Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsaron jirgin
Dajin haka sai gimbiya walisa tayi tsaki sannan tace
Wato ke kina nufin ke kadai zaki iya bamu kulawa akan dukkan abindaya doso mu?
Dajin haka sai marfuza tayi murmushi tace kwarai kuwa maganarki gaskiya ce don haka sai ki zuba ido ki gani
Tana. Gama fadin haka sai ta juya musu baya taci gaba da aikinta
Su kuwa su sarki aryan sai suka shiga daki suka fito da kayan abincinsu suka ci suka koshi
Suna gama cin abincin sai sarki aryan ya dauki kwano guda daya ya hau saman inda marfuza take ya mika mata kwanon abincin yace
Gashi nan kema kici domin na tabbatar da cewa kema kina da bukatar sa
Cikin farin ciki marfuza tasa hannuwanta ta karbi kwanon fuskarta cike da murmushi
Bisa ganin yadda sarki aryan ya nuna kulawarsa agareta
Tace yakai wannan sarki mai daraja ina matukar godiya agareka
Amma inda son raina ne da nice zanzo na karba da kaina ba sai ja taso ba
Dajin haka sai ya dora hannunsa guda biyu akan kafadumta a wannan lokaci taji wani irin yanayi ya ratsa mata kwakwalwar ta
Yace ai bai kamata ba mu ci abinci mu cika cikinmu ba alhalin ke kina nan domin tsaron lafiyar mu ba
Don haka yanzu ke sai ki sauka kici naki abincin ni kuma na ci gaba da aikin da kikeyi
Cikin murmushi tace ai shi kenan, kawai sai ta mike tsaye taka matattakala ta sauko
Shi kuma sarki aryan sai ya canjeta ya zauna akan kujerar da take zaune shima
Ya ci gaba da aikin da takeyi, ita kuwa marfuza tana sauka kasa
Sai ta wuce inda gimbiya walisa take itama ta sami guri ta zauna
Tana mai fuskantar gimbiya walisa suna cin abinci suna hira abinsu kamar wadanda suke zaune acikin gidansu
Suna cikin hirar ne gimbiya walisa tace da marfuza yanzu ya kike ganin zamu tsara wannan tafiyar tamu tunda dai yanzu dare ya soma yi kuma kema kinsan ba zamu kwanta barci gabaki dayanmu ba?
Dajin wannan tambaya sai marfuza tace kwarai kuwa maganarki gaskiya ce
Amma ni ina da wata shawara guda daya shawarar kuwa itace
Ni dake zamu sami guri mu kwanta muyi barci koda na sa'a biyune sarki aryan yayi gadin mu tsawon lokacin da zamu dauka

Sannan mu tashi sarki aryan shima sarki aryan yazo ya samu yayi nasa barcin kamar yadda mukayi
Da zarar ya farka sai dukkan mu mu tashi mu ci gaba da tafiyar da mukeyi acikin daren nan
Ba tareda gardama ba walisa ta yarda da shawarar data bata
Don haka daga inda take zaune ta kwallawa sarki aryan kira ta sanar dashi shawarar da marfuza ta bayar shima ya yarda
Sannan suka samu guri suka kwanta kwanciyarsu keda wuya sai barci ya daukesu
Kamar yadda suka tsara haka al'amarin ya kasance
Suna yin sa'a biyu sai suka farka shima sarki aryan ya kwanta abinsa
Shima bayan sa'a biyu nayi ya farka sannan suka kunna fitilun itatuwa masu yawa wadanda zasu dinga haska musu hanya
Sarki aryan ya koma can saman jirgin ya tsaya cak shima domin tabbatar da tsaro
Su kuma su walisa sai suka kama hanya matukan jirgin suka fara aikin turashi gaba da damatsansu
Nanfa jirgin yaci gaba da tura su gaba suna kara kutsawa cikin tekun

WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GASU GIMBIYA WALISA
BAYAN SUN SAMI NASARAR KASHE ALJANI DARGATUL AMNAR KUMA SUN SHIGA CIKIN JIRGI DOMIN YA KETARE DASU TA CIKIN TEKU

