Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

za,a ce a tsallaka aje har sashen Baba samaila,
Baba Buhari zai yi magana malam yace a,a ya bar,ta ta ba da yaro guda daga fan,ninta,,
Ba kunya ba tsoro mama Ladi ta shirya Samira tace a tafi da ita,,,

Jama,an gidan malam manya da yaran, su, su,ka taru kofan gidan malam don yiwa mutanen Lagos rakiya,
Abubakar ya na zaune kafa tankwashe, saman tabarma a gefen malam.
Inda malam din ke kara ja mai kune akan al,amarin duniya,,
Ita kuma Sadiya tana tsaye jingine a gaban mota tana wani yatsunar fuska,
Su,ko mutanen gidan sun daga gefe sai kallonta, su keyi suna yatsunar fuska su ma,
Wasu kuma daga cikin su haushin yadda take masu kallon bazan suke ji,
A can kuma gefe Samira ce da yara yan uwan ta suna ta yi mata suraita irin na ke kan Samira kinji dandin ki za,a dake har Lagos,,,
Ita ko samira sai washe baki takeyi don jin dadi za tai wa yan uwan ta tazara,,

Tun fara hanyar su Samira ta fara rena kan ta don
Tambayar ta Abubakar ya fara yi da cewa, wani makaranta kike zuwa,
Cikin dan nuna tsoro da kuma nauyi Samira tace, salamatu Husaini,government girls secondary school,
A jinki nawa a can ?tace, aji uku zan je hudu,
Sai kuma yai shiru ya ci gaba da tukin da ya,keyi,
Da har Samira na murnan tamabayar ya kare,
Sai taji an jefo mata wani tambaya again,
Shekarun ki nawa yanzu, ?
Cikin rawan murya tace mama tace wai goma sha, hudu nake yanzu,
Suka yi ido biyu dashi tai saurin dukar da kai da sauri don tsoron fuskan shi take ji,,
Izunki nawa yanzu,?
Goma sha, takwass,,,
Bata karasa fadi ba taji ya ce takkwala kawai,
May kike jira har, yanzu baki sauka ba ?
Haba ai tai kokari inji Sadiya wace, ke tauna chewingun,
Common shut, up my friend ke nawa kike balle har ki sa min baki,
Cikin sauri tai wani cewa Allah ya baka hakkuri ni dai,
Allamun tsoro su ka kara baiyyana a fuskan samira wace tai da ta sani bata biyo yayan nata ba,
Tun yanzu wanan tambayar haka kamar dan jarida
Can kuma ya kara tambayar ta yaran baba wani nawa ne sai ta fada mai,
Ita kuma gwago wance fa diyan ta nawa yanzu, shima sai ta fada mai,
Har dai zuwa lokacin da tafiya yai nisa duk kan su su,kayi shiru don gajiya,

A cikin dare suka isa garin Lagos wanda yawan cunkoson shi, Samira ba zata iya gane komai ba, a cikin ida suka dosa,,,
A kofar wani gida mai hawa kusan uku suka tsaya,
Gaskiya gidan ba laifi don ba yabo ba fallasa a cikin shi,
Gaba dayan su har yayan nata suka fara kwasan kayan su zuwa cikin gidan, sashen da taga Abubakar ya sa dan makulli ya bude kofan,
A hawa na biyu suke da zama su, don haka ba suyi wani shan wahalan hawa ba,
A tsakiyan falon gidan sukai ta jibge kayan da sukayo tsaraba da ga gida da kuma nasu na sawan su,
Duk da dai shi Abubakar ya ce wa mahaifiyar shi basai Samira tazo da kaya masu yawa ba, acan,
Amma duk da haka tadan zo da yan gwargwado daga abinda take so,
Wani daki yayan nata ya nuna mata ya ce ta kwashi kayan ta zuwa ciki a nan zata zauna,,,
Dakin yana dauke da dan gado guda daya sai mirrow, a gefe,
Samira na kallo Sadiya ta dauki dan trolley din ta ta nufi dakin kwanan su,
Inda tabar sauran kayan nan gurin da aka zube su da farko,,,
Baki bude Samira ke kallon yadda yayanta ke ta faman kwasan su zuwa ciki inda ya kamata ya kai komai,
Ita ko Sadiya tun shigewar ta dakin bata kara fitowa waje ba,
Take away din da ya saya masu tun a hanya shine ya bawa Samira, guda daga ciki tare da nuna mata kitchen din su,
Shigan samira kitchen din sai da gaban ta ya fadi don shirgin da ta gani kamar ba,a ciki ake girki ba,,,,

