Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Abba yace "to fatima mai jiki
dai ga shi nan sai yadda Allah yayi, soyayya ce
mai wahalarwa ya hdu da ita, sai dai hakuri.
Mama dai shiru tayi tazuba tagumi tana ganin
ikon Allah, magana in dai ta khalifa ce abba ba ya
kawaici akanta, yaci gaba da fadin "fatima dubi
halin da khalifan yake ciki har yanzu bai san
wanda yake kansa ba, ni wlhi ban taba ganin inda
akewa mutum irin son da khalifa yake miki ba, ga
shi ba mu da ikon bayar dake gareshi, shin yaya
za muyi da wannan tashin hankalim.
Kukan fatima yafito karara tana juya kanta mama
tace "Alhaji bai kamata kadinga fitowa da fatima
irin wadannan maganganun ba sbda aikin gama
ya gama alkalami ya bushe, hakuri dai khalifa
zaiyi Allah yatashi kafadunsa.
Cikin sanyin murya abba yace "ai nima ba wani
abu nace ba.
Fatima tace "Abba don Allah karoki babna ya
janye mganar aurena da musbahu yana jin
maganarka tare da girmama bukatarka, wlh nima
khalifa nake so.
Mama tarike hannunta tace "fatima mun san kina
son khalifa Allah ne bai kaddara Khalifa mijin ki
bane shiyasa duk abinda yafaru yafaru, wannan
son zuciya ne karara idan har muka nacewa
iyayanki da rokon su bawa khalifa ke,sbda shima
musbahun yana sonki ba ya son yarasaki, idan
mukayi amfani da wata dama da muke da ita
muka rinjayi iyayanki suka ba khalifa auranki
bamuyi amfani da hadisin manzon Allah dayake
cewa imanin dayanmu ba ya cika har sai ya
kasnce mun so wa yan uwammu abinda muke so
wa kanmu, sannan na biyu mutane za su zagemu
don a zahiri munyi rashin adalci mu mun san
iyayanki basu hana mu auranki dan kiyayya ba
sai dan girman alkawarin dasuka wa musbahu.
Fatima takara rikicewa da kuka tana kallon dr.
khalifa take cewa wallahi mama ba na son
musbahu, khalifa nake so, ba ina fadin hakan
bane don a gabanku ne ina son shi ne kawai don
shi ne ra'ayina na amsa wa iyayena auran
musbahu a lokacin da ban san meye so ba, yanu
na fahimci inda rayuwa ta dosa don Allah mama
kutaimaka ku fahimtar da iyayena kada su dauran
auran da ba na so xan iya shiga ko wani hali idan
ban auri khalifa ba.
Aka yi tsit dakin kukan fatima kadai ke tahi,
ummi kallon iyayan khalifa da fati kawai take
tana girgiza kai ta ji dadi da hawayenta basu
zuba ba domin ta gaji da kuka lokacin kuka ya
wuce a gunta illa neman mafita, son kai ba
musbahu kadai ake naman yi mawa ba har ita
gara ma musbahun da yake so ake kwace masa
matr ana ta nanata yadda za ayi dashi ita kuwa
ba wanda yadamu da damuwar ta idan ma
mutuwa za tayi tayi ta mutu, wai fati ce ke kuka
a gaban iyayan khalifa tana rokonsu ita dai tana
son khalifa, takallesu gaba daya tagirgiza kai tare
da cije lebe.
Anty sadiya tace "mama kinga abinda nake gaya
miki wai meye amfanin yin shirun da akayi alhalin
an san halin da zuciyoyin yaran nan ke ciki. ya
kamata ayi musu adalci, shi musbahu bai san
aure nufi ne na Allah ba, a zaunar dashi a yi mas
bayanin kudubi halin da khalifa ke ciki daga ganin
fa katin daurin auranta yashiga wannan halin ina
ga idan an wayi gari yasan an kaita gdan
musbahu?
Tagirgiza kai.
