Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace "Abbakar ina matukar bakin
cikin hanaka auran fatima amma kayi hakuri Allah
ne bai sa matar ka bace, akwai abubuwa da
dama da Allah kan jarrabi bawansa don yagwada
imaninsa, idan yajure yayi hakuri sai Allah
yamusanya mai da abinda yafi wannan alheri
sakamakon hakurin da yayi da abinda Allah
yajarrabe shi dashi.
Duk kokarin da dr. khalifa yayi na mayar da
hawayen da suka taru a idonsa don kada malam
ya gani abin yaci tura, domin sai da yadinga
sharar kwalla yana jan numfashi da kyar, daga
karshe kasa ci gaba da tsayuwa yayi sai
durkusawa yayi, hankalin malam yatashi sosai
tun yana iya magana har yayi shiru ya zurawa
khalifa ido, yaji tausayinsa a wannan lokaci
,tausayi mai tsanani, zuwa can khalifa yatashi
yatafi gida ba tareda yakara cewa da malam komi
ba.
Malam ya jima yna kallonsa sannan yashige ckin
gida ya iske inna itama na ta jikin a sanyaye,
yazauna yace "kai yaron nan dagaske yana son
fatima.
"Itama tana sonsa malam ".
Inna tafadi tana kallonsa.
Yace "wane irin tana sonsa kuma da maganar
musbahun a kanta take son wani.
Tace "wallahi kuwa fatima ta yi abinda ban taba
zato ba a yanayin rayuwarta, tadubi idona tace a
yanzu ita khalifa take so tana son mu fasa ba
musbahu auranta mu bata shi in bar da tana son
sa za tayi haka? tunda tagaya min wannan
maganar jikina ke rawa hankali na yatashi sosai,
ni dai yin wannan rana na yi shi ne kawai amma
zuciyata tana cike da sarkakiya da damuwa, sbda
fatima ta ban mamaki ta ba ni tsoro, duk abinda
fatima za ta budi baki tayi magana akansa ba
karami bane, tana da kunya sosai da zurfin ciki,
tunda harta iya magana to da gaske tana son
khalifa, yawan kukan datakeyi shi yake dada
dagan hankali har na rasa yadda zan bullowa
lamarin.
Malam yace "amma wannan zancen banza ne, ni
za ta mayar karamin mutum, sa rai da ci shi ke
kawo jin yunwa in barda ta sa soyayyar ta sa ai
ba za ta daga hankalinta akan shi ba, tun yaushe
aka sa wa musbahu rai da batun auran ta, ya
saki jiki itace matarsa kawai sai ta dawo tace ga
wanda take so, a gun nan nafada mata idan ba ta
son musbahu ba zan mata dole ba tace ta ami?
ce, yanzu ya kike zaton mutane za su daukeni
idan nafasa ba musbahu naba khalifa, kwadayi?
Babu ta inda zan fidda kaina a gun musbahu da
yan'uwansa dasauran jama'an gari na sayowa
kaina zagi.
Inna tace "wallahi malam ni ma ban goya mata
baya ba don na san son zuciya ne karara tazo
dashi.
Haushi yakara kama malam ya kwalawa fatima
kira, tafito tana rabe rabe ta tsuguna ybuga mata
harara yace "na fahimci cewa ke ce kika ba
khalifa fuskar yazo gdan nan yazo min da batun
auranki alhalin kina sane da musbahu, kin ba ni
mamaki fatima ban taba shakku akan lamarinki
ba sbda biyayyar ki garemu kada ki bamu kunya
kada kija abinda zai ja mana damuwa alhali
muna zamanmu lafiya.
Fatima tayi doguwar ajiyar zuciya tace "kuyi
hakuri baba ni ma banyi tsammanin zan wayi gari
ckin wannanyanayi ba, ni kam ina son khalifa don
Allah ku ba musbahu hakuri....
"Salamu Alaikum
Muryar musbahu knan, suka daga kai a razane
suka zuba mai ido fuskarsa a cunku she yazauna
jagwab kusa da malam muryarsa na rawa yace
"Baba hakika na ji duk tattaunawar ku da fatima
kuma na ji matsayina a gunku, ba ni da abi? da
zan ce muku sai godiya, kyautatawar dakuka mini
Allah ne zai biyaku domin don shi kukayi.
