Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta
tafi, fatima tabita tana fadin "ummi ai gdanku za
ni Allah ne yataimaka bamuyi sabani ba.
Ummi tajuyo suka hada ido ,kallon datake mata
yana dagawa fatima hankali, tawuce dasauri
tabar gun, ta tsaya sororo tabi ummin da kallo.
Dr. khalifa ya iso gabanta yace "fatima don Allah
ki tsaya ki saurareni, zuciyata tana matukar so da
kaunar ki don Allah ki tausaya min.
A fusace tace "ai kai ba abin tausayi bane, babu
wani dalilin dazaisa a tausaya maka, tunda kaima
ba ka tausayin mai sonka, tun yaushe ummi take
fama da ciwon sonka a zuciyarta amma ka ki
kadubeta kake walakanta ta sbda kawai tana
sonka ?
Yazuba mata ido yana murmushi wai shi yarinya
kamar fatima ke wa tsiwa haka, son da yake
mata ya yi tasiri da isarsa ta namiji ba zai yi
komi a kanta ba, a iya rayuwarsa bai taba samun
kansa a yanayi irin wannan ba.
Tayi tafiyarta tabarshi a gun yana binta da kallo,
gumi yana yanko masa har ta bace sannan
yashiga motarsa yaja zuwa gdansu.
Baiyi tunanin nan gdan na su fati za tazo ba sai
yaganta za tashiga yayi murmushi kawai ,tafizge
kanta tashiga ckin gda tayi sa'a mama ta fita
anguwa sai 'yan aikin gdan suna hidimomin su,
ta iske ummi a daki tana hada kayanta .
Ta amsa sallamar fatin ba tare da ta kalleta ba,
fatima tazauna a bakin gado muryarta a kasa
kasa takira sunan ta, ta waiwayo tace,"na'am
fati.
Tace "ummi meye laifina akan wannan al'amarin
lokaci daya za kijuya min baya ki tsane ni ? shin
ni na budi baki nace ina son khalifa ? ko zuwa
nayi sashensa naja ra'ayinsa don yasoni ?
Ummi tayi mata wani lalataccen kallo tace "ke ki
kama kanki, kin san dai ban tare ki dawata
magana ba akan khalifa, don haka ba na bukatar
kiyi ta nemana dawasu maganganu.
Fatima tadaga murya tace "wlh ummi ko kusa
bakiyi min adalci ba, na yi zaton a gun ki zan fara
samu shaidar wani da namiji va zai taba samun
masauki a zuciyata ba, ko ina son khalifa ko babu
maganar musbahu a kaina ba zan taba ba, dr.
khalifa fuska ba sbda na san waye shi a gunki,
ballantana kwanaki suka rage a daura min aure,
hakanan ba na son shi ba na ra'ayin shi to meye
na damuwa, don Allah ummi kada kidauki alhaki
na kada ki watsa mana zumunci ki kwantar da
hankalinki insha Allahu ta hanya ta za ki iya
mallakar dr. khalifa in dai Allah ya kaddara mijinki
ne zan yi amfani da damar dana samu a kansa in
ja ra'ayinsa gareki amma fa sai in na samu hadin
kanki.
Ummi tayi dif tan juya maganganun fatima
wadanda sukan saurin fisgar hankalinta tadawo
natsuwarta, idanunta da zafin kishi yasa suka
rufe suka bude domin ta fara jiyo kamshin nasara
a maganganun fatima.
Ta taso tadawo kusa da fatin tazauna muryarta a
hankali tace "kiyi hakuri fatima a cikin gaba daya
al'amura na ba na wasa da dr. khalifa sbda
soyayyar danake mishi, ban taba jin za a wayi
gari watarana inji ba na san na budi ido in ganki
ba sai ranar da dr. khalifa yabudi baki yace min
"ke ce mace daya dayake so ya aura a duk fadin
duniyar nan, a wannan lokacin ji nayi na tsaneki
fatima duk da na san ba laifinki bane ba ke kika
sa yasoki ba amma wannan baiyi tasirin daya
Hana inga laifinki ba.
