Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'aya daga ciki, ko kuma dukkaninsu, ku tuntub'emu ta wannan layi:
07067364721

_______________
*ELEVEN*

*KANO*

Hannunta na kama na d'aga sai naga ya saki ya dawo k'asa, wani kuka ne ya zo mini me d'aci, kuma ya tsaya iya mak'o gwaro, daga haka nidai ban san me ya kuma faruwa ba, na dai farka na ganni jikin Inna tana rik'e da carbi har lokacin hawaye na zuba a idonta, sai mutane dake zaz zau ne a d'akin, bin kowa nake da kallo kamar wata sokuwa, anan mukai ido hud'u da su Aysha suka cemini.
"Sannu Teemah ya hak'uri? ”
Rintse ja ja yen idanuwana na yi ya yin da k'wal k'walwata ta tuna mini abinda ya faru, wani d'aci zuciyata take mini, k'irjina nayi mini zafi da rad'ad'i, babu wanda zai fuskanci irin yanayin da nake ji sai wanda ya d'and'ani irin abin da na d'an d'ana, hannun Inna na kama na rik'e k'am nace.
"Inna Ummi”
Sababbin hawaye ne suka biyo kuncinta na mugun tausayina tace.
"Kiyi hak'uri Munassah, Allah ya saka mana gado me wahala, duk tsananin k'aunarka da mutum, dole wata rana sai ya tafi ya barka, kuma kaima irin ranar tana nan tana fakon ka, Ummi ta tafi inda ba za ta tab'a dawowa ba, har an riga an dawo daga kaita, addurmu kawai ta ke buk'ata a halin yamzu tun daga yanzu ya kamata ki fara aiki da nasihar da ta bar miki. ”
Kau da kaina gefe nayi, idanuwan gaba d'aya sun soye hawaye yak'i zuwa, kawai tasbihi nake ja a zuciyata.
'Wai meyasa Ummi ta tafi ta bar Duniyata? Bayan ta san Abba da Yaa Nazee sun dad'e da barin CIKIN DUNIYARMU, shine itama ta ta fi ta barni, yanzu ya take so na yi da rayuwata, dama ashe ta san mutuwa za ta yi shi ya sa d'azu ta dinga mini nasiha?
Ya Allah ga baiwarka me raunan niyar zuciya, Allah ka jib'anci lamurana, ka bani ikon cinye dukkanin jarabawo yin da nake fuskanta cikin rayuwata, Allah Ubangiji ka sa hakan shine hanyar shigata jannatul firdausi, Amin ya Allah'
Sai a lokacin wasu siraran hawaye suka biyo kuncina, na kuma rintse idona nak'i yadda na bud'esa ko kad'an, gani nake idan na bud'e zanga Ummita, wayyo rayuwa, shikenan ta tafi itama, ya Allah, na kuma furtawa a zuciyata don gudun yin sab'o, yayin da duka 'yan d'akin tausayina ya dinga tsin tsinka musu zuciya.




______________
*ENGLAND*
A hankula ya tura k'ofar ya shiga, a kwance ya hangota an gark'ama mata wannan robar, ga na'ura a gefenta ta nan ake ganin numfashinta, zuciyarsa ce ta kuma tsin tsinkewa, tausayi da nadama gami da zazzafar soyayyarta su suka kuma lullub'esa, kamar mara laka haka ya taka ya isa gaban gadonta, hannunta ya kama ya rik'e k'am yana kallon fuskarta, gani yayi fuskarta ta kuma yin kyau, tana bada wani annuri, ga wani murmushi da take saki, kamar murmushin bankwana, baiyi aune ba, sai tsintar kansa yayi yana tsiyayar hawaye, wata takarda ta saka masa cikin hannunsa, sannan ta sakar masa sanyayyan murmushi gami da matsa hannunsa, ji yayi k'irjinsa ya buga a lokaci d'aya, yayin da ita kuma tayi wata shak'uwa, idanuwanta suka k'ak'k'afe na urar da ke gefenta ta tsaya cak da aiki, amma murmushin dake fuskarta bai b'ace ba ko kad'an.



Kuyi hak'uri da wannan, nasan zaku ce yayi muku kad'an, wallahi kamar na kece da kuka haka na rubuta wannan page d'in.

