Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Baba yana yawan ziyaranta inda in yazo Meenat, zata dinga jawo mutane azo aga mahaifin ta,
Shiko Baba samaila yanajin dadin hakan da yar na shi take yi mai a cikin yan uwanta,
Saboda gudun surutu yasa idan an samu hutu mai gajeren zango Meenat bata zuwa birnin kebbi,
Saidai idan dogon zango ne takan je tayi hutu a cikin yan uwanta,,,,

*** *** ***
Mama Ladi wace tun ganin yadda Meena ta koma da tazo hutu sai hankalinta ya tashi,
Amma a fili sai cewa take yi sokoto fa kawai mutum ya tafi amma daga uwa har uba duk sun rude sunawa mutane wani zance wai diyar su na karatu sokoto,
Wanan irin abin da, mama ke yi duk wanda yasan yadda matan wanan shiyan suke, ba wani bakon alamari ba ne wanan,
Don haka abinta sam bai damu Zurian Baba Samaila,
Ita mama Ladi bawai Baba samaila take wa wanan kyashin ba kowa ne na gidan idan taga mai da alamar dan haskawa,
To fa da ita da mai shi kwana biyu sai anji su don sai sanadin da tai fada da mutum tai mai gori,,

*** *** ***
Salawatu wata matashiya ce ma aikaciya a ma,aikatan su Abubakar,
Fittaciya ce agurin aman tana yawan ji da kan,ta gata yar gaye irin na karshen nan,
Tana duke saman computer dake a gaban ta tana aiki,
Muryan aminiyar ta kuma babban kawar ta, lubana, taji tana cewa kai,
Amma wanan gayen karshe ke nan bai da inda yake da makusa,
Ji tafiyan shima kawai don Allah,
A hankali Salawatu ta dago kan ta daga abinda takeyi,
Gaban ta ne ya ba da ras don ganin irin haduwar da guy din yayi,,
Amma dai wanan bako ne ko ?
Salawatu ce ke tambayar,
Lubana ta bata ansa da cewa shine mana aka cenza mai,makon Emos,,
Da mamaki suke kallon Abubakar har ya karaso inda suke ya wuce,
Bayan shi suka bi gaba daya da kallo a lokaci guda, suna, mamakin halittan shi,
Don dai su ya yi masu a rayuwan su sai dai matsala guda shine da alama baida sakin fuska,
Salawatu tace Lubuna ki sa aranki daga yau cewa kamar na samo kan shi na gama, ko,
Amma fa ni abinda na hango Salawatu kamar wanan bazai wani girmay ki sosai ba,
And so what ?
Ta fada cikin wani irin yin har da idon ta,
Shine ma ai daidai move, di na, idan baki sani ba,
A cikin hausan na yan yaren garin Abuja suke magana,

*** *** ***
Tun daga wanan ranan Salawatu ta fara shi,shigewa Abubakar, da gaisuwa ta fara mashi a cikin ladabi,
Sai kuma ta fara dan canza shigar ta irin na yaran hausawa ainihi,,,
Duk yadda tasan za tayi su hadu a rana sai Salawatu tayi don su hadu, da Abubakar ,
Sadiya da Samira duk sun dawo nan Abuja yanzu tare da shi,
Inda ma,aikatar su, ta bashi gida maikyau ga kuma girma sai dai ba,a cikin kwatas din su bane,
Sadiya yanzu da yake andawo arewa tana dan ganin yadda mata ke gyara ,
Hakan yasa ta itama tadan fara gyaran jikin ta amma sama,sama,,,,,,
Yanayi yanzu ya canza sosai don cigaba ya samu sosai gurin Abubakar,
Bin kwakwafi irin na Salawatu har saida ta gane gidan Abubakar,
Da sannu har ta dan fara kaiwa matar shi sadiya ziyara agida,,,,,



ZEEE MAKAWA YELWA
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸🕸🕸
1⃣0⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA


SIRAATAL- LAZEENA AN'AMTA `ALAIHIM,GHAYRIL-MAGHDOOBI `ALAIHIM WALAD-DA,AALLEEN (AMEEN)

