Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suna masu kallonsa da idanunsu
Domin ganin samansa sukayi sumul kamar ba kan tsauni ba
Kuma a samansa gaba daya babu bishiya ko tsiron tsirrai guda daya ma'ana dai filine fetal ta yadda babu wani abu da zai boye maka
Koda sukaga wannan fili sai duk jikinsu yayi sanyi domin sun san tabbas ruwa baya tsami banza dole akwai dalilin faruwar hakan
Cikin sauri suka zare makaman yakinsu suka rukesu da hannuwansu domin zaton koda yaushe za'a iya kawo musu farmakin bazato
Suna tafiyane cikin sanda kuma duk su ukun sun jingina jikinsu a guri daya sunki yadda su rarrabu don gudun kar a shammacesu
Hatta kasar guri idan zasu taka basa yarda su bada gaba dayan karfinsu agurin don gudun tsautsayi
Suna cikin wannan tafiyar ne kwatsam ba zato ba tsammani sai sukaga kasa ta tsage ta haifar da wani wawakeken rami mai girman gaske dukansu suka fada cikinsa
Dukkansu sai suka kwarara uban ihu mai karfin gaske
Suna ruftawa cikin ramin ne sai shi kuma dutsen ya koma ya hade kansa kamar bai taba budewa ba
Su kuwa su gimbiya walisa acikin iskar sai suka ruke hannayen juna ba tareda sun yarda sun cika hannayen junansu ba
Haka dai sukayita yawo a saman iska suna saukowa kasa ba tareda sun sauka kan kasa ba saboda zufin da ramin yake dashi
Zurfin wannan ramin kadai atakaice zaikai zurfin gaba dubu
Kuma ba hakar mutanen wannan zamanin ba saidai hakar mutanen farko wato samudawa sannu a hankali suka sauka a kasan dutsen
Koda suka sauka kasansa sai suka cika da mamaki sakamakon ganin girmansa domin girmansa kusan kamar gari guda yake
Kuma gaba ki dayansa babu wata matattakala wacce zaka kama domin fita daga cikin wannan tsaunin
Saboda tsananin mamaki marfuza bata san lokacin da tace
Wannan wanne irin dutse ne?
Dajin wannan tambaya sai sarki aryan yayi tsaki yace
Ai dukkan mu baki ne a wannan guri don haka babu wanda zai iya baki amsa sai abinda idanunmu suka gane mana
Walisa tace kwarai kuwa maganarka gaski…… ..
Kafin ta gama fadar abinda zata fada sai kawai ta jiyo hucin sautin harbin kibiya
Cikin sauri ta daka tsalle daga inda take ta kaucewa harbin kibiyar
Kawai sai kibiyar taje ta cake ajikin bangon bangon dutsen gaba dayanta
Koda ganin wannan abu daya faru sai dukkanninsu suka waiwaya domin suka daga inda wannan kibiyar take amma basuga kowa ba agurin
Daga can sai sukaji an bushe da dariya wacce ta amsa kuwwa agaba daya cikin kogon dutsen ta yadda ba zaka iya tantance daga inda sautin dariyar yake tahowa ba
Daga can sai sukaji ance barkanku da zuwa kogon hallaka
Kogon da duk wanda ta shiga cikinsa bai isa ya fita daga cikinsa araye ba
Idan akwai mai wasiyya acikinku saiya fada domin mu isar masa da ita
Dajin haka sai sarki aryan ya daka wa muryar tsawa yace karyarka ta sha karya
Ko wanne irin bala'i aka tana da acikin wannan ina tabbatar maka da cewa dole sai mun tarwatsa shi kuma mun fita daga cikinsa lafiya ba tareda dayanmu ya rasa rayuwarsa ba
Kuma sai mun tarwatsa dukkan zaluncin da kukeyi mun wuce lafiya ni da abokan tafiyata.… .
yana cikin fadin haka sai walisa ta rufe masa baki da hannunsa don kada ya sake yin magana
Itama ta fada cikin daga murya tace ai duk wasu maganganu da zaka fada karyane
Kuma bazaiyi tasiri akanmu ba saidai akan kananun jarumai idan har kun isa mazaje ku fito muyi gaba da gaba daku domin yakin buya yakin tsoro ne
Koda gama fadin haka sai ta sake jin an bushe da dariya daga can kuma sai sukaji ance
Ku kwantar da hankalinku a sannu zaku ga mutuwa akan idanunku ba sai kun tsokanota kusa daku ba koda akazo daidai nan amaganar sai take sautin komai ya dauke aka daina jinsa
Da jin haka sai duk suka dubi junansu sukayi wata inkiya da hannayensu
Sannan suka ci gaba da tafiya ba tareda fargabar komai ba
Saida sukayi tafiya mai dan nisa sai sukaji kasa ta fara tsagewa da dukkan bangwayen dutsen kamar zasu rufto su fado kansu su dannesu
Koda ganin haka sai duk sukayi sauri suka hade jikinsu guri guda suka suka gyara rukon makaman yakinsu a hannunsu
Sannu a hankali saiga wasu irin gajerun aljanu suna fitowa daga cikinsu
Su dai wadannan aljanu 'yan kananu ne wadanda gaba daya
girmansu baifi na bijimin sa ba kuma bakunansu dogayene
kamar irin na ungulu saidai suna da tsawo sosai haka suma
kunnuwansu fala fala ne masu matukar fadi bayan haka wadannan aljanun suna da matukar tsananin yawa
Kai da kaga wadann zaka san cewa jinsine na aljanu masu shan jinin bil'adama
Kuma ko kadan basu da tausayi sannu a hankali wadannan aljanun suka gama fitowa daga cikin ginin sukayiwa su walisa kawanya
Nanfa dukkanninsu suka tsaya suka fara kallon kallo atsakaninsu
Daga can sai aljanun suka afko kansu walisa da nufin suyi musu gunduwa gunduwa da sassan jikinsu
Nantake suma su walisa suka afka kan aljanun suna masu karaji da kururuwa
Nanfa aljanun sukayiwa su walisa rubdugu aka ruguntsume da masifaffen yaki atsakiyar kogon dutsen
Sai gashi aljanun suka kaiwa su walisa farmaki da ta ko wanne bangare da sama da kasa
Domin su kacalcala su walisa su shanye jinin jikinsu
Nanf gurin y cika da karar haduwar karafa d zarar makamansu walisa sun hadu da jikin wadannan aljnun sai aji wata kara ta tashi kal !!
Kamar sautin haduwar karf da karfe tareda tartsatin wuta
