Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da tunanin wace ce ita? Cikin d'aki ta shige ba tare da ta tsaya a falon ba, dai² nan Inna ta fito, fuskarta ce ta fad'ad'a da murmushi ganin Miq a tsaye, "Ka tsaya ka zauna mana.” Tace da shi, ta shiga kitchen ta d'auko plate nd knife, Apple ta d'auko a fridge ta yan yanka a plate d'in ta had'o da lemon gouva ta kawo masa, murmushi ya yi yace. "Sannunki Inna, Allah ya saka da alkhairi.” "Amanarka fa aka bani, kuma ina jinka kamar d'an da na tsuguna na haifa.” "Ni d'anki ne Inna, ki ma cire kamar d'in nan. ” Murmushi ta yi tace. "Sai naji mutuwa kuma? ” "Wallahi kuwa Inna, ya za'ayi da ikon Ubangiji?” "Babu kuwa sai hak'uri, Allah Ubangiji ya jik'anta ya gafarta mata, Allah ya kawo wasu yaran masu albarka.” "Amin Inna. ” Yace yana kai apple d'in bakinsa. "Naji mutuwar sosai wallahi, rana d'aya suka mutu da Yayata dake kano, wannan yarinyar da kake gani 'yarta ce, mariniya ce ba uwa ba uba, amanarta mahaifiyarta ta bani shine na taho da ita, ina neman alfarmarka ta zamana tare da ita a gidan nan.” "Haba Inna, nan fa gidan d'anki ne, kina iya kawo duk wanda kika ga dama cikinsa ya yi rayuwa, Allah ya jik'anta ya baku dangana. ” "Amin ya Allah, na gode da karam cinka, Allah ya k'ara tsareka daga sharrin mak'iya.” "Amin Inna. ” Yace yana cigaba da cin tufar kafin wayarsa tayi ringin............



Naji k'orafinku, tun ina free page na bayar da uzurina na rashin wuta, wutarmu ta lalace har yanzu bamu da wuta sai yawan kai chargi ba ko yaushe zaka k'arar da chagin gurin typing ba, hakanne yasa randa naga ina da isasshen chargi nake muku typing, idan kuwa kunga na kwana biyu ban turo ba to matsalar chargi ce.
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*


[8:14PM/11/3/2020]


Folow me on wattpad @Rashuna.

_Fitattu shida na siyarwa ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_
__________________
*EIGHTEEN*
Daddy ne ke kiran wayar tasa, da hanzari ya yi picking. "Assalamu Alaikum.” "Amin wa'alaika salam, gani a cikin gidan, kana ina? saboda ba na son kowa ya san nazo. ” "Ina gurin Inna, amma bara na fito.” "A'a yi zamanka bara nazo. ” Yana fad'in hakan ya datse layin, yayin da shi kuma ya ci gaba da cin tufarsa har Daddyn ya shigo d'auke da sallama, d'auke da fara'a Inna ta amsa masa sallamar ya shigo ciki ya zauna, gaisawa suka yi cikin mutumci, kana ta tashi ta shiga kitchen, sai gata d'auke da tuwon alkama and okro stew, Munassa ce tayi mata shi d'azu, amma ita ko da lauma d'aya Munassan ba tayi ba. Saving d'insa ta yi ta mik'a masa tace. "Ga mutuminka. ” "Kamar kwa kin san ban zauna naci abinci ba, na kwa gode. ” Miq ne yace. "Au Inna ni shine ko tuwon baki bani ba, da yake Daddy ne ga shinan kin basa. ” "To ai naga ba ku had'a hanya da shi bane shiyasa, amman indai zaka ci bari na sako maka. ” "A'a bar shi, bayan ba'a bani ba tun farko.” "Ci ne dai baza kayi ba shiyasa ka fake da haka. ” Daddy da ke danna loma yace. "K'yale shi ai ya bar dad'i wallahi, anya kuwa ba zakiyi murabus ki komo K/durbi da zama ba? ” Murmushi Inna ta yi, don ta san santi ne ya saka shi fad'in hakan don itama tuwon ya yi mata dad'i sosai, Miq ne yace. "Ai Daddy mai rabamu da Inna sai mutuwa.” Saboda ya saka laumar tuwon a baki bai samu ya bashi amsa ba, shi kuwa Miq ji ya yi tuwon ya ba sa sha'awa, d'aukar spoon d'in ya yi yai loma d'aya ia bai aune ba sai gani ya yi sun cinye tuwon tare tas, Inna sai dariya take masa, sai cewa ya yi. "Ai don yunwa nake ji shiyasa na iya ci, amma ba cin haka me zanyi da tuwo?” Ba wanda ya kulasa sai dariya da suka fashe masa da ita, murmushi shima ya yi yana shafa kai ya d'auki lemon guova ya kora da shi. "Inna gurinki nazo da magana mai muhimmanci.” "Tom ina saura ranka Alhaji. ” "Da fatan dai mu kenan a gidan? ” Har za tace eh sai kuma ta tuna da Munassah sai cewa ta yi. " A'a akwai yarinyata a d'aki, 'yar Yayata ce da ke kano, to yau kwananta hud'u da rasuwa, mahaifinta kuwa zai yi wajen shekara d'aya da rabi da rasuwa.” "Allah sarki, Allah ya jik'ansu ya yi musu rahama.” "Amin.” suka amsa baki d'aya, kallon Miq ya yi yace. "Sadauki ba mu guri, ita tunda tana d'aki ba jin tattaunawarmu za tayi ba. ” Murmushi kawai ya yi ya tashi ya fita. Kamar yarda Miq ya bashi labarin mutuwar Fareesah da rayuwar Babynta da aka b'oye haka shima ya bawa Inna, kana ya d'auko takardun wasu daga cikin kadarorinsa da ya mallakawa tilon jikarsa ya dank'awa Inna kana yace. "Na baki wannan labarin ne don na aminta da ke, ke kad'ai ce nake ganin zan bawa amana ki rik'e mini ita amanar kwa da ko cikin 'yan uwana ba zan iya bada ita ba, ki rik'e wa'yan nan takardun a hannunki saboda idan na ajiyesu gurina Mariya ta na iya binciko su kuma duk sunan little Fareesah ne a jiki, yardar da nayi da ke da kuma amanar da ke tsakaninmu itace ta saka na kuma damk'a miki wannan amanar wacce ko shakka ba nayi zaki rik'e mini ita k'am².” "Ina fatan Allah Ubangiji ya tayani rik'on wannan amanar, amma kamar yarda Miq yace zaman Fareesah a hannun Hisham ba zai yu ba, saboda Sumayya ta san Hisham, kuma dukkan wani motsi da Miq yake yi akan idonta ne, ta na da wayo, ta na ganin wani abu da bai mata ba dole za ta yi bincike a kansa, na dad'e da zargin da saka hannunta a mutuwar yaran da Fareesah ke haifa, kawai na yi shiru da bakina ne. ” "To yanzu dai na kasa samun matsayar inda za'a ajiye yarinyar wallahi, duk inda na waiga sai naga hakan bazai yu ba, ba na son itama su kashe mini ita wallahi, amma kuma na rasa ya ya zanyi wallahi, shi yace raino zai kaita wani guri da ban ni kuma ba na son hakan.” "Insha Allahu babu abinda zai same ta, amman idan ba'a samu matsaya ba dole ba yadda za'ai sai dai ya kaita rainon. ” "Tom shikenan, zan dai duba na gani kafin nan kan ranar bakwan Fareesah, tun da yace washe garin ranar zaije ya kai yarinyar raino. ” Yana kaiwa nan ya mik'e da shirin tafiya, Inna ta k'walowa Munassa kira don ta gaishe sa, cikin muryarta da ta kuma yin k'asa sosai ta amsa ta fito sanye da hijabi, har k'asa ta tsuguna ta gaishe shi ya dubeta cike da tausayi, hak'uri ya dinga ba ta yana mata 'yan nasihu, Inna tace. "Ai ina jin sai na nema mata rubutun dangana, tun ranar mutuwar har yau ba taci wani abun kirki ba. ” Kallonta ya yi yace. "Ita mutuwa wajibi ce akan kowa, muma duk daga haka muka rasa namu iyayan, kuma muka yi hak'uri, rashin cin abincinki ba shi zai dawo miki da ita ba, kin san ta riga ta tafi inda ba zata tab'a dawowa ba, don haka ki fauwalawa Allah lamuranki sai kiga komai yazo miki cikin sauk'i, amman rashin cin abincinki sai dai ya saka miki wani ciwo da ban azo ana fama dake, don haka ki daure ki dinga cin abinci kinji 'yata.” D'aga masa kai tayi idonta yana son zubar da hawaye, dama abinka da mai danshin ido. "Yauwa, ko zaki sha fura a kawo miki? ” Nanma d'aga masa kan ta yi yace. "A'a ni da bakin ki nake son ki mini magana. ” "Eh zan sha.” Ta fad'a muryarta na rawa, sallama ya yi musu ya tafi yace za'a kawo mata furar insha Allah. _____________________ An yi sadakar bakwai d'in Fareesah, Inna ma sai da tayi d'an abin sadaka na mutuwar Ummi, gobe ne Miq yace zai tafi england amman kuma har yau Daddy bai samu tsayar yar shawara ba, duk wani tunani yayi aamma ya kasa samun matsaya d'aya, wata shawara zuciyarsa ta yanke masa to itace yake ta tunanin yadda zai b'illo mata, idan ya tuno da abinda yaji d'azu Sumayya na gayawa mahaifiyarta sai yaga shawarar da ya yankewa ransa itace dai² da yadda zasu nuna musu izina akan duk abinda Allah ya riga da ya tsara babu wani mahaluk'i da ya isa ya ja da shi, wannan tunani da ya yi shine ya kuma k'arfa fa mishi guiwar bin shawarar zuciyarsa, amman dole ne sai yaji ta bakin wacce shawarar ta shafa.........
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*


[7:19PM/10/3/2020]


Folow me on wattpad @Rashuna.

_Fitattu shida na siyarwa ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_
__________________
*NINETEEN*
Bayan ya gama tsayar da abinda zuciyarsa ta yanke masa, Amininsa ya kira, Alhaji Abdullahi mai tangaran da ya tafi kaduna gurin matarsa da ke can a yau bayan anyi Addu'ar bakwan Fareesah, shawararsa ya nema akan abinda ya yankewa zuciyarsa, ai kuwa ya bashi goyan baya d'ari bisa d'ari, kuma yace idan komai ya kammalu ya d'auki ragamar yin komai anan ba tare da sanin kowa ba. gani kuma ya yi dare ya yi, idan har ya fita to idon Mom na kansa, hakanne yasa ya sakawa k'ofarsa key ya shiga toilet nanma ya saka masa key gudun kar Mom ta shigo, wayar Miq ya kira, sai da ya fara tambayarsa yana ina, da fatan ba ya tare da kowa, yace masa eh kana yace ya had'asa da Inna. A lokacin Inna ta na ta zabga g'yangyad'i, Munassah na gefenta a kwance cikin nazarin rayuwa ji ta yi ana nocking, tsoro ne ya kamata, ita tun zuwanta gidan mai gidan kawai ta sani, shi kad'aine yake shigowa kullum ya gaishe da Inna, wani lokacin yaci abincin da suka girka, girgiza Inna na yi nace ana knocking, fir gigit ta farka, ta fita don ta bud'e k'ofar a ranta ta na cewa. 'Ko waye cikin daren nan? ' Tun fitowarsa daga sashensa Sumayya ta hangosa, bayansa ta biyo ba tare da ta masa magana ba, abinda ba ta sani ba yana ankare da tana biye da shi, hakanne ya saka Inna ta na bud'e k'ofar ya mik'a mata wayar. "Sai da safe.” Kawai yace ya juyo, itama Sumayyan da ta hango ne yasa ba tace komai ba ta rufe k'ofar ta juya ciki. Da mamaki yake kallonta, irin bai san ta biyo bayansa ba. "Ke kuma ina zaki da tshohon daren nan?” "Gurin Inna zani hira, tun da dai yau ka mini nisa.” Ta fad'i hakan ta na jin wani d'aci a ranta, murmushi ya yi a ransa yace. 'Lallai Sumayya makira ce ba kad'an ba, tun zuwan Inna gidan bai fi sau d'aya ta shiga inda take ba, saboda ko da suke a k/durbi ba shiri suke tsakaninsu ba, amma kuji wai hira zata gurinta, lallai ta raina mini hankali, da ada ne fa da tsafinta ke yawo a jikina yadda zanyi da maganarta? me kwa zai hana, tun da sau wajen nawa tana raina maka wayo irin haka, amman kuma ta riga ta gama nata wasan, yanzu ni aka bawa fagen.' Rungumota jikinsa ya yi, ya shiga gaya mata wasu kalamai da bai bari na jiyo muku ba, ya nufi sashenta da ita. Wayar da ya bata ce ta hau ringing, ganin Daddy ne ke kiran yasa ta yi tunanin ko shi yace ya kawo mata wayar, picking ta yi d'auke da sallama a bakinta, daga d'aya b'angaren Daddy ya amsa mata sallamar, kuma k'asa ya yi da muryarsa sosai wadda Innan ce kawai ta san me yake fad'a, ni kuwa duk tsurkuna na kasa jiyo muku tattaunawar Inna da Daddy in ban da sai da safe da naji sun yiwa juna, bayan yace ta bawa Miq wayar, tace ai wayar ya kawo mata kawai ya tafi, d'aya layin Miq d'in ya kira yace masa ya d'aga tafiyarnan zuwa jibi. ____________ Washe gari na ji Inna ta na ta yiwa Munassa k'us² ina ta kasa kunnena naji me take ce mata amma ko kad'an na k'asa jiyowa, can dai na ji Munassan tace. "Inna a yanzu ke kad'ai nake gani naji dad'i, bani da kowa cikin duniyata idan ba ke ba don haka duk yadda kika juya duniyata hakan dai² ne a gareni, bani da wani zab'i a yanzu sai abinda kika yanke a kaina, kuma nayi miki alk'awarin biyayya akan duk abinda kika sakani muddun hakan zai sanya ki farin ciki, don ni a yanzu babu wani sauran farin ciki da ya rage mini cikin duniyata. ” K'walla ce ta zubowa Inna ta tausayina tace. "Allah ya yi miki albarka Munassa, insha Allahu nan gaba zaki yi alfahari da hakan, ni na san babu nadama a cikinsa sai tarin alkhairi, ina ji a jikina ta dalilin hakan zaki shiga cikin yalwar farin ciki mai d'orewa.” Daddy ta kira a wayarta ta gaya masa yadda suka yi da Munassan, godiya ya shiga yi mata sosai, kana ya yiwa amininsa tex a waya, yana gani ya shiga ya goge shi. misalin k'arfe goma 12 na ranar sak'o ya shigo wayar Daddy da hanzari na lek'a don na gano me aka rubuto, Alhamdlillah an, kawai na hango Daddy ya hankad'ani ya d'aga wayar sama, ganin fuskarsa nayi da annuri ta na ta walwala da annushuwa, ya d'auki key d'in mota don shi kad'ai yake buk'atar fita, tun a motar ya kira Miq yace su had'u a k'ofar guga, gidan Miq d'inne da yake gininsa amma ba'a gama ba, Daddy bai jima da zuwa ba sai ga Miq d'in yazo, motar Daddyn ya fito ya shiga, kallonsa Daddy ya yi yace. "Sadauki.” "Na'am Daddy. ” "Na yanke hukunci ba tare da saninka ba, a karo na biyu kenan ina yimaka hakan, kuma ina fatan kamar yarda ka yimini biyayya a wancen kayi mini biyayya a wannan, ba wai ina yimaka hakan bane don na nuna k'arfina na mahaifinka ba, sai don ina son kuma gina maka rayuwarka da ake neman rushewa, duk wani tunani nayi na wanda zan bawa rik'on jikata na rasa, saboda ina tsoron a rabani da ita hakanne yasa na yanke wannan hukunci, don shine abu mafi sauk'i a gareni, an d'aura maka aure yau d'in nan da .... .”


Kuyi hak'uri da wannan ban jin dad'i wallahi.
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*


[6:9PM/13/3/2020]


Folow me on wattpad @Rashuna.

_Fitattu shida na siyarwa ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_
__________________
*TWENTY*
"An d'aura auranka yau d'in nan da Munassah, wannan yarinyar da ke gurin Inna, tun ranar da na fara ganinta tausayin ta ya yi mugun shigata, naji kuma ina sonta, hakanne yasa na shigo da ita cikin zuri'ata, don ina jin a jikina ita alkhairi ce a garemu, dalili na biyu da ya saka kuma na shigo da ita ahalinmu shine, ina son na inganta rayuwarta, zan tafi da ita London zan saya mata gida a can, zan kuma nemi wacce zata zauna da ita, sannan zan sakata a makaranta na kuma bata amanar jikata, nan da shekaru biyar jikata ta girma itama kuma ta kammala karatunta zata dawo cikin gidanka da zama a zuwan 'yar yar Inna ce auranta ya mutu, a lokacin ne za'a fara buga wasan, ba sai na gaya maka abinda zaka yiba, amma ni na san zaman yarinyar a cikin gidan sai mak'iyanka da ke b'oye sun fito, tarko zakai ta d'ana musu da ita, kuma bance bayan dai daituwar al'amura ka raba auranka da Munassa ba, ko bayan raina idan ka yi hakan baka kyauta mini ba, bazance ban yafe maka ba, saboda ban nemi umarninka ba a sanda na d'aura muku aure, nidai ina fatan ka rik'eta a matsayin iyalinka har k'arshen numfashi. ” Ba k'aramin gir giza zuciyarsa ta yi ba a sanda Abba yace ya d'aura masa aure da wacce ko sunanta ma bazai ce gashi ba, a hak'ik'anin gaskiya shi bai jin zai kalli wata mace da soyayya ko kuma ya amsheta a matsayin matarsa ba domin bashi da wata zuciya mai numfashi da ta rage masa a b'angaran soyayya, tun da Fareesah ta mutu itama ta mutu murus, abu d'aya ne zaisa ya karb'i auran nan da Daddy zai masa shine don a rik'e masa 'yarsa cikin amana, kuma kamar yarda ya tsarawa ransa nan da shekaru biyar zata dawo cikin duniyarsa amma kuma bai san ta wani b'angare ba sai gashi Daddy ya kawo masa hanya mafi sauk'i, amman kuma da ya sani bai d'aura aure tsakaninmu kawai a biyata kud'in aikin da za ta mana, ni dai da ya bi shawarata tun farko hakan zance masa ayi, amma babu komai, al'amura suna dai-daituwa zai sawak'e mata ko don itama ya bata 'yancinta. Numfasawa ya yi yace. "Ka da ka damu Daddy, kamar yadda na maka biyayya a na farko wannan ma ina mai shaida maka ba za ka yi kuka da ni ba sai dai ka yi alfahari da ni, gaba d'aya muk'ullin rayuwata yana hannunka Daddy duk ta inda ka bi da ni ta nan zan b'illa, ba na fatan ganin ranar da zaka ce mini na bi hanya na canja wata hanyar da ban, ina matuk'ar alfahari da kai mahaifina, gaba d'aya duniyata kaine ke zagaye da ita. ” Shafo kansa yayi ya shiga shi masa albarka yana jin dad'i da godiya ga Ubangiji da ya bashi d'a d'aya tilo tamkar da dubu. "Idan Allah ya kaimu goben kai ka fara yin gaba, zuwa jibi kuma sai ka samemu a London d'in, saboda za'ai mata shirye²n tafiya, ka saka Faisal ya kaita can kaduna gidan Mai tangaran, a can za'ayi mata dukkan wasu shirye² na tafiya, kuma ina tunanin a can zan samu matar da zan had'asu tare, ni kuma gobe zanje kadunan jibi jirginmu ya d'aga, sauran abinda ake ciki kuma zamui waya, amman fa a kula sosai kar wani ya ganta tare da ku, don Inna tace mini babu wanda ya san da zamanta cikin gidan sai mu, mai gadi ne kawai, shima kuma ba ganeta zaiyi ba nan gaba. ” "Tom insha Allah za'a kiyaye, Allah ya k'ara girma ya kuma bamu nasara, ya d'oramu akan mak'iyanmu.” "Amin” Suka ce a tare kana suka yi sallama ya fita ya koma motarsa, da gudu ya ja motar ya na jin zuciyarsa ba dad'i, ace wai yau kwana takwas da mutuwar zumarsa ya yi aure, anya kuwa Zumarsa zata yafe masa? don ya yi mata mugun laifi, laifin da da za ta dawo cikin duniya baza ta tab'a jin dad'insa ba, ya tabbata da shine ya mutu to har yanzu tana gadon asibiti ba ta san wanda ke kanta ba, sai gashi shi kuma har ya kuma wani auran, duk da bashi da masaniya da auran har sai da aka riga da aka d'aura amman zuciyarsa sam tak'i gas gata masa bai yiwa zumarsa shahararran laifi ba, kafin ya isa gida kansa ya d'au mugun chargi don hakane ma yasa ya kulle phart d'insa baki d'aya, tex ya yiwa Faisal da. _Ka sayo wannan abin da mata ke rufe fuska, ka kaiwa Inna kace ta bata ta saka ta fito ku tafi, kaduna zaka kaita gidan Alhaji mai tangaran._ yana tura masa ya sulale ya kwanta yana mai zurfafa tunaninsa. Duk wata dauriya na yi don ganin ban yi kuka ba don ka da Inna taga kamar matsa mini ta yi, amma har ga Allah zuciyata ba na jin dad'inta kuka kawai nake buk'atar yi ko zan ji sanyi a raina, nik'af Inna ta kawo mini tace na saka zamu tafi, karb'a na yi na d'aura a fuskata, dama sanye nake da hijabi har k'asa, rungume Inna na yi na fashe da kuka, rungumeni itama ta yi a jikinta tana sakin kukan da take b'oyewa, itace ta yi juriyar cireni daga jikinta tace. "Kije ana jiranki, kiyi hak'uri shekara biyar kamar yauce, kamar kinke yin karatu ne k'asar, kuma kema makarantar zakiyi a can, Allah yana tare da ke a ko ina, da fatan kin d'au takardun naki?” D'aga mata kai nayi don bazan iya magana ba a halin da zuciyata take ciki, ganin na tsaya nak'i motsi yasa Inna ta kamo hannuna muka fito, motar tana bakin k'ofar, Inna ta bud'e gidan baya tace na shiga. "Allah ya kiyaye ya tsare, ya kuma kaiku lafiya.” Ban iya amsawa ba sai a zuci, sai da taga ya zuzzuge glass d'in motar ya fara janta a hankula kana Inna ta koma ciki. Ticket ya siya mana guda biyu, ko d'ar banji ba saboda na saba shiga jirgin dama, shi kuwa Faisal kasancewar yau ne farkon shigarsa jirgi a mugun tsorace yake da jirgin zai ta shi, mamaki ne ya ishe shi da yaga ko d'ar babu alamunta a fuskata. A sashen 'yan aiki na gidan anan aka saukeni, sai washe gari wani yazo ya d'aukeni mukaje passport, da yake aikin na kud'ine nan da nan aka mini visa, ranar da daddare Daddy yazo, amma ban gansa ba sai washe gari da jirginmu zai

Please Login or Register in order to submit comment