Fatima tayi murmushi tace "ke ma ba ki da laifi
ummi domin ba laifi bane don mutum ya yi kishin
abinda yake so, ballantana soyayya irin ta ki ga
dr. khalifa, hnkalina ya tashi don sabon danayi
dake ta ina zuciyata xa tasake kin juya min baya,
ummi inason ganin kin mallaki dr. khalifa don
haka zn daure shi da jijiyoyin jikinsa tunda ya ce
yana sona to ya kawo kansa garemu, kiyi hakuri
da duk abinda za kiga yana nuna mini na so,
kafin mu cimma burimmu, kuma kibashi hadin kai
a duk maganar dazai miki a kaina ki nuna mai kin
goyi bayansa, xai kasance yana son magana dake
sbda hirata da kuke.
Nan take ummi taji zuciyarta ta yi mata wasai,
kaunar fatima takaru a zuciyarta, tafasa hada
kayanta tabar gdan kamar yadda tayi nufin yi,
bayan tafiyar fatima gda takira wayar hajiyarta
tashaida mata yadda sukayi da fatima, hajiya
tace "anya kuwa dagaske take ummi ? kada fa
tayaudare ki, sai wahala ake awai wata manufa a
zuciyarta.
Hajiya tace "to ki dai yi taka tsan tsan kuma
kisan yadda kikayi kika kawo mana abubuwan da
malam yace a kawo wadanda suka shafi khalifan.
******
Cikin dacin rai fatima tadawo gida tana takaicin
son zuciyar dr. khalifa duk da ta san ba zaiyi
nasara a kanta ba amma abin yana ba ta haushi
sosai, ga mamakinta sai ta iske mama da anty
sadiya a gdan na su suna hira da inna ga zogala
a gabansu suna ci.
Ta fadada fara'arta tace "lah mama dama nan
kika shigo.
Tace "eh amma mun biya kasuwa kafin mushigo
nan din.
Inna tatashi tace "bari in tuka tuwon nan in hada
miya in dawo.
Mama ta ji dadin fitar inna tace " 'yammata na
zo ki zauna anan kiji wata magana.
Daf da ita fati tazauna tace "wannan zuwan na ki
ne don gunki muka zo.
Tace "ni mama.
Tace "kwarai kuwa fatima ko baki kai matsayin
daza muzo gunki ba.
Tayi kasa da kanta tana girgiza kai, mama tace
"fatima munzo da kanmu ne nan dan kidauki
abinda mukazo miki dashi da mahimmanci, a
wani lokacin idan za kagawa mutum abu mai
muhimmanci to kadubi yanayin dazaka fada masa
dan yafi kama batun da daraja. fatima na san
matsayin uwa nake a gunki ckin gdan nan na san
bbu abunda xan nema in rasa shi sai fa in ba ku
dashi.
ko da yake maganar danazo miki da ita mai nauyi
ne amma duk da haka nauyinta ba zai hana in
gaya miki ba, sbda na san wacece ni a gunki, ba
kuma ina nufin yin amfani da wannan damar bane
in tursasa ki ba a'a alfarma ce nake fatan kiyi
min.
Fatima dan uwanki khalifa ne ke neman alfarmar
ki amince mai ya aureki sbda ke kadai ce
zuciyarsa ke so, kuma ta aminta ya aura.
Tunda mama tafara magana fatima tasan inda
tadosa, dataji ta yi shiru tace "mama duk abinda
kika fda haka yake, kuma alfarma kowace iri zan
yiwa kowa a gdanku amma a wannan karon sai
dai in ba ki hakuri mama abu guda daya ne zai
hana in amsa wa yaya khalifa soyayyarsa itace
ummi.
Ummi kuma fatima ?
Me ya kawo ummi ckin wannan maganar ?
