Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a kowanne fanni karfin damtse da kuma karfin sihiri
Amma yanzu tambayar da nakeson yi miki itace a ina kika samu sihirin tsafi mai karfi?
Dajin wannan tambaya sai itama walisa ta sami guri ta zauna sannan ta dubeshi
Tace
Kada fa ka manta ni 'yace ga sarki fadarul munnar ka sani cewa tun muna jarirai ake shayar damu tsumin tsafi tun kafin mu fara shan nonon mahaifiyar mu
Haka aka ci gaba da yi mana har zuwa girman mu ba'adaina tsuma mu acikin tsumin tsafi ba ni da yarima walisu
Hakika nima nayi mamakin yadda ruhin boka sahibul ukub
Ya iya shiga jikinsa har yake sarrafa shi,
Yanzu dai zaifi kyau mu ajiye batun hira a tsakaninmu
mu samu muyi barci domin rama barcin da yake cikin idanun mu
Ku sani cewa idan har muna cikin wannan daki babu mahalukin da zai iya shigowa cikinsa komai karfin sihirinsa
Saidak yarima walisu kadai shi dinma kafin ya shigo sai mun san da zuwansa ta hanyar wannan dutsen
Nantake ta sanya hannu acikin aljihunta ta dauko bakin dutsen da boka makassar ya bata tun kafin ta baro gida
Kunga wannan dutsen shine zai yi mana ishara da zuwansa idan har ya bayyana
Tana gama fadin haka sai ta sami guri ta kwanta ba tareda ta kara cewa komai ba

Koda sukaji wannan bayani nata sai duk suka cika da al'ajabi
Suka tabbatar da cewa tabbas walisa da walisu sun sami horo sosai da kuma kariya daga iyayensu
Don haka dole ta fita daban dasu
Take suma duk suka sami guri suka kwanta
Abinka da gajiyayyu
Aikuwa suna kwanciya sai barci mai nauyi ya dauke su
Basu farka ba saida safiya tayi lokacin rana ta gama budewa ta haska ko'ina
Acikin dakin sannan suka farka daga barcin aikuwa suna farkawa kuwa atake duk suka hada kayayyakinsu suka nufi birnin labtarul halkam tun daga nesa suka fara hango dakaru atsaitsaye abakin kofar birnin ruke da makaman yaki a hannunsu sai muzurai sukeyi
Da ganin haka sai jaruma marfuza ta dubesu tace
Zaifi kyau dukkan mu mu boye siffofinmu don kada wadannan dakarun su san gaskiyar su waye mu
Domin idan har suka sani ba zasu bari mu gama aikin da mukazo yi da wuri kuma acikin sirri ba
Zai fi kyau duk mu sauya kamanninmu tunda ba zama mukazo yi cikin birnin nan ba
Har yanzu akwai aiki mai yawa agaban mu, kodajin wannan shawara sai dukkaninsu suka aminta da shawararta
Don haka take dukkansu sai suka rikide suka koma siffar tsuntsu hankaka
Sannan suka tashi sama suka shiga cikin birnin
Duk wannan abu dayake faruwa dakarun dake tsaye abakin kofar basu kula ba
Saida tsuntsayen suka zo giftawa ta saman kofar inda masu gadi suke
Sai kawai sarkin kofa ya daga kai ya karewa hankakin kallo
Nantake yaji zuciyarsa bata sami nutsuwa dasu ba don haka dole akwai alamar bakin haure ne su ba tsuntsaye ba don haka sai kawai ya girgiza kansa sannan ya koma kan aikin da yakeyi
Lokacin da wadannan hankakun suka gifta ta saman dakarun da suke tsaron kofa basu wuce ko'ina ba
Sai cikin babbar kasuwar birnin don haka sai hankakun suka sauka abayan wata rumfa acikin kasuwar
Sannan suka rikide suka koma ainihin siffarsu suka fito daga cikin kasuwar
Kai tsaye suka zarce cikin wata rumfa inda suka tarar ana sayar d abinci
Nantake suka karasa cikin rumfar suka zauna mai sai da abincin tazo ta tambayesu mai suke bukata
Kowa ya fada mata kalar abincin da yakeso
Cikin kankanin lokaci kuwa matar ta kawo musu abincin
Sukaci suka bata kudinta sannan suka tashi suka kara gaba
Koda suka nausa cikin wannan kasuwar sai suka cika da mamaki
Domin gani sukayi kasuwar ta fita daban da kalar kasuwannin da suka sani
Babu abinda ake kwance hajarsa acikin wannan kasuwa face tarin litattafai marasa adadi maimakon makaman yaki, fatun dabbobi ko kuma kayan abinci
Wannan ne ya nuna musu cewa su wannan birnin babu gasar da sukeyi face gasar ilimi
Domin sai ka sami mutum guda wanda ya iya magana da harshe guda ashirin
Kuma duk kalar littattafan da mutum yazo dasu da wuri ake siyesu
Wannan al'amari ba karamin basu mamaki yayi ba
Don haka sai suka ci gaba da tafiya acikin kasuwar suna kallon yadda mutane suke gudanar da rayuwarsu
Suna cikin tafiyar ne suka hango wani guri ya cika makil da jama'a suna kallon wani abu a tsakiya
Cikin sauri walisa tace dasu aryan
Mai zai hana muje can gurin muga wacce irin gasar jarumtakar ake gudanar wa
Cikin sauri kuwa dukkansu suka dunguma suka nufi wannan guri
Suna zuwa duk sai sukaga abin mamaki domin ba komai ake yi ba face gasar ilimi
Tsakanin wasu yara wadanda shekarunsu ba zasu gaza goma sha biyar ba su hudu
Kowannensu a zaune akan mumbari suna ta musayar yare
Kowanne daga cikin wadanan yara yanajin yarurruka sama da guda ashirin
Su kuma mutanen gari sun kewayesu suna alkalanci domin suga wanda zai kada wani
Da ganin wannan al'amari sai gimbiya walisa tayi murmushi ta dubi sarki aryan tace
Hakika kowa da kiwon daya karbeshi, kamar yadda abirnin ka ake hada gasar jarumtaka su kuma wannan birnin gasar ilimi ce burinsu, duk wanda baiyi yawon duniya ba bai more kallo ba
Dajin wannan batu sai sarki aryan yace kwarai kuwa maganarki gaskiyace
Adaidai wannan lokacin ne sukaji filin ya cika da shewar mutane
Duk da cewa basu san maganganun da ake tattaunawa akansu ba
Amma sun fahimci cewa daya daga cikin yaran wanda akewa lakabi da himsad shine ya cinye gasar
Ga mutane nan sai cin cirindo akeyi wajen daga shi yayin da aka tafi kaishi can gidansu anata faman yi masa kirari
Da ganin haka sai jaruma marfuza tace dasu walisa ai zama bai kamamu ba dolene muma mu bi wannan yaron domin muga inda zasu kaishi in yaso sai mu nemi alfarma agurinsa ya sanar damu abinda mukazo nema
Kodajin wannan batu sai dukkansu suka amince da shawarar data bayar ma'ana suka bi yaron a baya
Har suka isa gidansu
Bayan kowa ya watse sai suka karasa kofar gidan suka kwankwasa ta da hannunsu
Basu dade ba saiga yaron ya fito koda himsad yayi arba dasu gimbiya walisa saiya firgita
Har yaja da baya da nufin ya gudu sai walisa tayi caraf tace
Kada ka firgita yakai himsad mu baki ne kuma bukatace damu agareka
Muna fatan zaka taimaka mana
Dajin wannan batun sai himsad ya kara dubansu cikin rashin fahimta yace
Wacce irin bukatace daku agareni?
Take walisa ta dauko masa wannan karamin littafin ta mika masa shi a hannunsa tace
Shin kasan yaren da aka rubuta littafin nan?
Himsad ya mika hannu ya karbi littafin daga hannunta ya kare masa kallo sosai yana nazarinsa
Daga can sai ya dago da kansa ya dubesu yace
Yaku wadannan baki gaskiya na tausaya muku domin ban taba jin labarin irin wannan yaren da kukazo dashi ba
Kuma kaf cikin birnin nan bana tunanin akwai wanda yasan wannan yare ko kuma zai iya koyar daku
Kodajin wannan batu sai hankalinsu ya dugunzuma suka dubeshi sukace
Muna rokonka da darajar abin bautarka ka taimaka mana idan har bukatar mu ta biya zamu biyaka ladan kudade masu yawa
Dajin haka sai himsad yace
Kuyi hakuri babu abinda na sani game da wannan yaren
Yana gama fadin haka saiya juya ya shige cikin gidansu
Yabar su gimbiya walisa a tsaye sunata faman zare idanu
Daga can sai sarki aryan yace ai shikenan sai mu ci gaba da tafiya ni na Tabbata mai nema yana tare da samu ba zamu bar wannan garin ba face bukatar ta biya
Yana gama fadin haka sai ya wuce gaba suma su gimbiya walisa sai suka bishi abaya
Suna tafiya suna tsayawa suna tambayar mutane kai a wannan ranar saida suka yini suna tafiya ba tareda sun sami nasarar abinda suke nema ba
Yamma tanayi sai suka sami gidan haya wanda zasu kwana aciki
Duk wannan sunturi da sukeyi ashe akwai wani kasurgumin barawo
Yana biye dasu duk inda zasu shiga domin ya kware sosai wajen iya sata da kuma sanin manyan mutane
Don haka tun daga sanda su gimbiya walisa suka shigo cikin birnin labtarul halkam
Yasan cewa dolene su kasance jinin sarauta don haka sai ya kudurce aransa cewa
Duk inda zasu shiga sai ya bisu kuma ya sace duk dukiyar da take hannunsu
Ana kiransa da suna kusail, mutane da dama sun sha dana masa tarko akan su kamashi saboda yadda ya addabesu da sata amma sun kasa saboda irin karfin sihirinsa
Lokacin da kusail yaga su marfuza sun kama gidan haya
Sai ya salallabo ya biyosu har cikin gidan ba tareda sun sani ba
Dare na rabawa lokacin daya tabbatar da cewa mutane sun kwanta barci
Sai ya fito daga cikin maboyarsa ya nufi dakin dasu gimbiya walisa suke ciki
Yana mai karanta wasu dalasiman tsafi wadanda indai yayi su babu mahalukin daya isa yaji sautin sahun kafarsa, ko kuma ya iya ganinsa da ido ba
Sannu a hankali ya isa bakin kofar dakin yana isa yasaka hannunsa ya murda mabudin kofar dakin ya kutsa kansa ciki kai tsaye

HAKIKA MASU IYA MAGANA SUNYI GASKIYA DA SUKACE
KOMAI SAMMAKONKA WANI A TAFE YA KWANA
KUMA RANA DUBU TA BARAWO CE RANA DAYA TAK KUMA TA MAI KAYA
INDA ACE WANNAN BARAWON YASAN ABINDA ZAI FARU DA BAIYI GANGANCIN AIKATA SATA ACIKIN WANNAN GIDANBA
DOMIN WADANDA SUKE CIKINSA BA KANWAR LASA BANE
Lokacin da kusail ya shiga cikin wannan daki sai ya tarar da cewa duk su gimbiya walisa sun sun kwanta barci Abinsu har da minshari saboda jin dadin barcin
Kai tsaye ya wuce inda yaga sun ajiye kayayyakinsu
Ya saka hannunsa ya fara dubawa cikinsu acikin jakar farko daya fara dubawa bai sami kudade masu yawa ba
Domin jakar jaruma marfuza ce amma koda ya bude ragowar jakunkunan sai ya kamu da farinciki mara misaltuwa
Domin gani yayi gaba daya jakunkunan cike da tarin dukiya wandada suka hada da darhami ,zinare da kuma lu'u lu"u
Saboda farinciki baisan sanda ya tuntsure da dariya ba
Wannan shine babban kukuren daya aikata
Domin abinda bai sani ba shine sihirin tsafinsa ba zaiyi aiki akansu gimbiya walisa ba
Lokacin da kyalkyala wannan dariyar dukkansu saida sukaji sautinta amma basu farka ba
Domin a zaton su
Acan waje akeyinta, sannan suka cigaba da barcinsu
Cikin farinciki kusail ya juyo da baya da shirin fita daga cikin dakin
Har ya gifta inda su walisa da sarki aryan suke kwance yazo daidai jaruma marfuza
Sai kawai yasa kafarsa ya taka kafarta da karfi saboda mugunta kuma yana zaton bata iya ganinsa
Sannan ya wuce gaba yana mai murmushin farinciki
Zafin wannan takun ne yasa marfuza ta watstsake daga barcin da take
Ahankali ta bude idonta cikin shammace, tana bude idanun nata sai tayi arba da wani matashin saurayi dauke da jakunkunan guzurinsu ahannunsa
Ya kama hanya da nufin ficewa daga cikin dakin har ya daga kafarsa zai sakata awajen kofar dakin sai tayi sauri ta kwanto wata doguwar sarka daga jikin kugunta ta jefa masa
Take sarkar ta tafi da gudun tsiya ta hardo wuyansa
Sannan jaruma marfuza ta finciko sarkar da hannunta guda
Sai gashi ta finciko kusail kamar ta finciko sillen kara
Ta gwarashi ajikin bango sannan ya dawo kan kasa kawunansa a durkushe agaban kafafunta
Sautin gwaruwar tasa ce ta farkar dasu gimbiya walisa daga barcin da sukeyi tareda zare makaman yakinsu don suga abinda ya kawo musu farmakin bazato
Cikin mamaki duk suka mike tsaye yayinda sukaga marfuza ta dora wuka akan wuyansa
Tana tambayar sa abindaya kawoshi
Cikin firgice da razana kusail yace kiyi mini rai yake wannan jaruma na rantse da abin bautarki barawo ne ni sata nazo yi muku
Dajin wannan magana sai ranta ya baci harta motsa hannunta da nufin yanka wuyansa
Sai gimbiya walisa ta dakatar da ita, take marfuza ta dauke wukarta daga kan wuyansa
Har saida jini ma ya digo kasa daga jikin wukar saboda saura kiris ta yanka makogaronsa don tsabar kaifinta
Sannan gimbiya walisa ta karewa barawon kallo alokacin
dataga gabaki daya jikinsa kyarma yakeyi saboda tsabar razanar da yayi kamar kace kyat ya saki futsari a wando
Ta dora hannunta na dama akan kafadarsa tace yakai kusail yanzu haka kana da zabi guda biyu

Koda yaji ta kama sunansa sai ya cika da mamakin yadda
akayi ta san sunansa amma daya tuna aikine na sihiri sai yayi shiru da bakinsa
Walisa ta ci gaba da cewa
Acikin zabin nan guda biyu dolene kayi daya
Kodai ka taimaka mana akan bukatar data kawomu garinku ko kuma yanzun nan wukar da take hannun jaruma marfuza ta zabtare makogaronka
Cikin rawar dari kusail ya dubeta yace
Yake wannan 'yar sarki wacce bukatace daku agareni ki gaggauta sanar dani ita
Ni kuma zanyi kokari duk wahalarta sai na biya muku ita muddin zaku barni da raina
Kodajin haka sai walisa tayiwa sarki aryan inkiya
Nantake shi kuma yaje ya daga wata shimfida wacce duk kallon kurillanka baknisa kace an ajiye wani abin akarkashinta ba
Kawai sai ya fito da sandar sadauki hassanul basari da kuma wannan karamin littafin
Ya nunawa kusail yace
Abin da muke bukata kayi mana shine ka kaimu gurin mutumin da kasan zai iya koya mana wannan yaren
Idan har kayi haka to ka tsira daga mutuwa kodajin haka
Sai ya karbi littafin ya ruke shi a Hannunsa ya kura masa ido yana tunani
Daga can kuma sai yayi murmushi yace indai wannance bukatar ku to na tsira
Ku sani cewa kaf birnin nan babu wanda zai iya koyar daku wannan yare face mutum daya
Wato dattijo kusaid shine kadai mutumin da kaf birnin nan wanda zai iya koyar dakai wannan yare
Nima nasan wannan sirribne sakamakon wani lokaci na taba zuwa giftawa ta gurin da yake zaune alokacin yana bitar wani littafi wanda rubutunsa anyi shine da irin yaren da akayi wannan rubutu
Tabbas idan mukaje wajensa bukatar ku zata biya

SHIN KUSAIL YANA KAISU GURIN WANNAN MALAMIN ?
TSAWON KWANA NAWA ZASU DAUKA SUNA NEMAN WANDA ZAI KOYAR DASU WANNAN ILIMIN?
SHIN KUSAIL YAUDARARSU YAKE SHIRIN YI KO KUWA GASKIYA YAKE FADA MUSU?
DON JIN AMSOSHIN TAMBAYOYIN NAN SAI MU HADU A KASHI NA GABA
DAGA NAKU
HABIBULLAH KBR
ASHA KARATU LAFIYA
LIKE, COMMENTS AND SHARE******************HATSABIBAN SADAUKAI

CI GABAN ZUBAR DA JINI

********************4 PART C

LBR

*****************HABIBULLAH KBR

Kaf cikin birnin nan kusaid ne kadai ya iya wannan yare
saboda haka ina da yakinin cewa idan har kuka mika masa
Kudade masu yawa to tabbas zai koyar daku duk abubuwan da kuke bukata
Kodajin haka sai walisa ta kalleshi cikin wani irin kallo mai kama da rashin yarda tace
Idan har gari ya waye muka fuskanci cewa karya kayi mana
To ka sani bama kai kadai zamu kashe ba hatta danginka gaba daya
Ko mutum daya bazai tsira da rayuwarsa ba domin duk sai na yanka wuyansu da kaifin takobi na
Cikin yarda da kai kusail yace na yarda da wannan sharadin naki
Adaidai wannan guri suka tsaida hirar da sukeyi suka daure kusail yadda bazai iya guduwa ba
Sannan suka koma suka ci gaba da barcinsu
Kashe gari da sassafe
Dukkansu suka shirya suka debi kayansu suka fito a wannan lokaci basu daure kusail ba
Domin sun san bazai taba iya guduwa daga garesu ba
Suna fitowa daga gidan sai suka janyo kofa suka rufe
Sannan suka tusa keyar kusail agaba domin ya kaisu gidan dattijo kusaid
Kusail ne a kan gaba su kuma suna biye dashi abaya
Sannu a hankali suka dinga kutsawa ta cikin gari lungu da sako
Haka kusail ya dinga bi dasu, duk inda suka gifta idan mutane sukaga kusail da mutane uku abayansa
Sai kaga kowa ya kame kyam tareda ruke baki domin
Sun san cewa yau rana ce ta kare masa don a wannan lokacin kallo daya kawai zakayi masa kasan cewa acikin daren jiya ya wahala kuma baiyi barci ba
Don ganin yadda yake tafiya yana tangadi, tun suna yawo acikin kasuwar garin sai da suka fita daga cikinta
Suka shiga cikin gari suna bi lungu lungu wani lungun ma idan suka shiga sai ka zata ba mai bullewa bane
Wani abin mamakin ma shine gaba daya mutanen wannan gari ba sa kiwon kowacce irin dabba
Sai aladu domin su kadai zaka gani suna yawo ko'ina na cikin garin
Tun su walisa suna tafiyar da kuzarinsu har sai da suka sare suka dauka cewa yaudarar su yake shirin yi
Don haka sai sarki aryan ya fusata ya zare takobinsa ya dora akan wuyan kusail
Tareda cewa
Kai mufa bama son raini idan har ka bata mana lokaci
Idan karya kake gwanda ka fadamana, cikin razana yace kayi hakuri ai mun kusan zuwa gurin da muka nufa
Kodajin haka sai shima ya mayar da takobinsa cikin kufenta sannan suka cigaba da bin kusail abaya
Daga wannan guri da suke sai da suka sakeyin wata tafiyar mai nisa
Suka isa wata 'yar karamar unguwa wacce mafi yawan mutanen cikinta talakawa ne
A tsakiyar unguwarne suka iske wani dan madaidaicin gida
Wanda kallo daya zakayi masa kasan cewa gidane na talakawa
Koda isowarsu kofar wannan gida sai sai kusail yaja tunga ya tsaya yace dasu
Nan gidan ne kadai zaku sami mutumin da kuke nema idan har baku yarda dani ba to na yarda ku kashe ni
Koda yazo daidai nan a zancensa sai gimbiya walisa ta girgiza kanta
Sannan ta karasa kofar wannan gidan bisa kafafunta tana isa sai tasa hannunta ta kwankwasa kofar
Jim kadan da bugawarta sai akazo aka bude kofar ta ciki
Sai ga wani kyakkyawan dattijo ya fito daga cikin gidan
Wanda shekarunsa ba zasu gaza saba'in sa biyar ba
Kallo daya zakayiwa wannan dattijon kasan cewa dolene ya kasance mutumin kirki

