Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daga kan aikinta wanka nayi na shirya cikin doguwar rigata bak'a da hijabi fari, sallama nayiwa Ummi ta bini da addu'ar Allah ya kiyaye.
Ina zuwa da murna da farin ciki Aunty Sakina ta tarb'eni.
"Ai da har naji ba dad'i da Aysha take gaya mini baki da lafiya, don har na fidda ran zuwanki, sai gaki kuma.”
Murmushi nayi don nasan dalilinta nayin murnar,saboda costomars d'intane, duk wanda yazo ni yake tambaya na kawo masa abinci, akwai wa'yanda in bana nan ma basa cin abinci a gurin, saboda ba wai yaban kai ba a duk ma'aikatan ta nafi kowa iya tsara girkuna kala² shiyasa ta tsani taga ban zoba, kuma take bani kulawa sosai da sosai.
"Nasan ai kinfi kowa damuwa da rashin zuwana Aunty Sakina, shiyasa na daure na taho saboda ke kad'ai”
Na fad'a ina kallon su Safnah, dariya tayi, don ta gane da su wa nake, aikuwa sai Safnah cewa tayi.
"To dama wa yake nemanki? Da kizo da kar kizo mu duk d'ayane a gurinmu.”
Jan hannuna Aunty Sakina tayi ba tare da na bawa Safnah amsa ba tana.
"Kinga taho muje kiyi aikin gabanki, in ba haka ba Safnah baza ta k'yaleki ba, bayan ita ba abinda ta iya sai tuwon semo.”
Dariya nayi na juya inaiwa Safnah gwalo da tasha kunu.
Daga zuwana na shiga yin abubuwan da nasan anfi zuwa cinsu, kuma nafi kowa k'warewa a kansu.
Tuwon rice agushi stew nayi da tuwon rice with okro stew da kuma tuwon semolina with okro da tuwon maiz with kuka soup.
Nan da nan aka fara cika restaurant d'in, wasu na shiga wasu suna fita Kuma har da masu yin take a way d'insa, ban manta wani Alhaji, kullum anan yake cin abincin rana da dare, rannan yana cikin cin Vegetable jollof rice with fruits tsabar santi sai cemini yayi.
Dan Allah in dinga zuwa gidanshi ina masa girki zai ninninka mini albashin da Aunty Sakina ke bani, karaf kuwa sai a kunnen Aunty Sakinan, aikwa ta rufe da masifa ba ji ba gani, kun san dai yaren mutum ba sauk'i in aka tab'osa, tun daga ranar idan yazo take hanani zuwa kai masa abinci sai dai wata da ban ta kaimasa, ko kad'an Aunty Sakina bata k'aunar abinda zaisa na bar aiki tare da ita, hakanne yasa albashin da take bani ya zarta na su Safnah.

Kamar kullum k'arfe 8:30PM muka tashi daga aiki, yau dai a mota hira muke tayi saboda basu yimin wulak'ancin bada abinci ba, Sarat ce tace.
"Nufin Aunty Sakina fa ko aure kikai baza ki daina aiki da ita ba ko? ”
Aysha tace.
"Haba dai sai kace ana hauka, ko wani miji ne zai yarda da irin aikin, bare ma muna fatan dukkanmu Allah ya kawo mana sauyin rayuwa. ”
Safnah tace.
"Hakane Aysha, amma ita Aunty Sakina a haukanta yarda Teema ke kawo mata kasuwa baza taso abinda zai rabasu ba ko da da aure, mu kuwa ba haka zamu so ba, muna son Allah ya bawa ko waccenmu gidan hutu da kwanciyar hankali yadda zamu manta da irin rayuwar da mukai a baya. ”
"To Allah yasa. ”
Nace, muka amsa da Amin dukkaninmu, dai² nan akazo layin su Safnah, sauka sukai suna yimana sai da safe, har muka isa layinmu babu wanda yace wani abu tsakanin ni da Aysha, kowa da kalar tunanin da yake a ransa.