***** ******* ******

Acan fadar da yarima walisu ke zaune kuwa
Lokacin daya umarci aljani dargatul amnar dayaje hanya ya tari su gimbiya walisa ya kashe su
Sai ya sami guri ya zauna akan kujerar tsafinsa yana mai fuskantar wani sundukin tsafinsa idanunsa a rufe yana mai nazari acikin zuciyarsa
A wannan lokaci gaba daya iliminsa na tsafi ya zuba akan sundukin nasa
Hannunsa na hagu kuwa ya runtse shi gam na damar kuma yana ruke da izgar tsafi yana mai bincike acikin hallararsa ta tsafi
Tsawon lokaci mai tsawo yana mai yin bincike a cikin tsafin nasa
Sai daya shafe wasu sa'o'i yana yin binciken sannan ya dago da kansa alokacin da gaba daya jikinsa ya jike da gumi sharkaf kamar wanda yayi wanka acikin kogi
Kallo daya zaka yi masa kasan cewa yana cikin tashin hankali
Ba komai ya gani a cikin binciken nasa ba face
An tabbatar masa da cewa tuni sadauki HASSANUL BASARI
Ya dade da mutuwa amma duk da haka akwai sauran gagarumin aiki a gabansa
Domin su gimbiya walisa sun karbi addinin musulunci
Har ma sun mallaki makamin hassanul basari
Wannan shine abindaya daga masa hankali bisa ganin su walisa sun sami kwakkwarar kariya wacce zata hanashi tasiri agaresu
Don haka sai ya shafi madubin tsafinsa don yaga abindaya faru tsakaninsa sa da su
Aikuwa saiga hoton aljani dargatul amnar ya bayyana ajikin madubin lokacin da yake tsala gudu domin ya gaggauta zuwa ya riskesu
Har dama fafarawar da sukayi a karshe suka sami nasara akansa
Tun kafin ya gama ganin wannan al'amari sai fusakarsa ta fara gyatsine
Da sauya launi don haka bai san sanda yasa hannunsa ya daki madubin tsafin dashi ba
Take kuwa madubin tsafin yayi bindiga ya tarwatse kamar nikakken gari
Sannan yaja gwauron numfashi daga can kuma sai yace
Lallai wadannan kananun yaran sun jawa kansu yanzu dolene
Nima na koma can bangon duniya gurin gunki larazub domin dama na ajiye ta ne domin irin wannan rana
Yana gama fadin haka kuwa sai take yayi girgiza ya rikide ya koma siririn haske
Sannan hasken ya ratsa ta cikin rufin fadar kamar giftawar tauraruwa mai wutsiya
Abinka da babban shu'umi ai kuwa cikin dakiku kadan ya isa can bagon duniya
inda adaidai gurin da ya sauka akwai wata tsohuwar rijiya hakar mutanen farko
Fadin bakin rijiyar kadai yakai fadin zira'i ashirin a saman rijiyar anyi mata murfi da wani murtukeken bakin karfe
Mai fadi da kuma girman gaske wanda inda za'a tara kattin aljanu majiya karfi guda hamsin ba zasu iya janye shi ba saboda nauyin da yake dashi
Itadai wannan rijiya guri ne mai matukar tarihi.
Domin tun farkon duniya aka samar da wannan rijiya
Inda Ita din ta kasance kamar cibiyace ta kirkirar tsatsuba
A sali wadansu shu'uman bokaye wadanda tun farkon duniya sune suka fara kirkirar tsatsuba
A wannan lokaci babu wanda yasan tsafi a duniya su wadannan bokaye sune a cikin binciken su suka fara gano dalasiman tsafi da kuma yadda ake amfani dasu
Tun daga wannan lokaci sai suka saka wadansu dakarun aljanu
Akan su haka musu wannan rijiya domin ta zamo cibiyar tsatsuba ta duniya baki daya
Su kansu wadannan aljanu sai da suka shafe kwanaki masu yawa suna hakar wannan rijiya da kuma kera murfinta
Tun da wadannan bokaye suka shiga cikin wannan rijiya babu abinda sukeyi face dada zurfafawa acikin ilimin tsafi
Daga karshe sai suka sana'anta wani babban gunki da zallan lu'u lu'u
Suka sihirce shi ta yadda zai dingayin duk wasu aikace aikace da mutum zaiyi
Kamar tafiya, motsi, magana da dai sauransu
Kuma sihirin nasu ya tabbatar musu da cewa dolene su mai da gunkin abin bautarsu
Haka kuwa akayi kullum babu aikin da sukeyi face bincike da kuma bautawa wannan gunkin

Ana cikin wannan hali wata rana aka sami sabani kan su wadannan bokaye sun dukufa wajen aikin bokancinsu
Har lokacin bautar gunki larazub yayi ba tare da sunje sun bauta masa ba
Jin haushin wannan al'amari ne yasa gunk larazub
Yayi amfani da nasa sihirin wajen hallakar dasu gaba daya
ana cikin rijiyar gawarwakin wadannan bokaye suka rube tsutsotsi suka cinye tsokar jikinsu ya zamana saura kwarangwal din jikinsu
Tun daga wannan rana wannan gunki ya kasance shi kadai acikin wannan rijiya

Lokacin da yarima walisu ya sauka abakin wannan tsohuwar rijiya
Sai ya dora tafin hannunsa akan rijiyar tareda tareda dauko wata 'yar karamar jemammiyar fata wacce akayi wani irin rubutu cikin yaren tsafi
Yana fiddo da wannan jemammiyar fatar sai ya budeta ya karanta abinda yake rubuce ajikinta
Take wani irin tiririn hayaki ya fito daga jikin takardar ya sauka ajikin murfin da aka rufe rijiyar dashi
sai gashi hasken ya ratsa ta jikin wannan murfi kamar yadda haske yake ratsa duhu
nantake wannan murfin ya zama kamar haske kawai shikuma yarima walisu sai ya tashi sama kan iska ys dulmiyar da kansa kasan rijiyar
Sai gashi shima ya ratsa wannan hasken ya shige cikin wannan rijiyar
Ita kanta wannan rijiyar ta cika mai zurfin gaske domin bazan iya sanar daku irin zurfin da take dashi ba abin dai sai wanda ya gani
sai gashi yana zabga gudu acikin iska a yayin da yake kara nutsewa acikin rijiyar
Sai da yayi tafiya mai tsawo aciki saboda zurfinta sannan ya isa karshenta
shi kansa kasan wannan rijiya yana da matukar fadi domin yakai girman wani karamin garin kuma komai na bukata a rayuwar duniya akwaishi aciki

Yana dira bisa turba sai ya fara tafiya bisa kafafunsa har ya isa bakin wata 'yar karamar fada
Wacce a karshenta gunki larazub ne a tsaye
Koda ya isa daidai wannan guri sai take wani haske ya fita daga jikin yarima walisu
Shi kuma yarima walisun sai ya sulale kasa sumamme saboda wata irin matananciyar kasala da yaji ajikinsa
Ba komai bane wannan hasken ba face ruhin boka sahibul ukub ne ya fita kamar yadda ya shiga jikinsa a baya
Kai tsaye ruhin ya tafi inda gunki yumatuna ke tsaye cikin sauri yana zuwa sai ya zube gwuiwoyinsa a kasa domin girmamawa
Daga can kuma sai ya dago da kansa ya dubi gunki larazub da nufin yayi masa bayanin abinda ke faruwa

Kawai sai yaga ya tuntsure da wata mahaukaciyar dariya
Mai kama da kukan jaki, daga can kuma sai ya tsuke bakinsa ga barin dariyar yace

