Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

4⃣2⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA


ALLAH-AL-LATEEF,,,,,

Assalamu Alaikun yan uwa musulmai, muji tsoron Allah ga al,amuran mu,
Mu daina yi wa Allah Ubangiji Izgili ga rayuwa kusani cewa,
Rahaman Annabin Rahama, Annabi Mohammed S,A,W itace muke samu a gurin Allah Ubangiji Subbahanahu,ta,ala,
Amma wai har shine mutum a zamanin nan zai san cewa ya aikata zunubi maigirma irin zunubin da, har wasu zamani saboda irin shi a juya wanan kasan tare da al,umman lokacin,
Yau sai gashi saboda samun guri har muna fitowa a fili mu ikirarin yin sa,
Wa,iyazubillah kuma a cijin diyan musulmai hausawa,
Ya Allah ka yafe muna kurakuran mu kasa mu mu,fi karfi zukatan mu
Ya Allah ka shiryar da duk kan Al,umman musulmi,
Ya Allah ka kare mu daga rudin shedan
Ya Allah kasa mugama da duniyar nan lafiya, πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘


Sayayya sosai nayi wa su, Anty Amarya da yaran ta harda ma Mummy da yaran ta,
Uncle dina tare da yaya Abubakar na sayo masu unders irin na maza masu kyau,
Tsab na shirya tare da hada kayan dakina wanda nasan cewa zasu yi min amfani gaba,
I zuwa yan,zu komai na hada don tafiya da safe kawai,,
Abinda nasan cewa idan na barshi a gidan yaya zai lalace na kwashe nakai wasu Fattu da Maman, Bi,u,
Sai murna su keyi da sa min albarka da fatan samun cigaba da nasara arayuwa,

A yadda na ke gani, kamar babu zancen yafiya na acikin wanan satin,
Allah, Allah naje yi kada yaya Abubakar ya ce min an fasa tafiya don,
Naga cewa bai kaunar zancen tafiyan nawa sam,
Sai zuwa dare na ya shigo dakin nawa ko ina yabi dakin da kallon mamaki irin yadda na parking din komai,
Murmushi naji yayi duk da fuskan shi yana a daure babu fara,a acikin ta,
Na kalle shi a cikin natsuwa ina mashi sannu da zuwa, a cikin murya mai sanyi, ba tare da ya ansa min ba,
Idanuwar shi ya zuba min zuwa wani lokaci sai yadan nisa,
Gefen gado na ya samu yadan zauna, tare da sauke ajiyar zuciya,
Meenatu naso ace na kaiki har Sokoto da kaina, sai dai gaskiya hakan bazai samu ba,
A hankali na dago kaina nadan kalli inda yake zaune cikin dan dafe kai da hannun shi,
Alamar ya na tare da gajiya a jikin shi,
Murmushi mai kama da yake na dan sake mai, ina cewa ai ba komai yaya,
Amma driver tare da malam Mudi zasu da matar shi zasu kaiki goben, insha Allah,
Ina fatan idan kin je zaki bawa Uncle da Anty Amarya hakkuri rashin zuwa na,
Kamar yadda nakara fada maki yau ma zan kara sheda maki,
Ki kula min da kan ki kirike amana na dake kan ki,,,,
A hankali na furta insha Allah,
Daga karshe yaya yace nai maki yan sayayya don kije dasu gidan uncle, saidai, basu da wani yawa sosai,
Har an riga ansa a motar da zaku tafi dashi gobe,
Godiya na kara yi mai tare da fatan alheri, kudi ya kara cirowa daga cikin aljihun shi ya turo min a gabana yana, ce min kirike don yin amfanin ki,
Da sauri na kalle shi ina cewa yaya da akwai kudi fa a hannu na har yanzu,
Kai yagyada yanacewa nasa, ai amma kuma kin san yanzu ba da bane ko?
Do ajwai bambanci garayun ki nada dana yanzu,
So ki aje agurin ki don tare lalura ba sai uncle yayi maki ba,
Ya mike tsaye yana cewa idan kinje ina gaida uncle da matar shi,
Murya nane kawai zai isar da sakon da zuciya na ke ciki a lokacin,
Don wani iri naji saboda rabuwan da zamuyi da yayana bayan dan sabon da mu kayi na dan lokaci,,
Yana fita bayan tafiyan shi na adana kudin da ya bani, don tafiya, na,
Mikewa nayi zuwa sashen Anty Sadiya don in sheda mata cewa zan koma, gobe,,,
Na samay ta a zaune tana gyaran yatsun kafan ta a dakin ta,
Sallamana da ta ji ya sata dago kai fuska a daure, ba fara,a ko ka dan,,
Wani irin kallon kurulla naga tana min badon komai ba sai irin yadda gyaran jikin da nayi ya maidani, a lokaci guda,,,
Gaishe ta nayi a daure ta amsa min a cikin da matse fuska, kadan,
Anty nazo in sheda maki cewa, gobe zan koma insha Allah,
Dan sasauta fuskan ta tayi tana cewa, gobe goben nan, za,a tafi, ?
Sai da na,dan yi kamar zan wuce saina ce anty don Allah ki yafe, min,
Acikin muryan nan nata maikama da agajiye take tace min,
Allah ya yafe muna baki daya na ansa da Ameen nabar dakin,
Bina tayi da kallon mamaki yadda cikin da lokaci taga na wani canza mata ,
Take wani irin kishi ya turnuke mata zuciya don sam bata san har yaushe na zama haka ba,,

