Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi tana jujjuya maganar da na gaya mata, tabbas tayi zaton hakan, duba da yadda ba suga gawarsa ba, zuwa kawai akai aka sanar da mutuwarsa, to shin yana in me yasa akai musu k'aryar ya mutu? Duk yadda akayi akwai wani abu a k'asa, tasan irin mugunta ta Baffa Sule, babu abinda bazai iya aikatawa ba don cikar burinsa, zata iya yuyuwa ma da bakinsa a sharrin da akawa Nazir, tabbas zata iya yuyuwa hakanne, don jin amsarta kuwa ya zama dole ta jure taje ta gano Nazir, domin jin wasu amsoshin daga bakinsa.
Wannan tunani da tayi shine dalilin da yasa tace gobe muna sayar da awara zamuje gurinsa, aikuwa washe gari mukai sa'a awararmu ta k'are tun k'arfe goma na safe, aikuwa muka shirya muka tafi.
Tun a runfar da ake zama Ummi ke sharb'ar kuka tana sharewa, nikuma sai yau Allah yasa zuciyata ta dake, me karb'ar sunane yazo na gaya masa sunan wanda muka zo gurinsa, can jimawa sai gashi yazo, yace mana wanda mukazo gurinsa an canza masa prison, nace wacce aka kaisa, yace suma basu sani ba, tun a gurin Ummi tace bibbiyu take gani, ji take kamar ana jujjuyata, nima dai dauriya kawai nake, a haka dai Allah ya kaimu gida lafiya, kamar jira ake mu shiga Ummi ta yanke jiki ta fad'i, kanta nayi ina kiran sunanta gami da sakin wani marayan kuka......


*HASKE A DUHU*
Aisha M Mahmud
(Meeesherh lurv)
*DUHUN DAMINA*
Maryamerh Abdul
(Kwaiseh)
*CIKIN DUNIYARMU*
BEBE'ARTH
*SARA DA SASSAK'A*
Qurratul'ayn
*ZAMANINA NE*
Munayshat

K’ungiyar Nagarta na farin cikin sanar da ku cewa zaku fara samun dukkan litattafan nan a farashi mai sauk’i wanda muke baku tabbacin babu asara cikinsa.
Litattafai ne da suka tara d’umbin ilimi, fasaha, tausayi, soyayya da duk wani abunda rayuwa kan iya tunkud’awa a babin d’an Adam.
Bamu baku tabbacin zallan farinciki a ciki ba, haka zalika bamu baku ta akasin haka ba. Ku yi tsammanin samun tirka-tirkan rayuwa a wadan nan litattafai, tabbaci guda da zamu iya mika muku, shine Zallar ilimi.

Zaki samu dukkaninsu akan 500, d'aya 200,biyu 250, uku, 350, hud'u 400, biyar 450.

Ku tuntub’emu ta wannan layi don tura katin waya:-
07067364721
Ku tura kudi ta wannan lamban akawun:-
Firdausi Salisu Aliyu
0430001991
GTB
Sannan a turo da tabbacin biya ta wannan lamba:-
07067364721
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*


[22/2/2020/5:53PM]


*FITATTU SHIDA*

*CIKIN DUNIYARMU*
BEBE'ARTH
*HASKE A DUHU*
Aisha M Mahmud
(Meeesherh lurv)
*DUHUN DAMINA*
Maryamerh Abdul
(Kwaiseh)
*SARA DA SASSAK'A*
Qurratul'ayn
*ZAMANINA NE*
Munayshat
*GASKIYA D'AYA*
Asisi B Aliyu



Fitattu 6 na siyarwa ne,
Idan kuna buk'atar d'aya daga ciki, ko kuma dukkaninsu, ku tuntub'emu ta wannan layi:
07067364721


