Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a lokacin na,dan farka daga barcin a hankali sai naga aiduk a jikin Yaya na keyin shi,,
Cikin yar murmushi yadan dagoni yana cewa Sarkin barci kin farka ko don ba AC,
Daga wanan garin bamu kara tsayawa ba sai cikin garin sokoto lokaci yamma ya fara sosai
Don haka , muka fara zuwa Yaya yai bucking, din daki shida driver shi,
Duk ban jin dadi jikin wani iri nake ji sai daurewa na keyi kawai don ban son, Yaya ya gane hakan,
Yaya yadan taboni jin nayi shiru yana cewa yarinya a garin Uncle din ta da Anty, amma bazata kwana gurin su ba,
Da sauri yadago kai yana cewa Meenat lafiya kike kuwa,
Cikin dakewa tare da langabe kaina nace ina ganin wahalan tafiya ne,
Girgiza kansa yayi tare da cewa, dole kiga likita, don ya dubaki,
A hankali na dan kara zuke jikina na, nade,sosai guri guda, nace,
Gajiyane kawai don ban tafiya mai tsawo haka, shiyasa kawai, badon ya yarda yasa mufita zuwa dakin da ya kama muna,
Kamar kada mu shiga dakin sai wani sanyi ya kara taso min a lokaci guda dole na dunkule guri guda, cikin bargo,
Aliyu ya nema yazo nan masaukin namu shine yai kokarin samo wanda zai dubani,
Likitan kamar abokin sune inda yai dan aune aunen shi ya shedawa yaya cewa gajiyane ya haifar min wanan zazzabin haka,
Inajin lokacin da yaya yakira Uncle yana sheda mai cewa muna acimin garin sokoto saidai banda lafiya shiyasa banzo gida ba,
Anty taso mu gaisa amma ina barci saboda maganin da nasha,,,,


ZEEE MAKAWA YELWA
[8/12, 05:33] Anty Lantana: ๐Ÿ•ธ๐Ÿ•ธ๐Ÿ•ธTARKO๐Ÿ•ธ๐Ÿ•ธ๐Ÿ•ธ
๐Ÿ•ธ๐Ÿ•ธ๐Ÿ•ธ๐Ÿ•ธ๐Ÿ•ธ๐Ÿ•ธ
5โƒฃ1โƒฃ

