Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka mai dani wofi,kana jina fa? Nace ka tsaya na fita,surutai sosai beauty keyi,tun tana gunguni har takai ga samun sararin d'aga murya,ganin har lokacin sameer tafiya yake bashi kuma da niyyar tsayawa yasa ta kwarma wani uban ihu da bashi ba ita kanta sai data firgita,lura da lokacin ya fita daga wajen mutane ya fara yankar daji yasa shi jan birki ya maida motar gefen titi ya tsaya,kana ganin sameer kaga wanda yake cike da b'acin rai basai an gaya maka ba,wani wawan kallo ya jefe ta da shi mai cike da tsana,kusan minti 2 yana mata shi ganin hakan bazai gama isar da sak'onsa ba yasa shi magana"tur da wayewar gari irin wannan a wajena,ina ma ace mafarki nake,wallahi da tuni na farka na shiga gari na hau sadaka,don wannan munin mafarkin yakai matuk'a!kaicona sai gashi wai a zahiri ne,ni ne yau kusa da mace fasik'a,fajira,wacce bata san k'ima da mutuncin kanta ba,balle kai tunanin samun tsarki tattare da ita,nikam Allah wadai da mace 'yar Allah bani musha kunin kanwa,wai ya ma akai kika zama 'yar ummah?how??duka yakai a sityarin motar rai b'ace cike da nadamar hakan!



Tun tana danne zafafan kalaman dake fitowa daga bakin sameer har abin ya fara kai ta mak'ura gashi yak'i ci gaba da tuk'in kuma yak'i yarda ya sauketa,wasu zafafan hawaye ne suke k'ok'arin gangarowa kumatun beauty cikin sauri ta sharesu dan kar sameer ya ga lagonta ko kasawarta,juyowa tai cike da tsiwa tace ya isa!ya isa haka malam,ka ishe ni da surutai nace ka sauke ni ko dole ne sai ka tafi da ni?
Cikin huci sameer ya amsa ta"dole sai na tafi dake,ke kanki kinsan hanyarmu ta sha ban ban in banda k'addara!hayaniya sosai suka shigayi ya fad'a ta fad'a kamar wasu karnuka,har takai ga ta big'e masa hannu don masifa,kan uban can!ni kika bige ma hannu?ai sameer be jira ta bashi amsa ba ji kake fau fau ta ko ina dukanta yake kamar an aiko shi,duk da wuyar dukan da take sha amma hakan baisa bakin beauty ya rufu ba,sai da yaga yayi mata lilis sannan ya kyaleta,nan ne kuma tai lamo saman kujerar mota tana maida ajiyar zuciya!
Sai a lokacin ya janyo goran ruwa dake sak'ale a marfin motar ya sha,sannan ya bud'e motar,hannunsa ya wanke kafin nan ya maida k'ofar ya rufe yata nanata astaqfirulla,shi ala dole ya tab'a mace(kun ji sameer fa)wata doguwar tsuka ya saki yana fad'in ni dai duk iskancin mace da makircin ta na fi k'arfinta don ni ba ta shin shaid'anu bane,in ma sune ke bibiyarki gara ki gaya musu su barki dan nan baza ku sami waje ba,sai a bari sai an koma *'jami'a* sai a ci gaba,yana kaiwa nan yayi saurin kai hannunsa ga cd rom d'in motar, kaset d'in qira'a ya kunna, a hankali kake jin muryar sudais na tashi aciki,cikin sanyayyar muryarsa mara sauti haka ya shiga raira qira'an yana wani kwantar da kai saman kujera,sannan ya tada motar yaci gaba da tafiya!
[10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: *'YAR JAMI'A*