Ina shiga gida naji gyaran muryar Ummi a band'aki, don haka kawai sai na juya gidan Maman Amira don nace mata na dawo ta markad'an waken, ina tsaye kuwa aka markad'an na d'auko, akan sallaya na tadda Ummi tana lazimi, tunda na shiga take jero mini sannu tana shi mini albarka, sai da na tace, sannan na hura ice na d'ora, kan kice meye wannan na gama nayi wanka, nayi shirin kwanciya, duk yadda Ummi taso naci abinci amma na k'i, rik'o hannunta nayi nace.
"Ummina. ”
"Na'am Munassata.”
Nafi awa nawa ina tauna maganar da zan gaya mata amman na kasa furtawa sai da naji tace.
"Munassa, ki gaya mini abinda ke damunki, a yanzu baki da kowa cikin duniyar nan da zaki gayawa matsalarki sama dani. ”
Sai da na k'ara damk'e hannunta sannan a hankula nace.
"Wai Yaa Nazee ne yace mini Abba yana nan da ransa bai mutu ba. ”
Zumbur Ummi ta mik'e tana bina da kallo.........

Kuyi k'ok'arin mallakar naku a hannu, tun kafin na gama bada pree page.

*HASKE A DUHU*
Aisha M Mahmud
(Meeesherh lurv)
*DUHUN DAMINA*
Maryamerh Abdul
(Kwaiseh)
*CIKIN DUNIYARMU*
BEBE'ARTH
*SARA DA SASSAK'A*
Qurratul'ayn
*ZAMANINA NE*
Munayshat

K’ungiyar Nagarta na farin cikin sanar da ku cewa zaku fara samun dukkan litattafan nan a farashi mai sauk’i wanda muke baku tabbacin babu asara cikinsa.
Litattafai ne da suka tara d’umbin ilimi, fasaha, tausayi, soyayya da duk wani abunda rayuwa kan iya tunkud’awa a babin d’an Adam.
Bamu baku tabbacin zallan farinciki a ciki ba, haka zalika bamu baku ta akasin haka ba. Ku yi tsammanin samun tirka-tirkan rayuwa a wadan nan litattafai, tabbaci guda da zamu iya mika muku, shine Zallar ilimi.

Zaki samu dukkaninsu akan 500, d'aya 200,biyu 250, uku, 350, hud'u 400, biyar 450.

Ku tuntub’emu ta wannan layi don tura katin waya:-
07067364721
Ku tura kudi ta wannan lamban akawun:-
Firdausi Salisu Aliyu
0430001991
GTB
Sannan a turo da tabbacin biya ta wannan lamba:-
07067364721
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*


[13/2/2020/7:14PM]


*CIKIN DUNIYARMU*
1⃣
Follow me on whatpad @Rashuna

PREE PAGE
__________________
*FIVE*

*KATSINA*
G.R.A
Tun cikin daren jiyan Sumayya ta shirya kayanta tsaf na tafiya, da safe Faisal ya kirata ya shaida mata jirginsu zai tashi k'arfe 12:00AM, aikuwa 11:30 yazo ya d'auketa, bata k'ara bin takan Khadija ba, bare kuma Fareedah, Mom ma a waya ta kirata ta shaida mata jirginsu zai tashi zuwa England, nanfa Mom ta buga shewa ta shiga zubaba mata kirari, a can England kuwa tunda aka kira Miqdad aka gaya masa jirginsu ya taso ya kasa samun sakat, sai zumud'in zuwan tauraruwarsa yake, Fareesah kuwa ta zama 'yar kallo, ga k'irjinta ke ta faman bugun lugude har yanzu, tana jinma yau kwata² cikinta bai motsa ba.
Tun ana saura awa d'aya jirginsu ya sauka miq yacewa Fareesah ta shirya su tafi airport ita kuwa tace baza ta ba, aikuwa fad'a sukai kace² shi ya rasa dalinlin da yasa dukan matansa suke fito da kishinsu fili, sab'anin Sumayya akwai ta da b'oye kishi, bata tab'a barinsa ya fito fili, gashi kuma itace duk a binda yace yana so itama zata soshi ko da kuwa bata son abun a ranta, kuma abu ko kore ne yace mata jaa ne zata bishi akan hakan, hakanne yasa yake matuk'ar girmamata a zuciyarsa, saboda yasan duk dalilin soyayyar da take masa ne yake jawo wa'yannan abu buwan.
Tana sauka a jirgi idonta akansa ya fara sauka, wani lallausan murmushi ta saki, tana jin tarin soyayyarsa da k'aunarsa na gudana cikin k'ofofin jikinta, tana son Miq soyayya mara iyaka, kuma tana matuk'ar kishinsa, hakanne yasa ta kore duk wata mace daga zuciyarsa, Fareesah ce kad'ai har yanzu ta kasa cireta daga zuciyarsa, ta rasa ta ya yarinyar ta kama zuciyarsa katamau haka har ya bata wani bigire na da ban a birnin zuciyarsa, amma ba komi idan ta kasa cireta daga zuciyarsa ai dole ta bar duniyarsa, don alk'awari ne tayi matuk'ar tana raye baza ta bari Miq d'inta ya kamu da soyayyar wata mace da ban ba ita ba, tayi matuk'ar k'ok'ari ma da ta bari Fareesah ta kawo har iwar haka cikin duniyarsu ita da Miq d'inta.