AFUWAN YAN UWA A POST DIN JIYA PLS GYARAN KU A GARENI YA NA KARA MIN KARFI DA KWAZO A KO DA YAU,SHE NAGODE KWARAI DA KULAWAN KU,,,,,,,

A, zaune yake cikin office din shi wanda yasha kayan electronic din ma,aikata,
Kan shi a duke yana faman aikin tun safe baida lokacin kan shi idan har yana office, din,
Hakan ya sa ba kowa ne yasan da shi ba a ma,aikatan, nasu saboda girman gurin,,
Abubakar yana hankalce da irin harin da matan ma,aikatan ke kawo mashi,
Sai dai yakan gwada masu tankar bai fahinci manufar su ba,,,
Don shi ko a gida bai faye son hulda da yan uwan shi mata ba,
Don a ganin Abubakar sakewa mace fuska raini ne hakan ke jawo wa mutum so,sai,,,
Hakan ya sa duk wata mace wace ta san ko waye Abubakar za ta shede shi da cewa mutum ne mai wulakanci sosai,
Don abin ya zama mai jiki irin tsare gidan shi ba mata ba kawai har ma mazan,

Tafiya, yake kamar mai hanzari, hannun shi guda saye a cikin Aljihun shi, hanyar zuwa, gurin saida abincin ma,aikatar nasu ya nufa,
Ba kasafai zaka ga Abubakar a wanan gurin ba,
Iya karshi, indan harka ganshi drink ne kawai zai sha sai snacks wani lokaci
Sauri ya ke yi don ya karasa gurin saboda yunwa yakeji gashi kuma da aiki a office da yawa,
Tun daga nesa,suka hango shi, a lokacin ita salawatu ta juya bayan ta tana waya,
Ta,bota Lubuna tayi da dan yatsunta ta na gwada mata shi,
Cikin sauri Salawatu ta juyo don idon ta ya gane mata shi ,
Shigan shi cikin restaurant din masu aikin gurin ya samay shi don jin ko may zai kawo mai,
A daidai wanan lokacin Salawatu suka karasa karasowa gurin ita da Lubuna,
Cikin wani, ladabi, na kissa suke gaishe shi harda dan rusun nawa,
Sir inji Salawatu, ya mutanen gida ?
Cikin mamaki yadan dago kai don jin abinda ta fada ,
Sai,dai yana mamaki wasu mutanen gida ne ta sani har take tambayar shi,
Mamaki a fuskan shi karara yadago kai da niyar tambayar ta,
A lokacin ne kuma drinks din da yai oda ya iso gare shi,
Ganin su gurin ya sa ma,aikacin ya tambaye shi a cikin ladabi da cewa,
Ko za,a kawo masu nasu abin shan ne, su ma, ?
Sai ya dago don jin may za su ce,
Lubuna tace kwarai kuwa mungode kwarai Sir,
Bayan wucewan ma,aikacin ne Lubuna tace,
Wanan sunan, ta Salawatu , nikuma Lubuna nake,
Mun yaba kwarai da mutuncin ka a wanan ma,aikatan ,
Muna ganin ka shine yau nace bari muzo don mu gaida kai,
Sai da ya kurba drinks din dake a cikin cup din dake hannun shi tukun tare da lumshe idon shi ,
Saboda mamakin irin karfin halin da su kayi na taron shi haka kai tsaye,
Dama yana da labarin yan matan Abuja tun lokacin da akai mai transfer ake bashi labarin su,
A takaice ya bata ansa da cewa nagode, Lubuna da mutuntawan ku,
Daga haka mai,kawo masu drinks, din ya iso dauke, da tiren drinks din su,,,
Daidai lokacin da zasu fara sha ne shikuma Abubakar ya mike da niyar barin gurin,,,
Cikin wani irin muryan kissa suke cewa mungode Sir,
Hannu ya daga masu alamar, is,ok, daga haka kawai ya sa kai abinshi ya bar gurin,,

