Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma aiwatar, don haka zance ya saura gare ki,
Dakike cewa haka ita Meenatu ba matar shi bace,
Wazo daurin auren ba mahaifin ta ba, ni wallahi irin rayuwan nan naki na jahilci shiyasa bazan taba shiri da ke ba,
Dariya sauran mutanen gurin suka sa masu don sanin cewa sun saba wanan badakalar a tsakanin su dama,
Su Baba basu tsatsaya ba washegari suka juyo zuwa Kebbi, abin su
Baba Wadda yaso ya biyo su, su dawo amma yaya Abubakar, yace yadan dakata su dawo tare dasu Mama Ladi,
Badon yaso ba yana gani suka juyo abin su zuwa gida,

****** ********* ******
Γ€nty Amarya ce bayan nadawo school take sheda min cewa har andaura auren yaya Abubakar da Salawatu,
Duk labarin bai min dadi ba amma sai kawai na dake a zuciya na,
A fili cewa nayi tau, Allah bada zaman lafiya, yasa ace gwanma da akayi,
Wanka na shiga tare da dauro alwalan Sallah la,asar,
Nakai wani lokaci zaune a gurin tun ina addu,a har na koma tunane,
Irin halin rayuwan da zan yi cikin manyan mata yar karama dani,
Yanzu duk irin zumudin da idan muna tare da yaya Abubakar yake nuna min ashe halin mazane,
Shiko dai don an bashi ni ne yasa zai min haka ?
Aure da wata hudu yace zai auro wata baya na, may narage shi dashi kamar yadda ake ta min nasiha akai,
Wasu irin hawayen bakin ciki da takaici ne naji sun silalo daga cikin idona zuwa kumatuna, duk sun wanke min fuska,
Waya na dake saman mirror dakin mu tana chaji naji tana kukan neman agaji,
Hannu na mika a hankali na dauko wayan sunan, yaya Abubakar ne na gani jikin wayan,
Ina kallon wayan har tagama ringing din ta tagaji ta katse don kanta, ban dauka ba,
Kira uku ban daga ba har ya gaji naji ya daina kiran nawa,
Daga karshs ma sai na kashe wayan gaba daya ta yadda ko ankira baza,a samay ni ba,
Mikewa nayi na fara shirin kwanciya duk da dai nasan cewa ba barcin zanyi ba amma sai nake ga kwancin yafi min a lokacin,,,
Anty Amarya ce ta shigo dakin tun daga kofa ta hangoni a kwance fuskana yana kallon rufin dakin,
Muryan Anty naji tana cewa, Meenatu badai damuwa kikasa a ranki ba haka ko ?
Murmushi na kirkiro a fuskana na dole, badon naso yin sa ba,
Gefena tasamu tazauna tana ce min, Meenatu ban son kisa damuwa ga al,amarin mazan zamani,
Duk namiji idan yana son aure, baijin has azamanin nan da muke a ciki,
Sai fa idan sunyi sun ji abinda ke nan, sanan hankali su ya kwanta su fara neman hanyar ceto,
Don haka tunda kikaga har iyayyen ku basu iya hana shi wanan auren ba ki sa masa ido, kawai kamar yadda na fada maki da farko,
Ke dai kawai ki rike mutuncin ki da kuma ibada kina kai kukan ki ga Allah,
Saboda haka idan ya kira ki dauka kar ki kara share ahi don Allah ,
Kyale shi ai shima yasan bai yi daidai ba tunda bai sanar da ke ba akai,
Ido na dago ina kallon ta yadda har tasan cewa ban dauki wayar shi ba,
Anty Amarya tace, yanzu ya bugo waya yana tambarya Uncle din ki ke wai ya kira baki daga waya ba,
Shine nake ce masu kin kewaya ne shi yasa isan kin fito zan fada maki cewa ya bugo,

