Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuwa su marfuza sai hankalinsu ya tashi suka kara zage damtse wajen yakar kadar
Kuma a wannan lokaci babu abinda yake tayar musu da hankali face rashin samun iskar da zasu shaka akasan ruwan
Ita kuwa kadar sai ta kara haukacewa gurin kawo musu mugayen hare hare yadda duk wanda yayi kuskure ta sameshi take duk kashushuwan jikinsa zasu kakkarye kuma ya mutu
Bisa wannan daliline yasa hankalinsu ya kara dugunzuma fiyeda kowanne lokaci

Don haka koda suka fuskanci idan suka kara daukar dogon lokaci a kasan wannan ruwan zai kai ga cewa bama zasu iya jure rashin shakar numfashin da suke ba
Don haka duk su biyun sai sukayi ninkaya suka daki ruwan dukkansu suka taso samansa
Take itama kadar ta biyosu saman ruwan amma kafin ta gama tasowa su marfuza sun rigata
Don haka koda tasowarta sai duk gaba dayansu suka haye kan gadon bayanta wanda fadinsa yafi kaurin manyan bishiyar kuka guda biyu
Wannan tasowar da kadan yayi saman ruwan shine ya baiwa gimbiya walisa wacce ta tsaya a makogaron kadan damar da itama zata shaki numfashi
Domin inda ace an kara daukar wani lokaci mai tsawo a kasan ruwan za'a iya kaiwa ga lokacin da ba zata iya jure rashin numafashi ba
Har ta fada cikin kadan
Don haka sai walisa ta saka hannunta na dama ajikin kugunta
Na hagun kuma yana ruke da takobin ta kwanto wata 'yar karamar wuka ajikinta
Ta dinga cakawa ajikin makogaron kadar ai kuwa sai kadan ya dada gigicewa ya manta da batun su sarki aryan da suke zaune a saman kansa
Ya dinga birgima a saman ruwan
Su kuwa su marfuza sai suka yita sukan jikinsa da makaman da hannunsu
Saidai kuma duk da cewa suna saransa da kuma sukarsa kuma makaman nasu suna tasiri ajikinsa sai hakan ya zama na banza domin duk abinda sukeyi masa jinsa yake kamar susa suke masa ajikinsa
Ana cikin wannan haline kawai sai kadan yayi wani irin gunji mai karfin gaske
Take jikinsa ya fara rikidewa zuwa siffar wani irin rikakkiyar gamsheka
Mai kawuna biyu girmansa kadai ya isa abin tsoro da kuma firgitarwa
Koda komawarsa zuwa siffar gamshekar sai take ta kumbura jikinta tayi jifa dasu marfuza da suke kanta zuwa kan wannan tsuburin
Take dukkaninsu suka yi sama suka fado akan tsuburin
Saboda buguwar da suka yi saida suka ji kamar kashushuwan bayansu duk sun kakkarye
Take wani jini yayi fitar burgu daga cikin hancinansu da kuma bakinsu
Cikin karfin hali suka mike tsaye suna masu dafe kugunsu
Da kuma gyara rikon makamansu
Ita kuwa gamshekar sai ta taho kasan wannan tsuburin dasu marfuza suke kai
Kawai sai ya ajiye kawunan nasa guda biyu akasan tsuburin
Sai ga kawunan guda biyun sun hade sun zama guda daya
Sannan ya fara kokarin amayar da walisa daga cikin makogaronsa
Take walisa ta fado daga ciki bakin nasa jikinta duk yana faman wani irin maiko mai kauri
Tana dira a kasa sai gamshekar ya kawo mata duka da katon kan nasa da nufin yayi mata rotse
Cikin bakin zafin nama ta daka tsalle sama ta koma can gefe daya
Kan nasa ya sami duke take dutsen da yake gurin ya dagargaje kamar an nikashi
Cikin sauri gimbiya walisa ta ruga da gudun tsiya shima macijin sai ya bita suka kasa tseren gudu suka dinga hawa kam dutsen kuma har a sannan bai daina kawo mata sara ba
Koda suja kusan zuwa karshen tsuburin sai kawai su jaruma marfuza suka dako tsalle daga inda suke tsaye suka kaiwa gamshekar mugun sara da nufin su datse kansa
Koda makaman nasu suka sauka ajikinsa sai wata irin kara ta tashi kamar haduwar karfe da karfe
Cikin zafin nama gamshekar ta shammacesu su biyun ta kanannadesu
Da jelarta yadda ba zasu iya kwacewa ba kawai sai ta sulale ta koma cikin tekun da gudun gaske domin ta cinyesu aciki
Koda walisa taga abinda yake shirin faruwa ga abokan tafiyarta sai ta kwallara ihu
Kawai sai ta falfala da gudu tabi wannan gamshekar da gudu tana mai karanta wata addu'a acikin zuciyarta
Bisa mamaki sai taga tana tafiya a saman ruwan kamar akan kasa kuma cikin wani irin mugun gudu
Kafin ta riski gamshekar tuni
Tayi kasan ruwa gaba daya ta daina ganinta nantake itama gimbiya walisa ta nutsar da kanta gaba daya zuwa kasan tekun
Tabi hanyar da gamshekar tabi suka kasa gagarumin tsere da ita
Tun suna iya saman ruwa saida suka nutse can kasan tekun
Adaidai kasan ne walisa ta hango wani irin katon gida mai girman gaske
Da zuwan gamshekar wannan gidan saita shige ciki zuruf
Cikin rashin tsoro da kuma dakakkiyar zuciya itama ta kutsa kanta cikin gidan
