Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'aga, tare zamu tafi da Gwaggo Zulai, dattijuwar mata ce dake aiki a gidan mai tangaran d'in. Gidan da muka sauka madai daicin gida ne, falo ne a cikinsa sai two bed rooms, gidan ya tsaru iya tsaruwa, Daddy sunyi waya da Miq yace masa sai washe gari zai iso london d'in saboda wata 'yar matsala da aka samu, shikuwa Daddy yana da abinda zaiyi washe gari ko harkar makaranta ta a hannun a bokinsa ya barta, don haka daga nan London d'in sai ya sauka a England yaje yaga jikarsa da zuciyarsa ta kamu da soyayyarta tun kan ya ganta, amman bai tafi ba sai da ya bar mana komai na buk'ata. A d'aki d'aya muka kwana da Gwaggo, saboda ni ba na son kwana ni kad'ai a d'aki, a kwana d'aya da muka yi tare ta fara nuna kulawarta sosai a kaina, ko abinci da nak'i ci ma duk ta bi ta damu kanta. Ni kad'ai ce a falon, Gwaggo na kitchen na had'o mini tea ta nace sai na sha tunda nak'i cin abinci, k'ararrawa naji an kad'a ta neman izinin shigowa, tun kan naje na bud'e naji gabana ya yanke ya fad'i, jiki ba kwari na isa bakin k'ofar, d'an lek'awa na yi don naga waye, idona na sauka a kansa zuciyata ta yi wani irin harbawa, kuma kad'a k'ararrawar aka yi, hannuna na kar karwa na saka na bud'e k'ofar, yana gani an bud'e ya ja siririn tsaki yana kuma gyarawa Fareesah kwanciya a k'irjinsa............
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*


[7:32PM/15/3/2020]


Folow me on wattpad @Rashuna.