****** ********* ******

Sanmako mu kayi kamar yadda yaya Abubakar ya umurce ni da yi,
Motar hilux, ce ni da Maman Hanifa zaune abaya,
Maigidan ta malam mudi wanda a yanzu yake na hannun daman yaya Abubakar, zaune tare da driver a gaban motar
Driver wani yare ne don inaganin baya jin hausa sai turancin yan Lagos su,keyi da malam Mudi,
Yadda yaya ya basu Umurni a ranan zasu dawo Abuja, kada su kwana wai su kai muna dawainiya,
Tafiya ya fara ni sa inda kewar mijina da kuma kaunar shi ya fara min yawo azuciya,
Sai yanzu nasan cewa mun dan shaku da yayana Abubakar, a dan zaman da mukayi,
Yanzu na gane cewa kada ka fadi halin mutum muddin baka zauna dashi ba,
Ada kallon mugu wanda baya da lokacin kowa, na ke,wa yaya Abubakar,
Amma dan zaman da na,yi dashi yasa na,gane cewa
Rashin sani ki shi waye yasa na ke mai itin wanan fassaran, da nai mai,,,
Abinda ya zo min a zuciya shi ne yadda mutane ke ganin cewa bazan taba samun guri a cikin zuciyad yaya Abubakar ba,
Ni kai,na nai tunane irin yadda zan zauna dashi a matsayin mijina,
Mutum gogage abin shawa da kyau gani ace wai nice matar shi,
Wanan irin tunanen ne nai tayi lokacin da malam yace wai ya daura min aure da yaya Abubakar,,
Mama Ladi ce tafado min a rai har nakai ga lumshe idona, a hankali,
Don ban san yaya zasu kwashe da dan nata ba zuwa yanzu,
Haka nai ta tunane barkatai a hanya tare da dan lumshe ido na
Acikin ikon Allah mun iso garin sokoto, da wuri sakamakon gudun da driver yai ta shararawa,da mu,,,
Da kwatance nai ta ma su nuni da hanyar uguwar mu har zuwa gidan Uncle dina,
Taka injin din motan da karfi driver yayi alaman cewa mun iso,
Da guda yaran gidan Uncle su ka fito azaton su ko, Baban su ne,
Gaba daya suka sa ihu da Eh Anty Meenat, Anty Meena,
Abinda ya jawo hankalin iyayyen su daga cikin gida ke nan,,
Da sauri Anty Amarya tafito hanyar shigowa cikin gidan ,
Inda mu kayi karo da ita rugumay juna mu kayi da yar ihun mu,,
Sai kuma ta sakeni tana min wani irin kallon mamaki,
Kunyane ya kamani nadan noke kaina acikin hannaye na,
Muryan Maman Hanifa, ce ke gaida Anty daga bayan mu ,
Sai kuma hankalin mu ya koma gare ta cikin mamaki Anty Amarya ke kallon maman Hanifa, don bata san ta ba,
Nan nai mata bayanin ko wace ita yayin da muke shiga gida,
Kayana aka dinga jidowa ana shiga dasu sashen Anty Amarya,
Sosai annuna minnkauna agidan uncle don ranan har da mummy cikin zuwa taro na sashen Anty na,,
Abinci aka zuba wa su malam Mudi, da driver da ya kawo mu
Ita kuma Maman Hanifa a tare aka zubo muna mukaci,
A falon anty ta kira ni nan naga irin kayan da yaya ya jib go muna,
Buhun shimkafane da jarkan manja da mangyada su taliya, da indomie, da su sweet, da sauran tarkace,
Su malam mudi ba suyi wani dadewa ba suka kama hanya don gudun kada dare yai masu a hanya,,
Abinda na bashi da kyat ya karba amna na nuna mashi banji dadin rashin ansan abin ba dole suka karba shi da driver,
Maman Hanifa, Ita ma na bata nata rabon, da,kuma wasu kayan jikina kala biyu, tana ta zabga godiya,