*** *** ***

Dawowan Abubakar Abuja yasa izuwa yanzu mutanen gidan su suna samun labarisa akai,akai,
Bakamar lokacin da yake zaune a Lagos ba da mai jin duriyan su,
Hakan yaza yanzu labaran ci gaban da Abubakar ke yawan samu yake isowa garin birnin kebbi,
Sai dai wanan labarin a gurin mutane har da kari sikeyi a kai,
Sadiya tafi Abubakar, rashin kula da,gida don ita indon ta na,ta ne ma suyi zaman su a can ba,tare da sun shigo kebbi ba,
Abu guda ne shi duk wanda yasan Abubakar idan har yai sa,an ganin shi zai dan iya wa mutum alheri kadan,
Sai dai kuma idan har sako zai yi zuwa gida, to fa mama Ladi, ita ce za tai kato,kato da sakon sai wanda ranta yaso abawa,
Duk da ko malam tsoho sai taga dama bashi abinda taga dama,
Hakan da takeyi shi ya kara tayarwa da malam tsoho hankali don yasan cewa nan gaba gaba,daya kan zurian nashi zai kasu ne daban,daban,,,
Yanzu kwata,kwata ta daina, bawa yan gidan alheri sai dai takai waje don bidan suna,

***** ***** *****
Zaune yau yake a office din shi aiki yai mai yawa kamar kullun,
Don yanzu komai kara bunkasa gaba gaba yake mai,
Dawowan shi daga gurin meeting ke nan yana kokarin ganin, ya shigar da abinda sukai meeting akai cikin net,
Sakatariyar office din su, ce ta turo kofa, ta shigo tana saye da wando da riga bakake,
Batare da ya dago kai ba, ya ke ce mata, yadai Ruth ?
Tace Sir cikin harshen turanci kana da bako kusan kwana biyu ke nan yana zuwa wai yana son ganin ka ne,
Cikin sauri ya dago kan shi yana mai kallonta,
Inda ya kara maimaitawa da cewa kwana biyu shine baki fada min ba Ruth sai yau,
Ruth ta dan sosa kai tace cikin rusunnawa,
Gani nayi miutumin bai cancanci ya ganka bane don baiyi kama da abokin hurda ba,
Ya fi yi kama da Beggars,
Cikin dan daka tsawa ya katse ta da cewa, ki ce ya shigo pls,
Umurni na baki daga yau kada ki kara hana bako na gani na kowani iri ne,
Umurni na baki kada ki kara kawo min naki uzurin,
Irin yadda yai magana yaba Ruth tsoro don haka jiki na rawa tafita da sauri don yiwa bakon iso,
Don tunda sabon boss din na su yazo bata taba ganin bacin ranshi ba irin yau,
Karan bude kofan tayi don shigowa da bakon da tace din yana ta ziyaran su,,
Ba, wani bane bakon illa Baba masijan su na Lagos watau, malam mudi,,
A cikin mamaki yace malam Mudi kaine a nan kuma ?
Barka da zuwa,
Kasa malam Muddi din yazube yana cewa Rankaidade barka da warhaka,?
Yau she kazo garin nan tashi mana Bissimilla ga guri kazauna yana mai nuna mai gurin zama,
A dan ta kure malam mudi ya zauna saboda yana ganin bai dace ya zaune kusa da shugaban shi ba,
Bayan ya sha rruwan da Ruth takawo maine dan kadan
Sai kuma yadago kai yana mai kallon Abubakar din,
Hawaye suka zubo mai inda yake cewa don Allah gurinka, nazo rankai dade ka tausaya min ,
Kai min hanyar da zandawo nan Arewa a cikin yan uwa na in har da halin yin hakan, ?
Dama sana,a nakeyi acan bayan yar kariyar arzikin da na samu shine wani yai mun hanyar wanan aikin,
Sai kuma ya kara sa yar sheshejan kuka, alokaci guda,
Subbahanallah haba malam ai zancen bai kai na kuka ba,
Ka tsaya muyi maganar fahinta kawai ina ga zaifi,,,,

