Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lahira.
Ni na san bbu namijin dazanso bayan kai,
Anisa....
Iya abinda takardar takunsa knan, har gumi yaji
yana keto masa sbda tsabar tausayin anisa,
yadinga jin wani iri a ransa yana tunanin rayuwar
dasukeyi wadda ba ta da wani amfani a garesu,
idan suna gaban iyayansu sai su dinga nunawa
su na kirki ne amma a bayan idon iyayan na su
suna aikata abinda suka ga dama.
Shin tsakanin iyaye da Allah wa ya fi dacewa aji
tsoro, in har suna boyewa iyayansu halin dasuke
cki ne don suna tsoronsu, Allah daya halicci
mutum shi yafi dacewa a ji tsoro, kuma Allah
yana kallon mutum a ko wani hali yake.
Wannan nasiha da khalifa yaiwa kansa yasa yaji
nan take komi ya fice mai daga rai ya tsani yan
matan dayake tare dasu na holewa, yana bukatar
yazamo natsatsen mutum wanda yake biyayya ga
Allah da manzonsa, takaicin abubuwa da dama
suka kamashi har yaji kyamar kansa da kansa
yakeji, yamike jikinsa ba kwari yafito daga dakin
yadawo dakinsa, ya isje shu bby har yanzu
baccinta take cike da nishadi da kwanciyar
hankali, yasa hannu yagirgizata dakarfi tabude
ido tana fadin "bacci ke damuna,yace " ba na iya
juriyar yunwa.
Tace "ina yar aikin gdan nan?
Yace "ba ta nan.
Ba abinda shukra tatsana irin girki amma da yake
khalifa ne haka tadaure tadafa ruwan tea da
dankali da plantain, ba wani kwarewa tayi da
girkin ba yunwa ce tasa kawai yaci.
*****
A DAREN FARKO
17
Tun daga wannan lokaci rayuwar khalifa ta sauya
gaba daya yadaina sauraror kowacce mace har
da ita kanta shuu babyn, hatta fAisal ya watsar
dashi sbda ya yi ya yi yaja hankalinsa don shima
yadawo hanya tagari faisal ya yi masa wani irin
kallo shekeke yace "kai kiwa meya sameka da za
kace mudaina rayuwarmu, tajin dadi mu takura
kanmu, ko mafarki kayi ka mutu an sa ka a
wuta?
Khalifa yace "ko kusa banyi wani mafarki ba na
dai yi wa kaina fada ne dan na fuskanci gaskiya,
na ga yakamata inja hankalinka kaima damu
daina wannan rayuwar kafin ranar nadama tazo
mana.
ko wata amsar kirkifaisal bai ka ra bashi ba
yamike yavarshi a gurin,hakan yasa khalifa ya
janye jikinsa yakoma rayuwarsa shi kadai, yanemi
masu dafa masa abinci da gyaran gida bai zuwa
ko ina sai makaranta inya dawo yakan kulle
kansa a dakinsa yayi ta nazarin abinda yake
karantawa ko karatun alkur'ani mai girma wanda
a baya ko bude shi ba ya yi sbda shagalta da
rayuwa da ya ya mata dayayi, sai yake jin dadin
rayuwarsa a haka hatta hotunan sa da
nambobinsa ya goge, yayi ta karfafar zuciyarsa
tare da neman gafarar Allah yana rokon Allah
yataimake shi yaraba shi da wannan rayuwa.
A haka a haka har Allah yataimake shi
yakammala karatunsa yakawo shi inda ya fito da
kyakyawan sakamako zuwa babban likitan mata a
lkacin ya dada kasaita irin mazan nan ne da dole
idan aka kallesu a kara sbda cikar zatinsu,
kwarjini da ilimi, 'yammata sun yi sunyi suja
ra'ayinsa kowacce tana fatan yasota amma ya ki
bada kai, matar aurance har yanzu baiga wadda
yagamsu yaji ta yi masa zai zauna da ita a
matsayin matar aure ba, amma dai mace ta
holewa ya yi alkawarin insha Allahu ya daina.
