Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da tsananin son sarauta da kuma zalunci azuciyarsa
Saboda ubangiji ya hore masa tsananin karfi damtse domin tun yana dan shekara shida
Idan ya fita yin sata ko kuma kwace ba iya sa'anninsa yake tarewa hanya ba
Harda wadanda suka girmeshi kamar 'yan shekara sha biyu
Ganin wannan baiwar jarumtakar da yake da itace tasa shi ya fara jin girman kai da kuma yarda da kansa aduk yanayin daya tsinci kansa
Kai a lokacin ma daya fara mallakar hankalin kansa sai abin yayi tsamari
Domin ba iya mutanen gari kadai yakeyiwa kwace da fashi ba
Harda dakarun sarkin garin wanda yake mulki a wannan zamanin ana kiransa da siddarul hussab
Shi kuma sarki siddarul hussab mutumin kirki ne domin duk zalunce zaluncen da sarakuna sukeyi a wannan karnin basu dameshi ba hasali ma shi ya tsani zalunci
Yana matukar kaunar talakawansa,
Aduk lokacin da dakarun sarki siddarul hussab suka
dawo daga karbar haraji a kasuwar garin ko kuma ya aikesu wani gurin sai jarumi yarmuna ya taresu akan hanyarsu ya kwace dukiyar da suka taho da ita yaje can wani kogon dutse ya boyesu
Koda sarki siddarul hussab yaga wannan tsaurin ido na jarumi yarmuna
Sai yayi tunanin dolene daga baya wannan yaron nan gaba idan aka barshi acikin birnin yayi yunkurin tayar da tarzoma acikin birnin gaba daya
Saboda hak ne
Yasa dakaru suka koreshi daga cikin birnin gaba daya
Shi kuwa jarumi yarmuna tun daga lokacin da koreshi daga cikin birnin amnatul kais
Sai ya shiga cikin daji yaci gaba da sabgar fashinsa da kwace acikin dajin
Kuma ahaka ya dinga tara dakaru masu yawa yana koyar dasu dabarun yaki da salon yaki
Cikin shekara guda ya hada guggun rundunar 'yan fashi wadanda saida suka addabi nahiyar gabaki dayanta kuma sunansa ya shahara a ko'ina cikin nahiyar kuma aka rasa wanda zai iya taka masa burki agabaki daya nahiyar
ana cikin wannan haline wata rana cikin dare alokacin gabaki dayan mutanen birnin amnatul kais suna ta sharar barci abinsu sai 'yan tsiraru daga cikin dakarun birnin ne basuyi barci ba idonsu biyu sun tsaya suna gadin birnin kamar yadda suka saba
Kwatsam sai sukaji dakarun jarumi yarmuna sunyi musu dirar burgu sunata sakar musu harbi da kibiyoyi ta sama da kasa
Nanfa dakaru suka dinga zubewa kasa matattu kamar ana ruwansu
Ba shiri suma dakarun suka shiga debo makamansu na yaki suna fitowa domin kare rayukansu
Suka hadu a bakin kofa akayita kafsa gagarumin yaki acikin wannan daren
Amma saidai kash aikin gama ya gama domin tuni dakarun harin sumamen sun gama kewaye birnin tako ina kuma sun fasa kofofin shigarsa da karfin tsiya sun shiga cikinsa
Sukayita ragargazar dakarun babu ji babu gani ta ko"ina
Kafin lokacin ketowar alfijir tuni sun gama karar da dakarun birnin gaba daya
Ya zamana cewa mutum dayane kadai a raye kuma ya kasance dattijo domin a akalla shekarunsa ba zasu gaza saba'in da uku ba
A zaune akan doki rike da wata sharbebiyar takobi yana ratsawa ta cikin dakarun sumamen ta ko'ina yana kai sara da takobinsa
Duk inda yakai hannunsa kuwa saidai kaga dakaru suna zubewa kasa kamar ana sassabe agona

Kayan da suke Jikinsa da kuma takobinsa kuwa tuni duk sun rine da jini kamar wanda yayi wanka acikin kogin jini
Shi kadai ne kadai yake ratsawa ta cikin dakarun kamar shaidani
Duk inda ya ratsa acikinsu saidai kaga dakaru suna ihu da karaji saboda tsananin jin radadin zafin fitar rai
Kawunan dakaru kuwa sai suka dinga shawagi kamar ana zubar da ganyayen bishiya
Jini kuwa ya dinga fallatsi daga jikin gangar jikinsu yana fallatsi a sama kamar an bude magudanar ruwa
Ba kowa bane wannan dattijon ba face sarki siddarul hussab
shine yaketa wannan gagarumar barnar domin yaga ya kare martabar kasarsa daga harin wadannan dakarun sumame