ZAINAB IDRIS MAKAWA

ALLAH - AL- MUQEET,,,


Allah da ikon shi, washegari sai na samu sauki kamar bani bace, jiya ba lafiya,
Ina zaune inda nai sallah Asubahi, Yaya Abubakar ya shigo hannun shi rike da tasbaha yana ja a hankali,
Kafin in masa ina kwana shi yafara yi min da cewa Meeanat ya kika kwana ya kika kara ji ?
Na,ansa da fadar Alhamdullahi Yaya naji sauki, ai
Ya ce, ashe kaunar tawa bata,son wahala daga yanzu idan zamuyi tafiya sai dai mu shiga jirgi ke nan ko,?
Murmushi nayi ina mikewa tsaye tare d nade Sallaya nace, ciwo daine yazo Yaya aikumaya bari,
Gado na koma nadan kwanta na dunkule guri guda kamar yadda yaro ke kwanciya cikin ciki,
Daga bathroom Yaya ya fito ya samu wayan shi da yasa caji tana kira,
Uncle naji ya ce bayan ya dauki wayan
Inajin haka nasan cewa Anty Amarya ce zata sa Uncle kira don jin ya jikin nawa, saboda nasan jiya batai barci ba da dadi,
Yaya ya cewa Uncle na samu sauki ai don har na tashi nayi sallah, ko,
Nan Uncle ke cewa wai kada mu ci abincin hotel an girka muna agidan shi,
Godiya naji Yaya Abubakar ya zabgawa uncle a wayan,
Nan naji yana fadin cewa bada safe zai wuce ba don yana son tsayawa yayi ta,aziya a nan sokoto don anwa abokin shi rasuwa,,
Bayan sun kashe wayan ne ya dan juyo gurina yana taba wuya na don jin zafin jikin nawa,
Alhamdullahi naji yace aijikin bazafi, zaki iya tafiya ke nan ko?
Gabana ya fadi don jin may yace, don nasan cewa da zaran mun shiga Abuja shi ke nan duk wanan tarairayan bazan samay shi full ba,
Mijin mai mata kenan komai na auren mai mata ragagge ne sosai wallahi,
Nace su Anty Samira sunji dadin su su kadai a gurin maza jen su,
Anty Aisha,ce ma naji ana cewa wai zata auri may mata inda nice ke da zabi ai bazan auri mai mata ba nace a rai na,
Karfe tara, da rabi mukabar hotel zuwa gidan Uncle don mu karya,
Dakin Anty na,shige na haye gado don sam zazzabin ya takura min sai dai banjin shi sosai sai alamomin shi kawai, nake ji,
Antu shigo dakin dauke da nawa kayan a hannun ta tana cewa,a,a kwanciyar kuma kika karayi Meenatu,
Wallahi Anty banjin kwarin jikin nawa sam ido ta kura min har dan wani lokaci sai take ce min tashi ki karya ko ?
Daidai lokacin da take zuba min ruwan zafi a cup ni kuma ina son mikewa zaune take ce min,
May likitan da ya duba ki yace ?
Nace cewa yayi,wai,wahalan hanya ce tai min yawa tare da sanyin Ac sai yaja min zazzabi,
Allah ya sauwaka tace tare da turo min cup din tea da plate din Irish da kwai soyayye, a gabana,
Tea din na dauka ina kokarin kaiwa a bakina, amma sai naji tankar zanyi amai dole na cire cup din da sauri na, aje,
Ido anty takara tsura min tace min lafiya cikin dan mararaice fuska nake ce mata,
Wallahi sai kawai naji bana son warin milk din da naji,
Anya kuwa Meenatu ?
Ba ciki kin ka samu ba ?
Wani iri naji datace hakan nace cikin shagwaba haba dai Anty don Allah daina zancen nan please,
Tace cikin dariya,to na daina na koma na dan kwanta ina cewa Wallahi likita yace wahala ce tai min yawa tunda ban saba ba,
Tace hakane fa kuma to amma aida kinci koda kwai ne da dan dankali ko ?
Ba don naso ba na kara mikewa zaune a hankali ina yar tsuki gefe, don sam ban san may ke min dadi ba,
Ba laifi don na dan ci Irish din da kwai, nacewa Anty barin sha ruwan Lipton zalla ingani ko zan iya sha,
Anty tamike da kanta tana hada min Lipton din zallah,
Tace min ance wai anwa mijin ku rasuwa a nan gari ko, ?
Nace eh haka naji suna magana da Aliyu, mijin kaunan Aliyu ne abokin shi,
Wace da ya tashi aure amma Mama ta hana wai yar boko ce,
Dama anan sokoto take aure, shine mijin ta ya samu accident, ankai shi kano jinya Allah yai mai rasuwa jiya,
Allah ya jikan shi na ce Ameen tamiko min cup din Lipton din na gyara don insha, Lipton din,
Tsab Anty Amarya ta gada min kayana ga trolls dina guda biyu, da mamaki na kalli Anty Amarya nace bafa zandade sosai bane anty wanan kayan sun yi yawa ai da arage su kawai,
Saida ta gama jan zip tai tsuki tace akai zaki dauka halan ?
Sanan ke san ko may zaki iske a can din, yanzu fa ba daga ke sai Sadiya bace,
Murmushi na yi tare da kokarin mikewa zaune nace, ai shiyasa surukin ki ya tambaya cewa halan kece ki ka gyara mai ni haka,?
Ke Meenat don Allah dai bari namike zaune da kyau na dauki, Irish' guda na jefa bakina nace tun ranan da muka shiga kasan Niger waahegari yake tambayana hakan?
Kunya ne ya kama Anty do komawa tayi saman gado tazauna tare da dafe fuskan ta,
Nan na dan fada mata yadda muka kwasa da shi har zuwa dawowan mu, sai dain in brief ba gaba daya na fada mata ba,
Uncle ne ya bude labulen dakin ta re da sallama yana cewa, maigidan ki yana falo yana magana da ke,
Gyalen na dan aza akaina na nufi falon Yaya yana zaune saman kujera one, seater, da waya a hannun shi yana dakila, a hankali,
Jin motsin fitowa na yasa shi dago kai ya tsura min ido kamar may son gano wani abu gare ni,
Da dan murmushin karfin hali ga idona na karasa gurin shi, zan zauna a kasa yace min come,up, dawo nan kizauna tare da danbubuga min gefen kujerar shi,
Kafada na dan make lokacin nakai zaune a kasan carpet ina cewa, nan gidan mune kada wani ya fito yagan mu hakana,
Hmmm kawai naji yace tare da cewa to yaya jikin naki ne yanzu,
Naji sauki nace tare da dan dago kai na kalli fuskan shi,
Uncle ne ya shigo falon da sallama abakin shi yana cewa, nayi magana driver yace gashinan cikin gari zai zo,
Sai lokacin Uncle ya, dan mai da kallon shi gurin da nake zaune yake cewa ,
Uhumm ki rubutawa kowa sunan shi a kayan shi yanzu driver zai zo ya kai masu sakon don kin ga baza mu wuce dashi har Abuja ba kuma,
Set set mu kai ta rubuta sunan nida Anty sai da mu kafidda na kowa,
Nafitar da wanda na sayowa Uncle da su anty sai hajiya Mama wace itin katon gyalen nan da manyan mata ke ya fawa na sayo mata,
Nono Rakumin da cukkui din da na sayo nace ma anty ta aje su anan amma sai tabani gora biyu wai in tafi dasu can,
Anty ta nosa tace Meenatu wanan irin tsaraba haka kamar wace ta tafi saudiya,
Murmushi nayi nace to anty ai shine daidai tace gaskiya ne kuma,
Kasamu kaci da wani shine samu inji Allah da mazon shi,
Uncle ya zo tare da driver yaya da wani suka kwashi kayan zuwa motan da zata,kai Birnin Kebbi,
Sai bayan tafiyan su ne Uncle ke sheda muna cewa, ai har da kayan masarufi ya tura masu da shi,
Sai dai abinda ya bashi mamaki shine su tufafin yace ace wai inji ki,
Murmushi nayi shine nake dan ba su uncle labarin yadda akayi sayen kayan,
Uncle yace shi yasa yake samun cigaba sosai agurin aiki don kinga shi mutum ne mai gaskiya ga al,amarin shi,
Don haka Meenatu, kisan yadda zaki zauna da wanan mutumin, kiji ko nace naji kawu,

