Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a b'oye ita take kulle zuciyata don ka da Fareesan ta yi tasiri a cikinta, abinda na lura da Fareesah kuma shine, ta na da sanyin hali babu ruwanta ga ibada da ta shiga jikinta ta zauna, ga kuma tsararran girki da kullum take yimana muna tand'ewa, sab'anin Sumayya da ko tukunya ina jin ba ta san yadda ake d'orawa ba, a hankali kuma sai naji hankalina yana kwantawa da Fareesah har wani bigire na zuciyata yake gaya mini ta dalilinta zan samu sanyin idaniyata, wannan ne yasa na raba musu kwana da Sumayya, ai kuwa Sumayya ta shiga tashin hankali mara misaltuwa ba tare da ni na gane hakan ba, don ba ta nuna mini ba, farkon fara tarayyata da Fareesah anan na kuma gano bam bancinsu da Sumayya, a zahiri Sumayya ta fi Fareesah kyau, a bad'ini kuwa Fareesah ta kerewa Sumayya fiye da zatonku ma's u karatu, ina mugun samun nutsuwa gurin Fareesah wanda a hankali ta fara samun mazauni a zuciyata kafin na bata babban matsayi a cikinta._
_Ba zan iya misalta muku farin cikin da na shiga ba yayin da na gano Fareesah na d'auke da gudan jinina, Sumayya ma ta tayani farin ciki wanda hakan yasa ta k'ara k'aimi a zuciyata na ji kuma ina mugun tausayinta, hakanne yasa nake k'ok'arin b'oye zallar cikina, Sumayyan ce ta shiga bawa Fareesah kulawa fiye da zatona, ni duk a ganina soyayyar da take mini ce ta janyo haka, ashe tana yi ne don ta samu hanyar da za ta b'arar da cikin, sai kuma Allah bai bata sa'a ba, tsafinta sam yak'i kama Fareesah, har sai da Fareesah ta haihu lafiya sumul, farin cikin da na shiga bazan iya gaya muku shi ba, bare kuma Daddy uban gayya, sai dai kaish kafin suna Allah ya karb'i abinsa, kuka ya dinga yi muka rasa me yake janyo hakan, da aka kaisa asibiti ma cewa sukai lafiyansa lau, babu yadda muka iya haka muka karb'i wannan k'addarar da hannu bibbiyu._
_Haihuwar Fareesah uku yaran na mutuwa, kuma duk an rasa me yake janyo hakan, ashe wai Sumayya ce duk ke soka musu allura guda takwas a tsakiyar kansu, har sai ta tabbatar sun lume baki d'aya, ana haka naje kano d'aurin auran wani abokina, munzo hucewa ta wani gida na dinga jiyo ihun mace, kuma ga mutane nan a bakin k'ofar gidan, haka kawai sai na k'asa jurewa hakan na tsaya a dai- dai k'ofar gidan...._


Gobe suna bai zama lallai nai typing ba, yau d'inma da k'yar na samu na yi, ku yi hak'uri babu zama ne.

ALK'ALUMAN NAGARTATTU.
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*


[7:4PM/2/4/2020]


Folow me on wattpad @Rashuna.

