Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya daki sandar da take hannunta
Take sandar ta kwace daga hannunta ta fadi a can wani gurin daban
Cikin wani rami mai matukar duhu kuma babu komai acikin wannan ramin face karafuna masu kaifi da tsini ta yadda koya mutum ya fada cikinsu to shikenan an gama da babin rayuwarsa
Lokaci guda dukkansu su uku suka fado kasa bayan duk sun gwaru da jikin bangayen fadar
Cikin karfin hali dukkansu suka mike tsaye suka kara tahowa kansa
Suna wani irin karaji cikin tsananin fusata shi kuma sarki aryan sai ya kwanto daya takobin da take sakale abayansa
Ya cillawa walisa ita ta cafe suna zuwa inda yake sai suka fara kai masa
Mugayen sara da suka tako'ina domin suyi gunduwa gunduwa da sassan jikinsa
WOHOHO!
GAKIKA WANDA YA RIGAKA KWANA DOLE YA RIGA KA TASHI
ai kuwa ana fara wannan fadan ne su walisa suka gane cewa
Ba da walisu suke fada ba da boka sahibul ukub sukeyi
Domin karfin saran da yake kawo musu alokaci guda ya ninka nasu sau goma
Hakama zafin namansa da kuma iya yakinsa
Duk irin karfin damtsen dasu walisa suke takama dashi
Sai gashi ya zamo na banza domin wani irin mahaukacin duka yake yi musu tako'ina
Duk sanda ta kawowa dayansu duka idan ya kare shi da takobinsa
sai ya durkushe har kasa bisa cinyoyinsa saboda karfin dukan nasa
Su kuwa ko sau daya sun kasa samin damar da zasu taba koda rigar jikinsa da makamansu
Duk wanda kuwa ya daka da hannunsa sai yaji kashin gurin ya amsa kamar zai karye
Kafin a dauki lokaci mai tsawo tuni ya hadawa su walisa jini da majina gabaki dayansu. A wannan lokaci saida suka tabbatar da cewa basu taka wani mataki ba a fannin jarumtaka
Kuma idan harsu sadaukai ne to shi buwayar sadaukai za'a kirashi
Cikin kankanin lokaci suka hargitsa fadar gabaki dayanta
Gininta ya dinga zabtarowa daga sama yana fadowa
Lokaci guda sai kaga ya shuri katon dutse mai girman gaske ya jefo musu
Inbadon suna kaucewaba da tuni sun dade da nutsewa acikin duwatsu kuma daya daga cikinsu bazai tsira ba
tun kafin su dauki wani lokaci mai tsawo har fadar ta rugurguje guri gudane wanda ginisa bai fadi ba
Wannan guri kuwa shine wajen da sandar hannun walisa ta fada
Koda walisu yaga abinda fadarsa take cikin sai ya bude fuka fukansa kamar tsuntsu ya shuri su walisa kamar yadda shaho yake shurar 'ya'yan kaji ya luluka dasu sararin samaniya
Sai gashi sun sauka a saman gajimare suna sauka sai yayi wulli dasu
Can gefe ya dube su yace mai kuke jira ai sai ku taso mu ci gaba.