Baba na san ina son fatima soyayyar da tasa
nake jin cewa idan na rasata zai wahala in yi
aure domin bansan ta yadda za ai in so wata
mace ba bayan ita, ko da yike komi na Allah ne
amma wannan soyayyar danake mata ba za tasa
in aureta alhali na san ba ta so na ba, kayi hakuri
baba kaba fatima khalifa...
Cikin zafin rai malam musa yace "yi min shiru
musbahu, wannan yarinyar bata isa tasauya min
ra'ayi ba, tunda tun farko da amincewarta aka sa
bikin auran nan kadarra cewa ma ka auri fatima
ka gama.
Ranar da aka sanya za a daura wannan auran ba
fashi, insha Allahu za a daura in dai ka ga ba a
daura ba sai dai in ranar ce tariskeni ba na
numfashi, za a daura auranku kuma za a kaita
gdanka, a ranar tahadiya zuciya tamutu a kawo
min gawarta.
Musbahu yabude baki zaiyi magana malam yayi
mai tsawa yace "in dai kaima ba so kake kabata
min rai ba kayi min shiru, idan Allah yakaimu
gobe kaje ka amso katunan daurin auran a kaiwa
kowa.
Yatashi yafice ,musbahu ma yabi bayansa, itama
innar tashige daki tabar fatima tana kuka.
Tunda take bata taba batawa iyayanta rai ba
ballantana suyi fushi da ita sai yau, shin me ya
shiga zuciyarta ne tasauya haka, a duk lokacin da
ake magana, soyayyar khalifa ce take karuwa a
zuciyarta, kamar ana hura mata wuta, idanuwanta
suka kada jawur tarasa yadda za tayi da ranta.
Soyayyar dr. khalifa ta gama rufe mata zuciya ji
take kamar ba xa ta iya rayuwa ba in ba shi,
gabaki daya ta watsar da batun ummi ta kanta
kawai take, tana ji a ranta in dai ta auri khalifa
duk abinda zai biyo baya me suki ne, iyaka dai
ummi tadaina kulata ita in dai tana tare da khalifa
bukatar zuciyarta ta biya, matsalarta yanzu
iyayanta wadanda sun dau zafi dayawa.
Ta daga kai ta amsa sallamar musbahu, haushi
yakara kamata tabishi da ido har yatsuguna
gabanta yace "fatima.
Bata amsa ba sai kallo yace "kiyi hakuri.
Ta mike tashige ckin daki a zuciyarta tana fadin
ai kai hakuri yakama ba ni ba.
Musbahu yayi zaman dirshan a gun yazuba
tagumi da hannu bibbiyu shin wani irin iftila'i ne
yasa me shi haka?da can bai rasa fatima ba sai
da yagama sakin jiki bai da mata sai ita, yakasa
juriya yabita dakin na su, ya isketa a kwance tana
kuka.
Yace "fatima baki min adalci ba don Allah ki
kwatanta idan ni nayi miki haka za ki so? a ce a
irin wannan lokaci in ce na fasa auranki wata zan
aura?
Ya tsuguna a gabanta kamar mai neman gafara
yace "don Allah fatima ki taimake ni wlh ba
karamin so nake miki ba, ni ban isa in ce
kwadayin duniya ne yasa kike son khalifa ba idan
akwai kwadayi ba za ki tsaya akaina ba, masu
kudi dayawa sunce suna sonki baki ba su hadin
kai ba.
Fatima batayi niyyar yi ma musbahu magana ba
dan ita kanta ta san ba ta da abinda za tace
musa, amma a bisa wannan maganar tasa da taji
ya dace tace wani abu a kokarinta na samin
mafita.
Tace "Nagodewa Allah dayasa da kanka kayi min
shaidar ba kwadayi yasa nace ina son khalifa ba,
ka san cewa soyayya ce don Allah, ina son kayi
hakuri kayi min adalici, soyayya Allah ne me
sanyata a zuciya ba mutum ba.