****** ********* ******
Ba mu samu wuce Abuja ba a ranan don yan zirga zirgan da Yaya yayi shida Aliyu da Uncle dina,
Sai zuwa yamma yazo ya dauke ni wai muje yiwa Fatima kaunar Aliyu da mijin ta ya rasu gaisuwa,
Gidan jama,a ne ciki cimjin tako ina, yan uwanta da na maigidan,
Aliyu ne yai muna jagora har dakin ta dakin yana da falo amma ita tana can daga kuryan dakin ta,
Tafito cikin wani katon hijab har kasa hannu rike da tasba,
Ta zauna gefen wata tsohuwa, tana muna sannun ku da zuwa,
Mun mata gaisuwa inda Yaya ya jajanta mata tare da mata addu,an Allah yasawa yaranta Albarka,
Idon ta sun kode sunyi ja saboda kuka, ta ansa a hankali da fadin Ameen,
Aliyu ne kewa wa tsofin ga matar shi nan ai wace malam.tsoho ya hadasu auren gidan,
Wani iri naji da yafadi hakan take idon kowa yayo kaina suna cewa Allah sarki tubarkallah
Wata daga cikin su tace ai daga nin su jini guda ke aiki don kamar su yayi yawa,
Sannu keji ai,ta hakkuri kin ji, zaman aure sai da hakkuri,
Fatima wace ta dago ido a hankali ta kalle ni sai kuma ta dan kalli Yaya Abubakar ta maida fuskanta kasa da sauri don, ganin yadda yai mata wani kwarjini,,
Wata tsohuwa ke tambayan cewa, daga Abuja yanzo ko ?
Aliyu yace Niger suka fito shine ya tsaya suyi gaisuwa,
Sai suka kama fadin aiko, angode angode, sannun ku da hanya,
Yaya Abubakar yasa hannu ga aljihu yadebo kudi zasu kai dubu hamsi ya aje mata a gaban ta inda ya waiga gurin da nake ya yace muje ko,
Na mike na bi bayan su shida Aliyu wanda ke muna jagoran fita daga gidan,
Gidan Uncle na koma don wai zasu fita shida Aliyu,
Acan gidan Uncle bayan nagama cin abinci mu kadan yi hira da Anty akan irin tausayin da Fatima kaunan Aliyu taba ni,
Don muna hanya dawowa Aliyu ke ma Yaya Abubakar hira cewa wai yan uwan mijin dama basu son Fatima, a gidan saboda haka suka sashi ya kara wani aure,
Baifi wata uku da auren matar ba ya samu accident din da yai sanadiyar shi,,,