Zaune suke a saman tabarman roba wanda aka shimfida a rufar dake tsakiyan filin sashen nasu,,,
Kasan cewa yau Jumma,a , ne duk kan su sunyi kwaliya, fes da su,,
Ga kuma shiyan nasu fes da shi kamar babu yara aciki har biyar,
Sallaya ne a hannun mama Sadiya tana kokarin nikewa da ga gurin da tai sallah,
A daidai lokacin Baba Samaila ya shigo gida da yaran shi su uku, maza, da ke, biye da shi a baya acikin shigar su ta sallah Jumma,a,ga kuma shiga na fararen shadda sun yi don, Jumma,a,,,,
Da sallamar su suka karaso cikin gidan, sannu da zuwa mama ke ma su inda su Meenat da ke daga ciki suka gane cewa mahainfin su ya dawo,
Nan su ka yo, waje gaba dayan su suna masu barka da Jumma,a
Bayan sun zauna a saman katon tabarman dake shimfede mama ta gabatar masu da abincin rana,
Kowa anzuba mai a nashi, plate, tare da abokin cin shi,
Tuwo ne na far shinkafa da miyar taushe, anzuba wa miyar kabewa bussashe, da kuma kulikuli,
Sai manshanu da aka lema a saman miyan kamshin shi yana tashi sama,
Mamace ta fara gane cewa yau Baba bai cikin farin rai,
Da alamar zuciyar shi ba ta da dadi sam don tun safe haka take gani tare da shi,,,
Loman da ya diba zai kai abakin shi ya tsaya a lokacin da ya ji muryan mama tana cewa,
Ai da ka daure ka ci abinci ko bakajin dadin shi,
A hankali Baba ya dago kai ya dube ta cikin dan sakin fuska mara walwala,
Fuskan matar nashi ya tsurawa ido don ganin cewa, ta fahinci halin da yake ciki,
Inda yaran su, suke zaune yadan kai kallon shi, gare su,
Hakan yasa mama gane cewa bai son yin magana a,gaban su a lokacin,,
Don haka sai mama tai shiru taci gaba da zubawa yaran maza miyan da suka shan ye,
Amma azuciyan Baba sai ya kasa daurewa don yasan cewa matar ta shi don, ta damu da damuwar shi,
Baba yai dan murmushi tare da yanko lomar tuwon ya ce,
Saratu ke nan ai dole ki ganni haka don al,amarin kiyayyan da Ladi ke gwada min yai yawa,
A lokacin ne ya jaye kulan abincin daga gaban shi ya jawo roban ruwan wanke hannu a,gaban shi,,
Mama tace ko ma may take nufi ai Allah ya fita Baban Meenat,
Na san da haka saratu to amma abin ne da daure kai don dai ni da da farko abin bai damu na sam,
Amma yanzu wanan abun da tai muna yasa na fara jin tsoron ta akan yaran nan,
Caraf Aliyu yaron su na uku ya sa masu baki azancen su da cewa,
Wai ce muna takeyi irin fulani irin tsiya,,,,
Murmushi Baba yayi a lokacin da Aliyu ya fadi haka nan,
Baba ya ce kada wanda yadamu da duk wani abin da Ladi zatai maku,
Nasiha Baba yaiwa ran sosai don irin yadda zasu zauna da mutane lafiya,,
Jin Meenat tai shiru a lokacin kamar bata a gurin yasa mama dan juyawa gurin da take zaune,
Ke lafiya kike kuwa kin yi shiru haka, kuma ko abincin ba,kya ci,,
Ba komai mama Meenat tace cikin muryan tausayi,
Muryan Baba ne ke cewa, Amina ina gani karama da ke kina aon sawa kan ki maganar manya ko ?
Murmushi Meenat har dan sautin ya fita sanan tace,
Baba ai ni nasaba da halin mama ba yau ba duk wani abinda zatayi nasan dashi ko ,
Takai hannun ta cikin plate din abincin dake gabanta tare da lumshe idon ta don takaicin irin yadda duk fadin gidan su ,su kawai mama tafi sawa a gaba,
Baba samaila yadan girgiza kai, acikin zuciyar shi yana tausayawa yarinyar nashi,
Ta,na da hakkuri da kuma, tausayin iyayyen ta dayan uwan ta,,,
Ga shi duk wani wahakan da mama Ladi zata sata ba ta taba nuna bacin ranta akai,
Baba Samaila ya Amina kwanan nan zan mai da karatunki Sakkwato, insha Allah,
Ki koma can kiyi makarantar kwana ina ga hakan zaifi ko,?
Murmushin jin dadi Meenat tayi don ta dade tana sha,awan makarantar kwana,,,
Amma sai mama saratu tace malam makarantar kwana fa kace, ?
Baba ya ce kwarai kuwa don hakan shine shirina ba yau ba don samun mafita,
Meenat cikin sanyi murya ta dan dago kai ta kali Baba tace,
Baba, malam tsoho ko zai yarda ?
Zan san yadda zan bullo mai insha Allah,,,
Hakan yasa Meena dan sake ajiyar zuciya a hankali,,,,,

Washegari da isan mutanen Lagos Samira tana kwance tana jiran abin kayarwa,
Jin shiru yai yawa yasa ta dan fitowa waje, don taga ko angama yana kitchen ne nata ,
Kamar yadda tabar kitchen din da dare haka ta samay shi ko yau da safe,
Samira tana son shiga kitchen din don dafa abu amma bata san ya zatai amfani da irin gas din su ba,,
Don haka tadawo falon ta zauna inda take bin kayan falon da kallo cikin mamaki, yadda kayan suke a jibge babu kulawa kamar ba mace agidan, ma sam,
Da hannayen ta bibiyu tai tagumi tana tunanen sabuwar rayuwan da ta wayi gari dashi,
Ita da a gida take da, yanzu ta na batun karyawa na biyune ko na uku,,
Shigowan matar gidan falon alokacin yasa Samira saurin dago kan ta daga tagumi da tayi,daga zaunen da take,
Cikin dan yake hakora tace ina kwana Sadiya?
Wani kallo tai mata sanan tace, lafiya lau, daga haka ta wuce kawai abinta,
Kitchen ta shiga sai ga ta tafito dauke da kufi a hannun ta,
Kunsan a,tare suka jefowa juna tambaya a lokaci guda,
Ita Sadiya na cewa kin karya ko ?
Ita kuma Samira tana tambayar ta, yaya Abubakar fa,
Ya fita office ai tun da safe,
Sadiya ce taba Samira ansa haka na,
Ita kuma Samira tambayar ne na Sadiya ya ba ta mamaki,
Tace banga komai ba da zanci aii, ?
Wani kallon mamaki Sadoya tai mata don jin may tace,
Kin duba kitchen babu abinda zaki dafa ne,
Ban an yayazan kuna gas din bane,
Tsuki, tayi tace muje ingwada maki yadda zakiyi ko ?
Jiki ba kwari duk yunwa ya ishe ta, tabi bayan Sadiya wace ke saye da wani shimi mara hannu,
A tunanen Samira atare zasuyi girkin amma sai taga kawai sadiya ta juya batare da ta fada mata ko may zata dafa ba,,,
A haka dai tai ta kokarin ko yo tana yi tana hawaye, tana gogewa da bayan hannu,,,

Samira nada sati da zuwa Lagos yayanta yasata wani makaranta dake unguwar su, na jeka kadawo,
Agida kuma yake dan samun time yana
masu karatu,
Samira ta fara fahintar irin halaiyar da yayanta suke aciki da matar shi,
A wanan yan kwanakin ta gane cewa, Abubakar , yana da wani irin baudadden ra,ayi arayuwan shi,
In har ba sanin halinsa kayi ba zakasha wuya gurin zama dashi,
Gashi miskili na karshe ga saurin fushi, dan abu kankani zai iya sa shi fushi ya bata mai rai,
Saidai dadin bai daukan lokaci mai tsawo acikin fushin,
Sannan kuma bai yarda sam Sadiya ta wulakanta mai yar uwa,,,,

Mama Ladi yau sai habaici take sakewa don jin cewa Meenat zata wuce sokoto karatu gobe,
Kirikiri ta shiga cewa iyakar dai mutum nan sokoto, badai mutum yakai Lagos ba,,
Kishiryar ta ce ta bata ansa yau da cewa hassada dai ga mairabo taki ce,,,
Sai kuma ta juya gurin ta da cewa mutum dai ya tsaya matsayin sa,
Idan kuma fitsari banza ce ai,kaza tayi mana,,,,,



ZEEE. MAKAWA YELWA
🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸🕸🕸
9⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA

SIRRATAL,LAZZINA,
AL,ANTA ALAIHIM,



A daidai wanan lokacin da mama Ladi ke wanan habaice, habaicen,
Abubakar yana kwancen a falon shi saman dogon kujera,
Zuciyar shi sai a cunkushe da bakin ciki da bacin rai,
Irin yadda daga matar shi har sister din shi babu wace ke iya gyaran ko da falo ne ko kitchen din gidan,
Hakan yasa yake jin wani irin radadi da zogi a lokaci guda,
Idon shi sama yana kallon silin din falon yadda yanar gizo duk ya lulube silin din,
Da sauri ya mike daga kwancen da yake kamar wanda aka mintsina, ya zauna,
Zaman bai mashi ba ya kuma mike tsaye yafara dan zagaye dakin,
Abind ya,gani jiya agidan abokin aikin shi wanda akaiwa kiran gagawa cewa yaron shi baida lafiya,
Suka tafi gidan gaba dayan su don ganin jikin yaron,
Duk da ga yara har biyu amma gidan fes yake kamar ba ataba zama acikin shi ba,
Ga wani kamshi na daban na tashi, a sassan gidan,
Duk da rana bai wani yi sosai ba a lokacin amna sun samu har tayi girki, rana nan aka zubo masu su ka kwasa,
Idon shi ya lumshe don wani gululun takaici da ya ziyarci zuciya,shi,
Don hango wasu tarin kayan wanki da yayi a kofan shiga bathroom din su,,,
Alama ya nuna mai cewa ko Samira ba ta da tsabta ke nan don idan har Sadiya bata gyara ba ai ita ya kamata ta gyara,
Sauki guda da ya samu yanzu shine Samira tana girka abinci su ci ya dai na yawon saye ko ya girka ,
Duk haka yake tilastawa kan shi cin abincin don rashin dadin shi,,,,