Lale marhaban da babban hadimi na a doron kasa kuma inayi maka barka da dawowa cikin fadata
Ka sani cewa ina sane da duk bukatar daka zo da ita
Ka sani cewa saboda irin haka ne ya sanya a baya na sihirce maka ruhinka
Ta yadda koda ka mutu zaka iya dawowa bayan dubunnan shekaru
Ba don haka ba da tuni an manta da shafinka
Don haka dolene ka zama mutum na daban acikin mutane wanda ba'a taba yin wanda yayi tsawon rai kamarsa ba
To ka sani cewa yanzu kuskurenka daya ne. Abaya shine na barin gimbiya walisa a baya tun karon farko da kukayi da ita
Duk da nasan cewa ba laifinka bane ba
Ba komai bane ya hanaka kasheta ba face wannan saurayin
Kawai sai yayi nuni da hannunsa zuwa kan yarima walisu wanda yake kwance a kasa magashiyan
Yace ka sani cewa ba komaine yasa kaki kashe gimbiya walisa ba tun abaya face jinin jikinta dana sa guda daya ne
Tunda tare aka haifesu kuma nono daya suka sha don haka akwai shakuwa mai tsanani atsakaninsu ta yadda koda baya cikin hayyacinsa ba zai iya kasheta ba tunda jininsa ce
Amma duk da haka. Ayanzu ya zame maka tilas kota halin kaka ka kashe su gimbiya
Domin kare martabarka da kuma tarihinka, ni yanzu burina guda dayane
Shine na ganka ka zama sarkin sarakai ta yadda duk mutane, da aljanu na duniya zasu mai da kai amatsayin ubangijin su
Kai kuma idan suka bauta maka sai ka zo nan fadar tawa kaima ka bauta mini
Wannan itace kadai bukatata agareka
Idan har kanason wannan buri naka ya cika dolene sai ka mike tsaye da dukkan karfinka
Domin yanzu suma su walisa sun sami kariya mai karfi
Bayan haka zan gargadeka da kada ka kuskura bayan mun rabu ka fita daga jikin walisu ko sau daya
Domin da shine kadai zaka cika burinka kuma da zarar kun sake ido biyu da walisa ka gaggauta kasheta
Koda jin wannan bayanin sai sahibul ukub ya dubeshi yace
Yakai yakai shugaban duk wata tsatsuba ka sani dolene zanyi duk abubuwan daka fada
Amma yanzu ina so ka dawo mini da sandar tsafi na wacce na fafata yaki da SADAUKI HASSANUL BASARI abaya
Bayan haka inaso ka kara mini sihiri mai karfi fiye da wanda nake dashi a yanzu
Dajin haka sai larazub yayi wani guntun murmushi sannan ya kalli tsakiya kan boka sahibul ukub
Take wani irin siririn jan haske ya fito daga cikin idanunsa ya ratsa cikin kansa
Sannan kuma ya daga hannunsa sama take sandar tsafin boka sahibul ukub ta bayyana
Kawai sai ya mika masa wannan sandar
Yana karba sai shi kuma gunki larazub ya bace bat daga kogon sahibul ukub ya daina ganinsa
Kawai sai yaji muryar larazub yana cewa yanzu sai ka tafi cika aikin da yake gabanka
Domin kai dodone kuma mai zamani biyu
Dajin haka sai ruhin sahibul ukub ya tashi ya tashi tsaye ya koma inda yarima walisu ke kwance
Ya sake komawa jikinsa, take kuwa yarima walisu ya mike tsaye ya sake tashi sama ya fice daga cikin rijiyar kamar yadda ya shigo hannunsa ruke da tsohuwar sandar sihirinsa
Yana fitowa daga cikin kogon sai take murfin rijiyar ya koma ya rufe kansa kamar yadda yake abaya
Kai tsaye ya kama hanyar komawa can fadarsa inda yake


WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GA YARIMA WALISU BAYAN YA JE GURIN ABIN BAUTARSA KUMA YA NEMI TAIMAKO DAGA GARESHI