Fatima tagyara zama tace "mama ummi itace za
tayiwa yaya khalifa shamaki dani domin kuwa ta
fi karfin in auri wanda maitar so da farautar
nema, ummi tana tsananin so da burin auran dr.
khalifa ,da wani ido xan dubeta in na aureshi,in
banda haka da a yau dinnan xan tabbatar miki da
matsayinku a gareni mama ta hanyar amsar
bukatar dr. khalifa, kiyi hakuri mama ki taimaki
rayuwar ummi ki ceto zuciyarta daga halin datake
ciki ta hanyar sa khalifa ya aureta, mama kin zo
gdan nan ne nasan sbda ttausayn sa di kikeji da
gudun fadawarsa wani hali idan bai samu yadda
yake so ba, mama to kisani ummi ta fidr. khalifa
kuncin zuciya don shi a cikin kwanaki kalilan yake
fama da ta shi damuwar yayin da ita tadade tana
fama da damuwa, akwai daran datake kwana
kuka akwai ranakun da ko abinci ba ta iya ci,
,kullum ciwon rai ke damunta akan dr. khalifa, in
dai akwai abin tausayi ta fannin soyayya to ummi
ce, kiyi hakuri mama kituno hadisin manzon
rahama (SAW) da yace imanin dayanku ba ya
cika har sai ya kasance yana sowa dan uwansa
abinda yake sowa kansa.
A DAREN FARKO
21
A cikin uwar dakin mama ita da anty sadiya ne ke
zaune suna fama da magana daya dai dataki
karewa, khalifa yashigo fuskarsa ba walwala
yazauna kan stool yana fuskantar mama yace
"gani"
Tace "khalifa don Allah kayi hakuri da batun
fatima ba za ta amince da batun auranka batunda
dai har nataka kafata har ckin gdansu na roki
alfarmarta bata amince ba, karshe ma tashiga
kawo min wa'azi wai yadda naji tausayinka a
matsayinka na da na har nake fafutukar ganin ka
samu abun da kake bukata to itama ummi in
tausaya mata in taimaketa ta aureka.
Khalifa yaja dogon numfashi yace "wlh mama ni
ma bansan abunda ke damuna ba, na kasa hakuri
da yarinyar nan wani irin abu nake ji a cikin
zuciyata kamar idan ban samu auranta ba
mutuwa zanyi, ina jinjina wannan yanayi danake
cki mama, a ni kaina ba na ra'ayin auran zumunci
ba zan auri ummi ba, fatima kuma yanzu nafara
sonta ki ci gaba da kokarin taimakona da addu'a
da duk abinda za ki iya mama.
Wayarsatafara ringing yatashi yafita, mama taja
tsaki tadubi sadiya tace "to yanzu me za muyi,
nikam ban san abinda za a zarge ni da son
zuciya, ba na son in ja wa kaina zagi.
Sadiya tace "kidaina damuwa mama in fa fati
matar khalifa ce sai ya aureta, dole muci gaba da
jan ra'ayin fatima tunda ita yakeso itace farin
ckinsa.
Bayan dr. khalifa yagama wayar da aka kira shi
dakin ummi yanufa tana zaune tana duba wani
littafi, ta amsa mai sallama cikin fara'a, yazauna
gefen kujerar dake gaban madubi ya amsa
gaisuwar tayi masa yace "ina fatima?
Tana gdansu.
Ya gyada kai "ummi"
Ta amsa "na'am yaya khalifa.
"Ba ki da wata hanya daza ki iya ja min ra'ayin
fatima, ina sonta dayawa fa.
Ba karamin namijin kokari ummi tayi ba gun
shanye damuwarta da tsananin kishi? ta tace
"yaya khalifa tunda dai kana son fatima zan
taim*e ka kasameta, ko ba komi dai na godewa
Allah dayasa kakejin irin abinda masoya keji a
zuciyarsu yayin dasuka rasa masoyansu.
Bata jira abinda zaice ba tamike tace "bari ma
inje in zo maka da fatin.
Ya bita da ido har tafita, ya ji ciwon maganar
data fada masa na karshe amma babu yadda
zaiyi soyayyar fatima ce taja masa, in bar da
haka har ummi ce ta isa tagaya mai magana,
yaja tsaki yayi tagumi.
dr. bashir ne ke dada karfaf masa lallai yanemi
taimakon ummi maganarta na da tasiri sosai a
gu? fatima kada yadamu da abinda zaiji yagani
domin duk abinda kake neman nasara a kansa
sai ka yi hakuri, ba abi? da yatsana irin raini,
Allah yasa ba alhakin 'yammatan daya wahalar
ke bibiyarsa ba.