Suma kuma dodannin da zara sun kawo wa su walisa hari da bakinsu idan suka kauce suka sami kasa sai kaga bakin nasu ya huda kasar gurin yayi dan karamin rami
Domin shi kansa bakin nasu kaifi ne da shi da kuma tsini kamar takobi
Nanfa gurin ya yamutsi karar karafkiyar karafa ta cika dodon kunne
Ihu tareda gurnanin aljanun ya cika kunnuwa sai ga su walisa sun zama kamar an ajiye mage a tsakiyar dubunnan karnuka
Nanfa su walisa suka barbazu atsakiyar aljanun kowanne daga cikinsu ya fuskanci bangari guda cikin mugun nufi da burin ganin ya tarwatsa su da karfin tsiya
Nanfa sukaci gaba da kai farmaki cikin bakin zafin nama ,juriya da bajinta kamar jikinsu bana jini da tsoka bane haka suka dinga ratsawa ta cikin aljanun rike da makamansu tsirara suna kai musu sara da suka ta dole suka dinga budawa kansu hanya da karfin gaske
Kamar sun kasance shaidanu amma duk wannan kokarin da sukeyi sai ya tashi abanza
Domin basa iya kashe ko guda daya daga cikin aljanun
Su kuwa aljanun burinsu kawai shine su kafa bakinsu ajikinsu walisa domin su zuke jinin dake jikinsu
Koda su walisa suka fuskanci nufin aljanun sai suka kara zage damtsensu wajen yakai aljanun
Don daga baya ma sai suka dinga daukar aljanun da hannuwansu suna ciccibar su duk girmansu suna yin jifa dasu
Amma da zarar aljanun sun sauka akasa sai kaga sun tashi sun murmure kamar wani abu bai taba samunsu ba
Saida suka shafe fiye da sa'a guda suna wannan bakin artabun
A sannan ne su walisa suka fahimci cewa tabbas idan aka cigaba da wannan yakin a haka to zasu iya gajiya
Kuma da zarar sun gaji shikenan dodannin zasu sami nasara akansu
Kodayin wannan tunani sai kawai ta kwallara uban ihu ta tarwatsa wadanda suke kusa da ita da karfin tsiya sannan ta dawo inda su sarki aryan da jaruma marfuza suke suka kawai tayi musu wata iriyar inkiya da 'yan yatsun hannunta
Sannan suka ci gaba da yakin da suke yi ba tareda sun tsagaita ba
Suna cikin wannan haline ba zato sai wani aljani ya shammacesu yasa bakinsa ya caki cinyar jaruma marfuza
Nantake marfuza ta kwallara uban ihu sakamakon tsananin zafi da zugin da taji
Koda ganin abinda ya faru sai sarki aryan ya daka tsalle daga inda yake yasa kafarsa ya naushi wannan aljanin saboda karfin dukan saida aljanin ya tashi sama sannan ya fado
Cikin sauri sarki aryan ya yagi jikin rigarsa ya daurewa jaruma marfuza wannan ciwon da yake kan cinyarta ita kuma walisa saita dinga karesu ita kadai da takobin dake ruje atafin hannunta bayan sarki aryan ya gama daurewa marfuza wannan ciwon sai duk su biyun suka mike tsaye sukaci gaba da fafata sabon azababben yaki
Wanda yafi na farko domin a wannan lokaci suna yin fadan ne domin su gano lagon wadannan aljanun ne don su gaggauta kashesu
Wani irin sabon salon yaki suka canja wanda acikinsa suka dinga tsalle tsalle da kwance kwance a tsakiyar dubunnan dodannin suna masu kai musu sara da suka ta kowanne bangare ba tare da sanin takamaiman gurin da zasuyiwa aljanun lahani ba
Ai kuwa basu dade da fara wannan sabon artabu ba wani aljanu ya sake kawowa marfuza cizo a kan cinyar daya cijeta da farko
Koda ganin abinda yake shirin faruwa batasan sanda ta daga takobinta sama ta sara ta a tsakiyar karan hancin aljanin
Aikuwa faruwar hakan keda wuya sai gurin ya dare jini yayi tsartuwa
Nantake alljanin ya sulale ya fado kasa matacce ba tareda ya koda shura ba
Cikin sauri ta juyo inda su walisa suke tayi musu ishara da wannan lagon data samo
Dajin haka sai dukkanninsu suka zage damtse suka dinga saran tsakiyar hancin aljanun babu kakkautawa
Take gurin ya cika da sautin ihun wadannan aljanu da kuma gurnanunsu
Saboda yadda su walisa suka bude kasuwar rayuka acikin tsakiyar kogon
Nanfa gawarwakinsu suka barbazu atsakiyar kogon duk inda ka duba babu abinda zaka gani face su da kuma jininsu wanda ya malale agaba daya cikin kogon kamar an bude magudanar ruwa
Kafin cikar rabin sa'a har sun gama karar aljanun 'yan kalilan ne suka tsira su din ma da sukaga uwar bari sai suka dinga bacewa suna shigewa cikin karkashin kasa don su tsira da rayuwarsu
Koda ganin wannan nasara da suka samu sai dukkanninsu suka nutsu ba tareda sun mayar da makamansu cikin kube ba
Daga can sai kawai sarki aryan ya mayarda takobinsa yace dasu
Ai da alama wadannan halittu ba zasu dawo ba domin suma yanzu sun san cewa mu ba kanwar lasa bane
Don haka dolene suyi shakkar kara tunkarar mu
Dajin wannan batu sai suma duk suka mayar da makamansu acikin kufe
Sannan jaruma marfuza ta sami guri ta zauna ta fara kokarin sakawa raunin dake jikinta magani
Da ganin haka sai suma su gimbiya walisa suka sami guri kusa da Ita suka zauna domin su huta
Sai bayan sun zauna agurin suka lura da yadda yanayin cikin dutsen ya canja zuwa duhu
Ganin haka sai suka fuskanci cewa tabbas rana ta fadi don haka dolene su sami guri su zauna domin su yada zango su kwana agurin in safiya tayi sai su tashi su ci gaba da tafiya
Da ganin haka sai walisa ta dubi jaruma marfuza tace
Sannunki jarumar gaske tabbas na gamsu cewa ke ba karamar jaruma bace don har kin wuce yadda nake zato
Dajin haka sai marfuza tayi dan guntun murmushi sannan tace
Ba haka bane nima ai dolece ta tilastani na ci gaba da wannan yakin don bana so na barku da wahala