Yaya ya bugo waya lokacin ina barci wana kuma yana gurin caji dakin Anty,
Don haka, dole ya kyaleni gidan Uncle na kwana ranan,
Cikin dare zafin jiki ya tadani daga barci, amma zuwa asuba saina samu barci don sai naji zazzabin ya bari,
Tun da safe bayan mun karya muka kama hanyar Abuja, inda driver yai ta sharan gudu damu don ya samu hanya,
Duk yadda naso in boyewa Yaya Abubakar rashin jin dadin jikina hakan bai yi ba don zazzabin ya kara rufe ni a mota again,,
Nan Yaya Abubakar yahau min fada cewa may yasa ban fada mashi tun can banji sauki ba likita ya kara dubani, na biyo hanya da ciwo, haka,

A kofan gidan kamar kulun Samarin dake zama a kofan gidan suna nan,
Tsayawar motan mu ya sa hankali su duk yayo kan mu baki dayan su,
Nice ta karshen fitowa daga motar abinda yasa hamza saurin mikewa da sauri ke nan,
Ya ce a Amarya tazo ke nan fa, ?
Wani daga gefen shi cikin suke tambayan shi wata amarya yace mai wanan da ta ke bamu abinci mana,
Sai suka mike gaba daya zuwa taron mu suna faman yi muna sannu da zuwa,
Makullin dakina na,ciro daga cikin jakkana na mikawa Hamza wanda sai a lokacin ya kula da cewa banda lafiya ne,
Cikin tausayawa yake mun sannu yayin da sauran abokan shi suka fara yi min sannu suma tare da cewa anzo lafiya,

