Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hannunsa ya cafeta ya fara kyalkyala dariyar farinciki
Yana cikin dariyar ne sai walisa ta dunkule hannunta ta karanta dalasiman tsafi
Take wata iriyar murtukekiyar sarka wacce tayi jajur kamar an sakata acikin wuta ta bayyana ahannunta
Cikin sauri ta jefawa sarki aryan da jaruma marfuza wannan sarkar suka ruke sannan suka jefawa maridin ita

Take kuwa sarkar taje ta kanannadeshi kamar wani fursuna

Nanfa suka soma wujijjiga shi duk da tsananin girma da karfin da yake dasu sai suka zama na banza

Wohoho hakika kyan fada shine kada afara shi idan yayi tsanani koda kai ne ka tsokano shi sai kayi nadamar zuwansa
Ai kuwa ana fara wannan salon fafatawar sai suka rikirkita maridin
Ya fara kokarin ya tsitstsinka sarkokin da suke jikinsa amma ina damar hakan taki samuwa agareshi
Sai gashi yana daga sarkokin sama yana wujijjigata da hannuwansa domin ta bar hannunsu walisa amma sukaki yarda hakan ta faru
Saidai kagansu suna yawo a saman iska tare da sake tamke wannan sarkokin ajikinsa
Kai tun maridin yana iya daga hannunsa hartakai ga cewa baya iya koda daga dan yatsansa
Sai wani irin mahaukacin gurnani daya dingayi wanda ya dinga ratsa ilahirin dajin kamar ana tsawa
Koda sukaga sun sami wannan nasarar akansa sai take
Suka daga kawunansu sama atare kuma lokaci guda
Take wata iriyar daskararriyar kankara ta sauko daga saman ahankali ta dinga bin maridin tana shanyewa
Har saida jikinsa ya daskare gaba daya sannan wani katon dutse
Ya gangaro daga saman yazo ya turmushe shi saida yayi daga daga da jikinsa
Sannan duk wadannan sarkokin suma suka babbace kamar basu taba wanzuwa ba agurin
Koda mutuwar wannan maridin sai dukkansu suka zunr akasa suna ta faman haki sabida wahalar da suka sha tsawon lokaci mai tsawo ba tareda dayansu yace da daya uffan ba
Saida suka shafe dakiku masu yawa azaune suna ta faman kallon juna
Daga can kuma sai walisa ta katse shirun da yake tsakaninsu ta dubi marfuza domin marfuza da nufin ta tambayeta lafiyarta
Sai kawai taga hankalin marfuza gaba daya yana kan sarki aryan sai faman satar kallonsa take a lokacin da yake kokarin sakawa kansa magani akan raunin dake jikinsa
Gaba daya bata kula cewa tana kallonta ba sai faman murmushi takeyi
Da ganin wannan abu gimbiya walisa sai taji tausayin marfuza ya kamata akan yadda take nuna soyayyarta ga sarki aryan
Kawai sai walisa tayi gyaran murya firgigit sai marfuza ta juyo suka hada idanu
Koda ta lura cewa walisa na kallonta sai kawai taji kunya ta kamata
Cikin fara'a walisa ta taso daga inda take ahankali ta dawo inda marfuza take ta zauna yadda suna fuskantar junansu da ita
Tace yake 'yar uwata inaso ki sani cewa kamar yadda kika kamu da soyayyar sarki aryan haka nima na kasance
Bayan haka ni na dauke ki be amatsayin 'yar uwata ta jini
Bazanso duk abinda zai bata miki rai ba ko kuma shiga tsakanin mu
Kuma ina matukar tausaya miki kan halinda kika shiga na soyayyar sarki aryan
Abu daya ni na yarda dashi a rayuwata cewa shi yaki kan soyayya halak ne
Don haka ina mai shawartarki daki dage iya kokarinki wajen ganin kin ja hankalin sarki aryan
Ni kuwa dama tuni ya dade da fadawa cikin soyayyata idan har kikayi nasarar samun soyayyar sa ni a shirye nake dana hakura na bar miki shi
Kodajin wannan batu sai mamaki ya turnuke marfuza tace
Akan me zaki yanke wannan danyen hukunci haka ai ni tuntuni na hakura do soyayyar sarki aryan domin na fahimci hankalinsa baya kaina kuma tuni ya kamu da soyayyar ki
Kuma kema haka don dadin dadawa dukkanku jinin sarautane sai kunfi dacewa da junanku
Dajin haka sai gimbiya walisa tayi murmushi sannan ta girgiza kanta tace
Ko kadan wannan abu da nayi ba danyen hukunci bane
Kuma maganar cewa kin hakura da soyayyar sa ba gaskiya bane
Kawai dai kinaso ki boye mini ne. akan me zaki hakura
Da soyayyar wanda zuciyarki ta dade da kamuwa da soyayyar sa alokaci guda wanda kuma akan soyayyar sa ashirye kike ki rasa rayuwarki?
Akan wannan daliline yasa nace ke ya kamata ki zama abokiyar rayuwarsa
Kuma inaso ki sani kamar yadda na kasance jinin sarauta ai kema jinin sarautarce……… .