ALK'ALUMAN NAGARTATTU.
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*


[25/2/2020/6:30PM]


*FITATTU SHIDA*

*CIKIN DUNIYARMU*
BEBE'ARTH
*HASKE A DUHU*
Aisha M Mahmud
(Meeesherh lurv)
*DUHUN DAMINA*
Maryamerh Abdul
(Kwaiseh)
*SARA DA SASSAK'A*
Qurratul'ayn
*ZAMANINA NE*
Munayshat
*GASKIYA D'AYA*
Asisi B Aliyu



Fitattu 6 na siyarwa ne,
Idan kuna buk'atar d'aya daga ciki, ko kuma dukkaninsu, ku tuntub'emu ta wannan layi:
07067364721



_______________
*TWELVE*

Ba shi kansa ba hatta jinin jikinsa ji yayi ya daskare gaba d'aya, har doctor d'in ya shigo, su dama sun tabbatar da ba za ta yi tsawan rai ba, hakanne ma yasa ba'a fita da ita d'akin hutu ba, jan zani yayi ya rufe mata fuska, har lokacin Miq ya kasa ko da k'wak' k'waran motsi, Nurse ce ta shigo ta k'ofar baya hannunta d'auke da jaririya nad'e da shawul fari k'al, karb'arta doctor d'in ya yi ya d'ora ta kan cinyarsa, sai a lokacin doctor ya lura da suman da Miq d'in yayi, d'aukar jaririyar yayi ya mik'awa nurse d'in ita yace ta tafi da ita, sannan ya shiga bawa Miq d'in taimakon gaggawa bayan ya adana masa takardarsa, ganin duk taimakon da ya basa amma bai farfad'o ba, sai ya gangarosa akan gadon marasa lafiya don ya canja masa d'aki, anan ne Sumayya dake tsaye da gawar jaririyar farin ciki fal ranta, tun kan ma taji mutuwar Fareesan, amma kuma ta d'auko damuwa sosai ta aza bisa fuskarta, hankali tashe ta tunkari likitan tana tambayarsa me ya faru, shi kuma a lokacin ya kira ma'aikatan asibitin sun gungura gadon da miq d'in ke kai, kallonta yayi cike da tsana, amma ya shanye yace.
"Ki kira can gida nigria ki sanar musu mutuwar Fareesah da abinda ta haifa, na saka a nema muku ticket kafin nan kan dare zaku isa nigeria, Miq kuwa ina jin sai nan da kwana uku zai iso, duk wanda ya tambayeki shi ki gaya masa haka, yanzu ki bada gawar yarinyar za'a had'ata da ta mahaifiyarta, kije gida ki had'a muku kayanku.”
Yana kaiwa nan yabi bayan inda aka nufa da Miq don ya ceto rayuwarsa, yayin da Sumayya tayi zaman 'yan bori tana risgar kuka wiwi² sai da tayi me isarta, sannan ta rarrashi kanta ta mik'e, mota taje ta shiga ta nufi gida, wayar Mom ta fara kira ta yi mata albishir, me makon tayi salati sai ta saki wata uwar shewa, kashe wayar Sumayya tayi, haka kawai kuma sai taji wani b'ari na zuciyarta ba ya farin ciki da mutuwar Fareesan, inama kawai ta sani d'an cikin nata ta kashe kamar yadda ta ke wa sauran, wayar Khadija ta kira ta sanar mata, kuka Khadijan ta fashe dashi ta sume a zaune, Dad ta kira ta sanar da shi mutuwar, shi kuma a lokacin yana shirin shiga jirgi zai isa nigeria, saboda a yaune Allah ya bashi nasarar ciro itacen bishiyar, sosai mutuwar Fareesan ta dake shi, duk tsanin son ganin jikansa da yake son yi, sai yaji ko kad'an bai damu da mutuwarsa ba, kamar yarda ta mutuwar Fareesan ta dake sa, inama iya jaririn aka d'auke aka bar mu su Fareesan, bai aune ba sai ji yayi hawaye na sauka akan kuncinsa, wayar mahaifin Fareesan ya laluba don ya gaya masa mutuwar, duk da bai damu da rayuwarta ba, matarsa ta raba su.




*KATSINA*
G.R.A
Gida ya cika damtsan da 'yan uwa da abokan arzik'i, domin mutuwar Fareesah ta zaga dangi, kowa ya iso ana jiran isowar gawarta, masu kuka nayi, masu farin ciki nayi, mahaifiyar Miq da danginta murna suke da mutuwarta, a cewar su itace tabi ta mallake Miq da dukiyarsa, yanzu dai gashi ta bar musu cikin duniyar, sai su kwashi abinda suke so, sai magariba gawar Fareesah ta iso nanfa gida ya k'ara b'arkewa da koke² ma'aikatan gidan kaf kuka suke da mutuwar Faresah, domin ta kasance me matuk'ar alheri a garesu, Khadija kuwa har aka yiwa Fareesah wanka ita da jaririyarta aka sallacesu ba ta san inda kanta yake ba.