Yana ckin wannan tunanin fatima da unmi suka
shigo dakin idanunsa akan fatima yaji wani irin
sanyi a ransa kamar yatashi yarungumeta nan
take yakara sallamawa al'amari ummi a gun
fatima, bai dada tabatar da haka ba sai da fatin
tarusuna ta gayar dashi tace "ga ni yaya khalifa.
Ummi tace "yawwa nikam na gama aikina, ke
fatima kinsan dai yaya khalifa yayanmu ne.
Ta gyada kai tace "na gane anty ummi.
Bayan fitar ummi, dr. khalifa yakamo hannun
fatima ya mikar da ita tsaye ya kura mata
kyawawan idanuwansa masu laushi da daukar
hankali, nan take yafara jefa mata wani bakon
al'amari a zuciyarta, nan da nan tayi kasa
dakanta tana jan numfashi dakyar, lamarin
dayasa takasa cigaba da tsayawa ta janye
hannunta ta zauna, yazauna daf da ita yace
"haba fatima dago idonki kidube ni mana, wai
meye aibuna da ba kya son kallona?
Ta maraice murya tace "don Allah yaya khalifa
kaji tausayin ummi ka amsa soyayyarta tana
sonka dayawa, kayi hakurin fiddani daga
zuciyarka, an riga an ba da ni kwanaki kadan
suke rage nazamo matar wani....
Yasa hannu yatoshe mata baki yace "in kina son
in a; hi batunki dago ki kalli kwayan idanuna.
Ba ta son kallon idonsa sbda idon na sa daban
yake dana sauran maza, amma bukatarta datake
son tabiya yasa dole tawatsar da abinda takeji
tawarware idonta ta dubeshi, ya lumshe ido yana
mata kyakyawan murmushi, tamaida kanta kasa
yace "fatima idan fa kina son in yi miki yadda
kike so sai dai kiyi ta kallona har sai na ce
kidaina.
Tun fatima na zamewa kallon na sa har tafara
rikicewa domin wani irin yanayi tafara ji a jikinta
wanda bata taba jinsa ba, yakara matsowa daf da
ita yasa hannayensa biyu yadafa kafadarta, "wlh
ina sonki fatima inajin kihar ckin jijiyoyin jikina
don Allah fati kada kibari kirasa ni kada kibari in
rasaki, fati duk wanda yayi ceton rai...
Yakasa cigaba da maganar sakamakon wasu
siraran hawaye dasuka shiga zubo masa, lamarin
dayasa fati tarude tana fadin "meye abin kuka
khalifa ?
Yace "ke ce bakiga abin kuka ba.
Yasaketa yamike, tamike itama tatsaya a
gabansa takasa magana, sun jima a haka daga
bisani yafice daga dakin yana cigaba da sharar
hawayensa, yawuce mama a falo yafita, gabanta
na faduwa sbda ta ga yanayin daya fito nan take
tsoro ya mamaye zuciyarta.
A cikin dakin fatima sororo a tsaye tana tunanin
khalifa, karo nafarko dataji tausayinsa ya kamata,
ta yaya za tayi da wannan al'amarin, abinda
yatsaya mata a rai shi ne hawayen khalifa da
kyakyawan murmushinsa,dr.khalifa ya zamo
namijin farko dataji lallai tanason taji ta a jikinsa
sbda burgetan da yyi.
Ta kwanta bisa gado tayi luf, a lokacin ne ummi
tashigo dakin da zumudin jin yadda sukai ganin
kwanciyar da fatima tayi da yanayin jikinta yasa
gabanta yafadi sosai.
Ko dai khalifa ya fara wa fati tasiri a zuciya, a
sanyaye tzauna daf da ita muryarta cikin wani
irin yanayi tace "fati yaya akayi naga kin zama
wani iri.
Fati tayi firgigit tamike zaune idnuwanta a waje
tana kallon ummi tace "an samu nasara domin
kuwa ya fara amsa min zai min duk abinda nake
bukata.