Cikin tsananin juriya su walisa suka mike tsaye suna masu dafe kugunsu suna layi kamar wadanda suka sha giya suka bugu
Kafin su karaso inda yake tuni yasa kafafunsa biyu ya dake su atsakiyar kirji
Harsai da sukayi sama sannan suka fado jini yana yoyo daga cikin bakin su
Cikin dariyar mugunta walisu yazo ya sunkuya ya ciccibi wuyan
Walisa da marfuza ya shakesu sannan ya daga su sama kamar ya ciccibi sillen kara
Har sannan bai daina dariyar da yake yi ba take idanunsu suka firfito waje
Suka fara ganin taurarin mutuwa saiga kafafunsu na wutsin wutsil a sama kamar kare ya kama kyanwa
Da ganin abinda yake shirin faruwa gasu walisa sai sarki aryan cikin dauriya ya daka tsalle ya kawowa walisu sara ta bayansa d nufin ya tsargeshi gida biyu
Saidai kash ya makara domin tuni ya ankara dashi kafin takobin ta sauka akansa
Tuni yasa fuka fukinsa guda daya ya makeshi
Take ya sulale kasa
Sannan ya saki su walisa suka zube kasa kamar matattu don ko kwakwkwaran motsi basa iya yi
Kawai sai yayi dariya sannan ya bude fuka fukansa ya tashi tare da runtse idanuwansa yana karanta dalasimansa na tsafi
Koda ya kara nisa acikin iska saiya juyo kasa yana mai nunasu da tafukan hannunsa guda biyu
Nantake wata bakar guguwa ta fito daga cikinsu ta dinga tura su walisa kasa
Ai kuwa sai iskar ta dinga turosu kasa kafin yan dakiku har sun bar saman gajimare sun sun dawo cikin fadar tasa
Amma duk da haka sai iskar ta dinga dannasu cikin rusasshen ginin
Har sai da suka nutse acikin karkashin kasa kuma har a sannan walisun bai daina binsu ba
A wannan lokaci duk su ukun babu wanda bai sami manyan ciwuka ajikinsa ba
A sannan ne suka lura cewa walisu ya yaudaresu ya karya alkawarin dake tsakaninsu yayi amfani da karfin sihirinsa
Da yin wannan tunani sai take suka fara karanta addu'o'i suna neman taimako ubangiji
Ai kuwa faruwar hakan keda wuya sai sukaji wani irin gagarumin karfi ya shiga jikinsu
Kuma wannan guguwar a take ta dauke dif kamar anyi ruwa an dauke
Nan ta gabaki dayansu wata iska ta shigo cikin karkashin kasar ta daukesu cak tayi sama dasu
Ta sauke akan kasa a hankali a wannan lokacine sukaji duk wani zafi da zugi da suke ji yafita gaba daya daga jikinsu
Koda walisu yaga wannan abin al'ajabi sai ya fusata
Ya daka tsalle ya taho a saman iska ya kawo musu wani mahaukacin sara
Su kuwa sai suka kwalla kabbara da karfin gaske suka sunkuya
Saran nasa ya sami wani katon dutse dake bayansu
Saboda karfin saran saida dutsen ya dagargaje kamar an nika gari
Nan sarki aryan yayiwa walisa wata inkiya da yatsun hannunsa
Kawai sai ta ruga da gudu zuwa inda sandarta ta fada
Jaruma marfuza tana biye da ita shi kuma sarki aryan ya tsaya suka ci gaba da fafatawa da walisu
Walisa na zuwa daidai ramin saita daka tsalle ta fada cikin ramin
Kafin ta dira kasa tuni marfuza ta kwanto sarkar dake kugunta ta jefa mata
Cikin zafin nama walisa ta cafe igiyar tana sauka cikin ramin kafin jikinta ya sauka acikin tsinin makaman dake ramin tuni ta zura hannunta ta zaro sandarta
Sannan ta kara daka tsalle ta taka jikin bango kamar ta kasance biranya
Ta fice daga cikin ramin tana fitowa ta iske walisu ya baro inda suke fafatawa da aryan yazo bakin ramin
Yana zuwa saiya kawo mata mahaukacin duka da sandar tsafinsa
Cikin bakin zafin nama tasa sandar hannunta ta kare dukan nasa
Koda haduwar wadannan sandunan guda biyu sai sandar tsafin walisu ta karye gida biyu
Kawai saitasa hannunta itama ta gabza masa wani wawan naushi
Harsaida hakorinsa guda yayi fitar burgu saboda karfin naushin take ya kwarara uban ihu saboda zafi da zugin da yaji
Bai san sanda yaja da baya ba su kuwa su walisa har a sannan basu daina karanta addu'o'in da sukeyi ba
Suna dada tunkaro inda yake da ganin haka sai ya fara amfani da sihirin tsafinsa
Domin ya tashi sama ya gudu amma sai yaji ya kasa koda bude fuka fukansa
Da ganin haka sai ya ci gaba da watso musu tsafi kala daban daban don ganin ya sami nasarar hallaka su amma ina
Ko kadan sihirin nasa yaki yayi tasiri akansu kuma basu fasa tunkaro inda yake ba
A wannan lokaci ganinsu yake kamar wani dunkulen garwashin wuta wanda yake barazana ga rayuwarsa
A sanda suka iso inda yake a daidai lokacin ne suka gama karanta addu'o'in da sukeyi
Suna zuwa sai suka tofa masa ajikinsa
Koda saukar tofin yawun da sukayi masa jikinsa sai take ya kwarara uban ihu
Ya sulale kasa kawai sai ganin ruhin boka sahibul ukub sukayi cikin siffar hayaki ya fita daga jikin walisu
Yana ci da wuta tareda kwarara ihun fitar rai kafin cikar dakika uku tuni ya kone kurmuS

Adaidai lokacin suffar yarima walisu ta sake bayyana kamar yadda da yake abaya
Fuka fukan jikinsa ma duk sai suka bace bat kyakkyawar suffar jikinsa ta bayyana
Kawai sai ya bude idanunsa a hankali domin yaga a inda yake
yana bude idanun nasa sai yayi arba da 'yar uwarsa walisa
Koda yin arba da ita a gabansa kuma yaga a gurin da suke saiya mike tsaye
Zumbur suka rungume juna suna masu farin cikin sake ganin juna
Sannan yace ya 'yar uwata tayaya kika iya zuwa wannan guri domin cetona ?
Dajin wannan tambayar sai nan take ta kwashe labarin komai ta sanar dashi
Sannan ta nuna masa su jaruma marfuza amatsayin abokan tafiyarta
Kawai sai ya saketa ya juya domin yayi musu godiya
Koda suka hada idanu da jaruma marfuza sai dukkansu suka kame kam
Kamar gumaka ko kifta ido basayi alokacin sai sukaji zuciyoyinsu suna bugawa da karfin gaske fiye da yadda suke bugawa a baya
Da ganin wannan bakon yanayi da suka shiga sai walisa ta shiga tsakaninsu ta katse kallon juna da suke
Tace haba walisu yanzu abindaya kamata kayi shine ka gaisa da abokan tafiya ta
Dajin wannan batu sai murmushin yake tareda sosa keya yace
Lallai yarinyar nan kin raina ni tunda har kika shiga tsakanina da wannan budurwar wacce itace mace ta farko da zuciyata ta kamu da soyayyarta
Kodajin wannan batu sai gabaki dayansu suka bushe da dariya

Kawai sai walisu ya karasa gurin sarki aryan ya mika masa hannu suka gaisa sannan yace
Na gaida babban sarki mai daraja mai mulkin birnin shawana
Kodajin wannan batu sai mamaki ya kama sarki aryan yace tayaya akai kasan ni
Alhalin baka taba zuwa birnina ba?
Dajin wannan tambayar sai walisu yayi murmushi yace ai bai kamata kayi mamaki don ganin na sanka ba
Domin nida 'yar uwata munsha ratsawa ta cikin birninka alokacin da kuke gudanar da gasar jarumta da kukeyi duk shekara
Kawai bamu taba sha'awar shiga wannan gasar bane
Duk sanda mukazo saidai mu tsaya kurum mu kalli salon fadanka sannan mu wuce
Dajin wannan batu sai sarki aryan ya dago. Suka hada ido da gimbiya walisa
Kawai sai ta girgiza kanta alamar gaskiyace maganar daya fada
Sannan walisu ya wuce gaba inda inda marfuza take ya mika mata hannu
Tareda yin murmushi agareta yace
Yanzu nasan kinsan komai akaina bazan ji kunya ba ko kadan idan kika ce bakya sona
Amma ki sani ita ribar soyayya akoda yaushe itace ka sami wanda yake sonka
Babu babban ciwo a rayuwa kamar kaso wanda baya sonka da soyayya
Idan har kin amince dani to zan maye miki gurbin 'yar uwarki dana hallaka miki alokacin da bana cikin hayyacina
Hatta duniya saita san da soyayyar mu yadda ko bayan mutuwarmu ba za'a manta damu ba
Kodajin wadannan kalamai sai marfuza ta kame ta kasa cewa komai
Domin take taji gabaki daya zuciyarta ta manta da babin sarki aryan
Soyayyar walisu ta mamaye zuciyarta gabaki gaba daya
Bata san sa'adda ta rungume shiba shima ya rungumeta suna masu kwantarwa da juna hankali
Daga nan gabaki daya suka dunguma suka sauko daga kan wanna tsuburin
Sannan suka yi nutso acikin wannan tekun harsaida suka ketare shi suna fita daga cikinsa sai tsuburin da fadar take kai gabaki dayansa yayi bindiga ya tarwatse
Duk wannan abu daya faru shima gunki larazub yana kallo daga cikin rijyar da yake a can bangon duniya
adai dai lokacin da ruhin boka sahibul ukub ya gama konewa a take shima ya kama da wuta gabaki daya fadar tasa shima ta tarwatse kamar bata taba wanzuwa ba
Bayan su walisa sun ketare tekun ne kawai sai sukayi arba da sarki fadarul munnar
Alokacin yana tsaye a bakin tekun yana kallon yadda tsuburin yake rushewa
Bai ma san cewa su walisa sun fito daga cikinsa ba shi a zatonsa suna cikin gini ya dannesu
Ba zato ba tsammani sai yaji an dafashi ta baya
Yana juyowa saiyaga su walisa gabaki dayansu sun fito a rate kuma tareda yarima walisu
Koda ganin haka sai nantake yace
Nayi imani da ubangijin musulunci domin shine kadai wanda ya cancanci. Abauta masa tunda har ya baku karfin da kuka iya karawa da boka sahibul ukub
Kodajin wannan batu sai farinciki ya lullube su shima walisu take a nan
Ya rungume mahaifinsa suna kukan farincikin sake saduwa da juna
Daga nan gimbiya walisa ta biya musu kalmar shahada suka maimaita
Daga nan suka dunguma gabaki dayansu suka kama hanyar komawa birnin madaril adfam suna masu karanta addu'o'in daurin kasa
Dalilin addu'o'in da suka dinga yine yasa tafiyarsu ta dinga sauri
Tafiyar mako biyu ita suka dingayi acikin yini guda kuma duk dajin da suka ratsa duk irin halittun da suke cikinsa
Ta farat daya suke gamawa dasu don haka tafiyar mako guda kacal sukayi suka isa birnin madaril adfam
Aranar da suka isa birnin mutanen garin sukayi kyakykyawan shagalin biki
Don murnar dawowar sarki fadarul munnar da ''ya'yan sa guda biyu wato yarima walisu da gimbiya walisa