****** ********* ******
Yaya Abubakar da yaga cewa yai kira uku ban dauki wayan ba yasa shi dan yi murmshi don yasan cewa yayi laifi, sosai, tunda har ba,a daga mashi wayan shi, ba yau,,
Don haka sai ya kira nomban Uncle dina don su gaisai kuma ya tambaya ko ina lafiya,
A lokacin Anty Amarya tana kusa da Uncle dina shinw take fada masu cewa, ai ina bandaki ne a lokacin,
Sai yake cewa Uncle ayi hakkuri fa auren ne nasa yazo mashi ba shiri,
Sundan taba hira da Uncle dina sanan sukayi sallama ya kashe wayan,
Shiru yadan yi tare da lumshe idon shi don yasan cewa kawai an dai kareni ne kawai,
Amma ina cikin fushi ne kawai irin na mata, murmushi ya dan yi kawai don yasan cewa sai kana son mutum kake kishin sa,
Wayan Salawatu ne daya shigo a lokacin ya katse shi ,,
Acikin wani irin muryan shagwaba take mai magana yau,
Sundauki lokaci mai tsawo suna hiran irin ta masoya,

Washegari koda ya shiga office mutane sai murna suke mashi cewa Ango Ango,
Shiko sai murmushi ya keyi baki yaki rufuwa sai nagode yake cewa jama,a kawai,
Yau, Salawatu shigan zani da riga tayi na atamfa, zuwa office din nasu,
Sai wani gyale mai shara,shara da ta yafa akanta har zuwa rabin kirjin ta,
Ita a ganin ta ,tarufe jikin ta ke nan,a hakan ta yi shigan matan aure,
Sai da tafara zuwa office din su suka gaisa da mutane suna ta mata, murna da fatan alheri,
Sai, nagode nagode take cewa da kuma Allahuma Ameen,
Acikin wani irin jin dadi ta isa office din maigidan nata,
Yana zaune aiki yai mai yawa yana kokarin tura sakonni,
Yaji an turo kofan shiga office din shi yadan dago don yaga kowaye yashigo mai batare da malam Abdullahi ya sheda mai shigowan mai shi ba,,
Salawa ce su kayi arba dashi tun daga kofan office din,
Wani irin dam yaji gaban shi ya yabada tankar ya fadi,
Sai yaga yau Salawa ta kara mai wani irin kyau da kwarji a fuskan shi,
Murmushi mai laushi mai sace zuciyan masoya suka sakewa junan su a lokaci guda,
Wanda su kadai,su ka san irin yanayin da suka shiga alokacin,
Da tafiyan jan hankalin maza ta karasa gaban table, din nashi,
Tana zuwa ta zube gwiwa bibibyu a,kasa gaban shi tana cewa barka da safiya maigida,
Cikin wani irin lumshe idon jin dadi ya amsa mata,,
Tare da mikewa tsaye yadan rugumota zuwa jikin shi yana mai wani irin sauke zuciya,
Cikin wani irin murya da sai ka saurara zakiji tace be my husband forever, dear ?
A hankali shima ya rada mata da cewa i,will insha Allah,
Suka kara rungumay juna cikin shauki da kaunar junar su,,
A hankali yaya Abubakar yafara zare cikin shi daga gare ta yana mai ce mata, yana sa aiki da yawa amna idan ya gama zai mata waya su fita,


ZEE MAKAWA YELWA,,
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈTARKOπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
4⃣6⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH-AL-GHAFOOR

FATAN, ALHERI GAREKU KO DA YAUSHE MASOYA NOVEL DIN TARKO,
BAZAN IYA LISSAFA SUNAYEN KU BA ANAN INA DAI MAKU FATAN ALHERI DA GAMAWA DA DUNIYA LAFIYA,
ALLAH YASA MU DACE DA RAHAMAR SA ALLAHUMA AMEENπŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘



Daga inda take kwance saman makeken gadon hotel din take kallon bayan shi,
Cikin wani irin so da kauna da ke fisgan ta, alokacin
Don zata iya cewa bata taba karo da namiji jan gwarzo irin Abubakar ba,
Daga bathroom yake yafito wanka, yana ko,karin shirya jikin shi, cikin tufafin shi da ya watsar saman kujeran dake dakin,
Sai a lokacin Salawatu ta dan zabura ta mike don ta fahinci cewa tafiya zai yi,
A daidai lokacin da yake zura wandon shi ajikin shi yaji muryan ta tana cewa,
Zaka tafi ne ?
Batare da ya juyo inda take ba ya bata ansa da cewa,
Eh a takai ce,
Cikin wani irin kashe murya take ce mai tun yanzu dear,?
Bai iya bata ansa ba sai da ya suri corth, din shi yana kokarin sawa,
A lokacin Salawa har takai, tsaye tana kokarin daura, towel a jikin ta,
Inda take ya juya ya nufa sai da ya mika hannu ya dauki keys din shi sanan ya dan riko ta yana cewa,
Zai je gida kada hankalin Mama ya tashi saboda bai Sanar da su inda yake ba,
Amma zai turo Bado driver ya dauke ta ya mayar da ita,
Cikin kashe murya, tace dear I think we, are going to spend our night here?
Murmushi mai kama da yake ya sake mata tare da kara gyara bottom din rigar shi,
Yace bana son family di and my Mama su, shiga damuwa saboda ban sanar da kowa gurin da nake ba, See you next,
Daga haka ya sa kai zuwa fita daga dakin batare da ya kara furta wani abu ba,
Yana fita ta koma saman gado tana sauke numfashi sama sama,
Don yau gaskiya ta samu abinda ta dade tana muradin samu a rayuwan ta,
Yanzu abinda ya rage shine yadda zata mallake shi gaba daya yazama na ita kadai,
Don yanzu bata jin zata iya sharing din Abubakar da kowa wace mace a duniyan nan,
Burin ta shine ta mallake shi ita ka dai bada kowa ba,,
Murmushin mugunta takara yi don gaba dayan su, sai tai waje road da su,

****** ********* ******
Tafe yake a motar shi, shi kadai sai faman tsuki, yake yi,
Sai dai ya rasa dalilin yin tsukin da ya ke tayi har yanzu, don bazai ce ga dalili ba,
Hamza ne ya bude mashi get, tare da yi mashi sannu da zuwa,
A tare suka shiga gidan da Hamza wanda zuwa yanzu ya zama dan gida sosai yana yawan shiga gidan,
A falo Mama su ke zaune ita da anty mariya,suna kallon TV da ke aiki,
Yana shiga mama ta mike tsaye tana cewa mai sunan malam ina kashiga haka yau, tun safe,
Ba waya ba, kuma aike balle mu san abinda, kake ciki,
Murmushi yayi yana cewa, mama, ai ba abinda zai samay ni insha Allah,
Kawai dai ai,yukane sukai min yawa yau na dan tsaya ti office,
Tambayar mama yayi da cewa mama kunci abinci ko ?
Ta tabe baki ta ce an kawo muna gidan wa yan nan bayin Allah masu bamu,
Amma ai mariya ta fara dan koyon yadda ake girki da na ku kayan girkin,
Ita Sadiya fa ba ta girka ba ,
Mama za tai magana ke nan sai ga, Sadiya tafito daga dakin tai kicin, kicin da fuskanta,
Wanda tun zancen daurin auren Salawatu da shi Abubakar suke cikin matsala,
Inda Sadiya ke fadin cewa bata taba sanin cewa wai Salawatu ce yake nufi zai aura ba,
Tace wanan yar barikin zai kwaso masu gida, ya halakasu, baki daya har shi,
Ashe dama zaman banza sukeyi da ita shiyasa komai nashi take shigewa gaba,gaba,
Ita ta zaci cewa zaman mutunci su keyi na suna office guda da juna,,,
Wanan maganan yaba Abubakar haushi sosai yace cikin kunan rai may kike nufi da muna tare, ashe,?
Ni ban taba zina ba don ki sani don dani mazinaci ne da kece zaki fara sakani yin zina,
Amma sai na godewa Allah bai yoni mai saba mashi ta wanan hanyan ba,
Fitowan ta daga Sashen ta taji yana tambayan Mama ita,,
Wani irin mugun kallo ta watso ma Mama tare da cewa, dama nasan anzone kawai don aga iyakar mutum,
Wani irin bacin rai yaya Abubakar yaji baisan lokacin da yayo kan taba a fussace,
Mama Ladi ce cikin karfin hali tace mashi kada ka fara ka taba ta kyale ta kawai,
A cikin kunan zuciya ya haye sama yana jin bacin ran shi na dada karuwa mashi,
Yana shigewa Sadiya tace ai kun kai ga yadda kuke so akai,
Amma ce kunzo kun zubewa mutane agida duk kun hana mutum shakat, banda daman in hutu ace yi wanan a yi wancan,
Ni gaskiya bazan iya ba don ba yar aikin kowa nake ba,
Cikin mamaki Anty Mariya da Mama Ladi ke kallon ikon Allah,
Don dazun da Anty Mariya ta shiga kitchen ta dauko, madaran peak zata hadawa Mama tea tace tana son sha,
Sadiya tana fitowa sai cewa tayi kada Anty Mariya ta kara daukan wani abu batare da ta fada mata ba,
Kuma ma ai wanan don ta aka siyo ba don su ba don ai da su kazo ba taga ya siyo wani ba da sunan su,,
Dole suka koma zaman taka, tsantsan, a gidan suna gudun yin dogon motsi suyi laifi,