PREE PAGE
_______________
*NINE*
Cire Fareeesah yayi daga jikinsa ya mik'e a hankula yaje ya bud'e mata k'ofar, tana ganin shine ta fad'a jikinsa gami da sakin kukan munafurci, rik'ota jikinsa yayi yana tambayarta lafiya, cikin kuka tace.
"Nemanka nake tayi tun d'azu, kayi tafiyarka ka barni cikin yunwa.”
Shi wallahi ya manta da wani abinci ma, kansa ya shafa yace.
"Ai muna da abinci a kitchen muje na baki.”
Ya ja hannunta zuwa kitchen d'in, ko da yaje sai ya tarar babu abincin sai Left over tuwo nd miyar kuka, kawai, kuma shima kad'an ne, yasan Fareesah ce ta ajiyesa zata ci, don haka sai yace mata tazo suje suyo take a way, cewa tayi baza taje ba yaje shi ya dawo, tayi hakanne don ta samu damar aikata shirinta yanda ta so, d'aki ya koma ya d'auki key d'in mota ya fice, ita kuwa maganin da tazo dashi ta d'auko ta faffesa shi cikin Tuwo nd miyar kuka d'in da yace na Fareesah ne, baza kice an sakawa tuwon komi ba, sai ita da ta saka, falo ta dawo ta zauna tana zaman jiransa.

Fareesah kuwa zamewa tayi ta kwanta akan gadon, wasu sabbin hawayen na biyo kuncinta, wayar Miq d'in ta d'auka ta turawa Dad da sak'on Miq d'in bacci yake, in ya tashi zata gaya masa, zai kirashi, daga haka ba ta san sanda bacci ya kwasheta anan ba.
Bai wani jima da fita ba sai gashi ya dawo, dama Sumayya ta tanadi plate d'inta da spoon don haka yana kawowa ta hau ci, shi kuwa kasa cin komi yayi haka kawai yake jin gabansa na yawan fad'uwa, kamar wani sabon al'amari zai faru da shi, d'akin da yabar Fareesah ya shiga, sai ya tarar tana bacci, zama yayi a gefenta ya zuba mata idanu yana ta kallonta. Wayarsa ya d'auka, anan yaga miss call d'in Dad d'insa, da hanzari ya danna kiran wayar Dad d'in, ringing d'aya zuwa uku ya d'auka.
"Hello Dad kana lafiya? ”
"Lafiya lau Sadauki, da fatan kaima haka, don hankalina ne ya kasa kwanciya har sai da naji muryarka cikin kwanciyar hankali. ”
Murmushi yayi cike da soyayyar mahaifin nasa kana yace.
"Lafiya lau nake wallahi, kaima ka san babu abinda zai samu sadaukinka matuk'ar duniyarsa na tare da Fareesah, amma a kwana biyun nan tana yawan fad'in zata bar duniyata, kuma ina jin tsoron haka. ”
Yakai k'arshen maganar kamar zai fashewa mahaifin nasa da kuka.
" Ka daina damuwa, insha Allahu lafiya k'alau zata haihu, kuci gaba da rayuwarku cikin duniyarku tare da 'yarku ko d'anku.”
Cikin sanyin jiki yace.
"To Allah yasa.”
"Amin” Dad d'in yace kafin ya jiyo muryar Sumayya ta wayar tana kiran Miq d'in, k'irjinsa yaji yayi wani irin bugu sannan yace.
"Muryar wa nake ji Sadauki? ”
Bakinsa na rawa saboda tsoro dak'yar ya tattara kalmomin sunan nata yace.
"Su may ya ce. ”

"Muddun na kafa maka doka indai akan Sumayya ne sai kabi ka rusheta gami da mutstsiketa, bansan meyasa kake min haka ba Miqdad, alk'awari ka d'aukarmun sai kuma gashi ka karya mini shikenan kaje gaka ga Sumayyan nan, duk abinda ya biyo baya babu ruwana. ”
K'it ya kashe wayarsa, yana jin wani rad'ad'i a k'irjinsa, shikenan zai kuma rasa jikansa karo na tara kenan, shidai yana jin bashi da rabon ganin jikansa a duniya, tunda Mariya ta shigo duniyarsa yake ganin ba dai² ba, ga shi sun had'u ita da 'yarta sun had'u suna ruguza musu rayuwarsu.

Miq kuwa wani mugun tashin hankali ne ya ziyarcesa, bugun da k'irjinsa yake akan da ya ninku, me Daddy yake nufi da duk abinda ya faru babu ruwansa, meyasa har yanzu Daddy ya kasa gane Sumayya baza ta tab'a iya cutar da abinda ya dangancesa ba, Har yaushe ne zai dinga zargin ita take kashe dukkanin 'ya'yan da Fareesah ke haifa?
Tsintar kansa yayi da addu'ar Allah ya raya abinda ke cikin Fareesah ko don Daddy ya daina zargin Sumayya.