Kuma acikin wannan ranar ne suka musuluntar da mutanen birnin gaba dayansu hadda boka makassar
Washe gari kuma aka daura auren gimbiya walisa da sarki aryan
Da kuma yarima walisu da jaruma marfuza a wannan rana anyi shagali sosai
Domin saida aka shafe mako uku ana shagalin wannan biki kuma anyi rabon dukiyoyi masu yawa
Kamar ba zasu kare ba
Mawaka, maroka, makada da masu rawa a wannan shekarar sun sami dukiyar da basu taba samun kamarta ba
Bayan an gama wannan bikine sarki aryan ya dauki matarsa gimbiya walisa gaba daya suka koma can birninsa na shawana da zama
Bayan sun isa birnin nasa ne shima ya musuluntar da gabaki daya mutanen birnin
Wadanda kuma sukaki yarda su musulunta sai ya koresu gabaki daya daga birnin nasa

Tun daga wannan lokaci duniya ta manta da fargabar da suke ciki
Ta yawaita ZUBAR DA JINI adoron kasa kuma aka daina samun banbanci tsakanin talaka da mai kudi ko mai mulki
Manyan sarakuna suka daina zaluntar na kasa dasu
Saida takai cewa talakawa ma sun ragu a duniya domin a kullum tattalin arziki kara bunkasa yake adoron kasa
Yawan kashe kashe da zalunci duk aka dainasu
Saboda zaman lafiya saida takai ga cewa dabbobima suna rayuwa cikin nishadi da kwanciyar hankali
Kai tun ana tunawa da sahibul ukub saidaya zamana cewa an manta dashi gaba daya a duniya sai mutane kalilan ne suke iya tunawa dashi

ALHAMDULILLAH ANAN NE KUMA A WANNAN RANA TA LARABA 9/10/2019
DA MISALIN 3:51
MUKA GAMA DA WANNAN LITTAFI MAI SUNA ZUBAR DA JINI
WANDA NI HABIBULLAH MUHAMMAD KABARA NA RUBUTA
KUMA INSHA ALLAH WANNAN POST DIN SHINE POST DINA NA KARSHE A WANNAN KAFAR SADARWA TA FACEBOOK
INA FATAN WANDA NA BATAWA RAI YAYI HAKURI YA YAFE MINI
BAI ZAMA LALLAI KU SAKE GANIN POST DINA BA SAIDAI NA WASU MARUBUTAN
DAGA YAU ZAIYI WUYA IN SAKE POST DIN LABARI
DON HAKA SAI MU CI GABA DA BASU HADIN KAI YADDA SUMA ZASU NISHADANTAR DAMU
KUMA BAYAN HAKA ZANYI AMFANI DA WANNAN DAMA WAJEN JINIJINA
GA DUKKAN MAKARANTA LABARAINA WADANDA DA KARFIN GWUIWARSU DA KUMA TAIMAKON UBANGIJI NA GAMA RUBUTA WANNAN LITTAFI SABODA NUNA DAMUWARSU AKANSA
KAMARSU

UMMU JAWAHEER
ZATION ASHFAT
SAYYADI LAWAL SOJA
SiILAT IBRAHIM
MUHAMMAD ADAMU YAHYA
WIZ BALE MASTER
ALHAJI JAMEELU UMAR
BASHIR A UMAR
MUHAMMAD AUWAL HABIBULLAH
UMAR ABDUL HADI MATI
AHMAD ZIZA DAN ZAKI
BADEEYAT DEEYAT
ZUBAIR A ZUBAIR
ISMA'IL ALIYU S FADA
NUSYBA YAHYA
ZEENAT ZEENAT
MURTALA SHU'AIBU KAMFA
IDRIS GONI LAMISULA
ANAS RABI'U RANO
SALAFUSSALIH SHAFI'U
NUSHFAT NURA
'YARLELE MARYAM
MARYAM MAI ZAMANI
SUFI DALHATU
UMAR AMEENU
ALHAJIN GALA GALA
MUFEEDAT MUHAMMAD
FADIMATU FADIMATU
IMRAN MIJIN HAJIYA
ABUBAKAR AHMAD
ENGR ZAIDU HARUNA
SULAIMAN HUMAIRA
MAJEE MAHMAH
LAMINU MUHAMMAD
ZULAIHART ISAH sHIRAH
MARYAM MADAKI
KADIJA ALIYU
SUFIYANU HUSSAINI MASA
SUFI DALHATU
SADIYA SHU'AIB DAN GANA GWANTU
IBRAHIM ALIYU
SANI YAHAYA FARSANGU
IMRANA SUNNAH DAMISAWA
ISMA'IL MIKO
MURTALA S FAWA WUDIL

DA'AKWAI MUTANE DA YAWA DA BASUJI SUNANSU BA
DON ALLAH AYI HAKURI ABINNE DA YAWA
DAGA WANNAN LOKACI NAKE MUKU FATAN
ALHERI DAGA NAKU HABIBULLAH KBR
WHATSAPP NUMBER
09081494322
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment