Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

🕸🕸TARKO🕸🕸
🕸🕸🕸🕸🕸🕸
1⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI


Da sunan Allah mai,rahama mai jin kyai, duk kan godiya da yabo ya tabbata a gare shi, wanda ya yi mu ya wadata mu da ni,imomin sa,
Wanda ya shari,anta yin addu,a zuwa gare sa, ,kuma yai muna ni,ima da baiwan shi, akan mu roke shi duk bukatocin mu,,
Ubangijin,mu wanda ya ce idan su ka tambaya a gamay da ni,
To ka basu labarin cewa ni din makusancin ne a gare su,
Ina karba adduan mai addu,ar mai, addu,a idan ya roke ni,
Ya Allah tsira da amincin ka su tabbata ga fiyayyen talikai,
Annabi rahama Muhammad S A W, da halaiyen sa da sahabban sa da ma duk wani musulmi wanda yabi tafarkin gaskiya har izuwa ranan Alkiyama,,,,,,,
Ya Allah ina rokon ka da da gode maka da ka bani wanan daman na rubuta wanan dan gajeren labari,
Ya Allah yadda ka nufeni da farawa lafiya Allah ka bani ikon kammalashi lafiya,
Ya Allah dani da na rubuta da wanda duk kabawa ikon karantawa, Allah ka yafe muna kurakuren mu,
Allah ka sada mu da rahamomin ka da ni,imomin ka ,
Ya Allah kasa Aljannan fiddausi tazamo makomar mu,,,,,,,,,

BARKAN MU DA SALLAH YAN UWA,,,,,,

A hankali ya sa hannun shi saman kan shi ya cire farin rawanin dake saye a kan shi,
Farin rawanin da a kasar hausawa sai wani mai, sarauta ko malami ko wani babban mutum ke sawa kan su shi,
Gefen guda daga inda yake zaune saman shimfidar dake a cikin rufan da ke kofar gidan shi,
Rumfar wanda ya a kayi manne da ginar zauren gidan, a ta gefe guda,
Sai shimfidar da akayi wa wani gadon kara dake a cikin rufar,
Shimfidar ya sha kayan laushi irin daddumar nan na da ja,jayen kala,
Daga gefe guda littatafan addini ne kala kala tare a guri guda,
Sai kuma wasu allunan katako, dake tare a guri guda,
Wanan abubuwan zai nuna wa mutum cewa runfar na wani malamin irin kasar hausa ne,
A hankali dan tsohon ya dan jawo jikin shi daga saman shimfidar da yake a zaune,
Gurin da wata butar silver mai ruwan gold yake a je da ruwa ya nufa, a hankali ya fara gabatar da alwala a tsanake, kamar yadda addini ya umur ta,
Bayan ya gama alwal ne ya kara gunda ruwa ga baki yayin da yake mikewa tsaye ya zubar a saman bangon shiga cikin gidan shi
A hankali ya ke dan takawa zuwa kofar fita cikin rumfar tashi,
Jama,a ne a,waje da alamar shi suke jira, daman yafito gaba dayan su , suka mike tsaye,
Bata lokaci aka fara gabatar da sallah azahar na ranan,
Bayan idar da sallah tsohon yadan kai wani lokaci a gurin zaune yana tasbihi,
Duk wanan jimawan da yayi a zaune bai hana mutane zanan jiran fitowar shi ba,
Ya fito fuskan shi dauke da annuri mai kama da murmushi a koda yaushe,
Yara ne daga gefe guda suna ta taruwa da alama karatu zasu yi a gurin,
Saboda irin yadda suke ta tururuwan fitowa daga cikin gidan,
Hakan ya nuna cewa gidan na malam Manya, babba gida ne mai tarin jama,a acikin sa,,

Tarin wanke wanke ne a gefe guda kuda na bin su,
Daidai lokacin da wata mata yar kimanin shekaru, hamsin da tafi daga dakin ta, tana kokarin gyara daurin zanin ta,
Gani kwanonin da ba,a wanke ba har izuwa yanzu yasa matar sake wani irin wawan tsuki, a lokaci guda ,,,
Takalman silifas din ta dake a kofan dakin ta take kokari zurawa kafan ta sai faman mita takeyi, tana cewa ace izuwa yanzu ba,a wanke kwanonin da akaci abinci a cikin sa ba,,,
Amma yau idan na kama wanan Yarinyan sai rayuwar ta ya baci,