Cikin d'an baccin da ya d'auketa, ta fara jin yunwa, a hankula ta bud'e idonta, ta saukeshi kan Miq da ya zurfafa cikin tunani, ba tabi ta kansa ba ta nufi kitchen, tuwonta ta d'auka ta nemi guri a kitchen d'in ta hau ci, sai da ta cinyesa tas hankali kwance sannan ta tashi ta nufi d'akinta, wanka tayi, ta gabatar da sallar isa'i had'e da shafa'i da wutiri, sannan tayi shirin kwanciya, tabi lafiyar katifa don wani azababben bacci take ji, aikuwa tana kwanciya baccin yayi awon gaba da ita.

Miq kuwa Sumayya tayi nasarar cire dukkan wani tunani daga kansa, bayan yayi sallah, wanka sukayo sukai shirin kwanciya, sam ta hanasa zuwa gurin Fareesah don batai aiki akan camera d'in gidan da ta saita ba, tana so ta gani da idonta ita ta bata abinda taci ta mutu, shikuwa Miq ziciyarsa da hankalinsa gaba d'aya suna gurin Fareesan.

Mafarki tayi wai Sumayya ta zuba mata wani abu cikin tuwon da taci, a firgice ta farka ta had'a tv ilai kuwa sai ga Fareesan na fesa maganin, wata zuface ta karyo mata, tana zulumin abinda Sumayyan ta bata taci, auwala tayo ta kalli gabas tana kaiwa Allah kukanta, akan kar yabar Sumayya taci nasara akan mugun nufinta akanta, kusan kwana tayi tana sallah domin baccinma yak'i zuwa kwata² ta riga ta saba bacci a jikin zumarta, sai gashi yau yayi mata nisa.

Sai da tayi sallar asuba gari ya fara washewa, tana zaune kan sallaya tana jan carbi bayanta da mararta suka fara ciwo, tun tana daurewa tana cije baki har yaso yafi k'arfinta, ga cikinta da yake mata wani mugun ciwo, a durk'ushe ta k'arasa bakin k'ofa ta bud'e, gudun kar ta mutu ita kad'ai cikin d'aki, da jan jiki ta isa falo tana k'walawa Miq kira.
A kwance kawai yake, amma ba bacci yake ba, zuciyarsa da tunaninsa suna ga Fareesah tun da yayi sallar asuba yake son zuwa ya ganota, amma ji yake kamar an d'aure masa jijiyoyin jikinsa an hanashi fita, yana ji tana kiran sunansa tun yana jin sautin muryarta har ya zamto ya daina ji, ita kuwa a halin yanzu ta riga ta galabaita babu wani k'arfi ko kuzari a tattare da ita bakinta yayi wani irin bushewa na azaba, tun Sanda take kiran Miq d'in Sumayya idonta biyu ta farka amma tayi kamar bata tashi ba, sai da ta tabbatar ta galabaita sannan ta farka, kallonsa tayi tace.
"Kaje ka gano Fareesah kuwa? ”
Idonsa ne ya kawo ruwa, ya kasa magana, wani tausayinsa taji ya lullub'eta, duk fa sanadiyar sonsa da k'aunarsa take aikata wa'yannan abubuwan, dirowa tayi daga gadon tana.
"Ya kamata dai muje mu gano me ciki. ”
Bata jira me zaice ba tayi gaba, a yashe ta tadda Fareesah a falo kamar matacciya, wani irin ihu ta saki da ya saka zuciyar Miq harbawa, sai a lokacin yaji wani k'arfi yazo masa ya fito da gudu ganin Fareesah cikin wannan halin ya kuma tsinkar da Zuciyarsa...........
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*


[19/2/2020/6:00PM]


*FITATTU SHIDA*

*CIKIN DUNIYARMU*
BEBE'ARTH
*HASKE A DUHU*
Aisha M Mahmud
(Meeesherh lurv)
*DUHUN DAMINA*
Maryamerh Abdul
(Kwaiseh)
*SARA DA SASSAK'A*
Qurratul'ayn
*ZAMANINA NE*
Munayshat
*GASKIYA D'AYA*
Asisi B. Aliyu