_Fitattu shida na siyarwa ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_
__________________
*THIRTY*
Juyi na yi na gyara kwanciyata gami da rufe littafin, lumshe idanuwana na yi ina girmama rashin imani na Sumayya a zuciyata.
'To yanzu shi yasan ta na aikata abubuwan nan kuma yaci gaba da zama da ita, ko kuma ina jin dai akwai wani abu da ya barwa zuciyarsa sani.'
Knocking d'in da naji ne ya katse mini d'an gajeran tunanin da na tafi, ta shi na yi da k'yar don wani bacci ne ke son fisgata, bud'e k'ofar na yi mukai ido hud'u da Daddy, kyakkyawan murmushi na saki gami da cewa.
"Reesah ga Daddy. ”
Da gudu ta baro wasan da take ta nufosa, d'aga ta ya yi ya cilla ta sama ya cafo suka saki dariya a tare kana ya juya ya nufi falo da ita, biyo bayansu na yi har lokacin murmushi yak'i barin fuskata don ina matuk'ar k'aunar Daddy, jinsa nake tamkar mahaifina, akan kujera suka zauna da ita ta na ta masa surutu, har k'asa na tsuguna na gaishe sa, murmushi akan fuskarsa ya amsa mini yana sakawa rayuwarmu albarka.
"Kici gaba da hak'uri da Sadauki, wata rana kece ta farko da za ki fara fad'in alkhairinsa, kuma ina mai tabbatar miki za kiyi alfahari da kasancewar sa cikin duniyarki, kamar yadda shi ma akwai rana mai zuwa da zaiyi alfahari da ke, don ke d'in kin zamo masa alkhairi shi kuma zai zamo miki haske cikin rayuwarki, ka da abin duniya ya saka ki canja daga yadda na sanki, duk wani abu da mutum zai tara ko yana so ko ba ya so dole haka zai ta fi ya barsu kuma tafiyar da babu dawowa cikinta, ka da kici amanarsa, kar kuma ki bari a ci amanarsa, da shi da Fareesah dukkaninsu amana ne a gareki, ina fatan kuma Allah ya ta ya ki rik'on amanar. ”
"Amin” Nace, yaci gaba da cewa.
"A hak'ura da zuwa makarantar Fareesan har zuwa sanda abubuwa zasu dai daitu, don ba mu san wani mak'iyin ne ke farautar rayuwarku tun kan ma ya san hak'ik'anin ku d'in su waye ba, zuwa gobe da safe zai zo ya maida ku gida, ni nace ya barku anan d'in saboda ina buk'atar ganin jikata. ”
Ya kai k'arshen maganar yana jan karan hancinta, don ta k'ura masa ido tana ta kallonsa kamar ba ta tab'a ganinsa ba.
"Ba mutuwa dai zan yi ba yanzu, har sai Mommynki ta haifo mini jikoki dozin.”
Yakai k'arshen maganar yana dariya, murmushi nima na yi ina sunkui da kaina cike da kunya.
"Daddy Mommy za ta siyo mini k'anne da yawa?”
Reesah ta fad'a cikin maganarta ta yara.
"Eh za ta siyo miki da yawa da yawa ma."
Ya ba ta amsa, sauka ta yi daga jikinsa ta saki tsalle da murna, murmushi ya yi irin nasu na manya kana ya mik'e gami da cewa.
"To zo muje ku karb'o tsarabarku.”
Yana mai rik'o hannunta ni kuma na biyo bayansu, sojoji ne birjik a harabar gidan, bud'e motar ya yi ya bawa Reesah ledarta da ban nima tawa da ban, rik'o hannunsa Reesah ta yi gami da cewa.
"Daddy anjima za ka dawo?”
"Eh”
Yace mata gami da sakar mata murmushi ya shafa kanta.
"Allah ya yi miki albarka, ya kare ki ga dukkan wasu azzaluman mutane, masu son ganin bayan rayuwarki da ta mahaifinki.”
Daga haka ya shiga motarsa ya jata yana jin zuciyarsa wani iri da ban yayin da nikuma na janyo hannunta muka koma ciki ina mai jin soyayyarsa na k'ara girma a zuciyata, rigima Reesah ta so ta yimini da k'yar na lallasheta na bud'e mata alawoyin da Daddy ya kawo mata.




_A tsaye suke suna hirarsu ta d'a da mahaifi cikin annushuwa da farin ciki sai k'yak'yata dariyarsu suke, baiyi aune ba yaga wata mace ta silalo ta bayan Daddyn fuskarta lullub'e da wani bak'in yadi ta caka masa wuk'a a wuyansa, wata gi gi tacciyar k'ara ya saki gami da kiran sunan Daddyn._
Gaba d'aya zufa ta keto masa da ya farka daga mummunan mafarkin da ya yi, Khadijah ma a firgice ta farka ta na tambayarsa lafiya, bai furta mata ko da kalma d'aya ba, don ji yake bazai iya d'aga harshensa ba muddun bai ji lafiyar Daddynsa ba, hannunsa na rawa ya lalibo numbersa ya kira.
Cikin bacci Daddy yaji wayarsa na k'ara, cike da tunanin mai kiransa a cikin wannan tsohon daren ya lalibo wayar ya yi picking da hanzari don gudun ka da ta katse, muryarsa cikin bacci yace.
"Sadauki lafiya? ”
Wata wawiyar ajiyar zuciya ya saki, gami da furta Alhamdlillah cikin kyakkyawan furuci.
"Lafiya lau Daddy, dama na kira ne naji lafiyarka. ”
"Kar ka damu Sadauki, babu abinda zai faru da mu sai abinda Allah ya rubuta mana cikin rayuwarmu, duk abinda kaga ya samu bawa dama muk'ad dari ne, ka dinga tunawa da hadisin nan da yake cewa:
Da dukkanin al'umma za su had'u don su amfanar da kai da wani abu to ba zasu tab'a iya amfanar da kai ba sai dai da abinda Allah ya rubuta a gareka, kuma da zasu had'u akan su cutar da kai da wani abu ba za su tab'a iya cutar da kai ba sai dai da abinda Allah ya rubuta a kanka, an d'auke alk'aluma kuma takaddun sun bushe.
Don haka dukkan wata rayuwa da za ka fuskanta ka karb'eta hannu bibbiyu Allahn da yake jarabtarka yana nan sane da kai, akwai ranar farin ciki tana nan zuwa, sai dai ina fatan lokacin yazo sanda nake kusa da duniyarka ba sai na yi nesa da ita ba, yanzu ka yi kwanciyarka ka kwantar da hankalinka babu abinda zai faru sai abinda Ubangiji ya tsara mana.”
Jikinsa ne yayi sanyi k'alau, yana jin yadda gabansa ke fad'uwa a kai² har sukai sallama ya kashe wayar, alwala ya yi ya kalli gabas don ko ya koma ya kwanta baccin ba zai zo ba.


Washe gari da safe Mom ta fice ba tare da sanin Daddy ba, abinda ba ta sani ba yana ankare da ita ta na fita yabi bayanta, shima kuma abinda bai sani ba tayi hakanne don ya biyo bayanta, cikin wani gida yaga ta shiga, ba tare da tunanin komai ba ya bi ta a baya, don idonsa ya rufe da sanin abinda ya kawo ta cikin gidan.
K'asa kunne ya yi jikin k'ofar da ya ga ta shiga, muryar Sumayya ya ji tana.
"Mom, yau Allah ya cika mini burina ina d'auke da ciki wata biyu, duk da ba cikin Miq d'ina bane amman kuma zai taso a d'ansa, zanyi amfani da wannan cikin don ganin na k'unta tawa duk wanda ya shigo Cikin duniyarmu ni da Miq d'ina........



ALK'ALUMAN NAGARTATTU.
[4/6, 11:10] Ummu Isma'il: *BEBE'ARTH*


[8:12PM/1/4/2020]


Folow me on wattpad @Rashuna.

_Fitattu shida na siyarwa ne, idan kina buk'atar d'aya daga ciki ki tun tub'emu ta wannan layi;07067364721_
__________________
*TWENTY NINE*
_A cikin sati guda Daddy ya d'aura aurena da Khadija, bayan ya ji duk abubuwan da suka faru da rayuwarta shima ya yi mugun tausaya mata, ba'a samu rikici ko tashin hankali ba daga gurin Sumayya da Fareesah, ko wacce ta yi mugun fahimtata, k'arara nake hango tausayin Khadijan a idanuwan Fareesah, watana guda da auran Khadija Inno ta hura mini huta sai na auri Fareedah._
_Fareedah 'yar k'anwar Inno ce uwa aya uba aya, tun da ta d'an tasa mahaifiyarta take son na aureta, hakanne yasa ta dinga amfani da Inno don ganin buk'atarta ta biya, tana son aurena da Fareedah ne don su samu dukiyata yadda ya kamata, bare ma idan burinta ya cika Fareedan ta samu haihuwa tare da ni, don a yanzu Daddy ba shi da wani buri da ya huce yaga jikansa tun kafin ta Allah ta kasance a garesa hakanne yasa suke kwad'ayin ganin jikan nasa ya fito daga tsatsansu don sun san zai samu matuk'ar ga ta mara misaltuwa_
_Kwata² ban bawa Inno fuskar auran Fareeda ba hakanne yasa nake kakkauce mata, don ni har ga Allah bani da ra'ayin yin mace sama da d'aya sai gashi kuma mata uku suna cikin k'addarata kuma babu yadda na iya Allah ya riga ya tsara hakan tun fil azal, to ashe ma Inno tana ta shirye²n bikina da Fareeda sai ana ya gobe d'aurin aurena da Fareeda aka kaiwa Daddy katin d'aurin auren ba tare da ni na sani ma, kirana Daddy ya yi ya nuna mini katin gami da mini nasiha akan na yi biyayya a gareta mahaifiyata ce aljannata na k'ark'ashin k'afarta idan har ina buk'atar shigarta to itama sai na mata biyayya kamar yadda nake masa ko ma fiye da hakan._
_Haka na tara matana na labarta musu auren da Inno ta k'ak'aba mini, suma sun karb'i sabuwar k'addarar da tazo mini da hannu bibbiyu._
_Had'ad'd'an gida na tafka ko wacce na mata phart d'inta da ban, Inna ma na yi mata na ta da ban, phart d'ina ne a tsakiyar gidan, na Sumayya da Fareesah a gefen damana, na Khadija da Fareeda a gefen haguna, na Inna kuma daga gefen gidan._