******* ********* ********

Acan birnin madarul adfam kuwa tun daga lokacin da yarima walisu ya bata
Kuma mahaifinsu wato sarki fadarul amnar ya umarci gimbiya walisa kan taje ta nemo walisu kuma ta hanashi aikata
Miyagun ayyukan da yake shirin aikatawa tun daga ranar da itama gimbiya walisa ta fita neman walisu sai sarki fadarul amnar ya shiga cikin kewar ýaýansa har takai ga cewa ya daina jin dadin sarautar gaba daya
Hatta abinci ma sai matarsa gimbiya nursiba ta sakashi agaba kamar karamin yaro sannan yake iya ci
Ba komai ta janyo haka ba face tsananin son da yake yiwa ýaýan nasa guda biyu
Duk da cewa yarima walisu ne kadai yake da ikon mulkin birnin tunda shine namiji
Sai ya kasa sukuni domin bashi da tabbacin gimbiya walisa zata iya kubuta daga sharrin yarima walisu matukar sunyi karo da juna
Domin yanzu yarima walisu ba sa'an karawarta bane
Wannan shine dalilin dayasaka shi kullum baya iya barci sai tsoro da fargabar halinda 'ya'yansa biyu suke ciki
Domin kullum idan ya kwanta barci sai anuna masa 'ya'yansa guda biyu
Sunata yaki da juna inda kuma zaiga duk sanda aka fafata gimbiya walisa da kyar take tsira da rayuwarta
Sai da takai hatta zaman fada baya iya fita
Daga karshe sai ya yanke hukuncin a kira masa babban bokansa wato boka makassar
Cikin gaggawa kuwa makassar ya bayyana ga sarki fadarul munnar
Da zuwansa yace ya shugabana dodon azzalumai kuma mahaifi ga tagwayen jarumai gani na amsa kira me kake da bukata?
Sai sarki fadarul munnar yace dashi yakai makassar yanzu haka ina so mu hada sihirin tsafinmu ni da kai a guri guda
Don musan halinda 'ya'yana suke ciki
Kodajin wannan batu sai makassar ya dago da kansa a razane yace ya shugabana kaima fa da kanka kasan hatsarin da yake cikin wannan aiki domin kamar binciken sirrin boka sahibul ukub ne tabbas zamu iya rasa rayukanmu ta dalilin haka
Koda yazo daidainan a zancensa sai sarki fadarul munnar ya daka masa tsawa yace
Dolene kuwa kayi wannan aiki kuma ina mai tabbatar ma zamuyi nasara kuma babu wanda zai rasa rayuwarsa acikinmu
Idan kuwa kaki to ni da kaina zan yakeka da karfin tsiya na hallaka ka
Kodajin haka sai kwalla ta zubo daga cikin idanun makassar saboda gaba daya ya gama razana da wannan al'amarin
Kawai sai ya dauko wani buzun fatar damisa daga cikin jakarsa ya shimfida akasa
Dashi da sarki fadarul munnar duk sai suka hau kan buzun suka zauna suna masu runtse idanuwansu tareda hada hannuwansu aguri guda daya kan daya
Sannan suka karanta wasu birkitattun dalasimai faruwar hakan keda wuya sai dukkansu jikinsu ya fara karkarwa kamar masu jin zazzabi
Har wata jijjiga suke yi mai makon gumi ya dinga tsatstsafowa daga jikin su
Sai kawai jini ya dinga tsatstsafowa daga jikin dukkan kofofin gashin jikinsu
Saida suka yi yan dakiku suna cikin wannan mawuyacin hali sannan suka bude idanunsu tareda kallon wani bangon turakar da suke zaune
Take wani dunkulen haske yayi fitar burgu daga cikin idanunsu
Ya bugi wannan bangon
Faruwar hakan keda wuya saiga hoton duk abindaya faru ga gimbiya walisa tun daga sanda ta bar gida da irin fafatar. Da tayi da yarima walisu da duk irin wahalhalun da tasha akan hanya har zuwa sanda suka karbi addinin musulunci
Sannan suka fafata yaki da aljani dargatul amnar kai hsr cikin jirgin ruwan da suka shiga saidaya bayyana ajikin bangon
Da ganin wannan al'amari sai hankalin sarki fadarul munnar ya dugunzuma ainun
Kawai sai ya dubi boka makassar yace
Aikuwa ya zame mini wajibi yanzu na tashi da kaina
Na tafi taimakon gimbiya walisa domin tana cikin mawuyacin hali da kuma neman taimako idan har banje inda take kafin su hadu da yarima walisu ba tabbas za'a sami gagarumar matsala

Kodajin haka sai boka makassar yace ya shugabana kada ka aikata haka
Zaifi kyau ka zauna a gida kuma kasa a ranka cewa walisa zata sami nasara
Domin yanzu shekarunka sunyi nisa ba zaka hada kanka dasu ba
Tunda su yanzu suke kan ganiyar samartakarsu don haka kai ba zaka iya hada kanka dasu ba
Tunda magabata sun fada mana cewa
Zamani goma sarki goma kaga kuwa yanzu lokacinka ya wuce yanzu lokacin 'ya'yanka ne