*** *** *** ***
Wanan ne karon ne farkon shigowar ta garin sokoto, iyakarta birnin kebbi sai ko gwandu ko kalgo gurin gwagon ta,
Hakan yasa tun shigowar ta take raraba ido gurin kallon yanayin garin,
Gidan dan uwar mahaiyarta Baba ya fara kai ta don ta san guri,
Malam Nafi,u malamin asibiti a cikin garin sokoto, yake aiki,
Yana da mata guda biyu da yara biyar, yana da dan rufin asirin shi, gwargwadon kima,
A gidan Baba zaibar Meenat yadda su ka yanke shawara cewa shi uncle Nafi,u ne zai kai ta idan weekend ya kare,,,
Ameenat tana tsaye kofan gidan uncle dauke da dan karamin yaron amaryan shi na goye,
Ida tayo wa mahaifinta rakiya don ya ce bazai kwana ba ranan zai koma gida,
Baba ya,ce tau, Amina ki kasance da halinki nagari da nasan ki dashi,
Nakawo nan karatune don ci gaban ki duk da dai kin ga malam ba wai yaso hakan bane,
Don Allah ki rike mutuncin ki,
Ki rike ibada ki tuna da irin gidan da ki kafito kada ki sawa, zuciyan ki kwadan duniya ko kadan,
Ki jira rabon ki don rabon mutum bai taba wuce shi, inji Allah,
Nan da nan idon Meena ya kawo hawaye amma sai ta wayan,ce da sherewa da bayan hannun ta,,
Ga wanan mahaifiyar ki nan duk abinda ya shige maki duhu ki sanar dashi don zai aiko min insha Allah,
Nabar ku lafiya Allah ya bada sa,a yasa a dace duniya da lahira ,
Wani irin kuka ne yazowa Meenat duk yadda take son zuwa boarding da kuma sokoto sai taji yau bata so kwata,kwata,
Kasan cewar yaune rana na farko da ta taba barin iyayyen ta zuwa wani gurin,,
Tayi da ta sani da ma ba,ta,zo ba ta,zauna gida tare da mahaifanta da yan uwan ta,,
Cikin gida takoma inda ta zauna folo don babu dakin wace zatace zata nufa daga cikin matan uncle din nata,,
Har kayan ta duk a nan suka bar mata su afolon gidan nasu,
Wanan bai hana Meenat mikewa don zuwa tattara kwanon da akaci abinci ta fara wankewa,,,
Tare da ita ranan uwargidan tai girki don kusan aikin Meenat ce tayi shi don ta iya,,,
Dan kwana biyun da Meenat tayi a gidan uncle din ta yasa amaryan shi Sakinat ta ja Meena ajiki don ta fahinci yarinyace wace bata son jikin ta,
Ranan da za,a kai Meenat makaranta uncle Shafi,u ya dan kara mata sayayyan provision masu dan yawa da dai yan sauran abinda zata bukata wanda Baba bai sayo mata ba,


*** *** ***

Tun tafiyan Meenat sokoto Baba suke wasan boya da malam mahaifin shi,
Da zaran anyi sallah asuba Baba ya fita bai,dawo,wa gida sai dare lokacin malam ya shige gida,
Saboda
tsoron haduwar su da malam din,wanda bai so tafiyan maryam karatu har wani gari ba,
Sati guda cif da tafiyan Meenat ranan Baba yadawo daga gurin neman kudin shi da yake yar buga bugan shi,
Baba Buhari ya tsayar dashi a kofan gida yana mai nasihan cewa ya tafi ya gaida malam don kwana biyu ke nan yana jin yana tambayar shi,
Jikin Baba samaila yai sanyi don haka ya yanke shawaran shiga gurin malam din yau,
Baba samaila bai yi sanyi a gwiwa ba yana gama gyara jikin shi ko abinci bai tsaya ci ba ya nufi sashen mahaifin shi,
Bayan sun gaisa sai yar shiru ya biyo baya kadan,
Muryan malam ce ta ratsa shirun da cewa Samaila guduna kakeyi kwanan nan ko don nace kada ka kai yar karatu wani gari,
Baba samaila yadan gyara zaman shi cikin ladabi yace ba hakana bane malam aiyukane sukai min yawa shinassa,
Murmushi malam ya yi tare da girgiza kan shi, yace,
Duk da na san cewa yanzu zamani yana tafiya,ne da ilimin zamanin,
To amma ita diya mace tarbiyan ta sai iyayen ta sune zasu tarbiyar da abin,su yadda ya kamata,
To amma naso ace ka kalli lamarin ta fuska biyu, addini da kuma zamani,
Don haka na kyale kane kawai don da gida biyu aka sanshi dama ,
Saboda kace gurin wan mahaifiyar ta zata zauna don yana garin,
Don haka na kyale ka ka tafi da ita amma nan gaba ban son gardama akan diyan ku,,
Baba Samaila yace a yi hakkuri malam baza,a sake ba insha Allah,,,
Bakomai inji malam ai Ameena yarinya ce mai natsuwa da hakkuri Allah ya bada sa,a ,,,,,