Fitattu 6 na siyarwa ne,
Idan kuna buk'atar d'aya daga ciki, ko kuma dukkaninsu, ku tuntub'emu ta wannan layi:
07067364721


PREE PAGE
_______________
*EIGHT*

Gashi kuma a yau yake son komawa kan ayyukansa, ga abinda yazo nema bai samu ba, haka dai zai hak'ura ya koma, in yaso ya gayawa malamin abinda ke faruwa dashi a hanyar zuwa samo itacen bishiyar, wayarsa ya d'auka ya danna kiran wayar dan nasa, amma haka tai ta ringin ba'a d'aga ba, ji yayi hankalinsa yayi mugun tashi, tunawa yayi ai tare da matarsa sukayi tafiyar, don haka sai ya juya akalarsa ga kiran wayar matar tasa.

Fareesah dake karatun al'qur'ani bayan ta idar da sallar taji wayarta na k'ara, sai da takai aya, ta kuma ci sa'a wayar bata katse ba da hanzari tayi picking ganin Daddy ne ke kiranta.

"Hello d'iyata kuna lafiya? ”
Shine abinda ya fara cewa, sai da tayi murmushi sannan tace.
"Lafiya lau Daddy, da fatan kuma haka. ”
"Alhamdlillah D'iyata, ya kwanan jikata, ko kuma jikana? ”
Murmushi tayi cike da kunya batace komi ba, murmushin shima yayi, don yasan baza tayi magana ba, hakan ne ke faruwa tsakaninsu idan har ya tambayeta jikansa, duk cikin matan d'an nasa, su biyu kawai yake matuk'ar k'auna, daga ita sai Khadija, amman kuma sai dai ya nuna musu soyayyar a b'oye, saboda bai isa yayi ta gaban matarsa ba, sai dai in soyayyar 'yarta zai nuna.
"To Allah dai ya rabaku lafiya, ya kuma yi albarka, na kira number Sadauki d'in ta tafi amma bai d'aga ba ko lafiya? ”
Yaci gaba, don yasan amin d'inma sai dai ta fad'eta a zuci. ”
"Ina kitchen ne ni, amma bari naje na dubo. ”
Kawai ta tsinci kanta da yin k'aryar hakan.
"Ok, tom, kice masa ina jiran kiransa. ”
Daga haka ya datse layin.
Da k'yar ta yunk'ura ta tashi, bayan ta ajiye wayar, saboda cikinta da yayi mata nauyi, yau ji takeyi cikin nata ya kuma yo k'asa sosai, don yauma saura kwana hud'u EDD d'inta ya cika, duk da duk haihuwar da tayi tana k'ara sati biyu a kai, a hankula take takawa har ta fito falon, idontane ya fara sauka kan Sumayya, ita kuwa Sumayyan cike da bak'in ciki take binta da kallo, ji takeyi kamar taje ta shak'eta ta mutu, ta huta da ganinta tare da bakin cikin jikinta, d'auke kanta Fareesan tayi, ta nufi d'akin Miq d'in, duka wayoyin nasa ta tarar akan mudubi, amman shi baya ciki, d'iban wayoyin tayi ta fito dasu, d'aya d'akin ta nufa don tana tsammanin yana ciki, murd'a k'ofar tayi, aikuwa ta bud'e, ganin haka yasa Sumayya tayo gurin da hanzarinta zata shigo d'akin, Fareesah tayi saurin rufe k'ofar tare da sanya mata key, gano shi tayi a kwance rik'e da kansa, cike da tausayinsa ta isa gareshi, dukkanin k'arfinta ta saka ta d'ago kansa ta aza bisa cinyarta, ga mamakinta hawaye ta gani bisa kuncinsa, wani zazzafan tausayinsa taji ya kamata, lallai abun babba ne, tunda taga hawayen soja, duk tsawon shekarun da suka d'iba tare bata tab'a ganin ko da d'igon k'wallarsa ba, wannan ya tabbatar mata ba k'aramin ciwo yake ji a zuciyarsa ba, hannu ta saka tana goge masa hawayen, ji takeyi kamar itama ta fashe da kukan, wara idanuwansa yayi akan fuskarta, nan taga yadda idanuwansa sukayi jazur dasu na ban mamaki, a hankula ya rik'o hannunta cikin sanyin murya yace.
"Zumata, ki dinga mini addu'a, duk da nasan kina yimin, wallahi ban san abinda ke damuna ba, nasan kwata ² bana saukewa Khadija da Fareeda hak'k'insu, amma ban san dalili ba, wani zubinma gara Fareeda tunda mahaifiyata tana tirsa sani akanta, amma Khadija ni na san har ga Allah tana matuk'ar hak'uri dani, don ba k'aramin k'wararta nake ba, kuma wallahi wani gefe na zuciyata yana matuk'ar tausayinta amma duk yayin da nayi yunk'urin tallafo rayuwarta sai naji na kasa, sannan na rok'eki dan Allah kar ki kuma yimini zancen Sumayya, wallahi kwanyata ba ta tab'a iya zurfafa tunani kan Sumayya, a duk sailin da nayi niyar yin hakan, na kanji kaina kamar zai dare ya rabu gida biyu, ni kad'ai na san irin azabar da nake sha, idan har kina son cigaban rayuwata to babu ruwanki tsakanina da Sumayya. ”
Wani kukane yazowa Fareesah jin lafazinsa na k'arshe, to tabbas babu tantama Sumayya ta riga ta tsaface Miq, banda haka wannan wata iriyar rayuwace haka?
Ganin tana kuka ya sakashi mik'ewa zaune ya rungumota jikinsa.
"Sorry Zumata, bayan haka ban san me zan gaya miki ba ki fuskanceni, dan Allah ki cire dukkanin wata damuwa daga ranki, ko don lafiyarki da ta babynmu.”
Shiru tayi masa ba tare da tace komi ba, sai shashshek'ar kukanta ne ke tashi kawai, bakinsa ya saka saitin kunnenta yana hura mata iska a hankula.