Ummi tayi ajiyar zuciya "fatima lallai idan kika
ceci zuciyata daga halin da take ciki kin yi
taimako.
Tadafa kafadarta tace "ba komai kidaina yawan
damuwa.
******
Tsakiyar dare ummi takira jidda dake londn ta
fayyace mata abubuwan dake faruwa, jiddah tace
"Dr. khalifa na son fatim
Tace "kwarai kuwa jiddah soyayya kuma ba gama
garin soyayya ba original one, domin kuwa tunda
yadora idonsa a kanta gaba daya ya rikice ya
rasa sukuni, kin san dai yadda khalifa ba ya sakar
min fuska ko ?
To a halin yanzu sbda in masa kamfen a gun
fatima za kiyi mamakin yadda yake ja na a jiki ko
kunyata ba ya ji.
Jidda tayi ajiyar zuciya tace "anya kuwa umi ko
dai dr. khalifa tsammani yake son wasa kike
masa.
Tace "haba jiddah wani irin wasa kuma, da dai
ace mun saba wasa ni dashi to zaiyi tunanin
haka, mutumin da bai min ko kallon arziki za kiyi
mamakin yadda yasauya akan son fatima abin
har tsoro yake ba ni jiddh.
Ta jinjina kai tace "to yanzu wani mataki kika
dauka akansu ? ko kin hakura dashi ?
In hakura jiddah ?
Tabdijam ai idan kika ga na hakura da khalifa to
numfashin karshe nayi a duniya, ma'ana
rayuwata ta kare amma idan ba haka ba matukar
ina numfashi ba zan hakura da doctor ba.
Jiddah tace "to ummi ta wce hanyar za ki
mallakeshi bayan kin san ko da akewa maza
auran dole a wani lokaci ba za ayiwa dr. khalifa
ba.
Tunda kinfi kowa sanin cewa mahaifinsa yana
fifita shi akan komi yana kara akan komi banda
khalifa.
Ummi tace "eh nima bance za ayi mai auran dole
ba kawai dai ba zan bar ma wata shi ba.
Jiddah tace "ko da fatiman ta ki ta aura ?
Tace "wannan ne abinda yafi daga min hankali
ban so yakasance dr. khalifa fatima yake so ba
sbda kaunar da nakewa fatima ba na son wani
abu na bacin rai ya sameta, in da nake dan
samun natsuwar zucia shi ne fatima ba son dr.
khalifa rtake va, bayan kasancewar saura
kwanaki kadan a daura auranta, fatima tanada
burin biyayya ga iyayanta shi yasa bata kula
kowanne da namiji, wannan yanuna kwanciyar
hankali.
A DAREN FARKO
22
Gaban abban yafadi ras yayi wa dr. khalifa wani
irin kallo yace "ai an kusan bikinta da musbahu.
Yace "na sani abba ai aaure nufi ne na Allah idan
matata ce sai kaga....
Ya katse shi yace "kai khalifa wannan abu ne da
ba xai yiwu ba nima na so auranka da fatima
domin yarinya ce mai hankali da sanin ya
kamata,to amma ta ina xanje in ce a fasa ba
musbahu aure a ba ka, gskiya sai dai kayi hakuri
Allah yabaka wata.
To shima khalifan ya san abun da nauyi soyayyar
dayake mata ne yasa yarufe idonsa yakeso ya
mallaketa kota wani hali, bai ka ra cewa ko ; i ba,
abba ya bishi da ido jikinsa gaba daya yai sanyi
ba ya son dan na sa yanemi wani abu yarasa a
rayuwarsa.
Nan da nan yanayin abba ya sauya ganin
damuwar da ke tare da khalifa, yamike yashiga
dakin mama, tamike dasauri daga kwanciyar da
tayi tace "daman ka fito Alhaji ?
Fuskarsa ba walwala yace "na fito, khalifa ne
yazo min da maganar data dagan hankali.
Mama tace "uhm Allah yasa ba maganar fatima
yakawo maka ba",.
Ya dada bata rai yace "af daman kinsan da
zancen baki fada min ba ?