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

61-65



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*



Duk da ba wani bacci beauty take ba amma haka tai shiru itama dai tana sauraron qira'ar da haka har bacci ya d'auketa!lura da yadda ta makure kanta waje d'aya sameer yayi,nan da nan ya k'ara k'arfin ac d'in motar inda ta ko ina kake iya jin sanyi,shi kansa sanyin yayi masa yawa amma don mugunta haka ya hak'urar ma kansa,can cikin bacci beauty ke jin sanyin a jikinta, juyowa tai ta kai hannu ido a rufe tana laluben makunnin ac,d'all...taji an kai mata duka a hannu,wani irin zugi taji hannunta ya d'auka ba shiri ta bud'e ido,kansa na a titi amma yasan tabbas shi take kallo yace,kar ki kuskura ki bari najasa ta tab'a tsaftataccen abu in ko ba haka ba,yanzu ki sake shan wani dukan!
K'ara gyara zamanta sosai beauty tayi har tana wani bank'aro k'irji waje ta murgud'o mai baki tace bismillah d'an halak ka fasa,
Kallo d'aya sameer yayi mata ya k'ara sakin wani tsakin yace kaga balama,wato na dake ki d'azu kin ji dad'i hankali ya kwanta,har da lumshe ido shine yanzu kike so jikina ya k'ara tab'a naki ko?toh na gano ki!gaskiya ke akuya ce ko wacce harawa ci kike!God forbid! Wannan irin rayuwa taki yarinya kamar tashin getto!
Marairaice murya tayi beauty uwa mai shirin kuka take nuna kanta da yatsa tace,ni nake son ka tab'a ni?kai kuwa kasan ni wacece?cikin tsiwa shi ko sameer ya dawo mata da amsa"ahaf ni ko nasan ko ke wacece,ko ba kece wannan karuwar malaman jami'ar ba? wacce sunanta yayi k'auri a wajen d'alibai kai har da malamai ko ina ka zagaya *'yar jami'a* duk mutumin banza ya sanki!bayan wannan sanin akwai wani sani da zan miki ne?don haka ina gargad'inki in kina son tafiyarmu ta k'are lafiya toh ki iya bakinki kuma ki nisanci zama a inda nake,bata jira taji k'ashen maganar tasa ba ta juya masa baya har da cire gyalen data yale kanta dashi ta rufe fuskarta!
Murmushin gefen kunci sameer ya saki me cike da mugunta yace dad'in ta dai kin ji a jikinki don haka in kunne ya ji,toh gangar jiki ta tsira,yana kaiwa nan ya basar da ita ya shiga bin qira'arsa yana tuk'i!

Har suka isa garin minjibir beauty kwance take fuska rufe,gashi yana son tambayar ta inda zai shiga amma zuciya tak'i barinshi,can dai da yaga ba haza dole ya k'ara d'aka mata wani dukan,beauty dake kwance tunani duk ya gama cikata ta sak'a wancan ta kunce wance,tai firgigit ta d'ago fuska tana cire gyalen fuskarta,dilla malam ni kar ka sake duka na ai ba jaka bace,shiru yayi mata don yanzu bashi da lokacin biye mata haka,ina zamuyi?ya tambayeta kansa na kalon gaba,karkato hannunta tayi tana nuna masa kwanar data yanki gefensa cikin saurin yayi baya da jikinsa sameer can kuma ya kallota yace ke dilla ba sai kin kara kanki da ni ba da baki zaki min magana!wani abu taji ya kawo mata wuya beauty wai shin me ya dauke ta haka yake ta wulak'antata?kwanar yasha ya shiga tafiya a hankali don sun shigo gari baya so ya wuce wajen!tafiya suke tayi ba tare data k'arayi masa magana ba sai ma chewinggum data fito a jakarta ta jefa baki,ta shiga tauna, har sameer ya kai k'arshen titi beauty bata tanka masa ba,a k'ufule ya juyo don yaga babu wani sauran gida gma inda suke sai gonaki na mutane, yace ke wai ina zami yi ne kuma?kwai beauty ta sakar masa ji kake k'as-k'as sannan ta saki wani kasalallen murmushi tace inda waccen akuyar take nan zaka bi!waige sameer ya shiga yi amma sam wajen baiga wata alamar ko kaza a wajen ba balle akuya,lokaci d'aya ya fahimci beauty bak'ar magana ta yi masa,juyowa yayi a b'ace yaga ta k'ara sakar masa wani kwan k'ato,ai bai san sameer lokacin daya cafko hannunta ya murd'a shi da k'arfin tsiya ba,ihu sosai beauty ta saki har da d'aga k'afa d'aya sama bayan ido data zaro waje,ji kake tana cewa wallahi baya ne,kwanar da muka baro ne,waccan kwanar ce fa ta baya,amma ina sameer k'af yak'i kulata sai da yaga ta ji jiki sannan yayi wurgi da hannun ya juya kan motar suka dawo baya,rik'e take da hannun tana juya shi da haka tayi ta masa kwatance a nutse har suka isa k'ofar gidan nan tace toh ka tsaya haka mun zo!
[10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: *'YAR JAMI'A*