Kafin ranar dawowarsa gida nigeria ya yi ta
neman yadda za ayi yaga anisa ya rasata haka a
kano bai san a ina zai ganta ba, yana yawan jin
tausayin ta tare da yimata addu'a duk sanda
yatuna ta.
Tunda ya daura damarar tahowa gida damuwarsa
itace yarinyar nan ummi ya san ta yi girma yanzu
sosai ta kara wayo a baya ma ta iya budar baki
tace tana son shi ballantana yanzu, bayan shi ba
wani sakar mata fuska yakeyi ba ballantana ace
shi kwata kwata ba ya da ra'ayin auran zumunci
kuma ko yana dashi ma ummi bata cikin
lissafinsa, cikin hikima yatambayi mamansa a
waya ko an yiwa ummi aure, tace ai bata fidda da
mijin ba ma ba ta sauraron kowa tun da tayi
candy abban k7ma ya ce ya dace ta fidda mijin
aure tunda mutane dayawa suna nunawa suna
sonta in ya so taci gabada karatun a gdanta sai
tace wai wanda takeso din ya yi doguwar tafiya
idan yadawo za ta gabatar dashi.
Wannan yafadarwa dr. khalifa gaba ya tabbatar
yarinyar nan in baiyi da gaske ba zata zame
masa matsala, har ranar dawowar tasa tunanin
da yake fama dashi a xuciyarsa knan, yarinyar
tashiga ran mamansa za a iya cewa sai ya
aureta ko da yake bai da matsala da abbansa,
maganar mamansa kuma da karfi a kansa baya
son bata mata rai.
*****
Karfe sha biyun rana fatima tagama shiryawa
cikin wata blue din batik mai haske riga da zani
ne amma kai kace siket ne sbda yadda kayan
suka zauna a jikinta suka yi mata kyau abin har
ba a magana, ita da kanta ta yi sha'awar kanta
sbda kayan sun mata kyau, telan dayayi dinkin ya
gwanance a fagen tsarawa mata dinki, ta jima
tana gyara gashinta ya dau kyalli ta tsara daurin
dankwalin sosai yadda yadace da adonta tazuba
fashion da mayafin da suka dace da kayan, ummi
ce ta bukaci taraka ta gdansu yau wato gdan
iyayanta, fati bata fiye son xuwa gdansu ummi ba
sbda jininsu bai haduwa da hajiyarsu ummin ba
tare da ta san abinda tayiwa hajiyar ba, tana cin
darajar diyarta ummi ne kawai sbda a halin yanzu
ummi tanad\ matsayi lamba daya a zuciyar
fatima ba ta da na biyu kowacce irin alfarma
fatima za ta iya yi akan ummi.
Innar tana zaune a kofar dakinta tace "inna sai
mun dawo.
Tace "adawo lafiya a gaida su.
Tayi sallama a kofar dakin malam musbahu
yadago yadubeta sai yayi saurin bude idonsa
gaba daya yace "kai fatima wacce irin kwalliya ce
wannan? kin ga yadda kikayi kyau kuwa?
Ta lumshe kyawawan idanuwanta tana murmushi
tace "ka manta na gaya maka za muje gdansu
ummi.
Yace "fatima gskiya in banda ummi na da
matsayi mai girma a gareni ba zan iya barinki fita
cikin wannan kwalliyar ba ban taba ganin ranar
dakikayi kyau a ido irin wannan rana ba, fatima
ina fatan Allah ya mallaka min ke.
Tace "malam ai ya mallaka ma saura kadan
yarage komi lokaci ne.
Ganin zai tsaida ita da maganganu na santin
kyaun datayi yasa tawayance tafice tabarshi yana
hadiyar yawu kamar yabi ta yayi ta kallonta yau
kyaun datayi masa daban ne.
Bayan sun gaisa da mama tawuce dakin ummi ta
iske ta tana shiryawa tace "mutuniyar kin hadu
kayan nan sun yi miki kyau bana wasa ba.
Fatima tace "kai wai ke ba kya gajiya da yaba
kyau na ne? kullum sai kin cena yi kyau.
Tayi dariya tace "to ai yabon gwani ya zama dole
kinyi kyaun ne ba na gajiya da kallonki fatima,
don Allah idan kinyi aure kada kidaina kwalliya
kina matukar yin kyau da kwalliya dukda cewa
idan ma bakiyi kwalliyar ba kyau kike yi ke kam
Allah ya yi miki baiwa da yawa fatima.
Tace "don Allah kiyi sauri mutafi kadda yamma
tayi ba kya gajiya da surutu.
A cikin mota suna tafiya ummi tana tuki fatima
tana gefenta suna hira, tace "duk inda muka wuce
fa sai an kalleki fatima ina kallon wani dazun da
danja ta tsayar damu sajra kadan yabuga wa
wani sbda kallonki, kidinga sa nikab kidaina
daukar hankalin mutane.
Ta dubeta tace "su sukaga za su iya ni bance
wani yakalleni ba duk wanda wani abu yasame
shi a dalilin kallona to shi yadauki alhakin kansa,
muyi wata hirar.
Tace "yawwa ai kuwa yau zan miki gagurumin
albishir.
Fatima tace "Allah sarki ai kuwa ni bani da wani
labari da nake son ji mai faranta rai daya wuce in
ga khalifa ya dawo ya amince da batun auranki
da shi, wlh a wannan rana bansan farin ckin
dazanyi ba, bansan yadda zan fassara wannan
rana ba, gskiya anty ummi ina kaunar khalifa ne
sbda son da kike mishi., duk da cewa na tsane shi
tawani fannin sbda ba ya da tausayi.
Ummi tayi dariya tace"ummi misali idan ke ce
wani namijin yazo yana miki irin son danake wa
khalifa za ki tausaya mai kiyarda da auran ko da
ba kya sonsa ?
Fatima tace "ummi ni mutum ce da ba na son
ganin musulmi dan uwana a cikin damuwa in dai
har na san yana zubda hawaye akan ciwon so na
irin yadda kike zubda hawaye akan son khalifa
zan tausaya mishi.
Ummi ta girgiza kai "to albishirinki soyayya ba
haka take ba.
Tayi saurin katseta da fadin "ko ma yaya take
ummi, khalifa ba shi da kirki, ba shi da tausayi,
ya kamata mutum yaso mai sonsa, ya kamata
mutum yakasance mai tausayi, nikam ba zan taba
yiwa khalifa uzuri ba, duk da haka don Allah ina
rokon idan khalifa yadawo kasar nan...... "
Ummi tayi fakin a kofar gdansu tace "ki kwantar
da hankalinki idan Allah ya kaimu gobe khalifa zai
dawo kasar nan.
Tadafe kirji tare da fiddo ido tace "don Allah
dagaske kike ?
Tace "kada kiyi shakkar hakan kizuba ido gobe za
kiga dr. khalifa.
Ita kantaa ummi bataji dadin samun hajiya saude
a gdan ba sbda a fili suke nuna ba sa son fatima,
yayin da ita kuwa ta tsani mutum ya nuna mata
ba ya son fatima, tana matukar kaunar fatima a
ranta.
Fatima tatsuguna har kasa tagayar dasu su ka
amsa kowacce fuska ba fara'a suka ja baki suka
tsuke, wayar fatima tafara ringing tamike tayi
sauri tafita ganin sunan malam musbahu, nan da
nan hajiya saude tazubawa ummi harara tace
"wai me kike nufi da yawo da wannan kodaddiyar
yarinyar, duk inda za ki sai da ita za ki, sai da ita
za kizo gdan nan ma kin dauko ta kina nufin duk
abinda xa mu tattauna akai sai dai muyi a
gabanta knan ba mu da wani sirri sai ta ji ?
Hajiya hauwa tayi tsaki tace "ba ma wannan ne
abin haushin ba saude sai yadda ummi take bata
rai idan munce muna son magana da ita wai lallai
sai duk abinda za a fada a fada a gaban fatima.
Bayan ita fatimar idan sun tashi na su sirrin da ta
ta uwar tafiya take gdansu suyi maganarsu ba a
gaban ummin ba.
Hajiya saude tace "ai ummi ba ta da wayo na
rasa wacce irin soyayya takewa fatima kamar
wadda ta asirceta, ga ta dai a haka kamar wata
mai wayo nan kuwa ba komi a ranta sai wauta,
mu da mukeso mu mallaki khalifa ta jawo
wannan mai kama da aljanu ta jawota gdan
kullum a gdan take yini idan yadawo ba kya jin
ba zai ce fatima yake so ba ?
Ummi tace "hajiya ya ya za ayi khalifa yace yana
son fatima bayan an kusa bikinta, kwanaki kadan
suka rage akaita gdan mijinta.
Hajiya tace "wohoho ummi sai yaushe za ki
fahimci halayyar mutane ne kidinga taka tsan
tsan dasu, ki guji sharrin wanda kika taimaka wa,
lokacin daka tausaya wa mutum kadakko shi
daga rana kayi masa gata kadawo dashi inuwa
bbu wanda zai tura cikin rana sai kai.
Kin ga dai ke ce kika wayar da fatima da iya
kwalliya da komi hatta magana ke kika koya mata
amma babu wanda fatima za ta fara yiwa illah
sai ke, tabbas idan bakiyi taka tsan tsan ba sai
kin ce na gaya miki.
A DAREN FARKO
18
Ummi takwana tana jujjuya maganganun su
mahaifiyarta tana musanta duk abunda suka fada,
ita kam ta yarda da fatima dari bisa dari bazata
cutar da ita ba ta tattara duk maganganun na su
ta watsar, ta fuskanci ranar dazata fuskanto ta
wato ranar dawowar mutumin da ba tasan abinda
sakamakon dawowar ta sa za tahaifar mata ba,
farin ciki ko bakin ciki dole a daya biyu ne don
haka a wannan daren bacci ta ragagge ne duk
sanda tafarka sai ta ji gabanta ya fadi.
Da sassafe takira fatima a waya tace don Allah
tazo, tace lafiya, tace "banjin dadin jikina ne da
zuciyata inason ki zo miyi hira.
Fatima tace "don Allah ki kwantar da hankalinki
khalifa fa ba wani bane illa mutum kamar kowa,
meye na(aga hankalin ki akansa ?
Tare da fatin suka shiga kitchen lokacin dataxo
gdan wuraren karfe tara na safiya, ko da yaushe
mama na yabawa yadda suke tsara girki da tebur
a halin yanzu fatima dai da iyayanta sun zamo
yan gda sosai a gdansu mama, suna yawan yi
musu alheri na kayan abinci da sutura, wani
lokacin mama dakanta take zuwa gun innar su
fatima suyi hira sosai tanajin dadin shawarwarin
datake ba ta akan rayuwa, sun shaku dayawa
haka malam da abban khalifa sun zamo aminan
juna ,idan kashiga gdan za kace fatima 'yar gdan
ce sbda sakewar da takeyi, ci mai kyau da sha
mai kyau ga kayan ado hakan yasa fatima tayi
kyau ba na wasa ba kamar a taba jikinta jini
yafito ta zamo kamar irin taurarin matan nan da
suke zamowa ababan kallo a duk inda suka shiga,
mafi yawan mazan dasuke shige da fice a gdansu
mama idan sunga fatima sukan nace suna sonta,
ba ta sauraron kowa duk kudin mutum da
kasaitarsa, fatima ba ta bari yashiga ranta sbda
alkawarin datayiwa babanta na auran malam
musbahu yana tsaye a zuciyarta, bata taba wasa
da maganar iyayanta ba koyaushe farin ciki ? su
shi ne ranta.
Gargadin karshe dasu hajia hauwa suka yiwa
ummi shi ne "ta sallami fatima daga gdansu
mama kafin khalifa yadawo kasar nan in ba haka
ba tai kuka dakanta, ta jiye ma kanta abinda
zaisa ta tayi kuka ba iyaka, bbu maganar data
kama ummi aciki face ma dariya dasuka bata,
magana daya tayi musu inda tace "su kwantar da
hankalinsu da ace fatima za tayi soyayya da wani
da tuni ta yi kafin ma khalifa yadawo sbda
mazaje dayawa masu matsayi da takama da
dukkan abinda da namiji yake takama dashi sunce
suna sonta bata taba sauraron wani ba, ta rike
maganar iyayanta dagaske ,tunda dai fatima bata
yi soyayya da wani da namiji ba ba za tayi da
khalifa ba.
Hajiya saude tace "haka kike gani, ke mesa kikace
ba kya son kowa sai khalifa ?
Tace "wannan kuma daban soyayya gamon jini ce
bai zamo dole don ina son wani yakasance wance
itama shi tame so, masu iya magana ma kance
abincin wani gubar wani.
Gaba daya ummi ta san basu gamsu da hujjojinta
ba, hankalinsu a tashe yake a bayan azahar in
yau sai da hajiya takirata tana tmbayarta "in ce
ko fatima ba ta gdan nan, na ji ance khalifa ya
iso gda nigeria yana Lagos yana shirin isowa
kano.
Ummi tace "hajiya itace take tayani hada mai
abinci, kin san yana son abinci mai dadi.
Taja tsaki takashe wayar har tarasa yada za tayi
da ummi.
Karfe hudu na yamma dun abubuwan ci da na
sha da sukaiwa khalifa sun hada a tebur, gida ya
dau kamshi an gayare mai dakinsa fes yanata
kamshi, bayan fati Ta idar da sallar la'asar tazura
dogon hijjabin ta da nufin tafiya gda.
Ummi ta fito daga wanka tace "zan tafi idan
bakon ya isa ki ce muna masa sannu da zuwa.
Ummi tace "ai kuwa baki isa ba dole ki tsaya
kiga khalifa ya dace kigan shi.
Tace "To ai na sanshi a hoto duk wanda ke
shigowa gdan nan ko bai taba ganinsa a fili ba ya
san shi a hoto ko ina a gdan nan fa hotonsa ne.
Tace "ai na san da hakan nace kitsaya kigan shi
duk yadda yake a hoto ya fi nan.
Fatima tayi dariya tace "na san zaifi haka ummi
idan za ki lura ai ban taba cewa kinyi laifi don kin
wa dr. khalifa son da kike masa ba, ya cancanci a
so shi dan ya hadu kowa yana son abu mai kyau,
ba laifi bane don mace ta so mijinta yakasance
mai kyau irin dr. khalifa sai dai bbu ,gskiya yi
hakuri ba zan boye miki ba ba na farin ciki da
gani ? khalifa, ina tayaki murnar dawowarsa ne
kawai don shi ne farin ckin rayuwar ki ina son
abinda zai faranta ranki ummi fiye da farin cikina,
da ace dr. khalifa ya amince ya karbi soyayyarki
da zan kasance cikin dumbin farin ciki mai yawan
gaske amma duk da haka....
Ta katseta "fatima in dai dagaske kina son farin
cikina tsaya dr. khalifa yazo don Allah.
Fati bata sake magana ba tafidda hijjabinta
tahaye gado takwanta, doguwar rigar shadda ce a
jikinta ruwan powder, daga sama ta matseta
yayin da tayi fadi daga kasa, babu kwalliya
fuskarta gashin kanta ne dai ya sha gyara
yakwanta a kafadarta ,a cikinsu babu wanda
tasan khalifa ya shigo gdan.
Ummi tace "don Allah fatima dako min ragowar
furar dana rage a fridge.
Fatima tafito a yadda take ko dankwali babu
tashiga kitchen din falo tadakko furar kwatsam
suka hada ido da dr. khalifa daya fito daga dakin
mamansa, abbansa na biye dashi da manyan
abokansa biyu dr. hafizu da dr. bashir, gaba daya
taji kunya ya kamata cikin karfin halin gaske
tarusuna tace "barka da isowa.
Kallon da yayi mata yasa jikinta ya hau rawa ta
wuce dasauri cikin dakin ummi tace "ke ai
mutumin na ki sun shigo.
Ummi tadafe kirji tace "don Allah ? furar da bata
sha ba knan tazuba wata doguwar riga amma ita
ta atamfa ce tayafa dankwalin a kanta ta fesa
turare ta fito falon, tuni har sun haye tebur sun
fara cin abinci.
Fatima tabude dakin taleko don taga kallon da dr.
khalifa zai yiwa ummi, ai kuwa fuskarsa baa
fara'a yake amsa mata gaisuwa, su dr. hafiz ne
masu zolayarta, shi kam gogar na ka ya yi dif
abinci kawai yake durawa cikinsa.
Wani irin takaici yakama fatima kamar taje
tashake dr. khalifa tahuta an masa abinci ko
yabawa ba zai yi ba yana walakanta wadda tayin.
Wai wane irin mutum ne haka, nan da nan tayi
takara tsanar sa, taja tsaki takoma kan kujera
taharde .
Ummi tashigo dakin harara tafara samu a idon
fati tace "mi yiwa Allah ki daina son dr. khalifa ba
shi da kirki.
Ummi jikinta a sanyaye tazauna tayi tagumi tace
"kiyi hakuri haka halayyarsa yake har in mutu ba
zan daina sonsa ba, shi kadai nafara so a rayuwa
rata, ba na iya hadashi da kowa ko bai aureni ba
ba zan hakura dashi ba kitayani addu'a kawai.
Fatima tafigi hijjabinta tace "to gaskiya ni ba zan
iya ci gaba da zama a gdan nan ina ganin wanna
abin haushin ba.
Bata ji kiran da ummi ke mata ba tafice, sai dai
abi ? takaicin dole tawuce ta falo gashi ba ta son
kara ganin dr. khalifa yayin da shikuma dr. din
kamar an ce yadago idonsa sai yadago karaf
akan fatima za tafita, shi kansa bai fahimci
muryarsa ba lokacin daya ke ce wa, "ke zo nan"
Tayi dan jim, ba wata a falon lallai ta san da ita
yakeyi, ya dace ta walakanta abin da ummi ke so,
ranta a bace ta nufo inda suke ta tsuguna a gefe
kanta na kasa tace "Ga ni .
To bai san dalilin dayasa yakirata ba, ballantana
yasan abinda zai gaya mata, ya samu kan shi da
zuba mata ido shi dai bai san ta a gdan ba, Dr.
hafiz ne yace "yammat don Allah ya sunanki ?
Fatima kawai tace.
Kafin wani cikin su yakara magana tamike
dasauri tabar gdan.
Dr. khalifa ya ajiye spoon din hannunsa yayi
ajiyar zuciya yace "fatima.
Kai wannan yarinya Allah ya hore mata kyau.
Dr. bashir ya kyalkyale da dariya yace "likita knan
bokan turai nan kuma kagano ance inda baki
yakarkata nan yawu ke zuba.
Fitowar mama takatse maganar tazauna suna
hira, dr. khalifa yace "mama ina kuka samo
fatima ?
Tace "yarinyar nan makwabtan mu ne wanda
kuka gaisa da babanta a waje dazun wanen
malam musa.
Ya basar da maganar kamar bai damu ba sukaci
gaba da wata hirar.
*****
Tun a daren masu zuwa yiwa dr. khalifa sannu
dazuwa suka fara cika gdan yawanci tsoffin
abokansa ne musamman na B. U. K da 'yan'uwa
da abokan ckin dangi, wayoyin sa ma kashe wa
yayi don yahuta, bai samu kansa ba sai sha biyun
dare yahada ruwa mai zafi yai wanka yafesa
turare yahaye gado, tunanin bai samu masauki a
zuciyarsa ba yahau bacci sallar asuba ma sai da
abbansa yatayar dashi suka nufi masallacin tare,
ita kanta sallar idanunsa a rurrufe yayi ta suna
dawowa yakoma wani sabon barcin.
Yayin da ummi takwana ckin fargaba da kai komo
a zuciyarta da tunanin tayaya za ayi dr. khalifa
ya aureta ? zancen haduwa yanzu ba a magana,
a tsaya bayyana tsarin kyau da Allah ya hore wa
dr. khalifa bata baki ne, zuciyarta takara rudewa,
sabuwar soyayyar data ninka ta bata ta karu
akan ta da, ummi ta ji kanta tamkar tsawa tsawa
yake mata.
Da sassafe kamar yadda tasaba tashiga kitchen
tafara hada abincin dr. khalifa na musamman,
mama ta fita tace mata takira fatima a waya tazo
tataya ta domin akwai wasu abokan dr. khalifa
daza suyi breakfast tare nan da karfe takwas.
An yi sa'a fati ba ta kashe waya, lokacin da
ummi tabayyana mata bukatarta amsawa kawai
tayi ba dan ranta ya so ba, hakanan take jin wani
irin abu a zuciyarta jininta bai hadu da dr. khalifa
ba, kallon da yayi mata ya firgita ta kwarai
dagaske, ba ta da matsala da inna da babanta
akan zuwa gdan mama, hijjabinta dogo har kasa
tasaka tafito zuciyarta cike da sake saken abinda
zai je ya xo.
Aikin suke kowacce da abinda zuciyarta ke
sakawa, karfe takwas komi yakammala a tebur
suka debi na su sukayi dakin ummi.
Kinga dr. khalifa ko fati ?
Ummi tayi tmbayar tana kallon idon fatima wadda
tagyada kai fuskarta a tsuke tace "eh na ganshi
meye. "
Ummi tasa gefen mayafinta tana sharar kwalla
takasa cigaba da magana, zuciyar fati ta kuntata
sosai yadda abincin yaki ciyuwa a gun ummi
itama kasa ci tayi, tace "ummi ko zuwa zanyi in
rokeshi yasoki.
Tace "karki yi haka ya gargade ni akan kada in
fadama cewa ina son shi, dole in kiyaye dokarsa
in dai inason in zauna lfya.
Fatima tace "to yanzu haka zamuyi ta zaman
damuwa ?
Ummi tace "damuwa ta kam ba zata gushe ba
amma na ci alwashin ba zan bar dr. khalifa ba ba
zan yarda in rasa shi wata tasame shi ba.
Tunda ummi take irin wadannan kalaman jinta
kawai fati take ta san me za ta iya ? hakuri ne
yazame mata dole in batayi ba tayi tashan
wahala idan so cuta ne hakuri kuma magani ne.
*****
A wannan rana malam musa mahaifin su fatima
yafidda bayanin cewa sati biyu rak za ayi bikin
fatin da musbahu akai tagdansa, har inna tace
"malam bai yi wuri ba har yaushe aka gama shiri.
Yace "shi kam wannan lokaci yasanya kuma ba
zai daga ba, fatima na dawowa gda malam
musbahu yatare ta da zancen yana cikin farin ciki
mai yawa, itama ta nuna gamsuwarta tare da
fatan alheri garesu baki daya, yatambayeta
abinda za tayi da kawayenta na shagalin biki tace
ta fi sha'awar walima a ranar jumma'a da
yamma amma dai za tayi shawara da antinta
ummi.
Data shiga ckin gda takira ta a waya tashaida
mata, ummi tarangada guda tace "amarsu ta
ango knan wannan sai mun zauna an tsara yadda
za ayi, zanso ganinki ranar wannan biki za kiyi
kyau na jan magana.
Fati tace "fatana aure dai Allah yasanya mai
alheri da albarka ba na na so inga anyi aure anyi
shagali aure na soyayya amma auren bai je ko
ina ba sai kiga ya lalace ko ayi ta samin matsala
a rasa laifin waye mazan ko matan ?
Ummi tace "kowa na da laifi fati a tsakanin
mazan da matan ko wanne akwai rawar dayake
takawa gun haifar da matsaloli ckin auran da
rabuwarsa, amma dake insha Allahu za kuzauna
lafiya da malam musbahu domin aure ne da aka
gina shi a bisa kyakyawar turba, kuma za ayi shi
ne don Allah,.