Tana shiga cikin gidan ba zato ba tsammani sai taji an dake ta baya
Take tayi sama sannan ta tumu da kasa
Kawai sai taga wannan gamshekar ya zo ya rufe hanyar gaba daya ta yadda babu ta inda zata iya bi domin fita daga ciki
Da kuma har a sannan su marfuza suna kanannade ajikin jelarta
Don haka sai walisa ta mike tsaye cikin yarda da kanta tana mai gyara tsayuwarta
Kuma har a sannan bata daina karanta addu'o'in neman tsari da kuma neman taimakon ubangijiba acikin zuciyarta
Kawai sai gamshekar ya sake kawo mata wani dukan da dukkan karfinta
Cikin zafin nama ta kwallara kabbara da karfi sannan ta sanya takobinta ta sari jikin jelar tasa take jelar ta gutsure gabaki dayanta
Su sarki aryan suka fado daga jikin jelar acikin wani irin mawuyacin hali mai kama da mutuws da rayuwa cikin sauri walisa ta debesu ta kaisu can gefe daya
kawai sai gamshekar tayi wani irin mahaukacin gurnani
Kawai ta taso kan walisa gabaki daya suka kachame da masifaffen fada
Sai gashi a wannan lokaci albarkacin addu'ar da takeyi suna samun wadatacciyar iskar da zasu shaka kamar akan doron kasa suke fafatawar
Kuma a wannnan lokacin saita rikirkita gamshekar da wasu mugayen hare hare
Cikin kankanin lokaci ta rikitashi gidan da suke ciki ya fara rugujewa saboda artabun da suke yi
Nanfa guri ya dada rincabewa da wannan bakin artabun da sukeyi
Ana cikin haka ne kawai walisa ta karanta wata addu'a ta tofa ajikin takobinta
Sannan ta kaftawa gamshekar sara aikuwa take jikinsa ya dinga narkewa kamar mai acikin wuta ya soma ihu yana karaji
Cikin sauri walisa ta dauko su sarki aryan a kafadarta
Kafin ta fito daga cikin gidan tuni ya gama rugujewa zai fado kansu ya turmushesu gaba daya ita kanta gimbiya walisa saida wani dutse ya bugeta akan ta
Saboda buguwar da tayi ne yasata ta fadi kasa sumammiya
Ba zato ba tsammani sai ga sarki fadarul munnar akan aljaninsa sun faso ta cikin ginin gidan sun shigo sun debesu gaba daya
Sannan suka taso saman tekun suka luluka
Cikin gajimare kamar kiftawar ido
Kafin kace meye wannan tuni sun kule acikin iska an daina ganinsu gaba dayansu
Kawai sai sarki fadarul munnar ya dora kan gimbiya walisa akan cinyarsa
Yasa hannunsa yana shafa kanta, baisan sanda wata kallar tausayi ta zubo masa ba
Domin duk wannan halin data shiga shine ya sakata aciki
Wannan dalilin ne yasa yaji ya kara kamuwa da matsananciyar soyayyarta
Haka dai aljanin yayita gudu dasu asararin samaniya
Cikin kankanin lokaci ya ketare wannan tekun ya yada zango dasu acikin wani daji
Dirarsu keda wuya sai wannan aljanin ya kafa musu tanti
Sarki fadarul munnar da kansa ya zauna ya sakawa su jaruma marfuza magani ajikin ciwukan da sukaji
Sannan ya koma kan gimbiya walisa ya daure mata gurin da jini yake zuba daga goshinta
Sannan ya dauketa ya shigar da ita dasu marfuza cikin tanti
Sannan ya fito wajen tantin ya tsaya yana mai gadin su
su sarki aryan basu jima ba suka fara dawowa hayyacinsu
Marfuza ce ta fara bude idanunta koda ta ganta acikin wannan tanti sai ta mike tsaye zumbur a razane tunda bata san sanda aka kawota wannan wuri ba
Kawai sai taga duk ciwukan da suke jikinsu an diddinke musu su kuma an saka magani
Da ganin haka saita cika da mamaki cikin karfin hali ta mike tsaye tana mai dafe gadon bayanta ta leko wajen tantin
Kawai sai ta hangi wani kyakkyawan dattijo ya juya musu baya cikin gagarumar shigar yaki
Koda dattijon ya jiyo motsi a bayansa sai kawai ya juyo suka hada idanu da marfuza
Koda tayi arba da fuskar sa saita kame kyam kuma ta cika da mamaki sakamakon ganin yadda suke matukar kama da gimbiya walisa da walisu kamar an tsaga kara
Banbancin kawai shine tsufan daya farayi
Kawai sai sarki fadarul munnar yayi mata murmushi yace sannu da kokari jaruma marfuza zaifi kyau ki koma cikin tantin
Dajin haka sai marfuza ta koma cikin tantin sarki fadarul munnar
Ya bita abaya suka shige ciki
Suna isa suka iske har su walisa ma sun gama farfadowa
Koda walisa ta hangi mahaifinta saita falfalo da gudu ta rungumeshi
Sannan tace ya abbana menene ya raboka da gida kabiyo bayanmu?
Idan har burinka shine ka taya mu zuwa neman walisu zaifi kyau ka koma gida domin karkasha wahala mu kadai ma zamu iya
dajin wannan batu sai yayi murmushi yace yarinyace ke baki da kaifin tunani
Ina tabbatar miki da cewa inbadon nazo akan lokaci ba da tuni gini ya fado muku ya turmushe ku gabaki daya