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

66-70



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*



Yi yayi sameer kamar ba ze amsata ba, sai kuma can ciki-ciki uwa mai gunguni yace toh!k'ok'arin bud'e k'ofa beauty ta shiga yi ta fita don taga alamar sameer bashi da niyyar fita, taji yace toh sai a kama kai nan dai gidan tsoho ne ba gala ba,wani miyau mai mugun zafi beauty ta had'e ta gyad'a kai ta fice abinta,kamar jira yake ta fito shima ya fito ya biyo bayanta, zauren gidan suka shiga tana gaba yana biye har suka cimma tsakar gidan sallama beauty tayi shiru ba motsin kowa sai data k'ara d'aga sautin nata fiye da wancan sannan ta ji daga can d'akin dake kallin kusruwar gidan wata dattijuwa ta amsa!
Wana ke ji kamar muryar jikalle?
Eh tsohuwa me ran k'arfe mune!
Toh! yagana ta fad'a tana yaye tsukakken labulen dake sak'ale a k'ofar tana fad'in lalle marhabun k'araso ciki!ta kai ayar maganar kenan kanta ya kai ga sameer wanda ke mak'ake bayan beauty!.
Auf ashe da bak'o kuke tare!hannu baba yagana takai saman katifar da ke shinfid'e tsakar d'akin ta janyo gyalenta ta yale akanta dashi sannan ta k'araso waje,cikin nutsuwa sameer ya tsugunna ya gaisheta ta amsa hannunta d'auke da tabarma!
Ashe ana ganin ku mutanen birni?cikin farin cikin ganinsu baba yagana ke jefo mata tambayar!

Hmm kaji baba ai yanzun ma wajen tsoho na zo ba ke ba!tana maganar yayin da take tallafamata wajen shinfid'ar tabarmar!
Yunk'urawa beauty tayi zata zauna baba yagana ta jefota da wani irin mugun kallo tace na bige ki anan guraren,ke zan wa shinfid'a ko siriki na?gafara can ki ba bak'ona waje ya zauna yau ta shi nake bake ba!"

Ba beauty ba hatta sameer se da maganar tayi masa mugun nauyi a kai!siriki kuma?nanata kalmar yayi cike da rashin fahimta,haka nan dai ya iya dai-daita nutsuwarsa ya nemi waje ya zaune,k'ara gaisawa sukayi nan kuma hira ta b'arke inda sameer ya ji komai game da raahin lafiyar tsoro dake can cikin k'uryar d'aki ya samu bacci!

"Gafara dai masu gida!e Muryar wani matashi kenan wanda a tsawo bai wuce na sameer ba ya shigo tsakar gidan rik'e da kekensa mai cike da damin harawa!
Baba yagana ce ta amsashi da gafara dai!tana kallon shi cike da nuna sanayya!
K'eeee.. suka ji ya saki keken k'asa ya shiga nuno su da yatsa yana fad'in kan uban can wazan gani zaune kamar hajjo?
Sororo hajjo tai tana kallonsa kamar zata iya tuno shi amma ina rashin zuwanta yasa ta kasa tuna shi!!