****** ********* ******
Tunda ya dawo sai yake ganin gidan tankar ba kowa acikin shi,
Yadda na tafi nabar shi da safe , shima yafita zuwa office haka yadawo ya samay shi,
Yadan dade tsaye a tsakar falo yana kallon kofan shiga daki na,
Kamar ya nufi can sai kuma ya juya zuwa, hawa saman part din shi,
Har ya gama abinda yakeyi ya fito, ba motsin Sadiya, a falon,
Alama ya nunamai cewa bazata girka masu komai ba ke nan yau,
A fusace ya nufi dakin ta tana tsaye tana kokarin gyara gadon ta da,ya cikwikkuykuye,
Bata iya ce masa sanun da zuwa, ba sa kawai tana kokarin ci gaba da abinda takeyi,
Haushine ya kama yaya Abubakar mace kamar tunkiya,
Bata san yakamata ba da bai kamata ba,
Gefen mirror ta inda yadan saba tsayawa idan zai mata magana don ya jingina jikin shi,,
Sadiya tadago ido ta kalleshi don jin yadda ya ambaci sunan ta,
Ita azaton ta ya zo ne neman wani abu agurin ta don yaga yau ita kadai ce a gida,
Tambayan da yai matane yasa ta saurin dago kai ta dan dube shi,
Sadiya may kike nufi da rashin dafa muna abinci, da baki da niyan yi,
Abinci zan dafa kuma kace bai yi kyau ba,?
Idan nace bai yi kyau ba basai ki gyara ba ki koya ko zaki yi mai kyau,
Gaskiya kada kace zaka kawo min wanan tun wuri bazan iya ba ni,
Aiko dole ki iya don ba mai zama yana dafawa ki na ci,,
Bari kiji in har kin samu Meenatu yarinya ce ko kuma tana yi maki a matsayin ta na yar uwar mu,,
Wace zata zo gidan nan yanzu nasan ba zata daukan maki wanan akidar ba,
Idan kace kar ta bani ko,
Da mamaki ya kalle ta yace wai ko Sadiya kina da hankali kuwa ?
Ki tashi ki fita ki girka muna abinda zamuci na dare,
Kuma barin fada maki daga yau, bazan kara sayo maki take away ba agidan nan,
Sai dai mu zauna ahaka idan ba za ki yi ba,
Gani fuskan shi ba wasa yasa ta biyo bayan shi, don zuwa ta dafa masu abincin,
Idomie ne ta dafa masu sai dai yayi yaji da yawa don bazai ciyu, bΓ  sam,
Dole drinks ya dan kara korawa sama ya samu guri ya kwanta,
Zuciyar shi cunkushe da bakin ciki, don ya rasa may ke mashi dadi a ran shi,
Shawara yake tayi akan yadda zai bullo ma wanan al,amarin na Sadiya,,,
Ace, mace kamar Sadiya bata,san yadda zata tafiyar da gidan ta ba,,
Amma wai har yarinya kamar Meenatu tasan yadda zata tafiyar da rayuwan shi acikin jin dadi batare da wani matsuwa ba,
Dasafe ma ruwan tea kawai da burodi ta tanadar mashi,
Irin abincin da nake muna na karyaw ne ya fado mashi arai,,
Gefen da take zaune tana faman loda bread a cikin ya ya kalla yana cewa
Harara yafara sakr mata sannan yace wai ke,
Ko Irish din baki yiya soyaba ke nan Sadiya sadiya kiwa kan ki fada fa,,
Wani jutar da kai tayi gefe guda kamar wace akai wa wani zance na daban,
Tsaki ya ja tare da mikewa tsaye idon shi duk sun kada,, yana cewa kada kiga kamar kin min ne,
Ya ce sam kan ki kiyiwa, do ke, ce zaki sha wuya nan gaba,,
Daga haka yasa kai yabar gidan zuwa office abinshi,,,,

