Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kai na gyada mai alaman na yarda da zancen shi insha Allah zan kula,
Rigar barcin da ke a jikina mai baiyyana surar jiki a fili, don haka komai gashi nan free,
Shi na ga ya tsura wa ido, jikin nawa ido a lokaci guda,
Gurin da ya,ke kallo nai saurin kallo sai na gane cewa kirjina ya tsura wa ido, wanda kunya ne ya kamani,
Idon shi naga ya lumshe tare da sauke ajiyan zuciya
Babu zato sai jina nayi a tsakiyar kirjin yaya Abubakar ya matse ni gam yana wani sauke ajiyan zuciya,
Dadircewa nayi kasancewar hakan sabon abune a guri na,
Amma shi yaya Abubakar, tuni yai nisa da inda yake,
Bai taba samun irin wanan rayuwan ba da har ya gigice a lokaci guda saboda mace,
Sosai hankalina ya tashi amma babu yadda zan yi in kwaci kaina, a lokacin,,
Kawai sai na sakar mashi kuka kamar jiya amma abinda bambanci don yau bai sarara min ba sam,
Kuka sosai nake mai da magiya da kyat na samu yaya ya sarara min
Ya koma, saman gado yana sauke numfashi guda,guda,,
Ya kai minti goma sha a gurin yana sauke nufashi guda guda,
Kukan da na keyi ne ya ke cin zuciyar shi ya mika hannu da niyar ya lalashe ni amma kuma sai ya kasa kai hannun shi gareni,
Don bai san may zai ce indan ya tabani da niyar bada hakkuri ba
Jikin sa duk a dake kamar ya yini a gona, yana aiki,
Gefen da nake kwance ya kalla idon shi ga kitson kaina wanda ya hargitse,
Lalai Aminatu daban ce daban take da sauran mata komai na yarinyar burgeshi ya keyi sosai, komai nata tun tana yarinya special, ne,,,
Dole ne yanzu ya sawa kan shi zama da ita kamar yadda iyayyen su ke bukata,
Da kyat ya mike ya mai,da rigar shi da ke yashe a kasa,
Bargo ya jawo ya rufa min har kai yana mai jin kukan har a cikin ran shi,
Falo ya nufa don ya sha ruwa a fridge saboda zuciyar shi da ya ke jin yana mai kuna,

****** *********** ******
Direct gurin fridge ya nufa ya dauko goran ruwa mai sanyi ya balle marfi ya sawa bakin shi,
Sai da ya kusa shaye ruwan ne yaga kamar Innuwar mutum zaune a saman kujera,
Goran ruwan yai saurin cirewa ya kallon gurin cikin mamaki,
Inda ya taka har zuwa gurin, Sadiya ce zaune cikin wani farin nightgown har kasa,
A hankali yaya, Abubakar, ya ce Sadiya lafiya may kike yi anan cikin wanan lokacin, haka ?
Dago kai tayi fuskanta duk hawaye shabe shabe sai she,shekan kuka takeyi,
Sai wani kallo take masa mai cike da zargi ganin yanayin ta yasa shi daure fuskan shi tama,u,,
Kara maimaita tambayan shi yayi gare ta da cewa lafiya dai ko ?
Cikin wani irin murya tace yanzu Abubakar don ka auri yar uwar ka,shine har zaka fara wulakantani,
Subbahanallahi yace a hanzarce,
May nai maki Sadiya,
Cikin wani irin ya mutsar fuska tace,
Girkina ne yau fa ka barni ka tako zuwa dakin yar uwanka don ku nuna min bambanci,
Tsaki ya ja mai karfi yace ke wace irin mahaukaciya wai Sadiya ?
Sam baki da wayo baki da hankali baki san komai ba banda kwanciya kiyi kallo,
Baya ga rashi ilimin addini harda ma rashin sani ka,idar komai baki sani ba,?
Ita yarinyar da kike ikirarin yar uwa ta ce wace iri ce ita,
Budurwa ko bazawara?
Kwana nawa aka yankewa wa budurwa a yi da ita indan an aure ta,
Sannan Bazawara kwana nawa za,a yi a ta re da ita ?
Tabe baki tayi tare da gyara tsayuwar ta wani bakin kishi ke cin ta a lokacin,
Ta ce yanzu kana nufin cewa sai, ka yi sati a tare da ita ?
Ke dakata na fada maki sai wanan yarinyar ta cika sati guda sanan zan dawo gurin ki,
Zubur ta mike tsaye tana cewa, dama nasan abinda za kuyi min ke nan ,
Gashi ba a,kai ko ina ba har kun fara nuna min,
Rai a bace yaya Abubakar yace, look Sadiya ban son abin surutu na fada maki yadda akeyi kije ki tambaya fakat,
Ya daga goran ruwan shi ya shiga kwankwada kamar yadda ya fito yi,
Nan ya barta ya juya zuwa hanyar dakin na, Meenatu,
Wanda tun fara rikincin su na kargamay kofana don gudun kar ta,shigo tai mun masifan ni ma,
Jin na rufe kofa yasa shi saurin juyawa inda ya fito nan yabar Sadiya tana ta rusa kuka wai ya cuce ta,
Dakin shi ya fada ya wuce zuwa bathroom kai tsaye yai wanka,