Ganin tayi shiru ya sashi k'arasowa ya nemi waje gefen sameer ya zauna nan ya mik'a mai hannu sukai musabaha sama-sama amma duk hankalinsa naga beauty,baba yagana ce ta katseshi da hannu tace kai wannan kallo haka d'an ladi kamar baka san taba?washe baki ya shiga yi yana kai hannu k'eya yana susawa yace"ai baba hajjon ce duk ta canja tayi fari tai gyau wallhi hala tana shan lemon birni(apple) ne?
dariya duk suka sa har da beauty!jim suka d'anyi da sigar shiru hakan ya baiwa sameer damar kai kallonsa ga bak'ar agogon dake sak'ale a hannunshi ya duba lokaci inda ya nuna 9:30a.m da sanyin jiki ya d'ago kai ya kalli baba dake jn gene da garu yace ina ganin baba yagana ya kamata a tashi tsoho haka yayi kumallo mu je asibiti ko? Don kar lokaci ya k'ure mana"baki sororo baba yagana ta bud'e baki hangam tabi sameer da kallo can kuma ta nisa tace kai d'an nan rufa min asiri ina yabon ka sallah kar ka kasa alwala mana,mu yanzu ina mu ina zuwa wani wajen asibiti kayan yahudu da nasara bakaji jami'an su ana kiransu likita bokan turai ba?wannan ai sai ka saka mu zama abin fae'e a yankin nan,toh bada niba wai shiga d'akin mayya!fad'a-fad'a,tsiwa-tsiwa haka baba yagana ke maganar kafin ta kai ga cigaba d'an lami yayi caraf ya karb'e maganar!
Ai dama wallahi baba ni nasan da walakin goro a miya tunda na yanko kwanar layin nan naga an kicciye mota gaban shagon sale me rake nasan cewa wa'adin tsoho yazo don na tabbatarda wannan d'an farin(nan ya nuna sameer da yatsa)uwa aljani ba haka nan yazo ba,toh wallahi ahir d'inka tsoho sai ya ga aure na don baza kai min haramiyar damun hatsin daya tanadar min ba yazama na magada!jin yarda d'an ladi ke ta zuro bayani ba ko tsagaitawa yasa beauty rai b'ace ta daka masa tsawa!

Kai dalla can kai wa mutane shiru,ashe kai har yanzu sokancin nan dai baka bar shiba?har kana wani d'aga wa mutane murya?toh bara kuji zuwa kamar anyi an gama"


Kin yi kad'an wallahi kin yi tsararo baki isa kizo cikin sanyin safiyar nan ki d'aga mana hankali ba,ko uwarki ina magana bata ja balle ke!
yau naga waze raba ni da d'an uwana"tana kaiwa nan a magana sai ta b'arke da wani irin kuka mai cike da k'ara baba yagana kenan, kai kace wani mugun abun akai mata!

Ganin yadda hayaniya ke tashi sosai ga kuka da baba ta saka yasa sameer matsowa kusa ita ya saisaita muryarshi k'asa-k'asa uwa mai rad'a ya shiga aikin lallashi! Da kyar baba yagana ta hak'ura ta tsagaita da kukan wanda lura da hakan ya baiwa sameer damar fara yi mata bayani!
[10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

71-75



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*


Ina so kisan wani abu baba mak'asudin zuwan mu gidan nan ba don komai bane illah mu nema wa tsoho lafiya,babu yadda za'ai muna ji muna gani mu kai shi inda zai wahala,tunda mu musulmai ne,bisani ma wannan jikarsa ce,maganar asibiti kuma da kika baba shekara nawa kuna zaune gida ana yin na hausa,wane sassak'e da mad'acin ne ba'a bashi yasha ba?ina ce duk an gwada amma jikin jiya i yau,kinga kuwa bazamu zuba ido ace haka za'a barshi cikin wahala ba dole a samu abin yi!kuma ina ganin son da zaki nuna wa tsoho shine ki barshi muje mu jarraba na baturen ko Allah yasa a dace!