Cike da takaici da bak'in ciki Sumayya ta bar bakin k'ofar, ganin Fareesah ta rufeta, d'aki ta koma ta d'auki wayarta ta danna kiran wayar Mom, ringing d'aya ta d'aga.
Babu sallama ba komi ta hau fad'in.
"Mom nidai na gaji wallahi, na k'agu naga Fareesah tabar duniyar Miq d'ina, zuciyar Miq an halicceta ne domin Sumayya kad'ai, nayi matuk'ar k'ok'arima da na kawo har iyanzu ma tare da wata cikin zuciyarsa, gashi ga dukkan alamu kamar ta san wani abu game da ni, dan haka wallahi a yau ko gobe zakiji labarin mutuwarta. ”
"Dakata Sumayya, wai ke meyasa baki da hak'uri ne ko kad'an, ita gaggawa da kike gani k'arshenta ba ya yin kyau, domin daga shaid'an take, kika kaho har iyanzu ma tare daa ita, bare 'yan kwanakin da suka rage miki, kinsan sarai dai kika bata tasha yanzu zata haihu lafiya ba tare da komi ya samu abinda ke cikinta ba, itace kawai zata mutu, amma idan kika bari ta fara nak'udar shine burinmu zai cika.”
"Nidai gaskiya na gaji Mom, kinga kuwa rashin mutumcin da take mini, yanzuma k'iri² ta hanani ganin Miq d'in, idan na cigaba da rayuwa da ita cikin duniyata, to tabbas nan da kwana biyu zakiji labarin mutuwata, don haka nidai zan bata, ko da yaron bai mutu ba ma kasheshi ta yadda muke kashe sauran.”
Bata saurari me Mom d'in zata ceba ta datse layin tayi cilli da wayar kan gado, ta nufo d'akin kamar mahaukaciya, knocking take da iya k'arfinta kamar ta b'alla k'ofar ta shiga...



Kuyi hak'uri na jina kwana biyu da kuke, da kuma gajeran typing, bamu da wuta ne har yanzu ba'a gyara ba, ba koyaushe zan dinga k'arar da chargin nawa ba a typing.

Free page ya kusa zuwa k'arshe, don haka masoyana kuyi k'ok'arin mallakar naku a hannu.