Gaskiya mama a san abin yi kada fa azo ana
nadamar da ba ta da amfani gara tun kafin lokaci
yagama kurewa a yi wani abin.
Abba yace "maganarki haka take sadiya tabbas a
yau din nan zan bi hanyar data rage tarage don
ganin ankawo karshen wannan matsalar wannan
lamarin na khalifa ya fi karfin a sa ido dole a
yiwani abin a kai.
Kofar dakin tabude dr. mansoor yashigo tare da
wata nurse a bayansa ya isa gaban gadon dr.
khalifa yace "har yanzu bai farka ba.
Abba yace "ai ko motsin kirki ba ya yi nifa in
banda ina ganin numfashinsa da yanzu na ce
khalifa ya mutu.
Dr. mansoor yadaga hannun khalifa ya mayar ya
ajiye, yadakko wata karamar na'ura yadaura mai
akan kirji yana latsawa tare dasa wani abu a
kunnansa, zuwa can yacire yajuyo yadube su
gaba daya yakira sunan nurse din da ke tare
dashi mai suna jamila yace "ki lura dashi sosai.
Tace "ba damuwa sir.
Yamaido ido ga abba yace"kuyi hakuri Alhaji
insha Allahu khalifa zai samu lafiya ni yanzu xan
tafi gida.
Abba yace "haba dr.yaya za kace za ka tafi
bayan har yanzu ko farkawa khalifa baiyi ba.
Dr. mansoor yace "Alhaji kada kadarra cewa
samun lfyar khalifa yana hannuna wannan
hukunci ne na Allah,Allah yahore mana taimakon
al'umma ta hanyar ilimi daya azurta mu dashi a
bisa yardarsa muke yin komi ,nan da dan lokaci
kadan likitan daya karbi aiki zai shigo yaci gaba
da kula dashi, Allah shi ne me ba da lafiya, kafin
dai in tafi inaso idan da hali ayi duk kokarin da za
ayi a nemo abinda zai sanya khalifa farin ciki
yayin daya farka ma'ana da zarar ya bude idonsa
yakasance ya ga wani abu dazai faranta masa
rai, wannan zai taimaka gun sanya natsuwa a
zuciyarsa.
Abba ya waiwayo yadubi fatima sannan yamaida
kallonsa ga likitan yace dashi "ka ga wannan
yarinyar?
Dr. mansoor yadubi fatima dake tsugune gefe
tana sharar kwallah abba yace "to itace yarinyar
da khalifa ke so kuma iace silar fadawarsa cikin
wannan halin.
Dr. mansoor yace "Alhaji kana nufin itace fatima.
Dasauri Abba yace "itace kuwa likita ina kasan
sunanta?
Yace "a jiya da kuka kawo khalifa lokacin da
numfashinsa yafara dawowa bayan salatin Annabi
da yayi sunanta muka ji yana ambata tun daga
nan muka kaddara cewa a dalilin mace yafada
ckin wannan damuwar, to tunda ga ta meye abin
tashin hankali ba sai a bashi auran na ta ba kowa
yahuta.
Abba yayi murmushin takaici yana girgiza kai
yace "Likita wannan yarinyar tafi karfin khalifa,
kudi ba sa sayan mutum da ace kudi na sayan
mutum ko nawa fatima takai sai na siyawa
khalifa dan in rabashi da wannan damuwar
dayake fama da ita, saura kwanaki biyu kachal
awa 48 fatima tazama matar wani ban san halin
da khalifa zai shiga ba, Inalillahi wa inna ilaihir
raji'un.
Dr. mansoor ya jinjina kai yace "gaskiyar magana
abba tunda halin da khalifa yashiga ya kai haka
to kanemi iyayan yarinyar nan ku daidaita
magana su zo suga halin da danka yake ciki su
taimaka kowa yataimaki wani Allah zai taimake
shi, kada kabari wani ya auri fatima alhali khalifa
na ckin wannan halin.
Akayi shiru gaba daya har Dr. mansoor yafita bbu
wanda yasake magana.
A DAREN FARKO
29
Karfe daya daidai Abba yace zaije gida yayi
wanka yayi sallah yadawo.
Mama ta biyo shi har mota tana rokon yadaure
yaci abinci.
Ya dubeta da jajayen idon sa yace "cikin nawa ne
bbu dadi tun dazun nake jin zuciyata na tashi
kamar zan yi amai ga kaina na juyawa.
Tace "kayi hakuri ka kwantar da hankalin ka
komai na Allah ne, duk wadannan abubuwan dake
fruwa idan Allah ya yi fatima matar khalifa ce zai
aureta, za kaga yadda Allah zai juya al"'amarinsa
daga damuwa izuwa farin ciki, babu abinda ya
gagari Allah shi ne me yadda yaso a lokacin daya
so, yayin da duk damuwar da za ayi da duk halin
da za a shiga idan Allah bai kaddara matarsa
bace sai dai mutari muyi hakuri muyi fatan
alkhairi.
Abban yadora kansa a kujerar da yake kai idonsa
na kallon sama ,sun samu shiru daga bisani yace
"Hakane sai na dawo. yaja motar ita kuma
tadawo ciki.
Tace "Fatima ku ci abinci kutafi gida ku huta don
Allah ki daina yawaita wannan kukan ba zai yi
mana maganin komi ba sai addu'a da hakuri.
Cikin shashekar kukan tace "ni kam mama a
idanuwa na ba za su taba daina zubar da hawaye
ba sbda tashin hankalin da take ciki.
Mama tace "kiyi hakuri fatima kada ki ja abin da
za ki bata da iyayanki bayan a baya kuna zaune
lfya kullum inna tana yabon halayyarki, iyaye suna
da kima sosai a gun dansu in dai da yana son a
gama da duniya lfya to yabi iyayansa, na
tabbatar ba za su so ace ba ayi auranki da
musbahu ba sbda shi ne xabinsu, hakan ba yana
nufin suna kin khalifa ba, idan muka ce iyayanki
ba sa son khalifa ba muyi musu adalci ba
tundamuna sane da yadda al'amuran suke.
Fatima duk da cewa ni na haifi khalifa na fi kowa
jin ciwon da tashin hankali halin nan dayake ciki,
idan a son raina ne izuwa yanzu yakasance kina
dakin khalifa a matsayin matarsa sbda son da
yake miki kowa ya san bashi dawani farin ciki
wanda yawuce ya mallae ki, yanayi ne wanda
kowa yasan khalifa bai taba samun kansa a ciki
ba, ai wannan dalilin ne yasa kowa yake tabbatar
da son da yake miki na gskiya tun yana fada da
baki har gashi yau a gadon asibiti bai san waye a
kansa ba, to amma duk da haka ba zan rufe ido a
kan abinda ba ma gskiya da adalci ba na hakura
na zubawa sarautar Allah ido idan Allah ya yi
khalifa zai rayi zai tashi, ni dai na san rayuwa
cike take da jarabbawa iri iri, komi lokaci gare shi
duk yadda tsanani ya tsananta insha Allahu
akwai sauki da zai biyo bayansa, a ckin alkur'ani
mai girma ma Allah (SWT) yana fadin, dukkan
tsanani suna tare da sauki.
A wannan lokacin fatima dora kanta tayi bisa
cinyar mama tana kuka har sai da hawayenta
suka jikawa mama zaninta, lamarin dayasa itama
mama takama sharar da kwallah duk kokarin data
dinga yi gun hadiye hawayenta tun safe abin ya
ci tura, wannan karon kuka take sosai, sai anty
sadiya da ummi ke basu hakuri.
Mutmryar khalifa tasa suka mike gaba daya a
rude suna kallonsa, idonsa yabude yana fadin
"Lahaula wala kuwwata illa billahil azim.
Gaba daya suka iso kanaa suna masa sannu.
Bai fahimci a inda yake b kansa a rude yake don
haka yamaida idonsa yarufe, rudewa tasa Fatima
ta manta tana tare da mahaifiyar khalifa takamo
hannun khalifa tana fadin "Don Allah katashi daga
barcin nan ya isa haka.
Kamar a mafarki yake jin muryar fatima, sai yayi
saurin bude idonsa, ai kuwa fatin ce a kansa ya
zuba mata ido har yanzu dai a tunanin sa
rayuwar mafarki yake, yace "Fatima.
Ta amsa "Na'am khalifa.
Ya matse hannunta yace don Allah fatima kada ki
auri wani ba ni ba mutuwa zanyi idan na rasaki,
mafarki nayi wai na ga katin daurin auranki
fatima bai dace ki yi min haka ba ko so ki ke in
mutu? Ni kadai iyayena suka haifa, ko su ya dace
ki tausaya wa.
Fatima tarufe me baki tace "ka kwantar da
hankalin ka insha Allahu za ka mallakeni kasan
nima ina sonka.
Bayan khalifa ya yi sallolin dake kansa yana
zaune kan darduma fatima thada mai ruwan
shayi shi kadai yace zai iya sha gaba daya jikinsa
yayi sanyi kallon kowa yake kadan kadan yake
iya bude idonsa, kowa yazamo dan kallo, fatima
ce ke da bakin magana a gun, shayin ma ita ta
matsa masa tace sai ya sha gudun kada tayi
masa hushi yasa ya hakura zai sha, amma bbu
abunda yake sha'awa.
Kofar dakin tabude, abba da malam musa mahain
fatima da musbahu da inna suka shigo.
Fati tatashi zumbur daga gaban khalifa domin
zaune take sosai a gaban na sa tana rokon ya
daure ya dan ci abinci ko kadan ne, kunya ce
takamata sosai musamman ganin kallon da
iyayanta ke mata duka fuskokin su ba walwala,
ballantana musbahu wanda yake jin kamar ita
kanta fatin ya shaketa kowa yahuta.
Bayan sun gama gaisawa da tambayar jikin
khalifa, musbahu yadubi malam da Abba yace
"Don Allah ku yi hakan baba a kawo karshen
wannan damuwar a yau, har abada hankalina ba
zai taba kwanciya ba idan ya kasance dan uwana
musulmi yana ckin damuwa a dalili na kuma zan
iya taimakawa gun magance masa damuwar.
Musbahu yayi shiru yakasa ci gaba da fadin abin
da yayi niyyar fadin sbda wani irin abu da yaji ya
tokare masa kirjinsa da makwagaronsa haka
bakinsa yayi masa nauyi idanuwa sun yi jawur,
dakin yayi tsit kowa kallon tausayi yakewa
musbahu sbda matsananciyar damuwar data
bayyana a fuskar sa.
Da kyar yaja dogon numfashi yaci gaba da fadin
"Baba na san ina son fatima har ga Allah ina jin
daci da ciwon rabuwa da ita amma ba yadda
zanyi kukan ya zame mini dole sbda in da baki
yakarkata nan yawu ke zuba, in ji masu iya
magana, tun kafin mukawo ga wannan halin na
tabbatar wa zuciyata fatima khalifa take so, na
auna abubuwa dayawa na ga dai hankalinta ya
karkata akai wannan ne yasa na tilasta kaina
nabar masa ita, na barwa khalifa fatima don Allah
baba ku ma kuyi hakuri ku ba shi ita, ku dubi
yanayin dasuke ciki ku kauda tunanin komi mu
kaddara haka Allah yanufa, wannan rana da aka
sa za a daura mana aure da fatima a daura da
khalifa ina fatan Allah yasa haka shi yafi alheri
gare mu gaba daya.
Mama tadaga mai hannu tace "gaskiyar magana
ba za ayi haka ba musbahu, tun yaushe kake son
fatima, tun yaushe aka ma alkawarin an ba ka
ita, amma lokaci daya a rufe ido a yi maka kwace,
wane irin kallo mutane za suyi mana knan?
fassarar da kowa zai mana ita ce ta rashin
adalci, khalifa ne zai yi hakuri da fatima.