Bayan ummi ta kashe waya tafito falo, ganin dr.
khalifa ya hakimce bisa kujera wata lafiyayyar
shadda a jikinsa maroon colour dinkin da
matasan zamani ke yi yayi, ya yi kyau har ya
wuce misali, farin gilashin idone a fuskarsa bai
damu da zaman ummi a gun ba yaci gaba da
fadin "mama kinsan maganar aure tana bukatar
nazari da bincike, wlh a rayuwata bbu auran dana
tsana irin je ka kadawo, ayi aure ana farin ciki da
zarar an je an zauna a kasa fahimtar jin dadin
dake ckin zaman auren, kullum kana ckin
damuwa matarka na ckim damuwa meye amfanin
hakan, amma idan aka natsu za asamu kwalliya
tabiya kudin sabulu sbda na sani bbu wanda ya
isa yakaucewa abinda Allah ya hukunta masa.
Yayi shiru anan yana nazarin fuskar mama don
ya fahimci yadda tadauki maganar, batace komi
ba tajuyo tadubi ummi tace "'yammata yaya
akayi ne yau fatin batazo tayin hira ba ?
A sanyaye tace "batazo ba waya tamin yanzu
tace malam ya ce idan Allah ya kaimu nan da
sati biyu za ayi bikinta.
Mama tatsuke fuska tace "wani irin sati biyu
kuma ?
Tace "haka dai tace.
Tace "to je ki kiramin fatin har yaushe akayi mata
shiryen shiryen amaren.
Dasauri ummi tabar gun tafada daki don tasamu
damar yin kukan data ke ta hadiyewa.
A falo kuwa dr. khalifa ne yaji wani irin abu ya
tsirga masa a cikinsa zuciyarsa takama bugawa.
Fatima Za ayiwa aure nan da sati biyu ko kuwa
wata fatin ce daban, nan da nan yanayinsa
yasauya gaba daya yawaiwayo tare da zare space
din sa yadubi mama yace "mama wace fatin za
ayiwa aure ne ?
Tayi murmushi "fatima yarinyar nan dai ta
makotanmu daka gani jiya.
Yace "doyar malam musa ?
Tace "yawwa ita kuwa.
Abinda yafito daga bakinsa shi kansa ya ba shi
mamaki don bai san sanda yace "Lallai da sake".
******
A DAREN FARKO
19
Mama tayi masa wani irin kallo tace "me kake
nufi ?
Anan ne yadan shiga natsuwarsa yace "mama
wannan yarinyar nakeso na aura don gskiyar
magana ita neke ganin ta dace da rayuwata da
tsarina haka nan zuciyata ta aminta da soyayyar
ta dari bisa dari don...
Ckin zafin rai mma tadaga mai hannu tace "kai
ya isa haka, saita bakinka kasan abinda kake
fada, fatima an yi mata miji tsawon lokaci mai
yawa kuma ba za a fasa ba shi a ba ka ba.
kada kasoma sanyawa zuciyarka soyayyarta
wahalar da kanka za kayi don baza kasame ta
ba.
Bai ce komi ba yamike yabar faol zuwa daki ? sa
yakira dr. hafiz yace "kana ina ? "
Yace"ina asibiti yanzu muka fito daga meeting..
Yace "to ina ka dosa ?
Yace "gida za ni akwai magana ne ?
Yace "kwarai kuwa magana ma babba ba karama
ba.
Yace "kasameni a gida mana.
Mota yadauka yanufi gdan dr. hafiz da ke hotoro
ya iske ya rigashi isa, yace "matar gdan fa da
yaran ?
Dr. hafiz yatabe baki yace "ai mata ba su da
matsalar data wuce biki, sunan wai kanwa ta ce
data haihu tun karfe bakwai tabar gdan nan ko
abinci ba a tanadar min ba kuma yunwa nakeji
sosai, yanzu sbda Allah a irin wannan tsarin idan
munce, za muyi aure

Please Login or Register in order to submit comment