Yanzu dalilin biyo bayanku da nayi shine inaso mu takaice gabaki dayan tafiyar dake gaban ku
Mu riski walisu acan inda yake domin ayita ta kare ni yanzu ban damu ba
Koda takai ga cewa zai rasa rayuwarsa akokarin rabashi da ruhin boka sahibul ukub
Dajin wannan batu sai hankalin walisa ta dugunzuma tace
Ya abbana ka daina wannan batun da kakeyi domin ina da tabbacin cewa ubangijin zai bamu taimako akansa
Ina fatan kaima zakayi imani da ubangijin musulunci domin tuni muma mun fahimci cewar tsafi karyane kuma zaluntar kaine
Babu wani ubangiji na gaskiya face Allah madaukakin sarki
Kodajin wannan batu sai jikinsa yayi sanyi yayi ajiyar zuciya
Sannan yace yake 'yata bazan tilasta miki ba akan ki bar addinin musulunci ba
Domin nima nasan akwai kamshin gaskiya acikinsa
Amma har yanzu lokacin yin imani na baiyi ba inaso ne na dada tabbatar da karfin ubangijin musulunci
Idan har ya bamu nasara akan takadirin boka wato sahibul a take zan ajiye addinin tsafi kuma na karbi wannan addini
Yanzu dolene mu zauna anan don kuyi jinyar raunikan dake jikinku
Inyaso. Daga baya sai mu tashi gabaki dayanmu mu nufi can fadar tasa
Domin ban baro gidaba sai da muka tsaurara bincike nida boka na
Kuma da kyar da makyarkyata muka gano inda fadarsa
Take
Duk wannan zance da sukeyi ashe aljanin daya dauko sarki fadarul munnar yanaji
Koda yaji inda suke shirin zuwa sai ya fashe da kuka
Ya fara rokon cewa sarki fadarul munnar yayi masa rai domin bazai iya zuwa fadar yarima walisu ba
Saboda tsananin bala'in da yake hanyar fadar*************HATSABIBAN SADAUKAI