Da gudu ta iso gareshi ya wara mata dukkanin hannuwansa ta shige cikin k'irjinsa da tayi matuk'ar kewa, wata kyakkyawar runguma yayi mata, baisan da yayi matuk'ar kewarta ba sai yanzu da yajita cikin jikinsa, Sumayya da ban ce cikin matansa, akwai ta da tsafta ta jikinta da muhallinta, kullum cikin gyaran kanta take, matsalarta d'aya ce girki, shine abinda bata iya ba sam² anan ne kawai Fareesah ta kere mata, amma har kyahun sura da fuska duk ta kere musu.
"Welcome my Dear.”
Taji saukar muryarsa cikin kunnenta, lumshe idonta tayi tana jin wata sabuwar k'aunarsa na zagawa ta koina a jikinta, cikin muryarta me matuk'ar dad'i da ke saukar masa da kasala tace.
"Thanks my Miq, I really Miss you over.”
Jan hannunta yayi suka nufi mota, tana tambayarsa Fareeda yace mata.
"Na barta gida ne bata jin dad'i.”
"Subhanallah! Amma shine ka barta ka taho, me makwan ka zauna sai kamin kwatancen gidan na taho, maza² ja motar muje, kar wani abu ya same ta.”
Tunda ta fara maganar yake kallonta da tausayawa, da zata san cewa tayi baza tazo tararta ba ya ya zata ji? Ita tana can tana kishin banza da ita, ita gashi tana nan tana rawar jiki a kanta daga yin k'arya bata da lafiya, to ta ya zai had'a wata mace da Sumayya a zuciyarsa?
Karb'ar key d'in tayi daga hannunsa ganin bazaiyi sauri ba taja motar da gudu, shi kuma sai binta yake da kallon tsumamman love.