****** ********* ******
Falon yai shiru duk da yake dai sanyi safiyane, Uncle dina ne azaune,
Tare da matan shi dukka kan su biyu, kayan da nazo da su ne zube a gefe gudan falon,
Uncle ya kara min sannu da zuwa yaku ma tambayen ni akan kayan da nazo da su,
Kamar yadda yaya Abubakar yai min baya haka na fadawa uncle dina,
Shiru yayi zuwa wani dan lokaci, can yace cikin wata murya mai sanyi,
Gaskiya banji dadin abinda Abubakar yai min ba,
Ada dakike gidana shike bani abinda zan ciyar da ke ne ?
Anty Amarya ce ta tare zancen da ce,
Haba dai dear ba haka yake nufi ba ,
Idan har ka lura shi aganin shi ai yanzu yana da hakki akan Meenatu kuma nasan yana ganin hakan zai yi ya fitar da nauyin ta dake kan shi,
Mummy ma tace nima dai abinda nagani ke nan ai,
Uncle ya dan furza da iska may sanyi daga bakin shi yana cewa,
Yanzu abinda za,a wanan shinkafa duk biyu zan turawa mahaifan ki suyi amfani dashi,
Mai kuma sai ku diba ku bada saura akai masu Saratu,
Zanyi magana Uncle yace min yadda ya ce haka za, ayi, da kayan dole na kyake ina kallo aka hada komai ya fita dasu zuwa tasha don ya turawa iyayye na,
Sauran tsaraban da na sayo masu, naraba nabawa kowa nashi
Atake gida ya rude da murna don kowa nasayo mai tsaraba mai muhinmanci,
Sai da mukaxkoma daki ne nakara fitar wa da anty amarya da yaranta wasu tsaraban da na sayo masu na daban,
Tsaye Anty Amarya take amma sai ta janyo, dan stol din mirror dakin ta zauna,
Tana yi min wani irin duba nason jin bayani daga baki na,
Kunya ne ya kamani amma sai na daure nake fada mata irin alherin da yaya Abubakar yai min a lokacin zamana dashi,
Allah mungode ma Anty Amarya tace tare da daga hannun ta sama ta shafa a jikin ta,
Meenatu takira suna na a hankali ,
Nasan cewa abu mai muhinmanci zata fada don haka na ansa mata da murya kasa,kasa,
Tace da farko na tsorata ainun da auren ki da mutumin nan,
Ga irin yadda nai ta jin labarin shi da kuma uwar shi,
Gama kuma da nagan shi a fili sai na kara tsunkewa da al,amarin sa,,
Amma kin ga abin Allah sai gashi duk zaton mu ba haka bane ashe,
Don haka yanzu abinda nake so dake ahine ki kara zage damtse gurin dankr mijin ki,
Yadda ba wata macen da zata iya shige maki gaba da komai,
Kin san dai yadda makiya sukayi wa auren ku yawa, don haka kara daurewa zakiyi kibawa marada kunya,
Na amsa da cewa insha Allah Anty, zan yi duk yadda kika ce din
Nan muka dan dauka n zama Abuja tare da yadda na hadu da Fattu da Uwar mijin ta,
Sai Monday na fara fita school sai da ban manta da maganan da yaya Abubakar yai min ba,
Akan in kula da rayuwata, bakomai yake nufi da hakan sai in tsare mutuncin kai na,
Wanda dama ni Allah ya rufa min asiri ban da wanan irin rayuwan,
Don ni ko kawa ban yarda da yi ba,a makaranta,
Abinda yakai ni shine nasa wa gabana don haka yanzu ma ba wasa don wani katon hijab baki na zumbuda ajikina wanda ya rufe min ko ina nawa,