Musbahu yayi murmushi tare da girgiza kai yace
"mu wuce wannan gun mama tunda har fatima ta
amince khalifa take so shi yadace a aura mata,
ita diya mace in har ana son a zauna lfya da ita a
bata wanda take so.
Ya kasa ci gaba da maganar sbda wani abu
dayake jin yana tokare masa makoshi, kirjinsa
yana mai nauyi gudun kada suga hawayansa
yatashi yafice daga dakin yanufi hanyar fita daga
asibitin cikin sauri yasamu wata hanya a bayan
asibitin yashiga yazauna a kasa yajingina dawata
katanga yahada kai da guiwa yana ajiyar zuciya,
a lokacin ne yasaki hawayen da yake ta boyewa
yakama kuka mai ciwo da karfi, hannunsa daya
dafe da kansa, kai da ganinsa ka san yana ckin
tashin hnkali mai yawa da damuwa, tabbas yau
ya san ya rasa fatima ya rasa yarinyar daya ke
matukar so so mai yawan gaske, yarinyar da bai
taba hadata da wata diya mace ba ballantana
yakalli wata da sunan so bayan ita ba, hakika ba
ka sanin kana son abu sai sanda karasa shi,
wannan ciwon dayake ji a ransa ya san har ya
mutu ba zai barshi ba, amma wajibi yayi hakuri
fatima ba ta son shi abinda yayi shi yafi masa.
A DAREN FARKO
30
A wannan rana aka sallami dr. khalifa daga asibiti
duk da ba jin sauki yayi ba ko a ganin ido idan ka
dubeshi ka san yana fama da ciwo irin na zuci
wanda fuska ke bayynar da shi, bbu wanda ya
samu bakin tattauna wata magana sai da suka
dawo gida gaba daya.
Jikin fati a sanyaye ta bi iyayanta zuwa gdansu
gaba daya a razane take domin fuskokin iyayanta
sun nuna mata akwai babbar magana wadda ba
za ta taba yi mata dadi ba, ta zauna lakwas a
rumfar inna tana jiran abinda za ace mata
musamman ganin yadda malam musa yazauna
ya lankwashe kafafu yace "fatima ai kamata yayi
tunda kin zabi khalifa sai ki koma gdansu da
zama a yi bikin na ku a can ko?
Inna tace "Ni ma haka na gani malam.
fatim tace "Don Allah baba kuyi hakuri kada kuyi
fushi dani, ba ni nace musbahu yafurta ya hakura
dani ya barwa khalifa ba shi yayi niyyar kansa.
Inna tace "ke da Allah rufewa mutane baki waye
sa'anki a nan da za ki zo mana da wannan
maganar ta bnza da wofi, da ace ba ki nuna
ra'ayin khalifa kike ba musbahun zai fadi haka,
misbahu ya san ciwon kansa kuma yana kishin
kansa dole yace ya hakura domin ba zai zauna a
walakanta shi a banza ba.
Malam yabude baki zai yi magana wani kanin
fatima me suna ibrahim yashigo yashaidawa
malam cewa ga abba can a waje yace yana son
ganinsa.
Tsaki yayi yamike yafito, ya umurçi Abba daya
shigo zaure, ibrahim yadebo kujerun zama na roba
suka zauna suka ka ra gaisawa.
Alhaju mahammadu yace "malam na yi wa khalifa
iyakar nasihar dazan masa Alhamdulillahi kuma
ya fahimceni ya amince da nasihata ya hakura da
fatima, na yi hakane sbda dogon nazarin da nayi
a kan al'amarin don Allah malam kuyi hakuri kada
kuyi fushi da fatima, fushin iyaye ba ya taba
gyara sai illa, a bata goma daya bata gyaru ba,
idan kukayi fushi da fatima al'amarin ne gaba
daya zai lalace ba za asamu mafita ba, idan dai
za muyi hakuri mu klli rayuwar yadda take tafiya
cikin yaran bbu wanda yake da lifi face haka Allah
yakaddara, kowane mutum da Allah ya halicce shi
yarubuta abinda zai faru dashi a rayuwarsa kuma
babu wanda zai kaucewa wannan kaddarar tasa.