Ya katseta zuciyarsa cike da daci yace "fatima ki
fito a gaban ido na kawai ki ce ba kya so na,
khalifa kikeso, na gode fatima nagode.
Yamike dasauri yafice yana goge hawaye.
Fati tace "innalillahi wa inna ilaihir raji'un.
A DAREN FARKO
27
izuwa wannan lokaci ummi ta tabbatar fatima ta
daina yi mata aikin komai ita takewa kanta, ta
fahimci soyayya suke shimfidawa da dr. khalifa ta
gaske duk da cewa rigima ake tafkawa a gdansu,
ga katunan daurin auren yau an fito dasu har an
kawo na Abba gdan, a kalla kwana uku kachal a
daura auran musbahu da fatima, har takaici da
kishi ya yiwa ummi yawa, yaudara ita take
fassara fatima ta yi mata tunda gashi ta fita
hanyarta tunda gashi ta fita hanyarta gaba daya
ko neman ta ba ta yi lallai mutum abin tsoro ne.
Ta iso gdansu da katin daurin auran ta nunawa
hajiyarta tace "to ai zance ma ya kare in dai aka
mata aure aka kaita dakin mijinta ai dole khalifa
ya hakura da ita duk maitarsa .
Unmi tace "kayya dai hajiya khalifa yana son
fatima in kinga abin da yake nunawa za kiyi
mamaki.
Tace "duk ihu yakeyi bayan hari shi zai bawa
kansa auran na ta? ki kwantar da hankalinki
malam yana nan yana buga mana aiki da kafarsa
khalifa zai zo gdan nan.
Ita dai ummi hnkalin ta ya ki kwanciya son da
khalifa ke nunawa dmfatima kadai ya isheta
takaici, ita ko kallon ta ba ya yi tamkar ba aiki
ake yi a kansa ba.
*****
Ummi ce take sha'aninta khalifa bai san an fara
rabon katin auran fatima ba sai da yamma daya
dawo daga asibitin su dr. hafiz ya iske katin a
hannun abbansa, yana gama karantawa yazube a
gun.
Abba yatashi a firgice yana jijjiga shi tare da kiran
sunan sa da karfi ina khalifa ko motsi baiyi ba
numfashinsa yatsaya cak, abba yafita dagudu
yakira mai gadi yace yazo sudauki khalifa ba lfya,
mama da anty sdiya ma suka fito daga daki
ganin yanayin khalifa yatashi hankalin kowa sun
shiga dimauta, suka nufi wani asibiti mai zaman
kansa har suka isa khalifa ko motsi abba salati
yake yana fadin "shike nan Khalifa ya mutu akan
son ftima na ga takaina.
Likitoci suka amshe shi ckin gaggawa suka kaishi
wani daki suka fara ba shi taimakon gaggawa,
dakyar suka lallashi abba y tsaya a waje dan
cewa yayi sai ya shiga dakin, gani yake kamar
khalifa ya mutu, mama datake mace ma ta fi
abba karfin hali, itatadinga ba shi baki tana nuna
masa cewa ba mutuwa khalifa yayi ba, yadinga
kai komo a kofar dakin ba likitan daya fito, yagaji
yashiga buga kofar yana fadin "ku fito min da
gawar khalifa na san ya mutu.
Wani bakin likita dogo siriri yafito yaja hannunsa
suka shiga dakin yaba shi kujera yazauna daf d
gadon da aka kwantar da dr. khalifa yace "Alhaji
duba kagani yana numfashi ko?
Anan ne abba yayi doguwar ajiyar zuciya, ashafi
fuskar khalifa zuwa wuyansa yaji sanyi kalau,
numfashinsa yadawo normal amma lokaci daya
yarame fuskarsa takara haske.
Likitannan mesuna dr. mansur yadan rusuna kusa
da abba yace"ka gamsu bai mutu ba ko?
Yace "hakane amma nikam likita jikina na ba ni
mutuwa zaiyi, khalifa ba zai yi dogon kwana ba a
duniya...