Gyaran muryar da sarki aryan yayi ce ta katse shirun da yake tsakaninsu yana mai cewa
Ai sai ku taso mu tafi mubar wannan saharar domin ba gurin zama bane ba mu kara gaba
Dajin haka sai dukkansu su biyun suka mike tsaye daga gurin da suke suka karkade tufafin jikinsu
Ba tareda bata lokaci ba suka debi makamansu na yaki da sauran kayansu suka kama hanya suka ci gaba da tafiya
Tunda suka fara wannan tafiya basa yarda su yada zango ako'ina
Saidai idan suna da bukatar cin abinci kuma abincin ma a tsaye suke cinsa idan kuma wata lalurar ta kam daya daga cikinsu
Saiya kebe aguri guda, idan dare yayi kuwa kuma suna da butar zama su huta sai shimfida kayansu agurin su yada zango zango su kwana agurin
Sannan su tashi su kara gaba
Saida sukayi kwana guda suna tafiya acikin wannan saharar kuma suna amfani da sihirin daurin kasa domin rage nisan tafiyar dake gabansu
Sannan suka fita daga saharar gaba daya suka iso wani wawakeken daji mai girman gaske da kuma tarin kwazazzabai sannan kuma ga manyan duwatsu acikin sa
Kallo daya zakayi wa dajin kasan cewa shi kansa dajin ya cancanci akirashi da dajin kare kukanka
Domin duk abinda wani zaiyi maka acikin dajin ba zaka sami mai taimakonka ba
Don haka kai da kanka zaka fahimci cewa dolene a sami abubuwa masu hatsari acikinsa
Kuma a farkon dajin an kafe wani katon allo wanda ajikinsa aka rubuta
BARKA DA ZUWA DAJIN MARGATUL WASDAR
DAJIN DA I DAN AKA SHIGO CIKINSA SIHIRI BAYA TASIRI SAIDAI ZALLAN KARFIN DAMTSENKA DA KUMA SA'ARKA SUNE ZASU TAIMAKA MAKA KA FITA DAGA WANNAN DAJI

