Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Fareesan za ta yi Sumayya ce take fara d'aukar jariran, ai kuwa yanzu dole ya godewa Ubangiji, ya kuma godewa amininsa da ya jajirce gurin ganin sunzo gurin malamin. A hanyarsu ta dawowa ma hirar Sumayan sukai ta tattaunawa Daddy yana k'ara masa haske akan irin makircin Sumayya da uwarta, kuma hatsabibabbu ne dole sai a hankula za'a d'ana musu tarko, don muddin baka iya kama b'arawo ba to wata rana shi zai kama ka, dan haka dole ne suma su saka rigar yaudara suci gaba da nuna musu har yanzu tsafinsu yana aiki a jikinsu hakanne zasu samu muk'ullin nasarar da suke nema. Bai yarda ya shiga ciki ba suka yi sallama da Dad gudun kar Mom ta matsa masa sai yaci wani abun kawai ya shiga mota suka bar harabar gidan, Shinkafi yacewa John ya nufa da shi, sauran motocin suka rufo musu baya, jiniyar motocin su ce kawai ke tashi a titi har suka isa shinkafi, dama tuni me gadi ya jiyo jiniyar tasu ya wage musu babban gate d'in gidan duka motoci hud'un suka shige ciki, bud'e masa motar akai ya fito ya nufi ciki. Mudansir k'aninsa ya gani da wata yarinya da bai san wace ba a falo suna shek'e ayarsu, ransa yaji ya mugun b'aci, ya tsani wannan halayyar, amma duk sanda yazo gidan sai yaci karo da irin haka, ba damar yayiwa Inno maganar sai tace babu ruwansa, ya barsu su wataya su da gidan mahaifinsu, rayuwar turai sukeyi ba irin rayuwarsa ta gidadawa ba, wani siririn tsaki yaja, ya daka musu wata uwar tsawa, sai a sannan suka ankara da mutum a tsaye a kansu, saurin sakin juna sukayi, mudansir yayi saurin yin ciki da gudu saboda bai manta irin masgar da yasha ba a wancan karan da ya tab'a kamasa, amma ranar Inno ba ta nan, shiyasa ya samu damar jibgarsa iya san ransa, wani kallon banza da k'yama ya jefi yarinyar dashi, sim² tayi ta fice tana duk'ar da kai. "Kai kuma meye haka? ” Inno ke cewa Mudassir dake faman b'uya a bayanta, ya kasa magana sai nuna mata hanya yake da hannunsa, siririn tsaki taja ganin Miq yakewa wannan mak'yar k'yatar...........
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*



[29/2/2020/7:55PM]


_______________
*FOURTEEN*
Kuma matse yarinyar yayi a k'irjinsa kamar ance za'a k'wace ta, yana jin wata zazzafar soyayyarta na shigarsa, d'agota ya yi ya na kallon kyakkyawar fuskarta, ya kasa gane tsakanin shi da Fareesah da wa yarinyar take kama, amma dai farar fatar Fareesah ta d'auko, bakinsa ya saka a kunnenta ya yi mata addu'oi gami da mata hud'uba, sannan ya d'agota ya ci gaba da kallon fuskarta hawaye na d'iga a idonsa.
"Na yi alk'awarin baki kulawa fiye da rayuwata, kuma na baki dukkanin wata soyayya, ba zan barki kiyi maraici ba kamar yarda mahaifiyar ki tace, kuma na miki alk'awarin yin bincike akan abinda Sumayya ta bawa Fareesah, wallahi ko wa na samu da hannu a kisan mahaifiyarki bazan barshi ba ko kad'an, Allah ya bani ikon rik'eki amana da cika miki alk'awarin da na d'aukar miki, ya kuma raya mini ke cikin aminci da salama bisa koyarwar Ma'aiki (S.A.W) Amin.”

Ta dad'e sosai rungume a k'irjinsa daga bisani ya mik'awa Dr.Hisham ita.
"Wa ka ka kaiwa ita, yau har tsawan kwana hud'u? ”
"Matata Haaya na kaiwa ita ta ke bata madara. ”
"Ka maida mata ita, idan na yanke yadda za'ayi da ita zan dawo, yanzu zanje na nemi ticket a yau nake son isa nigeria.”
"Da zaka bar mana ita, wallahi nayi maka alk'awarin rik'eta amana ba tare da ta yi kukan maraici ba.”
"Zancen na bar Fareesah a hannunka Dr. bai taso ba, Sumayya ta san matarka k'aramin ciki ne da ita, dole zata bi diddigin ta yadda akai aka samu wannan yarinyar, kuma ta san da cewa kaine ka karb'i haihuwar Fareesah, ina son yiwa Sumayya wasa da hankali fiye da yadda tayi wasa da nawa, ka yi hak'uri Dr. wai ba na hanaka bane don ba zaka iya rik'e mini ita ba sai don wannan hujjar tawa, na gode k'warai da gaske, Allah yabar Zumunci.”
kallonsa Dr. d'in ya yi yace.
"Wani suna ka saka mata?”
"FAREESAH.”
"Allah ya raya mana.”
"Amin, muje ka sauke ni gida. ”
Fitowa su ka yi ya bawa Nurse Fareesan akan ta mai da ta gida, shi kuma yaje ya sauke Miq d'in a gidan.


Tun da ya shiga gidan mamakin Sumayya kawai yake, ya kuma gas gata zancen Fareesah domin ya nemi camera sama da k'asa ya rasa, da dukkan alamu Sumayyan ce ta d'auke, koma dai mene ne ya yiwa kansa alk'awarin bincike akan duk wani me motsi cikin duniyarsa, zai shayar dasu ruwan mamakin da basu tab'a tunanin shansa ba, kaya ya sauya zuwa k'ananun kaya da suka kuma fito da kyahun haibarsa, danma fuskar nan a murtuke take kamar murmushi bai tab'a zama akanta ba, babu abinda yake matuk'ar k'ona masa rai irin yadda Fareesah ta dinga kiran sunansa akan ya kawo mata d'auki amma yayi biris da ita, zuciyarsa na san zuwa amma gan gar jikinsa ta hana.
Ko da ya je ya samu jirgi zai tashi zuwa nigeria k'arfe biyu dai², don haka sai ya komo gida kafin lokacin ya cika.





*KATSINA*
______Kafin mu isa katsina na fita hayyacina sosai, muna sauka daga mota na shiga shara ra amai, cike da tausayawa Inna take duba na tana jero mini sannu, mota ta tsayar mana da zata kaimu gidan da take a zaune. G.R.A naji tace da shi, muka shiga, a k'ofar wani danka'areran gida 50 by 50 ya ijiye mu, duk tsaruwar Teemah Nazz, sai naga wannan gidan ya taka shi a kyahu sosai wai tun kan ma na shiga ciki, sai da ta k'wank'wasa me gadin a tsorace ya dinga tambayar waye, ya yi tambayar ne ma kar yaje uban gidan nasa ne yayi isowar dare, Inna ce ta yi masa magana sai naga ya bud'e, gaisawa sukayi sama² saboda ta na rik'e dani, wani yanki naga munbi daga gefen gidan muka tsaya bakin wata 'yar k'ofa, muk'ulli ta saka ta bud'e sai gamu cikin wani falo me matsakaicin kyau, d'aki d'aya ne kuma a cikinsa, cikin d'akin muka shiga ta kwantar da ni akan gado, ta shiga toilet ta had'a mini ruwa me d'an d'umi naje nayi wanka, ko da na fito daga wankan sai na tarar ta had'a mini tea me d'an kauri, kasancewar ta na da komi na buk'ata a ciki, bayan na sha ta bani paracetamol shima na sha, ban jima da shansa ba wani wahalallan bacci ya kwasheni, ba ni na farka ba sai da ana kiraye²n sallar asuba, tun da Ummi ta rasu rabon da nayi bacci me nauyi irin wannan, garau da ni na farka, amma sai na fad'a cikin tunanin rayuwata tun da ba sallah zanyi ba ina cikin hutu ne.

Da gari yayi haske ne bayan munyi wanka mun shirya, sai Inna tace mini bara ta shiga su gaisa da mutanen gidan, ni ba zan bita ba sai me gidan yazo ta gabatar da ni a gurinsa tukun, to kuma sai ga Inna ta dawo tana kuka ba, hankalina ne ya tashi na shiga tambayar ta lafiya, tace mini matar me guidance ta rasu yau kwana uku kenan, tana da kirki wallahi babu ruwanta, ta iya zama da duka kishiyoyinta k'alau, haihuwarta takwas duk suna mutuwa, wannan shine na tara ta mutu itama yarinyar ta mutu, ni kaina sai na ji ba dad'i naji ina tausayawa me gidan.