Dr. mansur yarufe me baki yace "haba alhaji ya
za kadinga wadannan maganganun a matsayinka
na musulmi? mutuwa daban ciwo daban, kayi
hakuri mun sha kan matsalar khalifa dimuwa ce
kawai takai shi ga shiga wannan halin in dai ku?
yi kokarin magance masa damuwarsa shi knan
komi zai tafi yadda yakamata.
Su mama ma an ba su damar shigowa ita da anti
sadia, gaba daya suka zubawa khalifa ido cike da
damuwa jikinsu ya gama sanyi da al'amarin .
Abba yagirgiza kai yace "hajiya wani irin tsari ne
haka, shi knan akan mace mutum yadaga
hankalinsa kamar zai bar duniya,ni wallahi har na
rasa yadda zan bullowa al'amarin na khalifa
tunda ga wanda iyayanta suka yiwa kawari na yi
na yi yayi hakuri ya ki fahimta,ban taba ganin
abinda khalifa ydga hankalinsa akan sa ba sai
akan fatima, wacce irin soyayya ce wannan, daga
ganin katin daurin aure.
Mama tagirgiza kai tace "wallahi abba nima
tunda khalifa yafara maganar yana son fatima
hankalina a tashe yake, sbda yanayin daya ke
nunawa abin fargaba ne, in an yi magana yace
wai a kyale shi b a san abinda yake ji bane, to
rayuwa za tatafi a haka, wani abun idan mutum
yana so yana samu wani abun kuwa duk
maitarsa da kaunarsa da abin ba zai same shi ba
sai hakuri.
To shi khalifa ji yake kamar ba zai ci gaba da
rayuwa ba idan bai mallaki yarinyar nan ba,.
Suka yi shiru kowanne idonsa kan khalifa, daga
bisani abba yaja numfashi yace "wai yaya za mu
bullwa lamarin nan ne?
Mama tace "to yaya za muyi kuwa abba in barda
muyi hakuri dole fa khalifa yahakura da fatima.
Abba yace "kai hajiya a irin wannan yanayin, dubi
fa yadda yake.
Tace "to idan bamuyi hakurin ba ta karfin tsiya
za mu ba shi fatima?
*****
Ga dai lokacin biki ya zo gadan gadan amma
gdansu fatima yanayin babu dadi domin kuwa
ango da amaryar suna cikin damuwar dataja jikin
kowa ya yisanyi babu mai walwala,Fatima ce
zaune kan kujerar zaman tsakar gida da wayarta
ta hannu ta kurawa sakon daya shigo wayarta ido
zuciyarta na azalzala sako ne daga khalifa yace.
Fatima soyayyarki xa ta hallakani bbu wani
taimako daza kimin don Allah kiji tausayi na kada
ki bari iyayanki su bawa musbahu ke wallahi na fi
son ki fatima.
Tagoge hawayen dasuka gangaro mata tayi ta
maimaita sakon tana girgiza kai, ta tashi tashiga
dakinsu tacimma katunan gayyata na biki da
musbahu yakawo mata da la'asar din dazu, ganin
idon katunan sun tsaru sun yi kyau amma ita
bakin ciki ne yakara turnuke mata zuciya data
gansu, ganin katunan yakara kusanto mata
lokacin bikinta knan kuma lokacin rabuwarta da
masoyinta dr. khalifa, kuma idan tayi wasa
wankin hula na daf da kai mata dare.
Shi kansa musbahun lokacin daya kawo mata
katin sai da yabata tausayi, tana sallah yashigo
yatsuguna bakin kofa kamar me neman gafara,
data idar bata kalleshi ba tajawo pillow ta
kwanta, a sanyaye yace "fatima ga katinan
gayyatar.
Tadube shi wani iri tace "to ajiye anan.
Ya matso daf da ita ya ajiye, uace "ko kina
bukatar wani abu daya danganci bikin?
Ta ki magana sai da yayi ta mata naci sannan
tace "Ni fa ba abinda nake bukata.
Yace "shi knan sai anjima.