koda suka gama karanta wannan alon sanarwar sai duk suka tsaya kyam suna masu kallon juna da nazari acikin zukatansu
Sarki aryan ya dubesu yace ai bamu da wata mafita ayanzu
Domin tunda muka yanka kazar wahala dolene sai mun figeta
Kuma bamu da wani zabi wanda yafi mu ratsa ta wannan daji kuma mu fuskanci dukkan wani kalubale daga nan har zuwa sanda zamu sami nasara akan dan uwanki yarima walisu mu rabashi da shedanin ruhin boka sahibul ukub da yake jikinsa
Dajin haka sai marfuza tace kwarai kuwa bai kamata mu bata lokacin mu awannan gurin ba tunda muna da aiki mai girma agaban mu
Duk wannan shawarwari da sukeyi gimbiya walisa kawai tayi shiru tana sauraronsu ne kawai
Amma gaba daya hankalinta ta mikashi ne kan wannan dajin tana nazarin yadda yake
Don haka koda suka gama maganarsu saita dubesu tayi murmushi sannan tace
Maganar da kuka fada gaskiyace amma fa ku sani tunda ya zamana sihirin tsafi ba zaiyi tasiri a wannan daji ba
To ina mai tabbatar muku da cewa akwai bala'i mai girma acikinsa
Wanda idan har mukace da karfin damtsen mu zamu dogara to ina mai tabbatar muku cewa
Dayan mu bazai tsira da rayuwarsa ba
don haka dolene sai mun hada da abu guda biyu wadannan abubuwa kuwa sune
Taimakon junanmu koda kuwa silar hakan zai iya zama silar ka rasa rayuwarka idan har ka fuskanci cewa yana matukar bukatar taimako
Abu na biyu kuwa shine amfani da kaifin basirar da muke da ita domin ina tabbatar da cewa za'a iya samun tarkuna masu hatsari
Koda gama wannan jawabi sai gimbiya walisa ta ruko hannun marfuza ta jata suka shiga cikin dajin
Nantake shima sarki aryan yabi aryan yabi bayansu suka shige cikin dajin sukayi ta tafiya ba tareda sanin inda suka dosa ba
Saida sukayi tafiyar sa'a guda suna tafiya basu tarar da wani abin cutarwarba
Sannan suka iso bakin wani katon tsauni mai girman gaske wanda ya tokare dajin gaba daya babu hanyar da zaka ratsa ka wuce face kabi ta samansa
Koda isowarsh daidai inda wannan tsaunin yake sai suka tsaya awannan guri saboda yunwa ta fara galabaitar dasu
Sukaci abinci suka koshi sannan suka tashi suka fara kama wannan tsaunin da hannunsa kamar kadangaru suna hawa samansa