Mama tace "to Alhaji idan na fada maka me za
kayi !? abinda zai yiwu ahi ake, ta yaya khalifa
zai samu auran fatima idan kuwa ba zai samu ba
meye amfanin tattauna maganar.
Alhaji yazauna gefen gado yana fadin "to haka za
mubarshi a ckin damuwa hajiya ? gaskiya ba zai
yiwu ba.
Mamaki yakama mama ganin yadda abba ke
neman rufe ido kiri kiri yayi son kai, tace "alhaji
gskiya sai dai hakuri domin ni da kaina naroki
yarinyar tanuna min gskiya ba zai yiwu ba,ni
abinda ke hadani da Khalifa shi ne idan yakallafa
ransa kan son abu ba zai iya hakura yabi abin a
hankali ba, sai dai ydga hankalinsa yadaga wa
wani hankali.
Abba yace "ba dole yadaga hankali ba, in bai
gaya mana damuwarsa ba wa zai gayawa, kin
san zafin soyayya kuwa ?
Tace "hakane ban sani basai ka nema mai auran
nasan dai sai da amincewar yarinyar da iyayanta
za ayi ko ?
Abba yace "Gaskiya ba zan bar yaron ckin
damuwa ba, dole in bi duk hanyar dazan bi don
ganin na samar mai dafarin ciki a rayuwarsa.
Yajuya yafita yayin da mama tabishi da kallo cike
da takaicin yadda abba ba ya son nunwa Khalifa
yadda rayuwa take.
****
Fatima ce zaune a runfar innarta ta yi tagumi ta
kasa cin abincin dake gabanta, innar tana dakin
malam, sauran kannanta duk sun tafi makaranta,
musbahu yashigo da sallamarsa, tadaga ido ckin
ladabi ta amsa muryarta a sanyaye tace "ina
kwana.
Idanuwan daya kafa mata yasa tayi kasada kanta
yazauna kusa da ita yace, "fatima a kwana biyun
nan kin sauya kamar ba ki da lfya sai ramewa
kike ko dai fargabar auran ne ?
Ya fada yana dan murmushi a kokarinsa na
kwantar mata da hankali, itama murmushin tayi
tace "lafiya kalau.
Yajawo abincin gabanta yafara ci yana fadin "kai
abincin nan yayi dadi da yawa na san ke kikayi.
Bata ce komi ba, yaci gaba "gaskiya fatima Allah
ya yi miki baiwa da yawa shi yasa zuciyata ke
kara sonki don Allah nima ki soni kuma kidinga
tausaya min wahala zan sha idan nasamu sauyi
daga gareki.
Anan ma shiru tayi masa don bata san abinda za
tace dashi ba, wani iri takeji a jikinta ko kallonsa
ba ta iya yi, yace "ftima don Allah kiyi min
magana ko zanji dadi mana kin san ina sonki.
Fatima bansan abinda zai same ni ba hakanan
nake jin zuciyata tana cik e da fargaba idan
nakwanta bacci kuma sai in ta mafarkai barkatai
marasa dadi wanda yafi daga min hankali shi ne
wanda nayi yau da asuba wai wani ya kwace min
ke ta karfin tsiya, shi ne jikina duk yakara sanyi.
Ga mamakin ta sai taji hawaye ya taru a idonta,
tatashi dasauri tashige daki tace dashi "ina zuwa
.
Misbahu yabita da kallo har yagaji dazama
yatashi bata dawo ba bai san meke faruw aba
baiyi tunanin binta ckin dakin ba yafice daga
gdan.
Itama inna data shigo dakin kallon mamaki tabita
dashi ganin yadda take saharar kwalla tace "lfya
fatima?
Tace "ba komi inna
Ba komi kike kuka?
Takasa magana domin itama batasan dalilin
kukan na ta ba ballantana ta bayyanawa inna,
inna ta jima a tsaye tana kallonta daga bisani
tadaga kai tafita .
Wayar fatima tafara ringing tadauko ta bakuwar
lamba ce, tadaga tare da sallama, daga can
bangaran aka amsa mata "Khalifa ne.
Gabanta yafadi "ko baki fahimci khalifan bane?
"Na fahimta.