***** ***** ***** So,sai duk wani girma na diya mace ya baiyyanawa Meenat,
Da ka ganta kasan cewa daga zurian gidan malam Manya take sabode ta debo irin jikin iyayyen ta maza, a gurin tsayi,
Sai dai ita abin nata ya raba gida biyu ne don duk fuskan ta da launin jikin ta na fulanin gwandu, ne,,,
Wanda yasan Meenat a baya yanzu idan ya ganta yasan cewa a kwai canji sosai ga lamarinta,
Ta waye ta zama yar birni sosai, ga turanci a bakin ta, kamar wace ta taso gidan da ake turanci tun tana karama,
Wayen Meenat ya karawa mama Ladi hassadan ta sosai a ranta don tasan cewa ko yar ta Samira wace ke can Abuja gidan yayan ta batai wanan kyaun ba,
Gashi duk Meenat zata zo gida sai Uncle Shafi,u yaba da motar shi ankawo ta cikin mutunci, tare da dan tsaraban ta duk da ba yawa amma sai ankasa an,bawa kowa tsaraban, a gidan,,
Ita ko mama wanan abin ke kara sa ta yanzu jin haushin Samaila da iyalan shi,,
Don duk wani motsi na, su da wani tako na,su duk idon mama Ladi yana kan su,
Babu karin haushi sai yadda Malam ke alfahari da yar jikar nashi,
Tundai da aka nuna su suna wani gasan karatu a NTA sokoto,
Wanda kowa ke murnan ganin ta cikin TV tana wasa kwakwalwa da sauran dalibai, yan uwan ta,,
Don haka ta raya arayuwan ta cewa bazata taba barin Samaila har yai nisa akan harkokin ci gaban shi ba,

***** ***** *****
Wanan zuwan hutu da yan makaranta suka samu na dogonzango, shi ya sa duk yan gidan a wanan lokacin suna gida tare da mahaifan su,
Ganin irin yadda karatun addinin jikan nashi ya samu ci gaba fiye da tsanmani shi,
Yasa shi kara yin alfahari da ita acikin zuciyar shi kamar yadda ya ke yi wa duk wani daga cikin iyalinshi da ya kyauta,ta mai,
Samira ma tasamu zuwa wanan hutun na dogon zango daga Abuja, kamar kowa, sai dai kuma zuwanta da kamar sati sai ga sakon yayan nata watau Abubakar yana bukatan komawan ta, don matar shi bata da lafiya wai,
Kuma ana zaton ko karuwa ne ta samu, na aure,
Hakan yasa Samira tayar da hankalinta sosai akan cewa bazata koma ba ita,
Asalima daga wanan dawowan ita tadawo gida ke nan kwata,kwata,
Ganin yadda samira taki yarda ta koma yasa malam manya yanke hukuncin cewa duk yan matan gidan su shirya tunda su cikin hutu ne su tafi gidan yayan nasu Abuja,,,,
Wanan tafiyan yasa rayuka da dama agidan sun baci saboda yawancin iyayyen yaran basu so ba,
Badon komai ba sai don mama Ladi wace sam bata son aje a gogi dan ta,
Amma malam ya rufe idon shi yace duk Abuja zasu tafi hutu,,

Abubakar baida labarin wanan tafiyan nasu sam don haka,
Bama zuan na kannen nashi wani tanadi yadda ya kamata ba,
Motar da Malam yai masu shata sai musalin karfe biyar na yamma ya shigo garin Abujan inda duk kan su su biyar a gajiye suke,
Direct gidan shi dake NYanya suka nufa akan jagoran Samira wace ta san gidan,
Tun saukan su gashi a gajiye suke amma tun a lokacin suka fara fuskantar matsala daga matar gidan,
Don da isar su gidan suka kwankwasa sai da aka dauki mintoci kafin suji anbude kofan,
Ganin haka a lokaci guda yasa ta waro idon ta waje tana mamakin hakan,
Abinda ya fito a bakin ta shi kune haka tafe ?
Daga haka ta samu guri ta zauna abinta,
Samira,ce ta ce masu su zauna ga guri nan, inda duk kan su sukabi kujerun da kallo don kuran da sukayi,
Nan take wani irin kazantar gidan ya dira a zuciyar Meenat,
Ido tabi falon dashi da kallo inda a take ta hango ko may gidan ke ciki,
Ruwa samira ta gabatar masu na sha tare da wucewa dakin da take zaune, a cikin ,
Kayan su ta umurci su kai don su, ajiye aciki kafin su san na yi,,,
A dadafe Meenat tai alwala a ban dakin nasu saboda kazantar shi,,,