Fuskarsa cike take da furfura sannan ya daura wani farin rawani akansa
Koda dattijo kusaid yayi arba dasu gimbiya walisa tsaye a kofar gidansa
sai fuskarsa ta fadada da murmushi kamar yaga 'yan uwansa na jini
Yace sannunku da zuwa yaku wadannan manyan baki ai sai ku shigo daga cikin gidan
Yana gama fadin haka sai ya juya da baya ya shige ciki
Su kuma su walisa suna biye dashi abaya ahaka har suka isa wani dan karamin daki
Wanda atsakiyarsa aka shimfida wani buzu na fata
Da zuwansu wannan daki sai kusaid ya umarcesu dasu zauna su jira shi
Nanfa dukkaninsu suka daga kai suka bishi da kallo cike da alamun mamaki akan fuskokinsu
Jim kadan da tafiyar kusaid sai gashi ya dawo hannunsa ruke da wani katon faranti
Wanda asamansa akwai kwanuka guda biyu da kuma kofuna hudu
Ya ajiye agabansu sannan ya basu umarnin da suci wannan abincin
Cikin mamaki dukkansu suka kalli junansu domin basu taba ganin mutum mai karamci irinsa ba
Koda kusaid ya ajiye musu wannan farantin abincin sai ya juya ya basu guri
Tafiyarsa keda wuya sai su gimbiya walisa suka sa hannu suka bude
Kwanukan abincin
Ba komaine acikin kwano na farko ba face gurasa da zuma
Na biyun kuwa gasashshiyar kazace acikinsa
Ba tareda bata lokaci da kuma tsoro ba
Suka ci wannan abincin harda kusail sannan suka sha ruwa
Basu dade sa gama cin abincin ba sai ga dattijo kusaid ya dawo
Har a wannan lokacin fara'ar dake kan fuskarsa bata gudu ba
Kawai sai shima ya zauna a can gefe daya da inda suke suna kallon juna atsakaninsu
Sannan yace
Yaku wadannan manyan baki ina yi muku barka da zuwa
Sannan in ba zaku daku ba inaso insan suwaye ku kuma daga ina kuke bayan haka wacce bukatace ta kawo ku guri
Dajin wadannan tambayoyi sai gimbiya walisa tace
Yakai wannan dattijo muna godiya da irin karramawar da kayi mana
Ka sani nice gimbiya walisa 'ya agurin sarki fadarul munnar, sannan ta nuna sarki aryan
Wannan kuma shine sarki aryan, waccen macen dake kusa dashi itace jaruma marfuza 'yar uwa a gurin sarauniya suzaila
Ya kai wannan dattijo ka sani cewa
Ba komai ne ya kawo mu gurinka ba face muna so ka sanar damu ilimi akan wadannan abubuwa
Take ta kwanto sandar hassanul basari daga gadon bayanta
Ta mikawa kusaid ita tare da ciro wannan karamin littafin daga cikin aljihunta
Taci gaba da cewa yanzu abin da muke bukata shine ka koya mana yadda ake karatu da rubutu na wadannan abubuwa harda ma yadda zamu fassarasu
Idan har kayi mana wannan to zamu baka dukiya mai tarin yawa
Koda ganin wadannan abubuwa guda biyu sai kusaid ya cika da mamaki
Ya dago da kansa alokacin da idanunsa suka cika da kwalla yace
Yaku wadannan baki masu daraja ku sani cewa wannan kwallar da nake bata komai bace face kwallar farinciki bisa ganinku
Ku sani cewa tun cikin shekaru talatin baya an sanar dani cewa zakuzo gurina
Kuma kune wadanda zasu karshen takadirin boka wato sahibul ukub
Amma kafin ku sami nasarar aiwatar da hakan dole sai kun fuskanci jarraba kala daban daban
Nima nasan hakan ne alokacin ina tashen samartaka
Alokacin na shiga cikin daji da zummar yin farauta kawai sai ba fada tarkon wasu shu'uman matsafan aljanu
Suka dana mini tarko domin su kasheni