Tun tasowar jirginsu ya kira Faisal ya sanar masa, yayin da shi kuma ya tanadi motar da za'aje d'auko sa, tuni motoci hud'u na alfarma sun isa filin jirgi don tarosa, gaba d'aya yaransa ne a cikin motocin, yana fitowa daga jirgi gaba d'aya suka sassara masa, sai suka ga fuskarsa ta kuma murtukewa akan ta da, ko da yake ai dole ne wannan mutuwa da aka zabga masa, bud'e masa gidan baya aka yi ya shiga nan motocin suka fita daga filin jirgin a layi.
Jiniyar motocin su ce ta isa ga me gadi tun shigowar su layin, don haka tun kan su k'araso ya riga ya wangale gate d'in, Sumayya da fitowarta daga wanka kenan ta jiyo jiniyar sai ta saki murmushin farin cikin Miq d'inta ya iso gareta, yanzu babu wata mace cikin zuciyarsa da zasuyi go gayya da ita........

ALK'ALUMAN NAGARTATTU.
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*


[6:55PM/ 9/3/2020]

Follow me on wattpad @Rashuna


Fitattu shida na siyarwa ne idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tuntub'emu ta wannan layin 07067364721.

__________________
*SIXTEEN*
Tura sa gabansa ta yi cikin yanayi na b'acin rai tace. "To gashinan dake sa na gani, tun da kai baka da mutumci baka kuma da zuciya, kare yabi duk ya cinyeta, ban da haka sau nawa zance maka ka fita sabgar yarana? Ka barsu su mori k'uruciyarsu don kai kana rayuwar gida danci sai kace kowa ma sai ya yi, to ka bar ganin ran nan ka dake shi na k'yaleka, to wallahi ka kuma kuskura hannunka ya tab'a jikinsa sai ka fuskanci b'acin ran da ban tab'a saka ka ciki ba.” Wani k'ulu lun bak'in ciki ne ya tokare masa wuya har wani d'aci² yake masa amma haka ya danne dukkanin b'acin ran da yake ji ya d'auko daraja da martaba ta mahaifiya ya risina yana ba ta hak'uri, Mudan kuwa tuni ya sirare ya gudu, ba tare da tace masa uffan ba ta k'arasa falo ta zauna kan kujera, haka ya kuma danne zuciyarsa da take mugun taso masa ya biyo bayanta, kuma risinawa ya yi a gabanta yana gaisheta, fuska kawai ta yatsina ba tare da ta amsa gaisuwar ba tace. "Me ya hana ka tura musu kud'i wannan watan? ” "Ban samu nutsuwa bane, ga kuma rashin da ya same mu.” Ya ce mata hakanne kawai amma a zahirin gaskiya ya yi wa kansa alk'awarin bazai kuma tura musu kud'i suna kashesu ta hanyar banza ba, ya shirya d'aukar dukkan wani mataki da Inno d'in zata d'auka. "Mutuwarta ba ta dame ni ba, don ni har na manta ma da anyi ta, don haka ka tura musu kud'i a yau d'in nan, don na gaji da rigimar da suke mini akan ba kud'i a Accaunt d'insu.” "Tom shikenan Inno, insha Allah zan tura musu.” "Yauwa to, sai kuma maganar Fareeda naji matsaloli da yawa daga gareta, watakan wulak'anta amanar da na baka kake yi saboda baka sona kafi son mahaifinka shiyasa kafi daraja amanar da ya baka, ko kuma dan itace ke haifa maka 'ya'yan da basa rayuwa, saboda 'ya'yan Allah bani ne don aci ga'do? ” Kasa magana ya yi tsabar jin yadda rad'ad'in magan ganunta ke tafar fasa zuciyarta, cigaba tayi da zuba masa ruwan masifa har da cewa a cikin watan nan taji labarin cikin Fareeda idan kuwa ba haka ba za ta yi matuk'ar sab'a masa, shi dai bai tanka mata ba ban da hak'uri da yake ba ta ya taso ya fito zuciyar nan tasa kamar zata kama da wuta, ido biyu su ka yi da Mahbub dake tsaye bakin k'ofa yana tsiyayar hawaye na tausayin wan nasa, ya rasa me yasa Inno take yimasa haka, bayan shine me matuk'ar yimata biyayya da kuma faranta masa rai, ji yayi zuciyarsa ta kuma karyewa amma ya danne ta saboda kada yaransa suga hawayensa, amma alamun b'acin rai gaba d'aya sun bayyana kan fuskarsa, girgiza kafad'ar Mahbub ya yi alamun kada ya damu ya fice, ita kuwa Inno k'wafa ta yi a ranta ta na cewa. 'Dole gobe na ziyarci malamina, don na fara ganin wasu sababbun al'amura na kunno kai.' Key ya sakawa phart d'insa don ya san Sumayya taji shigowarsa kuma wajibine sai ta biyo bayansa shi kuma a halin da yake ciki yana buk'atar kad'aici, rage kayan jikinsa ya yi ya fad'a toilet, ruwa ya sakarwa kansa ko zaiji sanyi a zuciyarsa, amma sanyin ya gaza zuwa har sai da ya had'a kansa da guiwa ya shiga risgar kuka, don yana jin wannan ce hanyar kawai da zata rage masa zafin rad'ad'in da yake ji a zuciyarsa, 'Wai me yasa ne duniyarsa tazo masa a haka, a yaushe ne kuma zaiyi alfahari da duniyarsa, ya rasa soyayyar mahaifiya tun yana tsumman goyo, haka ya taso rayuwarsa cikin garari mahaifinsa ne kawai ke k'aunarsa fiye da k'aunar da yakewa kansa, a tunaninsa Mom ce ke masa soyayyar da ya rasa gurin mahaifiyarsa ashe yaudararriyar soyayya take masa, farautar rayuwarsa take tun yana yaro, me yasa Allah bai bata sa'ar rabani da rayuwar duniyar baki d'aya ko na huta da rad'ad'in da nake fama da shi na zuciya?' Astagfirillah ya shiga na na tawa cikin zuciyarsa don ganin yana k'ok'arin yin sab'o, Allah yana rubutawa dukkanin wani bawansa irin rayuwar da zaiyi cikin duniya tun kafin yazo cikinta tana nan tana zaman jiransa, an d'auke alk'aluma kuma takaddun sun bushe, yana matuk'ar godiya ga Ubangijin da ya jarab ceshi da irin wannan rayuwar, yana kuma fatan ya cinye wannan jarabawar da kyakkyawan sakamako. Kukan da ya samu ya yi sai yaji zuciyarsa ta d'an yi sanyi, yayo wankan ya fito, jallabiya ya saka ruwan toka da ta saukar masa har k'asa,ya feffeshe jikinsa da turaruka masu dad'in k'amshi, masallaci ya nufa don yaji ana kiran sallar la'asar hakanne ma yasa ya d'auro auwalarsa, bayan ya gabatar da sallar ya dad'e yana lazumi daga bisani ya mik'awa Allah kukansa, yana fitowa daga masallacin phart d'in Sumayya ya nufa, nocking d'aya yayi aka zo aka bud'e, Nana ce 'yar aikinta da hanzari