Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

munyi laifi ? ko yanzu da
zance zanyi aure sai ka ji bala'i na tashi nakan
rasa su mata wane iri ne.
Dr. khalifa yabushe da dariya yace "na san duk
yunwa ce tasaka wannan surutun ai kai da sauki
ma tunda ka iya shiga kitchen ka sarrafa
abincinka kaci ni ko tea ba na iya dafawa.
Dr.hafiz yace "to ai kuwa ka koya mata ba su da
tabbas surutu da soyayya a waje suka iya idan
an shigo gdan sai a hankali musamman idan an
fara ajiye yara, bara in dafa indomie kaina har
ciwo yake sbda yunwa.
Bayan ya gama dafa indomie din suka mike a
kasa suna ci yace "mutumina wai wace babbar
magana ce ?
Yace "ina fatan ka gane fatima"
Dr. hafiz yace "ba zan kasa fahimtarta da wai ba
domin na fahimci zuciyarka ta amsheta da
gaggawa.
Yace "kwarai ba ka yi fahimtar kuskure ba, kallo
daya nayiwa yarinyar naji zuciyata ta aminta
tazamo mata ta.
Dr. hafiz yace "to ai bbu matsala yarinyar datake
rayuwa a cikin gdan ku na yi farin cikin han.
Dr. khalifa yace "kai dakata saura sati biyu
bikinta.
Dr. hafiz yace "to ba sai a lalubo wata ba abinda
ga matan nan dayawa dakansu suke cewa ma
suna so.
Dr. khalifa yace "kai likita mata suna suka tara,
duk yawan dasukayi irin su fatima daban suke, a
iya budewai idona da yawace yawace na ban taba
ganin mace mai kyaun fati ; a ba, tare da kyaun
fuska ,dubi yadda tsarin halittar jikinta
yake,habawa wannan ai itace mace mutumi na.
Dr. hafiz yayi dariya sosai yace "kai wani irin
kayatarwa fatima tayi maka, ne karude haka ?
Haba likita kada kabari fatima taji za ta rainaka
ka ga yarinya ce karama ko ka mance kana cewa
ba ka son karanar yarinya ?
Dr. khalifa yace "kai tafi chan wannan lokacin ya
wuce ba zan iya hakura da yarinyar nan ba.
Dr. hafiz yabata rai yace "kai Abbakar muyi
magana ta gaskiya yarinyar daya rage saura sati
biyu bikinta yya za ayi kace kana sonta ? ko a
shari'ance ba kyau nema cikin nema ,kayi hakuri
kawai mace in dai mace kake bukata za kasamu
wadda tafi fatima kyau sai dai in fa fatima kake
nema.
Dr khalifa yadan marairaice yace "haba dr. hafizu
yaya za ayi ka sanyayar min da jiki ? bayan ka
san ban taba nuna maka wata diya mace dana
damu da ita ba ballantana har in nuna damuwata
akan sonauranta, tunda nagaya maka ai ka san
dagaske nake ya kamata kataimake ni da
shawarar dazan samu mafita ba kasace min
guiwa ba.
Dr. hafiz yace "to ai ni banga hanyar mafitar bane
Abbakar, sati biyu fa yarage biki sai kuma muce
muna so ? wannan ai son kai ne da zuciya, kuma
kasani son kai da zuciya ba dabi'a ce ta mutan
arxiki ba.
Dr. khalifa yace "knan so kake kace min sai dai
inyi hakuri da fatima ?
Yace "Don Allah kayi wannan hakurin sai Allah
yabaka wacce tafita....
Dr. khalifa yace "kai hafiz daina min wannan
maganar da wuya in za tayiwu bakasan menake ji
bane game da wannan yarinyar, ban taba sanin
haka so yake ba.
******
Tun a wannan rana mama tafara shirya amarya
fatima da kayan gyaran jiki na mata suka tunkari
lamarin dagaske, batasan rikicin da dr. khalifa ke
ciki game da matsananciyar soyayyar fatima da
ta damki zuciyarsa ba, a wannan daren yakasa
sukuni yakwana yana tunanin tawace hanya zai
samarwa kansa mafita.
Abin da dai yasawa kansa shi ne ko ta wani
hanya zai mallaki fatima babu yadda za ayi yayi
sakacin dazai rasa ta, bai san haka ciwon so
yake ba sai yau.
A gdan fatima takwana suna tattauna yadda biki
zai kasance, abinda fati take jaddadawa ummi shi
ne "ta sani khalifa sbda ba ya da tausayi, tace "ni
kam ummi na rasa yadda zanyi da takaicin dana
ke ji a raina game da yaya khalifa, ko ganinsa ba
na son yi sbda kawai ya nuna ba ya sonki.
Ummi tayi murmushi tace 'to yaya zanyi na
zubawa sarautar Allah ido na zubawa dr. khalifa
ido, na tabbaatarwa raina ko ban samu dr. khalifa
ba to zan tabbatar wata diya mace bata same shi
ba, idan narasa shi sai dai kowa ma yarasa .
Fatima tace "kina nufin za ki hanashi aurene ?
yaya mutumin da ka kaasa jawo ra'ayinsa
yasoka za kasawa ranka cewa za ka iya hana shi
aure ?
Ummi ta girgiza kai "ba aure xan hana shi ba ban
isa in hanashi aure ba ni dai na ce sai dai kowa
yarasa .
Riga da zani na atamfar egyptian ce a jikin fatima
tana tsaye ita kadai a kitchen tana suyar kosai,
kawai ganin mutum tayi a kusa da ita yana fadin
"fatima aiki ake yi ne ?
A firgice tawaiwayo tadubi dr. khalifa yana sanye
da doguwar riga fara kal kamshi mai dadin gaske
yana tashi a jikinsa, ta matsa gefe ganin yadda
yatsaya daf da ita kamar zai taba ta, yayi
murmushi yace "ya kike matsawa haka kamar
kinga wani dodo ? zo ki kwashe kada yakone.
Ta katsa motsawa sai gabanta ke faduwa a
lkacin ummi tashigo tana fadin "fatima kin
gama ?
Ganin wanda ke tsaye a kitchen din yasata
tsayuwa turus tana kallonsa shi da fatima, ganin
ummi yasa yatsuke fuska yafice daga kitchen din
ummi takwashe kosai tana fadin "yau kuma meya
kawo doctor kitchen din nan ko wani abu yake
nema ?
Kokarin da fatima tayi shine na daidita muryarta
don kada ummi tazargi wani abu a ranta tace "ni
ma gani nayi ya shigo.
Kallon da ummin tayi mata shi ne yasa tafahimci
kuskuren ta a bisa abinda tafada, to sai dai kuma
batasan abinda za tafada din ba in ba hakan
tafada ba, jikinta yakara sanyi sosai ganin ummi
bata sake magana ba, takwashe kosan tace
tadakko kunun gyadan dasuka dama zuwa falo.
Bayan sun gama shirya tebur din ne tadubeta
tace "ki je kigayawa doctor an gama shirya tebur
kada yai sanyi yakasa ci.
Cikin dacin rai fati tace "ni ce ma zan fadi mai ?
kin taba ganin na nufi hanyar dakinsa.
Ummi ta tabe baki tace "ai ba abin zafi bane gani
nayi ya fi son yi miki magana fiye dani amma kar
ki damu bari ni inje in gaya mai.
Fatima taja tsaki tawuce daki, yayin da ummi
tanufi dakin dr. khalifa ta kwankwasa yace
"waye ?
Tace "ni ce ummi.
Ga mamakinta sai yace "shigo"
Ta bude jikinta ba karfi yana kwance bisa gado
yanuna wata kujera yace "zauna in miki tambaya.
Ummi na son kallon fuskar dr. khalifa yana yawan
burgeta nan da nan taji hawaye ya taru i donta
tayi kasa da kanta, yana sane da halin datake
shiga idan tana kusa dashi yashare domin shi ma
din a halin yanzu abin tausayi ne duk yadda take
son sbi ya fita son fatima kuma ya fita shiga
hadari domin kuwa gab yake da yayi babbar
asarar rasa fatima.