Jama'a dai masu raka ta gidanta na gaskiya Fareesah ta same su, sai fatan dacewa da gidan aljanna, domin ta samu shaidu a bakin mutane da dama, mahaifinta yaji mutuwar d'iyar tasa sosai, har sai da tsimin soyayyarta ya taso masa, yayi kuka sosai na tunowa da irin wahal halun da tasha a sanda tayi rayuwa a inuwarsa, har sai da Dad ya cirota daga k'angin rayuwa ya had'ata aure da d'ansa, gashi yanzu ta bar duniyar baki d'aya, sam bai rik'e amanar da Allah ya bashi ba ta dalilin kuma makirar mace da ya ja jibowa kansa bala'i.

Daddy da mahaifinta su suka dinga karb'ar gaisuwa a bakin mutane tunda Miq ba ya nan, tun da Khadija ta far fad'o tak'i sakin jikinta, mutuwar Fareesah sosai ta girgiza duniyarta, Sumayya ma tana nuna damuwarta a fili don cire zargi daga idanuwan mutane, a haka dai suka ci gaba da kar b'ar gaisuwa har aka yi sadakar uku babu labarin Miq.





********

*KANO
Tun ranar da Ummi ta rasu, rabona da d'an d'ana abu kenan a bakina, bana sha'awar komai dake cikin duniyar nan, babu kuma wani abu da zance yana bur geni a cikinta, lallami da nasihai ba wanda Inna ba ta yi mini ba, amma haka ta hak'ura don nak'i cin komai, ban da ruwa da nake sha, shi ma kad'an ne ke tafiya, sosai ake zuwar mana gaisuwa, 'yan Teemah Nazz kuwa babu wanda yazo in kika cire Baffa Amadu da matarsa da kuma Nucyy, itace k'awata kuma aminiyata a sanda mukai rayuwa a cikin gidan Teemah Nazz, sun tausaya mini sosai, da kuka muka rabu da Nucyy, ta karb'i number Inna saboda gudun wata rana, ni dama yanzu bani da wata waya, don bani da nutsuwar yinta ma.

Sai a yau da akayi sadakar uku sai ga Baffa Sule, yace zuwa yayi ya d'aukeni wai Hajiyar Kaduna tace a bata ni, Inna tayi jan ido tace ba inda zanje, ko Hajiyar makka ce ba ta kaduna ba, amanata aka bata don haka babu wanda ya isa ya karb'e ni a hannunta, baran² dai sukayi da Inna har yace mu fice masa daga gidansa, hakanan dai muka d'ebi abinda zamu iya d'auka a cikin gidan muka fito ina wai wayen sa, domin anan ne na rasa Ummita.

Yamma lis muka shiga motar katsina, ku gano mini sanda zamu isa, kifa kaina nayi na dinga risgar kuka wanda ya haddasa mini ciwon kai har da zazzab'i me zafin gaske, kan muci rabin tafiya ma na fara fita daga hayyaci na........



ALK'ALUMAN NAGARTATTU.
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*



[27/2020/9:50PM]