Tabbas sarki siddarul hussab ya cika gagarumin gwarzon
mayaki wanda ya cancanci a yaba masa domin har yanzu
birnin amnatul kais suna tunkaho da irin jarumtakarsa da kuma jajurcewarsa
Ana cikin hakane wani badakare mai tsananin naci ya shammaci
dokin da sarki siddarul hussab yake kai kawai ya caka masa mashi adaidai kahon zuciyarsa

Take dokin yayi turjiya adaidai inda yake tareda daga
kafafuwansa sama yayi haniniya sannan ya fadi kasa ya danne sarki siddarul hussab akasa

da ganin haka sai nantake dakarun sumamen suka yi cincirindo suka lullube shi da nufin suyi masa gunduwa gunduwa
Koda ganin abindake shirin faruwa sai nantake sarki siddarul hussab yayi kukan kura
Lokaci guda ya ciccibi dokin daya danne shi ya daga shi sama yayi wulli dashi can gefe daya ya turmushe wasu dakarun
Sannan ya shuri takobinsa yayi katantanwa a tsakiyar dakarun dake kewaye dashi
Ai kuwa take sai gasu duk sun zube kasa babu kafafu da hannaye a jikinsu
Sannan yasa kafarsa dukkansu ya bangajesu da ita
Kafin yayi wani yunkuri tuni wasu dakarun sun kara yanyameshi kamar kiyasai saboda matukar yawansu
(HAR NA TUNA LOKACIN DA NAKE KAN GANIYAR SADAUKAN TAKA TA
TABBAS NIMA NA SHEKE DAKARU DA YAWA A FILIN DAGA WADANDA BANSAN ADADINSU BA
GASKIYA DOLENE TARIHI YA TUNGA TUNAWA DANI DON NIMA BUWAYAR SADAUKAI NE)

Koda dakarun suka kara yin rubdugu akansa sai ya sunkuya ya bugi kasa da hannayensa

Kuma ya yi tsalle yayi alkafira sau uku a sama sannan
ya dawo kan kasa fuskarsa tana wani gyatsine alamar
cewa yana cikin tsananin bakin ciki burinsa kawai shine
yaga yayiwa wadannan dakarun muguwar barna koda kuwa zai rasa rayuwarsa

Koda dirarsa akan kasa saiga kawunan wadannan dakarun
da suka kewayeshi suna zabtarewa daga jikin gangar jikinsu suna faduwa kasa
Ita kuwa kasar gurin tuni itama ta dade da rinewa da jinin dakarun in banda karnin jini babu abinda hanci ke ji
Sai kuma karar karafkiyar karafa, sai gashi sarki siddarul hussab yana nunawa dakarun sumamen cewa tsohon kashi ba wasa bane kuma shima bai gaji sarautar birnin a banza ba sai daya sha gagarumar wahala ya kafsa da manyan mazaje da matsafa

TAYA SARKI SIDDARUL HUSSAB ZAI IYA GAMAWA DA WADANNAN DAKARUN SUMAMEN?
SHIN DAKARUN SUMAMEN SUNA SAMUN NASARA AKANSA KUWA ?
SHIN ALJANI DARGATUL AMNAR YANA ZUWA BIRNIN AMNATUL KAIS KUMA HAR YA AIWATAR DA UMARNIN UBAN GIDANSA ?
ME YARIMA WALISU ZAI GANO ACIKIN HALWAR TSAFIN DAYA SHIGA?
SHIN YAUSHE SU GIMBIYA WALISA ZASU FITO DAGA CIKIN KOGON DUTSEN DA SUKA FADA

DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU AKASHI NA GABA NA CIGABAN WANNAN LABARI MAI SUNA HATSATSABIBAN SADAUKAI
DAGA NAKU
HABIBULLAH KBR
LIKE ,COMMENTS AND SHARE*******************HATSABIBAN SADAUKAI