Dajin wannan batu sai sarki fadarul munnar ya takarkare ya bushe da mahaukaciyar dariya
Wacce tasa boka makassar ya saki baki kawai yana kallon sa
Sai da yayi dariyar ta isheshi sannan ya tsuke bakinsa ga barin dariyar yace
Haba makassar ko ka manta wanene ni?
Ka sani komai lalacewar tsohon zaki yafi saurayin kare
Nine fa wanda tunda nake fita filin daga jinina bai taba fita daga jikina ba
Ni kadaine sarkin da idan na fita yaki ba tareda dakaru ba
Komai yawan abokan gaba firgita suke su zubar da makamansu su ruga aguje don tsira da rayuwarsu
Ni kadaine sarkin da yake iya shafe mako guda ina yaki ba tareda na gaji ba
Saidai abokan gaba su janye kafarsu da kansu daga filin daga su barni ni kadai
Su kansu su gimbiya walisa din ai daga jikina suka sami duk irin jarumtakar da suke da ita
Kuma har yanzu ni mai zamani ne
Zamana anan gida bazai zamo komaiba face asara kuma sai ayi nadamar hakan a ba muddin ban fita na taimawa walisa ba
Yana gama fadin haka sai ya tashi ya wuce yabar boka makassar azaune kamar gunki ya kasa magana
Saboda jin maganganun daya fada masa
Kai tsaye sarki fadarul munnar ya wuce turakar matarsa gimbiya nursiba ya sanar da Ita halinda ake ciki
Dajin hukuncin daya yanke saita fashe da kuka ta fara rokonsa akan ya janye wannan nufin nasa
Amma ina ko kadan yaki yarda da maganganunta
Sannan ya fita ya koma can turakarsa jim kadan sai gashi ya fito cikin wata gagarumar shigar yaki
Wacce rabon dayasa wadannan kayan tun yana tashen samartakarsa
Hakika kayan sunyi masa matukar kyau sosai komai jarumtakar mutum idan ya ganshi cikin wannan shigar dolene zuciyarsa ta karaya saboda matukar kwarjininsa

Kai tsaye ya wuce cikin fada da isarsa ya aika sarkin fada da yaje ya kirawo duk 'yan majalisun birnin
Take kuwa sarkin gida ya tafi cika umarni jikinsa na rawa domin ya zaci wani gagarumin yakin za'a fita

Maimakon sarki fadarul munnar ya zauna akan karagar mulki sai ya sami guri ya tsaya kan kamar gunki ko motsi bayayi har sai da 'yan majalisu suka gama hallara
Sannan ya sanar dasu cewa zai fita gagarumin aiki kuma ba zai dawoba sai tareda 'ya'yansa guda biyu
Kodajin wannan batu sai dukkan 'yan majalisun suka soma kallon kallo suna kus kus a tsakaninsu
Harsaidaya daka musu tsawa sannan suka dawo hayyacinsu
Daga karshe ya sanar dasu ya mika ajiyar birninsa ga matarsa gimbiya nursiba
Kuma koda bai dawoba itace zata cigaba da mulkin wannan birnin

Yana gama fadin haka sai tafa hannayensa tareda karanta wasu dalasiman tsafi sau uku
Faruwar hakan keda wuya sai rufin fadar masarautar ya yaye gaba daya
Saiga wani matashin kyakkyawan aljani ya shigo ta cikin saman fadar
Yana dira sai yayi sujjada ga sarki fadarul munnar ba tareda bata lokaci ba
Sarki fadarul munnar ya haye bayan aljanin ya tashi dashi sama kamar kiftawar ido suna fita daga cikin fadar sai rufin fadar ya dawo ya hade kansa kamar yadda yake abaya

KAKA KARA KAKA !!!!
YA ZATA KASANCE TSAKANIN WADANNAN TAWAGOGI GUDA UKU?
SHIN SARKI FADARUL MUNNAR YANA RISKARSU GIMBIYA WALISA?
YAYA KAKE ZATON YARIMA WALISU ZAI KOMA?
DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU AKASHI NA GABA NA WANNAN KAYATACCEN LABARI
MAI SUNA HATSABIBAN SADAUKAI
DAGA NAKU HABIBULLAH KBR