ta bashi hanya tana risinawa had'e da d'iban gaisuwa, cikin kulawa ya amsa gaisuwarta ya nufi d'akin Sumayyan, tana kwance a gado tayi zurfi cikin tunanin dalilin da yasa Miq d'inta ya yi mata haka, ace ya shigo cikin gidan nan tun d'azu baizo gareta ba ita kuma taje ta tarar ya sakawa k'ofarsa key, ko dai mutuwar ce har yanzu ba ta sakesa ba? Ta tambayi kanta, sai kuma ta bawa kanta amsa da ai ko mutuwar ce ba ta sakesa ba yaci ace ya nemeta, ba taji alamun shigowarsa ba sai dai k'amshinsa tuni sun kawowa k'ofofin hancinta ziyara, lumshe idanuwanta tayi ta wara su bisa kyakkyawar fuskarsa, kallon juna suka tsaya suna yi, shi yana mamakin dalilin da yasa ta sakawa zumarsa abinda taci ta mutu, yayin da ita kuma take jin zazzafar soyayyarsa na kuma bijiro mata, tashi ta yi taje ta fad'a jikinsa ta na sakin kukan kissa, wani takaici yaji ya kama sa, amma haka ya danne domin yana buk'atar nasara akan dukkanin mak'iyansa na b'oye don haka dole ne ya saka rigar yaudara, wata kyak kyawar runguma yayi mata a k'irjinsa ya shiga tambayar ta abinda ya faru yana yi kamar yana mata rad'a a kunne. "Kawai naji ba dad'i ne ace wai ka shigo gidan nan tun d'azu ba tare da idanuwana sun sauka a kanka ba, amma tunda yanzu na ganka ka wanke laifinka, ya k'arin hak'urinmu, da kuma k'arfin jikinka?” Wani birkitaccen murmushi ya saki da yake kuma birkita ta cikin zallar k'aunarsa da shauk'insa kana yace. "Naji dad'i da na wanke laifina don bana buk'atar nayi laifi ko kad'an gurin gimbiyata, hak'uri Alhamdlillah, nima kuma naji sauk'i.” "To Allah Ubangiji ya jik'anta yasa aljanna ce makomarta, ya k'aro mana dangana a zuk'atanmu” "Allahuma Amin.” yace yana k'ok'arin zare ta daga jikinsa ita kuma tana k'ara shigewa jikinsa a kunne ya rad'a mata. "Pls kiyi hak'uri mana, da daddare har sai kin gaji da kwanciya a jikina. ” "Ba na fatan ganin ranar da zan gaji da kwanciya a jikinka Miq, ina zaka? ka barni mana a jikinka pls.” "Zan lallek'a su ne naga ya suke. ” Ji tayi k'irjinta ya yi wani irin bugu, wani azababben kishi ne ya taso mata iya wuya amma tayi k'ok'arin danne shi, murmushi ta k'ak'alo tana sakin fara'a tace. "Amma naji dad'i sosai da hankalinka ya karkata garesu, dama haka nake so ko da yaushe ka dinga kwatan ta adalci a tsakaninmu. ” Tana kawowa nan ta bar jikinsa, murmushi shima ya yi yace. "Ai na san k'aunar da kike mini baza ta bari ki so na tashi ranar alk'iyama da shanyayyen b'arin jiki ba. ” Ba tare da ya jira amsarta ba ya fice daga d'akin ya barta cikin tunanin maganarsa, a dai² phart d'in Fareesah ya tsaya ya k'ura masa ido kamar ance zai ganta a tsaye a gurin, ganin hawaye na son sauka kan kumatunsa yasa shi barin gurin ya nufi phart d'in Khadija.......
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*