****** ********** ******
Hajja ce a cikin damuwa saboda yau gaba daya Dodo ya hana ta shakat kamar zai halakata,
Saboda kwana biyu bai samu abin da tai mai alkawarin samu ba,
Gashi duk yadda yaso shiga gidan wanan bakuwar yarinyar ta hanashi duk ta kona shi da abinda ta keyi duk dare,
Allah Allah ta keyi Asuba yayi tabar gidan zuwa gidan mai,lassa,
Ta yi diban ruwa har ta gaji ta hakkura, takoma gefe tana mai nadama da wanan rayuwan da ta jefa kan ta, a ciki, saboda kwadayin duniya,
Don yanzu ta koma kamar mujiya a cikin mutanen gari,
Ko yaro ke abu yanzu za,ace akai shi wurin hajja manya,
Bata da dama ta shiga taron mata yan uwanta sai su watse su ce ai ita muguwa ce,
Ga dukiya kamar ya kashe ta amma bata iya ci don bata iya amfani dashi,
Gashi yar ta Sadiya dake a birnin taraiya Abuja tana aiko mta da sako jefi jefi,
Idan da tasan da hak gaskiya da bata sa anta acikin fitina ba,
Yanzu tana da buhuhunan shikafa sukai dari, biyu, taa da wake tana da gyada da diyan dorawa,
Amma bata iya kashe su ga harkokin ta idan ka ganta mutsu,mutsu da ita, kamar mahaukaciya don wahala,
Wani kugi da wanan abin boyen nata yayi don azaban da yake ji, shiya kara firgita ta,
Kusan duk mutanen dake a farke lokacin a unguwar nasu sai da su kaji wanan kugin,a dodon Hajja, mutane suka tsorace,,,,
Bai samu shakat ba sai zuwa sallah asuba yasu ya dan lafa acikin randan roban da yake ciki,,,,,,

