Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kula da hakkin makotaka
yakai Alhaji sai son barka yana samun yabo a
bakunan mutanan unguwar, su kam alhaji babu
abunda bai yi musu ba ko kusa bai cancanta suki
dansa ba.
Ya daga ki yace "Don Allah alhaji kar kayi
tsammanim hana khalifa fatima nake son yi.
Abba ya katse shi da sauri yace "wallahi ba haka
nake nufi ba, ko a baya damuwar da khalifa ke
ciki tasa idona yarufe na shagala daga baya nayi
nazari na sawa zuciyata hakuri.
Malam yace "Alhaji na gamsu da bayananka na yi
fatan Allah yasa haka shi yafi alheri garesu gaba
daya, na bawa khalifa fatima.
Abba yace "don Allah abba kada kayi hushi da ita
albarkar auran nan ake nema in dai kuna fushi da
fatima wannan albarkar ba samuwa za tayi ba.
Sai a lokacin xuciyar malam ta dan sassauta
daga damuwar da yake fama da ita, bayan tafiyar
Alhaji ya dawowa inna da bayanin abinda abin da
abba yazo mai dashi, inna tace "kai ni dai kam ba
zan fasa fadar cewa wannan abu bai yi min dadi
ba, to idan ma naboye ban bayyana a bakina ba
Allah na gani xuciya b dadi .
Malam yace "ba komi. mu barshi a haka Allah
yakaddara din mu yi fatan alheri ,fushi ba namu
bane. fushin mu ba zai yi maganin matsalar ba
face yakara jagula al'amarin, duk yadda zamuyi
ba za mu ba musbahu fatima ba tunda Allah bai
kaddara matarsa bace.
Tace "to malam yanzu ina musbahun?
Yace "Ni tunda yafita daga asivitin nan ban kara
ganinsa ba, ban san ina yayi ba wayarsa ma
gashi a kashe take tun da muka dawo banganshi
ba nake ta kiranta bata shiga ba.
Inna tayi tsaki tace "Duk fatima ce taja tun farko
in da bata ba khalifa fuskar yaso ta ba zai so ta?
mutumin da ya san an yi masa baiko ina shi ina
kula wani namiji. Fatima ta ban mamaki Allah
malam wannan halayyar arota kawai tayi ba ta ta
bace, ina matukar jin kunyar yaron nan yagama
sawa ransa ba shi da mata sai ita lokaci guda
ace yarasa? haba ai abin da ciwo.
Fatima dai na daga dakinsu tana ji bata ji dadin
abubuwan a ranta amma soyayyar da takewa
khalifa tasa tashare komi in dai za ta samu cikar
burinta akan dr. khalifa xancen ya kare.
Yawan kuka datayi ya haifar mata da zazzabi da
ciwon kai, tasamu babban zani ta kudundune
kanta a ciki tana wasi wasi wayarta tafara ringing
ganin nomban khalifa yasa tadaga dasauri.
Muryarsa a sanyaye yace "Fatima me ki ke yi
yanzu?
Tace "A kwance nake zazzabi ne yarufeni.
Yace "Subhanallahi *in sha magani?
Tace "yanzu dai zan sha.
Yace "zan iya zuwa in ganki?
Tayi shiru, yace "ko akwai matsala?
Tace "Gani nayi ba ka da lfya.
Yace "na ji sauki tunda na sameki dama rasaki da
naga da gaske zanyi ne yaja min ciwo, lokacin
danaga wannan katin na tabbatar na rasaki sai
naji gaba daya duniya ta min kunci, abin cikinta
ma ya min kunci, hankalina ya tashi gaba daya
na kasa mallakar kaina, ,na yi kokarin in daure
damuwa ta ta kai matakin data kai amma da
yake ba ni ne nasa kaina a damuwar ba hakan bai
yiwu ba gareni dole sai da kowa ya fahimci
matsalata da farko na yi zaton mfarki nake ashe
gskia ne don Allah fatima ki nemar mini iso gun
inna da malam su amince in ganki zuciyata ba ta
da juriya a kanki ba zan iya jurewa rashin ganin
ki ba.
Fati ta runtse ido tabude tace "Ba komi kazo
gdan kuma zan fito zaure kaganni.
*****
A gdansu Dr. khalifa xanceb da ake ta nanatawa
knan za a daura auran khalifa da fatima nan da
kwana biyu masu zuwa, reshe ya juye da mujiya
,nan da nan Abba yashiga kiran abokansa da yan
uwa a waya yana shaida musu batun daurin
auran dan lelen dansa biki daisai bayan sati daya
domin ba abu ne na wasa a tare dasu ba, auran
khalifa abin alfahari ne a tare dasu sai kowa
yasan ana yi, mama ce dai bata nuna farin cikinta
sosai sbda ta tsani abinda za ace ta yi son kai
ko son zuciya wanda tabbas ta san sai an
fada,anty sadiya tai ta tsaki a ranta.
Ko yushe tananuna mata cewa aure nufi ne na
Allah babu wanda za ya auri matar wani, Allah
yayi fatima matar dr. khalifa ce dole shi zai auri
matarsa, surutun mutane ba karewa yake ba duk
yadda kaso da taka tsantsan dinka sai an yi
surutun, idan b a yi maka akan wani abin ba sai
an yi a wani abin shiyasa idan mutum yagane to
yasa*i ransa yayi komi kansa tsaye kawai
yahuta, mutum ya fuskanci Allah a cikin
al'amarinsa to karya damu da surutun mutane.
Mama tace "kai sadiya duk fa yadda za ki kare
abin nan ba zan fasa cewa Khalifa yayi son kai
ba.
Tace "to mama shi yace sai an ba shi ta karfin
tiya? muna zaune fa aka ce an bashi to sai ya ki
karba don kada mutane su ce ya yi son kai?
A bisa dole mama tahakura don bata samu goyon
baya ba ta kowanne fannin, dayake harka ce ta
masu kudi duk da kasancewar baa gayawa yan
uwa ba tun auran da wuri ba amma daga lokacin
da aka fara bada sanarwar daurin auran gdan
yafara cika da mutane maza da mata yan taya
murna.
Ummi tana gdansu tun lokacin da dr. khalifa
yafito daga asibiti ta tabbatar za a yi auransa da
fatima ta karasa rikicewa hankalinta a tashe
tajewa hjiyarta da labarin, ta bayyana mata duk
yadda abubuwan suka faru tace "Hajiya mama da
abba babu abunda suke sosai farin cikin dansu,
Abba da kansa yaje ya sanar da mahaifin fatima
halin da dansa ke ciki a kan yarsu, suka taho
asibitin da niyyar dubashi lamarin dayasa musbhu
yace ya barwa khalifa fatima sun manta ina son
khalifa tun kafin yaso fatima, bbu wnda yadamu
da hlin danake ciki ana nan an fara shirye shiryen
auran gadan gadan.
Hajiya tashare mata hawaye tace "Daina kuka
ummi in dai ina raye a gdan duniya nan zanyi
miki maganin damuwarki, ba zan taba cewa
kidaina son khalifa ba don ita zuciya ba a rabata
da abinda take so a zauna lfya, idan har muka
hakura da khalifa to mata muka rako duniya,
wannan dogon lokacin damuka dauka muna
nemansa ba zai tashi a banza ba, tashi mu koma
gun malam.
Ummi tadanyi jim sannan tace "hajiya bai dace
mucigaba da wahalar da kammu a gun zuwa
gdan mlami ba da wahala idan hakan zai amfanar
damu tun da a baya bai mana amfanin kmi ba.
Hajiya tafiddo ido tace "ke saurara nsara a hankli
samunta idan lokacin samuwarta ya zo za kiyi
mamakin aikin malam, ke de muje muji ta
bakinsa, motsi ai yafi labewa, bari in karasa
miyar can yunwa nake ji.
Ummi tace "ni don haushi ma ko yunwa ba ta
damuna. ina mamakin son kan da ake nunawa
kowa akan khalifa amma ta watsar da komi ta
kanta kawai take ko kunyar idona ba ta ji.
Hajiya tace "duk ki kyalesu son zuciya bacinta da
sannu dukka za sugane kurensu.
Ummi ta tashi tashige dakin hajiya ta tsaya a
gaban madubi tana karewa kanta kallo tare da
tuno siffofin fatima a idanuwanta tajinjina kai tare
da ajiyar zuciya tace "ba komi.
Sai bayan sallar isha'i suka isa gdan malam
shima yana mamakin ganinsu a wannan lokacin
ya san ba lfya. suka baje masa bayanin komi.
Unmi ta marairaice tace "Don Allah malam
kataimakeni xan rayu ckin bakin ciki mai tsanani
idan narasa dr. khalifa dole in yi kishin fatima
domin ta san sirrina ta san abinda ke ckin
zuciyata, ko zan hakura dr. khalifa yarayu da
wata diya mace ba dai fatima ba, na amince in
rasa shi amma kada wata ta mallake shi.
Malam yabushe da dariya yaja ra'ayinsu ya fara
zane zane yana bajewa lokaci mai tsawo suna
kallonsa sannan yadago kai ya dubesu yace
"haba ko da naji ai uwar Khalifa ce tashiga
malamai aka tsare mata jikin khalifa don kada
wata macen tasamu damar asirce shi ta rabata
da shi, tunda tasan yammata za su so shi da
yawa ita kanta fatiman don soyayyar da yake
mata ta ra'ayin kansa ce shi yasa duk ayyukan
da muke jifansa dasu ba su tasiri akansa, to
amma ba komi akwai aljanin da zamu hada shi
da shi sai yayi tasiri a kansu shi da fatiman kuna
zaune za kuga ya tsaneta hankalinsa ya dawo
kan ummin, amma sai an sayi sa babba wanda
za a yanka shi a yi aikin a kan sa aiki irin
wannan karfi gareshi sai an yi yanka.
Ganin sun yi jim yasa yaci gaba dayi musu dadin
baki tare da kwadaitar dasu amfanin aikin idan an
yi, yace "wa kukaga ya ji dadi ba tare da ya sha
wahala ba, duk wadannan abubuwan tarihi za su
zama idan Khalifa yazo hannu sai ya baku
tausayi ku dai ku daure.
Suka dawo gida suna tattauna yadda za su nemo
kudin sa, sun yi ammana aikin malam zaici, ummi
tace "Hajiya dole ne in saki jiki wurin gudanar da
al'amarin bikin nan xan nuna kamar bbu wani avu
a zuciyata xa ayi komi dani, amfanin hakan shi ne
dan in samu kudin da za muyi amfani dasu.
Hajiya tace "Lallai kin zo da dabara, idan har kika
nunawa khalifa cewa kina son auran sa da fatima
komi za musamu a jikinsa da abbansa, kin ga
knan mun jefi tsuntsu biyu da dutse daya.
A DAREN FARKO
31
Ana ya gove daurin auren fatima da khalifa
wasikar musbahu ta iske mallam inda yake
shaida masa cewa kada su daga hankalinsu a
dalilin rashin ganinsa ya kauracewa gdan ne don
ya samar da zaman lfya da walwala yayin bikin
fatima, a cikin wasikar yace.
"Malam idan naci gaba da zama kana ganin
damuwata za ku dinga jin zafin fatima yayin da ni
kuma zuciyata ba za ta taba yi min dadi ba in dai
yakasance kuna jin ahushin fatima a sbda ni da
ace da ace zan iya shanye damuwata da zan
dawo amma hakan hakan ba zai yiwu gareni ba,
zuciyata ba ta da wannan karfin. Baba da inna
ina rokon ku yi hakuri don Allah ku dauki wannan
al'amarin a matsayin kaddara kada kuyi fushi da
fatima, fushinku matsala ce babba ga rayuwarta
ina nan ina ta mata fatan alheri, insha Allahu da
zarar an gama bikin an kaita gdanta zan dawo.
Sun ji tausayin al'amarin kwarai da gaske sai dai
ba yadda za suyi al'amarin kaddarar nan dai da
kowa ke fada itace dole ayi hakuri a karbeta,
surutun da ake gudu shi ake tayi a cikin unguwa
da dangi, kwadayi kwadayin abin duniya shi ake
tafada musamman lokacin da sanarwar daurin
auran ta cika gari ta hanyar kafafan yada labarai
dake arewacin kasar nan ba ma nan kano kadai
ba tare da sanarwar za ayi gagarumar wlima
bayan daurin auren da yamma amma na maza
zalla,tuni aka cikawa malam gdansa da nau'ikan
kayan abinci na alfarma wanda za ayi amfani
dasu a gun bikin, hatta nama kala kala aka kawo,
kayan da amarya za tasa lokacin biki mama da
anty sadiya suka tsara mata su gun kwararrun
telolinsu dake tsara musu dinki, kaya ne msu
tsadar gaske haka dinkunan sun sha kudi amma
fa sunyi kyau sun dace da amaryar, kayan lefene
suka ce sai an gama hidimar daurin aure ango da
amaryar za su tafi da kanta za ta xabi irin kayan
da take so da kanta.
Anty sadiya ta hurawa mama wuta akan lallai su
za su gyara amarya tun daga kan fatarta da
abubuwan da ake sha masu kawo ni'ima ga
amarya, mama tarike baki tace "sadiya wannan ai
na su ne na iyayanta da yan uwanta ina dangin
miji ina gyaran amarya.
Sadiya tace "Tabdijam ai kuwa mama anan ne
ma yadace ki yi gyaran da hujja, me yasa kikayi
mata a baya lokacin da za ta auri musbahu, kika
gyara don dan wani ma ballantana na mu, ai ajiye
kunya za muyi mi tattalin farin cikin danmu
zamanin duhun kai ya wuce ina innarta za ta iya
irin wannan abub tana fama da kunya.
Mama tayi dogon tunani taga gaskiyar fa sadiya
barin kashi a ciki bai maganin yunwa, musamman
yadda taga khalifa yana cike da tsananin farin
cikin auran daya samu ko kawaici bai iya yi.
Lokacin da ummi ta iso gdan da safe tashaida
mata cewr tana son tadan yi dabarar da dan ja
hankalin fatima tadawo gdan nan tazauna a yau,
duk abinda aka fada akan fati sai ummi ta ji
tsigar jikinta ya tashi, sai dai bata bari a fahimci
damuwarta ta saki ranta sosai, a wannan lokacin
ma fadada fara'arta tayi tace "Ba damuwa mama
ai ke ce uwar amarya uwar ango mu kuma mune
kirjin biki.
Bayan sun gama cin abinci tanifi gdansu fatiman
ta iske su ita da ango dr. khalifa a soron gdan
suna hira, tarike baki tana murmushi tace "to ai
dai aski ya zo gaban goshi yaya khalifa meye na
mannewa anan?
Ni na dauka ma ka fita.
Ya bata rai yana harararta yace "ke wai ni abokin
wasanki ne xan dauki mataki akanki idan baki
shiga taitayinki ba.
Tace "a'a yi hakuri kamaida wukar ni dai
katayamu murna Allah yasa rakiya tayi nisa.
Suka bushe da dariya gaba daya ita da fatiman
tawuce cikin gida tana fadin "Bari mugaisa da
inna kafin kugama.
Khalifa ya matso kusa da fatima yana dan
rausayar da kai fuskarsa dauke da murmushi
yace "Wallahi fatima har na rasa wacce hanya
zan nuna miki soyayya duk abin da nayi miki don
in tabbatar maki da soyayya sai in ga ya yi kadan
matsayinki ya wuce nan.
Ta kwantar da kanta a jikin bango tana kallonsa,
shadda ce a jikinsa ruwan kwai, iya guiwa rigar
ta tsaya masa ta dan matse me jiki, fuskar nan
fes fes tamkar kullum kyau ake kara masa, bbu
wani da namiji da fatima take tsayawa tamasa
kallon kurilla sai jan gwarzanta Abbubakar saddik,
sbda ahi take kallo taji sanyi a ranta, duk
damuwar datake ciki in dai za taga khalifa sai taji
sanyi a ranta kuma sai taji lallai ta gamsu ta ga
da namiji cikakke wanda in dai ka kalleshi ka san
ka ga da namiji.
Khalifa yaci gaba da fadin "Fatima Allah ne yayi
ke rabona ce shi yasa nadawo gida a dai dai
wanna lkacin, godiya nakewa Allah daya ba ni ke,
domin da na rasaki ban san halin dazan samu
kaina ba fatima.
Wani irin kallo take masa tana dan lumshe ido
tana budewa tare da marairaice fuskarta domin
za tayi kuka, lamarin daya dagawa dr. khalifa
hankali sosai yakasa rike kansa yakara matsowa
daf da jikinta yakai bakinsa kunanta yace "Don
Allah fatima zo mu shiga dakin nan in dan ji
dumin jikinki zuciyata za ta fashe yanzu.
Tayi wal da ido ta waiwaya gaba da baya ba
kowa.
Ko me yasa bata iya musu da dr. Khalifa tana
sane dacewa bukatarsa gareta bata dace ba
amma ba za ta iya kaucewa abin da yake so ba,
sai kawai tabishi suka shiga dakin musbahu
wanda yake zauran gdan, dasauri ya rungumota
sannan yayi ajiyar zuciya mai karfi yayi mata
kiss, ya saketa yace "to zo ki shiga gida.
Mamaki yasa ta tsaya galala tana kallonsa,
yakama dariya yace "ai dama ba wani abu mai
yawa zan miki ba soyayya ce ta yi mini yawa, shi
yasa idan idan ina gabanki bana iya jurewa, ki yi
hakuri daga gobe idan Allah yakaimu na zamo
mijinki za ki ga abubuwa da dama a tare dani,
kada kidamu soyayya ce wadda za takasance
abar alfahari gareki, sai kinyi tsammanin kin fi
kowace mace sa'a a duniya, zan tabbatar miki ina
sonki, zan baki kaina kiyi yadda kika ga dama
dani fatana dai kiji tsoron Allah, kiyi min adalci
kada kiyi amfani da wannan damar ki wahal dani,
kiyi hakuri mu zauna lfya shi ne kadai abinda zai
sa in samu farin ckin rayuwata.
Babu abinda fati ke iya ce masa sai kallo da ido,
abubuwan datake ji game dashi a zuciyarta ya fi
karfin ta iya fda masa da baki sai dai tabarwa
zuciyarta, ita dai ta san tana son dr. khalifa kuma
in dai haka soyayya take hakika masoya suna
fama da wahala, meye wahala? wahalar ciwon so
daban ba kamar kowacce wahala bace, in da
wahalar take shi ne in dai mutum bai ga wannan
masoyin na sa ba to zuciyarsa na cikin fitina da
garari.
Yarike hannunta kam kam yayi mata kiss, sannan
ya saketa ya fice, ita kuma tashiga gida ta iske
ummi da inna suna hira.
A cikin daki ummi tadubi fatima tarike kugu tana
murmushi tace "amarsu ta ango in ji ko dai dr.
khalifa ya fara latsa jikin ki ne.?
Tafiddo ido tace "Ban son sharri ummi.
Itama ta tsareta da na ta idon tace "ke fatima
kada ki mayar dani yarinya karama mana daga
lokacin da soyayya ta tsumu a zuciyar mace
budurwa mai tashen kuruciya irinki har takai
namiji ya fata tabata sai ta sauya.
Duk da kyau da ki ke dashi a baya amma yanzu
kina da bambamci, idan ke baki san yanayin
jikinki ya sauya ba ni na san ya sauya.
Fatima taja doguwar ajiyar zuciya ta zauna gefe
tana kallon immi, takasa magana.
Ummi ta kyalkyale da dariya tana tafa hannuwa
tace "Daman akwai lokacin da za ki iya
soyayya ?
Tadan yi murmushi tace "Anty ummi ai dr.
khalifan ne ya isa a so shi ya hadu.
Ummi taji wani dam a jikinta da zuciyarta kamar
za ta shaki wuyar fatima tace "tashi ki shirya fita
zanyi a yi miki gyaran jiki mun dai makara jibi a
cigaba.
A kofar gdansu dr. khalifa, fatima ta kafe akan ba
za tashiga ba ita kunya take ji, ummi tace "ki
rufa wa kanki asiri idan mama taji kin ki shiga
fushi za tayi dake, idan ma kin sa wa zuciyarki
surukuta da kunyar mama to wahala za ki ba
kanki tunda kin san ita wayayyar mace ce bbu
ruwanta da irin wadannan abubuwan.
A harabar gdan suka ci karo da mama ta yowa
baki rakiya, bata amsa gaisuwar fatima ba sai
harararta datayi tace ke kin dauke kafarki daga
gdan nan wai ke suruka ko ?
Fatima ta sunkuyar da kai tana murmushi, ta
gayar da baki, tawuce ckin gda da sauri jin mama
tana fadama bakinta cewa wannan ce amaryar
khalifa.
Ai kuwa suka fara fadin "kai msha Allahu wannan
yarinya da kyau take ya more mace ga kyau ga
kuruciya.
Daya daga ckin bakin tace "to ai ta fishi morewa
a wannan zamanin samun namiji irin da na
khalifa sai an tona kinga kuwa mu za muyi yanga
va mu za a yiwa yanga ba, tunda duk inda danmu
yake rububinsa ake.
Bayan sun tafi mama tadawo ckin gida ta
samesu a falo tare da anty sadiya ,tace "yawwa
"yammata a zo a dafa ma abba abinci saura yan
mintuna kadan bakinsa su iso.
A ? ty sadia tace "mama munada abubuwa da
yawa da za muyi fa lokaci zai kure mana.
Tace "ai komi za ayi dole a tsaya a yiwa mai
gidana abinci in kuma ba haka ba a fasa fitar.
Ummi tace "tabdijam ai kuwa mama a yadda
muke ji da amaryar nan tamu yau ko tsakar dare
za mukai a gdan mai gyaran jikin nan xa mu kai,
mai kunshin ma daukarta za muyi mutafi da ita.
Mama tace "Lallai abin naku nayi ne sai ku kira
angon a waya yazo yabada kudin kunshin don
kuwa bbu wanda zai biya masa kudin kunshin
matarsa tunda don shi za a yin.
Anty sadiya tace "Eh ko zai bayar kema sai kin
bayar da wani abu mama kudin fa da yawa.
Tace 'Au tausayin khalifa kukeyi ni baku tausayi
na ? duk fa abubuwan nan da ake yi ko sisinsa
bai kashe ba hatta walimar nan da za ayi idan
allah yakaimu goben su dr. hafiz ne suka dauki
nauyi da wani abokinsa da sukayi karatu a jamus,
to ko nawa yabayar gun kunshi ai ba wani abu
ko ?
Ummi takirashi a wya tace "yaya kana ina ne ?
Yace "mun fita dasu dr. bashir.
Tace "To muna bukatar kudin kunshin amarya da
gyaran gashinta.
Yayi wani mur. ushi yace "Da kyau ummi idan har
aka yiwa amaryar nan tawa adon daya birgeni ni
nasan kyautar da zan miki ko nawa ne zan biya a
yi mata in dai zai yi kyau.
A DAREN FARKO
32
Ummi tayi dariya tace "yaya knan in dai batn
kyau ne yau za mukai amaryarka in da za ka
kasa gane ta sbda kyaun da za tayi.
Khalifa ya kyalkyale da dariyan da bata taba jin
ya yi ba yace "kia ina ja fa ummi amaryata fa me
kyau ce shi yasa na zabeta a cikin dubban mata
nace ita kadai zan aura sbda dogon nazari nayi a
kanta tun daga lokacin da idanuwa na suka fara
gani? ta.
Ummi ta cije lebe tare da runtse ido har wani
gumi taji yana tsiyayo mata sbda daci da ciwon
maganganun da khalifa yake yaba mata, ji take
kamar ruwan zafi ake watsa mata a jiki, shi yasa
nan take tajike da gumi, a hankali tace "yaya
khalifa wai don Allah me yasa kazabi fatima ka
fifita ta akan duk wata diya mace, har kabata
matsayi me girma a zuciyarka?
Yace "Ummi na ji dadin wannan tambayar da kika
yimin domin ina son in ji ina fadawa wanda
yashafi fatima matsayin fatiman a zuciyata don
yarinka karfafa mata xuciya tana sanin cewa
dagaske nake.
Ummi tace "to in banda abinka daman yaya
khalifa ai fatima ta san kana sonta ,yanayin
soyayyar dakake nuna mata ne ma yake karfafa
mata zuciya take kara sonka tare da sakin
zuciyarta ta yarda da son da kake mata, in ban
da haka fati za ta iya sanya shakku a zuciyarta
game da kai sbda yanayinka.
Khalifa ya dan tsuke fuska yace "sbda me kika ce
hka ummi? wannan magana ta ki ta ban mamaki
don Allah yi min karin bayani.
Tace "yaya khalifa a yanayin rayuwa irin na
fatima dole taji tsoron sakin jiki dakai idan tana
kallon yadda rayuwarka ke tafiya, kayi mata nisa
nesa ba kusa ba, amma dayake kana nuna mata
soyayya mai karfi ta yarda dakai ta amince akan
kana mata so na gskiya, ina ganin idan haka ne
ba ka da bukatar wanda zai ci gaba da nusar da
fati soyyarka gareta.
Khalifa yace "kuma hakane amma duk da haka
ina bukatar taimakon ku fatima yarinya ce.
Bayan sun yi sallama ummi ta ajiye wayar a gefe
tayi tagumi, wannan soyayyar da dr. khalifa kewa
fatima tana da yawa, fidda fati daga zuciyarsa
abu ne mai wahalar gaske, wace hanya za tabi
knan, ta ina za tasamu khalifa?
Duk kudin da suke kashewa a gun malamai abin
ya ci tura tamkar suna asirin karawa dr. khalifa
soyayyar fatima ne, aiki ne ja a gabanta tun da ta
tabbatar wa ranta ba za ta hakura tasa ido wata
diya macen ta mallaki khalifa ba in dai tana raye.
Tayi kwafa tamike tabi fatima da anty sadiya
inda suke girkin abincin Abba.
Suna ckin shirya tebur khalifa yashigo gdan cikin
sauri tare da dr. Bashir, kai tsaye suka wuce
tebur din wai dama yunwa sukeji, mama ta harare
su tace "ai duk yunwar ku ba za kuci wannan
abincin ba.
Khalifa yaduvi fatima zai yi magana mama tace
"oh za kace mini matarka ce tayi ko?
Yarufe baki yana dariya, fatima dai tabar dakin
dasauri tanufi dakin ummi suka yi sallar azahar
ummi tashigo musu da abinci suka ci a tsatsaye.
Kudin da dr. khalifa yaba ummi na gyaran jikin
amarya sai da suka firgita su sbda yawansu, ta yi
murna sosai domin abin nema ya samu a ranta
tace "ka ba da kudin da za a yaki soyayyar fati a
zuciyarka da sannu za kagane kuskurenka.
Mama ma tadada musu kudin tace su sayo duk
abu! uwan dasuke bukata har na su ma kansu ita
da anty sadiya.
Da yake lamari idan nakudi ne bbu matsala suna
zuwa gdan gyaran jikin aka watsar da kowa a ka
dukufa akan fatima babban guri ne kamar wata
ma'aikata, ayyuka sukeyi kala kala, cikin awa
biyu xuwa na uku fatima ta sauya gaba daya ta
dauki walwali abin ba acewa komi, anayi ana
turara mata jiki da turaren wuta masu kamshi mai
sanyi da shiga rai ga humra ana mulkawa.
Bayan an gama da nan aka zuba mata kamshi
kafa da hannu masu gyaran gashi na tsaye
sunayi fatima tazamo tamkar tauraruwa a cikin
taurari hatta su ummi da sadiya lalacewa sukayi
gun kallon fatima sbda kyau datayi ya wuce
misali, ga wani kamshi mai dadin gaske na tashi
a jikinta, basu dawo gda ba sai karfe sha dayan
dare, tuni angonta yadamu da son ganinta yanata
kiransu a waya suna mishi dariya.
Yana tsaye yana waya dawasu abokansu yan
kaduna yaga shigowar motarsu, yayi saurin katse
wayar yace zai kira yafito.
Kafin ya iso garesu anty sadiya taja hannun
fatima suka shige gida, suka turata toilet wai tayi
wanka ba ta son dr. khalifa ya ganta lokaci guda
yarikice.
Jikin fatima kawai yake bukata, yashiga dakin
mama tana zaune tana hada wata zuma da tsimi
da za taba fatima. Tayi mai wani irin kallo ganin
yanayin daya shigo dashi tace "kai kuwa lfya?
Yace "Mama ina fatima?
Tayi tsaki tace "wai kanka daya kuwa? da tsakar
daren nan kake nemanta me za tayi maka?
Ya dan langabar dakai yashiga in ina yarasa
abinda zai cewa mama, karshe yace "wai da
indomie za tadafa min.
"To da basu dawo da ita nan gdan ba fa?
Wa zai dafa maka? ta watso mai tambayar tana
harararsa tace "to bace min da gani kaje kace
ummi tadafa maka.
Zaiyi magana tace "Allah idan kana matsa mata
xan hanaka ganinta.
Yafice zuwa falo abinda yasawa ransa shi ne ba
zai iya barci ba sai ya rungumi fatima a jikinsa
ko ta halin kaka.
Anty sadiya tafito daga dakin dasu fatin suke za
tashiga dakin mama ganin shi a tsaya yasa tace
"yaya akayi boy?
Ya tsareta da ido fuskarsa ba walwala yace "ina
fatima?
Tace "wanka take.
Bai ce komai ba yasa kai dakin ummin, ta bishi
da kallo tana jinjina kai tashige dakin maman
tazauna kusa da ita tace "in kin gama ki ban in
ba ta tasha ba za tasaki jiki tasha a gabanki ba.
Mama tamika mata a sanyayae tace "kazar "yar
sokoto ta kawo ma yana kitchen idan za ta iya ci
ki hada ki bata wannan fitinannan yaron za a sha
matsala dashi dole sai an gyara fatima, sai dai ni
kam jikina ya yi sanyi wannan soyayyar da khalifa
ke nunawa fatima ta yi yawa, kada fa idan sun je
aun zauna tayi amfani da wannan damar tadinga
juya shi kamar waina.
Anty sadiya tace "don Allah mama kada ki sawa
ranki irin wannan damuwar kowa da lokacinsa
kuma a yanayin fatima ba za tayi haka ba
yarinyar

Please Login or Register in order to submit comment