Kan malam na kasa nauyin maganar Abba sun
masa nauyi aka har sai da yaji kunya ta kama shi
sosai wato Abba ya fahimci ba sa son ba wa
khalifa auran fatima shi yasa yadanne damuwarsa
duk yadda yake son khalifa ya auri fatima ya
hakura, ko kusa bai cancanta suyi wa Alhaji
muhammadu haka ba duk yadda mutumin kirki
yake mai son mutane da kula da hakkin makotaka
yakai Alhaji sai son barka yana samun yabo a
bakunan mutanan unguwar, su kam alhaji babu
abunda bai yi musu ba ko kusa bai cancanta suki
dansa ba.
Ya daga ki yace "Don Allah alhaji kar kayi
tsammanim hana khalifa fatima nake son yi.
Abba ya katse shi da sauri yace "wallahi ba haka
nake nufi ba, ko a baya damuwar da khalifa ke
ciki tasa idona yarufe na shagala daga baya nayi
nazari na sawa zuciyata hakuri.
Malam yace "Alhaji na gamsu da bayananka na yi
fatan Allah yasa haka shi yafi alheri garesu gaba
daya, na bawa khalifa fatima.
Abba yace "don Allah abba kada kayi hushi da ita
albarkar auran nan ake nema in dai kuna fushi da
fatima wannan albarkar ba samuwa za tayi ba.
Sai a lokacin xuciyar malam ta dan sassauta
daga damuwar da yake fama da ita, bayan tafiyar
Alhaji ya dawowa inna da bayanin abinda abin da
abba yazo mai dashi, inna tace "kai ni dai kam ba
zan fasa fadar cewa wannan abu bai yi min dadi
ba, to idan ma naboye ban bayyana a bakina ba
Allah na gani xuciya b dadi .
Malam yace "ba komi. mu barshi a haka Allah
yakaddara din mu yi fatan alheri ,fushi ba namu
bane. fushin mu ba zai yi maganin matsalar ba
face yakara jagula al'amarin, duk yadda zamuyi
ba za mu ba musbahu fatima ba tunda Allah bai
kaddara matarsa bace.
Tace "to malam yanzu ina musbahun?
Yace "Ni tunda yafita daga asivitin nan ban kara
ganinsa ba, ban san ina yayi ba wayarsa ma
gashi a kashe take tun da muka dawo banganshi
ba nake ta kiranta bata shiga ba.
Inna tayi tsaki tace "Duk fatima ce taja tun farko
in da bata ba khalifa fuskar yaso ta ba zai so ta?
mutumin da ya san an yi masa baiko ina shi ina
kula wani namiji. Fatima ta ban mamaki Allah
malam wannan halayyar arota kawai tayi ba ta ta
bace, ina matukar jin kunyar yaron nan yagama
sawa ransa ba shi da mata sai ita lokaci guda
ace yarasa? haba ai abin da ciwo.
Fatima dai na daga dakinsu tana ji bata ji dadin
abubuwan a ranta amma soyayyar da takewa
khalifa tasa tashare komi in dai za ta samu cikar
burinta akan dr. khalifa xancen ya kare.
Yawan kuka datayi ya haifar mata da zazzabi da
ciwon kai, tasamu babban zani ta kudundune
kanta a ciki tana wasi wasi wayarta tafara ringing
ganin nomban khalifa yasa tadaga dasauri.
Muryarsa a sanyaye yace "Fatima me ki ke yi
yanzu?
Tace "A kwance nake zazzabi ne yarufeni.
Yace "Subhanallahi *in sha magani?
Tace "yanzu dai zan sha.
Yace "zan iya zuwa in ganki?
Tayi shiru, yace "ko akwai matsala?
Tace "Gani nayi ba ka da lfya.
Yace "na ji sauki tunda na sameki dama rasaki da
naga da gaske zanyi ne yaja min ciwo, lokacin
danaga wannan katin na tabbatar na rasaki sai
naji gaba daya duniya ta min kunci, abin cikinta
ma ya min kunci, hankalina ya tashi gaba daya
na kasa mallakar kaina, ,na yi kokarin in daure
damuwa ta ta kai matakin data kai amma da
yake ba ni ne nasa kaina a damuwar ba hakan bai
yiwu ba gareni dole sai da kowa ya fahimci
matsalata da farko na yi zaton mfarki nake ashe
gskia ne don Allah fatima ki nemar mini iso gun
inna da malam su amince in ganki zuciyata ba ta
da juriya a kanki ba zan iya jurewa rashin ganin
ki ba.
Fati ta runtse ido tabude tace "Ba komi kazo
gdan kuma zan fito zaure kaganni.
*****
A gdansu Dr. khalifa xanceb da ake ta nanatawa
knan za a daura auran khalifa da fatima nan da
kwana biyu masu zuwa, reshe ya juye da mujiya
,nan da nan Abba yashiga kiran abokansa da yan
uwa a waya yana shaida musu batun daurin
auran dan lelen dansa biki daisai bayan sati daya
domin ba abu ne na wasa a tare dasu ba, auran
khalifa abin alfahari ne a tare dasu sai kowa
yasan ana yi, mama ce dai bata nuna farin cikinta
sosai sbda ta tsani abinda za ace ta yi son kai
ko son zuciya wanda tabbas ta san sai an
fada,anty sadiya tai ta tsaki a ranta.
Ko yushe tananuna mata cewa aure nufi ne na
Allah babu wanda za ya auri matar wani, Allah
yayi fatima matar dr. khalifa ce dole shi zai auri
matarsa, surutun mutane ba karewa yake ba duk
yadda kaso da taka tsantsan dinka sai an yi
surutun, idan b a yi maka akan wani abin ba sai
an yi a wani abin shiyasa idan mutum yagane to
yasa*i ransa yayi komi kansa tsaye kawai
yahuta, mutum ya fuskanci Allah a cikin
al'amarinsa to karya damu da surutun mutane.
Mama tace "kai sadiya duk fa yadda za ki kare
abin nan ba zan fasa cewa Khalifa yayi son kai
ba.
Tace "to mama shi yace sai an ba shi ta karfin
tiya? muna zaune fa aka ce an bashi to sai ya ki
karba don kada mutane su ce ya yi son kai?
A bisa dole mama tahakura don bata samu goyon
baya ba ta kowanne fannin, dayake harka ce ta
masu kudi duk da kasancewar baa gayawa yan
uwa ba tun auran da wuri ba amma daga lokacin
da aka fara bada sanarwar daurin auran gdan
yafara cika da mutane maza da mata yan taya
murna.
Ummi tana gdansu tun lokacin da dr. khalifa
yafito daga asibiti ta tabbatar za a yi auransa da
fatima ta karasa rikicewa hankalinta a tashe
tajewa hjiyarta da labarin, ta bayyana mata duk
yadda abubuwan suka faru tace "Hajiya mama da
abba babu abunda suke sosai farin cikin dansu,
Abba da kansa yaje ya sanar da mahaifin fatima
halin da dansa ke ciki a kan yarsu, suka taho
asibitin da niyyar dubashi lamarin dayasa musbhu
yace ya barwa khalifa fatima sun manta ina son
khalifa tun kafin yaso fatima, bbu wnda yadamu
da hlin danake ciki ana nan an fara shirye shiryen
auran gadan gadan.
Hajiya tashare mata hawaye tace "Daina kuka
ummi in dai ina raye a gdan duniya nan zanyi
miki maganin damuwarki, ba zan taba cewa
kidaina son khalifa ba don ita zuciya ba a rabata
da abinda take so a zauna lfya, idan har muka
hakura da khalifa to mata muka rako duniya,
wannan dogon lokacin damuka dauka muna
nemansa ba zai tashi a banza ba, tashi mu koma
gun malam.
Ummi tadanyi jim sannan tace "hajiya bai dace
mucigaba da wahalar da kammu a gun zuwa
gdan mlami ba da wahala idan hakan zai amfanar
damu tun da a baya bai mana amfanin kmi ba.
Hajiya tafiddo ido tace "ke saurara nsara a hankli
samunta idan lokacin samuwarta ya zo za kiyi
mamakin aikin malam, ke de muje muji ta
bakinsa, motsi ai yafi labewa, bari in karasa
miyar can yunwa nake ji.A DAREN FARKO
30
A wannan rana aka sallami dr. khalifa daga asibiti
duk da ba jin sauki yayi ba ko a ganin ido idan ka
dubeshi ka san yana fama da ciwo irin na zuci
wanda fuska ke bayynar da shi, bbu wanda ya
samu bakin tattauna wata magana sai da suka
dawo gida gaba daya.
Jikin fati a sanyaye ta bi iyayanta zuwa gdansu
gaba daya a razane take domin fuskokin iyayanta
sun nuna mata akwai babbar magana wadda ba
za ta taba yi mata dadi ba, ta zauna lakwas a
rumfar inna tana jiran abinda za ace mata
musamman ganin yadda malam musa yazauna
ya lankwashe kafafu yace "fatima ai kamata yayi
tunda kin zabi khalifa sai ki koma gdansu da
zama a yi bikin na ku a can ko?
Inna tace "Ni ma haka na gani malam.
fatim tace "Don Allah baba kuyi hakuri kada kuyi
fushi dani, ba ni nace musbahu yafurta ya hakura
dani ya barwa khalifa ba shi yayi niyyar kansa.
Inna tace "ke da Allah rufewa mutane baki waye
sa'anki a nan da za ki zo mana da wannan
maganar ta bnza da wofi, da ace ba ki nuna
ra'ayin khalifa kike ba musbahun zai fadi haka,
misbahu ya san ciwon kansa kuma yana kishin
kansa dole yace ya hakura domin ba zai zauna a
walakanta shi a banza ba.
Malam yabude baki zai yi magana wani kanin
fatima me suna ibrahim yashigo yashaidawa
malam cewa ga abba can a waje yace yana son
ganinsa.
Tsaki yayi yamike yafito, ya umurçi Abba daya
shigo zaure, ibrahim yadebo kujerun zama na roba
suka zauna suka ka ra gaisawa.
Alhaju mahammadu yace "malam na yi wa khalifa
iyakar nasihar dazan masa Alhamdulillahi kuma
ya fahimceni ya amince da nasihata ya hakura da
fatima, na yi hakane sbda dogon nazarin da nayi
a kan al'amarin don Allah malam kuyi hakuri kada
kuyi fushi da fatima, fushin iyaye ba ya taba
gyara sai illa, a bata goma daya bata gyaru ba,
idan kukayi fushi da fatima al'amarin ne gaba
daya zai lalace ba za asamu mafita ba, idan dai
za muyi hakuri mu klli rayuwar yadda take tafiya
cikin yaran bbu wanda yake da lifi face haka Allah
yakaddara, kowane mutum da Allah ya halicce shi
yarubuta abinda zai faru dashi a rayuwarsa kuma
babu wanda zai kaucewa wannan kaddarar tasa.
Kan malam na kasa nauyin maganar Abba sun
masa nauyi aka har sai da yaji kunya ta kama shi
sosai wato Abba ya fahimci ba sa son ba wa
khalifa auran fatima shi yasa yadanne damuwarsa
duk yadda yake son khalifa ya auri fatima ya
hakura, ko kusa bai cancanta suyi wa Alhaji
muhammadu haka ba duk yadda mutumin kirki
yake mai son mutane da

Please Login or Register in order to submit comment