_Fitattu shida na siyarwa ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_
__________________
*TWENTY ONE*
Hanya na bashi ya huce, kaina a k'asa ba tare da na dube sa ba, sautin muryarsa na ji a kausashe yace. "Ba zama nazo yi ba.” juyawa na yi zan koma ciki, yayin da shi kuma ransa ya yi mugun b'aci, hannunsa d'aya ya saka ya fisgoni da k'arfi ya jingina ni jikin k'ofa, rintse idanuna na yi ruwan hawaye suka biyo kuncina. "Me kike ji da shi da zaki tafi ki barni a tsaye, ko an gaya miki sa'an wasanki ne ni? ” Girgiza masa kai nayi wasu sababbin hawayen na kwaranyowa bisa kuncina, wata arniyar tsawa ya daka mini gami da cewa. "Ba'a mini magana da ka, ki bud'e baki kimin magana ko yanzu na sassab'a miki.” Cikin muryar kuka nace. "Yi hak'uri. ” Rintse isonsa ya yi ya bud'e yana kau da kansa gefe saboda sam bai son ganin zubar hawayen nata, haka kawai sai yake jin zuciyarsa ba dad'i. "Bcikinani dogon bayani da zan miki game da auranmu saboda kin riga da kinsan komi, Fareesah amana ce a gurin ki, kada ki sake wani abu ya samu rayuwarta idan kwa kika yi wannan saken to ki kuka da rayuwarki, kashedi na gaba kuwa shine kada zuciyarki ta kamu da soyayyar mahaifinta,don ni bani da wata zuciya mai numfashi da ta rage mini a fannin soyayya, mahaifiyarta ita kad'aice macen da nayiwa son da bazan tab'a yiwa wata 'ya mace da ban ba, na sota fiye da so babu misali bare na nuna, don haka na yi miki alk'awarin al'amuranmu suna dai daituwa zan baki takardarki kema ki samu 'yancinki. ” Bud'e fuskar yarinyar ya yi ya k'ura mata ido wani b'ari na zuciyarsa yana jin kamar bazai iya shekaru biyar ba tare da ya sakata a idonsa ba yayin da d'aya b'arin zuciyar tasa ke gaya masa dole ne ya jajirce ya kuma cije har zuwa nan da shekaru biyar d'in ma's u zuwa ko don b'atar da tunanin Sumayya, wani kyakkyawan kiss ya sauke mata a kumatu da goshinta kana ya mik'o mini ita, hannu na saka na karb'eta ina jin wani mugun takaicinsa a raina, an gaya masa ni wawiya ce da zan bari zuciyata ta kamu da sonsa? Ko an gaya masa shi kad'aine zuciyarsa ta daina numfashi a fannin soyayya, da zuciyata zata kuma son wani da tun akan Ahmad za ta fara yadda ya matsa mini da neman soyayyata daga k'arshe haka ya hak'ura don ya kasa samun damata. "Ki kula. ” Shine abinda yace mini bayan na ansheta ya juya ba tare da ya k'ara furta ko da kalma d'aya ba, rufe k'ofar na yi na dawo ciki ido biyu mukai da Gwaggo, hannu na saka ina goge hawayen fuskata, ina tuno nasihar Ummi gareni, kamar kwa ta san wani sabon al'amarin zai tutso kai cikin duniyata, hannu Gwaggo ta mik'o mini na bata Fareesah, mik'a mata ita na yi ina zarcewa d'aki don ina buk'atar zubar da hawayen da suke mini mugun rad'ad'i a idanuwa. Washe gari Daddy yasa aka kawo mini akwatina cike da kaya na alfarma guda shida, na jikarsa guda goma na Gwaggo guda uku, ni kuma har da sabuwar wayata mai bala'in kyau har da sim a ciki, satinmu guda na fara zuwa makaranta, Gwaggo na mugun kulawa da mu tun da ta lura ba na iya cin abinci sosai da kaina ta ke bani har sai nace mata na k'oshi, a hankula na ji soyayyar Reesah na shiga raina, jinta nake kamar d'iyar da na haifa da cikina, a haka rayuwa ta fara mik'awa ina karatuna cikin kwanciyar hankali, na mai da kai sosai gurin ganin na yi abin da zanyi alfahari da shi, kuma ko da Yaa Nazee da Abbana sun dawo duniyata zasu yi matuk'ar alfahari da ni, Daddy yana yawan lek'o mu haka zaizo su sha wasa da jikarsa, har ta riga ta saba da shi sosai, shi kuwa Miq ba ma a zancensa don yanzu harkokin aikinsa ma sun ishe sa, bare kuma dama bazai k'ara waiwayen su ba har sai sun komo nigeria, tsakaninsa da matansa kuwa yana kwatanta adalci sosai, duk wani k'ok'ari na Sumayya don ganin ta kawar da hankalinsa daga kansu abin ya ci tura, duk wani tsafi da za ta yi yak'i kama sa don sosai ya tsaya kan adduoi da shan rubutun da Malam Jadda ke yi masa, inda hankalinta ya kwanta, da taga har yanzu soyayyarta na nan cikin zuciyarsa amman duk da haka sai da suka shirya wani plane d'in da zata k'ara d'aga darajarta a cikin gidan, k'imarta ta kuma fitowa, kowa da kowa ya k'aunaceta k'auna mai girma don za ta kawo hasken da dukkanin matan Miq suka gaza kawowa. Ta b'angaran Inno kuwa Miq ya k'aurace mata gaba d'aya saboda ta yi mugun matsa masa kan turawa su Mudan kud'i a Accaunt d'insu, shikuwa fir yak'i sai dai duk wata ita zai tura mata a nata Accaunt d'in, tun da ya fahimci kud'insa take so ba shi ba, duk wani asiri da take kuma bunko masa har yau Allah bai bata nasara ya kama sa ba. Shekarar Reesah uku a duniya amma Allah ya bata kafirin wayo, magana ras a bakinta kamar 'yar shekara biyar, hakanne yasa Daddy ya sanyata a makaranta, duk zaton Daddy Miq yana zuwa gurinmu, kuma ko da wasa ban bashi k'ofar da zai san Miq d'in ba ya zuwa ba, a yanzu jin soyayyar Daddy nake mai matuk'ar girma a zuciyata, jinsa nake tamkar mahaifina, don shima ya d'auke ni tamkar d'iyarsa, duk wani abu na more rayuwa yana yimana shi bare da yaga yadda nake ji da jikarsa, don wallahi ba k'arya ba ina matuk'ar k'aunar Reesah a raina don itace ta dawo da murmushi kan fuskata, ta kuma dawo da dariya kan fuskata, har na ji ina son cigaba da rayuwa tare da ita na har abada, muna waya sosai da Inna
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*


[7:4PM/10/3/2020]


Folow me on wattpad @Rashuna.

_Fitattu shida na siyarwa ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_
__________________
*TWENTY TWO*
Har take ce mini Nucy ta kirata ta na nemana aikwa nace da Inna ta turo mini number da ta kira tan, da na kirata kuwa munsha hira sosai anan take gaya mini Abbanmu ya aikowa da Abbansu wasik'a yace a bamu, ga shi yanzu ta rasa ta yadda takardar za tazo gurina, nace mata idan na dawo zan nemeta, ranar naci kuka kamar zan yi me, wa takan dai ya tabbata Abba yana raye a duniya, ko wani azzalumin ne ya raba shi da Duniyarmu ba ki d'aya, a ina yanzu yake rayuwa? Me ya hana shi dawowa garemu har ga shi Ummi ta bar Duniyarmu baki d'aya? Sai naji gaba d'aya na matsu na koma nigeria ko don naji me takardar da Abbana ya turo ta k'unsa. Karatuna ya mik'a sosai Daddy ya saya mini mota ya saka aka koya mini, yanzu a ciki nake zuwa makarantar a sauk'ak'e abina, amma fa Allah² nake na kammala karatuna na koma gida, sai ga shi cikin hukuncin Ubangiji na kammala karatuna tare da nasarori masu yawa, a lokacin Reesah na nurthry two, a washe garin ranar da muka yi graduation muka d'ungomo zuwa nigeria, mu muka fara yo gaba kafin Daddy ya taho saboda tsaro, dama mun riga mun yi sallama da shi tun a can.

Inna ta yi matuk'ar farin cikin ganin yadda na koma, alamar hutu duk ta bayyana a jikina, fatata har wani yellow² ta ke yi, yau kwananmu uku da dawowa amma bamu saka shi a idonmu ba, ashe wai ba ya gari sai jiya da daddare ya dawo. ___________
" *REESAH*” Na biyota da gudu ina kiran sunanta, don ban kula da ta fito ba sai yanzu da naga tana k'ok'arin kaiwa bakin gate.
Cak ya tsaya sakamakon jin sunan da na ambata zuciyarsa tana masa wani irin dokawa, Sumayya dake gefensa ta tsaya tana kallon yarinyar da nake k'wallawa kira zuciyarta na harbawa yayin da shikuma ya sauke idonsa a kaina, ganin irin kallon da yake min yasani nazarin kayan dake jikina, doguwar riga ce ta shaking material da ta bi jikina ta kwanta, kaina ba d'ankwali sai perking in kaina da nayi a tsakiya, saurin d'auke idonsa yayi daga kaina ya maidasa kan yarinyar da nake kira lokacin ita har ta isa gurin me gadi tana masa surutu.
'Yau tsahon shekaru kusan biyar kenan rabon da ya ganta, tun tana jaririya ya danne zuciyarsa ya raba kansa da ita dan cimma wani buri nasa'
Saurin basarwa yayi ya k'arasa ga bakin motarsa, sojan dake jiransa ya bud'e masa gidan baya ya shige, shi kuma ya zaga ya shiga ya tada motar suka bar harabar gidan, motocin da ke jiransa a waje suka bi bayansa.

Da sassarfa na k'arasa gurin me gadi na d'auki Reesah ina.
"Sai na fara d'aure miki k'afafunki tukunna zaki shiga taitayinki da fita yawo.”
Sumayya dake tsaye tun d'azu ta kasa motsi tabi bayanmu da ido cikin dokawar zuciya, har muka shige sashin da yake mallakinmu,
sashin Khadijah ta nufa fuuuuuu kamar zata tashi sama.
Ina shiga na kulle k'ofar don gudun kar ta sake fita, sannan na ajiyeta nace maza ki tafi gurin Inna, d'aki na shiga ina rik'e saitin zuciyata dake dokawa tun d'azu, yau tsawon shekara biyar kenan rabon da na sakashi a idona, magan gananusa kawai ke yawo a zuciyata.
_Mahaifiyarta ita kad'ai ce macen da nayiwa son da bazan tab'a yiwa wata 'ya mace da ban ba, na sota fiye da so babu musali bare na nuna_
Wannan maganar tafi ko wace magana yi mini zafi a zuciya kuma ban san dalilin haka ba
wani siririn hawayene ya biyo kuncina.
'Wai yaushe ne zanyi alfahari da DUNIYATA? Na taso DUNIYATA zagaye take da mutane uku, ABBANA, UMMANA, YA NAZEENA gashi yanzu babu ko d'aya a CIKIN DUNIYATA tun lokacin da na rasasu nayi bankwana da murmushi, dariya farin ciki da nishad'i har sai da REESAH ta shigo DUNIYATA.
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: .*BEBE'ARTH*


[7:4PM/17/3/2020]


Folow me on wattpad @Rashuna.

_Fitattu shida na kud'i ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_
__________________
*TWENTY THREE*
"Khadija kin ga kwa abinda na gani? ”
Da kamar Khadijan ba za ta yi magana ba, sai kuma tace. "Me kika gani? ”
"Wasu bak'in fuska na gani a cikin gidan nan mana, kuma sashin wancen munafukar matar naga sun yi.”
"To ai sai kije ki tambayi munafukar matar ko kuma ki bari in mijinki ya dawo ki tambayesa.”
"Ai bai da masaniya da zuwansu, kuma gani na yi kece me shiga gurinta zaki iya sanin ko su
waye.”
"Toh baki gani dai dai ba, don ban san da zamansu ba, yau kusan kwanana biyar rabon da na shiga gurin Inna.”
Tsaki ta ja ta fice ba tare da tace komai ba, haka kawai sai ta ji wani b'ari na zuciyarta bai yi na'am da bayyanar wa'yan nan halittu cikin duniyarta ba, bare ma da taji ana kiran sunan yarinyar da sunan da tafi tsana sama da komai a duniya, itama Khadijan tsaki ta ja, tabi bayanta da haramatsalaabinta ta d'auka ta fito ta nufi sashin Inna don ta kwana biyu ba ta lek'a ba, Innan ta samu a falo ta na cin vegetable jollof rice with fruits, sai Reesah da ke wasa a gefenta, gurin Reesah ta dosa ta d'agota tana sakar mata murmushi.
"Inna ina kika samo kyakkyawar yarinya haka? ”
Ta fad'a tana dariya, don Allah ya saka mata k'aunar yara a zuciyarta.
"Jika tace.”
Inna tace da ita.
"Allah sarki, ina Mamanta?” Ta na d'aki ta na sana'arta, uban yarinyar ne ya rasu amma har yanzu tak'i ta sakawa zuciyarta dangana. ”
"Allah sarki, Allah ya yi masa rahama.”
"Ya sunanki? Ta kalli Reesah tana tambayarta.
"Reesah.” Tace mata cikin muryarta ta yara, murmushi Inna ta yi tace.
"Sunanta Fareesah, mahaifiyarta ce me kiranta da Reesah. ”
"Allah Sarki, itace ta biyu da na sani mai sunan nan bayan murgaiya. ”
"Ehi, ni kaina sai da na tuno ta, mace mai kirki da sanin ya kamata, ita kad'aice ke shigowa muna gaisawa a kulli yaumin, ai naji mutuwa wallahi. ”
D'an murmushin yak'e Khadija ta yi, tace.
"Ai nima kawai ji nake wani sa'in ban son fita, amma ina son in dinga shigowa muna gaisawa.”
"Ai ba komai Khadija, hakanma da kike shigo mini ina jin dad'i, kin d'aukeni da mutumci ba a 'yar aiki ba, matso muci abinci.”
Matsawa ta yi, don tun da ta shigo abincin ya burgeta, kamar yarda ya burgeta a ido haka ya yi mata matuk'ar dad'i a baki tace.
"Inna ta yi dad'i wallahi sosai, haka nake so naga na iya girki. ”
"A'a toh, tun yaushe nake fama da ke ki koyi girki kink'i ki mai da hankali ki koya, a ce duk cikin ku ukun babu wacce ta iya girki sai dai yazo gurina yaci, da babu ni kuwa duk matsayinsa sai dai ya dinga yawan restaurant.”
"Wallahi Inna ina mugun jin haushin rashin iya girkina, ni kenan kullum cikin cin indomea.”
"Idan dai har da gaske kina son koyan, Munassa babu abinda ba za ta koya miki ba, don itace ma ta yi wannan girkin.”
" Kai aikuwa ta yi mugun iya girki, na yi k'awa wallahi, na manne mata kenan har sai na gwanance a fannin girki, bara naje mu gaisa. ” Ta fad'a tana nufar d'akin, murmushi Inna ta yi, tana mugun k'aunar Khadijan a ranta, kuma duk tausayinta ne ya janyo hakan.
Da sallama ta shigo d'akin, ta sameni a zaune idanuwana sun kod'e saboda kuka, amsa mata sallamar na yi, ita kuwa a ranta cewa take.
'Dole Reesah kiyi kyau, ashe haka mahaifiyarki take da bala'in kyau.'
Hannu ta mik'o mini, nima da yake na gane nufinta na mik'a mata nawa hannun.
" I am Khadija, nice matar mai gidan nan ta uku, ina son mu zama freind, Inna ta gaya mini wani abu game da ke, ina son zaki dinga koya mini girke ²."
" I am Munassah, ba matsala, duk sanda kika shirya ki mini magana. ”
"Thanks. ”
Tace da ni ta na sakar mini murmushi ta juya ta fita.