****** ********* ******
Zaune su ke saman wasu manyan kushin din kujeru, masu siffan kunkuru a falon,
Yar tsohuwan tayi dani in zauna a saman daya daga cikin kujerun da ke falon kamar yadda suke zaune ita da yar ta amma na ki zama,
Ina kasa zaune gefen kafan ta ga goran fura mai sanyi an aje muna agaban kowan mu, har ita yar dattijiwan,
Sai da ta kurba furan daga gora ba tare da ta tsiyaya a cup ba tace,
Meenatu hakkuri zakiyi kin ji, Aure bautan ubangiji ne,
Don haka abarwa Allah, al,amarin sa kawai, don ko kin tayar da hankalinki indai namiji ne baya jin has, a lokacin sai fa yayi binda yai niyar yi,
Balle nasan cewa ke bawai wani laifi kikai mashi ba har ya kai shi ga yin wanan auren ba,
Illa kawai sun dade da ita yarinyar ne wata, kila zancen ta yana gaban na ki,
Shiyasa yai haka don ya burge ta ko ya wanke laifinsa gare ta,
Musan man ke Meenatu da ku ke yan uwa dashi,
Dan ke fa yar uwar shi ce, bazai damu da cewa sai yayi ta rarashinki ba don dole dai ki zauna dashi,
Kinga idan baki kwantar da hankalinki ba, tabbas rayuwanki zata shiga cikin tashin hankali da matsaloli mara misali,
Don dole kuma kiyi hakkuri duk yadda ta kasance, da ke,
Kibar komai ga Allah kirike ibadun ki ki taimaka mashi wurin taimakon yan uwan ku mabukata, dama wanda ba yan uwan ku ba,
Haka zai kara maki haske sosai gareshi dama kowa na,ku
Anty Amarya dake gefe zaune tana wasa da wayan ta zuciyan ta tana mai,jin haushin abinda mijin Meenatun yai masu, tace wa mahaifiyar ta
Ni Mama hajiya, yanzu abin,da nake so shina Meenatu ta fahinci yadda zama cikin irin wayan nan manyan matan ya ke,
Haka hajiya Mama ta fara min nasiha cike da kissa da kuma wayarwa akan zaman aure,
A karshe take ce min dole ne in fara kwantar da kaina in fahinci halin kowacen su,
Daga baya sai in koma nima karuwan dakin mijina sai sun girgiza, dankan su,
Ina zaune cikin ladabi, ina sauren hajiya Mama take ce min
Kar ki yarda ace girkin ki ya zo batare da kin wa mijin ki wani tana di ba daga jikin ki,
Wanda hakan ne kawai zakiyi mashi ki kwato incenki ga kowan su,
Duk da na san cewa, suma din ba bayaba gurin gyara irin nasu,
Duk abinda zakiyi kada ki yawaita cushe cushe a jikin ki ya na ragewa mace daraja ga mijin ta idan har ya gane, hakan,
Dan zai zaci cewa kina masa wani asirine don ki mallake shi,
Akwai hanyoyi daban daban da zaki bi wanda zai kawo maki dau,ka ka, a,waje maigida ki koma, tankar yar leda,,
A take ta dinga jero min irin dabarun su na mutanen baya wanda bai kawo wa mace illa, ajikin ta,
Sai wanda zaki dinga hadawa da kan ki a gida ki,na sha, ga bakin ki a koda yaushe, ,
Anty Amarya ta dinga rubutawa inda taba hajiya mama kudi a sawo min goran zuma na ainifi kauye don inje dashi,
Sai kudin da za,a siyo min sauran abubuwan bukata da hajiya mama zata tura kauye,