ME ZASU TARAR A SAMAN WANNAN DOGON TSAUNIN?
LIKE AND COMMENTS*********-*--******HATSABIBAN SADAUKAI

CIGABAN ZUBAR DA JINI

********************-2 PART B

LBR

HABIBULLAH KBR

lokacinda su gimbiya walisa suka fara kama wannan dogon tsaunin suna hawa kansa da hannayensu kamar kadangaru
Idan ka kallesu awannan lokaci dolene su baka mamaki
Ganin yadda suke tsananin sauri har suna neman yin 'yar rigen rige atsakaninsu
Kamar masu tafiya akan doron kasa suna cikin wannan tafiyar ne saida suka shafe fiye da rabin tafiyarsu akansa kawai sai santsi ya debi sarki aryan ba tareda ya kula ba hannunsa ya zame ya sulmuyo kasa
Koda ganin haka cikin sauri sai jaruma marfuza tayi sauri tasa hannunta na hagu ta rukoshi dashi
Ba tareda ta kyaleshi ya sulmuyo kasa ba
Cikin mamaki sarki aryan ya dago da kansa sama domin yaga wanda ya rukoshi bisa mamaki sai yaga jaruma marfuza ce fuskarta cike da murmushi hannunta n dama kuma tana ruke da wani bangorin dutse
Kawai sai ya tuna cewa abaya fa yayi yunkurin kasheta
Don haka kawai sai yaji kunya ta kamashi tareda dadin nadama akan abinda yayi mata
Kawai yasa hannunsa shima ya kama wani bangorin na dutsen ya saki hannunta ya ci gaba da tafiyarsa akan tsaunin, duk wannan abu daya faru gimbiya walisa tana kallo don haka sai kawai sai tayi musu murmushi sannan ta kautar da kanta ga barin kallonsu
Daga wannan guri basu kara shafe wata sa'a guda dinba suka isa can karshen tsaunin kafin su isa karshen tsaunin saida dukkan farcunansu suka kakkarye saboda kama duwatsun da suka dingayi da hannayensu
suna gama hawa kan tsaunin sai suka tsaya cak suna masu kallonsa da idanunsu
Domin ganin samansa sukayi sumul kamar ba kan tsauni ba
Kuma a samansa gaba daya babu bishiya ko tsiron tsirrai guda daya ma'ana dai filine fetal ta yadda babu wani abu da zai boye maka
Koda sukaga wannan fili sai duk jikinsu yayi sanyi domin sun san tabbas ruwa baya tsami banza dole akwai dalilin faruwar hakan
Cikin sauri suka zare makaman yakinsu suka rukesu da hannuwansu domin zaton koda yaushe za'a iya kawo musu farmakin bazato
Suna tafiyane cikin sanda kuma duk su ukun sun jingina jikinsu a guri daya sunki yadda su rarrabu don gudun kar a shammacesu
Hatta kasar guri idan zasu taka basa yarda su bada gaba dayan karfinsu agurin don gudun tsautsayi
Suna cikin wannan tafiyar ne kwatsam ba zato ba tsammani sai sukaga kasa ta tsage ta haifar da wani wawakeken rami mai girman gaske dukansu suka fada cikinsa
Dukkansu sai suka kwarara uban ihu mai karfin gaske
Suna ruftawa cikin ramin ne sai shi kuma dutsen ya koma ya hade kansa kamar bai taba budewa ba
Su kuwa su gimbiya walisa acikin iskar sai suka ruke hannayen juna ba tareda sun yarda sun cika hannayen junansu ba
Haka dai sukayita yawo a saman iska suna saukowa kasa ba tareda sun sauka kan kasa ba saboda zufin da ramin yake dashi
Zurfin wannan ramin kadai atakaice zaikai zurfin gaba dubu
Kuma ba hakar mutanen wannan zamanin ba saidai hakar mutanen farko wato samudawa sannu a hankali suka sauka a kasan dutsen
Koda suka sauka kasansa sai suka cika da mamaki sakamakon ganin girmansa domin girmansa kusan kamar gari guda yake
Kuma gaba ki dayansa babu wata matattakala wacce zaka kama domin fita daga cikin wannan tsaunin
Saboda tsananin mamaki marfuza bata san lokacin da tace
Wannan wanne irin dutse ne?
Dajin wannan tambaya sai sarki aryan yayi tsaki yace
Ai dukkan mu baki ne a wannan guri don haka babu wanda zai iya baki amsa sai abinda idanunmu suka gane mana
Walisa tace kwarai kuwa maganarka gaski…… ..
Kafin ta gama fadar abinda zata fada sai kawai ta jiyo hucin sautin harbin kibiya
Cikin sauri ta daka tsalle daga inda take ta kaucewa harbin kibiyar
Kawai sai kibiyar taje ta cake ajikin bangon bangon dutsen gaba dayanta
Koda ganin wannan abu daya faru sai dukkanninsu suka waiwaya domin suka daga inda wannan kibiyar take amma basuga kowa ba agurin
Daga can sai sukaji an bushe da dariya wacce ta amsa kuwwa agaba daya cikin kogon dutsen ta yadda ba zaka iya tantance daga inda sautin dariyar yake tahowa ba
Daga can sai sukaji ance barkanku da zuwa kogon hallaka
Kogon da duk wanda ta shiga cikinsa bai isa ya fita daga cikinsa araye ba
Idan akwai mai wasiyya acikinku saiya fada domin mu isar masa da ita
Dajin haka sai sarki aryan ya daka wa muryar tsawa yace karyarka ta sha karya
Ko wanne irin bala'i aka tana da acikin wannan ina tabbatar maka da cewa dole sai mun tarwatsa shi kuma mun fita daga cikinsa lafiya ba tareda dayanmu ya rasa rayuwarsa ba
Kuma sai mun tarwatsa dukkan zaluncin da kukeyi mun wuce lafiya ni da abokan tafiyata.… .
yana cikin fadin haka sai walisa ta rufe masa baki da hannunsa don kada ya sake yin magana
Itama ta fada cikin daga murya tace ai duk wasu maganganu da zaka fada karyane
Kuma bazaiyi tasiri akanmu ba saidai akan kananun jarumai idan har kun isa mazaje ku fito muyi gaba da gaba daku domin yakin buya yakin tsoro ne
Koda gama fadin haka sai ta sake jin an bushe da dariya daga can kuma sai sukaji ance
Ku kwantar da hankalinku a sannu zaku ga mutuwa akan idanunku ba sai kun tsokanota kusa daku ba koda akazo daidai nan amaganar sai take sautin komai ya dauke aka daina jinsa
Da jin haka sai duk suka dubi junansu sukayi wata inkiya da hannayensu
Sannan suka ci gaba da tafiya ba tareda fargabar komai ba
Saida sukayi tafiya mai dan nisa sai sukaji kasa ta fara tsagewa da dukkan bangwayen dutsen kamar zasu rufto su fado kansu su dannesu
Koda ganin haka sai duk sukayi sauri suka hade jikinsu guri guda suka suka gyara rukon makaman yakinsu a hannunsu
Sannu a hankali saiga wasu irin gajerun aljanu suna fitowa daga cikinsu
Su dai wadannan aljanu 'yan kananu ne wadanda gaba daya
girmansu baifi na bijimin sa ba kuma bakunansu dogayene
kamar irin na ungulu saidai suna da tsawo sosai haka suma
kunnuwansu fala fala ne masu matukar fadi bayan haka wadannan aljanun suna da matukar tsananin yawa
Kai da kaga wadann zaka san cewa jinsine na aljanu masu shan jinin bil'adama