Sai bayan sallar isha'i ya shigo gidan, sashinsa ya nufa yaje ya yi wanka, sannan ya fito sanye da k'ananun kaya, yunwa yake ji sosai, hakanne yasa ya nufi sashin Inna.
Bayan sun gaisa, taga yana cil cilla ido murmushi ta yi tace.
"Ta yi bacci tun d'azu, tana d'aki. ”
Murmushin shima ya yi, ya nufi d'akin yana mamakin yadda aka yi ta san abinda ke ransa.
Ina zaune na jingina bayana da jikin gado, idanuwana a rintse suke, sai da zuciyata ta fara dokawa, sannan na jiyo dad dad'an k'amshin turaransa, ko da naji tsayuwar mutum a kaina hakan bai sa na bud'e idanuwana ba, jin shirun ya yi yawa ba shi da alamun yin magana yasa na bud'e idanuwana aikuwa suka yi kyakkyawan masauki a cikin lumsassun idanuwansa, saurin yin k'asa da nawa idon na yi ina jin zuciyata na Harbawa.
Na san d'iyarsa yazo gani, hakanne yasa na cireta daga jikina na kwantar da ita kan gado na fita daga d'akin, ina fita ya zauna kan gadon yana shafa fuskarta cike da so da k'auna da kuma mugun tausayin kansu ga baki d'aya, d'agota ya yi ya rungumeta a k'irjinsa ya jima sosai a haka daga bisani ya kwantar da ita ya fito, ina ganin ya fito na ta shi na koma ciki.

White macaroni and vegetable sauce with drink, Munassa ta yi, yana fitowa Inna ta zubo masa, dama saboda shi Innan tace wa Munassan ta yi, tun a lomarsa ta farko ya san d'an d'anon abincin ya sauya, amma baice komai ba yaci gaba da cin abincinsa, sai da ya kammala ya d'an huta kana ya yiwa Inna sai da safe ya fito, phart d'insa ya koma don yana da aikin da zaiyi a lap top d'insa, yana shiga kuwa ya duk'ufa sosai akan aikinsa, da yake kwanan Sumayya ne itace ta shigo cikin wata fitinanniyar rigar barci, ganin aiki yake yasa ta nemi guri ta kwanta, don ta san ba ya had'a komai da aikinsa.