"To ai na ji kinyi shiru.
Tace!"bansan abinda zan ce bane.
Yayi dariya "za kisani yanzu kuwa, so nake kizo
mugaisa tun da natashi idanuwa na ke son
ganinki zuciyata na azalzala min da yawa don
Allah kidaure ki zo.
Tace "haba khalifa meye ma'anar zuwana
gareka? me ganin zai haifar maka, me yasa kke
mantawa na kusa zama matar wani ne....
Ya katse ta.
Don Allah kidaina gayamin wannan maganar ki
daure ki zo muyi wa kanmu maslaha.
Shi knan a ina zan sameka?
'Yawwa tawan ina kofar gdanmu ckin mota ta.
Hijabi tasa wanda yazo har kafafunta ydda
idanunta ke kode sunyi ja haka tafita bayan ta
shaidawa innarta cewa za ta gun ummi..
Ta wuce musbahu a kofar gda tare da wani
abokinsa mai suna Aminu, khalifa yana hangota
ya bude mata kofar motar tarike kofar tana kallon
sa tace "idan na shiga mota ina zamu? ko a cikin
motr za muyi magana?
Yace "inaso kiyi min rakiya wani wuri. ne ba nisa.
Ta waiwaya tadubi musbahu ita yakafawa ido, ta
dawo da idon ta kan khalifa tace "kn ganin hakan
y dce?
"Eh ya dace mana kowa ya sanba na satar
mutane, Fatima maslaha muke nemawa kanmu
ina bukata kema haka in haka ne ki shigo mutafi.
Bbu abinda ummi ke kallo sai rayuwar ummi
wannan ce damar da zatayi amfani dan tallafawa
ummi, sai ta zuke fargabarta tshga motar tarufo.
.
Ta gabansu musbahu, kbalifa yawuce idon ta ckin
na musbahu taji gabanta ya fadi an ya ta yi dai
dai kuwa.
Gdan dr. bashir yanufa da fatima, matar dr. bashi
ta asheta hannu biyu zuwa falonta takawo musu
abinci da shayi, dr. khalifa yahada tea yafara sha,
dr bashir ya harare shi "wato haka Za kadinga
son kai ko ita amaryar fa.
Don Allah ku rufa min asiri ina tare da matsaloli
ko yanzun ma na biyo shi ne domin in fahimtar
dashi.
Farida tahada mata shayin taja hannunta zuwa
ckin daki tace "fatima don Allah dagaske ba kya
son Khalifa?
Fatima tawaro ido tace "me son na shi xai
amfana min, a rayuwata bbu abin da na tsana irin
in yi abu in dawo ina nadama.
Farida tace 'dr khalifa yadaga hnkli akan tsananin
sonki, da za ki amsa soyayyarsa xa ki mori
rayuwar aure, irin su tsada garesu.
Fatima tace kin san kyaun mijin daxan aura da
halayansa? an masa adalci in nabarshi na auri
Khalifa? aminiyata na tsananin son khalifa ya
kamata in watsar da batunta in aure shi? abinda
khalifa ke nunawa fa son kai ne kuma ba dabi'ar
musulmin kwarai bane, ya kamata kidnga fadwa
Khalifa wadannan, don ydinga sa hkuri a
zuciyarsa a rayuwa ba komi mutum ke so yake
samu ba.
Farida tarasa abin da xa tace sbda hujjojin fati
sun daure mata jijiyo tamike tadawo falo tace da
Khalifa da wuya fati ta amince yahakura kawai.
Khalifa yace kai ba zai yiwu ba turo min ita, ban
taba neman abu na rasa ba ba xan fara akan
fatima ba, fatima ba ta ckin matan da za a iya
hakuri dasu.
****
Tun daga ganin yanayin fuskarsa ta san ba lfya,
bayan sun gaisa ta tambayeshi "yace "ummi don
Allah ko kin san wani abu tsakanin ummi da
khalifa?
Tace "wani abu kagani?
Yace "kwana biyun nan na fahimci wani abu na
damunta ta ce min ba komi, daxun kuma naga ya
dauketa sun fita a motarsa, na kira wayarta bata
daga ba.
