Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ukub zai iya tasowa
harma ya nemi hanyar da zai fishi karfin sihiri
Sai take ya
sihirce kogon tsafin tsafin ta yadda koda bayan ransa bai
isa ya shiga cikin kogon ba
Ba'a dade da yin haka ba shine sahibul ukub ya kashe
mahaifinsa don ya mallaki sirrikan tsafinsa kuma duk saidaya
mallaka abu dayane bai mallakaba wannan abin kuwa ba komai bane face wannan kogon sirri

Likacinda su sarki aryan suka bayyana tsulum acikin wannan kogon sirri
Kai tsaye sai suka wuce da gimbiya walisa walisa kan wani
dan karamin gado na katako suka kwantar da ita akansa
Cikin sauri aryan ya dubi marfuza yace menene ya faru ga gimbiya walisa
Nantake marfuza ta kwashe labarin komai ta fada masa ba
tareda ta boye masa komai ba
Tun daga sanda dakaru suka kamo gimbiya walisa suka kaita
kurkuku har zuwa lokacin da yarima walisu ya bayyana
harda sanda taje ta dauko gimbiya walisa daga cikin kurkukun
Daga karshe ta sanar dashi cewa tayi mamakin yadda taje ta
tarar da gimbiya walisa afarke alhalin an sanya mata cutar dogon barci
Kodajin wannan labari yayi sarki aryan ya girgiza kansa yace
Aikuwa yanzu take zamuyi mata magani acikin kogon dutsen
nan domin ta dawo cikin hayyacinta
Kuma Ina da tabbacin cewa babu wanda ya farkar da ita
daga wannan cutar barcin face yarima walisu
Domin shine kadai zai iya karya sihirin tsafin 'yar uwar ki sarauniya suzaila
Cikin mamaki marfuza ta dubeshi tace tayaya kasan wannan sirri alhalin baka gani da idanunka ba
Bayan haka ta wacce hanya kake ganin zaka iya yi mata
magani idan har ta tabbata yarima walisu ne ya saka mata
wannan cutar ta kamewar jijiyoyin jiki?
Dajin wadannan tambayoyi sai ya gyada kansa yace tabbas
hakane banida sihirin yarima walisu
Amma inaso ki sani wannan ba aikinsa bane aikin 'yar uwar ki ne
Shi nasa aikin kawai shine farkar da ita daga dogon barcin
da aka saka mata don taga yadda yadda zai bazar da birninku gaba daya
Shi tun farko dama bashi da burin hallakata don haka nema ya kyaleta tun a karonsu na farko da ita .
Dan gane da tambayar ki ta farko kuwa yanzu zan nuna miki amsarta ta zahiri akan idonki

Yana gama fadin haka sai yasa hannuwansa ya tashi gimbiya walisa zaune daga kwanciyar da take
Duk da cewa idanunta abude suke amma ko kadan ba zata
iyayin magana ba saboda karfin gubar da take jikinta
Sannan ya karanta wadansu dalasiman tsafi guda uku ya tofa acikin kwayar idanunta

Nantake wani haske ya fito daga cikin idanun nata ya daki bangon kogon
Sai ga hoton komai ya bayyana ajikin kogon tun daga
sanda yarima walisu ya bayyana akanta har da irin tattaunawar da sukayi da ita
Sannan kuma hoton komai ya bace shima hasken ya dauke

Sarki aryan ya juyo ya fuskanci jaruma marfuza yace
yanzu dai kin gani da idanunki kuma kin tabbata yarima walisu bashi bane ya sanya mata wannan cutar ba
Game da tambayar ki ta biyu kuwa shine hanya daya zamubi mu karya wannan sihirin da yake jikinta
Hanyar kuwa itace dolene mu mu bada jinin jikinmu
mu zubashi acikin kwalba sannan mu dura wannan garin maganin aciki mu bata tasha