******
Wata shak'uwa ce mai k'arfi ta shiga tsakanina da Khadija, girkuna kala² nake koya mata kuma ta mai da hankali sosai, Fareeda kuwa ban santa ba ma, ban sani ba ko ita ta sanni, Sumayya ta san dalilin zuwana gidan da kuma ni d'in wace ce, abinda ke mugun damunta shine ganin yadda mijinta ya d'auki soyayyar duniya ya d'orawa Reesah, idan idonta ba gizo yake mata ba wani zubin Reesah har kama take mata da murgarya Fareesah hakanne yasa ta d'auki tsanar duniya ta d'ora mata, ga shi duk inda Miq yake tana manne da shi sai dai idan ba ya gida, in tai masa maganar sai yace sunan zumarsa da take da shine ya janyo komai, nan fa hankalin Sumayya ya yi k'ololuwar ta shi musamman yanzu da ta lura in ya shiga cin abinci gurin Inna yana mugun dad'ewa akan wanda yake yi da, hakanne yasa take zargin wani abu na afkuwa tsakaninsa da Munassa, duk da ta yi masa tsafin da babu shi habu k'ara aure a duniya amman haka kawai take jin hankalinta ya gaza kwanciya, ta ma fara zargin akwai wata b'oyayyar manufar da ta saka suka shigo musu duniyarsu, kuma ta d'auki k'udirin binciko manufarsu ko ta halin k'ak'a.
Wata tsadaddiyar makaranta, mai matuk'ar k'ok'ari Daddy ya saka Reesah, Faisal ne ya yi komai da komai na makarantar ta ta, ya saka shi ya kawo mini wata arniyar mota a ciki nake kaita na d'aukota don ban yadda kowa ya kaita ba, amma Miq yaso na bari a dinga kaita, ba ya k'aunar fitar da nake yi sam, amma ya rasa ta yadda zaimin magana kar na d'auki zancensa da wata manufa, hakanne yasa ake bin bayana idan zan kaita na d'aukota saboda tsaro.
Yau mukai da Nucy naje filin jirgi na anshi takardar da Abba ya kawo mini, ta aiko wani d'an uwansu da zaizo katsinan, ta ba shi number wayata nima ta bani tasa, ina d'aukan Reesah daga makaranta na zarce filin jirgi, ashe wanda Miq ya saka ya dinga bin bayanmu yana can waya bai lura na ja motata na yi gaba ba, ina zuwa filin jirgin, jirginsu na sauka, tsayawa na yi har sai da ya sauko, layina ya fara nema yace mini ya sauka, nace nima ina cikin filin jirgin, gurin da nake na kwatanta masa yazo, bayan mun gaisa ya bani takardar na yi masa godiya mukai sallama na taho, wata mota da ban naga tana ta binmu a baya, gabana ne ya yanke ya fad'i, ga Reesah ta cikani da uban surutu, k'ara gudu na yi da tawa motar ba sai naga itama motar ta k'ara gudu ba, wani irin murd'awa cikina ya yi na mugun tsoro.......



ALK'ALUMAN NAGARTATTU.
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*


[7:4PM/20/3/2020]


Folow me on wattpad @Rashuna.

_Fitattu shida na siyarwa ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_
__________________
*TWENTY FOUR*
Gudu nake sosai yayin da k'irjina ke kuma gudun lugude, ga gari ya yi bak'ik' k'irin ya had'e murtuk ruwa na son sakkowa, ina gano motar ta mudubi ta na k'ara gudu, wani layi kawai na gani na yanka cikinsa da gudu ba tare da na san ina zan b'illa ba in na bisan, ina ta sharara gudu sai da na yi nisa sosai da naga basa bina sai na tsaya, fitowa na yi na d'auki Reesah da ta yi bacci ta gaji da mini surutu ba na kula ta, rufe motar na yi nai mata key, tafiya na dinga yi a k'afa, sai da na tabbatar na yi nisa sosai, ga kuma ruwa da ya fara sakkowa kuma na rasa 'yar mafakar da zan fake, ga shi ba na son ruwa ya jik'a mini Reesah ko kad'an, wani d'an kango na gani na shiga ciki sai naga ba wani d'an gurin da zan samu mu fake, ga shi na fara jiyo k'arar mota kamar ta na yowa gurin, lafewa na yi daga wanlafiya lungu, na saka Reesah a ciki na yi mata rumfa dan kar ruwa ya jik'ata, duk da haka sai da na cire hijabin jikina na lullub'eta da shi, haka ruwa yaci gaba da sauka a kaina ga shi ba d'an kwali a kaina.


"Hello Hajiya, yarinyar nan fa ta shiga layin da idan muka shigesa akwai babbar matsala, saboda tun tuni ta fuskanci muna binta a baya. ”

Rai a b'ace Sumayya tace.
"Garin ya kuka yi saken da ta gano kuna biye da ita? So na yi ku taka mini kansu da mota gaba d'aya. ”
"Ai Hajiya Yarinyar tana da matuk'ar wayo ne.”

"To dai duk yadda za'ai kar ku bar bakin layin na tabbata za ta fito don ba ta san gari ba.”
"Ok to Hajiya an gama.”
Zagaye d'akin ta shiga yi ta na addu'ar Allah yasa ta fito su kama ta, ko kuma su b'ata gaba d'aya a huta, don ta san muddun ta tsira ta dawo gida ba za ta kuma saken da zata fita ita kad'ai ba.

Inna ta kasa zaune ta k'asa tsaye, hankalinta idan ya yi dubu ya ta shi, duk da tace mata za ta biya filin jirgi ta anshi sak'o ai yaci ace

Please Login or Register in order to submit comment