_______________
*THIRTEEN*

*ENGLAND*
Idan ya farka fusge² kawai yake yana wata iriyar firgita, hakanne yasa Doctor Hisham yayi masa alluran bacci masu matuk'ar k'arfi, wanda har sai da ya yi kwana uku kafin yasan inda kansa yake, a hankali ya bud'a idonsa da ya ke jin yayi masa matuk'ar nauyi, jin sa ya ke ma kamar ya kumbura, rik'e saitin zuciyarsa ya yi da ta ke masa rad'ad'i.
'Yanzu shi kenan Fareesah ta bar duniyarsa? ta tafi inda ba za ta tab'a dawowa garesa ba har abada, ta kuma tafi ta bar shi da gib'i a zuciyarsa, domin rashinta garesa hakan zai dinga azabtar da ruhinsa, Fareesah da ban ta ke a cikin zuciyarsa da ba zai iya misalta muku yarda ta ke ba, bai kuma sanin ta yi nisa cikin zuciyarsa ba sai da ya tabbatar da ya yi rashin ta gaba d'aya a cikin duniyarsa, wayyo mutuwa! Me ya sa ba'a shawara da ke ne? Dan da kinyi shawara da ni ba zan bari ki d'auke mini Zumata ba, ni zance ki fara d'aukewa ita ki barta, ya Allah'
Ya fad'i hakan a can k'asan zuciyarsa, Dr.Hisham ne ya shigo, murmushi yayi don ganin ya farka, shi kuwa Miq ko kallon inda ya ke bai yi ba, toilet ya shiga ya had'a masa ruwa me zafi² don yaji dad'in jikinsa, da lallami da lallamawa ya samu ya shiga wankan, tun da ya fito daga wankan jallabiya kawai ya zira, ya jero sallolin da ake binsa, yana kuma kaiwa Allah kukansa, bayan ya idar ya jingina da k'arfen gadon, sai a sannan yaji hawaye masu matuk'ar d'umi na sauka akan kuncinsa, tausayinsa ne ya lullub'e Dr Hisham, lallai ya kamata yayi kuka, domin Allah ya d'auke masa macen da tafi soyuwa a ransa, tun da soyayyar da ya ke wa Sumayya ba daga Allah take ba, soyayya ce ta sihiri wacce take k'ok'arin juyar masa da k'wak'wal wa, me k'ok'arin saitasa a hanya ga shi kuma sun raba ta da duniyar baki d'aya, amma kuma ta bar abin da zai zame musu izina, wanda take fatan sanadiyar kasan cewar ta ne zai kawo kawo sauyi cikin duniyar Miq baki d'aya.
Waya ya kira, yana ajiye wayar sai ga wata nurse ta shigo d'auke da jaririya a hannunta tana nad'e da wani shawul pink me matuk'ar laushi, kar b'arta Dr. Hisham yayi, nurse d'in ta juya ta fita, kallon Miq d'in yayi da ya tsunduma cikin kogin tunani, sai ambaliyar hawaye ake akan fuskarsa kamar wani mace, d'ora masa jaririyar ya yi akan cinya, d'agowa ya yi ya kallesa ya kuma kalli abinda ya d'ora masa, alamu yana son k'arin bayani, takardar da Fareesah ta bawa Miq da Dr.Hisham ya d'auke masa, ita ya d'auko ya basa kayansa, karb'ar takardar yayi yana war wa re wa, sai a lokacin ya tuna da Fareesah ta dank'a masa takarda a hannunsa, rungume jaririyar ya yi a k'irjinsa, yana jin soyayyarta na huda duk wata k'ofa ta zuciyarsa duk da bai san jaririyar waye ba.
_Zumana, na san a san da zaka karanta sak'ona na riga da na jima da barin duniyarka, dan haka ina me neman afuwarka idan har na tab'a sab'a maka a zamana tare da kai._
_A yau Allah ya azurtamu da samun k'aruwa ta 'ya'ya biyu duk mata, kuma da kaina na haihu ba tare da an mini aiki ba, amma yarinya d'aya ba tazo da rai ba, ni na rok'i abokinka Doctor Hisham da yace yarinyar da na haifa ta mutu, kar a san 'yan biyu na haifa, saboda idan mak'iyanka suka san da rayuwarta to itama zasu kasheta ne kamar yarda suke kashe mana 'ya'yan da muka haifa_
_Na san baza ka yadda da magana ta ba, amma Sumayya tana d'aya daga cikin mak'iyanka, ba zance itace take kashe mana yaranmu a baya ba, saboda ba ni da wata hujja k'wak' k'wara, amma ina shaida maka itace ta zuba mini magani a tuwona dan naci na mutu ni da abinda ke cikina, ka duba camera da nace maka na saka za kaga komai, kayi bincike sosai akan mutanen dake zagaye da rayuwarka, ta hakanne zaka gano makasanka, bance ka aminta da kowa ba, ga yarinyarmu nan ka kula da ita kamar ina raye, kar ka bari tayi maraici ko kad'an, kuma ban yarda da kowa ya san da rayuwarta a duniya ba har sai asirin makasan babanta sun bayyana, Daddy kad'ai na aminta da ya san da rayuwarta a duniya, idan ta girma ka bata labarina ka gaya mata ba a son raina na tafi na barta ba, da zab'i aka bani bazan so na tafi na barta cikin tsumman haihuwa ba, ka gaya mata ina sonta, itama ta rayu da soyayyata._