****** ********** ******
Yau kan a cikin daurewa na, mike saboda karfin hali irin na fulani,
Ina jin jiki amma dole indaure in fita don hadawa yaya abin kari kafin ya fita,
Sai da na tabatar da na gama dafa komai na koma daki na watso ruwa,
Nafito daure da dan guntun towel sanin cewa ni ka dai ce a dakin nawa, ina kokarin daukan wani sabulu don wanda ke aciki ya fadi kasa,
Zaune yake saman sabon zanin gafon dana kara shimfidawa da safe, bayan nai sallah,
Wayana ne a hannun shi yana game din snake a ciki,
Gabanane ya fadi don ganin shi da nayi a daki lokacin,
Wani irin dip naji kamar in dauke wuta ko in shige kasa, don kunyan yadda ya ganni a haka,
Ido ya zuba min, duk sai na rude nakasa koda motsawa,
Da kyat na iya cira kafana zuwa bakin drower mirro, don in dauko sabulun,
Daidai zan taso naji an riko ni tabaya na ji na yi ya rungumay ni tsam a jikin shi,
Ido na a runtse ya zagayo dani muna fuskantar junar mu,
Cikin wata irin murya nake cewa don Allah yaya kayi hakkuri na saka hijabina pls,duk a cikin runtse ido na.
A daidai saitin kunnuwa na naji muryan shi ya na cewa a hannun shi a gashin kaina yana dan yamutsawa a hankali,
May yasa jiya don nafita shan ruwa kika rufe min kofan daki,?
Naji shi ya kara cewa Uhmmm?
Kai na a kasa ido a runtse na ce kayi hakkuri yaya nazata ka wuce ne,
Abinda naji a lokacin ya hanani ko da motsin da kafana,
Ina jin lokacin da ya cire dan guntun towel din dake a jikina,
Inda kyakyawan surar jikina ya baiyyana afili ta yadda zai iya ganin komai nawa,
Wani irin ajiyan zuciya naji ya sauke da karfi hankalisa kamar baya a jikin shi,
Duk abin da ya keyi idona yana a rufe don bazan iya budewa na kalleshi ba, saboda nauyi da kunya,
Hawaye naji suna biyu fuska na a hankali
Kuka again Meenat ?
Why pls?
Ko ba kya so na ne ?
Kai na girgiza mai cikin rufe ido ,
To ki daina kuka Meena ni mijin ki ne a yanzu ina da right din da zanyi duk yadda nake so dake,
Iya wahala na shashi ranan a gurin yayan nawa kuma miji na inji Allah,
Ina jin lokacin da ya gama abinda zai yi yafita dakin nawa,
Da kyat na samu na tashi zuwa bathroom, sosai na gasa jikin ina kiran mugu macuci kawai, jarababbe,
Malam tsoho da su baba sun cuce ni sun hada ni dan barikin mutum,
Wando ko kunya baiji a matsayi na yar uwar shi kuma kaunar shi yake bude min tsiraici haka agaban shi,
Sai naji wasu sabbin hawaye sun kara biyo fuska na masu zafi, nasa bayan hannu na na goge,

Kallo guda zakai min yau kasan na fada sosai don fuskana yai wani zurun,zurun, kamar nai ciwo,
Ina kokarin zura riga a wuya na, naji shigowar shi dakin
Tun daga nesa na fara kokarin mikewa inja baya don kaduwa da tsoron da nayi,
Haba Meenat sai kace kinga dodo ki saki jikin ki da ni please ba zan cuce ki ba fa, ko in zalunce ki,
Cikin wani irin murya nace don Allah yaya kayi hakkuri, ka kyaleni hakana please,
Murmushi ya yi mai nuna yarinya ai yanzu nake ni,
Sa kaya kizo mu karya ke muke jira, awaje,
Ina fitowa mukayi arba da Anty Sadiya wace idon ta yai ja don kuka,
Kau da kai nayi gefe tankar ban ga yanayin ta ba sai da nace ina kwana Anty Sadiya,
Ta ansa min ciki,ciki da cewa, Lafiya,
Ta wani kau da kai gefe da sauri,
Yaya da ke a gefe ya girgiza kai don takai ci
Kujera na jawo na dan zauna a hankali gefe guda,
Sam na kasa sakin jiki inci abincin sai wasa da spoon din hannuna nake yi,
Kur da ido yaya yai min bazaki daure ki kici koda kadan,ne ba ?
Anty Sadiya ce naji ta dangwaran da plate din da take cin irish ta mike zuwa part dinta,
Gaba dayan mu muka bita da ido har ta bace zuwa ciki,
Murya yaya naji ya na cewa, ko inzo in baki a baki ne?
Da sauri nakai spoon guda abaki na, badon naso ba,,,, ,,


ZEEE MAKAWA YELWA,,,
[7/28, 05:45] Anty Lantana: 🕸🕸🕸TARKO🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸🕸🕸
3⃣6⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA,,