CI GABAN ZUBAR DA JINI

*******----------3 PART C----

LBR

*********HABIBULLAH KBR

Hakika a wannan ranar dakarun harin sumamme sun tabbatarwa d kansu cewa yau sun gayyaci guguwar annoba da hannunsu
Ana cikin wannan haline kwatsam sai ga jarumi yarmuna yazo gurin da kansa
Koda yaga irin muguwar barnar da sarki siddarul hussab yakeyiwa dakarunsa
Sai ya fusata ya kwarara uban ihu, nantake ya zari wata kibiya daga cikin kufensa
Ya dorata akan baka sannan ya tabe ya harbawa sarki siddarul hussab Ita akan kirjinsa
Nantake kibiyar ta taho da gudun gaske ta cake a tsakiyar kirjinsa ta faso ta gadon bayansa jini yayi fitar burgu daga gurin
Cikin sauri ya dago da kansa don yaga wanda yayi masa wannan mummunan harbi
Ai kuwa sai sukayi ido biyu da jarumi yarmuna alokacin fuskar kowa tana gyatsine
Kawai sai sarki siddarul hussab ya daka tsalle daga inda yake
Bai bayyana a ko'ina ba sai daidai kan jarumi yarmuna take ya daga takobinsa sama
Ya kai masa mummunan sara adaidai dokin wuyansa da nufin ya tsarge masa kai
Cikin bakin zafin nama ya kaucewa saran amma duk da haka sai da kaifin takobin ya yankeshi a kafadarsa
Tabbas in ba don yayi saurin kaucewa ba da tuni an manta da shafinsa

Take jarumi yarmuna ya dakawa dakarunsa tsawa ya umarcesu dasu matsa su bashi guri
Aikuwa take duk suka buda musu fili dagashi sai sarki siddarul hussab atsakiyar fili Sunayi musu kida
Daga can sai duk su biyun sukayi kukan kura suka afkawa junansu da masifaffen yaki mai matukar muni
Wanda saidaya firgita gaba daya dakarun da suke kewaye dasu
Domin kuwa gumurzu ne na banbance aya da tsakuwa da kuma kece raini
Tsakanin tsohon kashi da kuma sabon kashi, kowannen daga cikinsu
Yana mai kaiwa abokin gwaminsa farmaki saida suka shafe fiye da sa'o'i uku suna fafatawa a tsakaninsu
A sannane dafin dake jikin kibiyar da jarumi yarmuna ya harbi sarki siddarul hussab ya gama mamaye jikinsa
Jiri ya soma dibarsa, ya dinga ganin abubuwa zuwa gida hudu
Wannan itace damar da jarumi yarmuna ya samu har ya dinga dankara masa sara tako'ina ajikinsa tun yana maidawa yarmuna martani har yazamana cewa ya kasa yin hakan
Koda ganin wannan nasara sai yarmuna ya maida takobinsa cikin kube
Kawai ya kalli sarki siddarul hussab ya bushe da dariya
Yace
Yakai wannan sarki ka sani cewa kuskurenka guda dayane a duniya
Wannan kuskuren kuwa shine barina a raye tun ina karami baka sa an kashe ni
Kuma tun a wancan lokacin bani da burin dayafi naga na mallaki karagar mulkinka
Wannan daliline yasa na dage wajen baiwa kaina horon yaki
Kuma na dinga tare dakarunka inayi musu fashi,
To ka sani cewa
Da wadannan kudaden dana kwata. Ahannun dakarunka dasune nayi amfani na tara wadannan dakarun
Kuma gashi yanzu dasune nayi amfani wajen rusa karagar mulkinka
Duk wadannan maganganun da yake fada sarki siddarul hussab yana jinsa
Daga can kuma sai ya dago da kansa a hankali yace
Lallai na yarda cewa yanzu kayi nasara amma ina mai tabbatar maka da cewa ba zaka dade ba akan wannan karaga domin mulki da zalunci basa taba dorewa
Kodajin wannan batu sai ran jarumi yarmuna ya baci
Don haka sai yayi kukan kura ya zare takobinsa danufin ya sarewa sarki siddarul hussab kai
Ai kuwa kafin takobin ta sauka akan wuyansa tuni shima ya daka tsalle ya zaro wata allura ajikin damararsa ya cakawa yarmuna ita a idonsa na hagu
Shi kuma yarmuna yasami nasarar tsinke kan sarki siddarul hussab
Take kansa ya tsinke daga jikin gangar jikinsa ya fadi kasa da murmushi akan fuskarsa
Shi kuwa yarmuna saiya kwallara ihu saboda bakin cikin rasa idonsa guda daya da yayi