Tun da ya fara karantawa yake zubar da zafa fan hawaye, Dr Hisham yace.
"Bayan ka kawo ta, na samu na ceto rayuwarta, sai kuma haihuwa ta tawo gan ga² duka 'ya'yan biyu a lokaci d'aya suka fad'o, ni na tabbatar da d'aya ba tazo da rai ba, shine ta rok'e ni akan nace ita ta haifa kuma ba tazo da rai ba, ita kuma d'ayar aka fita da ita ta k'ofar baya, takadda da biro tace na bata don tana jin kamar mutuwa zatayi, tana cikin rubutun num fashinta ya fara ciccijewa, shine na saka mata robar shak'ar numfashi, tun da naga tana ta yafitar hannu nasan kai take so na kira mata, hakanne yasa nace kazo tana nemanka, abinda yasa kwa nace maka aiki za'a mata, don na d'auke hankalin Sumayya ne don tana da matuk'ar wayo da dabara, ni kaina na sha gaya maka ban yarda da Sumayya ba, amma duk sanda zan kawo maka maganarta da fad'a muke k'arewa, idan da baka tashi ka binciki me ke faruwa da rayuwarka ba, ka tashi tsaye yanzu don ganin rayuwar jaririyar nan cikin duniyarka....... ”





ALK'ALUMAN NAGARTATTU
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*



[6:37PM/1/3/2020]