*** *** ***

Yau Monday, ma,aikatar su Abubakar sun bude Monday su da, transfer a hannayen su,
Wada daga ciki su har da Abubakar wanda ya samu karin girman bazata, saboda kwazon shi ga aiki,
Gashi kuma an turo shi Abuja , babban headquarter su da ke can, da zama,,,
Sosai sauran abokan aikin shi musaman hausawa suka fara farin ciki wani hanya kuma suna bakin ciki rabuwa da mutum kamili irin Abubakar din,
Inda ba bata lokaci suka yai haraman zuwa yin reporting,

*** *** ***
Mama Ladi ne zaune daki da yaranta mata biyu da ke aure a cikin gari,
Bukin suna akeyi a gidan can sashen baba su, guda,
Mama Ladi ce ke magana, da yaran nata alokacin,
Inda babban yar ta ta kawo zancen, dan uwan su Abubakar da cewa,
Mama yanzu shi mai sunan malam haka zai zauna da mace bata haihuwa kuma bai damu ba, ?
Cikin Fushi mama Ladi tace wa yar nata, shi da ke zama da ita ya ce maki yagaji da hakan ne,
Binta wace itace ke bi wa Abubakar gurin haihuwa tace,
Cikin murmushi, haba mama ke dai baki son sam ayi zancen wanan matar ta mai sunan malam,
Mace sai dan banzan tsiwa, taurin kai da nakasa ga kekessasshiyar zuciya da rashin sanin ciwon kai,
Idan Baba Wada yana bada labarin ta wallahi mama kare bai ja,
Mama kin san fa shi ba wai zai taba zuwa gida ya fadi irin halin rayuwan da yake ciki da ita bane,
Tafarkon mai suna maryam tace, nidai wallahi mama ke ce mai son wanan hadin tun farko,
Don dai wallahi Abubakar bai dace da wanan matar ba sam,,
Shin wai ina ruwanku da wanan zance ita naga ta dace da shi shiya sa na hada su,
Shikuma Wada dama munafunci ya tafi yi shi yasa bai fadawa kowa ba lokacin da zai tafi, don da ban yarda ba,
Gaba dayan su suka yi shiru da bakin su, don sun san cewa Sadiya bata taba baki a gurin maman su,,,
Maryam ce tace ai Samira tana can zamu ji komai abakinta idan ta dawo,,,

*** *** ***

Saye yake cikin bakaken suit, kai tsaye ya ke tafiyan shi mai kama da ta kasaita da isa,
Yana rike da wayar shi a hannun shi na dama sai briefcase din da ya rika a hannu guda,
Idon shi ya na manne da farin glass mai kama da medicated,
Tun daga nesa mutanen da ke zirga,zirga a maikatar suke satan kallon shi,,
Kallo guda za kai mashi ka gano cewa namiji ne jan gwarzo don a cikin azama yake tafiyan shi,,,
Office din shugaban su ya nufa kai tsaye tare da taimakon wani lebura, Abdullahi wanda suka hadu tun a bakin get,
Abubakar ya yaba kwarai da kyawon gurin inda, girman gurin da kuma yawan ma,aikata yasashi gane cewa ba karamin guri yazo ba yanzu,
Office din shi babban fiye da tsan manin shi don kusan ya kai wani taki mai tsawo,
Bai wani tsaya bata lokaci ba don dama shi mutum ne mai kwazo ga aiki,
Farin jinin jama,a ke gareshi duk inda yake to amma kuma gashi shi mutum ne wanda baida surutu,,

Meenat yarinya mai hazaka inda ta hadu da wata Yarinya, Aisha,yar kauyen, sokoto Bodinga,,
Meenat da Aisha sunyi mugun shakuwa a tare su ke komai nasu, kasancewan a rana guda aka kawosu makarantan,
A haka rayuwan su yaci gaba da kasancewa a tare da junan su,
Kokarin Meenat yasa aka santa cikin dan lokaci don duk wani abinda za,ayi a makarantar na kokarin, da ita a ciki,
Wanan ne yasa mata farin jini gurin yan uwanta dalibai da malaman su,


2 Comments On TARKO
avatar
maryam-2-4-2

1 year ago

Reply

Ya zanyi in karanta duka

avatar
maryam-2-4-2

1 year ago

Reply

Ya zanyi in karanta duka

Please Login or Register in order to submit comment