Tana zaune, a falo, cikin shigar wani dogon wandon jeans da wani bakin riga mai dogon hannu,,
Hamzs ya shigo gidan da sallaman shi, da sauri ya nufi part dina yana budewa,
Salawatu ta mike tsaye tana masa wani irin kallon rainin hankali, za tai magana ke nan na shigo gidan da Sallama na ,
Baki na ya sauke da addu,oin tsari kamar yadda kakana ya sanar dani,
Kallon mamaki take min don da farko bata gane ni ba sai da taga shigowan Yaya Abubakar yana cewa akai kaya a part dina,
Hamza ke daga kofa yana shiga da kayan cikin dakina,
A hankali na ina bude bakina ina ce mata ina wuni acikin muryana da yasa ta kara sandarewa, tsaye,
Ban san ko ta karba don ni wucewa nayi don in samu guri indan kwanta,
Hamza ke cewa barin fadawa Fattu cewa kin zo ba lafiya daidai lokacin da na shiga dakin,
Bai bata lokaci ba ya fita kiran Fattu a lokacin ne Yaya Abubaka ya shigo dakin nawa,
Gadon ba zani gado saman shi, sai dai katifa hakana kwanta sama ina jin wani irin amai na taso min,
Inna Allah Allah Yaya ya fita dakin in samu in shiga bayin dakin,
Ganin yana kokarin taba ni yasa ni mikewa da sauri har ina ture shi na fada bandakin
Amai nayi sosai sanan na samu sa,ida na wanke baki na da fuska na nafito dan kwalina a hannu,
Yaya yana tsaye daga kofan bayin ya tsura min ido cikin tsarguwa,
Yace Meenat har baki da lafiya haka kika bari mukabi wanan hanyan mai tsawo da ke,
Sallaman Fattu a kofan dakin shi ya dakatar dashi,
Yace mata bissimillah ko ?
Tashigo tana cewa Amarya ba lafiya kuma kukai wanan tafiya haka,
Dan dariyan yake nai mata nace a hanyane ciwon ya kamani ai,
Fita Yaya yayi zuwa gurin sauran matan shi yabar mu da Fattu,
Ita ce ta taimaka min da gyaran dakin take dakin ya koma neat, kamar bashi ba, takawo room Fresh ta fesa ko ina har bayi take guri ya dauki kamshi,
Anty Sadiya ce ta shigo da Sallamanta fuskanta ba yabo ba fallasa a cikin sa,
Ina zaune ina shan ruwan Lipton da Fattu tasa Hamza ya kawo min daga gidan su,
Acikin muryan nan nata kamar bata son magana tace, ,
Meenatu ba lafiya kuma ga tafiya, a hankali nace sannu Anty,
Tace yawa, kun zo lafiya ya mutanen gida ya karatu?
Na ansa da Alhamdullahi, daga inda Fattu take tana kokarin sa min trolls dina guri guda tacewa Anty Ina wuni Anty,?
A dasashe ta ansa wa Fattu ba a cikin dadin raiba,
Daga haka anty ta juya tana cewa Allah ya sauwa ka, muka karba mata fadin ameen,
Lafewa nayi saman gadon kamar may barci yayin da Fattu take zaunw daga gefe guda ta zura min ido,
Yaya Abubakar ya shigo dakin yana cewa in tashi mu tafi asibiti,
Badon naso ba muka tafi asibiti da shi, akai min alluran malaria da kuma kwayoyin sa akaba bani,
Da na dawo na samu Mama Bi,u tazo tana zaune a dakina don haka ranan tsohuwar mai mutunci itace ta kula dani,
Washe gari na tashi jikin nawa da sauki don muyi waya da Anty ina mata bayanin yadda jikin ya kasance min,
Ta tambayeni ko ya muka kwashe da Salawatu, sai da na ja tsaki nace ni tun shigowa na ban ganta ba ma har yau,
Kina nufin ba tazo dubaki ba ke nan na cewa Anty gaskiya hakane,
Share muna fuka kawai ki kama harkokin ki bakin ciki takeyi dake don may ki kazo,,
Kada ki yarda ki biyewa jikin ki ki mike kifara harkokin ki a cikin gida kamar kowa,,
Na amsa mata da to ร€nty na gode takara ce min kadafa kiji tsoron kowa ki dake kawai ki kama harkokinki na kara cewa to Anty nagode,
Muna gama wayan da Anty sai naji tankar tabani wani magani ne a jikina don sai kawai na mike tsaye, na shiga yan gyare gyare a dakina har zuwa dan corridor din sashe na,
Daga nan na fada kitchen don indan sa ruwan zafi wanda zan sha ruwan Lipton shayi,
Salawatu tana cikin kitchen din tana aiki wanda hakan ne yasani gane cewa, ita ce da girki a gidan,
Sallamu Alaikum na ce tare, cewa ina kwana lafiya kawai tabani ansa,
Direct gurin Gas din da ba bu komai a sama na nufa don in kunna wuta,,
Muryan Salawa naji daga baya na tana cewa, wanan dayan Gas din zan yi amfani dashi yanzu,
Amsa na bata a takaice da cewa ruwa kawai zan dafa sama,
Naci gaba da abinda nakeyi, sai dai bakina ya dauke da addu,an haduwa da muguwar kishiyya,
Komai na hada daga Lipton har kayan yaji a cikin ruwan har ya fara batun tafasa,
Muryan Yaya Abubakar naji daga baya na yana cewa,Sallawa har kin samu lafiyan fitowa hada girki,
Dan murmushin irin ta ma,ana na sake nace ba girki bane Yaya dan ruwan Lipton zan dan dafa da kayan yaji inzuba a flasks dina,
Ashe Salawa tana a bayan shi sai naji yana cewa bakin ce ta,tare maki gurin girki da nata girkin ba, ?
Batare da na kula suba tankar basu gurin najawo flasks dina a gaban shi na fara daurayewa tare da daukan dan soyoyon tace ruwan zafi, nafara tace ruwan a cikin flasks,
Ina jin lokacin da yaya ya juya yana cewa cikin murya kamar a zafi zuciya yace, bazan yarda da zaman fitina a gidana ba fa,
Idan ke baki sani ba su sun sani ai don na riga na fada masu, tun farko
So, Mind your self,,,
Sororo Salawatu tayi tabi bayan mijin su da kallo don ita ba haka tazo ba,
Daga in da nake tsaye na sake wani irin ajiyan zuciya,tare da numfasa,
Na kashe Gas din tare da dauraye tukunyar na zubar da kayan yajin a dustbin, din kitchen,,
Fitana daga kitchen din tabi bayan nawa nima da kallo har na bace mata ga gani,
Dakina na fada na aje flasks din a gefen mirror na,
Bakin gadona na zauna nafara tuna nen cewa ashe zancen Anty Amarya gaskiyane, na cewa sai nayi fama da kishin Salawatu,
Na mike tsaye ina cewa ashe akwai aiki kenan a gaba na bari kawai in murjewa wanan macen ido,
Abincin da yasa dokar cewa a tare za,a dinga ci sai naga ba,a kirani ci ba
Tunda nadan sha ruwan Lipton dina tare da magani na sai na samu guri na kwan ta don dama ina bukatan hutu,,