AL'K'ALUMAN NAGARTATTU.
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*


[23/2/2020/5:46PM]


*FITATTU SHIDA*

*CIKIN DUNIYARMU*
BEBE'ARTH
*HASKE A DUHU*
Aisha M Mahmud
(Meeesherh lurv)
*DUHUN DAMINA*
Maryamerh Abdul
(Kwaiseh)
*SARA DA SASSAK'A*
Qurratul'ayn
*ZAMANINA NE*
Munayshat
*GASKIYA D'AYA*
Asisi B Aliyu


Fitattu 6 na siyarwa ne,
Idan kuna buk'atar d'aya daga ciki, ko kuma dukkaninsu, ku tuntub'emu ta wannan layi:
07067364721


FREE PAGE
_______________
*TEN*
Da gudu ya koma ya d'auko key d'in mota ya sunkuceta ya fita da ita da gudun gaske, Sumayya saurin d'auko mayafi tayi tabi bayansa, don ta san bazai zaman jiranta ba, cikin mota ya sakata ya zaga ya shiga mazaunin driver da hanzari Sumayya ta shiga gefen ko dai daita zamanta ba tayi ba yaja motar da gudun gaske, dama tuni an dad'e da wangale gate d'in, suna isa asibitin Emergency aka nufa da ita aka shiga bata taimakon gaggawa, daga miq har Sumayya sintiri kawai suke a bakin k'ofar d'akin da aka shiga da ita, Sumayya addu'a take Allah yasa su shek'a barzahu daga ita har abin cikin nata, yayin da Miq ke addu'ar Allah ya sauketa lafiya, gaba d'aya ya rasa nutsuwarsa, ak'alla za'a d'auki wasu awoyi uku kafin likitan ya fito yace masa, sun samu numfashinta ya dai daita, amma kuma bata da k'arfin da zata haihu da kanta, ta riga ta galabaita sosai k'arfin nata ya k'are gaba d'aya, don haka aiki za'ai mata, abubuwan da duk ake buk'ata ya bashi, yaje ya biya kud'in da za'ai mata aikin, sannan ya kawo musu abinda suke buk'ata da kuma kayan haihuwa.

Hawaye ne ke zuba a idonsa sosai yayin da yake saka hannu a takardar aikin da za'ai mata, gani yake kamar shi ya janyo mata, da ace ya fito a sanda take kiransa da duk hakan bata faru ba.
Tunda aka shiga da ita d'akin da za'ai mata aikin suke sintiri a k'ofar d'akin shi da Sumayya, sosai itama ta nuna damuwarta a fili, ko wace addu'a tazo bakin Miq yinta yake gaba d'aya ya fita daga cikin nutsuwarsa, a k'alla sun d'ebi tsahon awonni hud'u basu fito ba, tun daga nan zuciyar Miq ta sare gaba d'aya, yana ganin likitocin sun fito k'irjinsa yayi wani irin bugu, kamar daga sama yaji d'aya daga cikin likitocin yana gaya masa sunyi nasarar ciro abinda ke cikinta, amma bata zo da rai ba ka shiga tana son ganinka, ya mik'awa Sumayya gawar yarinyar a kwali.
Kalmar Innalillahi kawai bakinsa yake furtawa ya kasa ko da k'wak'k'waran motsi, ji yayi k'afarsa tayi masa wani d'an iskan nauyi dak'yar ya iya janta ya nufi d'akin, a hankula ya bud'e k'ofar d'akin ya shiga.





________________
*KANO*

Ashe Ummi tana cikin damuwa sosai b'oye mana takeyi, amma damuwar Yaa Nazee sosai tayi mata illa har ciwo yake neman fin k'arfinta, tsakiyar dare take tashi tasha kukanta, sannan tayi sallolinta na nafila takaiwa Allah kukanta, yaudai sosai ciwon yake son fin k'arfinta, ni kuwa tun tashina nake lura da ita ko gurin aikima k'in zuwa nayi, nima haka nake jin gab'b'an jikina duk sun sare, ji nakeyi duniyata tayi mini wani iri na da ban, irin wannan yanayin shi na dinga ji a sanda Abba zai bar duniyarmu, shiyasa yau gaba d'aya hankalina yake kan Ummi, tsorona kawai kada ta bar duniyata, don idan ta barta ban san yadda rayuwata zata k'are ba, gani nake ma gaba d'aya duniyata ta wargaje, ni da murmushi kuwa mun riga munyi bankwana, Allah ma ya kiyaye, shine abinda d'aya b'arin zuciyar tawa ya gaya mini.