Jimm baba yagana ta d'an yi uwa mai nazarin wani abu kowa ita yake jiran jin abinda zai fito daga bakinta,kwatsam suka fara jin k'uhul...k'uhul...k'uhul....alamun k'arar tari na tasowa daga d'akin dake gefensu,cikin sauri baba yagana ta mik'e suka rufa mata baya sukai cikin d'akin!
Kwance suka iske shi yana yunk'urin mik'ewa amma ba hali don wani matsanancin rawa da jikinsa ya soma va shiri sameer ya k'ara suka dashi bai jira cewar suba yadda yaga jikin tsoho na gyargyarwa ya sungume shi yayi yayi waje dashi,haka suka k'ara d'ungumowa gaba d'ayansu suka yo waje banda kuka da kururuwa babua binda baba yagana ke sumbud'awa"

Abakin k'ofar zaure ne suka ci karo da malam sale mai shago wanda kukan baba da ya jiyo yasashi shigowa ba shiri,ganin yadda aka fito da tsoho ranga-ranga yasa shi shima kwarma uban salati ya ja gefe ya tsaya,ba wanda ya iya bi ta kansa suka haura sukai waje,cikin aljihu sameer ya fiddo key ya mik'a wa beauty nan ta bud'e motar ,gidan baya sameer ya zauna shi da tsoho d'an ladi na k'ok'arin turo kai ciki ya dakatar dashi yace a'a ka zauna gida ka kula da baba yanzu zamu dawo,badan yaso ba haka d'an ladi ya ja gefe yayi turus!
Juyawar da sameer zai yi ne kicib'is suka had'a ido da beauty dake gefen baba tsaye hannu rike da mukullin mota"cikin tsawa ya furta mata" ke dalla malama ki shiga ki drivern namu kikai tsaye akan mu kamar sanda,ba ta bi ta maganar saba duba da yadda jikin tsoho ta tsananta ta nufi driver seat da sauri ta shiga ta kunna motar,ta nufi asibitin dake k'auyen!


Da idarsu asibitin waje beauty ta samu ta aje motar wanda har lokacin numfashin tsoho ya kasa dai-daito cikin sauri sameer a bud'e k'ofar ya d'akko tsoho suka fito beauty na take musu baya,cuncurundon jama'a kad'ai kake hangowa ta ko'ina acikin asibitin ga hayaniya na mutane duk inda ka juya mara lafiya ne zaune,abinka da ba'ai saba shiga waje haka ba kafin kace me duk sameer ya rikice ya rasa ina ma zai yi dashi,waje ya gano gefe da wata mata dake goye da yaro ba kowa cikin sauri ya isa wajen ya zaunar dashi juyowa yayi ya kalli beauty rai b'ace yace ki kula dashi ina zuwa kuma banda nuna hali!yana kai wa nan sameer ya sakai yayi gaba" sakayau beauty ta bishi da kallo fuska yamutse uwa mai shirin kuka ta shiga zancen zuci"toh wai shi wannan me ya d'auke ni akuya ko kuwa tunkiya da duk inda naje sai na bi maza?ba takai ga baiwa kanta ansa ba ta jiyo tarin tsoho ba shiri ta katse guntun tunaninta ta nufi wajensa ta na mai sannu!