Yamike yafita yayin da tabi bayansa da ido cike
da takaici.
Gabadaya dr. khalifa ya sauya mata yanayin
rayuwarta, kafin dawowarsa tana zaune lafiya ba
ta damuwa da komi babu abinda yake tayar mata
da hankali sai daya dawo.
Tun randa dr. khalifa yafara cewa yana snta bata
kara samun kwanciyar hankali ba, gabadaya ya
jefata a ckin damuwa da rudani kullum tunani, ta
zamo abar tausayi akan kanta domin yanayin da
zuciyarta ke ciki ba dadi, ba ta jin dain halin data
sanya musbahu sbda babu abinda yayi mata, ya
rayu yana tattalin abin da take so tun tana yar
karama yake tattalin rayuwarta har maganar aure
ta bullo a tsakaninsu, ya dauki son duniya ya
daura mata kullum kamar zai lashe ta, ba ya son
abinda zai daga mata hankali, kowa ya shaidi
musbahu da kyawawan dabi'u ababan so ga
kowacce mce, dari bisa dari ta amince da batun
auransa, shi yasa bata tava kallon wani da namiji
da sunan so ba, sbda ita dai yardar Allah kawai
take nema a rayuwarta, bata taba damuwa da
kyale kyalen duniya ba, bbu kwadayi ko son
zuciya tsarinta, shi yasa tafiyarsu da musbahu
yaxo daya svda shima akan wannan tsarin na ta
yake tafiya. kowa yana kyautata zaton za su
zauna lfya a dalilin kowannen su ya dauki rayuwa
dasauki, iyayanta suna cike da murnar auran ba
su da fargabar komi, sai da abin yazo daf dr.
khalifa ya bayyana cikin rayuwarta shi knan
zuciyarta tasauya.
*****
A DAREN FARKO
28
Tana cike da jin nauyin musbahu, soyayyar dr.
Khalifa ce take da karfi a zuciyarta shi yasa
takasa tuna komi.
A bangare guda da ummi, ummi ta taka
muhimmiyar rawa a kanta ta hanyar nuna mata
kauna da aminci na gaskiya takuma haifar da
cigaba a rayuwarta, a daidai lokacin datake
kokarin taimakon ummi don ta cimma kufurinta a
kan dr. khalifa soyayyar khalifan yakama
zuciyarta, wanda a wannan lokacin ne ta fahimci
meye so tasan zakinsa da dacinsa kusan wahalar
da zuciya ke sha akan ciwon so, tausayin ummi
ya yawaita a zuciyarta domin ta dade tana fama
da ciwon son khalifa, alhali ba ta da tabbas din
komi a kansa, ga misali itama dayake son ta
tanayin ciwo me zafi a rayuwarta na son sa ina
ga ummi da ta tabbatar ba ya sonta ,kowannansu
kam abin tausayi ne, ama dai ita ta fi zama abun
tausayi tunda ita tana sa ran samun khalifa wani
abu ne yake neman yi mata shamaki dashi, ummi
kuwa dama tana sa rai ne tana cire ranta, tunda
ta san bai karbi soyayyarta ba.
Wannan shi ne tunanin fatima.
*****
A bisa wani dan benci dake kofar gdansu
fatima,musbahu ne zaune ya yi tagumi lokaci
lokaci yana fidda nannauyar ajiyar zuciya wadda
ke cike da damuwa da dacin rai,idanuwansa sun
kada jawur ,yau so yake yi ma yayi kuka ya kasa,
wai shin me ke faruwa dashi ne, da can bai
fuskanci matsala da fatima ba sai yanzu, an ya
ba mafarki yake ba, fatima ce tadawo ko ganinsa
ba ta son yi, a baya ko yaushe in suna magana
idan ya kutso mata maganar rayuwa takan bata
rai tace ita kuwa me za tayi da wani namijin
bayan ga zabin da iyayanta suka yi mata, ta
kance k kwantar da hankalinka ba ni da abin da
yafi iyayena in dai zuciyarsu za tayi haske to ni
burina ya cika ba ni da damuwa .