Amma sai wani kyakkyawan matashin aljani mai matukar kwarjini da cikar kamala
Ana kiransa da suna khadimul islam yazo shi kadai ya fasa rundunar su da karfin tsiya ya kwace ni daga hannunsu
Tun daga wannan ranar muka kulla abota tsakanina dashi
Kuma tsawon wannan lokaci nima ina cikin addinin bautar gumaka
Shi kuma ya kasance ma'abocin addin musulunci
Saida muka shafe lokaci mai tsawo muna abota atsakaninmu
Ba tareda yana tilasta mini kan dole saj na karbi addininsa ba
Daga bayane ni da kaina na gamsu addininsa ne addinin gaskiya
Kuma na nemi daya shigar dani cikin wannan addinin
Agurinsa na karbi addinin musulunci kuma shine ya koyar dani yaren da aka rubuta wannan littafi dashi
Kuma ya umarceni da in boye addinina har zuwa sanda wasu matasa guda uku zasu zo wajena domin na koyar dasu wannan yaren
Yaku wadannan jarumai ku sani cewa akwai gagarumin aiki agabanku
Kuma ubangijin musulunci ne kadai zai taimakeku ya baku nasara akansa
Kuma tabbas zan koyar Daku duk abubuwan da kuke bukata amma fa ku sani hakan bazai taba amfanar daku komai ba
Har sai kun ajiye addinin tsafi kun yi imani da ubangijin musulunci
Domin shi musulunci haskene kafirci kuma duhu kuma dole kunsan haske da duhu basa haduwa guri daya face hasken ya kashe duhun
Kunga kuwa dolene ku ajiye tsafe tsafenku kuyi imani da ubangijin musulunci akowanne lokaci sannan in zaku nemi taimako ku nema daga gareshi
Kodajin wadannan kalamai sai duk su ukun sukayi tsit kuma jikinsu yayi sanyi hardashi kansa barawo kusail
Daga can sai sarki aryan da jaruma marfuza suka dubeshi suka ce
Duk munji batunka don haka idan ba zaka damu ba zamuso ka bamu dama domin mu danyi shawara tsakaninmu
Dajin haka sai kusaid yayi murmushi yace ba matsala kuna da damar hakan domin a addinin musulunci babu takurawa
Take su sarki aryan suka koma gefe marfuza ta duni aryan tace
Yakai abokin tafiya shin kana ganin cewa mu ajiye addinin mu mu karbi wannan sabon addini
Kada ka manta da cewa dukkanmu muna kan tafarki dayane na samar da zaman lafiya acikin duniya
Kuma ina ganin wannan addinin shine babban makamin da zamu tunkari yarima walisu dashi
Kodajin haka sai shima yace kwarai kuwa bamu da wani zabi face karbar wannan addini
Domin ina da tabbacin gaskiyane komai na cikinsa
Take duk su biyun suka koma inda suke zaune
Suka dubi juna su da gimbiya walisa tareda gyada kansu
Kawai sai suka dubi kusaid sukace mun amince da wannan addini naka dari bisa dari
Don haka ka gaggauta shigar damu cikin wannan addini naka
Dajin haka sai farinciki ya lullube kusaid nantake ya biya musu kalmar shahada tareda kusail
Nantake duk su hudun suka maimaita

Tun a wannan aranar kusaid ya fara koyar dasu tsarki da kuma ilimin addinin musulunci
Tareda koya musu yadda zasu karanta rubutun dake cikin littafin
Da ike dukkansu allah ya basu kaifin kwakwalwa sai gashi suna haddace duk wasu abubuwa da yake koya musu cikin kankanin lokaci
Kamar rubutashi ake acikin kwakwalwarsu shi kansa kusaid yayi matukar mamaki yadda suke saurin haddace abinda yake kowa musu
Saida suka shafe mako biyu acikin wannan gida sannan suka iya wannan yare sosai
Kuma har suke iya karanta wannan littafi tareda

Please Login or Register in order to submit comment