ALLAH-AL-MU`IZ,,,

Zaune take a farfajiyan gidan su ita kadai tana tunane,
Duk da a lokacin duhun dare ya tsala ko ina bakikirin za ka ga guri amma ita duhun bai damay taba a lokacin,,
Yau idan zata iya lissafawa kwana kusan hudu ke nan rabon da ta ga Yallabai kamar yadda take kiran shi,
Don dai tun ranan da a,kace anbashi, rikon a counter din su gaba daya,
A yan kwanakin da su ka wuce bai tafiya gida sai tare da ita,
Amma yanzu sai kawai ta ga ya sa kai abin shi ya wuce before ta iso, gurin motan shi,
Mutumin da aka san shi da ko,karin over work a ma,aikantan baki daya, amma yanzu sam ya daina, wanan cikin kwanakin nan gaba daya,
Shi wai wace irin yarinyace ko kuma mata Yallabai din ya aura ne wai da har zata saurin jaye mai hankali haka,?
Dole ta bincika taji ko ya wanan matar take, shin yarinya ce, tsohuwa ce yar kauye ce, ko kuma wai ma yaya take, ne wai ?
Malam Audullahi masinja ne ya fado mata a,rai, gurin shine za ta dan samu wanan labarin amma fa sai ta hanyar, zolaya don taji komai a gurin shi,,,
Da wanan shawaran ne ta mike zuwa cikin dakn kwanan su don ta kwanta kamar yadda kowa ya natsu, don yanzu karfe daya da rabi ke nan na dare,

Washegari a gurin aiko kowa sai harkokin gaban shi ya keyi a lokacin,
Amma ita tunane takeyi yadda zata dan kebe da mudi ko malam Audullahi,
Don duk cikin ma,aikatan su da su biyu ne kawai yake hurda sosai ta gani,
Kamar kullun a zaune suke su biyu suna hira kamar yadda suka saba,
Salawatu ce ta zo cikin shigan irin nasu na yan gayu,
Buje ne na atamfa amai tsaga ta baya har zuwa sharaban ta,
Idan tai tako daya zaka iya ganin naman kafarta a fili,
Dinkin rigar mai umbrella ne har kusan gwaiwan ta mai dan tsawon hannu,
Tana rataye da handbag mai shige da launin kayan,
Daurin dan kwali har a gaban goshin ta, fuskanta ya sha makeup kamar kullun,
Takalman kafarta tsinin shi kamar marfin biro ya ke,,
Tun daga nesa malam mudi ya hade ran shi don dai shi sam baya kaunar wanan yarinyar da bawan Allah ga ,
Saboda ba irin tarbiyan su guda ba kai shi agurin shi basu ma dace ba sam gaskiya,
Da takon ta mai kama da karan kofato ta iso gare su,
Yau, ba, ta tsaya har su gaishe ta ba ,
Ita,ce ta dan sakata a gaban su tana cewa sannu ku fa,
Ya kuke ya kwanan iyali,?
Shikan malam Mudi ya sha toka bai son wani alaka da ita ta ko ina, amma shi malam Abudullahi cikin washe baki ta ke cewa,
Malam Abudullahi duk shan miyar amarya ne yasa yanzu daga ku har Yallabai ba,a ganin ku ko ?
Gaba daya suka jiyo suna kallon ta a cikin mamaki don sam basu da labarin cewa ubangidan nasu yai aure,
A cikin nuna yar zakuwa da son jin zancen malam Abdullahi ke cewa kai hjy yaushd akayi haka ?
Tace au boye min kuma zakayi bayan shi da kan shi angon ke fada min cewa,
Amaryan shi ta tare acikin satin nan da ya shige,
Gaskiya bamu da labarin cewa yai aure don dai bai fada muna ba,
Amma kila shi abokin aikin nawa ya samu labari ban sani ba ko ?
Malam Mudi yace cikin yar matsewa ai ba sai na sani ba don bani na biya mai sadaki ba,
Sam bata ra,ayin wanan bakin bakanen a rayuwan ta don ta na sane da cewa ya tsane ta,
Muryan malam Abdullahi ne ya ratsa mata kunnuwa da cewa aiko,
Abin yai kyau, wallahi ga amarya ga karin girma,
Sai shi malam Mudi ya ce kaga ke nan amarya tazo da nasarorin rayuwa ta shigo da far kafa ke nan,,,
Sai kuma taji sun bala,in bata haushe da abinda suke fadi,
Watau auren yarinyar shi ya kawo wa Yallabai good luck,,,
Wuf ta fada cikin office din Abubakar ran ta a bace
Ama a irin yadda ta hango shi zaune a cikin annuri da annu shuwa yana aikin shi hankali a kwance,
Ga wani irin kwarji da haske da dan kiba da ta ga ya kara mata,
Gaban ta ya ba da dammm kar dai ace zance munafukan mutanen da ta baro waje gaskiyane,
Da takon da girgizan dole ta karasa gareshe cikin dan sakin fuska,
Oh, Salawa how are you?
Sorry, please two days bamu hadu ba saboda ban samun tsayawa
Don new wife dina bata faye lafiya ba,
Wani irin kishine ya turnike mata girjin ta alokaci guda,
Da kyat ta iya seta kan ta, har ta dawo normal, sai dan dariyan yake da tayi afili,,
A sorry sir ashe new madam ce ba lafiya kardai har an samu yan baribari ne ko ?
Fuskan shi ya daure don baiga abin da zai sa ta ce haka ba?
Da ta ga haka sai tai saurin cewa Allah sarki wata kila bakunta ne, takeyi hakan,
Ci gaba yayi da aikin shi sai kuma ya dan dago kan shi ya ce barin kira malam Abdullahi ya baki drink ko ?
No ka barshi kawai I am ok,
Ta mike tana dan gyara bayan bujen ta koda yadan tatare zaman da tayi,
Sai ya dago kai sukayi arba dashi yadan sake mata guntun murmushi ya ce I will called you back indan na rarage yanzunan ina busy ne pls,
Ita,ma dai yar dariyan da bata kai ciki bane ta sake a lokaci guda, tana cewa zan tafi ba matsala ai,
Sai gaban ta wani irin mugun faduwa yakeyi tankar zata shude a gurin saboda bacin rai,
Saboda wani irin bala,in da take ji sai take ganin ma,aikatan yau yana juya mata,
Tafiya takeyi tana cewa Yallabai ne, yau yake nuna min cewa yana son yarinyan nan ke na,
Yarinya da shi da bakin shi yake ce min a gidane aka hadasu bai ma san ta ba,
Kai lalai,ma namiji abin tsoro ne gaskiya,
Wai yau Yallabai din tane da bakin shi ke fada mata zance akan wata mace,
Tunda har yake bata lokacin shi, haka sosai bai ko iya boye wa,
Zaune take a cikin office din su duk rayuwan ta yai mata kunci ta rasa may ta ke ciki ne wai,
Idan ba tayi da gaske ba fa abin zai bashe ta, gaskiya ita bazata iya zama batare da ta mallaki miji irin yallabai ba,
Gashi ta samu kuma yana batun kurce mata daga hannun ta,
Lubuna ce tsaye a kanta tana karewa kawar nata kallo a cikin mamaki lokaci guda ta ga duk ta canza mata,
Kafadan ta, ta,dafa sai da Salawatu ta dan girgiza kadan don tayi zurfi a cikin tunane ko
Dago idanuwan ta da sukayi jawur tayi saboda bacin rai, ta dan sauke ajiyan zuciya,
Tace Lubuna Abubakar yana son yai min yawo da hankali na wallahi,
Bayan ya gama sani na yarda dashi 100%, sai gashi yana son ya kawo min sabon zance kuma,
Cikin wani irin takaici lubuna ke kallon aminiyar nata ,
Irin yadda ta tsaya saboda so tana son wahal da rayuwan ta ga banza,
A gaskiya Salawatu ki na bani mamaki kwarai da gaske,
Wai shim Oga Abubakar shi kadaine namiji a Abuja?
Kar ki manta kina da masoya da yawa fa akan maye zaki tsaya kina son batawa kan ki lokaci ne haka,?
Kodai kawai don shi yaki ku tsaya kuyi Roncy a waje kamar sauran maza,
Ke kuma kin riga da kin mutu a kan shi, idan ba kin dandana shiba bazaki iya hakuri da shi ba,
Hawaye ne suka biyu fuskan ta zuwa sauka kasan fuskan ta,
A cikin takaici take cewa Lubuna ina son wanan guy din kema kin sani
Kuma I am lucky yace zai aure ni,
Idan bashi din da yazo min da zancen aure ba kinga wani wanda yazo muna da zancen aure ne,
Dubi irin zaman da mukayi da oga,Yusuf har wuce kinji zance aure ga bakin shi,
Gaskiya Lubuna bazan so in kare rayuwana a haka ba?
Don lokaci yayi da ya kamata mutum yaiwa kansa fada ,
A yanzu bani da burin da ya wuce in auri Yallabai Abubakar,
Amma gidan su da yan uwan shi suna son suyi muna tsakani, da shi,
Tausayi taba aminiyar nata don haka takai zaune tana mai kallon ta acikin tausayi,
Mutun mai karfin hali da dauriya irin Salawa ace yana kuka haka akan soyayya,
Salawatu ke nan inji Lubuna tana murmushi irin na bacin rai,
A gaskiya ni nasan cewa dama zaki fuskanci irin wanan matsalan gurin mai mata sai gashi kuma ya kara yin wata matar,
Don a gaskiya yan Yallabai sun nuna maki cewa basu kaunarki acikin su,
Don zancen auren ki yana gaba da na wanan da suka daura mashi,
Yanzu tunda har kin nuna cewa zaki iya zama dashi a hakana da mata dayawa ai ba matsala sai mu san yadda mukayi, ai,
Da sauri Salawatu ta daga kai ta kalle ta cikin mamakin jin abinda ta ce,
Kiyi shiru kawai mugani in har ya ce zai guje ki zai gamu da aikin mu sosai,
Munyiwa banza ma balle wanda muke son zama dashi,,,,

****** *********** ******
Yau, satina gudu atare da yaya Abubakar, wanda dan zaman da mukayi a tare yadan jawo muna yar shakuwa kadan a tsakanin,
Koda yake shakuwar tamu sai idan muna atare ne saman gado inda ba haka ba,
Sam bazaka gane farin cikin dan uwan nawa ba don a koda yaushe fuskan shi a daure nake ganin ta,
Nasan cewa kwana bakwain da mukayi tare da yaya Abubakar,
Ya dan bude min wani sabin babin rayuwan da Anty Amarya ta dade tana lurar da ni amma ban fahinta ba,
Ya Abubakar gwarzon namij ne, wanda yasan yadda zai tafiyar da macd a cikin ruwan sanyi,
Har ta mantar da damuwan ta don sannu a hankali yadan kawar min da damuwar irin zaman da ada nake hage dashi,

Yau Anty Sadiya ce zata karbi girki a gidan don haka kamar yadda na tsamani sai ban ga wani alamar karban girki daga gare ta ba,
Saboda banga fitowan ta zuwa dora muna girki ba kamar yadda yake,
Ina zaune saboda rashin abin yi na gyara daki na da bayi yafi a kirga, sai kamshi ke tashi ta ko ina,,
Karan shigowar motan yaya Abubakar cikin haraban ne yasani gane cewa ya dawo a lokacin,
A hankali ya turo kofan falon gidan hannu shi guda dauke da yar briefcase din shi guda kuma acikin aljihun wandon shi,
Shiru yau ya samu falon don kwana biyu kamshin turaren falo da na girki ne kan tare shi,,
Mamaki ne ya kama shi don ba haka yasaba gani kwana biyu ba,
A hankalo ya tako zuwa cikin falon inda ya aje yar case din shi saman center table,
Dakina ya nufa da ganin shi a gajiye yake, don daga tafiyan shi zaka gane hakan,
Daga kofa ya tsaya inda ya dan jingina jikin shi da dan katangar kofan dakin,
Zaune nake saman stol din dressing mirror dina ina gyara gurin,
Jin shigowan shi dakin nawa ne yasani dan juyowa ina kallon shi,
Cikin jin yar kun ya nake ce mai sannu da dawo yaya,
Sai da yadan tako har zuwa bakin gado yadan zauna yana cewa
Yauwa ya gida, da aiki Meena,?
Ban bashi ansa ba sai murmushi da na dan yi,

2 Comments On TARKO
avatar
maryam-2-4-2

1 year ago

Reply

Ya zanyi in karanta duka

avatar
maryam-2-4-2

1 year ago

Reply

Ya zanyi in karanta duka

Please Login or Register in order to submit comment