Tunda ya fita ya barta take shan kuka babu k'ak'k'autawa, ta rasa ta yaya² zata fahimtar da Miq Sumayya ba masoyiyarsa bace ta asali, duk ta inda ta b'ullo sai taga Sumayyan ta dad'e da toshe hanyar, ta riga tayi masa dabaibayi me matuk'ar wahalar kuncewa.
A inda ya tafi ya barta anan suka zo suka sameta taci kuka ta k'oshi idanuwan nan sunyi luhu² sunyi jazur, da gudu Sumayyan tazo ta tallafo ta jikinta tana jajjero mata sannu, ita kuwa Fareesah wata sabuwar tsanar Sumayyan taji ta kamata, a fakayce ta zabga mata harara, murmushi Sumayyan tayi tana kallon Miq.
"Miq ai ba muga ta zama ba gwara mu tafi asibiti ko don lafiyar Babynmu. ”
Baice mata k'ala ba yayi shigewarsa d'akinsa, tana ganin yabar falon ta saki Fareesan daga jikinta, dama ji take yi kamar ta rik'e garwashin wuta, wani banzan kallo ta jefeta da shi tayi k'asa² da muryarta gurin fad'in.
"Ni nasan lafiyarki k'alau, kinyi hakanne don kawai kar kizo tara ta, saboda kina bak'in cikin zuwana inda kuke, to ko zaki had'iyi zuciya ki mutu sai na kasance tare da Miq, ke ba wai kina murna gaki me miji ya d'aukoki kun taho, saboda ke kad'aice me haihuwa cikinmu, to ko zaki ajiye masa 'ya'ya dubu baza ki tab'a kai matsayin da na kai a zuciyarsa ba, ganin damata ne yasa na barku kuka taho a lokacin saboda akwai abu me muhimmamci da nake, don haka sai hak'uri yau nice da zumarki, haka kike kiranshi ko? ”
Ta tambayeta tana d'age mata gira d'aya, k'asa Fareesah tayi da kanta ba tare da tace mata komi ba, sai tsananin tsanar Sumayyan dake yaho a cikin jikinta, kuka take matuk'ar sonyi a yanzun amma baza ta iya yi a gabanta ba, mik'ewa tayi da k'yar ta shige d'akinta ta rufo k'ofa, zubewa tayi a gado ta saki wani sabon kuka me tarin bak'in ciki, tun sanda taji tattaunawarsu da Khadija, taji Sumayyan tana furta kalmar tsafi, ta gasgata zatonta akan ba haka Sumayyan ta bar Miq ba, daga baya ta koma gurin Khadija babu yadda batayi da Khadijan ba akan ta gaya mata matsalarta da Sumayyan, amma fir tak'i sai kuka da take kamar ranta zai fita, kuma tayi mata gargad'i akan ta fita sabgar Sumayya idon har tana son kanta da lafiya, tun daga lokacin take cikin muguwar matsala, gashi bata da wanda zata gayawa matsalarta Miq d'inne shikuma matuk'ar akan sukar Sumy ne bazai tab'a saura ranka ba.
Kuka take sosai, ita sai a yanzu ma take alak'anta mutuwar duka 'ya'yanta da Sumayyan.

Bayan shigewar Fareesah d'aki, Sumayya ta tab'e baki ta nufi d'akin da taga Miq d'inta ya shiga, a kwance ta taddashi akan gado yayi rigin gine, kwanciya tayi akan faffad'an k'irjinsa, ta saka hannunta kan gemunsa dake ta shek'i da k'yalli tana wasa dashi, d'aya hannun nata tana yawo dashi a k'irjinsa tayi k'asa da muryarta gami da narkar da ita tace.
"My Miq, don Allah kazo ka lallab'ata muje asibiti, ni ko ba don ita ba, ko don Babynmu ai maso muje, tunda muna son mu rayu dashi CIKIN DUNIYARMU, amma ba yadda banyi da ita ba, daga k'arshema ta kullo k'ofarta. ”
Shiru yayi mata, ya lumshe kyawawan idanuwansa, ta kuma cewa.
"Miq da kaifa nake.”
Ta fad'a a shagwab'e.
Janyota jikinsa yayi ya shiga yimata sabon wasu launuka, yana nuna mata ba k'aramin kewarta yayi ba,don yasan hakanne kawai zaisa ta manta da batun Fareesan, itama kuwa batai k'asa a guiwar bud'e masa sababbin pagikan da baisan dasu ba..........


Kuyi k'ok'arin mallakar naku a hannu, domin akwai babbar tafiya a gaba.


ALK'ALUMAN NAGARTATTU

*HASKE A DUHU*
Aisha M Mahmud
(Meeesherh lurv)
*DUHUN DAMINA*
Maryamerh Abdul
(Kwaiseh)
*CIKIN DUNIYARMU*
BEBE'ARTH
*SARA DA SASSAK'A*
Qurratul'ayn
*ZAMANINA NE*
Munayshat

K’ungiyar Nagarta na farin cikin sanar da ku cewa zaku fara samun dukkan litattafan nan a farashi mai sauk’i wanda muke baku tabbacin babu asara cikinsa.
Litattafai ne da suka tara d’umbin ilimi, fasaha, tausayi, soyayya da duk wani abunda rayuwa kan iya tunkud’awa a babin d’an Adam.
Bamu baku tabbacin zallan farinciki a ciki ba, haka zalika bamu baku ta akasin haka ba. Ku yi tsammanin samun tirka-tirkan rayuwa a wadan nan litattafai, tabbaci guda da zamu iya mika muku, shine Zallar ilimi.

Zaki samu dukkaninsu akan 500, d'aya 200,biyu 250, uku, 350, hud'u 400, biyar 450.

Ku tuntub’emu ta wannan layi don tura katin waya:-
07067364721
Ku tura kudi ta wannan lamban akawun:-
Firdausi Salisu Aliyu
0430001991
GTB
Sannan a turo da tabbacin biya ta wannan lamba:-
07067364721
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*


[17/2/2020/4:20PM]


*FITATTU SHIDA*

*CIKIN DUNIYARMU*
BEBE'ARTH
*HASKE A DUHU*
Aisha M Mahmud
(Meeesherh lurv)
*DUHUN DAMINA*
Maryamerh Abdul
(Kwaiseh)
*SARA DA SASSAK'A*
Qurratul'ayn
*ZAMANINA NE*
Munayshat

Fitattu 6 na siyarwane, idan kuna buk'atar d'aya daga ciki, ko kuma dukkaninsu, ku tuntub'emu ta wannan layi:
07067364721


PREE PAGE
_______________
*SEVINE*

*KANO*

Kuka nake sosai, ina jijjigata ina kiran sunanta, ganin ko motsi bata yi ya sakani na yo waje da gudu, kacib'is mukayi da Innan katsina, rik'oni tayi tana tambayata lafiya? Kasa bata amsa nayi, sai nuna mata ciki da nake da hannu, don magana baza ta iya fita ba a halin da nake ciki ko kad'an, cikani tayi, ta shiga ciki da hanzari, ni kuma nayi waje, har da gudu nake had'awa kafin na isa titi na taro adai-daita, ko da nazo na tarar Inna ta tallafota jikinta tana ta kuka, nace.
"Inna na samo mota kamota mu tafi asibiti. ”
Ina fad'ar hakan na shiga d'aki na harhad'o abinda Allah ya hore mana nazo muka kamata muka saka a mota, muna rik'e da ita ta gefe da gefe muka tafi, tsabar gi gita ko rufe gidan namu banyi ba.
Taimakon gaggawa aka bawa Ummi, ance jininta ne ya hau sosai, yanzu dai anai mata k'arin ruwa an rubuta mata magun guna, kud'in dake hannuna da wanda Inna tazo da su dasu na had'a mukai amfani.

Kwanan Ummi hud'u a asibitin aka sallamemu, taji sauk'i sosai, su Safnah har da Aunty Sakina duk sunzo sun dubata, ban jigata sosai ba kasancewar ga Inna ita ke lura da ita, kuma Ummin taji dad'in zuwan Innan, naji Innan tana gaya mata sai ta kwana biyu kafin ta tafi, saboda wa'yanda takewa aiki basa nan, ragowar kud'in da ya rage mana dasu nayo siyayyar awara, Inna ce ma ta k'arb'i aikin awarar ta hanani nayi, don haka washe gari da huri na tafi gurin aikina.

A kwana biyun nan na samu sok'i, kasancewar zuwan Inna, gurin aiki da wuri nake zuwa na lura Aunty Sakina ma taji dad'in hakan, don yanzu cinikin nata ya kuma bunk'asa.




______________
*ENGLAND*

Wani d'aki da ban ya shiga ya kulle kansa, k'wak'walwarsa wani irin juyawa take, magan ganun Fareesah ne kawai ke yawo a kwanyarsa, sosai magan ganun nata suka zurfafa tunaninsa har suka haddasa masa zazzafan ciwon kai.
Sumayya kuwa tsafinta ya nuna mata Fareesah bata san komai game da ita ba, sai dai tana zargin abinda ke tsakaninta da Khadija, kuma ta shirya d'amarar kunce k'ullin da tayiwa Miq, hatta camera da ta saita a gidan tsafinta ya nuna mata, wani shu'umin murmushi ta saki a ranta tace.
'Fareesah kenan, kinyi kad'an ki warware mini dukkanin shirina, zan mik'aki inda babu ke babu dawowa cikin duniyar Miq da Khadija bare kiyi yunk'urin kare su daga tarkona, dukkaninsu tarkona ya riga yabi jinin jikinsu shi da barinsu sai ranar da numfashinsu ya d'auke gaba d'aya, zanyi gaggawar aikata shirina akanki Fareesah tun kafin ki b'illo mini da hanyar da bazan iya toshe ta ba.’
Fitowa tayi ta nufo d'akin Fareesan, ita kuwa Fareesah tun fitar Miq daga d'akinta bata bari kuka yaci k'arfinta ba ta shiga band'aki ta d'auro alwala ta kalli gabas, hakanne yasa ko da Sumayya tazo sai ta tarar da ita tana sallah, toilet d'in d'akin ta duba taga miq d'in ba ya ciki don haka sai ta fita, tana tunanin inda ya tafi to, gashi yabar wayoyinsu a d'aki, a falo ta zauna tana jiran ta inda zai b'ullo.



________________
*MISRA*

Ya dad'e da sanin matarsa da 'yarta ba k'aunar tilon d'ansa suke ba, amma sun riga sun saye zuciyarsa da yaudarar riyar soyayya, wacce ta shiga jikinsa ta cud'anya da jinin jikinsa, abu kad'an bazai tab'a iya ganar dashi yaudarar riyar soyayyar da suke masan ba, abin mamaki shine, shi kansa ya kasa d'aukar mataki a kan hakan, duk sanda yayi yunk'urin nema masa taimako sai yaji abin ya fita daga ransa sam, amman ta dalilin abokinsa kuma amininsa sai da sukaje gurin wani malami don nema masa taimako, shine malamin ya sanar musu tsafi akayi masa me wuyar sha'ani, akwai wata bishiya a misra, itacen bishiyar zai samo, da ya samosa insha Allahu tsafin dake jikinsa shi da yaron nasa zai war ware, wannan shine dalilin zuwansa k'asar, ba tare da kowa ya san inda yaje ba, amman yau tsahon watansa guda a k'asar, duk sanda ya fita da niyar samo itacen saidai ya tsince shi a wata hanya ta da ban.........


ALK'ALUMAN NAGARTATTU.
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: [2/16, 6:04 PM] RASHUNA: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/L7ZWZtJoVg39WGbG36r78I
[2/16, 7:47 PM] +234 903 709 3702: *BEBE'ARTH*


[2/11, 10:57 PM]



*CIKIN DUNIYARMU*
1⃣
Follow me on whatpad @Rashuna


________________
*SIX*

*ENGLAND*

Bayan lafawar komai, sunyo wankansu tare sun gama shiryawa, da kulawa Sumayyan ta kalleshi tace.
"Dan Allah Miq kaje ka gano Fareesah, ko bakayi don ita ba, ai kayi don Babynmu dake jikinta. ”
Ba tare da yayi magana ba ya tashi ya fita, don ya gaji da naci irin na Sumayya tai nanata zance kenan har sai an mata abinda take so.
Tana kife akan gadon tun d'azun tana ta shan kukanta ya shigo, da,sassarfa ya isa gareta ya d'agota, saboda ganin irin kwanciyar da tayi.
"Baki da hankali ne zaki irin kwanciyar nan, ko so kike ki kashe mini d'aa. ”
Cikin shashshek'ar kuka tace.
"Ai gara ni na kasheshi tunda ba sonshi kake ba, har ka zab'i a kashe mana shi. ”
Sumayya dake bakin k'ofa tana jiyo abinda suke cewa maganar ta sauka a kunnenta, gabanta ne ya yanke ya fad'i, kaddai Fareesah ta san abinda ya kawo ni nan?
Ta shiga tambayar kanta, idan kwa ta riga da ta sani, aikina yana gab da lalacewa, da sauri ta bar bakin k'ofar ta koma d'aki