Ire iren wadannan maganganun suke ba shi
cikakkiyar natsuwa da kwanciyar hankali,
musamman a bisa la'akari da rayuwar fatima ba
mai tsada bace in ban da haka kallonta kadai ya
isa hnkalinsa yayi ta tashi sbda kyawun halittar
da Allah yayi mata zai dinga jan hankalin mazan
zamani kanta, to kuma si gashi abubuwa sun
sauya a lokaci guda fatima tajuya masa baya
khalifa take so, yadinga jin wani azababban kishi
da takaici yana tafarfasa zuciyarsa kamar zaiyi
hauka, iyakar tunanin sa bai san yadda zai
bullowa al'amarin fatima ba haka zai aureta
hankalinta na kan khalifa ya girgiza kai, inama
sai da akayi auransu khalifa yadawo, da ba zai
ganta bama ballantana yace yana sonta har
yadaga mata hankali yadagawa kowa.
Yashiga harar kwalla, sai yanzu yaji zuciyarsa ta
yi masa dama dama daya samu hawayensa suka
zubo, tabbas yana son fatima amma yanzu fati
tsoro take ba shi "kukan me kake musbahu?
A firgice yadaga kansa yadubi malam wanda yake
tsaye a kansa yana kallonsa, yaci gaba da sharar
hawayensa ba tre da y ce komi ba, malam yace
"Biyoni ckin gida.
Ckin sassarfa musbahu yake tafiya suka shiga
dakin malam din suka zauna, yakara maimaita
mai tambayar "kukan me kake?
Muryarsa a dashe yace "baba ban san yadda za
ayi in shawo kan fatima hankalinta yadawo kaina
ba, ina jiyewa kaina tsoron abubuwa da dama
game da fatima.
Malam yace "musvahu ni ne fa na haifi fatima ni
ne na yarje ma auranta, har a halin yanzu ina
dada tabbatar maka da cewa in dai ranar daurin
auran nan tazo ina raye ba zan daurawa fati
kowa ba sai kai, to meye na tayar da hankalinka
kan fatima in dai in dai tana ckin gdan nan tana
karkashin ikn mu za a kaita gdanka kuma dole ne
tayi biyayya gareka in har tana son zaman lafiya
damu, ita kanta ta san ba na kwadayin abun
duniya bana son zuciya a kanta kuma ba zan fa
ra ba.
*****
A son ran ummi tayi zamanta a gdansu kada
takoma gdansu khalifa wai a tunanin ta hakan zai
sa hankalinta yakwanta, ta huta da bakin ckin dr.
khalifa da fatima ke haifar mata amma ina lokacin
da dare yayi dare sai taji hankalinta ya tashi
sosai khalifa kawai take bukatar gani.
Tabdijan ashe dai tana da jan aiki a gabanta ace
duk sanda ba ta gdansu hnkalinta ne zai ding
tashi haka, knan va za ta iya rayuwa ba sai tana
ganin khalifa? ta mike zaune zaman ya gagara
tamike tsaye anan ma tashiga sunturi ta dauki
wayarta tayi kiran nomban khalifa bai daga ba
bata san abinda za tace masa ba amma dai in
taji muryarsa watakila tasamu tayi bacci ta huta,
in dai a haka xuciyarta za ta tafi tana da babbar
matsala.
Takira nomban fatima bugu daya fatima tadaga
tayi mata sallama da siririyar muryarta, tace
"fatima bakiyi barci ba?
"Eh banyi ba.
"Meya sa?
Tayi shiru.
Tayi murmushi tace "na san tunanin dr. khalifa ne
yahanaki bcci, don Allah haka ne.
Fatima tayi ta maza tace "Na san kin san haka
ne unmi shiyasa kika fada.
Tayi ajiyar zuciya tace "fatima da ma na san ba
za ki iya kaucwa soyayyar dr. khalifa ba duk da
cewa a baya na mi? ce har ckin zuciyata za ki
taimake ni a kan dr. khalifa to sai ga shi kema....
Haushi yakama fatima ta tabbata soki burutsun
na rashin abin yi ne yasa ummi ke mata wannan
shiriritar dan haka takashe wayarta.