Ke ummmi gaya min dangantakar ki da fatima".
Abin da yace da ita knan lamarin dayasa tadago
cikin sauri zuciyarta na bugawa sosai tace "ban
gane ba yaya khalifa.
yamike zaune bai ce komi ba, tunanin da yake kai
komo a zuciyarsa shi ne shawarar da dr. bashir
yaba shi duk a daren jiya lokacin daya same shi a
waya yabashi labarin halin daya ke ciki yace
"Bash don Allah kada ka kashe min guiwa ba zan
iya hakuri da fatima ba ni kadai nasan halin da
zuciyata ke ciki.
Dr. bashir yayi shiru kamar ba zaiyi magana ba.
Khalifa yce "ya ya naji ka yi shiru.
Bashir yayi ajiyar zuciya yace "Abbakar ta yaya
xa a maido wannan aure a kanka bayan sati biyu
yarage kace ayi mata aure.
Yayi tsaki yace "amma dai ni ne nafada maka
saura sati biyu ayi bikin ko ? ka ga ba na bukatar
kasanar dani shawara dai nanemeka bashir.
Yace "to shi me rai ba ya rasa motsi, hanya daya
ce wata kila idan munbi za mu iya dacewa.
"Fadi inji"
Bashir yace "ta hanyar ummi da mama ne kawai
za mu iya yin nasarar jan hankalin fatima idan da
rabo sai ayi nasara.
Ummi tace Bashir ?
Ya amsa "ita nace dalilin dayasa nace ita kuwa
inada labarin cewa fatima ba ta da kawa aminiya
abokiyar shakuwar data wuce ummi, ummi na iya
sauya ra'ayi da tunanin fatima sbda yarda da
amincin dake tsakaninsu, yayin da mma ke da
girma a idon ummi ba ta iya musa maganar
mama.
Dr. khalifa yajinjina labarin a ransa yace "hakane
Bashir to amma fa kada ka manta ba wanda
ummi ke so sai ni, ban amince da auranta ba ta
yaya za ayi ta amince da wannan batu ?
Ba ka ganin za tayi amfani da wannan damar gun
lalata min al'amarina da fatin ?
Bashir yace "to ai daman ba kai tsaye za kagaya
matan ba sai ka bi tawasu hanyoyin na hikima
wanda zaisa ta fahimci kana sassauta zuciyarka
akanta,ma'ana kadinga sakar mata fuska kuna
hira kuma karara kanuna mata cewa kana
bukatar ta taimaka maka akan fatima za kayi
mata duk abinda take so, idan kayi mata za ta
amince tunda tana sonka ba ta son damuwarka,
sannan ita kuma mama ka marairaice mata sosai
kanuna mata ba za ka iya rayuwa ba fati ba, so
so ne amma son kai ya fi da sannu za ta tausaya
maka tagoya ma baya.
Dr. khalifa yakashe wayar kansa a daure tamau
yana jinjina yadda zai iya jan hankalin ummi har
ta taimaka masa, bayan magana ma ba yi mata
yake ba, ya kwana yana tunanin abin ga dumbin
ciwon so na karuwa a zuciyarsa har yana jin ina
ma zai iya fidda son fati daga ransa ya huta,
amma ina duk yanayin dazai shiga in dai zai
mallaki fatin dole yajure tunda mallakar ta shi ne
kadai kwanciyar hankalinsa da farin cikin
rayuwarsa, amma fa yana takaicin hakan bai
damu da lallaba mama ba ya san tana sonsa da
tausayinsa, ummin ce dai matsalarsa kuma ya
amince ta hanyar ummi zai iya cimma nasara..
Wannan shi ne dalilin dayasa da gari yawaye
yanufi kitchen ya san ummin ce ke dafa abincin
safe a gdan ga mamakinsa sai yaga gimbiyar ce
a kicin din...
Yakatse tunaninsa anan yadawo da ganinsa ga
ummi wadda tayi tagumi tana goge hawayenta
wadanda tayi kokarin tsaida su suka ki tsayuwa
takyalesu suyi ta zubar lokacin su ne.
Ummi"
Muryar dr. khalifa ya ratso kunnanta da sassan
jikinta tadago kai suka kalli juna tace "Na'am".
Ina son ki yi min wani taimako daya za ki iya ?
Idan bai fi karfina ba insha Allahu zanyi maka,
fada min inji"
Ummi "inason kawarki fatima.
Inason in aureta za ki iya taimaka min ki ja min
ra'ayinta a fasa ba musbahu auranta a bani ?
Wai shin mafarki ne wannan ko gaske ?
Dr. khalifa datake tsananin so ne yake gaya mata
da bakinsa cewar fatima aminiyarta yake so ya
aura har yana neman ta taimakeshi. wane irin
raini khalifa yake mata, wani irin cin fuska ne
wannan ?
Hawayen idanuwan ummin suka kara ballewa
tashiga kuka kamar ranta zai fita, Dr. khalifa yace
"ummi idan ba za ki iya taimako n ba kitashi ki
ban guri.
Tace "ya ya khalifa ba ka da tausayi kuma baka
san darajar soyayya ba, baka san ciwon so ba, da
ka san zafi da dacin rai dake cikin ciwon so da
baka nufeni da wannan maganar ba, ka san
yadda nake ji a zuciyata kuwa ? tamike tsaye
idanunta tazuba kansa wadanda suka kada jawur
tana huci tace "khalifa na sani ba ka so na, ba
zan yi maka dole kaso ni ba, kuma ba zan taba
bin wata hanya don kaso ni ba,, ni kam ina sonka
son da ba zan taba dainawa ba, abu daya nake
son tabbatar maka wanda shi ne ba zan taba
barwa wata kai ba sai dai kowa yarasa ni kam na
ami ? ce na rasaka....
Amma ba zan hakura ba.
A fusace tabude kofar tafita, yabiyota dasauri
yasha gabanta ya sausauta murya yace "haba
ummi kitsaya ki fuskance ni da kyau mana na yi
miki alkawarin zan miki duk abinda kikeso
matukar na mallaki fatima.
Murmushi tayi masa tace "ka yi kuskure babba
doctor daka fuskance ni da wannan maganar.
Ta zagaye shi tashige cikin gida.
Abba da mama ne kawai a falo suna breakfast,
tashige dakin dasauri dan ba ta son sukalli
idonta.
Ba karamin faduwar gaba fatima tayi ba ganin
ummi ta shigo tana kuka, tamike tariko ta tana
tambayarta lafiya ? me khalifan yayi miki ?
Ta ja hannunta suka zauna tana goge mata
hawaye, ummi tace "ummi babu abinda dr.
khalifa yayi min fyace ya shaida min cewa yana
sonki yana son in taimake shi yasamu auranki.
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN. fatima
kefadi muryarta na rawa tace "bai san an kusan
bikina bane, ke ko ba a kusan biki na ba ina ni
ina shi.
Wani irin abu ummi taji ya tokare mata zuciya,
kirjinta yamata nauyi, kanta ma yashiga sarawa
nan da nan taji jiri ya fara dibarta, tadaure tatashi
tadauki hijjavinta tayi sa'a abba da mama sun
shige daki tafice daga gdan taja mota sai gdan
mahaifiyarta.
Hajiya Hauwa na barci ummi tafada jikinta tana
kuka mai tsanani, a rude hajiyar tatashi tana
tambayar lafiya lafia ?
Wa ye yamutu ?
Tace "hajiya na ga takaina na shiga uku, wai
khalifa ne yau din nan yakirani yana shaida min
cewa ba macen da yake son aura sai fatima.
Yana son in taimake shi yasamu hadin kan
fatima.
Hajiya tace "yawwa abinda nake gayan miki ya
auku ko ? ai lokacin da muke gaya miki gani kike
ba zai taba yiwuwa ba, bayan mu munsan
faruwarsa abu ne mai sauki, idan kika kalli fatima
da tsarinta mace ce da maza ke burin mallakar
irinta, ta yaya khalifa yana ganinta a gdan zai
hadiye maitarsa.
Ummi kuka take tana karawa fargaba da takaici
sun sa ta kasa samun abinda za tace yayin da
hajiya ke ta fadace fadacenta inda take shiga ba
nan take fita ba, takira hajiya saude a waya tace
"kinga abinda muke gudu saida ya auku, taurin
kan yarinyar nan zai ja mana asara.
Bayan saude ta saurari abinda ke faruwa daga
bakin hajiya hauwa tace "kujirani za mu yi
maganinsu dukkansu wannan karon sai mun bude
musu wuta duk tsawon lokacin da muka dauka ya
tashi a banza knan ? wannan abu ne da ba zai
taba yiwuwa ba.
Ba afi minti daya ba hajiya saude tayi dirar
mikiya a gdan tadubi ummi tace "kukan banza da
wofi idan mutum bai aiki da shawarar na gaba
dashi yana tare da nadama, gun malam za mutafi
yanzun ba za mu rangantawa khalifa ba.
Hajiya hauwa ta tabe baki "ba sai in za tayi
abubuwan da aka ce mata ba.
Tace "to kada ma tayin batayi ba ta isa tazo tana
mana kuka anan ?
Har suka isa gdan malam din kuka sosai ummi
takeyi ita takaicin ta ace dr. khalifa yarasa wa
zai so sai aminiyarta fatima, tunda su hajiya suke
gaya mata abin da zai iya fruwa ganin take bazai
taba yiwuwa ba ashe kuskure tayi babba, hajiya
hauwa da hajiya saude ke ta tattaunawarsu kan
matsalar ita kam ta sunkuyar da kanta tana
tunanin yadda za takasance in har fati ta amshi
soyayyar dr. khalifa koda yake abu ne da take
ganin kamar zaiyi wahala sbda koyaushe fatima
na tabbatar mata da cewa bbu abinda zai hana yi
ma iyaynta biyayya, tanayin wannan magana ne
idan wasu daga kawayensu suna cewa"kyaun
halittarta ya fi karfin ta auri malami almajiri irin
malam musbahu wanda ba wayewa a tare dashi,
to anan ne take tabbatar musudacewa "malam
musbahu ya fi kowanni namiji a gunta tunda shi
iyaynta suka zabar mata dole tayi iyayya gasu
sbda yardar Allah take nema a cikin al'amuranta
ba wai kyale kyalen duniya da abinda ke cikinta
ba.
Ummi tana cigaba da gasgata abubuwan da fatin
ke fada ne ganin yadda bata kila kowani irin da
namiji duk matsayinsa, hakan ne yasa ummi ta
tabbatarwa kanta cewa ko dr. Khalifa yadawo ya
ce yana son fati bazata amince da batunsa ba,
sbda akidar biyayyar iyayanta data sawa
zuciyarta to in dai haka ne ma me zaisa in daga
hankali na ? Ta tambayi kanta in dai fatima
bazata amince da dr. Khalifa ba me zaisa ta
tayarwa kanta hankali, to a daidai lokacin da
wannan tunanin ke tasiri a zuciyar ummi har
tafara jin saukin zafin da zuciyarta tadauka sai
kuma dai wani gdfen na zuciyarta yafara tunasar
da ita cewa fa dr. Khalifa kyakyawan namiji ne ga
ilimi ga naira, mata kuwa ba abinda suke so a
gun da namiji wadanda suka wuce kyau da naira
ballantana abin yahadu da ilimi da wayewa,
kadan ne suke la'akari da addini da kyawawan
dabi'u, fatima kam tanada banbanci da sauran
matan zamani, iya zaman ta da ummi ta tabbatar
za ta mata wadannan kyawawan shaidar a ko ina
fatima ba ta da kwadayin abin duniya don da
tanayi da dr. khalifa bai dawo yasa meta, wannan
tunanin duk yake kara kuna a zuciyar ummi
sunada tasiri mai karfi don ta tabbatar da hakan.
Ummi na wannan dogon tunani ne kafin malam
yabasu damar shigowa, hajiya suka shaida masa
abinda ke tafe dasu, yajawo wani rairayi dake
bayansa yafara zane zane yana tambayarsu wasu
abubuwan dasuka shafi dr. khalifa da fatima da
iyayanta.
Malam yajinjina kai yace "hakika khalifa ba
karamin so yakewa fatima ba, kai hasalima bai
taba jin son wata diya mace a ransa
kwatankwacin yadda yake son fatima ba, kuma
ya yi dammarar auranta ko tawani hali.
Wannan bayanin na malam yasa ummi tunani
kamar kirjinta zai tarwatse sbda faduwar gaba,
hajiya hauwa tace "to malam yanxu knan khalifa
ba zai auri ummi ba, kuma kana ganin auransu
da fatima mai yiwuwa ne dukda cewa an kusan
bikinta ?
Malam yace "to ni dai na gaya muku abinda
nagano tar da khalifan ne, batun yiwuwar auransa
da ummi idan kun bi abubuwan dazan tsara muku
anyi an gama, fatima kuwa zan fatattaki
soyayyarta ne daga zuciyarsa, amma gskiyar
magana ba aiki ne mai sauki ba.
Hajiya saude tace "malam indai za asamu nasara
wahala mai sauki ne kuma me wucewa ne me ake
bukata ?
Malam ya gyara zama yace "dafarko kamar
yadda nagaya maku a baya za ku kawo min
kasar da khalifa ya taka, za ku kwao gashin
kansa da hankicinsa da hularsa da hotonsa, za
ku biya kudin fararan raguna guda uku, jajayan
akuya guda uku, jajayan zakaru bakwai, sauran
abubuwan kuma mu za mu samo su, kudin aiki
dubu dari, ku zuba ido za kuga aiki da cikawa.
Suka tsaya akan cewa bayan kwana biyu za
akawo duk abinda aka bukata har kudin, suka
dawo gda da shawarar yadda za asamu kudin
dasuka kama har kusan dubu dari biyu, a karshe
dai Alhaji muhammad mahaifin dr. khlifa aka
buga wa waya suka mai karyar cewa asibiti za su
yace zai aaiko musu da kudin dama sun saba
dahaka duk abinda suka bukata zai musu iya
ikonsa amma ba sa gani, su dai matarsa da
dansa ne ba sa so dashi kansa sai dai dukiyarsa
A DAREN FARKO
20
Fitar ummi yakara dagawa fatima hankali sosai
takifa kanta a cinyarta tana sharar kwalla,
meyasa dr.khalifa zai mata haka, ya ya za ayi
yarasa wadda zai fadawa cewa ma yana sonta
sai ummi wannan ba karamin cin fuska bane da
walakanci, duk abinda zai sa ummi tayi hushi da
ita abin ya yi yawa ko da yake ta san dole ne
ummi tayi fushi da ita akan dr. khalifa, ba wanda
ummi ba za ta iya juyawa ba sbda son datake
masa ba kadan bane, ta gaji da kukan bakin ciki
da takaici tatashi a sanyaye. zata tafi gda taci
karo da mama a harabar gida tana magana da
ado me musu wanki da guga, yanayin ta da
mama tagani yasa tayi saurin matsowa daf da ita
tace " 'yammata lafiya ? kukan me kikayi haka ?
Ba kuka nayi ba wani abu ne yafada min ido.
Tace "ina ummi ?
Tace "ta fita ban san ina taje ba.
Tace "ke ina za ki yanzun ?
Tace "gida za ni yanzun xan dawo.
Kamar zata hanata tafiya sai tayi tunanin bai
dace ba batasan abin da za tayi ba don haka ta
kyaleta tatafi tadawo falo tazauna.
Dr. khalifa yashigo cikin shirin fita yazauna suka
gaisa tace "ba za kaci abincin bane naga ka yi
shirin fita ?
Ya girgiza kai"ba zan iya cin komi ba xuciyata
tana ckin damuwa bansan mafita ba a cikin halin
danake ciki.
Mama tayi murmushi tace "khalifa Allah (SWT)
daya halicce mu cewa yayi "ban halicci mutum da
aljan ba sai don su bauta min, to ni dai a ganina
ba wani abinda zai dagawa mutum hankali akai
in dai ba bautar Allahn nan ba, to ita kanta
bautar Allah ba zafafa mana akai ba, Allah ba ya
daurawa wata rai sai abinda za ta iya, in kuwa
haka ne bbu abinda zai zamo mai tsanani a cikin
wannan rayuwa ko meye shi kuwa, musanman
ida mutum yana la'akari da rayuwar duniya,
wadda fararriya ce kuma kararriya, duk wani abu
dakasani dayake a cikin duniyar nan a dayan biyu
yake, ko dai ka kare kabar shi ko shi yakare
yabarka, to meye dalilin damuwa.
Khalifa yayi ajiyar zuciya yace "mama na san za
ki yi min shaidar hakuri da kau da kai a cikin
al'amarin rayuwa idan yataso min, mama a
wannan karon na samu kaina a yanayin dana
kasa mallakar kaina, don na sa hakurar da
zuciyata tayi hakuri da abinda take nema.
Wallahi ji nake k ; ar zan mutu sbda ciwo fmda
radadin da nakeji a zuciya ta.
Mama tayk mai zumu da ido tana kallon fuskarsa,
tabbas yanayin fuskarsa ta nuna tabbatar da
abinda yake fada haka ne, tausayin sa yakamata
amma tjure don kada ta dada karayar mai da
zuciya tace "khalifa daman akwai abinda ba za a
iya hakura dashi ba a duniyar nan ? a matsayin
mu na musulmi munyi imani da cewa dukkan
abinda yasa me mu haka Allah ya kaddara mana
kuma ba mu da ikon kaucewa abinda Allah
yakaddara mana ,kadaure kayi hakan mana.
Yace "mama ba zan iya hakuri da fatima ba, don
Allah ki taimake ni duk yadda za kiso alheri a
gdan wanda za a ba auran fatima ba kamar a
gdan nan ba.
Mama ta jima kanta a kasa tarasa abinda za
tace, Dr. khalifa yaci gaba da fadin "wlh mama
babu abinda zan iya aiwatar wa a rayuwa ta in
dai ina cikin wannan yanayin ni dai kisha min kan
yarinyar nan da iyayanta ina matukar kaunarta.
Tace "khalifa wace irin son zuciya kake son mu
aiwatar ne ? don Allah kayi hakuri.
Ya tareta dasauri yace "don Allah kada ki ba ni
umurnin yin hakuri ina son fatima dayawa zan iya
kowani irin hali idan ban mallaketa ba, ke za kiyi
hakuri ki taimakeni ba wai ni zanyi hakuri ba
waye zai iya hakuri da abinda yake so mama"
Tace "ahi ke nan kabani kwana biyu zanyi tunani.
Nan take mama tgano dalilin kukan da fatima ke
yi knan, to kuma meye dalilin fitar ummi da safen
nan ba tare da ta sanar dakowa inda za ta ba, ta
kira wayar ummin a kashe takira hajiya hauwa ita
kuma tana ringing ba a daga ba, ta aje wayar a
gefe tayi tagumi tunani ya sha mata kai, shin
yaya za ta yi da wannan al'amari, tana bukatar
shawara, ko dayake duk wata shawara ba ta
wuce ta lallashi khalifa yayi hakuri ba domin
wannan son zuciyar ba yiwuwa zaiyi ba.
Takira sadiya kanwarta dake tayata zama a gdan
a dalilin mutuwar auranta tashaida mata abinda
ke faruwa.
Sadiya tace "tabdijam wannan ai babbar magana
ce.