Nandai sukayita hira atsakaninsu daga can kuma sai suka
dauko abinci sukaci suka cika cikinsu sannan suka raba
kwanciya barci domin su samu su huta idan safiya tayi sai suci gaba da tafiya
Amma sai suka raba daren gida biyu ma'ana
Gimbiya walisa da jaruma marfuza zasu kwanta suyita barci abinsu har zuwa tsakiyar dare shi kuma sarki aryan sai ya tsaya yayita zaman gadinsu
Idan tsakiyar dare yayi sai ya tashi gimbiya walisa sannan shima yaje ya kwanta ita walisan ta zauna taci gaba da gadinsu
Ita kuma marfuza sai sukayi mata uzuri domin ta samu ta dan huta saboda ciwon dake jikinta
Haka kuwa akayi kamar yadda suka tsara haka al'amarin ya kasance
Wato a wannan guri shka samu sukayita sharar barci abinsu domin su huce gajiyar dake tsakaninsu
Basu farka ba saida safiya tayi sannan suka tashi suka debi makaman yakinsu da dukkan komatsansu suka kara nausawa cikin kogon dutsen sai bayan sunyi tafiya mai nisa ne suna tafiya a wannan lokaci gimbiya walisa tana ta faman kalle kalle da dube dube acikin kogon kwatsam saiga wani katon mulmulallen dutse ya gangaro daga sama zai turmusheta kuma shi wannan dutsen daya zo akanta zai fado
Kuma idan har hakan ta faru take anan dutsen zaiyi daga daga da naman gimbiya walisa
Cikin sauri sarki aryan da jaruma marfuza suka fara kwallawa gimbiya walisa kira domin ta kauce amma ina
Ko kadan bata iya jinsu ba domin ta fada cikin tunanin dan uwanta yarima walisu da kuma mahaifinsu wato sarki fadarul munnar

ME ZAI FARU SHIN GIMBIYA WALISA TANA MUTUWA TA SILAR WANNAN DUTSEN?
DON JIN AMSA SAI MU HADU A KASHI NA GABA
DAGA NAKU
HABIBULLAH KBR

LIKE, COMMENTS AND SHARE********************HATSABIBAN SADAUKAI

CI GABAN

ZUBAR DA JINI

***********************2PART C

LBR

*********************HABIBULLAH KBR

lokacin da su jaruma marfuza da sarki aryan suka dinga
kwallawa gimbiya walisa kira domin su ankarar da ita cewa ga dutse nan yana tunkarota

Koda suka fuskanci cewa hankalin gimbiya walisa baya jikinta
sai kawai nantake duk su biyun suka falfala da gudu
kamar kiftawar ido kafin dutsen ya sauka akan ta
Tuni
sunzo sun janye ta daga gurin take kuwa dutsen ya dira akan kasa
Daidai gurin da ya fadima saida ya wawake ya haddasa
wani rami wanda za'a iya bunne mutum biyu acikinsa
Cikin bacin rai sarki aryan ya daga hannu da nufin ya mari gimbiya walisa
Amma koda hannun nasa ya kusa sauka akan fuskarta sai yaji ya kasa
Bisa dole ya sauke hannun nasa tareda nadamar daga mata shi
Da ganin haka sai walisa tace menene ya hanaka idda nufinka akaina?
Dajin haka sai kunya ta kama sarki aryan kawai sai yayi yake tareda sosa keyarsa yace

Haba ai har abada hannu na bazai taba yin gangancin
shafar wannan fuskar taki ba kuma nayi imani da cewa
Duk abinda ya koro bera daga rami har yazo ya fada cikin wuta to tabbas yafi wutar zafi

Don haka na fuskanci cewa ba komai kike tunani ba face
yadda akayi ke da dan uwanki kuka zama kuna farautar juna kamar wasu dabbobi

Cikin mamaki walisa ta juyo ta dubeshi tace tayaya akai kasan hakan ?
Kawai sai yace ai labarin zuciya fuska ake tambaya
Don haka duk abinda yake cikin zuciyarki akan fuskarki na gani
Suna cikin wannan zancen ne sai sukaga wasu irin duwatsun
masu yawan gaske suna gangarowa daga bayansu
zasu turmushesu, koda ganin wadannan duwatsu sai dukkanninsu suka bar wannan tattaunawar da suke
Suma suka nufi hanyar da take gaba dasu cikin azababben gudu
Wohoho nanfa aka kasa Azababben tseren gudu tsakaninsu
da wadannan mulmulallun duwatsun domin su ceci rayuwarsu
Domin sun tabbatar da cewa wadannan duwatsun turo musu
su akayi kuma wani ne yake sarraf su
Sai gashi a wannan lokaci su walisa suna gudun da basu
taba yin kamar sa atarihin rayuwarsu ba
Domin a wannan lokacin basu da damar da zasuyi amfani da karfin sihirin tsafinsu
Sai da suka jima suna wannan gudun domin har idanunsu
sun rufe yadda basa kula da abin da yake gabansu
Kawai
sai ganinsu sukayi a bakin wani tafkeken rami
Wanda
suna kara koda taku daya daga imda suke take zasu fada cikinsa
Kuma da zarar sun fada din babu wanda zai tsira daga cikinsu
Koda ganin wannan katon ramin duk sai suka tsaya sukayi cirko cirko
Suna kallon ta hanyar da zasu bi su ketare shi kuma har a sannan
Wadannan mulmulallun duwatsun basu daina binsu ba
Kawai sai suka hango wata siririyar gada acan gaba
dasu wacce fadin bai wuce takun mutum daya ba
Da ganin
wannan gadar sai dukkansu suka kara falfalawa da gudu
suka nufi gurin da wannan gadar take
Duk da sun san cewa gadar bata da karfin da zata debi mutane fiye da daya
Amma sai duk suka haye kanta basu tsaya bata lokaci ba
Kuma basu daina gudun da suke yi ba har saida suka
je tsakiyar gadar ba tareda wani abu ya same su ba
Koda suka je tsakiyar kan gadar sai suma wadannan duwatsun duk sukayi bindiga suka tarwatse kamar gari
Yabi iska kamar basu taba wanzuwaba,
Kuma
adaidai lokacin ne su gimbiya walisa suka ga wannan
gadar ta fara jijjiga kanta a sama tana kokarin karyewa
Tareda wata irin hadaddiyar curin dunkulen bakar wata data kama akasan gadar
Wacce indai mutum yayi sakaci ya fado cikinta tun kafin
ya sauka akanta ma zai babbake ya kone kurmus saboda tsananin zafin wutar
Itama wannan gadar saita kara kaimi wajen jijjiga kanta asama
Ta yadda duk wani abu da yake kanta zai fado kasa
Koda su walisa suka fuskanci haka duk sai suka hada
hannayensu guri guda suka ruke ba tareda sun yarda sun cika ba sannan suka ci gaba da gudun a haka basu daina ba
Haka itama gadar bata daina girgizar da take ba nanfa
suka dage iya karfinsu domin suga sun kai karshen gadar don tsira da rayuwarsu
Kuma inda matsalar take shine mutum biyu ko uku basu isa suyi tafiya akanta a jere ba saboda kankantar ta
Dole saidai mutum daya bayan daya, daga can kuma sai gadar ta fara karyewa tana fadawa cikin wutar
Da zarar karfen ya fada cikin wutar saidai kaga nantake ya narke
Tare kuma da wani sauti mara dadin sauraro ki kake yana
Cuuuuuuuuu, alokacin da karfen yake narkewa, duk wannan
halin da ake ciki gimbiya walisa ce akan gaba sarki aryan yana biye da ita
Sannan jaruma marfuza tana biye dashi abaya, har sukaje karshen gadar
Gimbiya walisa tana dauke kafarta daga kan gadar sai nan take gadar ta karye
Gadar tayi kasa dasu Sarki aryan da jaruma marfuza
Koda ganin abindaya faru sai nantake walisa itama ta daka tsalle ta bisu
Kafin su fada cikin wutar tuni walisa ta shuri sarki aryan ta jefoshi saman gadar
Sannan jaruma marfuza, duk su biyun suka fita daga cikin ramin
Kash hakika rashin sani yafi dare duhu
Koda ta gama fito dasu daga cikin ramin sai itama ta dako tsalle domin ta fito daga cikin ramin,

Amma ina sai ta kasa domin tayi nisa acikin ramin
Kuma tana daf da riskar fadawa cikin wutar

Da ganin haka sai nantake jaruma marfuza ta kwanto wata doguwar igiya daga jikinta ta jefa cikin ramin
Sannan shima sarki aryan sai shima ya daka tsalle ya ruke wannan igiyar ya fada cikin ramin
Kafin gimbiya walisa ta fada cikin wutar tuni sarki aryan
yasa hannunsa na hagu ya riko ta dashi
Ita kuma gadar ta nutse acikin wutar ita kadai
Cikin
matukar mamaki gimbiya walisa ta dago da kanta suka hada idanu da sarki aryan
Kawai sai tayi masa murmushi, itama jaruma marfuza
wacce ke ruke da igiyar saita yiwa gimbiya walisa murmushi
Nanfa yasa hannuwanta biyu ta fara kokarin janyo sarki aryan da gimbiya walisa
Wohoho hakika gaskiyane da ake cewa karfi jari ne kuma
ko wanne abu yana da rana a duniya
Koda ta fara janyo su sarki aryan sai damatsan hannunta
suka tashi sukayi burdin burdin Duk da cewa kuwa bata da girman jiki amma a wannan lokaci sai surar jikinta ta dinga rikidewa
Suma gabobin jikinta suka dinga budewa,
Sai gashi tana janyo sarki aryan da gimbiya walisa a tare
Har saidata fito dasu gaba daya daga cikin ramin suna
sauka akasa sai duk suka zube akan kasa suna ta faman
yin haki aka rasa wanda zaice da wani kala daga cikinsu
Daga can sai marfuza ta dubi walisa tace
muna matukar godiya bisa ceton rayuwar mu da kikayi
Amma ina da tambaya shin menene dalilin daya sa kika sayar da rayuwarki domin ceton tamu rayuwar?
Dajin wannan tambaya sai walisa tace ai amsar wannan tambayar a bayyane take

Idan har na rasa ku ku biyu tabbas zanyi babban rashin abokai arayuwata
Domin tun daga tasowata ban taba yin aboki ko kawa ba
Babu wanda na sani sosai kamar iyayena da kuma dan uwana yarima walisu

Yanzu kuma kaddara ta rabani dasu kuma tazo ta sake hadani daku amatsayin sababbin abokan rayuwa
Shin tayaya kuke ganin zan iya yin kasadar rabuwa daku?
Koda ace ni na rasa tawa rayuwar to nayi imani da cewa ku biyun nan zaku taimaka mini ku cikawa mahaifina burinsa
Kodajin wannan batu sai su sarki aryan suka girgiza
kansu alamar gamsuwa da bayaninta Bayan sun dan huta
a wannan guri tsawon lokaci mai tsawo suna hira a binsu kamar ma sun manta da gagarumin aikin dake gabansu
Sai kawai sarki aryan ya katse hirar da sukeyi da fadin cewa
Yanzu dai dukkanku kunga irin halinda muka shiga acikin wannan kogon dutse
Tabbas na yarda cewa ilimin tsafi kogi ne ni dai a iya binciken
da nayi bantaba sanin da akwai wannan kogon dutsen
da har sihiri baya tasiri acikinsa ba sai yanzu da muka tsinci kanmu acikinsa
Yanzu kuma na yarda cewa wannan gida ya amsa sunansa gidan mutuwa
Kuma gidan bala'i domin duk sihirinka ba zai kwaceka
ba acikinsa koda kuwa kaine yarima walisu ko kuma ince boka sahibul ukub
Kodajin wannan batu sai dukkansu suka jijjiga kansu
sannan marfuza tace kwarai kuwa maganarka gaskiya ce domin ina ganin cewa hakan ne ya hana yarima walisu shigowa cikin wannan kogo
Dajin haka sai walisa ta jijjiga kanta tace yake marfuza idan har haka kike tunani

To ki gaggauta canja tunaninki, domin kamar yadda
duk nan kuke takamar jarumtaka .To shima walisu yana jin
haka domin tare dashi aka bamu horon yaki, ki sani cewa karfin damtsena, iya yaki, da kuma karfin sihirina daya yake da nasa
Saidai kawai yanzu nasan yafini domin bashi kadai bane ,kai in takaice maka labari ma
Shi kansa boka sahibul ukub ba kanwar lasa bane a fannin jarumtaka
Tararsa gaba da gaba daidai yake da mutum yace zai
nada gammo akansa a dora masa dakon duniyar nan
Ba karamin sa'a bace ba zata taimaka mana har mu iyayin gaba da gaba dashi mu sami nasara akansa ba
Tunda yanzu mutum biyu ne a hade yarima walisu da boka sahibul ukub
Kunga kuwa dolene sai mun dage wajen kokarin cika burikan dake gabanmu
Yanzu dai zama bai same mu ba dolene mu tashi mu ci gaba da tafiya

Da gama fadin haka sai ta mike tsaye ta dubi su jaruma marfuza tace
Idan kun shirya sai ku mike tsaye mu tafi aikin dake gabanmu
Domin zama anan gurin ba aikin mu bane kuma daidai yake da hutun jaki da kaya aka
koda jin haka sai dukkansu suka mike tsaye tareda gyara tsayuwarsu
Sarki aryan ya kalli marfuza yace ina matukar tausaya miki akan wannan ciwon dake jikinki
Kuma ina fatan bayayi miki ciwo ?
Koda jin wannan tambaya sai marfuza tayi murmushi tace
Ai ko kadan wannan ciwo baya damu na domin maganin da na saka masa yana da karfi wajen hana ciwo zugi da radadi
Koda gama fadin haka sai tayi shiru ba tareda ta kara cewa komai ba
Ba tareda da bata lokaci ba suka kama hanya suka ci gaba da tafiya acikin kogon dutsen
Kuma suna tafiyar suna hira atsakaninsu kamar babu
wani tashin hankali da zasu tarar agabansu, ko kuma
ince kamar suna tafiya acikin gidansu Kuma suna tafiyar
suna hadawa da dube dube tako ina domin suga ta inda za'a fara kawo musu hari
Har sukayi doguwar tafiya basu hadu da wani abu ba na tashin hankali ko kuma cutarwa ba
Don haka sai suka sakin jikinsu tun da ragowar hasken rana har saida itama ranar ta fadi gari ya soma yin duhu alamar dare yayi
Da ganin haka sai walisa taja tunga ta tsaya ta dubesu tace
Zaifi mana kyau mu dakata da tafiyar mu a wannan guri domin tafiya mu acikin wannan duhu babbar matsala ce agare mu
Koda jin haka sai dukkanninsu suka yarda da maganarta
Don haka sai suka fara duba guraren da suke kewaye
da gurin da suke domin su tabbatar da lafiyar gurin saida
suka tabbata babu wani abu akusa dasu sannan suka dawo suka kwance guzurinsu
Suka fito da abinci sukaci suka koshi sannan suka raba tsarin
kwanciya barci kamar yadda sukayi abaya amma wannan karon harda jaruma marfuza
Kuma a wannan

Please Login or Register in order to submit comment