Wanan zancen da hajiya mama, tai min yasa na dan rage jin zafin da nake ji araina,,
Ba muje gida ba sai da anty ta kaimu shagon Gazali mai kayan mata a cikin kasuwa, ta sayo min yan kasan Indonesia masu kyau da tsada,
Muna tafe Anty na jan mu a mota hanyan komawa gida,
Ta ce min Meenatu na ansa a hankali da cewa Na,am Anty,,
Tace kin,ga duk abubuwan nan da mama tafada maki to walle idan ki ka tsare yin su to ke more auren ki,
Don ke gan,ni nan badon Allah ya ban uwa mai tawakkali da kuma hikima irin Mama ba,
Da ina ganin gidan Uncle dinki nika shi don iyayin su, Samira ba kadan naba,
Kin san dai kowa yasan yan gidan doctor, ka,oje nan garin, ko?
Amma dole sun ka bar ni dakina tama,
Amma fa haka bai samuwa kamar yadda mama ta fada makine,
Addini sadaka alheri kyautatawa duk su shige maki gaba, kuma tsakani da Allah zakiyi badon ganin ido ba,,,, ,
Ki tai kiyi hakkuri keji,,insha Allahu babu abinda ka samuwan ki, sai alheri,
Hawaye masu zafi ne suka tsiyayo daga idona a lokaci guda na ke furta kalman nagode Anty,
Tace kai haba Meenatu mizaki godemawa tun da duk yiwa kai na,
Allah dai yasa mu dace kawai,
Na ansa da cewa Ameen a hankali ba wai lalai anty taji ba,

****** ********* ******
Tun bayan shigan shi dakin shi duk zuciyar shi tana mashi wani irin zafi da su ya,
Wanka ya karayi ko zai dan samu relief a ran shi irin yadda yake ji,
Zaune yake a bakin gadon shi inda ya dafe kai da tafin hannayen shi,
Yabaro gurin salawatu da bacin rai ga kuma sadiya ta kara mashi wani,
Numfasawa yayi irin na an,gufu ba,a tsiraba ke nan,
May zaice da wanan damuwar ta shi ne wai karfa ace anazaton, wuta a makera sai gata a masaka,
Da sauri yace kai hakan ba zai yuyu ba ai dama kowa yasai rariya yasan zatayi yoyo ai,
Wanan sai in yaso mamaki acikin don mace kamar salawtu, dama ai,dole haka zai samu gare ta,
Point din farko kenan da ya fara karo dashi daga gare ta,, yafurta a hankali SALAWATU,,
Amma ita kuma Sadiya yasan mai gyarata sai Allah amma idan har zama yai zama ai dole ta canza wasu halaiyya nata,
Amma kuma ai rashin mutuncin ta yai yawa har da mahaifiyar shi, za,taiwa rashin mutumci,
Matar da tai Sanadin auren shi da ita,
Matar,da, bata taba yarda wani ya aiban ta Sadiya a kusa da ita ko kadan,
Duk da mama tai mashi fada akan kada yace mata komai,
Gaskiya baiji cewa zai iya kyaleta taciwa mahaifiyar shi mutunci a,gaban shi,ba,
Don haka ya aiyyana a rayuwan shi zata gane kuren ta sosai,
Haka ya zauna daki batare da yafito gurin su mama sun dan,yi hiraba kamar yadda ya saba yi dasu duk dare,
Kwance ya,kai ta baya cikin yanayin damu daga saman gadon da yake zaune,
Idon shi ya dan ritse kamar gizo yaga Meenatu, cikin irin yanayin ta na alkunya kamar kullun tana dan murmushin nan nata kasa, kasa,
Fitgigit ya bude ido yana tuna cewa rabon da yakira Meenatu fa yau kwana biyu ke nan,
Dama ita ba gwana bacs gurin kiran shi, indai ba zuwan Mama ba da takan dan kira taji ya jikin Mama
Wayan shi ya jawo tare da saurin neman nomban ta,
Har kiran ya katse kamar ranan ba a dauka ba daga bangare na,
Wayan na daga gefe na tana ruri koda ban duba ba nasan cewa shine awanan lokacin
Don tunda rana munyi waya da iyayyena mun gaisa ko kamar kullun don neman albarkan nan da suke sa min idan munyi waya dasu,
Wani sabon kira ne yashigo again daga gare shi, inna kallon wayan naki daga,
Anty Amarya ce ta shigo dakin gab da wayan ya katse sai ta girgiza min kai alaman in dauka,
Bamusu sai dai raina baiso daukan wayan ba a lokacin,
Ina jin ya sauke ajiyan zuciya daga cikin wayan tankar a fili yake gaba na,,
Cikin wata irin murya da ban san ina da ita ba nake cewa
Assalamu Alaikum, Assalamu Alaikum Assalamu Alaikum,
Ni kadai sai nake cewa ayya ba network sai na kashe daga ban,gare na,
Kafin in kashe a lokacin da nake tacewa ba network wani irin murmushin kasaita naji yayi,
Nasan cewa yan san ina jin shi bandai da niyar daukan wayan ne kawai,
Murmushi sosai yaya Abubakar ya yi don ya fahinci ban dai son daukan wayan nashi ne, kawai,
Don ya nuna min ya fini wayo da dubara sai ya kira ni ta layin Uncle dina,
Da gudu karamin yaron mummy Ansar, ya kawo min wayanyan yaron na ta haki don gudun da ya yi,
Da sallama again na karba wayan nashi inda yake tambaya na da cewa
Yanzun dai kina jina ko ?
Naam sa mai da eh, ina ji,
Gaishe shi nafara yi sai kuma nai shiru,