Kafin ya gama bayanin da yake mata tuni tasa waata
'yar karamar wuka ta yanki hannunta da ita
Sannan
ta zaro kwalba acikin jakarta ta zuba jinin aciki
Da ganin
haka sai shima sarki aryan ya sa wukar ya yanki nasa hannun
shima ya zuba jinin a cikin kwalbar data zuba nata jinin
Yace da mata
Gaskiya nayi mamakin yadda kika kasance mai saukin kai
sabanin 'yar uwar, tunda har kika sake aminta dani duk da
cewa nayi yunkurin hallaka ki abaya
Ina mai neman afuwarki akan wannan kuskuren dana aikata
Kodajin haka sai take fuskarta ta fadada da wani murmushi tace
Menene zai hanani yarda da wanda na kasance ina mutuwar kaunarsa fiye da rayuwata

Ka sani cewa koda yau dinnan na mutu to zan mutu cikin
farin cikin ganin jinina da naka sun hadu aguri daya
Dajin abindata fada sai sarki aryan yayi shiru bai sake bata amsa ba
Kawai sai ya bude tafin hannunsa yayi wasu siddaru
faruwar hakan keda wuya saiga wani kullin garin magani ya bayyana atafin hannunsa
Cikin sauri ya ya kwance maganin ya durashi acikin kwalbar jinin nasu
Sannan suka bude bakin gimbiya walisa suka dura mata shi
Ai kuwa bata gama shan maganin ba sai gashi ta fara yin
aman dafin daya shiga jikinta har dama na harbin da kunama tayi mata a yayin fafatawar su
Sannu a
ahankali sai gashi ta fara motsa jikinta,
Daga can kuma sai gata ta mike zaune sosai ta zauna da kafafunta
Kawai sai ta juyo ta kalli su sarki aryan da jaruma marfuza tace
Ina mika godiyata agareku bisa ceton rayuwata da kukayi..
Caraf sai marfuza ta tari bakinta tace ni bana bukatar ki gode mini
Domin tun farko nice ya kamata na gode miki tunda kece kika fara ceton rayuwata lokacin da nake gangaren mutuwa
Dajin haka sai walisa tace duk da haka dolene na baki hakuri bisa abin daya sami birninku

Domin duk nice silar haka in ba don na sauka acikinsa
ba da haka bata faru ba kuma ina mika ta'aziyata agareki
bisa ga rashin 'yar uwar ki da kikayi
Koda jin haka sai kwayar idanunta suka ciko da kwalla tace
Duk abindaya faru baki da laifin komai 'yar uwatace ta ta janyo domin sune suka daukoki da kansu alokacin bakya cikin hankalinki
Yanzu dai zama bai kamamu ba dole ne mu ci gaba da
bibiyar dan uwana don ganin inda ya nufa kuma mu hanashi aiwatar da shirinsa na gaba
Dajin haka sai mamaki ya kama ya kama marfuza tace da ita
Shin dama wannan azzalumin mutumin dan uwanki ne kuma kuna da dangantaka dashi?
Walisa tace
Kwarai kuwa maganarki haka take sai dai shi dan uwana
yarima walisu mutumin kirkine kuma tare aka haifeni dashi kuma muka karbi horon yaki tare

Saidai kuma duk wannan abinda yake faruwa shima bada sanin sa yake ba
Take ta kwashe labarin komai ta fada mata

Sarki aryan ya dubi gimbiya walisa yace
Yake wannan
jaruma akan me zaki ce mu fita daga cikin kogon nan bayan
kinsan cewa yanzu haka dan uwanki yana nan yana neman
mu kuma nan gurin da muke shi guri mafi sirri da zamu zauna acikinsa kuma mu tsira daga sharrinsa
Dajin haka sai take walisa tayi murmushi tace
Ai kuwa ni
dolene na fita daga cikin wannan kogon tunda har na riga na sami lafiya domin yanzu ba wasan buya na fito ba
Idan har na zauna anan ba zan taba cikawa mahaifina burinsa ba
Tana gama fadar haka sai kawai ta runtse idanunta tareda buda tafin hannunta ta karanta wasu dalasiman tsafi masu matukar wahalar karantawa
Nantake take saiga duk makaman yakinta sun bayyana akan tafin hannun nata
Koda ganin haka sai sarki aryan ya dubeta yace ai shikenan muma a shirye muke da muyi karo da kowanne irin kalubale koda kuwa zamu iya rasa rayuwar mu
Koda gama fadin haka sai duk suka hada hannuwansu guri daya atare suka suka karanta dalasiman tsafinsu take sai wata iriyar guguwa mai karfi ta ta taso ta debesu gaba daya tayi sama dasu

KUYI HAKURI A CIKIN KWANAKIN NAN INA EXAM NE BA KODA YAUSHE NAKE ZAMA RUBUTU BA SHI YASA KUKAGA INA YIN TSALLAKE BA KAMAR YADDA NA SABA KWANA 3 BA
SHIN INA SU WALISA SUKA NUFA?

WANNE HUKUNCI YARIMA WALISU ZAI DAUKA ?

MU HADU AKASHI NA GABA
LIKE AND COMMENTS*************HATSABIBAN SADAUKAI

CIGABAN ZUBAR DA JINI

****************1 PART C

LBR

HABIBULLAH KBR

Lokacin da iska mai karfi ta zuke su gimbiya walisa basu bayyana
ako ina ba sai a kan turba cikin wani irin daji mai tsananin
yawan sahara wanda basa iya ganin karshenta
Kuma
awannan lokacin ana tsaka da zafin rana dajin gaba daya ya cika da zafin rana
Hatta ita kanta iskar da take kadawa agurin zafi take fitarwa
da turiri saboda tsananin zafin rana
Inda ace za'a ajiye danyen kwai agurin cikin dakika uku zai dafa kansa
Babu abinda idanu suke iya gani face dogayen doron
sahara wadanda sukayi tsiri asama kuma dole sai anbi ta kansu domin cigaba da tafiya

In badon da takalma masu tudu ajikin kafafunsu ba da basu
isa su iya jurar tafiya acikin wannan saharar ba
Koda bayyanar
su a wannan guri sai duk suka dago da idanunsu suka kalli
junansu suna mamakin bayyanar su a wannan guri mai matukar wahalar rayuwa
Abinda basu sani ba shine haka ka'idar wannan kogon tsafi yake
Duk sanda nemi tsira alokacin da kake daf da hallaka to dolene idan ka fita daga cikinsa ya kaika guri mai hatsarin gaske
Wannan shine dalilin dayasa suka tsinci kansu acikin wannan daji
Cikin sauri gimbiya walisa ta kalli sarki aryan tace
Shin acikinku akwai wanda yasan cikin nahiyar da muke?
Dajin wannan tambaya sai duk suka gyada kawunansu alamar basu sani ba

Kawai saita girgiza kai tace yanzu dai na fuskanci cewa mun
tsirane ta wani fannin amma awani bangaren bamu tsira ba
Don haka ya zame mana dole sai munyi kula kuma munyi taka tsantsan da rayuwarmu
Kafin ta gama fadin haka tuni tuni jaruma marfuza ta shige gaba ta ci gaba da tafiya

Sarki aryan da gimbiya walisa ma sai duk suka bita abaya ba tareda sanin inda zasu je ba

Ai kuwa suna fara tafiyarne duk jikinsu ya fara fada musu
Domin wannan saharar ta fita da ban da wacce suka sani
domin ita tana da matukar laushi
Hakan ne yasa gaba daya dudduniyar kafarsu take nutsewa
acikin ta da zarar sun daga daya kafar tasu
Zafin gurin
kuwa ya dinga ratsa har cikin takalman nasu yana yana laso kafafun nasu

Wohoho hakika Ita wahala ba'a sabo da ita domin duk sanda
ka shiga cikin ta saika raina irin wacce kasha abaya
Basu dade da fara tafiyar ba duk sukaji jikinsu ya fara gajiya
Kafafunsu sun fara gajiya da tafiyar da suke kuma babu
abindake daga musu hankali face idan suka hangi gabansu
suga basa iya ganin karshen saharar saidai doron da saharar
tayi masu mugayen tsayi agabansu
Bayan haka ga itama iska wacce take kadawa acikinsa mai zafin gaske da kuma hucin zafin da take fitarwa

Ita kanta wannan iskar ta isa ta hana abubuwa masu rai rayuwa acikin wannan daji

Haka dai su marfuza sukayita tafiya acikin saharar ba tareda
dayansu yace da daya kala ba kamar wadanda aka daurewa
bakunansu an rasa wanda zaice da wani kala
Ba komai
ya jawo hakanba face tunane tunanen da suke yi mai zurfi
kan wacce irin kalubale zasu fuskanta acikin wannan dajin

Saida suka shafe sao'i hudu suna tafiya acikin wannan
dajin bisa kafafunsu alokacin ne sukaji wata iriyar yunwa
mai karfi ta kama cikinsu a yayinda sukaji cikin nasu yanata murda musu
Bisa dole duk suka tsaya suka sami guri da nufin su zauna su dan huta
Har sun zauna ba shiri sai suka mike tsaye saboda ji sukayi
zafin gurin ya kama mazaunansu kamar zai konasu
Sarki aryan ya kallesu yace aikuwa dole babu yadda zamuyi
saidai muci wannan abincin a tsaye Yana gama fadin haka sai ya kwanto jakar guzirinsa ya bude ya fito da abinci
Kawai sai yaga jaruma marfuza ta kura masa ido sai a sannan ya tuna cewa ita bata taho da abincin guziri ba
Kawai sai ya kalleta yayi mata murmushi akaron farko yace
Bai kamata naci wannan abincin ni kadaiba dole sai kinzo munci.
Dajin haka sai taji wani farinciki ya shiga zuciyarta
Don haka
batareda musu ba saita tafi wajensa
Har takai hannu da zummar ta faraci sai taji gimbiya
walisa ta ruke hannunta ta baya Cikin sauri ta juyo da kanta ta
kalleta sai taga walisa tayi mata murmushi sannan tace

Haba yake wannan budurwa mai karamci ai tunda kika ceci rayuwata
Nima ya zame mani dole na baki kulawa kamar yadda kika
sayar da rayuwarki kika ceci tawa Ina neman alfarmar
kizo muci nawa abincin tare kodajin haka sai suka raba mata
hankali ta rasa ina ya kamata taje
Na farko dai shi sarki aryan tana matukar kaunarsa kuma cin
wannan abinci tare dashi zai kara mata kusancine a gareshi

Ita kuwa gimbiya walisa ta ceci rayuwarta alokacin da shi
sarki aryan yake kan gangarar halakata
Nanfa suka raba mata tunani ta rasa gurin daya kamata taje
Daga can sai tace ai wannan abu mai sauki ne duk sai mu
hada abincin aguri guda sannan muci
Kodajin wannan hukuncin nata sai sukayi murmushi sukace kwarai kuwa maganarki gaskiya ne
Ba tareda gardamar komai ba suka hada abincin nasu
suka tsaya atsayen sukaci suna nishadi tsakanin su kamar sun kasance 'yan uwan juna
Cikin kankanin lokaci suka cinye abincin suka sha ruwa sannan suka ci gaba da tafiya

Saida la'asar ne kwatsam suna tafiya sai suka ji wata iriyar
guguwa mai karfi tana kadawa acikin saharar kura ta turnuke
cikin sararin samaniya sai kawai suka hango sahara tayi tsiri asama ta nufo inda suke da gudun gaske
Koda sukayi arba da wannan guguwa sai suka ruga da gudu
domin tserewa wannan guguwar
Kaico hakika wahala bata da dadi kuma duk sanda mutum yaga
hallaka zai iyayin abinda bai taba zaton yinsa kuma kaima mai
karatu idan aka sanar dakai zaka iya zaton cewa karyane
Nana aka kasa azababben tseren gudu tsakanin su da wannan
guguwar domin ceton rayukansu
Gaba daya ma sai suka manta da laushin wannan saharar
Suka dinga gudu kamar suna tafiya akan doron kasa kamar kiftawar kibiya

Domin suna gudun ne kuma suna hadawa da amfani da karfin sihirinsu

Duk da cewa suna amfani da sihirinsu saiya tashi abanza
domin duk sanda suka juyo bayansu sai suga guguwar tana daf da riskarsu
Kai duk da karfin gudun nasu duk sai ya zama na banza domin guguwar kara kusantarsu take

Koda suka fahimci cewa lallai wannan gudun ba zai kai
musu ba sai suka fara tunanin wacce hanya ya kamata
su bi domin suga sun kubuta daga sharrin wannan guguwar
Nanfa duk su ukun suka fara magana da junansu cikin alkaluman tsafi domin ko kadan bakinsu baya motsawa
Kuma ba tare da suna kallon junansu ba
Walisa ce ta fara magana cikin alkaluman tsafin tace
Kaicon mu da wannan gudun da mukeyi wanda bamu da tabbacin tsira acikinsa
Dolene mu yi tunanin hanyar daya kamata mubi domin ceton rayukan mu
Dajin haka marfuza tace gaskiya ne maganarki amma
acikinku wacce hanya kuke ganin zamubi domin muga mun sami nasarar kubuta?

Caraf sai sarki aryan ya tari bakinta yace akwai hanya
guda daya wannan hanyar kuwa itace dolene muma
mu kirkiri tamu guguwar wacce zata je ta tunakari waccan dake bayanmu
Dajin wannan shawara tasa duk sai suka amince da ita
Nantake suka hada baki a tare suka karanta dalasiman tsafi
suka bugi kasa da hannayensu Faruwar hakan keda wuya
sai nantake wata iriyar guguwa mai karfin gaske ta taso daga bangaren da suke
Itama ta nufi wacce ke bayansu cikin azababben gudu har
tana dunkulewa asama tamkara curin nakiya
Tana gudu
tare dafitar da wani sauti mai karfi
Wohoho aikuwa koda guguwoyi guda biyun suka hadu sai
wata irin sautin kara mai karfi ya tashi tareda tashin
walkiya har saida su walisa suka saka hannuwansu suka toshe kunnuwansu dasu domin gudun kar kunnuwan nasu su sami matsala

Cikin sauri suka dakata da gudun da sukeyi suka juyo bayansu
domin suga abinda yake faruwa
Ba komai suka ganiba face haduwar goguwoyin guda biyu
atsakiyar fili suna rigima da junansu
Kamar sun kasance mutane ko kuma dabbobi

Daga can kuma duk su biyun sai sukayi bindiga suka tarwatse
Ganin wannan abu daya faru sai duk sai suka ji farinciki ya turnukesu
Suka tsaya agurin suna faman haki saboda gudun da suka sha
Abinda basu sani ba shine har yanzu tsuguno bata kare
musu ba akwai sauran aiki agabansu ko kuma ince fafatawa atsakaninsu
Bayan dakiku kadan da tarwatsewar wadannan goguwoyin sahara guda biyu

Sai kuma suka hangi wata sabuwar kurar ta sake turnukewa asama
Nanfa suka zuba ido domin suga menene zai faru awannan guri
Sannu ahankali sai sukaga wannan kurar saharar ta soma dunkulewa guri guda kamar curin bishiyar dabino
Yana karawa kansa girma da fadi kuma suffar jiki tana kara bayyana ajikinsa
Kafin cikar wasu dogayen dakiku tuni wannan saharar ta rikide ta koma siffar wani katon
mummunan maridi mai matukar girma, tsawo da kuma kauri
wanda tunda su walisa suke arayuwarsu basu taba ganin halitta mai matukar girmansa da kwarjinininsa ba
Koda halittar ta gama cika suffar wannan maridi sai duk su ukun suka kalli junansu cike da mamaki acikin zukatansu
Jaruma marfuza bata san lokacin data ce hakika yau mun kawo kanmu tsakanin mutuwa da rayuwa ba
Dolene sai wata babbar sa'ar ce zata fitar damu daga cikinsa
,dajin haka haka sai walisa tace kwarai kuwa, maganarki gaskiya ce
Kogon nan da muka shiga ba kogon tsira bane saidai akirashi da kogon hallaka

Shi kuwa sarki aryan shiru kawai yayi yana kallonsu
domin ya kasa cewa komai saidai nadamar shiga cikin wannan kogon da sukayi kawai yake acikin zuciyarsa
Suna cikin wannan halinne kawai sukaji maridin ya bushe da wata mahaukaciyar dariya mai karfin gaske
Wacce ta amsa kuwwa da amo acikin dajin gabaki dayansa
Wani irin tururin zafi ya fita daga cikin bakinsa kamar an bude ruwan da yake tafasa

Cikin sauri duk su ukun suka juyo suka kalleshi alokacin da yake kyakyata wannan dariyar

Kawai sai gani sukayi wannan maridin ya wangame bakinsa
Cikin wata iriyar kakkausar murya mai kama da kukan jaki
Ya sake bushewa da dariya akaro na biyu yayi tayi kamar
bazai dainaba daga can kuma Saiya tsuke bakinsa kamar
an aiko masa da sakon mutuwa ya murtuke fuskarsa ya kallesu gaba daya wasu 'yan mitsi mitsi agabansa yace
Lallai yaro yaro ne yaku wadannan tawagar matattu hakika gaba dayanku kun yaudari kawunanku da har kuke zaton cewa zaku iya tsira daga tarkunan da mai gidana yarima walisu ya kafa muku
To gaskiya kun tabka babban kuskure arayuwar ku don haka duk wani guje guje da kukeyi anan gurin zan kawo karshensa na rantse harda darajar mai gidana yarima walisu
Sai na kawo karshen duk guje gujen da kukeyi kuma daya daga cikin ku bai isa ya tsira da rayuwarsa daga sharrina ba
Koda maridin yazo nan azancensa sai su gimbiya walisa suka kalli junansu atare sannan kuma sai suka bushe da dariya
Atare kamar ba zasu daina ba wacce dariyar tasu saidata baiwa maridin mamaki
Daga can kuma sai suka tsuke bakinsu ga barin yin dariyar
Suka tsaya cak agabansa ba tare da shakkar komai ba suna masu gyara tsayuwarsu domin tunkararsa
Daga can walisa tace
Kai banda ganganci irin naka tayaya zaka tunkari abindaya gagari mai gidanka
Ai inda ba kasa nan ake gardamar kokawa
Tana gama fadin haka sai nantake ta ruga da gudu zuwa
kansa tana mai kwallara ihu da karfin gaske
Take
suma su sarki aryan suka rufa mata baya cikin karaji da kururuwa irinta manyan sadaukai

wadanda suka saba kwarmatsuwa afilin daga kowannensu
takobinsa tana ruke ahannunsa tsirara koda ya rage baifi
saura taku uku ba atsakaninsu dashi ba sai suka daka tsalle
sama daga inda suke suka kaiwa maridin wani irin mugayen sara da sukansu
Cikin zafin nama maridin yasa hannuwansa guda biyun
Ya damke su gimbiya walisa dasu ta yadda ba zasu iya fita daga cikin sa

YAYA ZATA KASANCE SHIN SU WALISA ZASU KUBUTA DAGA SHARRIN WANNAN MARIDIN?

TAYAYA YARIMA WALISU YA IYA GANO INDA SU GIMBIYA WALISA SUKE KUMA HAR YA IYA AIKO HADIMINSA?

YA LABARIN SARKI FADARUL MUNNAR MAHAIFIN SU WALISA
SHIN YANA FITOWA DA KANSA SHIMA DOMIN NEMAN DANSA NA CIKINSA WATO YARIMA WALISU KAMAR YADDA WALISA TA FITO?

DONJIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA NA WANNAN

KAYATACCEN LABARAI MAI SUNA HATSABIBAN SADAUKAI

LIKE AND COMMENTS*****************HATSABIBAN SADAUKAI

CI GABAN ZUBAR DA JINI

******************2 PART A

LBR
HABIBULLAH KBR

Lokacin da wannan maridin ya sanya hannuwansa ta damke su gimbiya walisa
Sai ya ruke su kamar ýar tsana acikin tafin hannun nasa
Sannan ya kare musu kallo irin na raini saboda kankantar da sukayi masa
Kawai sai yayi tsaki sannan ya bude bakinsa ya daga su sama da nufin ya watsa su acikin bakin nasa ya taunesu gaba daya ya hadiye duk da yasan ba zasuyi masa maganin yunwar sa ba
saida hannun nasa ya kai daidai bakin nasa zai watsasu
Kwatsam ba zato ba tsammani sai duk su ukun suka rikide jikinsu ya narke suka zama yashi
Shima kuma yashin sai ya zube akan kasa ya saje acikin saharar da take wajen
Daga can sai yashin ya tashi ya bi iska sannan ya sake rikidewa zuwa suffar gimbiya walisa, sarki aryan da kuma jaruma marfuza tsaye bisa turba fuskarsu cike da murmushi
Take suka kara afkawa kan maridin suja sake kachamewa da azababben yaki mai matukar muni atsakaninsu
Inda ace akwai mace mai juna biyu a gurin lokacin da suke wannan fafatawar dolene na kuda ta kamata kuma ta haife dan da yake cikin cikinta ba tare da ta sani ba saboda tsabar firgita
Idan kuwa futsari mutum yake ji take zai sakeshi agurin
Kai idan mutum ma matsoraci ne faduwa zaiyi kasa ya hadiyi zuciya ya mutu sabida tsabar firgita
Domin zata zakayi cewa kamar sama da kasa ne zasu hade awannan lokacin saboda tsabar bala'in rigimar tasu
Nanfa kasa ta fara girgiza kura kuwa ta tashi ta turnuke a sararin samaniya yadda ba zaka iya ganin abindake tsakaninku ba
Babu abinda ido yake iya gani face hasken giftawar makaman yakinsu
Su kuwa ko kadan babu abinda ya damesu babu abinda wannan kurar take boye musu
Saboda sabon da sukayi da gumurzu afilin daga
Nanfa guri ya yamutse karar karafkiyar karafa ta cika dodon kunne
saida suka shafe sao'i biyu suna wannan fafatawar ba tareda dayanzu ya sami nasara akana abokin gwaminsa ba
Koda su gimbiya walisa sukaga wankin hula yana nema yakaisu dare
Sai sukayi wa junansu wata inkiya sannan suka ja da baya atare
Sannan suka daka tsalle sama daga inda suke atare suna masu karaji da kururuwa suka kai masa mugayen suka akan cikinsa da nufin suyi masa kisan farat daya
Aikuwa koda makaman suka sauka ajikinsa sai suka ratsashi suka wuce kamar yadda zaka ratsa ta cikin haske ka wuce
Kafin su ankara tuni maridin ya sanya kafarsa guda ya doki jaruma marfuza da ita
Saboda karfin dukan saida tayi sama kamar an doka tamole (bal) sama tayi tsiri sosai

Koda suka ga abindaya faru ga jaruma marfuza kuma suka tabbatar da cewa idan har ta fado dolene kashushuwan jikinta su kakkarye ko kuma ta rasa rayuwar ta
Suna cikin wannan tunanin ne suka dira kan turba amma ko dakika daya basu kara ba
Sai suka bugi kasa da hannayensu take suka kara tashi sama kamar an harba kibiyoyi suka ratsa cikin iska atare suka cafo jaruma marfuza zasu sauko da ita kasa
Koda maridin yaga Abindake shirin faruwa sai ya sake kai musu wani saran da takobinsa da nufin ya tsinkasu gaba daya acikin lokaci guda
Aikuwa kafin takobin ta sauka ajikinsu tuni sun wurkila kansu a saman sun kaucewa harin nasa
Ya sari iska ji kake wuuuff!!!!!!
Sautin hucin takobinsa, take suka dirgo kasa duk su biyun dauke da marfuza akan hannunsu
Suna sauka kasa sai suka dire jaruma marfuza ta tsaya kyam akan kafafunta kamar babu wani abu daya sameta
Nanfa suka sake tsawa su da maridin suna kallon kallo cikin nuna tsan tsar kiyayya ga junansu
Suna cikin wannan kallon kallo ne maridin ya shammace ba tare da sun sani ba ya jefo musu takobinsa ta tsakiyarsu domin ta tsargesu
Kafin takobin ta karaso inda suke tuni sun kauce mata
Amma duk da haka saboda girmanta saidata ratsa ta tsakiyar sarki aryan da gimbiya walisa ta yanki kowannensu akan damatsansa
Shi dai sarki aryan a dantsen hannun dama ta yankeshi kuma gurin yayi zurfi
Ita kuma gimbiya walisa a damtsen hannunta na hagu ne
Take duk su biyun suka yagi jikin rigunansu suka daure yankan takobin
Ita takobin da maridin ya jefesu da Ita take ta koma

Please Login or Register in order to submit comment