Duban Ummi nayi nace.
"Ummi sai nake ganin kamar baki da lafiya. ”
Murmushin k'arfin hali tayi ta shafa kaina gami da cewa.
"Lafiyata k'alau Munassah kada ki damu yanayi ne kawai. ”
Nidai kawai naji tane amma hankalina ya kasa kwanciya, kwata ² na k'asa d'auke idona daga kanta, nabi na manne mata, babu yadda ba tayi dani ba akan na tafi gurin aiki amma fir nak'i, duk sona da awara ranar ko gutsire ban iya sakawa a bakina ba har Inna ta gama sayar da ita, duk yanayin da nake ciki tana lura dani itama duk haka take jin zuciyarta wani iri.

Rik'o hannuna tayi d'aya hannun nata kuma ta saka shi a kaina tana shafawa, kallona take, yanayin kallon da take mini kamar tana tausaya mini ne, tace.
"Munassah, kiyi hak'uri da dukkan wani sabon al'amari da zaizo miki cikin duniyarki, ita rayuwa juyi² ce, kinga dai yadda rayuwarmu ta faro cikin jin dad'i da walwala, ba mu tab'a tunanin zata juya mu fuskanci rayuwa irin wannan ba, amma duk hakan yana cikin K'ADDARAR RAYUWARMU, jarabawa ce da Allah yake mana don yaga k'arfin imaninmu, don haka Munassah ina kuma umartarki da hak'uri akan dukkan wata rayuwa da zaki fuskanta anan gaba, kada kiyi k'azafi ga kowa, ki rayu da kowa lafiya, kada kici mutumcin kowa, ki zama ta kowa, kar kuma kici amanar wanda ya yadda dake, kiyiwa kowa kyakkyawan fata, kada ki tab'a damuwa da masu miki sharri ko hassada domin sune gishirin rayuwarki, idan kika rik'e wannnan babu abinda zai girgiza duniyarki, Allah ya albarkaci rayuwarki d'iyata ya baki ikon karb'ar ko wace iriyar rayuwar da zaki karb'a anan gaba da hannu bibbiyu.”
A dabarance ta goge k'wallar idonta ba tare da na gani ba, ni kuwa kuka na fashe dashi don zuciyata ta kasa jurewa, ban san dalilin Ummi na yimini nasiha haka ba, duk da tana yimin d'in amma na yau da ban yake da na kullum, ganin ina kuka yasa Ummi ta shiga lallab'ani, kuma ta dinga k'arfafa jikinta don naji dad'i muka dinga yin hira gaba d'aya har Inna.

Waje jen sallar la'asar jikin Ummi ya tsananta, duk dauriyarta sai da na gane na fita taro adai daita kawai don mu kaita asibiti, ko da na taro motar na dawo sai na tarar da ita jikin Inna, jikinta gaba d'aya ya saki, kan Inna kuma a k'asa tak'i d'ago ido ta dubeni, ga dukkan alamu kuka take, zaman 'yan bori nayi gaban Ummi ina rik'o hannunta...........



Kaishhhh masoya a CIKIN DUNIYARMU anan na kawo k'arshen free page me bbuk'atar jin yadda duniyar su Miq, Fareesah, Sumayya, Kadija, Fareeda, Munassah take k'arewa yana iya biyo number da take a sama, sai na jiku masoyana kar ku manta yanzu aka fara tafiyar, littafin yazo muku da sabon salo tare da tab'a zuciyar me karatu.


ALK'ALUMAN NAGARTATTU
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*


[24/2/2020/10:24PM]


*FITATTU SHIDA*

*CIKIN DUNIYARMU*
BEBE'ARTH
*HASKE A DUHU*
Aisha M Mahmud
(Meeesherh lurv)
*DUHUN DAMINA*
Maryamerh Abdul
(Kwaiseh)
*SARA DA SASSAK'A*
Qurratul'ayn
*ZAMANINA NE*
Munayshat
*GASKIYA D'AYA*
Asisi B Aliyu



Fitattu 6 na siyarwa ne,
Idan kuna buk'atar

Please Login or Register in order to submit comment