LIKE, COMMENT AND SHARE*****************HATSABIBAN SADAUKAI

CI GABAN ZUBAR DA JINI

***************5 PART C

LBR

**********************HABIBULLAH KBR

Al'amarin su gimbiya walisa kuwa saida suka shafe mako guda suna tafiya acikin wannan tekun
kwatsam wata rana suna cikin tafiya sai sukaga igiyar ruwan ta fara kadawa da karfi sosai fiye da yadda take kadawa
Domin ganin ruwan sukayi yana dunkulewa yana tsiri a sama kamar zai tokare da sararin samaniya
Ruwan kuwa ya dinga hautsinewa yana tambal tambal dasu kamar zai nitsar dasu gaba daya
Koda ganin wannan al'amari sai sukaji gaba daya hankalinsu ya tashi kuma ya dugunzuma ainun
Suka fara juyar d akalar jirgin nasu zuwa can wani bangare da suke hango wani tuburi
Alokacin kuma ruwan yake kara hautsinewa yana batsewa
Ba zato ba tsammani sai sukaga wani katon rikakken kada
Ya faso kansa daga kasan ruwan ya taso sama tunda su walisa sukazo duniya basu taba ganin kada mai girma da ban tsoro kamar wannan kadan ba
Domin harma ya ninka wanda walisa ta fafata dashi a baya girma Da kuma kwarjini
Tsananin girman kadan ne yasashi baya iya rayuwa agefen tekun saidai a tsakiyarsa
Kuma shi kadaine ya kori dukkan sauran halittun da suke rayuwa atsakiyar tekun dukkansu ya korasu can gefe daya
Tsakiyar ta zamo kamar fadarsa, koda bayyanar wannan kadan sai ya sa bakinsa
Ya gatsa jirgin dasu walisa suke ciki take kuwa jirgin ya rabe gida biyu kamar wanda ya tauna tsinke
Sannan ya daga su walisa dake cikinsa ya zazzagesu acikin ruwan
Take duk suka nutse acan kasan tekun shikuwa kadan sai ya nutsar da kansa kasan tekun yabisu can kasan ruwan
Tun kafin su isa kasan tekun tuni kadan ya kawo musu wafta da bakinsa da nufin ya taunesu gabaki
Cikin zafin nama dukansu suka kaucewa harin nasa
Ya wafci iska sannan suka zare makaman yakin da suke hannunsu suka shiga fafatawa da wannan kadan acikin
Kasan ruwan in badon su walisa sun sami horo na zama akasan ruwa ba da basu isa su iya koda kaucewa wannan kadan ba
Dadin dadawa kuma zafin namansu ne yake dada taimakonsu kuma yake karesu daga sharrin kadan
Sai gashi dukkansu sun kewaye kadar atsakiya suna fafata kazamin fada atsakaninsu
Haka shima kadan shi kadai yake birkita ruwan da suke
Domin da zarar ya kaiwa daya daga cikinsu duka da jelarsa idan ya kauce sai dai kaga ruwan gaba daya ya hautsine saboda saboda girma da kuma kaurin da take dashi
Kai hatta kananun halittu da suke cikin tekun irinsu tarwada da karfasa
Wadanda suke rayuwa acikin kasan shuke shuken dake cikin tekun saida gaba dayansu suka gigice
Suka fara canja sheka domin tsira da rayukansu
Su kuwa su walisa sai suka kara zage damtse domin ganin sun tsira daga sharrin wannan kadar
Suna cikin fafatawar ne kadan ya shammaci gimbiya walisa yayi mata farat daya
Ta fada bakinsa da nufin ya hadiyeta ba tareda ya tauna namanta ba
Koda walisa ta fada bakinsa saj da takai daidai makogaronsa zata fada cikinsa sai tayi caraf ta caka tsinin takobinta adaidai bakin makogaron kadar
Kuma taki yarda ta saki wannan takobin don kada ya sami damar hadiyeta

Take kadan yayi wani irin gunji tare da ihu saboda tsananin zafi da zugin da yaji
Su

Please Login or Register in order to submit comment