Sorry pls kuyi hakkuri da wanan banda da caji wlh,


ZEEE MAKAWA YELWA
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈTARKOπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
4⃣7⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH - ASH - SHAKOOR


Ya Allah muna rokon ka ka kawo muna karshen yin rawan yayan musulmai a cikin film din hausa
πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘
Cikin wani irin murya mai tada hankalin maisauraron ta mai juya wa mutum lissafin tunanen sa, na ji ya ce,
MEENATU,,
May yayan ki yai maki bakya daukan wayan shi ne, ?
Nace acikin siririyar murya na bakin dankan wayan nayi ba, network ne bakyau,
Hmmmm na ji ya ce tare da numfasawa a hankali,
Ya karatu ya mutanen gida,?
Na amsa mashi da duk lafiya kalau Alhamdullahi,
Daga inda yake kwance ya dago idon shi da suka kada sukayi jajir, yana kallon rufin darkin nashi,
Yarasa may zai cewa yarinyan don haka jin yai shiru ne nace mai,
Sai anjima tare da saurin kashe wayan batare da na tsaya sauraren may zai fada min ba,
Tashi nayi na shirya a cikin wata yar farar rigar barci na,
Ina kokarin daure dogon gashina da ribon ne Anty Amarya ta bude labulen kofan namu, tana cewa,
Meenatu badai har zaki kwanta ba yanzu ?
Nadago kai na a hankali na kalli inda Anty take tsaye nace, Eh ina son tashi da safe da wuri idan ran mu ya kai,
Anty Amarya tace Meenatu bakyaji ko sai da nace ki dauki wayan bawan Allah nan idan ya bugo amma sai ki kaki,
Gashi har uncle din ki ya fara suspecting din ko kin sawa kanko kishi ne,
Da sauri nadan dago kaina ina kallon ta don jin abin da tace uncle yace a kai na,
Jikina ne yai sanyi a lokacin nace cikin wata irin murya tankar zanyi kuka,
Anty ni ba fushi nakeyi da shi ba, kawai dai, ban jin dadi ne,
Hmmm naji tace taci gaba da cewa gaskiya meenatu, baki kyauta ba

2 Comments On TARKO
avatar
maryam-2-4-2

1 year ago

Reply

Ya zanyi in karanta duka

avatar
maryam-2-4-2

1 year ago

Reply

Ya zanyi in karanta duka

Please Login or Register in order to submit comment