CI GABAN

ZUBAR DA JIN

*******************6 PART A

********************LBR

HABIBULLAH KBR

Koda sarki fadarul munnar yaga yadda hankalin aljani zarikul laham ya tashi
Sakamakon jin cewa zai daukesuu ne ya kaisu can fadar yarima walisu
Bai san sa'addaya tuntsure da dariya ba yana nuna zarikul laham da dan yatsansa yana ci gaba da dariyar
Sai da yayi dariyar ta isheshi sannan lokaci guda kuma ya tsuke bakinsa ga barin yin dariyar
Yace dashi
Gaskiya ka bani kunya duk da kasancewarka matashi kuma mai jini a jika amma kace kana tsoron mutuwa
Ko mu da muke bil'adama bamu sa karaya ba acikin zukatan mu
Ka tuna fa cewa wannan aiki da za'ayi yafita daban da wadanda muka sabayi abaya
Domin zamuyi shine domin ceton duniya daga kangin zaluncinsa
Ya zame maka tilas ka daukemu dukkanmu ka kaimu can fadarsa
Domin ceto al'umma daga kangin da yake shirin sakasu nan gaba
Mu yanzu ashirye muke da muyi wannan tafiyar koda kuwa hakan zai zamo sanadin ajalinmu
Idan kuwa kaki yarda ni da kaina zan yakeka da kaina
Dajin wannan kalami sai aljani zarikul laham yaji duk wani tsoro ya gudu daga cikin zuciyarsa
Kawai saiyace
Ka gafarta mini ya shugabana kuskure ne yasa na firgita da farko
Amma yanzu ji nake kamar zan iya yakar sa ni kadai
Kodajin wannan batu sai sarki fadarul munnar yayi murmushi
Ko kaifa abin kunyane agareka ace kana tsoron mutuwa

Da gama fadin haka sai ya juya inda gimbiya walisa ke
Ya dora hannunsa akan sai ki cire duk wani tsoro daga zuciyarki
Kuma kisa a ranki cewa wahalar da kikasha abaya kamar share fagece
Domin yaki yana nan gaba tun kina marmarinsa harsai kin kosa da agamashi
Gaskiya dolene a jinjinawa SADAUKI HASSANUL BASARI