Sakon Uncle dina ya samu isa gurin iyayyena wanda mutane na ta mamaki daga ina wanan kayan ya fito haka ?
Sai gulma akeyi ako, wani sashe, na gidan mu inda abin yadan yi sauki dan gidan Baba Shaibu da yaraka yayana Ibrahim gurin dauko kayan a tashar mota,
Shike fada masu cewa,daga gurin Kanin Mama Saratu sakon ya fito,
Hakan yasa zancen yadan lafa,
Bayan dawowan Baba na gida yasau sakon kayan da Uncle ya turo mai dasu,
Kwana biyar biyar,aka debawa ko wani sashe tare da zuba masu manjan a wani kwano,
Sai shigowa sukeyi zuwa godiya mazan su da matan su,
Wasu kuma na cewa, ta inda ake zaton abin ya fito sai gashi bai fito ta gurin ba,,,

Zaune matan gidan suke suna zancen abin duniyar dake gudana musanman a gidan su,
Matar Baba Shaibu ce ta fara cewa, ita waccan may, bakin cikin,
Ta,na nan dan tana can na wa duniya, yayafin arzikin shi,
Sai matan Baba musa take cewa ai, ko bakin cikin ta ita zaici don dai a yadda malam ke fadi,
Yanzu wani irin daula ne na arziki ya taso mashi amma nan gashi tare tako ina kada wani yaje ya lakato,
Matar Baba Hamza tace, aiko zata sha mamaki nan gaba don muddin yarinyar nan ta kara nan gaba bazata iya tare ta,ba,
Ai dai gamu gani inda rayuwar mu zamu sha kallo a gidan nan,
Baki gani yadda Saratu ta canza cikin kwanakin nan sai wani sheki takeyi kamar mai sabon ciki,
Wace tafara maganar tace, to ita kan ta mama Ladin, ai a wahalce take,,
Ace wai danka nada hali irin na mama ladi amma daki ko gurin zama babu ballr shimfidar kwarai,
To wai ku kuna mamakine baku gani gidan ga kowace mace dan uwan ta na zuwa amma ban da dangin mama ladi,
Duk tabi ta kakabe su, ba mai zuwa gurin ta saboda mugun hali,
Yanzu ai Hajja ce dangin nata inji matar Baba musa,
Dagin sheri ba tunda mugun abin su iri guda,ne ai shiyasa nasu yazo daya,,

****** ********** ******
A kwance yake saman gadon dakin shi sanyi AC kawai ke tashi a dakin, sai faman juyi ya keyi
Daga inda yake kwance ne yake kallon yadda dakin ya hargitse babu gyara, tun bayan tafiyan Meenatu wace ke gyara mashi, a kullun take da girki
Gyara kwanci ya kara yi rigingine sanyin na ratsa mai jikin shi,
Kewar matarshi ne kawai ke damun shi don sai yanzu ne ya san cewa sun shaku da yariyan fiye da tsan manin shi,
Gyara kwanciyar shi yayi don cigaba da tunanen shi,
Idon shi ya lumshe saboda tuna abubuwa da dama akan ta,
Tarbiya, tsabta, girki, iya soyayya cikin dabara, take tafiyar da komai,
Wayan shi dake gefen shi, ya lalabo, tare da neman laban wayan ta,
Kira yake wayar kamar zata katse, sai yaji na dauka acikin siririyar muryan nan tawa,
Wani irin sanyi yaya Abubakar yaji ya ratsa zuciyar shi saboda jin murya na da yayi kawai,
Jin muryan kawai ya jefa shi ackin wani irin nishadi a lokaci guda,
A hankali nace ina wuni yaya ?
Lumshe idon shi yayi Γ§ikin wani irin ya na yin jin dadi,
Ya gajiyan aiki yaya?
Da kyat ya iya tataro natsuwar shi guri guda ya amsa min da cewa,
Tau da sauki dai,
Acikin damuwa nace da sauri lafiya kuwa yaya,?
Sai da yadan nisa yace ina fa lafiya Kaunar yaya kin wuce kin bar yaya acikin tunane da kewar ki,
Kunya maganar tashi taba har nadan sake murmushin jindadi ta yadda zai iya jina a inda yake,
Hakan yasa yaya Abubakar lumshe idon shi a hankali saboda wani irin abu dake fisgan shi
,

ZEEE MAKAWA YELWA
[8/4, 21:37] Anty Lantana: πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈTARKOπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
πŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•ΈπŸ•Έ
4⃣3⃣

ZAINAB IDRIS MAKAWA


ALLAH- AL- KHABEER


Jiki da jini yau Allah da ikon shi an wayi gari Mama Ladi ba lafiya,
Tun safe Mama Ladi ta kasa koda fitowa kofan dakin ta,
Ganin irin yadda jikin ya matsa mata Mama, Sa,a wace Mama ladi ke ji tankar ta shaketa kowa ya huta,,
Itace taji shiru Mama Ladi bata leko ba kuma bata motsin ta ba a sashen ta,
Don haka ta daure ta zagayo zuwa sashen mama Ladi din,
Kwance ta samay ta acikin wani irin yanayi mai ban tausayi,
Ta,yi amai duk jikin ta ya baci ko ina da aman, ga wari dakin kamar may,
Da sauri ta karasa gurin Mama Lafin wace ke kwance cikin mawuyacin hali,
Ganin dai abin bana wasa bane yasa ta komawa da sauri zuwa kiran maigidan su wanda ke waje gurin mahaifin shi suna karatu,
Dan aike na fada mashi bai bata lokaci ba ya garzayo zuwa ciin gida,
Da shi da Mama Sa,a ne suka gyara,mata jikin ta suka canza mata sutura,
Da sauri Mama Sa,adatu ta, tada yaro yaje gidaje da yaran ta su ke aure ya fada masu halin da mahaifiyar su ke ciki yau,
Ba bata lokaci sai gasu gabadayan su suncika gida,
Hankalin kowa a tashe yake ganin irin yadda jikin ya matsawa, Mama Ladi,
Samira ce ta dauki waya ta bugawa yayan su Abubakar ,
Nan ta ke sheda mashi irin halin da mahaifiyar su ke ciki tun safe,
Waya yakira abokin shi Aliyu dake cikin Birnin Kebbi da yazo ta kai ta asibiti,
Gado aka bawa Mama Ladi don ciwon yai mata tsanani, sosai,
Mama Saratu itace ta farko aika masu da abinci asibitin,,
Inda sauran mutanen gidan ba wanda ya kai mata komai, don sunce ko ciwo su keyi sai Mama ta ga dama take zuwa gaida kai, balle ma idan yaron kane baida lafiya,,
Wanan dalilin suka rike yau su ma suka ce sai sun rama,
Babana Samaila shine yazo da motar shi yace duk wace zata gaida ita tazo ta shiga su tafi,
Wanan daman yasa matan gidan namu zuwa shiga mota don suje suyo gulma,
A kai akai yaya Abubakar ke bugo waya ranan don jin ya karfin jikin mahaifiyar nasu,
Andai tabbatar mai da cewa i yanzu ta dan samu sauki sai dai tana jin jikin har yanzu,
Wanan zancen ne yasa yaya Abubakar, shiryawa zuwa kebbi dan ganin halin da mahaifiyar shi take aciki,bai tsaya wani shiri, washe gari ya kama hanya,
Saboda yazo ya ganewa idon shi halin da mama take aciki idan ya kama a tafi da ita, Abuja ne gurin su sai ya wuce da ita,,,

****** ********* ******
Fitowa na daga lectures ke nan gurin da, nake yawan zama kusa da school mosque, na zauna ina jiran lokacin sallah azahar, yayi,
Wayana dake acikin jakata ke ringing alamar kira ya shigo min,
Ganin mai kiran nawa cikin wanan lokacin ne ya bani mamaki,
Nomban yaya Abubakar ne kiran yai matukar ba ni mamaki sosai don baya kirana da rana sau dadare lokacin da yasan cewa ina free,
Bayan na dauka mun gaisa yake sheda min cewa yana hanya ya kusa shigowa sokoto, zai tafi Birnin kebbi,
A hankali na ke tambayan shi ko lafiya zai

2 Comments On TARKO
avatar
maryam-2-4-2

1 year ago

Reply

Ya zanyi in karanta duka

avatar
maryam-2-4-2

1 year ago

Reply

Ya zanyi in karanta duka

Please Login or Register in order to submit comment