Tun daga wannan rana jarumi yarmuna ya kwace karagar mulkin birnin amnatul kais da karfin tsiya ya zama sarkin garin
Kuma ya kafa mulki na zalunci tsantsa wanda ko kadan babu tausayi ko tausayawa talakawa acikinsa
Akullum burinsa shine ya mamaye nahiyar gaba ki dayanta ako'ina ya kafa karagar mulkinsa
Ya ajiye wakili

Kuma duk tsawon wannan lokaci ya manta da wasiyyar da sarki siddarul hussab yayi masa akan cewa bazaiyi tsawon raiba akan wannan karagar mulki
Wannan shine takaitaccen tarihin sarki yarmuna da yadda ya kwaci mulkin birnin amnatul kais
Lokacin da aljani dargatul amnar ya nufi nahiyar bakaken fata domin gabatar da kudurin uban gidansa wato yarima walisu
Bai isa birnin amnatul kais ba sai da dare ya raba mutane suna ya sharar barci abinsu
Don haka sai kawai yaga idan yace zai yakesu a wannan dare
Duniya zataga kamar yayi yakin cikin tsoro ne,
Don haka sai ya sami wani katon tsauni wanda yake kusa da birnin ya zauna akansa har zuwa safiya mutane suka fara fitowa daga gidajensu
Saida kowa ya gama tashi daga barcin da yakeyi ya kama sabgoginsa yanayi sannan aljani dargatul amnar ya kada fuka fukansa ya tashi sama ya dira acikin birnin amnatul
Shi kansa sautin kada fuka fukan saidaya haddasa guguwa agurin
Koda mutane sukayi arba da shi sai suka firgice suka fara iface iface suna gudun ceton rayukansu
Kuma adaidai wannan lokacin ne wani irin duhu irin mai dum dum dinnan ya mamaye birnin gabaki dayansa
Ai kuwa take mutane suka kara furgicewa fiye da ko yaushe
Shi kuwa aljani dargatul amnar sai ya wanzu yana mai shayar dasu gidauniyar mutuwa
Da zarar ya bude bakinsa saidai kaga harshesa ya karawa kansa tsawo ya fito daga cikin bakin
Yana tsinkewa mutane kawunansu kamar an saka resa
Alokaci guda sai ya cirewa mutum dari kawunansu ya taune acikin bakinsa
Saidai kaji sautin karyewar kashushuwa rukukus kamar mutum ya sami kuli kuli

Babu abinda zai baka tausayi a wannan lokacin face yadda zaka gangar jiki babu kai ajikinta tana gudun ceton rai bayan kuma ta tabbatar da cewa mutuwa zatayi babu makawa
Nanfa dakarun birnin suka dinga ciccidowa tako"ina domin su baiwa birninsu kariya amma da zarar
Sun yi arba da irin kisan da aljani dargatul amnar yakeyi musu
Sai kaga sun zubar da makaman yakinsu su falfala da gudu
Amma duk irin gudun da zasuyi sai ya bisu ya kure musu gudu ya lankwame su
Ana cikin wannan haline aljani dargatul amnar ya runtse idonsa ya karanta wasu sirrikan tsafi
Faruwar hakan keda wuya sai ga wuta ta kama gabaki daya
Sassan birnin har da gabaki daya gidajen dake cikin garin
Kuma wutar mai tsananin karfi har tsiri takeyi asararin sama
Nanfa wutar ta kara gigita duk wani mai rai acikin garin
Suka fara kai kansu da kansu har inda aljani dargatul amnar yake ba tareda sun sani ba
Nanfa jini ya cika garin ya zamana babu abinda kunnuwa sukeji face
Koke koken mutane yara da manya maza da mata,
Jini kuwa ya dinga shatata yana gudu acikin kwatocin garin yana gurbata da kasa
Kamar an bude magudanar ruwa
Hakika tashin hankali bashi da dadi kuma ba'abin nema baneba
Domin shine kadai abinda yake iya sakawa mutum ya zauce
Ya manta matsayinsa, dukiyarsa da danginsa domin kowa a sannan ta kansa yakeyi
Saida mutanen birnin baki dayansu suka mutu ya zamana babu mai rai a cikin su
Kawai dargatul amnar ya bushe da dariyar farinciki kan nasarar daya samu akaron sannan ya juya da nufin ya kama hanya ya tafi
ba zato kawai sai yaga wani saurayi ya dako tsalle ya faso wani tubalin gini
Wanda wuta takeci asamansa ya fito daga ciki hannunsa ruke da wasu sharba sharban adduna guda biyu yana mai kwarara uban ihu irin na manyan mazaje