Domin shi kadai ya tunkari duk wani kalubale na boka sahibul ukub
Kuma har ya sami nasara akansa ba tareda ya nemi taimako daga gurin kowa ba
Dolene daga yanzu mu dauki kwararan matakai tun daga yanzu
Domin tunkarar gagarumin aikin dake gaban mu, dajin wannan batu sai walisa tace kwarai kuwa yakai abbana
Su kuwa su sarki aryan da jaruma marfuza sai kawai suka bude bakunansu suna mamakin yadda sarki fadarul munnar ya iya isowa akan lokaci da kuma yadda suke tsananin kama kamar an tsaga kara
Don haka sai sarki aryan yaji ba zai iya jurewa ba dole ne yayiwa fadaul munnar tambaya
Kawai yace dashi
Yakai wannan babban namijin duniya ina da wata tambaya guda agareka kuma ina fatan zaka amsa mini ita ?
Kodajin haka sai fadarul munnar yace kwarai kuwa ka fadi duk irin tambayar da kake da ita ni kuma nayi alkawarin amsa maka ita indai har ina da amsar
Sarki aryan yace
Kai kuwa tayaya ka iya isowa wannan guri adaidai lokacin da muke shirin mutuwa akasan teku?
Dajin wannan tambaya sai sarki fadarul munnar ya bushe da dariya daga can kuma saiya tsuke bakinsa ga barin yin dariyar yace
Ai duk wannan abinda nayi bai kamata kuyi mamaki akansa ba
Domin dukkanku kunsan karfin sihirin da nake dashi
Saidai kuma duk wannan bai kai aikinda kukayi abin al'ajabi ba
Domin kun nuna jarumtakar da ba kowanne jarumi ne zai iya yin kamarta ba
Saboda tsawon lokacin da kuka dauka akasan teku kuna fafata yaki
Yanzu haka abu guda daya ne yake dada bani tabbacin cewa zamu sami nasara akan boka sahibul ukub wannan abu kuwa ba komai bane face
Addinin musuluncin da kuka karba nasan cewa shine kadai makamin da zai taimaka mana wajen tunkarar sa
Domin tun a wancan zamanin shine makamin da ya hanashi samun danar cika burinsa
Koda yazo daidai nan azancensa sai aryan yace indai kuwa har kayi imani da ubangijin musulunci zai taimake mu
To mai zai hana ba zakayi imani dashi ba ?
Kodajin wannan tambaya sai fadarul munnar ya hade fuskarsa kamar wanda yake cikin fushi
Daga can kuma sai yayi murmushi yace
Lokacin da zaka san wannan dalilin baiyi ba amma nayi muku alkawarin muddin muka sami nasara akansa to a take anan zan karbi addinin musulunci
Yana gama fadin haka saiya tsuke bakinsa
Bai kara cewa komai ba ya fice daga cikin tantin da suke zaune
Ya koma waje ya cigaba da aikin tsaron lafiyarsu
Saida suka shafe kwanaki goma sha daya suna zaune a wannan guri
Sannan ciwukan jikinsu suka warke sumul don haka sai suka hada kayayyakinsu
Domin ci gaba da tafiya kowanne daga cikinsu a wannan lokaci
Yayi gagarumar shigar yaki domin su nufi can fadar da yarima walisu yake zaune
Ba tareda bata lokaci ba suka haye bayan aljani zarikul laham
Shi kuma ya bude fuka fukansa ya tashi dasu sama kamar kiftawar ido haka ya danna kansa cikin gajimare ya bace bat aka daina hangoshi
Cikin kankanin lokaci ya dinga shafe tafiya mai nisan gaske
Suna tafiyar suna hira abinsu kamar babu wani abu da yake damunsu
Saida suka shafe sa'o'i goma suna tafiya suna dada keta hazo domin zuwa fadar da yarima walisu yake zaune
Domin a wannan lokaci hatta fadar tasa ya canjata daga inda take ya koma can yammacin duniya bisa kan wani dogon tsauni
Kafin mutum ya iya isa inda wannan tsaunin yake dolene ya fuskanci tarkuna kala kala
Masu cike da ruwan bala'i akan hanya ,domin dolene
ka ratsa ta cikin wasu sihirtattun dajijjika masu cike da
nau'ikan bala'i kala daban daban kuma abinda zaka
tarar acikin daji na biyu yafi abinda yake daji na farko bala'i
Haka suke rukuni rukuni dole saika wuce ta wadannan
tarkuna sannan zaka isa can fadarsa inda kuma nane yafi ko'ina hatsari da kuka bala'i
Saboda komai na wannan fada ya fita da ban da wanda ke cikin dajijjikan dake baya
Abune mawuyaci mutum ya iya ratsawa ta cikin wadannan dajijjikan har ya iya shiga cikin fadarsa ba tareda ya rasa rayuwarsa ba

WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GASU SARKI FADARUL MUNNAR BAYAN SUN TASHI DA NUFIN ZUWA FADAR DA YARIMA WALISU YAKE ZAUNE

**** ******* *********

A can kuwa bangaren yarima walisu kuwa tun daga lokacin daya baro can rijiyar da abin bautarsa yake
Wato gunki larazub kamar kiftawar ido haka ya bayyana abakin fadarsa wacce yake zaune acikinta
Da zuwansa sai ya daga hannunsa na hagu ya dunkuleshi
Take sai fadar tayi bindiga kamar ansa mata nakiya
Ta ruguje gabaki dayanta da komai da komai na cikinta sannan ta kama da wuta ta kone kurmus
Faruwar hakan keda sai ya bushe da dariya sannan ya juya ya bar wannan dajin gabaki daya yana mai cewa yanzu na gama da wannan fadar wani sabon mulkin zan kafa
Cikin kankanin lokaci ya isa can karshen duniya bangaren yamma
Cikin wani kungurmin daji mai cike da abubuwan firgitarwa
Da isarsa tsakiyar wannan dajin saiya nuna wani dan karamin dutse dake tsakiyar dajin
Take wannan dutse ya kumbura alokaci guda kamar an buga masa isa
Ya zama wani irin zabgegen tsauni tareda tangamemiyar fada. Asamansa
Duk acikin abinda bai wuce dakiku goma ba
Ita kanta wannan fadar ba karamin girma ne da itaba

Kai tsaye ya tashi sama kamar tsuntsu mai fuka fuki ya haye saman sabuwar fadar tasa hawansa keda wuya sai ya nuna iyakar dajin da sandar sihirin dake hannunsa
Yin hakan keda wuya sai ga wasu irin mugayen halittu sunata ciccidowa daga cikin karkashin kasa marasa adadi
Wanda idan mutum yayi ido biyu dasu take zai iya zaucewa idan har baida dakakkiyar zuciya
Kuma wadannan halittu jinsi daban daban ne ba dayaba
Bayyanarsu keda wuya sai duk suka dinga warewa kowanne yana zuwa inda jinsinsa yake suna dunkulewa guri guda
Suna gama haduwa duk sai sukayi sahu sahu suka durkusa suka yiwa yarima walisu sujjada
Faruwar haka keda wuya sai ya tuntsure da dariya ya kallesu gaba dayansu da kwayar idanunsa
Nantake wata iska mai karfi ta fito daga cikin idanunsa
Ta shuri wadannan halittu gabaki dayansu ta rarraba musu mazauni
Sannan ya juya ya shige cikin fadar tasa wacce ta kawatu ainun da kayan alatu fiye da wadanda suke cikin tsohuwar fadar tasa
Saidai kash !!!
Komai na wannan fadar kyan dan maciji ne dashi idan har kayi kuskure akansu
Komai da yake cikin tsohuwar fadar tasa a kwaishi acikin wannan
Harma yafi wancan na da din amfani da karfin sihiri
Yana isa tsakiyar fadar saiya iske karagarsa ta tsafi wacce aka san'anta ta da zallan haske kai tsaye ya haye kan wannan karagar tareda fuskantar madubinsa na tsafi wanda aka sana'anta shi da zallan dutsen lu'u lu'u sai sheki da walwali yake
Yana dallare idanu saboda haskensa
Zamansa keda wuya saiya shafi madubin da tafin hannunsa
Take sai hoton su sarki fadarul munnar dasu gimbiya walisa ya bayyana ajikinsa tun sanda wannan kadar sihirin ya farmakesu a tsakiyar teku suka fafata yaki dashi har suka kashe shi
D kuma sanda suka taso da nufin zuwa sabuwar adarsa domin yakarsa
Da ganin wadannan abubuwa saiya bushe da dariyar mugunta
Domin yasa cewa su da kansu suke kawo kansu ga halaka
kuma suna shirin hutar dashi ne saboda yana da tabbacin muddin suka taka kafarsu suka shigo cikin iyakar dajinsa babu guda daya daga cikinsu wanda zai tsira da rayuwarsa
Saboda yasan irin bala'in daya zuba a cikinsu
Saida yayi dariyar ta isheshi sannan yace
Hakika yau shekaru dubu biyu da 'ya'ya zasu maimata kansu
Kamar yadda a wancan lokacin HASSANUL BASARI ya shigo cikin fadata ya yake ni
Saidai kuma a wannan karon nine zanyi nasara domin har a bada bazan sake yarda na fadi kasa ba
Harsai na mallaki duniya ta dawo zuwa karkashin ikona don a nan gurin zan zauna na jira isowarsu nan cikin fadata idan har sun cika HATSABIBAN SADAUKAI
Kuma koda ma sun sami damar shogowa cikin fadata da hannuna zan kashesu gabaki daya na shayar da jininsu ga gunki larazub
Yana gama fadin haka saiya mika hannunsa kan wani teburi dake can wani bangare na fadar
Take hannun nasa ya kara tsawo kamar ana jansa yaje har inda wannan teburin yake ya dauko wani kofin zinare dake ajiye akansa
Kawai saiya kafa kofin a bakinsa ya shanye ruwan da yake ciki
Shan ruwan keda wuya sai yaji ya kamu da wani matsanancin barci
Alhalin rabonsa dayin barci tun a ranar daya shiga jikin yarima walisu
Shi kansa yayi matukar mamakin wannan al'amari don haka koda yaji wannan sauyin yanayin
Kuma shima ya tabbatarwa dakansa cewa yana da bukatar ya sami hutu na tsawon lokacin daua dauka yana barcin
Sai kawai ya sanya hannunsa akan fuskarsa ya shafata
Take ya rabu gida biyu, ma'ana wani yarima walisun ya sake fita daga jikinsa kuma kamarsu daya sak babu banbanci
Kuma duk abinda shi yarima walisun na gaskiyar zai iya yi to shima zai iya
Da bayyanar wannan sabon walisun
Sai na gaskiyar yayi murmushi yace yanzu nima zanyi barci na mai dadi
Ba tareda an sami wani kuskure ba alikackm da nake barci
Yana gama fadin haka sai wannan karagar tasa ta rikide ta koma katon luntsumemen gado
Shima na haske mai taushin gaske ba tareda fargabar komai ba ya kwanta kwanciyarsa keda wuya sai barci ya daukeshi
Shi kuma sabon yarima walisun sai ya sami guri ya tsaya cak ya kurawa allon tsafin ido yana kallon su sarki fadarul munnar
Yana cikin kallon ne kawai yaga har sun kusan isowa bakin iyakar daji na farko
Da ganin haka sai kawai shima yayi dolene ya darsa musu da tsoro acikin zukatansu
Da gama wannan tunani sai ya runtse idanunsa ya karanta wasu dalasiman tsafi
Sannan ya bude idanun nasa ya nuna su acikin madubin tsafin da babban yatsansa
Take wata irin guguwa tayin fitar burgu daga cikin da yatsan nasa ta shiga cikin madubin tsafin nasa

Su kuwa su sarki fadarul munnar a wannan lokaci suna bayan aljani zarikul laham
Yana ta tsala gudu dasu a sararin sama a wannan lokaci kawai sai aljani zarikul laham yaji kamar an daure masa dukka fuka fukansa
Sannan sukaji wata irin kwalleliyar tsawa daga sama wadda saboda karfinta
Sai da sukaji kamar zuciyoyinsu zasu fashe su faso kirazansu su fito waje gabaki daya suka manta da wasu addu'o'i saboda dama kuskuren da sukayi kenan tun farkon tasowarsu hira kawai sukeyi sun shagala ga barin addu'o'i acikin zukatansu
Kwatsam ba zato ba tsammani sai sukaga kasa dare ta haifar da wani wawakeken rami mai zurfin gaske
Wanda basa iya ganin karshensa saboda zurfinsa kasan ramin kuwa wutace takeci ganga ganga har tururinta yana iya laso inda suke daga cikin ramin saboda matukar zafinta
koda ganin wannan al'amari sai dukkaninsu suka shiga cikin taitayinsu domin suga me zai faru a wannan guri
Shi kuwa sarki fadarul munnar saiya dakawa aljani zarikul laham tsawa
Yace kai kuma tsayuwar me kakeyi anan kaja mu muyi
Gaba daga nan inda muke mubar wannan guri ko bakaga irin hatsarin da yake gurin bane
Dajin wannan batu sai kwallar takaici ta zubo daga cikin idanunsa
Yace ya shugabana kayi hakuri anan gurin ba zan iyayin
komai ba domin yanzu haka ji nake kamar an daure
mini jikina da manyan sakokin bakin karfe ba zan iya komai ba face yadda shi wanda yayi wannan sihirin ya sarrafa ni
Dajin wannan batu sai ran sarki fadarul munnar ya baci
Take shima ya fara karanto nasa dalasiman tsafin cikin wani irin birkitaccen yare irin nasu na matsafa faruwar hakan keda wuya sai jikinsa ya fara karkarwa kamar

Please Login or Register in order to submit comment