________________
*FOUR*

*KANO*

Duk yadda nakai ga juriyar kada Ummi ta ga'no ni sai da ta ga'no ni, ilai kuwa hankalinta yayi mugun tashi, ganin haka yasa na k'ara k'arfafa jikina, na nuna mata naji sauk'i, amma sai cewa tayi dole sai munje camise, nace.
"Ummi kar ki damu naji sauk'i, idan munce ma camise d'in zamu da wani kud'in to? ”
"Da kud'in awarar zamuje, ai lafiya itace gaba da komi Munassah.”
"A'a ki bassa Ummi nidai naji sauk'i, ciwon kaine kawai, shima yanzu zan siyo magani nasha, tunda idan muka tab'a kud'in awarar da me zamu juya gobe? Awarar nan da ita muke samu muna rufawa juna asiri, tunda aikin da nake shi sai wata ake biyanmu. ”
"Tom shikenan, bari na lek'a gidan Hajiya Safiya ko Baffa ne na bashi ya amso miki maganin. ”
"Tom" Nace da ita ina rik'e kaina da yake mugun sara mini, maganar Yaa Nazee ce kawai ke yawo a kwanyata, na kasa samun matsayar shin na gayawa Ummi ko kuwa?
Tana mik'a kud'in ta dawo, ta d'auko awarar da ta ajiye mini da kunu ta bani naci, babu laifi naci awarar sosai, saboda ina sonta, tana gama bani Baffa ya kawo maganin shima ta bani nasha, ina sha kuwa bacci yayi awon gaba dani, bani na farka ba sai kusan k'arfe 5:00Pm, jikina a mugun kasale na tashi, Ummi ta had'a mini ruwa me zafi da ta d'ora mini kan kwal bayan ta gama girki, wankan naje nayo abina, sai naji jikina a hankula yana war warewa, shiryawa nayi, sannan na tayar da sallah, bayan na idar ne nake cewa Ummi anyo siyayyar kayan awarane? Shine tace ai taga banjin dad'i shiyasa ta bari a wuta gobe, nace mata ai zan iya, da k'yar dai ta bani kud'in naje na siyo kayayyakin, ina zuwa muka had'u muka gyara waken nakai markad'e nan mak'otanmu, ana markad'an nazo na tace na had'a wuta na gingima tukunya akai na zuba, kasancewar ina da maka mashi ga kuma icen me ci nan da nan awarar tayi.
Ko da mukazo kwanciyar bacci haka nayi ta sak'e²n ko na gayawa Ummi abinda Yaa Nazee yace, amma kuma ina gudun kar ciwonta ya tashi, a haka dai har bacci yayi awon gaba dani.

K'arfe 11:00Am na gama siyar da awarata, ina tashi

Please Login or Register in order to submit comment