Mamaki yakama ummi ta jima tana kallon
wayarta wai yau ita fatima ke ma haka, bata ma
da lokacin saurararta, hakika ya zamo dole ta
dauki mataki mai kwari akan fatima.
Da gari ya waye da sassafe ta tashi tayi wanka
ko tunanin cin abinci batayi ba tashirya tace da
mahaifiyarta "na tafi gdansu khalifa.
Hajiya na zaune a kicin tana suyar wainar fulawa
tayi mata wani irin kallo tace "wai me ke daminki
ne ummi, abin ci ma ba za kidinga tsayawa kina
cinsa ba sbda khalifa? wannan wainar ma sbda
ke nake yinta na san kina sonta amma ki ce
tafiya za kiyi?
Tace "don Allah hajiya barni in tafi hankali na a
tashe yake ko barci banyi ba jiya.
Tana tuka mota tana wasi wasi a haka har ta iso
gdan masu aiki suka tarbeta da mummunar labari
a asibiti dr. khalifa yakwana ba shi da lfya, tayi
saurin kiran nomban mama tayi mata kwatancen
asibitin dasuke tafigi mota ta nufi can.
Hankalin ummi yakara tashi ganin yadda taga dr.
khalifa mike isa gado, yana wani irin bacci wanda
ga duk alamun bai san a inda kansa yake ba,
mamane zaune bisa dadduma a kasa sadiya a
gfenta abban na zaune kan wata kujera dake
gefen gadon khalifa yazuba masa ido kawai.
Ta tsyguna ta gayar dashi tare da jajanta masa
ciwon khalifa ta zauna kusa da mama tana
tambayarta "me ye musababbin ciwon ne?
Mama ta tabe baki tace "katin daurin auren
fatima yagani.
Ummi tafiddo ido gabanta na faduwa tace "don
ya ga katin daurin auran fatima yashiga wannan
halin?
Mama tace "kwarai kuwa tunda muka kawo shi
asibitin nan bai farka ba har yanzu, nasarar da
akaci dai nu; fashinsa ya dawo dai dai sabanin
lokacin da muka kawo shi dan ko numfashi bbu,
ni zatona ma ya mutu.
Jikin ummi yakara mutuwa murus takoma jikin
bango itama tayi shiru har tarasa abin da za
tace.
Wato wannan soyayyar har ta kai zafin haka, ina
aikin da malamin su yace zai musu mai zafi
wanda yaci musu alwashin zai raba soyayyar
fatima da khalifa da ta duk wata diya mace sai
ita ummin,. Amma abin mamaki kamar karawa
dr. khalifa soyayyar fatima ake, me malamin nan
ke nufi knan, aikain yake musu ko yaudararsu
yake"
Ta jinjina kai a baya kam ta san dr. khalifa yana
son fatima haka yanayinsa yanuna, to amma yau
ne yadada tabbatar da soyayyar nan ba ta wasa
bace duk inda ake tunanin abin ya wuce nan,fidda
soyayyar fati daga zuciyar khalifa abu ne mai
wahalar gaske.
Tadubi mama tace "to yanzu me likitocin suka
ce?
Mama tace "cewa sukayi a samar masa da
abinda yasaka a ransa yana so din idan ana son
rayuwarsa.
Tace "to wani mataki aka dauka?
Mama tace "har yanzu bamu san abinda za muyi
ba. fatima dai tunda ba mu da ikon ba shi ita ai
sai hakuri .
Ta jinjina kai tace "To Allah ya sawwaka bari inje
gda in kawo muku abinci ko zai farka ya bukaci
wani abu.
Mama tace "ga abin cin nan na asibiti an kawo.
Tace "ai khalifa ba zai iya cin abincin asibiti ba
bari dai in dafo wani abun.
Lallai dr. khalifa ya yi nisa ba yadda za ayi yaji
kira, gdansu fatima tafara shiga sai ita kadai a
rmfar inna tana fama da waya, inna tana dakin
malam suna hiran bikin fatima.