_______________
*FIFTEEN*

Motarsu zata shiga cikin gidan kenan aka kira wayarsa, ganin Daddy ne me kiran ya sa ya yi picking da hanzari.
"Sadauki, idan ka iso kafin kaje gida ina son ka fara biyowa ta gurina. ”
"Toh” Yace masa ba tare da yace masa ya riga da yaje gida ba, yacewa driver d'in nasa me suna Jhon.
"Mu juya k/durbi.”
K'ok'arin kwana ya fara yi da motar, yayin da motocin da ke biye da su suma sukai kwana suka mik'i titi, sun san bazai huce Daddy ne yayi masa kiran gaggawa ba.
Tunkan su iso me gadi ya riga ya wangale musu gate, saurin bud'e masa motar aka yi ya fito cike da k'asaita, fuskar nan kamar hadarin kaji, cikin gidan ya dosa shi kad'ai ba tare da wani ya bi bayansa ba, saboda sun san ba ya son hakan, suna gama aikin sune yayin da ya shigo gida.
Mom ya tarar a falo, tun da ta jiyo jiniyarsu zuciyarta ta gama b'aci, wata muguwar tsanarsa take ji tana taso mata amma ta yi k'ok'arin danne ta tun kafin ya shigo, hannu ta bud'e masa kamar yadda ta saba a duk sailin da ya yi tafiya, murmushi yake ya isa gareta, kamar yadda itama ta d'auko murmushin k'arya ta aza bisa fuskarta, rungume shi tayi tana shafa kansa.
"Welcome My Son.”
Sannan ta karyar da muryarta gurin fad'in.
"Ya k'arin hak'urinmu?”
Barin jikinta ya yi, yace.
"Alhmdlillh Mom, na sameku lafiya? ”
"Lafiya lau. ”
Tace tana jan hannunsa zuwa saman Daddyn, kallonta kawai Daddy yake, yadda ta k'ware da nuna yaudararriyar soyayya, murmushi yayi yana kawar da damuwar da ke ransa, sai da suka zo har gaban Daddyn sannan ta saki hannunsa, ta juya tana bari ta saka a kawo masa abin motsa baki, durk'usawa yayi gaban Daddy yana gaishe shi, hannu ya saka yana shafa kansa yace. "Allah ya yi maka albarka Sadauki, ya k'arin hak'urinmu?” "Amin ya Allah Dad, hak'uri Alhamdlillah.” mik'ewa Dad d'in ya yi yana me d'aukar hularsa da ke kan kujera yace. "Tashi muje fita zamui.” Ba tare da ya tambayeshi inda zasu ba ya mik'e ya biyo bayansa, sun fito kenan ita kuma Mom zata shigo da tray a hannunta sukai kacib'is, damuwa ta d'ora kan fuskarta gami da cewa. "Ya zaka fito bayan baka motsa baki ba? ” zamu fita da Dad ne, amma ki ajiye mini in na dawo zanci, kamar sakara haka ta bisu da kallo ba tare da ta tambayi Dad d'in inda zasu ba, sab'anin da da ko wani hali su biyun suke ciki a gabanta za'a kashe matsalar, babu wani sirri tsakanin Daddy da Miq wanda Mom bata sanshi ba, zuciyarta ce ta kasa nutsuwa har sai da ta kira wayar Sumayya ta gaya mata abinda ke faruwa, Sumayya tace. "Shiyasa kenan bai shigo ba, ina ta zaman jiransa, to ma dai ko me suke k'ullawa dole mu sanshi, tare da yaransa suka fito? ” "A'a naga motar Dad d'in suka shiga yanzu suke k'ok'arin fita. ” "Ok tom bari na saka Rahama ta taresu ta bi bayansu don ta gano mana inda zasu. ” "Allah yayi miki albarka. ” Mom tace tana ajiyar zuciya, sai taji hankalinta ya d'an fara kwanciya ta kuma cewa. "Amma sai kince ta lura fa sosai kar wannan kumurcin ya gano ta. ” "Kar ki damu Mom Rahma ta gwanance a bin mutum a baya ba tare da ya ankare shi take bi ba.” "Tom shikenan maza kirata naga sun fita yanzu. ” tana gama fad'in haka ta datse layin ta zauna kan kujera tana dafe kai. Daddy ne ke jan motar Miq na gefensa suna hirarsu ta d'a da mahaifi, wanda ma mafi akasari akan aikinsu suke tattaunawar,a haka suka gangaro kan mutuwar Fareesah, anan ya zayyanawa Daddy duk abubuwan da suka faru. Tun isowar su babban titin da zai kar kasa su gida hud'u yake ankare da wata mota dake bin bayansu amma kuma bai gayawa Dad ba, duk yadda akayi me bin bayan nasu k'wararre ne, yasan abinda yake yi, murmushi kawai ya saki ya turawa Faisal sak'o ta waya. " _Kuzo tare da wasu mutanen, amma kar ka kira su john su na barosu gida su jirani na dawo, muna kan titin UMYUK wata mota ce ke bin bayanmu, ina so ku gano mini mutumin dake cikin motar kawai, motar bak'a ce k'irar venza amma an cire number ta_ Cigaba sukayi da hirarsu da Dad hankali kwance, shi kuwa Faisal yana ganin sak'on suka bazamo suka taho, kar kasuwa suka yi har suka cimmasu, suna ganin motar su Miq ta huce suka had'a wani uban goslow, dukan setiarin Rahma tayi cike da mugun b'acin ran ganin abinda ke faruwa, gashi har motar ta shige ta. Ji tayi ana k'wank'wasa glass d'in motarta, zuge glass d'in tayi, ganin mutumin dake tsaye gabanta sai da k'irjinta ya buga. "Hey Madam, ina number motarki? ” ya fad'a da wata iriyar muryarsa da kaji ta kasan bai iya hausa ba sosai, d'auko number motar ta yi ta mik'o masa gami da cewa. "Cirewa ya yi zanje yanzu a saka mini. ” bai yarda ba sai da ta d'ebo masa takardun motar dukansu ya duba sannan ya bata, Faisal yana gefe yana ganinta ya ganeta, wani murmushin takaici ya saki, don ya san Sumayya ce ta saka ta, amma har yanzu mai gida yak'i fahimtar wani irin zama Sumayya take yi dashi. Ko da goslow d'in ya ragu kwata² Rahama ta rasa wata hanya su Miq suka bi, haka ta juyo cike da sanyin guiwa, ta kira Sumayya ta sanar mata, ita kanta Sumayya ba taji d'ad'i ba sam, addu'arta ma Allah yasa ba ganowa Miq d'in ya yi ana binsa a baya ba. Gurin Malam Jadda su Daddy sukaje, ya basu addu'oi masu k'arfi da zasu lazimci yi, ta hakanne ragowar tsafin dake jikinsu zai sakesu kuma ko da wani aka yi musu bazai shige su ba, sai da ya basu rubutu suka sha a gurin, saboda gudun kar su tafi dashi matansu su gano suna neman magani, godiya suka yimasa suka ajiye masa alheri me yawa, Daddy yaji dad'in maganinsa saboda yaga canji sosai gurin Miq, tunda har ya bud'i baki yace yana zargin Sumayya da mutuwar Fareesah, ai kuwa an samu babban cangi, kuma har ya iya b'oye mata yarinyar da aka haifa masa tana raye, sakamakon da da duk haihuwar

Please Login or Register in order to submit comment