Cikin gidan babbane mai sassa guda dai,dai har goma sha, biyar, duk sassan gidan na 'ya'yan malam Manya ne, sai mutum uku ne kawai diyan yan uwan shi da ya karantar kuma yai masu aure suna zaune a tare dashi,
Duk diyan malam suna da aure sai mutum guda wanda shine autan malam wanda ake cewa Isah,
Amma Abdullahi ya bace wada suke kiran shi, da shi saboda acewar mahaifiyar shi tun haihuwar shi da tasamu kudin suna ta, sai dabbobi tana kiwo shine suke ta kawo mata kudi,
Mahaifiyar Audi, itace matar malam na karshe wacce daga ita bai kara wani aure ba,,

Dan malam na farko shine baba Buhari, sai na biyu Sha,ibu, sai Musa, sai Gwago, Laira, gwago Lanto, sai Hamza,, Yahaya, duk diyan mace guda ne,
Ismail, shi da Habiba uwar daya amma ta rasu dadewa, tun gurin wani haihuwa,
Asiya, Rabi, da Audi su kuma diyan mama Rukaiyya ce Amaryam malam, ta yanzu,
Wanan babban gidan na malam manya, yana nan a cikin uguwar da ake kira da Shiyan Sarakuna, dake a cikin garin Birnin Kebbi,
Wanan shiyan kowa yasan cewa shiya ce ta haifaffun gari da kuma baki masu asali, ke zama gurin,
Yanzu haka, zaka samu mazauna unguwar duk kowa yasan kowane gasu da yawan ilimin addini tare da na zamani,
A tsakiyar unguwan zaka samu gidan malam Manya, wanda shi da daukacin iyalin shi suke a ciki,,
Babban diyarn Buhari mariya, sai, Abubakar wanda ya ke bi matan sai mata ne har su biyu, su ke bi mashi, sai daga baya mahaifiyar tasu ta samu maza,biyu da mata biyu,,,
Don haka yaranta sune manya a gidan gaba dayan, saboda, a kusan jere tai ta haihuwan ta,
Ba karamin kokari malam Manya keyi ba gurin ganin cewa hankalin iyalin shi, ya zamo guri guda,
Amma duk da haka akwai, baraka a tsakanin matan wanan babban gidan don sun kashi kashi dakashi a tsakanin su,,,,,
Yanzu haka ita matar malam wace a,ke,cewa maman Audi,
Kansu a hade yake da Amaryan malam watau maman Audi,
Wanda hakan ya samu asaline don kusan a lokacin da malam ya auro ta ita mahaifiyar su Audi,,,,
A tare suke hurda da mama Ladi, wace da ma bata kaunar zama da mahaifiyar mijin ta,
Hakan yasa da malam ya auro maman Audi, sai Ladi ta jata a jiki,
Shiko Ismail da kaunar shi wace da mahaifiyar su bata da rai, a gidan sai aka ware su,
Hakan ya sa Shi Ismail yake da kwazo da neman na kan shi,
A can cikin dangin mahaifiyar su gwandu ya auro matar shi,
Wace take zaman hakkuri a gidan tare da yaran ta,
Sai dai sauran matan yan uwan Buhari sam basu yarda, da wulakancin mama Ladi ba sam, saboda suna ganin cewa bata fisu ba,
Ya sa sam ba su yarda da da wanan cin fuskan da,takewa sauran matan gidan,