Ummi ta fiddo ido "fatiman? yace itafa abin ne
nima yabani mamaki da yawa shiyasa nakasa
aurewa sai sun dawo nazo inji ta bakinki na san
kin san komi.
Ummi tayi shiru kanta na kasa ".
Lamarin daya dada firgita musbahu gabansa
yashiga faduwa yashiga rokonta da Annabinsa in
ta san wani abun kada taboye masa.....
A DAREN FARKO.
23
Dr. khalifa yaci gaba da cusawa fatima
maganganu a cikin kunnuwanta, suka dinga ratsa
mata zuciya ga hgangar jikinta, lamarin daya sa
ta kuma jin tsigar jiki? ta tana tashi tarabu da
marsh war zuciyarta ,lokacin da dr. Khalifa ya
fahimci ya yi ntasirin jan hankalinta sai ya saketa
ya zaunar da ita gefen gadon yazauna a kasa.
yace "fatima kiyarda in zama mijinki zan shayar
dake zumar soyayya, zan dandana miki wata
rayuwa wadda mafarkin ki bata taba ba ki ba, duk
wani jin dadi da kwanciyar hankali da diya mace
take fatan samu a gdan mijinta zan ba ki shi ba
dan komi ba sai don ina sonki, ni kaina na san
zuciyata tana sonki ba zanyi wasa da duka
abinda yshafe ki ba.
Abinda ke tafiyar da fatima shi ne son kallon
fuskar Khalifa da idanuwanta ke nacin yi, idan
kuma takalle shin sai taji wani irin abu nai mata
yawo a cikin zuciya d jiki, ckin kasalalliyar murya
tace "wai don Allah ya kakeson in yi da
matsallina ? yaya xanyi da musbahu da ummi.
Yaja tsaki yace '"don Alah ki ce kin amince dani
kina sona za ki aureni, musbahu na san yadda
zanyi dashi, unmi kuwakadaki kara min
maganarta tunda nace ba na sonta ban sonta ba
zan auri matar da ba na so ba.
Tace" amma docter ya dace katausaya mata
yadda kake son kaima. a tausaya maka yadda
kake kokawa a bisa soyayyar dakake min tana
wahal ma da zuciya, kowa fa yataimake wani
Allah zai taimaka masa.
Ya dan harare ta yana murmushi.
"To na ji sarkin iya wa'azi.
Takara langabe kai "to baka ce komi ba.
Yace "to wai so kike in hakura dake in auri ummi
,ko kuwa in aure ku tare.
Yana tsaye ne kyam a gabanta, kai wannn bawan
Allah dakyau yake Allah ya yi halitta anan, ta
hadiyi yawu tace"ni dai ina so ka aureta.
Yace "to baki amsa ba in hakura dake ko in
aureku tare ?ki je kiyi tunani ki zo min da amsa
nan da gobe tashi mutafi gida.
A hanyarsu ta komawa gda yatsaya a wani
makeken super market yadinga zabar mata kayan
kwalliya masu tsadar tsiya da burgewa sannan
yajuya kan ciye ciye da na masarufi sai daya
jibgesu a kujerar baya tana kallonsa.
Wannan karon ma musbahu yana zaune shi kadai
a kofar gidansu fatima kan benci, khalifa yayi
parking, sakinbaki yayi yana kallonsu har suka
fito tashige cikin gida dasauri yayin da khalifa
yashiga kwasar kayan da zai iya, yakira wasu
yara suka dinga deban buhunhunan shinkafa da
kwalaye suna shiga dasu, duk wani abu na
kurewar jin dadi a fannin ci da sha khalifa ya siye
shi ba kadan ba.
Inna tana tsaye a tsakar gida tana kallon ikon
Allh ana ta jibge kayn tatmbayi yaran sukace
khalifa ne yace a kawo.
Fatima kam daki tashige, xuwa chan dr. khalifan
yashigo inna takarbe shi da fara'a zuwa rumfarta
"duk dawainiyar da ke damu bata isa ba si anyi
wata.
Yace "don Allah kar ku damu inna ni

Please Login or Register in order to submit comment