Ta amsa sallamar ummi ckin fara'a tamkar ba
wani abun, tukukin bakin ciki yakara turnukewa
ummi zuciya, tayiwa fati kallon sama da kasa
lokacin datake ce mata zauna mana anty ummi.
Tace "ba zama nazo yi ba zuwa nayi in tamvayeki
ina amsar taimakon dakika dauka za kimin a gun
dr. khalifa.?
Nan fatima tarasa abinda za tace tayi shiru,
ummi tace "dama na san bbu abinda za ki iya
cewa, tunda ba ki da abin fada din kinyi amfani
da damar dakika samu kinja ra'ayin dr. khalifa
har soyayyar dayake maki ta kaishi ga kwanciyar
ciwo, to yana asibiti bai san inda kansa yake ba a
dalilin ya ga katin daurin auranki da musbahu, sai
kije ki duba shi kafin yakarasa mutuwa.
Tajuya za ta tafi fati tajawo hannunta tace "Don
allah ummi kar ki tai zauna ki taimake ni nasamu
kaina a wani irin hali.
Wani taimako zan maki fatima? ni van taimaki
kaina ba wa zan iya taimakawa? in kura na
maganin zawo me yasa batayi wa kanta ba?.
Fati na kuka tace "ai rai ba ta rasa motsi ummi
tasaya kiji.
Ta jingina da bango tare da rungume hannayenta
a kirjinta tana kallon fatima, fati tace "a wane
asibitin khalifa yake?
Tace "idan za ki wuce muje.
Gaba dayansu sun rasa abinda za su cewa
junansu kowacce tana neman taimakon 'yar
'uwarta ne ,unmi tace "tunda baki da abin fadi
nima na rasa abinda zan ce miki kisameni a gda
zan hadawa khalifan abinci sai muje asibitin,
dasauri tfice daga gdan.
Yayin da fatima tanufi dakin babansu ta durkusa
tashaida musu cewa za su je karbar dinkin tada
mama tayi musu na biki da ummi, sukace a dawo
lfya.
Ta sauya kaya ko wanka batayi ba tafice daga
gdan, musbahu na kallonta tashige gdansu khalifa
ba shi da ikon yi mata magana sai kallo, fatima
ta fi karfin sa yanzu.
Ummi na kicin tana ta hada abincin cikin
gaggawa, fatima ta yi zaune a falo tana ta kallon
hoton khalifa gabanta sai faduwa yake, wani
babban hotonsa ne yakewa mutum maraba da
zarar ka shigo falon, murmushi yayi a hoton
murmushin dayayi matukar kayatar da fuskarsa,
takagu ummi tagama su tafi taga halin da
masoyin ta ke ciki.
Bayan ummi ta kammala komi a mota tashiga
dakinta da niyyar yin wanka ganin ta jima bata
fito ba a fusace fatima ta bita ckin dakinta
tashiga buga kofar toilet din tana fadin 'haba
ummi wane irin jan rai ne haka? kinsan fa jiranki
nake.
Ummi tace "to don kina jira na ba zanyi wanka
ba, karki dameni malama asibitin ma ganin damar
kaina nayi ko kin sani ne ba sai da na gaya miki
ba.
Fatima tarasa me za tace da ummi don haushi,
kuma karin haushi ne yasa bata kara ce mata
komi ba sai da tagama abinda take a
toilet,sannan tafito tafara shiryawa,fatima takara
fusata a karo na biyu tace "ummi idan ba za ki
rakani asibitin nan ba ki gaya min in yi tafiyata.
Ummi tarausayar dakai tana murmushi tace "yi
hakuri taso mutafi.
A cikin mota tafiya suke kamar wasu kurame,
kowacce da abinda take fama dashi a zuciyarta,
da suka shiga harabar asibitin tasamu wuri tayi
parking fatima ta tayata diban kayan abincin
suka shiga dakin.
Abba ne yakama fara'a yana fadin "fatima ke ce
da kanki?
Kunya da tausayi suka kamata lallai abba na
cikin damuwa ta tsuguna tagayar dasu tare da
tambayarsu mai jiki,

Please Login or Register in order to submit comment