Sau kusan biyu Yaya Abubakar ya yana lekowa ya ga ko na farka daga barci, don yaji ko nasha magani na,
Wanan abin ya matukar bakan tawa Salawatu rai don tun zuwan ta gidan ta, tare komai tana nuna kamar ita ka dai ce matar gidan,,
Ita Anty Sadiya ko a jikinta, don ita har kan su baya gaban ta
Duk wani duniyan cin da Salawatu zatayi bai a gaban ta,
Hakan ke sa bata damu da fita waje ba don bata da lokacin su,
Ita ko Salawatu sai take gani kamar duk a cikin samun gurine hakan agareta,
Amma yau sai gashi kan yar karamar matar sa har yake ta zuwa da dawowa,

****** ********* ******
Driver yana shiga garin Birnin Kebbi bai tsaya ko ina ba sai kofan gidan malam ,
Abinda ya jawo hankalin al,umman uguwar ke nan zuwa kallon motan da ta tsaya kofar gidan tsohon,
Driver wanda ya fito ya nufi wurin da malam yake cikin rufan kofar gidan shi,
Babu abinda zaka hango sai farin gemun shi tun daga nesa,
Shima kansa malam din kallon mamaki ya kewa driver motan,
Sun gaisa da malam a cikin mutunci tare da taron hababa daga malam din har sauran mutanen dake gurin,
Mutumin ya dubi malam yace sako ne da Alh Abubakar na gidan nan,
Yace ina zo in,baka wanan sakon hannu da hannu ya mika masa envelope,
Kudi ne acikin envelope din da yar takarda, mutumin yace, yace wa yancan kayan aba Wadda ya rabawa kowa ga takarda wai a bashi,
Cikin mamaki malam yace a ina ka gan shi bawan Allah,
Yace Sokoto sun fito Niger da shi da matar sa, saboda bai samun zuwa shi da matar sa yaba da sakon akawo,
Take guri ya dauki zance cewa Abubakar ta turo wa iyayyen shi da abinci mota guda taf da kaya,
Baba Wadda aka nemo a cikin gari yazo da sauri inda ya fara fitar ma da kowa da nasa rabon,
Har zuwa makwabtan su da ya sa sunan su a cikin don sun zama tankar yan uwa,
Sai kuma kudin sabon mashi wanda za a saiwa Baba Buhari,,
Baba Wadda yaba kowa shadda da kudin dinkin da yaya Abubakar yace masu nice na sayo masu tsaraba a kasar Niger,
Haba gari ya dauki ciri cewa, Abubakar ya aiko wa iyayyen shi da sako,
Wasu ce ai yanzu ya daina daukan shawaran Mama Ladi ne,
Wasu suce ai saboda yanzu yana auren yar gida yasa yafara kula da gida, tau kowa dai yasan halin dan Adam,,,
Ranan Mama Ladi kamar zata kama da wuta don may zai yo sako bai fada mata ba sunyi shawara,
Ita Meenatu aiki takeyi da zata samu kudin sayen irin wanan kayan haka?
Sam baza ta yarda a mallake mata da ba

2 Comments On TARKO
avatar
maryam-2-4-2

1 year ago

Reply

Ya zanyi in karanta duka

avatar
maryam-2-4-2

1 year ago

Reply

Ya zanyi in karanta duka

Please Login or Register in order to submit comment