Bai wani jima da tafiya ba sameer sai gashi ya dawo gefensa wani matashi da alama likitane sai wasu samari suma dai cikin fararen kaya dake nuna jami'an lafiya ne,ko da suka k'araso samarin nan cikin sauri da nuna gogewar aiki haka suka janyo gado a wani d'aki dake gefe damu suka d'aura tsoho suka nufi can wani sashen na asibitin,biye muke binsu har suka isa wani b'angare da hayaniya ta tsagaita a wajen,office dake ciki suka nufa muna k'ok'arin biyo su ciki likitan dake biye damu ya d'ago musu hannu badan sunso ba dole yasa suka dakata anan!

Waige sameer ya shiga yi ko ya samu wajen zama can ya hango wasu kujeru da basu wuce 4 a jere a k'arshe wajen ba take ya nufi wajen yazauna itako beauty ta shiga sintiri tana kai kawo a wajen!

Har kimanin minti 30 babu alamar motsi ko fitowa daga ciki! gajiya beauty tayi da zagayen dole ta nemi gefen wata window dake nan ta jingina tana kallace-kallacen jama'ar waje!
Can suka fara jiyo taku na tahowar mutum ido duk suka k'ura wa k'ofar sai gashi d'aya daga ciki samarin nan ya fito hannunsa d'auke da takarda!mik'ewa sameer yayi da sauri ya nufoshi inda itama beauty ta yo kansa tana fad'in dan Allah malama ya jikin nasa?bai iya tanka mata sai ma kallo da yakai ga sameer yace yallab'ai dr.ya rubuto allurai da ruwa da za'a siyo,karb'ar takardar sameer yayi k'ok'arin yi sai yaji yace dashi,a'a yallab'ai ai wannan aikin ba naka bane kadai bayar a siyo,lummm sameer ya d'anyi sai kuma can ya wuce gaba yace muje toh wajen!


tafiya suka shiga yi har sun kai k'ofar barin wajen sameer kamar wanda yayi mantuwa ya juyo ya kallo beauty wacce itama dai su take kallo yace toh sai ki samu waje gashi can ki zauna a bar lek'en taga don babu abin gani kuma dai a kama kai don nan gidan HIV ne,yana kaiwa nan yasa kai ya fice abinsa!beauty dake tsaye hannu sak'ale da k'aramar jakarta bata ankara ba taji wasu zafafan hawaye sun fara kwaranyo mata a fuska wanda sam batasan dalilin hakan ba!
[10:15am, 16/01/2017] Àúńţý jîđđĕřh: 📓 *'YAR JAMI'A*📓

_BY_*HERWWERH JIDDERH*
*A.K.A*
*PRINCESS QUE~DEE*

76-80



💕In Devotion to yuh my Dearies:


*ANEESA ABUBAKAR RIMI*
*(NEESAHLURV)*

&

*UMMEE ADNAN*
*(TAWAN)*



Kusan minti biyar kenan da fitar su sai gasu sun shigo rik'e sa ledoji biyu,office d'in saurayin ya shige shi ko sameer ya dawo nan ya nemi waje ya zauna!

Kawo lokacin beauty na zaune saman kujerar ta duk'e kai k'asa tana nazarin halin da tsoho ke ciki,
Sallama har sau biyu sameer yayi amma ina beauty tayi nisa a tunani"wasu dai anyi asarar kud'in tara wallahi ace sallamar ma basu iya amsawa ba"furucin da beauty kenan ta tsinta daga sameer hakan ya tabbatar mata da sun dawo don haka ta d'ago kai tana kallonsa"kafin daga bisani ta saki doguwar tsuka had'e da tab'e baki ta d'aura k'afa d'aya kan d'aya ta juya masa gyeya! Dariyar k'arfin hali sameer ya saki mai cike da tuhuma sannan ya furzar da wani zazzafan iska waje yace"Wato in aka ce dai akuya wallahi an gama da kai,don kuwa ita ko ina sai ta nuna halinta sai dai in bata samu waje ba! Bai kai ga sauke lumfashinsa ba kamar wacce aka mintsina beauty ta juyo a kufule ta shiga gyad'a masa hannu taba magana"kai malam shiru-shiru fa ba tsoro bane gudun magana ne,ko dan kaga tun d'azu ina raga maka shiyasa kake ganin kai ka isa,toh wallahi ina yi maka kashedi na k'arshe ka fita a harkata tun kafin na nuna maka kaina a zahiri"
A razane sameer ya mik'e tsaye ya dafe k'irje had'e da fad'in wa iyazu billahi yanzu banda wannan munanan ayyukan da kika shahara dau kina so kice min har akwai wasu na xahiri?ehh toh lallai ke tashin shuri ce don daga gani bade rainon mutim basai dai aljani!