Idar da sallah su abuna farko da gidan ya fara cin karo dashi shine gyaran bandakin su, dukka biyu,
Dare yayi don haka Meenat ta bari sai zuwa gobe ta gyara falon,
Amma duk da haka sai da ta dan taba gyara, sama sama ita,ma,
Dawo wan Abubakar ya samu bakin shi unexpected a gidan nashi,
Cikin mamaki yake tambayar su yadda akayi sukazo gaba dayan su,
A lokacin Meenat tana can dakin samira tana dan gyaran inda zasu kwanta,
Wanan training din Meenat ta kara samun shine a zaman da takeyi tare da amaryan uncle din ta na sokoto ,,,
Uwa uba kuma ga maman ta mace mai mugun tsabta iyaka dai ace ita a local waje take da zama,
Shima dai maigidan tun bayan ganin da sukai mai basu kara ganin shi har kwana biyu da zuwan shi,,,,,,,,,,


ZEEE MAKAWA YELWA
[7/2, 12:55] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸🕸🕸
1⃣1⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,

MAALIKI YAWMID-DEEN,,,,,,,,,

A, zaune suke a dakin na Samira da ke acikin gidan yayan nasu Abubakar,
Kusan duk kan su biyar idan ka dubi fuskan su babu an,nuri a cikin sa,
Murja diyan baba shaibu itace ta fara kau da,shirun da dakin yayi da cewa,
Yanzu Samira ana nufin cewa a haka kike zama da wa yan nan mutane har tsawon shekara kusan biyu fa ake neman yi yanzu ,
Samira wace tana zaune tana gyaran kumbar kafan ta ta,ce hmm murja ke nan,
Ai saukin abin ma kawai, wani lokacin nakan dan samu kulawa daga shi yayan namu,
An ma ita wanan mai kama da an shuka dusar a haka rayuwan ta yake,
Hmmm ni wanan matar tun farko ban taba jin son ta azuciya na ba wallahi,
Meenat cikin mamaki ta dago kai da sauri ta kalli Aisha tace,
Haba dai Anty Aisha bai,dace kice haka ba ga matar dan uwan mu,
Ita,ma yanzu fa a matsayin yar uwa take gare mu,
Wani harara, Nafisa ta watso mata tace ke ko Meenat, zaki fara irin zancen ki ke nan,
Yau,she zata zama yar uwan mu a haka,?
Ki duba fa tun ranan da muka zo yau kwanan biyar a gidan nan amma ko sau guda wanan matar bata samu time din mu,
Kina gani da ace mu yan uwanta ne zatai muna haka ?
Ni dan Allah daga ita har mijin ta kuma daina mun zancen su pls,
Wallahi badon kawai ina,son inzo inga Abuja ba da ba,abinda zai sani zuwa wanan wajen,
Wasila, da itama karo na farko ke nan da ta fara magana tun zaman nasu sai cewa tayi,
Kamar babana yasan may zamu tarar da zamuzo yaba kudi yace duk yadda muka gani in samu abinda zan saye,
To yanzu may zaki gani wanda zaki saye anan bayan ko kofan gida bamu taba lekawa, ba,
Ke ni fa in badon malam tsoho da rikicin shi ba da ba abinda zai sani zuwa,
Murja tace wa ya isa yace wa malam bazamu zo ba cikin su baba,,
Baki ganin ko mama Ladi dole ido tasa mai don ba yadda, zatayi da masifan baba idan ya tashi,
Inko, badon haka ba da, mama ba,zata bari muzo ba, sam,
Meenat ce ta numfasa don jin hiran su tace gaskiya yamma tayi ya kamata ace mun shiga kitchen fa,
Ganin ba su da niyar tashi yasa Meenat shiga kitchen din don dora masu abincin dare,
Ga garin sai lema ruwan sama akeyi wanan ya,nayin ya,sa mutane jin sanyi,,
Tuwon semovita, ta tuka masu da miyar egusi, wanda ya sha, nama da tagani a cikin fridge duk ya kankare,
Sai kusan gaba aikin tane Samira ta shigo kitchen din don taya Meenat din aiki,
Amma kuma sai ta samu ta kusan gamawa don saura kadan,
Don haka ta dan taimaka mata da dan abu kalilan,
Suna kitchen a lokacin da sukaji sallaman yayan su Abubakar,
Meenat wace, sai,mamakin yadda mutum ya iya tukin mota cikin wanan ruwan da ake tsulawa,
Daga kofan kitchen din suka dan hango bayan shi yana shigewa a lokacin bedroom din su hannu shi dauke da yar briefcase, din shi,,,,
Mamaki ne ya kama Meenat ganin irin yadda yayan nasu ya shigo cikin gidan ba tare da nuna wani damuwa akan su bakin shi ba,
Kuma, ma ga Sadiya a falon zaune tana kallon season's film, amma sai ta ga bai tsaya ba,
Mugun hali ta furta a zuciyan ta tare da cewa wanan ai, ba halin sunna bane,
A take uncle din ta na soko, ya fado mata a rai irin yadda yakeyi masu idan yadawo daga gurin aiki,
Amma kuma ai har da laifin ita Sadiyan don dai tun jiya take ganin ta a cikin wanan dogon rigar ai ,
Ita abinda, ta gani tun a gidan su har izuwa gidan uncle din ta shine,
Da zaran yamma ta yi dai dai lokacin da mazaje ke dawo wa gida daga gurin neman kudi, ko aiki,
A lokacin ne zaki ga mace tai wanka ta chaba ado tankar wace zata anguwa ko, gurin wani gagarumin buki,
Shima kuma Uncle idsn zai dawo zai sayo dan tsara ko da bana ci ba ko dangin kayan miya ne,
Da kuma duk wani abu wanda ake yayinsa a lokacin,
Kamar rake, yalo agwalama, lemo kankana, gyada,dafafa, masara gasassa, caras, da,sauran su,,,
Wani lokaci ma ganye zai kwaso masu dafaffa irin su zogala da kuli ganayen rama, dinki, tafasa, da,sauran su dai,,,
Duk da ba wani tsada garesu ba zaki ga mata da yara suna murnan cewa baba ya dawo sai a shiga rabo,
A lokacin kuma za a fara kaeo mai gaisuwa dagida dagu da ana mai sannu da dawowa,
Wani lokaci kuma shi da kan shi yake leka ko, wani daki don jin damuwar iyanlishi idan yadawo daga aikin,
Kusan kuma hakane ai ta gani a gidan iyayyen su duk da gidane na talkawa,
Amma suna kokarin kula da iyalin su sosai kamar yadda sharia, yace,
Wani lokaci kuma malam tsoho shi da kanshi zai saye kwaryan nono da fura akai cikin gida a raba ko wani sashe na gidan,
Amma ga wanan shi ko halin kowa bai kwasa ba shi wani irin mugune haka,
Kwana biyar a gidan ka amma ace ba kasan wanda yazo gurin ka ba ma ba ma balle karramawa,
Tsuki ta sake wanda har ya baiyyana a fili ba tare da ta sani ba,
Sai jin muryan Samira tayi tana fadin may ya faru Meenan su,Baba,,
Ajinyan zuciya ta sauke tare da cewa ke dai bari sister,

*****

2 Comments On TARKO
avatar
maryam-2-4-2

1 year ago

Reply

Ya zanyi in karanta duka

avatar
maryam-2-4-2

1 year ago

Reply

Ya zanyi in karanta duka

Please Login or Register in order to submit comment