Sashin mata daban a makarantan sashin maza da ban
Matan suna zaune kusa da kakan su inda suke daukan karatu,
Malam baya yarda yarinya ta girma batare da ta sauke alkur,ani maigirma ba,
Don duk wace zaiwa aure a gidan dole sai ya kasan ce ta sauke littafi mai tsarki,
Don haka komai kankantar yarinya dole tana zama da zaran lokacin karatu yayi don gudun makara saboda bulalan da malam ke dan shada masu a hannun su idan sunzo a lati,,,
Sauri takeyi don gudun makara don tasan cewa malam yanzu ya fito daga cikin massalaci,
Saboda agogon bango dake sagale dakin mahaifiyar ta ya nuna mata cewa, biyu da minti talatin daidai,
A cikin saurin da ta keyi ne suka hade hanya da mama Ladi wace ta zo sa shen nasu don neman Meenat din
Meena wace ganin mama ladi yasa gaban ta faduwa don tasan cewa ko banza sai kunuwar ta yasha murda gurin mama,
Da sauri Meena ta ja baya daidai inda mama ta kai mata bugu ta gwauce,
Gaba ta sata da masifa inda dole ta aje Alon ta zuwa sashen mama ladin,
Sai da ta wanke kwanonin tas sanan ta, dauki allon ta zuwa kofan gida,
Tun fitowar ta hankalin malam Manya, yake a kan yariyar wace, ke ta dan sharan kwalla, da habar hijabin ta,
Malam,Yasan duk abinda ke gudana agidan
Amma hali irin na manya yasa shi, kawar da kai tankar bai san may ke gudana ba,
Azaton Meena malam zai mata bulala yau sosai saboda irin makaran da tayi, ga kuma sauran yan uwan ta duk sun zuro mata ido suga yaya zasu kwashe ita, da malam,
Sai dai tana zuwa sai malam ya nuna mata, gurin, da zata zauna a hankali ta zauna a tsorace don gudun kada ya fyedo mata bulala daga inda yake zaune a gefen su,
Da guda guda su kai ta zuwa gaban shi suna biya allon su,
Meenat tana isowa agaban malam, maimakon ya fara biya mata sai yace mata cikin tausa murya Amina ki dinga kula daga yau da duk wani aikin da za,a saki, a gida bana son kina makara haka don gudun kar a barki a baya,,,
Kai kawai ta gyada mai don a zaton ta har yanzu zai mata bulala da ta makara,
Amma har aka tashi, bai mata bulalan ba, hakan yasa ta sakin jikin ta,
Ba komai asa Meena take tsoron bulalan malam don ganin irin yadda bai kaunar dukan ta duk cikin su,,,
Hakan yasa Meena ke jin nauyin ace, tana cikin masu makara,
Dawowan ta sashen su, ta yi dakin mahaifiyar ta inda ta samu mahaiyar ta na gyara dakin ta don ganin yamma ya gabato,
Hijabin ta ta cire tana kokarin karban tsintsiyar dake a hannun mahaifiyar ta,
Jeki ki duba kigani idan da, sauran aikin da zakiyi, wa maman ku ki karasa mata, kafin dare yayi,
Cikin sanyi jiki Meena ta bar sashen nasu zuwa,,, gurin ina ladi don ta share mata guri,
Kamar yadda ta saba yi mata akoda yaushe, don dama takamar maman ladi shine taita bautar da yar mutane saboda mugun kiyayyan da takewa Meena din haushin uwar ta take ji,,,,,,,


A yi hakkuri da wanan yan uwa barkan mu da sallah,
Allah yasa wanan novel din ya samu karbu gurin fadakar da ku kamar kullun,
Taku ZAINAB MAKAWA,,,,,,,,,,,,,,,,,,,
🕸🕸TARKO🕸🕸
🕸🕸🕸🕸🕸🕸
2⃣


ZAINAB IDRIS MAKAWA
YAURI

SADAUKARWA
Na, Sadaukar da wanan littafin ga Anty na yayana kuma masoyiyata Antyna Nafisa Harzami tare da duk sauran yan uwan mu maza da mata yan Harzami Family,,,,,,

JINJINA
Jin,jina gare ki MAMAN FARIDA

TUKUICI
Wanan littafin tukuici gareki Anty SAFEENA MAMUD, MAIDUGURI,,,,,

FATAN ALHERI GAREKU DUK KA MASOYANA MASOYA NOVEL DIN ZEE MAKAWA,,,

YA ALLAH Kabani ikon gama wanan littafin lafiya kare ni, da ga rubuta duk wani abin da bai dace aciki ba,,,,



A karkashin babban itaciyar cediyar da ke a tsakan gidan gurin da matan gidan ke taruwa suyi hira, daka da sauran yan aikace, aikacen su,
Yau ma zaune akasarin matan gidan suke a guri itacen
Wasu na yan aiyukan su wasu kuma suna hira ne kawai saboda basu da aikin yi a lokacin,
Mama ladi ce tafi don rakiyar kawar ta aminiyar ta kuma uwar matar da ta zabawa Abubakar din ta,
Kusan matan gidan dake guri alokacin duk sun, wa hajja, sallama,
Sai dai kusan duk idon matan akansu yake tun dai irin yadda suka ga mama ladi na washe baki don ganin Aminiyar nata,
Daga cikin mata ukun dake zaune, suna hira duk suka bisu da kallo a lokacin da suka bada baya,
Matar shaibu ce tace ni dai sam wanan matar bata kwanta min a zuciya na ba, wallahi,
Sai dayar matar da suke a zaune tace ,"ke ki iya bakin ki da wanan zancen,
Guda tace ke ina ruwan ki da zancen da bai shafe ki ba kina zaman ,zamanki ki jawa an kifitina,
Hakan bai sa Maimuna shiru ba har sai da takara cewa
Mata da wani iren fuska babu fara,a, walle, duk sanda nigga wagga mace hankali na tashi shi,kai,,,
Daga haka zancen nasu ya tsaya don ganin mama Ladi da sukayi ta juyo zuwa cikin gida,,,,

Abubakar ne zaune tare da malam a turakar shi suna hira, a washe garin da ya dawo daga karatun shi ,
Dama Abubakar sunan malam ne yaci don haka malam manya ke kiran shi da mai suna,,,
Mai suna inji malam
Yanzu kan Alhamdullahi ko?
Tunda guri ya cika ankamala wagga karatu gashi har ankai ga aiki yau,
Murmushi Abubakar yayi yadan sadan da kan shi kasa cikin girmamawa,
A cikin taushin murya yace wa malam din malam da taimakon Allah da naku ai wanan gurin nawa ya cika,
Nagode ma Allah da yanufe ni yau kana raye malam saboda irin yadda kai min tarbiya da kokari a cikin rayuwana,
Kudi ya ciro masu yawa daga cikin aljihun shi, ya a je su a,gaban malam din,
Ido malam ya dan tsurawa kudin da Abubakar ya aje a gaban shi,
Cikin tambaya yace kudin maye wanan kuma mai suna,
Abubakar yace kudin da akafara bani na albashina ne, shine nace barin kawo ma don asan yadda za,ayi da su,
Shiru malam yayi yana nazarin wani abu a cikin zuciyar shi,
Gyaran murya malam yayi da farko tare da gyara zaman shi kadan,
Mai suna inji malam Abubakar din yadan dago da kan shi kadan yana mai kallon malam,
Wanan kudin ka kasa shi kashi hudu,
Kashi biyu ka kwasa nakane,da sauri ya dago kai ya kalli malam don shi a ganin shi ai kudin sun mai yawa duka don ba wani abu yake saye ba ai,
Malam ya gyada kai yace kwarai kashi biyu kai zaka a je a gurin ka,
Kashi guda kabawa mahaifinka da mahaifiyar ka,
Sauran kashi daya sai a rabawa sauran iyayyenka maza da mata,
Cikin sauri Abubakar yace amma malam sai naga kamar ace na baba Samaila zai fi yawa, don bazan manta da irin halarcin da yai min ba gurin ganin ci gaban karatuna,
Kwarai malam yaji dadin wanan zancen don da alama jikan nashi zai yi jin kai ga yan uwa, da sauran al,umma,
Abubakar bai tashi gurin malam ba har sai da suka cirewa kowa abinda ya dace tundaga ubannen shi har zuwa matan gidan,,,

Zaune take wanan karon a gaban malamin ta tana fada mai irin yadda take son sanar ta ya bunkasa a cikin lokaci guda,
Malamin yai yar murmushi yace ai wanan ba komai bane zan maki kokari inga cewa, duk wanan nahiyar ansan da ke,
Hajja ta gyara zama cikin jin dadin zancen malamin nata,
Sun dauki lokaci malam yana mata bayani tace duk taji zata iya abinda yace, mata,
Ta dawo gidan ta da farin ciki, da jin dadi don tana ganin kamar har komai ya kammala ma ko
Yar ta Sadiya ce a zaune tsakar gida tana karatun novel,
Tai mata,sannu da zuwa tare da kawo wa mahaifiyar ta ruwan sha wanda aka surka da kunu, koko,
Tunda hajja ta kafa kai ga kwanon ruwan bata sauke ba har sai da ta shanye ruwan kwanon dukka,
Hakan yasa yar nata tagane cewa ba karamin kishin ruwa mahaifiyar ta ta kwaso ba,
Don haka abinci ta kara gabatar mata,
Hajja na zaune tana cin abincine Sadiya ta kawo wa hajja wani leda baki da ke dauke da sabulan wanka dana wanki,
Tace wai inji mama Ladi tace akawo maki a fada maki cewa danta Abubakar ne yazo jiya da dare daga inda ya samu aiki,
Cak hajja taja ta tsaya don jin sakon da yar ta ke fada mata,
Cikin sauri tace Abubakar din yazo gidan nan ne ,kai sadiya ta gyada mata alamar a,a baizo ba,
May Ladi take nufi da rashin zuwan dan nata gurinki bayn mun riga da munyi magana akan hakan,,,,,

Wanan zuwan mahaifiyar Abubakar bata bata bari ya koma ba,sai da ta gabatar mai da zancen auren da take son hada shi da yar kawar ta aminiyar ta,
Abubakar baida zabi a rayuwar shi don shi ba mutum bane mai,rigima,
Hakan yasa uwar ta samu sa,an shi saboda ita Sadiya irin matan nan ne da basu da fasali,
Doguwa ce baka mai dan kiba hancinta a baje saman fuska, kanta baida gashi mai yawa aciki,
Itama Sadiya mace irin masu mugun hali wa yan da sam basu kaunar na kusa da su ya rabe su,
Ba wai don wani abuba, a,a halin natane kawai a hakan,
Zaku iya kwana guri guda da ita amma ba za zatai ma mutum magana ba, sai in ta kama dole,
Sai dai dama ita tana mutuwan son Abubakar a rayuwar ta, tun farko,

Sam malam Manya bai so wanan hadin ba amma sanin da yayi cewa yanzu mutum bai zagewa sarakan zamani yasa shi jan bakin shi yai shiru,
So sai ake shirin buki daga bangaren amarya da na ango,
Sai dai rashin samun wadattacen lokaci da ango bai yi ba yasa bukin ya dan rage armashi,
Amma duk da hakan ba laifi, don, yan uwa da abokan arziki sun nuna farin cikkin su da wanan bukin gida ya cika sosai a ranan,
Bayan buki da kwana biyu ango da amarya suka kama hanyar Lagos can inda Abubakar yake, aikin sa yake kuma zaune,,
Sai dai da amarya zata bar gidan ma haifiyan ta uwar nata taba wani ruwa tare da yin hayaki, a cewar ta na neman tsari ne, da samun sa,an daki,
Gidane ma daidaici suke a ciki, acikin rufin asiri da wadata,
Zama sukeyi na,rufawa juna, asiri da mutun tawa a tsakanin su,
Sai dai matsala daya shine Sadiya bata da kuzarin aiki, sam, don haka bata damu da wai dafa abinci ba,,
Zata iya kai wani lokaci tana barcin abinta ba tare da ta dafa ko mai taci ba,,
Gyaran gida kusan weekend take yin shi don ita sam kazanta bai damay taba,
Don a gida neman kudi ne kawai a gaban su shine tun safe za,ai tayi batare da an yi wani girki ko gyaran gida ba ,
Saukin al,amarin babu yan uwan Abubakar da suke ziyaran su a lokacin,
Wanan shine, shimfidar labari da zan bayar,,,,


Mama ladi, ce zaune a tare da aminiyar ta, suna dan tataunawa,
Mama, Ladi ta marairai ce kai tana fadawa aminiyar ta, da muwar ta,
Sai da Hajja ta gama sauraron maganar da Aminiyar ta tazo mata da shi,,,
Hajja ta ce tau,Ladi yanzu yarda da mutum abin tsoro ne,
Da sauri Hajja ta dago kai cikin nuna mamakin da jin abinda Hajja tace,
Cikin mamaki tace Hajja ashe yanzu har akwai wani abinda zaki ji shakkun gaya min a tsakanin mu,
Ba hakana ba,ne Ladi abin ne bai son yawan surutu kuma,siri ne mai girma a tsakani,
Kinga ke nan ba zanso har wani yaji wanan zancen ba gaskiya,
Kara matsowa Ladi tayi kusa da Hajja don ganewan da tayi cewa, maganan da zasu yi, mai, muhin mancine sosai
Hajja tace wa Ladi, ki bari zuwa jibi in,Allah ya kai mu akwai inda zan kai ki,
Da murna ladi tabar gidan don farin cikin ta kusa samun mafita,
Buhari yana a majalissan malam mahaifin shi ya hango, dawowan maidakin nashi acikin zafin rana,
Cikin rayuwan shi yake masifa da ita yana fadan rashin zaman gida irin na Ladi,
Amma tana iso gurin da suke sai cewa tayi a gaishe ku,
Yan kadan ne suka karba mata, da ingwaiyya Ladi ke dawo,?
Ta ansa da fadar Awo, Allah ya maisan da ni lafiya,
Daga haka ta,shigewan ta ciki, inda malam da dan shi buhari, takaicin ya hana,su cewa kala,

Acikin gida ma, haka mata suka dinga gaida Ladi da dawo,
Idan sunce mata Aho, yaya,
Ita ko sai cewa takeyi ingwaiyya, agaishe ku, dai,,,
Tas, ta samu shiyan ta don Meena ta gyara mata shi tas,,
Amma halin

2 Comments On TARKO
avatar
maryam-2-4-2

1 year ago

Reply

Ya zanyi in karanta duka

avatar
maryam-2-4-2

1 year ago

Reply

Ya zanyi in karanta duka

Please Login or Register in order to submit comment