Ita kuwa Fareesah bata ma san ta furta wannan kalmar ba ko d'aya, yayin da shima Miqdad in ya sanya maganar tata a shirme, wata kyakkyawar runguma yayi mata, yana hura mata iska me matuk'ar d'umi a kunnenta, lak'was tayi a cikin jikinsa tana jejjero ajiyar zuciya, cikin sanyin magana yace.
"Ki rage kishi zumata, ki koyi kishi irin na Sumy. ”
"Nikam nafi son na k'are rayuwata da irin nawa kishin, domin na gasgata kishina ba bak'in kishi bane, kishi ne irin wanda ko wace mace zata so tayi koyi dashi, ba irin na Sumayya ba, Sumayya bak'in kishi ne da ita me matuk'ar muni, wanda babu mahaluk'in da zaiso yayi koyi da irinsa, amman kai idanuwanka sun makance akan Sumayya, ka toshe kunnuwanka babu ta yarda za'ai ka fuskanci inda ta saka gaba, ka ruga ka bata dukkanin wata yarda taka da amincewarka, yayin da nikuma nake ji a jikina ha'intarka take.”
Kallonsa tayi cikin ido, ta sakar masa murmushi, don tana ganin yadda ya k'ufula, k'iris yake jira ya fashe tana tab'o masa 'yar gaban goshinsa, tashi tayi taje ta rufe k'ofarta ta saka mata key, sannan taci gaba.
"Ina jii a jikina kamar rayuwata ta kusa zuwa k'arshe, sai naji bana son na tafi na barka cikin mugayen mutanen dake zagaye dakai amman kai baka sani ba, kuma kak'i ka bawa kowa damar da zai fuskantar dakai, a matsayina na masoyiyarka bazan bar duniyarka ba har sai na fara haska maka wani abun, ko da ta sanadiyar hakan zaka rabu dani.”
Tv ta had'a, sai ga vidion abubuwan da suka faru tun daga shigowarsu ta d'azu, cike da mamaki da al'ajabi Miq ke kallon Sumayya, murmushi me ciwo Fareesah tayi, sannan tace.
"Na rasa ta yadda zanyi na fuskantar da kai yadda Sumayyan ke d'aukarmu a bayan idonka na rasa, domin ta riga ta toshe dukkan wata kafa, amma sai d'azu tunanin had'a camera ya fad'o mini, shine dalilin da yasa nayi hakan, don ka gani da idonka kafi gas ga tawa, ba nayi hakanne don na b'ata tsakaninku da Sumayya ba, sai dai nayi hakanne don na gyara mu'amalar dake tsakaninmu a b'oye, ina so kabi Sumayya a hankula ka binciketa, ba wai ka tare ta nake nufi ba, ina nufin ka saka mata ido, domin akwai wani b'oyayyen al'amari tsakaninsu da Khadija, kuma Khadija ce ke azabtuwa da hakan, babu yadda banyi da ita ba ta gaya mini abinda ke faruwa tak'i, k'arshe ma cewa tayi idan ina son cigaban rayuwata na fita hanyar Sumayya. ”
Share k'wallar idonta tayi sannan ta k'arasa gabansa ta rik'e hannuwansa biyu idanuwanta na tsiyayar hawaye taci gaba.
"A kullum bani da wani buri da ya wuce na fuskantar da kai kuskuren da kakeyi a rayuwa, duk yayin da nayi yunk'urun yin hakan da fad'a muke k'arewa, amma yau dole na gaya maka, ko da zamuyi rabuwar da babu dawowa cikinta.
A matsayin ka na shugaba a tsakaninmu, dukkanmu mu hud'un hak'k'inmu ya rataya a kanka, kuma dole ne ka saukewa ko waccenmu hak'k'inta da ya rataya akanka, amma bakai hakan ba, ni da Sumayya kawai kawai kake sauke mana hak'k'ok'inka, su kuwa biyun me sukai maka, baka tsoran Allah ya kama ka da hak'k'insu?
Barema Khadija bata da kowa a duniyarnan da zai kula da lamarinta sai kai, amma ka banzantar da lamarinta, gashi tana cikin k'uncin rayuwa, duk tabi ta lalace, amma ka kasa fuskantar hakan, a hakan kake ikirarin Sumayya ta rik'e maka gidanka?
Macen da bata san ta sai.....”
"Dakata Fareesah”
Ya fad'a a tsawace, bud'e k'ofar yayi ya fice a fusace yana doko mata k'ofar.




___________
*KANO*
Kwana Ummi

Please Login or Register in order to submit comment