Kuma ko kadan basu da tausayi sannu a hankali wadannan aljanun suka gama fitowa daga cikin ginin sukayiwa su walisa kawanya
Nanfa dukkanninsu suka tsaya suka fara kallon kallo atsakaninsu
Daga can sai aljanun suka afko kansu walisa da nufin suyi musu gunduwa gunduwa da sassan jikinsu
Nantake suma su walisa suka afka kan aljanun suna masu karaji da kururuwa
Nanfa aljanun sukayiwa su walisa rubdugu aka ruguntsume da masifaffen yaki atsakiyar kogon dutsen
Sai gashi aljanun suka kaiwa su walisa farmaki da ta ko wanne bangare da sama da kasa
Domin su kacalcala su walisa su shanye jinin jikinsu
Nanf gurin y cika da karar haduwar karafa d zarar makamansu walisa sun hadu da jikin wadannan aljnun sai aji wata kara ta tashi kal !!
Kamar sautin haduwar karf da karfe tareda tartsatin wuta
Suma kuma dodannin da zara sun kawo wa su walisa hari da bakinsu idan suka kauce suka sami kasa sai kaga bakin nasu ya huda kasar gurin yayi dan karamin rami
Domin shi kansa bakin nasu kaifi ne da shi da kuma tsini kamar takobi
Nanfa gurin ya yamutsi karar karafkiyar karafa ta cika dodon kunne
Ihu tareda gurnanin aljanun ya cika kunnuwa sai ga su walisa sun zama kamar an ajiye mage a tsakiyar dubunnan karnuka
Nanfa su walisa suka barbazu atsakiyar aljanun kowanne daga cikinsu ya fuskanci bangari guda cikin mugun nufi da burin ganin ya tarwatsa su da karfin tsiya
Nanfa sukaci gaba da kai farmaki cikin bakin zafin nama ,juriya da bajinta kamar jikinsu bana jini da tsoka bane haka suka dinga ratsawa ta cikin aljanun rike da makamansu tsirara suna kai musu sara da suka ta dole suka dinga budawa kansu hanya da karfin gaske
Kamar sun kasance shaidanu amma duk wannan kokarin da sukeyi sai ya tashi abanza
Domin basa iya kashe ko guda daya daga cikin aljanun
Su kuwa aljanun burinsu kawai shine su kafa bakinsu ajikinsu walisa domin su zuke jinin dake jikinsu
Koda su walisa suka fuskanci nufin aljanun sai suka kara zage damtsensu wajen yakai aljanun
Don daga baya ma sai suka dinga daukar aljanun da hannuwansu suna ciccibar su duk girmansu suna yin jifa dasu
Amma da zarar aljanun sun sauka akasa sai kaga sun tashi sun murmure kamar wani abu bai taba samunsu ba
Saida suka shafe fiye da sa'a guda suna wannan bakin artabun
A sannan ne su walisa suka fahimci cewa tabbas idan aka cigaba da wannan yakin a haka to zasu iya gajiya
Kuma da zarar sun gaji shikenan dodannin zasu sami nasara akansu
Kodayin wannan tunani sai kawai ta kwallara uban ihu ta tarwatsa wadanda suke kusa da ita da karfin tsiya sannan ta dawo inda su sarki aryan da jaruma marfuza suke suka kawai tayi musu wata iriyar inkiya da 'yan yatsun hannunta
Sannan suka ci gaba da yakin da suke yi ba tareda sun tsagaita ba
Suna cikin wannan haline ba zato sai wani aljani ya shammacesu yasa bakinsa ya caki cinyar jaruma marfuza
Nantake marfuza ta kwallara uban ihu sakamakon tsananin zafi da zugin da taji
Koda ganin abinda ya faru sai sarki aryan ya daka tsalle daga inda yake yasa kafarsa ya naushi wannan aljanin saboda karfin dukan saida aljanin ya tashi sama sannan ya fado
Cikin sauri sarki aryan ya yagi jikin rigarsa ya daurewa jaruma marfuza wannan ciwon da yake kan cinyarta ita kuma walisa saita dinga karesu ita kadai da takobin dake ruje atafin hannunta bayan sarki aryan ya gama daurewa marfuza wannan ciwon sai duk su biyun suka mike tsaye sukaci gaba da fafata sabon azababben yaki
Wanda yafi na farko domin a wannan lokaci suna yin fadan ne domin su gano lagon wadannan aljanun ne don su gaggauta kashesu
Wani irin sabon salon yaki suka canja wanda acikinsa suka dinga tsalle tsalle da kwance kwance a tsakiyar dubunnan dodannin suna masu kai musu sara da suka ta kowanne bangare ba tare da sanin takamaiman gurin da zasuyiwa aljanun lahani ba
Ai kuwa basu dade da fara wannan sabon artabu ba wani aljanu ya sake kawowa marfuza cizo a kan cinyar daya cijeta da farko
Koda ganin abinda yake shirin faruwa batasan sanda ta daga takobinta sama ta sara ta a tsakiyar karan hancin aljanin
Aikuwa faruwar hakan keda wuya sai gurin ya dare jini yayi tsartuwa
Nantake alljanin ya sulale ya fado kasa matacce ba tareda ya koda shura ba
Cikin sauri ta juyo inda su walisa suke tayi musu ishara da wannan lagon data samo
Dajin haka sai dukkanninsu suka zage damtse suka dinga saran tsakiyar hancin aljanun babu kakkautawa
Take gurin ya cika da sautin ihun wadannan aljanu da kuma gurnanunsu
Saboda yadda su walisa suka bude kasuwar rayuka acikin tsakiyar kogon
Nanfa gawarwakinsu suka barbazu atsakiyar kogon duk inda ka duba babu abinda zaka gani face su da kuma jininsu wanda ya malale agaba daya cikin kogon kamar an bude magudanar ruwa
Kafin cikar rabin sa'a har sun gama karar aljanun 'yan kalilan ne suka tsira su din ma da sukaga uwar bari sai suka dinga bacewa suna shigewa cikin karkashin kasa don su tsira da rayuwarsu
Koda ganin wannan nasara da suka samu sai dukkanninsu suka nutsu ba tareda sun mayar da makamansu cikin kube ba
Daga can sai kawai sarki aryan ya mayarda takobinsa yace dasu
Ai da alama wadannan halittu ba zasu dawo ba domin suma yanzu sun san cewa mu ba kanwar lasa bane
Don haka dolene suyi shakkar kara tunkarar mu
Dajin wannan batu sai suma duk suka mayar da makamansu acikin kufe
Sannan jaruma marfuza ta sami guri ta zauna ta fara kokarin sakawa raunin dake jikinta magani
Da ganin haka sai suma su gimbiya walisa suka sami guri kusa da Ita suka zauna domin su huta
Sai bayan sun zauna agurin suka lura da yadda yanayin cikin dutsen ya canja zuwa duhu
Ganin haka sai suka fuskanci cewa tabbas rana ta fadi don haka dolene su sami guri su zauna domin su yada zango su kwana agurin in safiya tayi sai su tashi su ci gaba da tafiya
Da ganin haka sai walisa ta dubi jaruma marfuza tace
Sannunki jarumar gaske tabbas na gamsu cewa ke ba karamar jaruma bace don har kin wuce yadda nake zato
Dajin haka sai marfuza tayi dan guntun murmushi sannan tace
Ba haka bane nima ai dolece ta tilastani na ci gaba da wannan yakin don bana so na barku da wahala