Ganin yadda sameer ya samu damar ci gaba da gaya mata magana son ransa yasa itama ta mik'e tsaye ta shiga jijjiga jiki uwa mai shirin dambe kana tace na lura kana wasa dani ko?da sigar ko in kula sameer ya bata amsa da,ni kuwa yaushe zanyi wasa da wacce tayi ikrarin kiran kanta da sunan 'Yar jami'a ai ban isa ba tunda ban tab'a bin wani malami tsoho mai nauyin shekaru ya prof KAS na buk'aci b'ata masa mutunci ba,ban kuma tab'a nuna tsiraici na afili don samun distinction ba kin ga kuwa baxan tab'a had'a kanki da ni ba!

Hucin da beauty ke fitarwa kad'ai zai zayyanar dakai irin halin da take ciki na k'unar rai na lura da duk wata gab'a da tabi don taga ta d'au fansa sameer ya kasa bata wannan damar! Awulak'anceta watsa masa wani mugun kallo had'e da sakin wani mugun zagi ta koma ta nemi waje ta zauna jiki ba kwari"abubuwa kala-kala ta shiga sak'awa a zuci ganin yadda ko da sau d'aya zatai nasara akan sameer amma nazarinta ya kasa bata,dole haka ta hak'ura na lokacin ba don ta janye k'udurinta arai ba dai don ta gama da jinyar tsoho tukunna!
shi ko sameer lura da yadda ta yi lagwas yayi don haka ya shiga murmushin mugunta ala dole ya iya furta hmm kad'an kika gani yarinya in dai kin ce ke 'yar jami'a ce toh mu masu gyara jami'a ne kuma dole ki ladabtu ko kin k'i ko ki so!daga haka shima ya nemi can nesa da ita ya zauna tare da janyo waya a aljihunsa ya shiga yin game na zima revenge ko ya samu sauk'in rai!

Haka sukai zaune har wajen azahar kafin nan dr ya fito hannunsa rik'e da wani abin kwajin numfashi ya nufosu,ko da sameer ya hangoshi tashi yayi fuska a sake ya nufi wajensa yana fad'in dr. Ya jikin nasa?murmushin k'arfin hali ya saki kafin nan yace c'mon down prince ba wani abu ne na tada hankali ba jimawa da yayi a gida ba tare da an kawo shi asibiti ba shiya haddasa masa hawan jini amma yanzu cikin ikon Allah mun samu munyi controlling nasa sai dai tarin da yake ne wannan sai a hankali kuma ana shan magunguna,yanzu haka yana ciki ya samu sauk'i sosai don nayi masa allurar bacci zaku iya shiga ku ganshi in har jikin naga ba matsala zuwa yamma kafin na tashi a aiki na sallame ku!

Amsa masa sameer yayi da toh sannan ya k'ara gode masa da namijin k'ok'arin da yayi yabar duk wani aiki nasa yayi nasu!musabaha suka yi kafin ya basu izinin shiga ciki shiko ya wuce waje,jami'an lafiyar da suke tare suka mara masa baya!

Duk bayanin dr. a kunnen beauty ake yi duk da tana can zaune amma hankalinta na kansu haka bata jira cewar sameer ba duk da tasan ba wani abu zai ce mata

Please Login or Register in order to submit comment