[7:4PM/10/3/2020]


Folow me on wattpad @Rashuna.

_Fitattu shida na siyarwa ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_
__________________
*SEVENTEEN*
A kwance take a tsakiyar gado ta yi matuk'ar nisa cikin tunanin yanzu ita haka rayuwarta za ta k'are tana kallon Sumayya tana aikata mugayen aiyuka amma babu halin da zata tona mata asiri? Yanzu dai ga shinan tayi nasarar kashe Fareesah da Babyn cikinta, yanzu kuma kowa zata kashe nan gaba, cikin ita da Fareeda ko wace zata samu ciki? Inama ace itace zata samu ciki ko ta kashe ta ta wuta da wahal halun rayuwar da take ciki, tun tasowarta take rayuwa cikin k'unci babu wanda ya damu da irin rayuwar da take ciki, sai Miq da ya tsamo ta cikin k'angin rayuwa kuma ya kawota cikin duniyarsa me matuk'ar rikici da rikitarwa. Tsabar tayi nisa cikin tunanin ba taji alamun shigowar mutum ba sai saukar tafin hannunsa akan kuncinta taji, a razane ta bud'e ido, don ta yi matuk'ar tsorata, ba ta tab'a tunanin ganinsa ba, ko a mafarki ba ta tab'a tunanin akwai ranar da Miq zai tako k'afarsa zuwa d'akinta ba, tun da ya aurota ya kawo ta gidansa bai kuma tako k'afarsa cikin d'akinta ba, idan har ta na son magana da shi sai dai taje phart d'insa ta same shi. Murza idonta ta yi don ta kuma tabbatarwa da kanta shi d'inne, yayin da shikuma tausayinta yayi matuk'ar kama masa zuciya, janyota jikinsa ya yi ya rungume ta yayin da ita kuma ta saki wani marayan kuka me k'arasa raunana zuciya, kuka take yi sosai kukan da ya dad'e yana cinta a zuciya amma ba ta samu ya fita ba sai yanzu da ta samu babban masauki, bubbuga bayanta yake yana lallashin ta kamar wata k'aramar yarinyar, ya san da ya cutar da rayuwarta, kwata² ba ta samun kulawa a gurinsa, yanzu da ace mutuwa ta riske shi ba tare da ya gyara kuskurensa ba me yake tunanin zai tsinta a lahira? Cikin raunanniyar murya da nadama yake cewa. "Ki yafeni Khadija, ki kuma bani damar gyara kuskuren da na tafka duk a baya.” Kasa magana ta yi har sai da tayi kukanta me isarta, kana tace. "Ban tab'a rik'eka a zuciyata ba, a kuma ko wace rana sai na nema maka yafiya gurin Ubangiji, idan mutum yayi maka alkhairi daga baya yazo ya maka sharri to ba'a son ka dubi sharrin nasa ka dinga tuno alkhairinsa hakan ne zaisa ka yi yafiya gareshi, don haka alkhairinka gareni bazai tab'a sakawa naga laifinka ba Miq, kayi matuk'ar nisa a zuciyata, nisan da bazan tab'a iya dawo da kai baya ba. Ya hak'urinmu na Fareesah?” Jin kalaman nan nata sai suka kuma k'ara mata girma a zuciyarsa. "Hak'uri Allahamdlillh Khadija, na gode Allah da yasa kika zamo mace mai duba alkhairi ba sharri ba, nayi alk'awarin gyara kuskurena kuma ina fatan Allah ya shige mini gaba. ” "Allah ya rahamsheta, ita kuma yarinyar da muka rasa Allah yasa me cetonmu ce, ya kawo mana wasu masu albarka.” "Amin ya Allah, me ke damunki haka duk naga kin kuma ramewa? ” "Mutuwar Fareesah ce ta dokeni wallahi, kawai sai fatan Allah ya k'ara mana dangana. ” zameta ya yi daga jikinsa yana k'ok'arin mik'ewa. "Ya kamata dai kije kiga likita, gobe da safe zan saka a kaiki insha Allah, bari na lek'a Fareeda. ” "Tom Allah ya kaimu, gashi bani da komai na d'an tab'awa saboda ban saka ran ganinka ba.” "Kar ki damu.” Kawai yace mata yana ficewa daga d'akin, tasowa tayi ta rakosa har bakin k'ofa. A falo ya tadda Fareeda ta na waya, ta na ganinsa ta yi saurin katse wayar, ba tayi tunanin zai neme ta ba ko kad'an, duk yadda akai Inno tayi masa fata² ita kuwa ba ta san yanzu ta gaji da zama da shi ba, hanyar da zai bata takar darta kawai take buk'ata, tun da dai babu amfanin auranta da shi, abinda akayi auran don shi bazai tab'a yuyuwa ba, to zaman me zata zauna yi? Ana yin sadakar bakwan Fareesah zata nemi takardar ta. Tsira mata lumsassun idanunsa ya yi, ya na mata kallon tuhumar da ta tsorata ta bakinta na rawa ta shiga gaishe shi, wani shegen murmushi ya saki ya amsa gaisuwar ta ta gami da cewa. "Na sameki lafiya? ” "Lafiya lau.” tace ba tare da ya kuma cewa komi ba ya fice, sashen Inna ya nufa yana sakin murmushi don ya san zai samu kulawa matuk'a, knocking ya yi a lokacin Inna na toilet sai Munassa dake zaune ta jingina bayanta da kujera ta zurfafa cikin matuk'ar tunani, Inna ce ta yi mata gyaran murya sai a sannan ta ankara, ji tayi k'irjinta ya bada wani irin bugu, jiki ba k'wari taje ta bud'e k'ofar, idanuwansu ne ya gauraya guri d'aya, a lokaci d'aya bugun zuciyarsu ya sauya k'irjinsu ya shiga dokawa, juyawa ta yi ta koma ciki shi kuma ya shigo zuciyarsa cike

Please Login or Register in order to submit comment