Nandai sukayita hira atsakaninsu daga can kuma sai suka
dauko abinci sukaci suka cika cikinsu sannan suka raba
kwanciya barci domin su samu su huta idan safiya tayi sai suci gaba da tafiya
Amma sai suka raba daren gida biyu ma'ana
Gimbiya walisa da jaruma marfuza zasu kwanta suyita barci abinsu har zuwa tsakiyar dare shi kuma sarki aryan sai ya tsaya yayita zaman gadinsu
Idan tsakiyar dare yayi sai ya tashi gimbiya walisa sannan shima yaje ya kwanta ita walisan ta zauna taci gaba da gadinsu
Ita kuma marfuza sai sukayi mata uzuri domin ta samu ta dan huta saboda ciwon dake jikinta
Haka kuwa akayi kamar yadda suka tsara haka al'amarin ya kasance
Wato a wannan guri shka samu sukayita sharar barci abinsu domin su huce gajiyar dake tsakaninsu
Basu farka ba saida safiya tayi sannan suka tashi suka debi makaman yakinsu da dukkan komatsansu suka kara nausawa cikin kogon dutsen sai bayan sunyi tafiya mai nisa ne suna tafiya a wannan lokaci gimbiya walisa tana ta faman kalle kalle da dube dube acikin kogon kwatsam saiga wani katon mulmulallen dutse ya gangaro daga sama zai turmusheta kuma shi wannan dutsen daya zo akanta zai fado
Kuma idan har hakan ta faru take anan dutsen zaiyi daga daga da naman gimbiya walisa
Cikin sauri sarki aryan da jaruma marfuza suka fara kwallawa gimbiya walisa kira domin ta kauce amma ina
Ko kadan bata iya jinsu ba domin ta fada cikin tunanin dan uwanta yarima walisu da kuma mahaifinsu wato sarki fadarul munnar