Tace "to sadiya nima haka nagani, na rasa ta ina
zan gano mafita.
Sadiya tayi murmushi tace "to amm fa mama so
so ne sonkai ya fi, tun kafin khalifa ydawo kasar
nan idan nakalli fatima nakanji sha'awar ina ma
itace khalifan zai aura, hakan yasa ba na so ma
in ji ana hirar auranta me zai hana tunda dai
khalifa ya nuna wannan damuwa ta sa mu san
yadda za muyi ya aureta dama ance matar
mutum kabarinsa wani bai auran matar wani.
mama tagirgiza kai tace "kai anty sadiya anya
wannan maganar ta yi daidai kuwa ?
Sadiya tace "ta yi dai dai mana mama abinda
yasa nace dake haka, idan khalifa bai samu auran
fatima ba ba zai maida kansa kan aure ba
sannan tunda ita yakeso in ya aureta hankalinsa
zai kwanta sosai, yarinya ce mai hankali da
natsuwa, gskiya mama kada muyi wannan
sakacin daga karshe mu zo muna nadama.
Mama takwantar da kanta bisa kujera idonta na
kallon silin, sadiya ma ta zo da maganar daya
cancanta a duba, abin ne da nauyi dole kam tsan
abin yi in banda wannan matsalar ta fi kowa son
khalifa ya auri fatima sbda fatima mace ce tagari
to ya ya za tayi tadubi fati tace tafasa auren
musbahu ta auri khalifa ???
******
Tunda fatima tashiga gdansu bayan gaisuwa
datayi da iyayanta bata kara cewa kowa kmi ba
tashiga dakin innarta takwanta tana ci gaba da
hawaye.
Inna ta tambayeta damuwarta tagaya mata komi
tace "tabdijam abin da malam ke gudu ne yafaru
kin san shi Alhaji baban khalifan ya taba cewa
yana son malam yaba dansa auranki yace ya riga
ya ba da ke.
Fatima tace "to ai inna ko da ba a bayar dani ba
bazan taba amincewa khalifa ba, sbda aduniya
dai banga da namijin da ummi ke so irin sa ba,
ummi ba ta da burin daya wuce mallakarsa, ta
kwallafa rai a kansa tana matukar so da
kaunarsa.
Matsayin ummi gareni ya wuce in yi mata haka,
don Allah inna kada ki saurari maganar khalifa ba
shi da tausayi bai da adalci.
Tace "to ina ma za ayi haka ? dole yahakura.
Fatima tadinga nacin kiran ummi a waya wayar a
kashe take, dole taje ta lallashi ummi, ummi ta fi
komi a gareta.
Bayan sallar azahar tashaidawa inna za ta
gdansu ummi tace sai ta dawo, ko ganin gdansu
dr. khalifa ba ta son yi ,sbda takaicin ya cuceta
ya hadata da babbar aminiyarta abokiyar
shawararta.
Tana tsaye bakin titin kan layinsu tana neman
adaidaita sahu kawai sai ganin mota tayi ta yi
fakin a gabanta, bakaken gilashin da aka zuge
yabata damar ganin wanda ke ckin motar. dr.
khalifa ne gabanta yafadi tsmatsa dasauri tana
masa wani irin kallo, yace "ina za ki ne fatima. "
Tayi shiru kamar ba da ita yake ba, yace "don
Allah kigaya min inda za ki in kaiki.
Anan ne ta hasala tace "ina ruwanka da inda za
ni, ni ba neman taimakon mota nake ba.
Yakashe motar yafito yana kare mata kallo daga
sama har kasa, yana murmushi a wannan lokacin
ne yadada tabbatarwa kansa yana son fatima
kuma ba zai iya sakacin dazai rsata ba insha
Allahu wannan yarinyar matarsa ce ta sunnah.
Kwatsam adaidaita sahu ta tsaya a gabansu,
ummi ce tafito idanunta fes akansu bata ce komi
ba tabiya dan adaidaita kudinsa tawuce za

Please Login or Register in order to submit comment