Ba kowa bane wannan saurayin ba face sarki yarmuna da kansa
Tun kafin ya dira akan kasa ya daidaici dai dai tsakiyar kirjin aljani dargatul amnar ya jefa masa wadannan addunan na hannunsa
Take duk addunan suka nutse acikin kirjinsa,
Maimakon aljani dargatul amnar yaji zafi kawai sai yayi murmushi
Ya sa hannunsa ya zaro wadannan addunan daga jikin kirjin nasa
Take kirjin ya koma ya hade kamar wani abu bai taba samunsa ba
Da ganin haka sai sarki yarmuna ya kara fusata ya sake dako wani tsallen a sama yana watsa

Masa nau'ikan sihirce sihirce nau'i daban daban duk abin
daya jefo idan ya sauka ajikin dargatul amnar sai nan
take kaga ya lalace ya daina aiki ya zube kasa daga can kuma sai ya saka hannuwansa
Ya cafo sarki yarmuna ya matse shi da hannunsa aikuwa
nantake sai kashushuwan jikinsa suka dinga kakkaryewa ji kake kararasssss
Saida yayi daga daga da jikinsa babu kyan gani sannan ya zubar da diddigar jikin nasa a kasa sannan ya tashi yaci gaba da tafiyarsa
Yana mai kyalkyala dariyar murna wacce ta amsa kuwwa a gabaki dayan rusashshen birnin

WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GA ALJANI DARGATUL AMNAR
BAYAN YAJE BIRNIN AMNATUL KAIS

**** ***** *****- *****
Can kuwa al'amarin su jaruma walisa bayan sun sami nasarar yaki
Da wadannan hatsabiban dodannin sun sami nasara akansu
Har suka sami guri suka zauna suna hutawa sai kawai duk sukaji cikinsu
Ya daure yana murdawa alamar cewa yunwa taci karfinsu
Kodajin haka sai duk suka tuna cewa babu wanda yaci abincin karin kumallo acikinsu
Kodajin wannan yanayi sai dukkansu suka dauko jakunkunan guzurinsu
Suka kwance sukaci abinci suka koshi a sannan ne suka ga duk abincin nasu
Ya kusa karewa, koda ganin haka sai hankalinsu ya dugunzuma ya tashi
Domin sun san cewa idan ya kare basu da inda zasu sami wani abincin acikin wannan kogon
Don haka dolene su san hanyar da zasu bi su fita daga cikin kogon da wuri
Bayan sun zauna sunyi hirarsu sosai sai kuma suka kara tashi tsaye suka kama hanya sukaci gaba da tafiya abinsu
Awannan lokaci gaba daya har sun manta da wahalar da suka sha a baya
Kuma burinsu kawai shine su gaggauta ficewa daga cikin wannan kogon dutse
Saida suka shafe sa'o'i hudu suna tafiya basu sake haduwa da wani abin tashin hankalin ba sannan sukazo jikin bango na karshe a cikin kogon

Da zuwansu daidai wannan bango sai sukaga bangon ya dare gida biyu kamar an bude littafi
Ya samar da wata wawakekeyar kofa a saman kofar an rubuta

SANNUNKA DA KOKARI YA KAI BAKON WANNAN GIDA
KA SANI CEWA KAINE KADAI MAHALUKIN DAYA TABA SHIGOWA CIKINSA KUMA YA FITA ARAYE
SABODA HAKA MUNA MAI TABBATAR MAKA DA CEWA DUK ABINDA KASA A GABANKA NAN GABA KADAN SAI KA CIKASHI
BISSALAM MUNA MAKA FATAN NASARA

koda suka gama karanta wannan allon sanarwar sai take hoton allon ya bace
Da ganin haka sai duk sukaji farinciki ya turnuke su don haka sai suka dubi junansu
Sannan suka saka kafarsu ajere suka fice daga cikin kogon
Aikuwa suna fitowa sai sukaji wani farin ciki ya kara turnuke su
Kuma sai suka tsinci kansu a cikin wani daji mai cike da tarin ni'imar abubuwan marmari kala daban daban
Da ganin haka sai jaruma tayi murmushi tace
Ashe dai da rabon zamu sake shan iskar wannan daddadar duniyar tamu?
Dajin haka sai gimbiya walisa tace kwarai ma kuwa gashi nan kina gani da idonki
Gaskiya muna da matukar sa'a acikin rayuwarmu
Shi kuwa
sarki aryan sai yayi shiru yaki yace dasu komai ya barsu su kadai sai hirarsu sukeyi
Haka dai sukaci gaba da tafiya suna ta hirarsu ,a sannan ne gimbiya walisa taji bukatar uzuri ya kamata
Don haka sai ta nemi izini a gurin abokan tafiyar tata nanfa ta tafi ta barsu su biyu rak a tsaye sunata faman hira abinsu cikin nishadi da kuma raha
Sannan ta zagaya bayan wani katon dutse da yake bayanta ta tsugunna ta biya bukatar ta
Har ta gama biyan bukatar tata ta kamo hanya da nufin dawowa gurinda 'yan uwanta suke
Kawai saita hango wasu 'yan kananun duwatsu guda biyu agabanta kadan
Duk da cewa a wannnan lokaci ana zabga rana amma a kewayen duwatsun babu rana

Sannan ga wasu kyawawan tsuntsaye sunata zagayawa
a saman duwatsun abin ban sha'awa
Koda ganin wannan abu sai take ta tuna da kalar tsuntsayen
data gani acikin mafarkinta tare da wannan bakon jarumin
kwanakin baya lokacin da tana gidan sarkin kasuwa yimana
Kuma wadannan tsuntsaye basu da banbanci da wadancan tsuntsayen
Tana gama tunawa da mafarkin nan nata kawai sai taji ba zata iya hakura taci gaba da tafiya ba
Dole ne sai taje gurin wadannan duwatsun ta ganewa idonta ke meye a gurin
Nan take ta kama hanya ta tunkari wadannan kananun duwatsu gadan gadan

ME ZATA TARAR A WANNAN GURI?
YANZU KUMA INA ALJANI DARGATUL AMNAR YA NUFA?
SAI MU HADU A KASHI NA GABA****-------**********HATSABIBAN SADAUKAI

*****************4 PART B

LBR

**************HABIBULLAH KBR

Lokacin dasu gimbiya walisa suka rikide suka koma suffar katuwar mikiya
Sai sukayita tsala azababben gudu kamar giftawar tauraruwa mai wutsiya
Kuma suna tafiyar suna hadawa da karfin sihirinsu don takaice nisan tafiyar
Ai kuwa sai suka dinga shafe tafiya mai nisan gaske cikin kankanin lokaci
Suka dinga giftawa ta saman manyan birane, tsaunika, tekuna, da kuma dajijjika
Cikin lokaci kankani ,saida mikiyar ta shafe mako biyu yana tafiya asararin samaniya ba tareda ta yada zango ba
Kuma akan hanyarsa ya hadu da abubuwan hatsari
Kala da ban daban, wadanda suka hada da manyan aljanu masu cin naman. Bil'adama, dodanni, dabbobin daji, da kuma mutane jinsin mayu
Amma da zarar wannan mikiyar ta riski wata barazana daga wajen wadannan halittu cikin kankanin lokaci
Take tarwatsasu da karfin tsiya ya kashe na kashewa
Wasu kuma su gudu da kafafunsu domin tsira daga halaka domin sun san wannan karon basu takali ruwan sanyi ba
Tsuliyar dodo suka tsokanowa kansu ko kuma ince tikitin mutuwa suka saya da hannunsu
A ranar da suka cika mako uku ne suka isa nahiyar bakaken fata a nesa kadan da birnin labtarul halkam
Koda isowarsu wannan sai mikiyar ta saki fuka fukanta ta sauko kasa kan turba
Sannan tayi girgiza take kuwa mikiyar ta rabu gida uku wato ta rikide zuwa siffar gimbiya walisa, sarki aryan da kuma jaruma marfuza
Dukkansu a wannan lokaci kallo daya zakayi musu kasan cewa a matukar gajiye suke, ko kuma once a jigace
Saboda tsananin wahalar da suka sha akan hanyarsu da kuma gwagwarmayar da suka sha
Kuma duk tsawon wannan lokacin babu wanda ya samu yayi barci ko kuma ya sha ruwa acikinsu har suka gama shafe wannan uwar tafiyar
Koda dirarsu akan doron kasa duk sai suka nemi guri suka zauna sunata faman haki
Kuma a wannan lokaci abincin kowa ya kare babu mai koda loma daya acikin jakar guzurinsa kai hatta ruwan da zasu sha ma babu
Haka dai suka zauna a wannan daji amatukar galabaice babu wanda ya sami damar koda rintsawa
Kaico hakika yunwa bata da dadi kuma babu wanda yake sabo da ita
Saida suka shafe dakiku masu yawa kawai suna kallon kallo a tsakaninsu ba tare da wani yacewa wani kala ba
Saboda mawuyacin halin da suke ciki ,
Suna cikin wannan haline kawai sukaga wani murgujejen zaki ya fito daga cikin kogon da nufin fita farautar abinda zai ci kuma ya kaiwa 'ya 'yansa ragowar
Koda ganin wannan zaki sai nantake jaruma marfuza ta zaro kibiya daga cikin kwarinta ta dora akan bakanta
ta saita tsakiyar cikin zakin nan ta harba nantake kibiyar ta tafi da gudun gaske ta cake atsakiyar cikin wannan zakin
Take zakin yayi wani gurnani sannan ya sulale kasa matacce
Cikin sauri marfuza ta tashi taje ta ciccibo gawar zakin ta kafa wuyansa
Abakinta ta kama shan jinin jikinsa ,da ganin haka sai suma su sarki aryan da gimbiya walisa sukayi koyi da ita
Koda suka sha jinin jikin wannan zaki sai suka fara dawowa cikin hayyacinsu
Sannan suka fede fatar zakin suka gyara shi daga baya kuma suka dauko duwatsun kyastu suka kunna wuta agurin suka gyara zakin sannan suka gasa shi
A wannan guri suka ci naman zakin suka koshi sannan suka dawo cikin hayyacinsu
Adaidai wannan lokaci ne sukaga dare yayi don haka dole suna bukatar su samu su kwana a wannan guri idan safiya tayi sai su tashi su shiga cikin birnin dake gabansu
Sarki aryan ya dubesu yace yaku abokan tafiyata ai yanzu bamu da wata fargaba a gaban mu
Tunda har mun iso birnin labtarul halkam yanzu zaifi mana kyau mu samu mu yada zango anan gurin idan safiya tayi sai mu tashi mu shiga cikin garin nan ido na ganin ido,
Dajin wannan shawarar tasa duk sai suka yarda da ita
Take kowa ya mike daga gurin da yake yayi shimfida kayan kwanciyar sa
Sannan gimbiya walisa ta kalle su gabaki dayansu tayi murmushi tace
Yau dai zamuyi barcin da tunda muka hadu daku bamu taba yin irinsa ba
Tunda kullum acikin tashin hankali muke tana gama fadin haka sai ta runtse idanunta sannan ta dauki wani dogon sanda
Idonta a rufe ta dinga zagayesu har sai da tayi musu da'ira
Tana gama yin da'irar saita karanta dalasiman tsafi ta tofa akanta
Aikuwa faruwar hakan keda wuya sai ga wani dan karamin daki ya bayyana
Daidai da kwanciyar mutum uku acikin dakin harda shimfidu masu taushi aciki
Su kuwa su sarki aryan koda sukaga faruwar wannan al'amari sai duk suka kame suka kura mata ido
Suna mamakin wannan karfin sihiri nata,
Har sarki aryan ya bude baki zaiyi mata tambaya sai ta tsai dashi ta hanyar cewa
Ba tambaya zaka tsaya yi mini ba kawai kaje ka zabi gurin da zaka kwanta
in yaso sai kayi mini tambayar da kake bukatar yi mini
Cikin mamaki sarki aryan yaje can kan shimfidar da take gefe daya ya zauna sannan itama
Marfuza taje ta sami gurin da zata kwanta suka bar walisa a tsaye
Sarki aryan yace
Yake walisa tabbas yau na dada tabbatar wa cewa kinyi mana nisa nida jaruma marfuza
Kwarai da gaske

Please Login or Register in order to submit comment