ME ZAI FARU SHIN GIMBIYA WALISA TANA MUTUWA TA SILAR WANNAN DUTSEN?
DON JIN AMSA SAI MU HADU A KASHI NA GABA
DAGA NAKU
HABIBULLAH KBR

LIKE, COMMENTS AND SHARE*********-*--******HATSABIBAN SADAUKAI

CIGABAN ZUBAR DA JINI

********************-2 PART B

LBR

HABIBULLAH KBR

lokacinda su gimbiya walisa suka fara kama wannan dogon tsaunin suna hawa kansa da hannayensu kamar kadangaru
Idan ka kallesu awannan lokaci dolene su baka mamaki
Ganin yadda suke tsananin sauri har suna neman yin 'yar rigen rige atsakaninsu
Kamar masu tafiya akan doron kasa suna cikin wannan tafiyar ne saida suka shafe fiye da rabin tafiyarsu akansa kawai sai santsi ya debi sarki aryan ba tareda ya kula ba hannunsa ya zame ya sulmuyo kasa
Koda ganin haka cikin sauri sai jaruma marfuza tayi sauri tasa hannunta na hagu ta rukoshi dashi
Ba tareda ta kyaleshi ya sulmuyo kasa ba
Cikin mamaki sarki aryan ya dago da kansa sama domin yaga wanda ya rukoshi bisa mamaki sai yaga jaruma marfuza ce fuskarta cike da murmushi hannunta n dama kuma tana ruke da wani bangorin dutse
Kawai sai ya tuna cewa abaya fa yayi yunkurin kasheta
Don haka kawai sai yaji kunya ta kamashi tareda dadin nadama akan abinda yayi mata
Kawai yasa hannunsa shima ya kama wani bangorin na dutsen ya saki hannunta ya ci gaba da tafiyarsa akan tsaunin, duk wannan abu daya faru gimbiya walisa tana kallo don haka sai kawai sai tayi musu murmushi sannan ta kautar da kanta ga barin kallonsu
Daga wannan guri basu kara shafe wata sa'a guda dinba suka isa can karshen tsaunin kafin su isa karshen tsaunin saida dukkan farcunansu suka kakkarye saboda kama duwatsun da suka dingayi da hannayensu
suna gama hawa kan tsaunin sai suka tsaya cak

Please Login or Register in order to submit comment