_Cikin matan nan nawa Sumayya da Fareesah ce kad'ai ke samun lokacina, kuma dukkaninsu suna matuk'ar k'ok'arin ganin sun dai daita tsakanina da sauran matan nawa amman hakan sam ya faskara, Fareesah ta sha yin fishi da ni haka za ta gaji ta sauko, ita kuwa Sumayya dama na munafirci ne, ba yadda ba tayi ba don ganin ta cire soyayyar Fareesah daga raina sai dai ALLAHN da ya dasa ta har yau bai bata damar cireta ba, kuma tana nunawa Fareesan soyayya da kulawa,ina yawan samun masu kawowa Sumayya suka amman ba wanda nake bawa fuska k'arshe ma sai dai mu b'arke da fad'a, sai da Fareesah ta yi haihuwa shida duk Sumayya na kashesu ba tare da ansan me take aikatawa ba, mun jajje neman magun guna gurare da dama an tabbatar mana ba sanyi ne ko zafi ne ke kashe mana yara ba, rayayyen ne Allah bai kawo ba, to dama abokin Daddy yana ta gaya masa mugayen halayen Mom da suke a b'oye yak'i yadda da shi, hakanne yasa ya dinga nema masa magani a b'oye, a hankali shima tunaninsa ya fara dawowa jikinsa, hakanne yasa ya kuma zuba ido akan takun Mom da Sumayya har ya fara samo haske kad'an daga cikin b'oyayyan halinsu hakanne yasa ya kuma mik'ewa tsaye gurin nemawa d'ansa magani._
_Khadija ta sha kama Sumayya tana tsafi amma kuma sam ta k'asa gayawa kowa, itama Sumayyan ta san Khadijan ta ganta hakanne yasa ta yi babban shiri a kanta, haihuwa ta bakwai da Fareesah ta yi shine Khadija ta kama ta tana sokawa jaririn allura a ka, firgita iya firgita ta yita da gudu ta nufi sashen Inna don ta san ko taje ga Miq ba zai saurareta ba, amman ko da taje gurin Innan kasa furta kalma d'aya ta yi, sai kuka da ta fashe da shi, ga abinda take son fad'i ya tsaya mata a mak'oshi kuma babu damar fitar da shi, tun daga lokacin nutsuwa ta bar jikin Khadija don sosai Sumayya ta sakota gaba, duk wani mugun abu in za ta yi ta daina b'oye mata don ta san ba za ta tab'a fad'e ba, sanin abinda take aikatawa shine babban kuskure a rayuwar Khadijan._
_Cikin da Fareesah ta kuma samu a shine suka yanke shawarar tura ta lahira gaba d'aya har abin da ke cikinta, yayin da shikuma Daddy ya k'udurci abu a ransa ba tare da ya sanarwa kowa ba, cikinta na shiga wata takwas Daddy ya turasu England ba tare da sanin kowa ba, ya kuma hana sa gayawa kowa daga cikin matansa, a lokacin da zasu tafi ne kuma ta gano abubuwan da ke faruwa tsakanin Sumayya da Khadija, babu yadda ba ta yi ba Khadijan ta gaya mata abinda ke faruwa amma fir ta k'i._
_Shikuwa Daddy ya tura su England ne ba wai don bai yadda da k'addara ba sai don k'ara gasgata makasan jikokin nasa yana tare da su. sai da ya yi masa gargad'i sosai kada ya sake ya sanarwa da kowa k'asar da suka tafi._
_Dr Hisham abokinsa ne tun na yarinta, shima d'an katsina ne a England ya yi karatunsa na likita shine suka rik'esa aiki a can, dalilin da yasa kenan yasa Daddy ya zab'i su tafi England._

Mun riga munyi abubuwan da suka faru a baya, sai kuma kuci gaba da biyo alk'alamin Bebe'arth don war ware muku abubuwan da ke gaba.



Mai buk'star cigabansa ya sameni Kai tsaye a wannan layin 09037093702

ALK'ALUMAN NAGARTATTU


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment